حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 38.*
^^^^^^^^
*#Verdict*
Tafiya suke cikin gidan hannunsu sak'ale dana juna,sai dai fuskokinsu kad'ai zai iya bayyana ma mutum bawai suna cikin yanayin jin dad'i bane,lokacin da suka k'araso apartment d'in Hajiya kai tsaye da sallama suka shiga,zaune suka iske maimartaba,Abba Galadima da su Ummi sai YASEER dake zaune shima a kusa da k'afafun maimartaba daga k'asa,cikin sanyin jiki suka isa suka nemi gurin zama suna sake gaida iyayen nasu,,,yanayin yadda suke amsawa nan take ya tabbatarwa ransa da sun riga sun samu labarin abunda ya faru,dan haka kansa ya sauke k'asa yana mai sauraren jin abunda zai fito daga gare su,Abba Galadima ne yayi gyaran murya sannan ya kalleshi yana cewa
"YAZEED..! Shin abunda d'an uwanka ya sanar damu game da wannan case d'in haka yake..??"
Kasa magana yayi dan shi kam baima san ta inda zai fara amsa tambayar ba,shirun da yayi yasa Abban sake maimaita masa buh still bai yi attempt na amsawa ba har lokacin sai da YASEER ya tab'a shi sannan ya d'an d'ago kai yana sakin numfashi
"Ehh Abba haka masu laifin suka yi bayani.."
Kowa jinjina lamarin yake a ransa da tsantsar mamaki,sun d'auki wasu mintuna duka parlor'n yayi shiru babu wanda yake iya magana a ciki,suna wannan halin muryan Hajiya ta dawo dasu duniyar su ta ainihi
"To me ake jira kuma..?? Tunda an tabbatar da wad'anda suka aikata ai sai a hukunta su dai² da abunda suka aikata..! Ina amfanin zama da mutane irin wad'annan,sune fa suke gurb'ata al'ummah,matuk'ar ace za suyi laifi baza'a musu hukunci ba tofa alfasha ce zata ci gaba da yawo a ban k'asa,saboda haka Aliyu kayi magana S.P aje a kamo su kawai a yanke musu hukuci.."
Cikin fushi take maganar wanda dukansu babu wanda zancen bai bashi mamaki ba,musamman ma shi Yarima da yake ganin kamar itane zata hana masa hukunta azzaluman biyu,fuskarsa d'auke da wasu irin expressions masu wuyar rarrabewa ya maida kallonsa kan Hajiya'n yana mata kallon tsantsar mamaki,a nan kuma muryan Maimartaba ta sake kwato tunanin Yarima YAZEED d'in zuwa gare shi
"Hajiya da fari dai ina ganin ya kamata ace kafin mu zartar da hukunci,mu basu damar da zasu gyara KUSKUREN su,yin hukunci farat d'aya a irin wannan lokacin kuma ga mutanen da duniya ta shaida muna da alak'a da su kamar zai zame mana disgrace,buh ba wai ina magana ne akan kada a hukunta sun ba,amma ya kamata mu sake yin bincike mukuma zauna da su muji mene ne dalilin aikata hakan ga d'an su idan an tabbatar suna da laifi shi kenan sai a hukunta su kamar yadda Shari'a ta tanada.."
"Zancen banza ma kenan kake yi d'an Abdu..Bayan mun riga mun fahimci wad'anda suka aikata laifin,sannan mun samu shaida daga bakin wad'anda aka sa mene ne kuma na jira..?? Ta yaya zamu yita tsaiwa muna basu wani damar gyara KUSKURE..?? Wane KUSKUREN ne zasu gyara d'in..?? Kawai sai muyi ta kyale su muna zuba musu ido a kan zasu gyara²..?? Wannan fa zato ne muke yi musu bawai muna da tabbacin zasu gyara ba,,,,idan har kai kana tunanin zaka ci gaba da tsaiwa da niuyar barinsu ne ko kuma kace ka yafe musu,ni nan da sauran wad'annan yaran da suke zaune zamu had'a kai ne wajen k'in yi musu afuwa,mu baza muyi ta zuba ido kamar yadda kake tunanin yiba,,,fisabilillahi har zuwa yaushe ne za'a samawa yaron nan adalci..?? Ko kuwa kai naka KUNDIN SARAUTAR ya fad'a maka kayi haka..?? Shin wannan shi ne irin adalcinka ga talakawan naka da kake fad'a.??"
Shiru duka parlor'n ya d'auka sai muryanta kad'ai ke tashi tana magana cikin zafi dan yadda lamarin ya matuk'ar b'ata mata rai,sai da ta yiwa Maimartaba fad'a sosai yayin da gaba d'aya su kuma suka sauke kawuna k'asa dan jin yadda Hajiya ta d'auki d'umi akan lamarin,sai data gama fad'an sannan ta juyo kan Yarima tana cewa
"Kai YAZEEDU maza ka kiramin S.P nace,,ina son ka sanar da shi sak'o na yanzun ba sai sun b'ata lokaci ba ina son su kamo min Adda da Suwaiba su gurfanar da su a gaban hukuma...!"
Yadda tayi maganar babu wasa yasa shi d'an tsayawa kallonta kad'an sannan ya juya ya kalli maimartaba,fuskarsa na bayyanar da y'ar damuwa sannan cikin wani irin murya ya d'auke kai yana sake kallon Hajiya da cewa
"Am sorry Hajiya.. Buh kamar yadda Abiiy yayi maganar ya kamata mu fara bin hanyar daya ce d'in,,,idan har munyi binciken zamu gano komai cikin sauk'i,sannan idan suna da rabon gane KUSKUREN su zasu gyara,,,if not kuma shi kenan sai ayi musu hukuncin daya dace.."
Had'e rai ta kuma yi tana kallonsa cike da takaicinsa shima
"Wato kaima saboda ka nuna min ban isa ba shi yasa zaka zab'i maganar mahaifinka akan nawa..?? Shi kenan kuyi duk yadda kuka so,ni ba zan sake sa muku baki a maganar ba,kuma dama ni ba don komai nayi wannan maganar ba sai don ina son a sama maka adalci kan zaluncin da ake yi maka,,,amma tunda kun nuna bakwa son maganata a ciki shi kenan kuyi duk yadda kuka so..."
"Dan Allah Hajiya kiyi hak'uri,,sannan ki fahimci dalilin da yasa nayi magana,duka fa ba abunda nake nufi ba kenan..Abunda kika fad'a gaskiya ne,amma shima Abiiy ya fad'i gaskiya,,duk da masu laifin sun ambaci sunan su hakan ba shi ne yake nuni da cewar sun aikata ba,kuma muma ba shi ne dalilin da zamu kama mu rik'e ba,zai iya yiwuwa su da suka ambaci sunansu sunyi hakane dan ya kasance akwai sa hannun nasu a ciki,zai kuma iya yiwuwa sab'anin haka,,buh idan duk muka tsaya akayi bincike mu da kanmu zamu fahimci gaskiyar da muke nema..!"
"Kai ni rufamin baki da wannan maganar taku..ni kuma me zan sake cewa bayan kun watsamin k'asa a ido..kuyi dukma yadda kuke ganin yayi muku.. Allah ya bada sa'a.."
Duk yadda yaso yayiwa Hajiya bayanin manufarsa akan lamarin k'in amincewa tayi da zancen sa,yayin da su kuma a b'angaren iyayen nasu duka a yadda yake jawabi suka fahimci abunda yake son nunawa Hajiya'n sai dai tak'i sauraronsa,haka su d'in ma koda suka gano nufin nasa babu wanda ya iya bayyana hakan a zahiri,dan gudun kada su janyo tayi fushi tace suma d'in sun goyi bayan maimartaba da Yariman,k'us² suka d'anyi tsakaninsa da YASEER a zaunen da suke ba tare da kowa ya fahimci hakan ba sannan yayi taking excuse ya fice,yana fita a harabar apartment d'in ya d'an tsaya yana fito da d'aya daga cikin wayoyinsa dake tare da shi,bai wani jima ba ya kira A.S.P Hood,cikin y'an mintuna da basu wuce uku ba ya shaida masa yanzun su taho masa da masu laifin dake hannunsu,,,suna gama waya da shi ya shiga k'ok'arin kiran Abba Matawalle,ko daya d'auka muryan Yarima da wani irin yanayi a tattare da ita mai wahalar ganowa ya bayan sun gama gaisawa sai ya shiga yi masa magana cewa
"Abba dama wani d'an matsala ne aka samu,,to kuma ana buk'atar ku a gida shi ne aka ce na kira na shaida maka.."
Cikin rashin jin dad'in yanayin da Yariman yake maganar yasa Abban tambayar sa dan ya fahimci akwai gagarumar matsala
"Ina fatan ba wani gagarumin abune ya faru ba ko..?"
"A'a Abba nima dai abunda kad'ai akace na sanar da kai kenan,,idan da hali har Hajiya Ummah duka kuna iya tahowa.."
Jin haka ya sake tabbatarwa Abban lallai koma mene ne yake shirin faruwa a masarautar ba k'aramin AL'AMARI bane da har zaisa a neme su cikin gaggawa haka,dan haka kai tsaye shima d'in yayi taking excuse a gurin bak'in dake tare da shi yayi cikin gidan da nufin sanarma Hajiya Suwaiba sak'on daya zo daga masarauta.
A gefen Yarima kuwa ko daya gama shaidawa Abba matawalle sak'on da yake son isarwa nan ya fara neman line Adda wanda ba k'amin mamakin nayi ba akan yadda akayi ya samu number nata,murya cike da walwala danma kada ta gano dalilin kiran,saboda yasan Adda da shegen wayo,sai yasa bai mata magana da irin muryar da yayi magana da Abba Matawalle ba,bayan sun gaisa da ita ya shiga nuna mata kamar wani abun jin dad'i ne yake kan faruwaa a masarauta dan haka ne ake nemansu da sauri yanzun,zuciyarta babu dad'i ta amsa masa,dan ita Adda sam a wannan lokacin bata fatan taga zuri'ar Hajiya a cikin walwala,da wannan yanayin Adda'n da ahalinta suka rankayo suma zuwa masarautar tana mai bak'in cikin koma mene ne yake faruwa d'in da bai kasance akansu ba,within a few minutes dayin magana da su duka su Adda'n har ma da Abba Matawalle duk suka iso gidan,a parlor'n Hajiya suka iske su nan suma kowanne ya nemi guri ya zauna,kasancewar case d'in na gida shi yasa basu yi tunanin kai lamarin fada ba aka zauna dan a warwarwe shi a gidan,y'an gaishe² da baza'a rasa ba suka yi da juna,wanda kafin a k'are sai da Hajiya ta kusa tona halin da ake ciki dan yadda ta dunga amsa musu a dak'ile,Abba Galadima ne yayi magana da ayi shiru haka nan ya kamata su bada had'in kai ayi abunda ya kamata,ko da parlor'n ya d'auki shiru nan ya juya ga Abba Matawalle yana tambaya
"Matawalle shin ko ka samu labarin abunda ya faru da gidan nan a safiyar yau...??"
Da mamaki Abba'n ya kalli Abba Galadima yana amsawa
"Ko kad'an banji wani labari daya danganci gidan nan ba,,shin wani abu ya faru nema da akayi irin wannan kiran cikin gaggawa..??"
Shima ya k'arasa maganar ta hanyar mayarwa da Abba Galadima da tambaya,jinjina kai yayi yana cewa
"Kayi hak'uri tukun zaka ji koma mene ne ya faru yanzun,amma bari muji b'angaren su Adda ko sun samu wani labarin.."
Tunma bai gama maganar ba Adda tayi saurin fad'in
"To ni Aliyu da nake gabas da gari ta yaya zan samu wani labari ne..?? Kawai ku shaida mana abunda yake faruwa a wuce gurin,ba wai mu tsaya maimaita abunda ya riga ya wuce ba.."
Duka parlor'n idanunsu akanta dan jin yadda take magana cike da izza kamar itace shugabarsu duka,babu wanda ya tanka mata a ciki saboda sun fahimci akwai abunda take ji da shi,magana Abba'n yaci gaba dayi yana cewa
"Alal hak'ik'a kamar yadda kuka sani ne cewa ba'a cika yin irin wannan kiran ba,haka nan cikin gaggawa ace an tashi meeting ana neman mutane a cikin k'ank'anin lokaci,kowa ya sani a mafi yawan lokuta ba k'aramin abu bane yake sawa ayi hakan,amma saboda wasu dalilai da nake da su,baza kuji faruwar komai a bakina ba.."
Yana fad'in haka ya juya ga YASEER yana cewa
"YASEER maza kayi musu bayanin abunda ya faru.."
Duka idanuwansu nan suka yi luu zuwa kansa,musamman ma su da suka zo yanzun,cike da dakewa shima YASEER d'in yana kallonsu cikin tsakar ka,bayan ya amsawa Abba'n nasa sannan ya shiga kwararo jawabai game da matsalolin da aka samu d'in kamar yadda Abba'n yayi masa umarni,tiryan² ya zayyana musu komai sai dai ya b'oye batun kama au JIBO da akayi,tun kafin ya kai aya nan itama Hajiya Suwaiba tayi tsalle tana kumfar baki
"Wollahi k'arya ake yimin,,,idan har ba anso ayimin K'azafi ba ta ina za'a k'ullamin wannan k'ullaliyar..?? Ina ni ina sabgogin gidan nan ma da za'ayi k'ok'arin saka ni cikin wannan k'ungurmin laifin..?? A'a ku dai kwa nemo wanda yake dasa hannu a ciki Amma ba ni Suwaiba ba.."
Mugayen kallo Abba Matawalle yake aika mata da su amma duk da ta kula da shi d'in hakan bai sa ta yin shiru ba,ga Adda kuwa jinjina kai kawai take tana kallon mutanen gurin fuskarta a d'aure tamkar bata tab'a sanin kowa a gurin ba,lokacin da Hajiya Suwaiba tayi shiru nan itama ta samu bakin magana
"A'a'a..! Hauwa kawai cemin za'ayi wannan taron cin zarafinmu ne aka tara,,,idan ba haka ba yanzun fisabilillah aa zaunar damu sannan azo ana tuhumar mu da aikata irin wannan laifin..?? Ta yaya mu da bama cikin gidan za muyi k'ok'arin aikata hakan..??"
"Ya isa haka nan AISHA..! Wannan duk boron kunya ne kike yi."
Muryan Hajiya ta ambata cikin fushi,ba Adda kawai ba hatta da duka ahalin wajen sai da duk suka juya suka kalleta dan mamakin yadda ta kira sunan Adda gatsau babu y'ar girmamawar data saba,baki bud'e itama Adda ta d'aga ido ta kalli Hajiya tana sake bud'e baki cike da tsantsar mamakinta
"Hauwa..! Yau ni kika kira da AISHA kai tsaye..?? Ehh! Lallai kam yanzun na tabbatar da abunda yake shirin faruwa..!"
Hajiya dai bata samu damar tanka mata ba,dan bata jin tana da lokacin Adda'n a halin yanzun,babban burinta shi ne ta samu a hukunta Adda bisa zaluncin ta,k'arar jiniya ta sanar da su isowar y'an sandan,wanda faruwar hakan yasa duka lamarin ya fara k'ok'arin sauyawa dan fir su Adda suka kafe kan basu san me akema magana akansa ba,Abba Matawalle kuwa tsantsar mamaki duk ya d'aure shi a inda yake a zaune dan ko kad'an shi a duka tarihin zamansa da Hajiya Suwaiba bai tab'a tsammanin hatsabibancin ta ya kai haka ba,,Maimartaba kuwa duk wad'annan zantuttukan da ake yi tun bayan zuwan su Adda bai sake yinbmagana ba har lokacin dan yadda yake gudun sake taso da fushin Hajiya,ya san matuk'ar aka ce ya sake yin magana akan a basu dama game da laifinsu zai iya fuskanci b'acin ranta,,,cike da takaici gami da zullumi dake shimfid'e bisa fuskar Abba Matawalle ya juya ya kallesu duka sannan ya mik'e tsaye yana Allah wadaran hali irin nasu Hajiya Suwaiba da Adda,wad'anda suka girma amma sun kasa sanin sun girman,saima k'ok'arin jefa rayuwarsa cikin bala'i da suke kan yi maimakon ace a shekarunsu sun koma ga Allah da neman gafarar zunubansu amma sai suka b'ige da aiki irin na jahilai kuma azzalumai,sai da yayi musu tas da kausasan maganganu sannan ya d'ora da fad'in
"Tabbas wannan *WANI AL'AMARI* ne daya kasance abun a duba,,,babu yadda za'ayi ace wad'anda aka kama sun ambaci sunan su a cikin wannan matsalar sannan ace wai k'arya aka yi musu..dole ne ya zama da akwai k'amshin gaskiya a ciki.."
Hajiya ya waiwaya ya kalla sannan ya furta
"Hajiya ina mai neman alfarma a gareku baki d'aya,sannan ina sake bada hak'uri bisa wannan matsala da aka samu,,,har ga Allah ban san da wannan matsalar ba,da tun farko ni da kaina na yiwa tufkar hanci,ni duk wani abu da yake faruwa walau a cikin gidana ko kuma a wani bigiren matuk'ar ya danganci mata ne bana saninsa saboda babu mai tarata ya fad'a min..Amma dan Allah Hajiya ina mai k'ara rok'on ku afuwa bisa sakacin dana gwada.."
Juyawa ya sake yi ga Maimartaba dasu Ummah Fulani duka suma ya sake basu hak'uri sannan ya juya ga Yarima yana fad'in
"Yarona..! Ina so ka kwantar da hankalinka,kada wannan abu daya faru yasa ka tada hankali,,a wancan lokacin daya gabata anyi maka *K'azafi* sannan aka janyo maka fuskantar hukunci ba tare da anyi bincike ba,,,saboda haka ni nan zan tabbatar da adalci ta hanyar hukunta duk wani mai hannu a cikin su kamar yadda sunansu ya fito a cikin case d'in,,da fari za muyi bincike mu tabbatar da gaskiya gudun kada mu sake aikata KUSKUREN da muka yi a baya,,,ina mai tabbatar maka cewa da zaran komai ya kammala zamu karb'ar maka hak'k'in ka akan duk wanda yayi k'ok'arin zaluntarka,,sannan ina k'ara kira gare mu,dukanmu ban ware kowa mu da muke zaune a wannan gurin dama wad'anda basa nan cewa,a duk lokacin da aka samu wasu sun aikata laifi ko suna shirin aikatawa,muna rok'on mutane babba da yaro da su taimaka su bada goyon baya,,a duk lokacin da aka samu wani ko wasu da laifi kuma aka samu wannan mutumin yana daga cikin makusanta ma'ana dangi da kada a mayar da maganar ta zama iya ta dangi a keb'e,,ya kamata a bari doka tayi aikinta akan koma waye aka samu da laifin.."
Fik'i² Hajiya Suwaiba suka fara da ido sai dai a wani gefen na zuk'atansu yana shaida musu kan cewa kada su tada hankulansu musamman tunda babu ta yadda za'ayi a gano su a cikin masu laifin,haka nan suna ganin tunda har sun riga da sun yiwa yaran nasu kashedin duk tambaya ko azabtarwar da za'ayi musu da kada su yi KUSKUREN nuna suna da alak'a da su,,,irin yadda Abba Matawalle yake magana azafafe a dai² lokacin yasa take suka fara shan jinin jikinsu dan aun fuskanci kamar yana yi musu GUGAR ZANA ne a cikin zance,,wanda k'afin suyi tunanin sake yin wani abu tuni har kowa yayi na'am da maganar ta Abba Matawallen,wanda kuma a dai² lokacin ne A.S.P Hood ya kira Yarima ya shaida masa sun iso,umarni ya bashi kan su shigo cikin gidan zaisa yanzun azo a taho dasu,yana gama maganar bai jira komai ba yasa wasu cikin bayin dake kula da apartment d'in da suje su taho da su,basu b'ata lokaci ba suka fice don cika umarnin da aka basun,mintuna goma suka d'auka da tafiyarsu da dawowarsi wanda suka dawo tare da rundunar y'an sandan dake dak'ume da su JIBO,har cikin parlor'n Hajiya aka shigo da su duka hannayensu a d'aure da handcuffs yayin da jikinsu kuma duk ya sauya kama saboda tsananin azabar da suka sha,tun daga shigowarsu kad'ai ya sake sawa su Hajiya Suwaiba tsoro gami da firgici,wanda take suka sake rikicewa dan sun tabbatar yanzun kam tasu ta gama k'arewa tunda har aka zo da su JIBO,,,su kuwa su JIBO ko da aka shigo da su basu yi k'asa a guiwa ba da akasa su mayar da zancen suka rattaba jawabin duk yadda aka yi,,zuwa lokacin jikin Hajiya Suwaiba banda keto da wani mahaukatan gumi babu abunda yake yi kan tsabar tashin hankalin data jefa rayuwarta wanda tunda tazo duniya bata tab'a cin karo da koda kwatankwacin shi ba sai a yau d'in,,,ga Adda kuwa sai aka samu bambanci dan kuwa duk da ganin su JIBO cikin wannan mugun yanayin ko kad'an bai sa hankalinta tashi ba,sannan duk da tana d'an jin yadda zuciyarta ke tsinkewa baisa tayi ko da gezau ba,dan tsabar taurin rai irin nata,,har zuwa lokacin da jawabai suka gama bayyana akan sa hannunta ita da Hajiya Suwaibar,nan gaba d'aya parlor'n ya d'auki surutai ta kowane b'angare kowa ya shiga furta albarkacin bakinsa,,bayan an d'an yi k'us² da shawara tsakanin manyan dake zaune wajen,ta inda wasu ke ganin ya kamata a d'auki case d'in a mik'a kotu,nan wasu kuma suke ganin a'a ya kamata dai kawai ace an yanke musu hukunci a nan saboda fita a tara mutane ko ajiye su duk b'ata lokaci zai zama,gara ayi komai a tak'aice a dank'a su hannun jami'an tsaro suyi gaba da su,,,an jima sosai ana tak'addama akan shawaran kafin a samu matsaya kan zartar da hukuncin a take,umarni aka yiwa Abba Matawalle daya zartar da hukunci kamar yadda ya fito daga bakin maimartaba,nanfa Abba Matawalle ya sake tashi yana mai binsu Adda da wani irin kallon na tir da halayensu fuskarsa cike da zallar gaskiya da son yanke hukunci ba tare da nuna sanyaya ba a tsakaninsa da su Adda,sannan ya shiga rattabo jawabi kan irin hukuncin daya kamace su daga su har mabiyansu a shari'ance kamar haka
"Kamar yadda muka tabbatar da amsawar laifi daga wad'anda suka aikata,,koda ma ace ba dukan su ne suka amsa d'in ba,dole ne mu tunda mun tabbatar ta hanyar bincike da kuma nazari mu zartar da hukunci akansu kamar yadda shari'a tayi umarni,,,bisa ga bangaren doka na Penal Code data tanada a zamanin gwamnatin arewa,wacce Alhaji sir Ahmadu Bello ya jagoranta a yayin kafa ta wanda ya wakana tun a shekarar 1963,,a bisa k'ark'ashin sashi na d'ari biyu da saba'in da hud'u na dokar,yayi tanadin kisa ga duk wad'anda suka kashe mutumin da suka yi garkuwa dashi,,ko kuma suka kashe wani a lokacin da suke k'ok'arin sace wani,,sannan kamar yadda dokar sashi na d'ari biyu da saba'in da uku shima yayi bayani,yayi tanadin rai akan rai ga ga duk masu satar mutane sannan suka nemi kud'in fansa.Wanda a k'ark'ashin kashi na biyu na dokar shi kuma ya bayyana mana cewa za'a yankewa mai laifin zaman kurkuku na ak'alla shekaru goma sha biyar ne tare da tarar naira dubu d'ari biyu da hamsin #250,000 ga wad'anda suka sace mutum ko suka yi garkuwa da shi,,bisa adalci irin na wannan kotu mai albarka,kamar yadda ta bibiyi wannan case da kuma tabbatar da duk abubuwan da suka faru gabanin afkuwar laifin,,sannan kamar yadda muka tabbatar da cewarr ba'a samu asarar rai ba a yayin musayar wuta daya b'arke tsakanin jami'an tsaro da y'an ta'addan wannan kotu mai alfarma ta zartar da hukuncin.................."
#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 39.*
^^^^^^^^
*#A hidden truth*
D'an shiru Abba Matawalle yayi yana kallon yadda duk suka zuba masa idanu suna jiran suji irin hukuncin da zai zartar akan su Adda,ko daya juya kan Hajiya Suwaiba yaga idanunta sunyi wani irin jaa cike da tsantsar fargabar hukuncin da zai biyo baya a hankali ya janye kansa daga gareta yana mai watsa mata wasu awful looks sannan yaci gaba da bayani kamar yadda ya fara
"Bisa adalci irin na wannan kotu mai alfarma,take shaida muku cewa zata zartar da hukunci kamar haka,,ga wad'anda aka samesu suna k'ok'arin sace mutum,amma Allah bai basu nasara ba,wanda mun tabbatar cewa da ace sun samu dama zasu iya tafiya da wanda suka zo satar,wannan kotu ta yanke hukuncin a tsare su a gidan kaso har na tsawon ak'alla shekaru bakwai tare da horo mai tsanani na ak'alla watanni biyar,,sannan bisa irin barazana da suka yi na kisa a yayin da suke yunk'urin aiwatar da laifin wannan kotu ta zartar musu da biyan tara na zunzurutun kud'i da suka kai ak'alla naira dubu d'ari biyu da hamsin akan kowane mutum daga cikinsu,,,sannan hukunci akan wad'anda suka sa ayi aikin,kotu ta zartar musu da hukuncin d'auri tare da horo na ak'alla shekaru takwas
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 55 Chapter of 63