tabbatar lokaci yayi daya kamata ace na d'auki FANSA..!"
Cikin fargabar jin kalaman da suka fito daga bakin Adda Aisha tayi saurin d'ago kanta daga kallon titin da take ta kallo fuskar Adda ta cikin mirror zuciyarta banda tsinkewa babu abunda take,ta cikin mirror Aisha ta sake kallon fuskar Adda,zuciyarta cike da taradaddin anya Adda ke wannan maganar ko kuwa wata ce daban a cikin motan,sake kallonta tayi a karo na Uku,nan kuwa ta tabbatarwa kanta Addan ce kuma ita tayi maganar,hankalinta ta mayar kan titi sai dai duk nutsuwarta bata tare da ita a lokacin,shewar ladidi ce ta cika mata kunne kan tsabar murnan furucin da taji yana fitowa daga bakin Adda'n da bata tab'a zato ba,a haka dai suka k'arasa wanda ikon Allah ne kad'ai ya kaisu amma badon Aisha na cikin mood en da zata iya kaisu ba,kowannensu kuma da abunda zuciyarsa ke sak'awa da warwarewa.
^^^^^
Kwanaki sun tura da faruwar al'amarin,wanda tun daga kansa babu wanda ya sake biyo YAZEED da maganar auren Aisha,haka nan kuma babu wani abu daya sake faruwa a tsakanin,a b'angaren Adda ma basu sake tunanin bi takan masarautar ba bare har su sake zuwa da niyyar neman afuwar laifukansu,suma kuwa cikin gidan babu wanda ya sake koda ambatonsu a cikin labari bare dan ganin basu zoba kwana biyu a tambayesu lafiya.
Randar Sunday tun da yamma mai girma governor Prof A.A Maji dad'i kasancewar baya k'asar ya yiwa maimartaba waya ya sanar da shi yana so washe gari ya tura su YASEER birnin tarayya,ba tare da yayi masa wani bayan ba kan abunda zai kaisu,haka ko bayan da suka gama wayan GALADIMA ya yiwa bayanin abunda mai girman governor yace sannan ya bashi umarnin ya sanar musu,hakan ce ta kasancewa dan tun a ranar ya kirasu ya shaida musu dan su kasance cikin shiri da safe subi flight gudun b'ata lokaci sannan ya sallame su,washe gari kam tun asubah suka kammala abunda za suyi sannan aka d'auke su zuwa airport,suka bi jirgin k'arfe bakwai sai birnin na abuja.
Saukar jirginsu babu jimawa tuni motoci har sunzo suna dakonsu,da zuwansu aka d'auke su sai fadar shugaban k'asa,ananfa suka ga k'arshen karramawa dan yanda ake nan² dasu kamar suna gida,direct daga nan ba'a zarce dasu ko ina ba sai *Primus International Super Specialist Hospital* dake nan a Karu new extension cikin Abuja Municipal,gaskiya asibitin k'arshe ne wajen had'uwa,haka ko ta ba'angaren aikinsuma sunyi fice musamman ta b'angaren duk wani abu daya shafi dashe ko surgery,indai k'warewa ne a wannan b'angaren,aiki da sanin makamar aiki wannan Asibitin suna lamba ta farko a cikin garin na Abuja,haka ko suma kansu na tabbata dalilin kaisu can ba don komai bane sai dan ansan zasu iya bawai dan suna y'ay'an wasu ba.
Cikin k'ank'anin lokaci da zuwansu tuni aka tashi meeting inda tun daga kan cleaner har zuwa sama babu wanda ba'a tattara ba dan a gabatar dasu,bayan gabatar dasu a tak'aice da y'an jawabai sa sua biyo baya,sannan kowannensu aka kaishi nasa office en a matsayinsu na manyan likitoci da suka had'a alak'a da b'angaren dashe.
Y'an kwanaki k'alilan da kama aikinsu a cikin asibitin duk wanda ya gansu da yadda suke gudanar da aikinsu cikin k'warewa dole ne ya tabbatar lallai sun san abunda suke,duk da kasancewar su y'ay'a da suka fito daga gidan sarauta sam idan suna bakin aiki baka tab'a bambance daga inda suke,saboda yadda suka iya bi da patients ensu,harma da sauran ma'aikata dake k'asansu,sai dai wani lokaci da dole ne sai an samu matsala tofa hakkan kan d'an faru sai dai ba sosai ba,dalili kuwa ko tsakanin harshe da hak'ori ma akan samu wannan mishkilar.
Rayuwa taci gaba da tafiya a haka,ba tare da samun wata matsala ko damuwa ba,sai dai ko wacce ba'a rasa ba,ta b'angaren aikinsu kam a iya wannan lokacin kusan ma iya cewa alhamdulillah! Dan babu wata matsala da suke fuskanta,haka nan ko bayan barinsu garin kimanin wattani biyar kenan tsakani sun shafesu ba tare da sun kalli hanyar Kano ba,yau kam kasancewar ranar ta jumu'ah,daga hospital direct basu tsaya ko ina ba suka d'auki hanyar Kano,dan yau kam tun tashinsu da safe sun rantse idan ba'a Kano ba basu ga inda zasu yi sallar jumu'ah ba,babu wanda suka sanarma suna hanya bare ayi tunanin taronsu,kawai sun tsara sai dai a gansu,sai bayan an sauko a masallaci sannan suka kama hanyar gida ba tare da sun yarda sun had'u da kowa ba cikin ahalin nasu,b'angaren Fulani suka fara nufa,tun daga shigowar su da suka ji gefen nata shiru suka tabbatar da yaran duka basa nan,a nan suka fara yada zango kafin suka kama hanyar apartment en Ummi,a can ne suka samu suka d'an dad'e dan sun jima suna hira da ita haka nan kuma dama sunfi sakewa da itan sosai kafin suka koma nasu b'angaren dan hutawa.Akano suka yi hutun weekend en na wannan lokacin,sannan suka kama hanya ranar Monday da asubah,bayan tafiyar su da y'an kwanaki,nan kuma wata sabuwar masifa ta b'illo cikin zuri'ar tasu inda bayan meeting da akayi wanda basu samu damar halarta ba abun sai ya zama magana,haka dai aka yita gutsira zancen wanda k'arshe har ya koma kunnen hajiya,inda wasu a cikima da suka samu faraga har suka sako zancen ya kamata ace maimartaba ya tattarasu yayi musu aure tun kafin idanunsu su gama bud'ewa,zantuka dai kowa da irin nasa gudunmawar a yake bayarwa wajen zancen,wasu kuwa cewa suke ai tunda ya turasu k'asar waje idanunsu sun riga sun gama bud'ewa shi yasa suka tsaya ruwan ido suka kasa auren kowa,wasu kuwa su ba laifin kowa suke gani ba face nasu su kansu,maganganu dai barkatai wasuma marasa dad'in sauraro duk babu wanda ba'a fad'a ba akansu,sanda maganar ta isa kunnen maimartaba sai daya shiga damuwa akan lamarin,sai dai kuma bisa ga yadda suka yi shawara da hajiya itama da dukkan alamu goyon bayanta ya tsaya ne akan aurar dasu en kamar yadda zancen yake yawo acikin zuri'ar tasu.Koda jin ta bakin hajiya bayan maimartaba sun keb'e su biyu da niyyan sake yin shawara da GALADIMA akan maganar da neman mafita ta yadda yake ganin zasu b'illowa lamarin.
Su enma dai rahin samun nutsuwa yasa su tsayawa kan matsaya guda wacce da zaran sun samu su YASEER en sun dawo hutun k'arshen mako za suji ta bakinsu idan yasoma duk abunda ya kamata ayi a wannan lokacin sai su yanke....................
*Sai hak'uri kam fan's Wollah kwana biyun nan sai a slow ne kawai.*
#Follow me on wattpad @jeeddahmu898.
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@Hawwa M.U Pindiga.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*ALLAHUMMA BALLIGHNA RAMADHANA BIL IYMAAN.....👏🏻👏🏻👏🏻*
___________________
*Pg 29.*
^^^^^^^^
Kasancewar ba ko wane hutun k'arshen mako suke samun dama su zo gida ba,yasa wannan karonma basu samu zuwanba,sai da suka shafe a k'alla weekend biyu,sai dai suyi waya da iyaye da y'an uwa kawai,cikin sati na uku da suka shafe basu zo ba sannan suka samu sararin tahowa cike da son zuwa gidan,tun daga yanayin yadda hajiya a lokacin da suka je gaidata,da YAZEED ya kalleta nan ya tabbatarwa kansa a kwai damuwa,sai dai kuma kasancewar bata fito ta sanar dasu dalilin da yasa take d'an had'e musu fuska ba yasa suma suka ja bakunansu suka tsuke ba tare da sun tambayeta abunda yake damunta ba,duk da dai YAZEED ya kusa yin hakan YASEER ya hana shi.
Da dare lokacin bayan sallar isha'a sun dawo daga masallaci suna kan hanyan shigowa suka gamu da Affan yana fitowa daga apartment en Ummi,cikin saurinsa ya nufo inda suke,cike da ladabi da girmamawa yaron ya gaishesu kafin ya isar musu da sak'on Abba galadima na nemansu da yake a cikin lokacin,sai da suka kalli juna sannan suka bi bayan yaron zuwa cikin turakar Ummi'n zuciyar kowa da abunda yake sak'awa akan kiran na Abba, Zaune suka iske Abban,Ummi da kuma Abir dake kwance jikin Ummi kamar wata y'ar goye,sai kuma shi Affan da suka shigo tare,neman guri suka yi suka zauna kafin suka gaida Abba GALADIMA bayansa kuma Ummi,Abir dake kwance itama ta gaida su cikin girmamawa.
Abba ne ya kallesu ita da Affan yana fad'in
"Abir maza ku bamu guri ko zanyi magana da yayyanku.."
"Toh Abba.."
Ta fad'a tana mik'ewa a jikin Ummi sannan Affan yabi bayanta suka fice zuwa gefen Fulani,bayan fitarsu Abba ya waiwayo ya kallesu su duka sannan yayi murmushi duk dan ya kwantar musu da hankali kada suyi zaton wani gagarumin laifi suka yi yasa har ya kirasu haka,musamman kuma da yaga suna kallon juna suna kallonsa tun shigowarsu
"Shin kun san dalilin da yasa na tura aka kiramin ku..??"
Abba yayi maganar yana kallonsa duka
"A'a Abba..!"
Shi ne abunda suka fad'a suna had'a baki suma,cike kuma son sanin dalilin na Abba,jinjina kai yayi sannan ya juya ya kalli Ummi da ita sam ma abunda suke ba shi ne a gabanta ba
"Dalilin kiran ba akan wani abu bane haka zalika ba wai wata matsala aka samu ba da zata sa nayi hakan,illa iyaka sai akan munyi magana da hajiya da kuma Yaya na son ganin kunyi Aure...!"
Tun kafin ya k'arasa fad'ar abunda yake shiri tuni har sun kalli juna sun koma kuma gareshi suna had'a baki wajen fad'in
"Aure kuma Abba..?"
Cike da rashin fahimtar yanayin da suka yi magana ya shiga kallonsa kafin yayi magana shima yana sake tabbatar musu da abunda ya fad'a
"K'warai aure..Ko baku shirya bane..??"
"A'a Abba.."
Suka sake had'a baki suka fad'a
"Towh..! Na zata ai ko baku shirya ba,yanzun na sanarwa da Yaya abunda kuka ce,dan shi ya bani damar zama da ku na tambayeku ra'ayin ku akan maganar,sai dai kuma kada kuji nayi muku wannan maganar kuyi zaton lokaci zamu b'ata,ko kad'an wannan ba abune da zamu zuba ido akansa ba,muna son ayi komai cikin k'ank'anin lokaci ne,ina fata kun fahimta.."
"To..! Abba Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi.."
Da ameen ya amsa musu,kana ya kalli YAZEED yana murmushi da cewa
"Yarima ince dai ko akwai yarinyar da kake nema yanzun..??"
Kallo² suka yi tsakanin sa da YASEER yana sosa k'eya,dariya YASEER yayi kafin ya amsawa Abba da
"Nanfa d'aya Abba,dan shi wannan da kake gani Babban gwauro ne..Ko sau d'aya bai tab'a tsayawa da ko wace yarinya ba bare yayi tunanin yin wata magana mai tsayi da ita.."
Gyara zama Abba yayi daga kishingid'ar da yake yana fad'in
"Ya salaam..! To kai malam YAZEED ya akayi haka kuma..?? Yanzun Fisabilillah.! Da nayi wannan maganar ai sai kayi hanzarin sanar dani ba wai kayi shiru ba.."
Dariya YASEER ya sake yi yana shirin yin magana YAZEED en ya zungureshi da k'afa yana masa nuni da yayi shiru
"To kai malam YASEERU fa,ko kuwa kai enma kamar san kake..??"
Maganar da Abba yayi itace tasa YAZEED yin murmushin mugunta a ransa yana fad'in
"Duk jirgi d'aya ya kwaso mu ai.."
Sai dai bai gama kaiwa aya ba amsar YASEER ta sashi saurin kallonsa
"A'a Abba akwai..!"
Da mamaki YAZEED yake kallonsa yana maimaita
"Akwai kuma..! Yaushe kayi budurwar malam..??"
Harararsa YASEER yayi sannan ya furta
"To me kaji da na fad'a ne..?? Cewa nayi akwai mana dama..!"
"K'arya yake Abba bashi da ita idan kuma akwai to wace ce..??"
Cike da k'warin guiwa ya furta
"ABEELA ce Abba.."
Mamaki sosai a kan fuskar YAZEED yana kallonsa cikin wani irin yanayi
"Kai malam dama wai soyayya kuke da ita..??"
Ba tare daya kalleshi ba ya bashi amsa da
"Ban sani ba..!"
Abba ne ya kallesu duka yana girgiza kai
"Wato ku kun girmanma amma halinku na nan.."
Sunkuyar da kai sukai suna murmushi dukansu,sai da suka sha tsokana a gurin Abba kafin ya dawo kan ainihin maganar da suke yana kallon YASEER,in a serious tone yana sake tambayarsa
"Malam YASEERU shin maganar da kayi yaya matsayinta yake..?? Da gaske ne har zuciyar ka ko kuwa..?? Kasan bana son wasa ko..?"
"Ehhh! Abba da gaske ne.."
Jinjina kai yayi yana sakin murmushin dake bayyanar da irin tsantsar farin cikin da yake ciki na jin wannan labari da yafi ko wanne faranta masa rai a tsayin yinin ranar,sai can daga baya sannan ya juya kan YAZEED yana fad'in
"To kai malam YAZEED yaya muke ciki da kai ne..Shin lokaci zamu baka ka nemo ko kuwa..?"
Kallon YASEER yayi ya zabga masa harara sannan ya sauke kai k'asa yana fad'in
"Abba ai duk yadda kace haka za'ayi.."
Murmushi Abba ya sake yi sannan yaci gaba da magana cikin tsokana
"Malam YAZEEDU.. Nima na d'ana yadda hajiya take yi ko..??"
Y'ar dariya suka yi duka har Abban
"To ko dai Abir zan baka ne...??"
Wata dariya YASEER ya saki kafin ya kalli YAZEED
"Ka amsa mana broh! Kaga sai kayi raino ba.."
Harararsa yayi k'asa² ya furta
"Ai kai baka cika maganar nutsuwar ba,duk maganar shirme kana nan agurin.."
Abba ne ya kallesu yana cewa
"To k'us² en me kuke kuma..?? Ko kuma dai maganar kuke tattaunawa akanta.."
Shiru suka yi basu yi magana ba,nan Abba shima ya maida maganar serious yana fad'in
"Aaa! Nima wasa nake..Wanna ai ba sa'ar aurenka bace,duka nawa Abir en take da za'a fara maganar aurenta..? Kawai dai abunda yake mafi muhimmanci shi ne ayi k'ok'arin dubawa daga nan zuwa wani lokaci kafin mu sake tuntub'arku..Allah yasa mu dace.."
Ameen suka amsa masa sannan ya sallamesu,sai da suka zauna hira a nan sannan daga baya suka tafi duk da Abban ya jima da sallamar su su en ne dai kawai basu shirya wa hakan ba.
Lokacin da suka koma side ensu kasa magana YAZEED yayi saboda yadda tunani yaci k'arfinsa a lokacin banda tunanin yadda za'ayi ya samu wacce zata soshi babu abunda yake,shirun da YASEER yaga yayi ne yasa shi kallonsa yana tab'a shi kafin ya jefo masa tambayar
"Lafiya broah...??"
Ajiyar zuciya ya saki sannan ya girgiza kai yana fad'in
"Wollahi broah maganar Abba tasa ni tunani..Sam bansan ma ta ina ya kamata nafara bane.."
Jinjina kai shima yayi kafin ya fara magana cikin tausasawa
"Dole ne broah..Nasan kuma wannan lokacin zai zo,shi yasa lokaci da dama nake baka shawaran ka daurewa zuciyarka ka jarraba had'a alak'a da wata amma sai baka sauraren ni ba,a lokacin da nake maka wannan maganar na tabbata gani kake kamar bansan me nake yiba,kuma kai kanka a lokacin kana tunanin duka halin mata d'aya ne,wata rana kana tsammanin abunda ya faru da kai zai sake faruwa..!"
"Haba mana Mr man..ya kamata ace wannan dogon labarin naka yazo k'arshe,kai da kanka ai kaji me kace da kace,so saboda haka mu manta da wancan lokacin,yanzun abunda yafi shine mu fuskanci gaba.."
Jinjina kai YASEER yayi sannan ya kalleshi
"To yanzun me kake so nace ne.??"
"Shawaran ka mana..ai kasan shi nake buk'ata ko..?"
"Haka ne amma ai nima tambaya nayi,sai kace min ga abunda kake buk'ata nace.."
Tsaki YAZEED yayi cikin jin haushi ya furta
"Kai wollahi ka cika abun haushi,yanzun dole ne sai nace maka ga abun daya dace kace..ko kuwa ni sanda kake tambayata ina maka irin wannan silly questions en..??"
Tsayawa kawai YASEER yayi yana kallonsa tamkar wani dolo,ko da ganin haka sai kawai YAZEED ya mik'e zai bar wajen cikin jin haushi,har ya kai dai² k'ofa zai shige corridor en YASEER ya furta
"Kai matsalarka ka cika ci da zuci... Sam baka tsayawa kaji abunda ya kamata lokuta da dama,shin yanzun daka tafi gurin waye zaka je ya baka shawaran da kake buk'ata sama da ni..??"
Juyowa yayi ya kalleshi irin kallon nan mai kamada harara kafin ya furta
"Ohoo! maka ko kuwa dan ka kasa sai akace maka babu wanda zan nufa ya bani shawara ne..??"
"Uhmm! Ka san dai ba kamar ni ba ko..kuma a rashina ne zai sa kaje gurin koma waye ko..??"
Bai kula shiba ya juya zai bar wajen kawai YASEER yayi magana
"Idanma zaka dawo ne gara maka ka dawo dan ni yanzun haka ma har na hango maka wacce ya kamata ka aura tunda Allah baisa ka iya tantancewa da kanka ba.."
Kamar wanda aka matsawa pause haka ya kafe a gurin har sanda YASEER yakai aya,saurin juyowa yayi yana takowa har inda yake sannan ya nemi guri ya zauna kusa da shi yana tambayarsa
"Wace yarinya ce itan da kake magana akanta...???"
Murmushi kawai YASEER yayi sannan ya d'auke kai daga barin kallonsa
"Ohoo! Maka nima ai na fasa tunda har saika ja min aji nida ba y'ar budurwar na zama ba.."
Tsaki yaja cikin jin haushi kawai ya tashi ya bar wajen duk irin kiran da YASEER en yake masa baiko saurare shi ba.
^
Kwanaki sun sake zuwa har sun wuce,haka suma a b'angarensu tuni har sun kammala hutun k'arshen mako sun koma bakin aikinsu,a cikin wannan lokacin kuwa tuni har GALADIMA ya sanarwa maimartaba labarin yadda suka yi da y'ay'an nasa,haka nan maganar har tayi nisa ta ko wane b'angare,a gefen hajiya ma kusan ma iya cewa tafi kowa farin ciki dan yadda abun ya zo mata duka a cikin zuri'ar tasu al'amarin ya kasance,zuwa yanzun tuni har an tsaida lokaci wanda ba wani mai tsayi ba sosai,yanzun haka ma su ake jira suzo hutu aji ta bakinsu.
^^^^^
Kuka sosai take tun tana kan hanya,driven enma da k'yar take yinsa saboda yadda hawaye yake cika mata ido lokaci zuwa lokaci tasa hannun ta goge,shigowarta harabar gidan ba tare data tsaya ta saita parking ba ta fice ko motan bata iya kashewa ba bare ta cire key en tayi cikin gidan tana sake rushe wa da kuka mai sauti.
Da Adda ta fara cin karo itama a lokacin kukanta ne yasa ta kamo hanya zata fito,tana zuwa kuwa Adda na rik'o hannunta da tambayarta
"Lafiya Aishatu..Me aka miki..waye ya tab'amin ke..??"
Duka tambayoyin Adda ta jero sune ba tare data samu amsar tamtayar farko ba,kukanta take sai data yi iya yinta sannan a hankali ta d'ago tana jan majina,idanunta har sun sauya color cikin sheshshek'ar kuka ta fara bawa Adda'n labari
"Yanzun Adda shi kenan aurena da Yarima ya tashi..??"
Cikin tashin hankali Adda ta kalleta tana tambaya
"Inji uban waye yace miki baza ki aure shi ba..??"
Hawayen daya zubo ta goge sannan ta bata amsa
"Yanzun nanfa Adda a supermarket na gamu dasu ABEELA take cemin wai kwana biyu bamu zoba,har ansa ranar aurenta ita da.."
Zaro ido Adda tayi cikin kid'ima ta furta
"Aurensu...??? Dawa kenan..??"
Wani sabon hawayen ne ya zubo mata sannan taci gaba da magana
"Itafa ABEELA wai itada YASEER aka sa musu rana..Kuma wai ba ita kad'ai ba har da Sajidar Abba matawalle,kuma Sajidar wai...wai..wai.. Ita da.!"
Sai kawai ta sake b'arkewa da kuka,cikin rashin fahimta Adda ta ja hannunta zuwa kan cuition tana kallonta da tambaya
"Wai..wai kike cewa kin kasa sanar dani..waye wanda aka sa mata ranar da shi..??"
"To ba ABEELA tace min wai..wai..aii!"
Nan ma kukan ta sake b'arkewa da shi fiye dana farko,yadda take risgar kuka kamar ranta zai fita yasa Adda kallonta,cikin tsanaki take kallonta tana tunani kafin tace
"Kina nufin da Yarima aka sa musu ranar..??"
K'arfin kukanta ta k'ara tana girgiza wa Adda kai cike da alamun tabbatarwa hakan ne,cikin wani irin mugun b'acin rai Adda ta tsuke fuska tana jinjina maganar har cikin zuciyarta kafin a fili ta fara magana
"Lallai Hajiya Hauwa kinci amanata a karo na biyu..Sai dana sakankance sannan zaki nuna min haramci..Shin wannan shi ne soyayyar da kike ik'irarin kina yi mana..?? Tabbas dole ne a wannan karon na mik'e tsaye domin nuna miki cewa nima ina son nawa ahalin..Tunda kika janye AL-K'AWARIN da kika min,ina tabbatar miki da ba zan tab'a barin bashin FANSA ba,dole ne na jefa zuri'ar ki cikin masifa da bala'in daya wuce shigar YAZEED kurkuku.....................!"
#Follow me on wattpad @jeeddahmu898.
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*Facebook:@RealSmasher.*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY SISTER'S♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*ALLAHUMMA BALLIGHNA RAMADHANA BIL IYMAAN.....👏🏻👏🏻👏🏻*
___________________
*Pg 30.*
^^^^^^^^
Ranta a mugun b'ace tayi furucin da har yasa Aisha d'agowa tana kallonta,cikin lokaci kad'an tuni har tayi scrubbing hawayen fuskarta tana kallon Adda dake ta faman sambatu
"Wollahi bazan tab'a kyaleki ba,dake da ahalin ki ba,dole ne ku d'and'ani irin d'acin dana ji a lokacin da kuka nuna min ni saniyar ware ce a cikin ku..! Bazan tab'a karb'ar asara biyu ba a rayuwata,dole ne sai kuma ku d'an d'ana wannan karon nima sai nayi nasara...!"
Kamar Aisha zata tambayeta abunda ya faru a wancan lokacin da taji Adda'n na kambamawa sai kuma taja bakinta ta tsuke tana sake kallon Adda'n dake faman safa da marwa ita kad'ai tana sambatun masifa,ko da ganin hakan da take yi bai yi mata ba nan a ake wata zuciyar ta bata shawaran abunda zai fishsheta,cikin tsantsan b'acin rai ta fizgo wayanta kana ta cillama a kan cinyarta kamar wayar ce ta mata kaifin take kuma k'ok'arin hucewa akanta tana fad'in
"Kiramin hajiya Hauwa a waya yanzu yanzun.."
Kai ta girgiza sannan ta fara lalubo number hajiya kana ta bud'e speaker wayan,yadda wayan ke duka lokacin da kiran ya faru tafi haka jikin Adda ke wani masifaffen
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 63