birkice sun cika taf da hawaye ta kalleshi tana son yin magana amma ta kasa saboda azabar ciwon dake nuk'urk'usarta..
Can a gida kuwa sam babu wanda yasan halin da ake ciki,har sai bayan fitarsu ne da aka samu wani cikin amintattun bayin gidan ya bi bayansu yaga inda suka nufa ya dawo gidan cikin azama,apartment d'in Ummi ya nufa kai tsaye sanda ya dawo d'in nan ya shaida mata abunda ke faruwa,salati ta shiga jerawa dan sosai taga wautar Yarima da har ya kasa sanarma kowa ya tattarata daga shi sai ita suka tafi hospital haihuwa,ita tayi k'ok'arin sanarma Umma'nsa da Hajiya sannan ta sanar da Abba Galadima,izinin zuwa asibitin yayi mata sannan ya shaida mata shima suna hanyan dawowa gidan kasancewar sunyi tafiya a lokacin shida maimartaba,cikin abunda bai wuce mintuna ashirinba motocin masarauta suka shiga jeren gwano akan titi daga nan har hospital d'in da suke,nan suka fara jeruwa a cikin harabar asibitin kan kace me tuni dogarai har sun kafa sun tsare ko ina ka duba sune birjik sansani²,Ummi ce kad'ai ta samu damar zuwa a tare da ita akwai bayin b'angarenta mata ak'alla su goma,kai tsaye bakin labour room d'in da take ciki ita d'aya suka nufa,wanda izuwa lokacin ta gama galabaita dan yadda kuzarinta duk ya gaza,ruwan nak'udan ma da aka sa mata dasu tablet d'in duka shima yak'i mata,yi ake amma abu yak'i kamar ba yi ake ba,fitowa Dr Zainab tayi tana share gumi a tare da ita akwai nurse d'aya suna tafiya while sauran har lokacin suna tsaye kan Jeeddah suna sake jarrabawa,office d'inta suka wuce kai tsaye nan Ummi da tawagarta suka rufa musu baya dan jin inda aka haihu a ragaya,kasancewar Ummi babbar mace mai cike da nutsuwa shi yasa tafi Yarima fahimtar bayanin nata,nan ta sanar da ita haihuwa babu labari kuma tana tsaka da shan wahala dan a lokacin kuzarinta da duk wani k'arfinta da ake tunanin zai tamaka mata ya soma yin k'asa,nan ne hankalin Ummi yayi matuk'ar tashi har ta nemi da taga halin da take ciki,babu musu Dr Zainab ta wuce gaba inda Ummi da tawagarta suka dafa mata daga nan har d'akin da Jeeddah take tana ta fama har lokacin............
_Dominku kad'ai yasa nayi k'ok'arin sake typing,coz bana son abun yayiwa Yarima yawa,kowa ya tashi magana *YARIMA* tunda naga har kun fara jin haushinsa..😢 gara na warware muku dalilin..Hope yanzun zaku gamsu.😌_
#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 26.*
^^^^^^^^
*#Enjoined*
Wahala kam Jeeddah tana kan shanta,tunda aka shiga da ita abu d'aya aketa maimautawa amma haihuwa shiru,dan haka Ummi ta yanke shawaran yin magana da Abba Galadima ko za'a samu mafita,da a barta taita wahalan gara ko CS ne ayi a cire abunda ke cikintan tunda idan an barta ba'a san ranar saukarta ba,hakan ne ta faru nan take ta kira shi,bayan sun gama waya da Abba Galadima tayi k'ok'arin yin magana da Dr Zainab akan suyi mata aiki a fitar da abunda ke cikin nata,ko da Yarima yaji sak'on Abba a matuk'ar tsorace ya kalli Ummi
"Ummi Pleasee..! Amma dai ba wannan sha² ne zasu yankata ba..??"
Wani kallo Ummi ta masa daya sashi saurin sunkuyar da kai
"Idan an bari kai zaka mata..??"
Shiru yayi yana sake sunkuyar da kai k'asa
"Wuce ni muje kayi signing a shiga da ita,kada lokaci yayi ta tafiya ba'a nemi yadda za'ayi ba..!"
Tabbas ba don Ummi na nan ba a gurin tofa yau kam da zai iya cewa bai ga mahalukin da zaisa baki akan ya kyale wannan likitar da bata san mene take yiba ta duba masa mata,direct office d'in babban likitan ya nufa bayan fitarsa a d'akin dan ya lashi takobin babu abunda zaisa Dr Zainab ta sake yiwa KHUSHI d'insa koda dannar ciki bare kuma akaiga yankawa,a nan yayi masa bayanin yadda yake so ayi duk da bawai yana tare da nutsuwarsa bane likitan ya amsa masa cike da girmamawa,tare suka fito zuwa ward d'in da suke nan aka shiga shiryata cikin kayan tiyatan,dai² ana shirin fita da ita a room d'in ta d'an mirgina kai tana kallonshi idanunta cike da hawaye har lokacin wasu na expelling wasu,cikin dasashiyar muryanta ta holding hannunsa cikin nata,a hankali ya d'ora palms d'insa d'ayan saman kanta sannan ya gangaro da shi zuwa saman fuskarta yana scrubbing mata tears dake sauka a chicks d'inta
"Don't cry KHUSHI ok..u will be fine in sha Allah..!"
Cikin k'arfin hali ta d'an sakin masa murmushi tana jan ajiyar zuciya
"It's unsupported except what Allah predestined..Idan rabb yayi bazan sake motsawa ba,please ka rok'amin gafaran kowa dana sani dama wanda ban sani ba,wanda na tab'a yima laifi cikin sani ko rashin sani,ina ji a jikina kamar bazan sake motsawa ba...idan rabb ya nufa na haihu ko abunda ke cikina ya rayu a lokacin da k'asa ya rufemin ido,ina son kamin alfarma a kai shi gurin Inno..."
Sai data ja numfashi tana sake sakin wasu hawaye masu zafi kafin taci gaba
"Abunda nayi maka tun daga farkon alak'armu,ina sani ko bana sani,ina rok'on afuwarka,mijina ka yafemin..ni dai nasan babu wanda ya b'atamin idan kuma har akwai to ina so ka shaida musu na yafe musu duka..fatan Allah ya sada mu da alkhairinsa...!"
Zuwa lokacin tuni kalamanta sun gama sanyaya masa guiwowi cikin wani irin commotions yake kallonta,duk da irin dauriya ta namiji data bambanta da mata amma a lokacin sai ga hawaye a idanunsa suna derby,daga gefen fuskarta yasa tashi hawayensa naci gaba da sauka babu k'ak'k'autawa,cikin rashin kuzari ta shiga k'ok'arin raising hannunta d'ayan,a saman curly hair d'insa ta azasu kadin ta shiga caressing masa su har zuwa spine d'insa,yana hawaye itama tana taya shi har sanda lokacin shiga da ita ya gabato,nan fa drama ta b'alle Yarima ya kafa ya tsare yace Allah ya karshi sai dai a shiga da shi duk abunda za'ayi sai dai ayi akan idanunsa,dai² lokacin da ake wannan tak'addamar su YASEER suka k'araso coz basu samu labarin abunda ke faruwa da wuri ba,nan asibitin ya dad'a cika ko ina ka wulga idanunka ahalin masarauta ne musamman ma bayin gidan,da kyar aka samu aka sha kansa shima dan Ummi ta sa baki ne shi yasa babu yadda zai yi ya hak'ura,nan aka fito da ita a kan gado ana turata zuwa theatre room,babu wanda bata bawa tausayi ba a gurin ga masu saurin kuka kuwa tuni suka fara mata hawaye,ABEELA da Abir kuwa kuka suke kamar mance musu ta rasu,jikin kowacce ya sake yin sanyi da lamarin,murmushin k'arfin hali tayi musu amma gare su kam duk sun kasa su iya mayar mata,har aka shiga da ita idanunta na kan Yarima,dai² nan ABEELA ta kalli YASEER dake aikin rarrashinta tana cewa
"Gaskiya indai haka zan sha wahala bana sake haihuwa..dubi fa yadda duk ta koma..!"
Rungumeta da yayi shi ne dalilin da yasa kalmominta datsewa,a hankali yake caressing bayanta,sun d'auki lokaci a haka kafin ya samu tayi shiru sai ajiyar zuciya take,Abir kuwa tana jikin Ummi ta lafe kamar mage itama dai nan a ranta lissafawa take matuk'ar akace haka kowace mace ke fama to ita ko aurenma ta hak'ura basai tayi ba.
Ummi kuwa tunda aka shiga da ita babu abunda bakinta keyi sama da addu'ar Allah yasa ayi aikin lafiya,yadda ta gantan nan ko ita ta sake tsinkewa da lamarin,sai dai kuma muna tamu ne ubangiji na nashi,wanda nasan shi ne dai².
*THEATRE ROOM...*
Can a cikin theatre room kuwa bayan an shiga da ita an gama shirya komai,aiki kad'ai ya rage a mata kamar yadda tun farko aka shigo da ita da wannan niyyara,cikin hukunci na ubangiji dai² lokacin sai ga ciwo ya dad'a tasota gadan²,yi take kamar baza ta rayu ba,ganin haka ne yasa likitan dake kanta a lokacin da nurses matsowa kusa dan gabatar da abunda ya shigo da su,handgrip ne a hannunsu duka da face mask d'akin yayi duhu sai iya lampshades na sama dake haska musu ita,Dr na niyyan ansar wuk'ar fid'a,ta saki wani remotely groan tana sake persist,dakatawa likitan yayi da abunda yake niyyan yi yana sake dubata,cikin azama yayi ma nurses d'in umarnin su maida ita kan wancan gadon,within a few minutes da maidata sai ga kan jariri ya fara appearing,gaba d'aya babu wanda baiyi mamakin abunda yake shirin faruwa ba,buh duk da haka sun tabbatar da cewa komai yin Allah ne shi kad'ai,taimakon daya kamata suka fara k'ok'arin bata domin har lokacin babu wadataccen k'arfin daya kamata a tare da ita,cikin hukuncin rabb sannan da taimakon Dr kan jaririn ya fito dan haka suka k'arasa taimaka mata aka zaro shi,ajiyar numfashi ta shiga yi nan su kuma nurses d'in wata ta karb'i jaririn tana k'ok'arin gyarawa bayan Dr ya yanke masa cibi,sai dai abunda ya d'aure musu kai duk k'ok'arin su a time d'in shi ne mabiyiyar tak'i fad'owa nanfa hankali ya kasu ana ta so a zaro amma abu yaci tura,sun sake shafe wasu y'an mintuna,gadan² kuma sai ciwo ya sake turnuk'eta yi take kamar zata shek'a mintuna ak'alla kusan ashirin sai ga mabiyiya ta fad'o,hamdala suka yi a tare sannan aka ci gaba da k'ok'arin gyara ta,sanda aka gama kimtsasu allurai gami da k'arin ruwa Dr ya jona mata dan ta samu isashen hutun daya kamata,daga nan aka gangaro su zuwa ward.
Idanun Yarima tunda aka shiga da ita suke a kan k'ofar room d'in,idan akace yana blinking nasu a wannan lokacin nasan da yawa zasu k'aryata afkuwar hakan dan yadda ya kafe gurin da ido,ko zama ya gagara yi sai safa da marwa yake a varenda d'in,ana fito da su already idonsa yana a gurin,nan take yayi zaraf yana nufan su tunma basu k'araso ba,yadda ya hangota kwance a saman gadon kamar matacciya shi ne abunda ya fara d'aga masa hankali,cikin gaggawa ya isa gurinsun cikin kid'imewa kuwa ya fara dubata
"Congratulations..! Mr YAZEED..!"
Wata nurse mai rawar kai a cikin wanda suke tura gadon ta fad'a tana d'an murmusawa,mugun kallo ya jefeta dashi na rashin sanin takamaiman halin da take ciki,ba tare daya amsa tayin murnanta ba ya fara magana
"What happen to my KHUSHI...?? Is she alive..??"
Tambayar daya fara zuwa bakinsa kenan lokacin daya tab'ata yana son gano dalilin da yasa bata motsawa,sun san me yake nufi ko ba'a fad'a musu ba,sai dai kowa tsoron magana yake dan yadda suka ga mugun kallon da yake sakin musu,Dr daya amshi haihuwan ne wanda kuma shi ne zai mata CS tun farko ya matsa kusa da shi yana dafa shi,fuskarsa d'auke da fara'a
"She will be fine..! Congregation Dr YAZEED..!"
"Is she alive..??"
Ya sake tambaya kamar wanda ya samu matsalar ji,kai kawai Dr ya fara jinjina masa dan ya fahimci zuwa wannan lokacin ya daina ganewa sosai akan matarsan nan
"Yeah..! She's okay..nd duka sai mu godewa Allah (S.W.T) domin cikin hukuncinsa da k'addarawarsa yasa ta sauka da kanta lafiya ba tare da an yankata ba..!"
A tare Ummi,YASEER,ABEELA har ma da Abir suka furta
"Alhamdulillah..!"
Shi ko gogan idanunsa na kanta kunnensa ne kad'ai a gurin Dr yana sauraren bayaninsa
"Sai dai saboda wahalan data sha yasa muka mata alluran da zai taimaka mata,da zaran ta samu isashen hutu everything will be alright..fatan Allah ya raya baby,madam kuma Allah ya k'ara mata lafiya..!"
Nanma tare suka sake amsawa wajen fad'in "ameen" sannan aka wuce da ita zuwa ward,a nan Dr ya shaida musu babu buk'atar su shiga inda take yanzun matuk'ar za'ayi hayaniya coz ana son ta samu hutu sosai,Abir da aka samu bakin magana yanzun kam nan ta kalli Dr tana washe baki
"Dr amma zamu iya ganin baby..??"
Bata kai ayaba Yarima ya wani waigo yana watsa mata kallon da yasa ta saurin rufe baki tana girgiza kai irin na ba sai sun ganshi ba a lokacin
"Yeahh..! Zaku iya amma dai ya kamata ku kiyaye da yawan surutu a kusa da ita coz zai iya sawa ta farka,wanda mu kuma ba hakan muke fata ba,mun fi so ta samu lokaci mai tsayi tana hutawa.."
Godiya sosai suka masa sannan ya wuce office ita kuma aka k'arasa wucewa da ita,da Yarima aka k'arasa kaita d'akin,after kuma duk nurses d'in suka fice ya rage daga Yarima sai ita da baby'nsu dake faman bacci,a gefenta ya zauna hannunta a cikin nasa ya rungume ba tare daya matsawa nan da can ba,a hankali kuma ya d'ora bakinsa yayi kissing hannunta sannan yaci gaba da aikin kallonta without blinking,har lokacin shi kam bai ko ji sha'awar d'aukan baby'n ya tsarga masa ba,tun misalin k'arfe 6:30pm aka fito da ita amma har aka yi sallan isha'a bata farka ba wanda zuwa lokacin tuni baby'n shi kam ya farka da kuka,Ummi ce ta fara d'aukansa bayan tayi masa addu'ah sannan ta bashi zamzam da dabinon data jik'a da ruwan zamzam,ko daya d'an samu hakan ganin ba samun abincinsa zaiyi a time d'in ba bacci ya sake d'auke shi, wasa² tun suna sa ran farkawarta a kusa har bayan 10pm shiru kuma duka a lokacin su Ummi suna hospital d'in,around 11pm su Ummi suka tattara da niyyan komawa gida nan aka tsaida maganar babbar baiwar Ummi ta yanzun zata kwana gurinta,kar kuso ganin rashin kunyar Yarima a lokacin dan take bai bari anja maganar da tayi ba yace musu kawai su wuce shi zai kula da ita idan ta farka,duk yadda Ummi taso su tafi tare yace mata kawai tayi hak'uri ta kyale,ko da taga taja shima ya ja sai ta hak'ura ta sake masa,nan suka tattara suka tafi aka barshi shi kad'ansa sai kuma dogarai dake gadin d'akin ta ko wane angle.
Sai bayan asuba sannan ta farko a lokacin Yarima bacci ya d'an fara fizgarsa saboda kwana da yayi a zaune,haka ko baby'n ma ya farka cikin daren tafi sau uku amma babu wani abu da yake samu daya wuce rarrashi,after yayi yayi sallar asubah nema sannan ya d'an sa kansa a gefenta wanda yin hakan take yasa bacci b'arawo ya fara d'aukan sa,cikin d'an baccin da bai riga yayi nisa ba yaji ana shafa suman kansa,hannun ya fara rik'owa dan yasan bazai wuce itane ta farka ba,yana d'agowa cikin azama akan fuskarta ya fara sauke idanunsa da suka fara k'ank'ancewa yana sakin nauyayyun ajiyar zuciya
"KHUSHI..!"
Ya kirata,cike da k'arfin hali ta sake masa murmushi kafin ta amsa masa,sannu ya fara jera mata,tun tana amsawa da k'arfin guiwa har abun ya fara bata kunya,shi kuwa ko a jikinsa har zuciyarsa yake tausayinta shi yasa ko yaya ta motsa zai rattabo mata sannu,ganin ya kasa dainawa ne yasa ta d'an kalleshi tana cewa
"Zanyi fitsari..!"
Bai ko jira ta sake cewa komai ba ya shiga k'ok'arin janye panoptic d'in da k'afafunta ke ciki ya d'auke ta,hannayenta tasa a saman wuyansa tana kallon fuskarsa,da murmushi kwance a fuskarta har ya kaita toilet d'in tayi fitsarin,sannan ya wanke mata baki ya dawo da ita,pillow yasa mata ta jingina shi kuma yana zaune gefenta hannayensu sak'ale dana juna
"Yallab'ai..! Me muka samu ne..??"
Ta jefo masa tambayar ba tare da zato ba,sai lokacin yayi k'ok'arin kallon cradles d'in da baby'n ke ciki,a hankali ya saki ajiyar zuciya yana d'age mata shoulders alamun bai sani ba,ido ta d'an zaro tana rufe baki,shi kuwa nan ya tsareta da kallon "what.?" Kai ta girgiza masa tana sake lumshe ido,kallonta ya d'anyi yana squeezing face,sannan ya tashi da kansa ya d'auko baby'n duk bata sani ba har ya dawo kusa da ita yana d'orashi akan cinyanta............
#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 27.*
^^^^^^^^
*#Phone call*
Her childish almond eyes tayi saurin bud'ewa tana zuba masa su,kamar za tayi kuka sai kuma ta d'an kalli baby'n dake motsawa a saman cinyanta alamun yana son tashi
"Nifa ba cewa nayi ka bani ba..just kawai na tambaya ne..!"
Finger d'insa ya d'ora saman lips d'inta yana fad'in
"Shhh!" Shiru ta masa nan ya zauna kusa da ita yana ratsata da hannunsa sannan ya d'an kwantar da kanta a kafad'arsa
"I know kin tambaya ne,although nasan kema ko ganin sa baki yiba shi yasa na kawo shi,sai mu kalla tare ko..??"
Idanunta ta d'aga ta d'an sake kallonsa
"Kaima baka gansa ba..??"
Tayi masa tambayar cikin sanyin muryanta,kai ya d'an kad'a mata yana tab'e baki
"Nopp.! Na ganshi d'azun..buh ba wani sosai ba,coz yana kuka nema ya tashi that's why ban gama ganinsa ba a time d'in.."
Yadda yake nunawa kamar bai damu da baby'n ba yanzun bayan zuwansa duniyar shi ne ya d'an bata mamaki,haka ta wani side d'in ya d'an tab'a mata zuciya kad'an,wanda ta riga da tasan a lokacin da tana da cikin yayi d'okin ganin ta haihu,baya ga burin da yaita ci akan cikin nata,yanzun kuma duk sai taga abubuwa sun sauya mata,"me hakan yake nufi..??" Ta yima kanta tambayar tana d'an runtse idanunta,sai dai tayi shiru bata furta masa damuwarta ba suka ci gaba da zaman shirun,almost 10 minutes da kawo mata shi sannan ya farka,cikin kukan su na jariran dake da cikakkiyar lafiya ya shiga rera kuka with his exquisite child voice,a hankali ta sake zuba masa ido ba tare data san abunda ya kamata ta fara yi masa ba tana tasbihi ga mahaliccin daya suranta siffar jaririn nasu,shima Yarima su ya sawa ido yana sauraren yaga abunda zata yima newborn baby'nsun dan ya bar kukan amma sai yaga kawai ta tsura masa ido kad'ai da alamunma ita bata ko yi monitoring halin da yake ciki ba,kuka sosai yake amma har lokacin ta kasa d'ago shi bare tayi niyyan rarrashi,tana can duniyar tunani har ta kai ga baby'n ya fara k'ok'arin kai thumb d'insa zuwa baki,daurewa Yarima yayi tunda yaga kallonta kad'ai bazai isar da sak'on ba,nan take ya mik'a hannunsa a bayanta ya janye zip zuwa k'asa,saurin kallonsa tayi lokacin daya katse mata tunaninta,amma sai taga shi idanun sama suna kan baby'n yana d'an motsashi a hankali,sunkuyar da kai tayi itama tana sake lumshe idanunta da bud'ewa akansa mai had'e da ajiyar zuciya,bata yi tunanin ko tsammanin me zai aikata ba sai data tsinto hannunsa a cikin riganta yana k'ok'arin fito da breast d'inta da suka yi wani irin cika,sake kallonsa tayi still nanma idanunsa basa kanta,shi yayi kid'an dan haka rawarma dole shi ya fara k'ok'arin takawa,ita dai kawai tayi masa zuru ba tare data yi k'ok'arin hana shi abunda yayi niyyan yi ba,cikin nutsuwarsa ya d'ago baby'n sannan ya jona masa teat d'in a baki while dukansu suna a jikinsa ya had'a su ya rungume,yaro kuwa dake kan tsananin buk'atar abincinsa yana jin an fara matsa masa take ya kama,kamawarsa ne tayi sanadin daya janyo Jeeddah ta saki k'ara tana fizge nonon a bakinsa,kamar taci chilli pepper powder haka take ta wani irin abu tana kuma duba saman teat d'in,shima baby'n jin an lasa masa zuma a baki ko gama tantancewa baiba har an kwace ya sashi sakin sabon kuka,harara ta sakar masa tana sake duba teat d'in coz zugi take ji har cikin kwakwalwarta,duk abunda ake idonsa na kansu kamar zai mata dariya dan yadda take sake duba wajen sai dai ya had'iye abunsa,wahalar data sha kafin ta haihu shi ne yasa shi zuba mata ido had'e kuma da d'aga mata k'afa a time d'in,sai dai a gefe d'aya na zuciyarsa kuma tausayin baby'n tuni ya masa mahaukacin damk'an da yake jin bazai iya hakur'in ganinsa yana irin wannan kukan ba,a dai² kunnenta ya d'ora bakinsa yana hura mata iska,cikin wani voice ya fara mata magana
"KHUSHI..! Pleasee mana kina ji yana kuka fa..do something zai yi shiru.."
Fuska ta kwab'e kamar wacce ana cewa kyat zata saki hawayen da suka taru a idanunta
"Gaskiya..gaskiya ni dai A'a'a..! Tabb' dafa zafi.."
Tun data fara magana yake kallont,haka kuma ga dukkan alamun iya gaskiyarta take son nunawa a time d'in dan yadda take tura abunta cikin riga tana sake adanawa
"Haba mana..! KHUSHI.. Ya kamata ace yanzun ya samu abincinsa tunda kin farko,do u know how long ya d'auke shi ba tare daya abincinsa ba..?? Kin san adadin farkawarsa duk kina bacci a time d'in..Pleasee don't tortured him,it's inappropriate ki nemi condemning nasa ta wannan hanyar ba..Pleasee!"
"Ni dai Allah bazan iya ba..kaji kuwa yadda naji..?? It hurts ba kad'an bafa..!"
Kamar yace mata "A'a" kan tambayar nata sai dai kuma yayi shiru yana kallon abunda take
"Ni dai Allah idan haka ne sai dai ya hak'ura a bashi madara.."
Wani birkitota yayi suna facing juna idanunsa a waje yana binta da wani irin kallo mai shiga jiki
"Repeat what u says..!"
Tsilli² tayi tana kallonsa dan yadda taga idanunsa ba kamar yadda ta saba ganinsu ba,kasa magana tayi sai ma k'ok'arin maida hawaye da take tayi
"Kina son raina ya b'aci ba..??"
Kai ta d'an kad'a a sab'ule tana ajiye idanunta k'asa
"Ok..feed him before..!"
"Allah kuwan..!"
"Keep ur mouth shut..kiyi abunda nace kawai now..bana son yawan magana..!"
A hankali hawayenta suka fara sakkowa daga cikin idonta,yana kula da abunda take yi sai dai baya son yin magana coz
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 45 Chapter of 63