ita ta samu tayi sallaba sai yanzun,tunanuka iri² tayi ta fama da su a lokacin na son gano wasu abun dake faruwa amma sam ta kasa,dan haka itama sai ta tattare komai ta ajiye a gefe taci gaba da sabgar gabanta,tunda ta fahimci bai shirya sanar da ita ba zata yi ta binsa da ido har sanda yaji son ya sanar mata.
Ga Yarima kuwa lokacin data fita ta barshi a bedroom d'in,yana zaunen d'aya a cikin wayoyinsa tayi alert alamun akwai sak'o akai,bai d'auka ba bare ya duba ya shirya cikin shiga ta alfarma sannan ya fita daga apartment d'in ba tare daya sanar mata ya fita ba,kai tsaye bayan apartment d'insu ya d'auki hanya yana bi,har lokacin zuciyarsa kuma a cunkushe take da tsantsar bak'in ciki zuwa sanda ya iso bakin gidan,sai da yayi knocking sannan d'aya a cikin masu tsoron gidan ya bud'e masa k'ofar ya shiga,mayar da k'ofar yayi ya rufe kafin yabi bayansa zuwa cikin gidan,duk gaisuwar da suke masa ko d'aya bai samu confidence na amsawa ba yayima kansa jagoranci har zuwa d'akin da take,babu komai a cikin d'akin face pray mat da wani kujerar robber guda d'aya tal kamar rai,bayan shi kuwa babu wani abu a cikin sa sai ko ta Inno d'in data zama cikon na uku,tun daga shigowarsa suke mik'a gaisuwa sai dai duk bai iya bud'e baki ya amsa musu ba,sai dai ya samu ya jinjina musu kai alamun amswar amma bai furta da baki ba,a gaban Inno ya dakata dai² lokacin guard d'in daya biyo bayansa ya matso masa da kujeran ya zauna,hannayensa yasa ya tallafe chin d'insa da su,sannan ya zuba mata idanunsa masu matuk'ar firgita mara gaskiya,ya d'auki tsayin lokaci yana kallonta ba tare daya furta komai ba sannan ya sake numfashi yana kauda kai gefe,cikin nutsuwarsa ya mik'e ya kama hanyar fita dan baya jin zai iya fad'ar abunda yake so a gaban idonta,bayan fitowarsu ya d'an dakata yana kallon guard d'in
"Kun samu wani abu ne zuwa yanzun...??"
Da sauri wanda ke tsaye a gefen nasa ya furta
"A'a Yallab'ai.. Tunda muka taho nan da ita bamu kai ga fara binciken ba,mun dai jirane muga zuwanka.."
Wani kallon sakarci yabi shi dashi kafin yaja wani malalacin crack
"Wane irin shirme kenan..?? Shin abunda na d'auko kuyi min kenan..??"
Cikin d'an hasala yayi maganar duk da bawai yana shouting bane
"Sorry sir..we thought da kace kada muyi wani abu,hakan na nufin ciki har da binciken ne..!"
Sabon tsaki yaja sannan ya kama hanya kamar zai fice a gidan yake fad'in
"Ka same ni a waje."
Ba tare daya jira cewarsa ba yayi wajen,nan shi d'in ya biyo shin a baya kamar yadda ya buk'ata,a k'ofar gidan Yarima ya dakata yana binsa da kallon me kuka tsaya jira da bakuyi abunda ya kamata ba,shi kam sauke kansa yayi k'asa yana jiran jin abunda Yarima zaice
"Idan har wannan shine kwarewar ku a aiki ya tabbata baku san komai ba..Mene ne amfanin d'auko ku na kawo nan matuk'ar ba aikin da nake buk'ata za'ayi ba..??"
"Sorry sir..!"
Ya sake fad'a yana sunkuyar da kai,siririn tsakin ya sake yi a ciki sannan ya sake furta
"Tunda kuka zo da ita babu wani alama da kuka gani a tattare da itane..?? I mean wani abu haka da zai bamu haske kan binciken..??"
Har yace masa babu,sai kuma ya furta
"No sir..tabbas a d'azun munji anyita kiran waya,nd at least ina tunanin an kira ya kusa twenty ×.."
Jinjina kai Yarima yayi sannan ya furta
"Ka tabbatar anyi hakan..??"
Tabbaci ya bashi kan lallai anyi,ga Yarima kuwa lissafawa yake me zaisa wani ya kirata kamar haka..?? Anya kuwa babu wani daban a bayan case d'in.? Idan har wannan aikin sata akayi,shin wane ne wannan mutumin da zaisa ayi k'ok'arin kidnapping jariri kamar wannan,sannan mene ne dalilin da yasa ake son sato shin..?? Irin wannan tunanukan sune suka cika zuciyarsa amma sai duk ya watsar da su dan ba sune abunda yake buk'ata ba a yanzun,bai bar wajen ba sai daya tabbatar ma guard d'in nasa kan cewar su kyaleta ta tafi tunda babu wani shaida da zasu iya samu a tare da itan,tsantsar mamaki ne ya rufe guard d'in har yaso ya musawa maganar da Yariman yayi na cewar da yayi su saketa,fuskarsa daya gani babu alamun wasa shine yasa shi amsa masa cikin gaggawa,nan Yarima ya fbar gurin ya kamo hanyarsa ta komawa gida,yana tafiya yana sakin kayataccen murmushin dana kasa fassarawa da gano ma'anar yinsu.
Bayan fitarsa da y'an mintuna itama Inno suka fito da ita,ita dai ganin wad'annan halittun suna matuk'ar bata tsoro idan ta kallesu,shi yasa mafa bata cika d'aga kai ba idan ta gamsu a kusa² da ita,sanda suka bata izinin tafiya,jiki babu isashen k'wari ta kamo hanya tana yi tana waiwayen bayanta da haka har ta fito daga cikin yankin jejin,sanda ta tsinci kanta a ainihin cikin gidan sarautar kuwa nan ta saki ajiyar zuciya mai cike da sukuni kafin taci gaba da tafiya cike da hanzarin da ita kanta bata san ta iya irinsa ba.
A b'angaren Yarima lokacin daya dawo kai tsaye bedroom d'insa ya sake shigewa,ko daya tarar har lokacin bata ciki nan ya lalubi IPad d'insa k'irar pro 11,while d'ayan hannun kuma yana rik'e da wani phone d'in yana clicking, a sawa a kunnensa ya kasata lokacin da yake d'an sauraren shigar kiran da yake yi,ko da aka d'auka bai tsaya wani gaishe² ba ya fara magana deeply
"Yawwa.! bilal yanzun zan turo maka wani number,make sure kayi min hacking nasa,nd bana so aikin ya haura 5 minutes...!"
Shiru ya d'anyi na wasu mintuna kafin ya sauke wayan a kunnensa yana sakin sanyayyar ajiyar zuciya,lokacin daya tabbatar ya kammala turata masa ne,ya d'an zame ya kwanta yana fad'in
"This is the beginnings.............."
#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 32.*
^^^^^^^^
*#Fear*
Almost 10 minutes kira ya sake shigowa wayansa,a kaikaice ya kalleta yana duba wanda ya kira,ganin HACKER yayi appear yasa da murmushi kwance a saman fuskarsa ya d'auka
"Sir an gama komai kamar yadda kace d'in.."
Abunda bilal ya fad'a kenan daga gefensa
"Ok thanks..!"
Shima yariman ya fad'a daga haka bai sake magana ba ya zare wayann a kunnensa,yana lalubar wani mini wireless bluetooth had'e da manna shi cikin kunnensa yana kuma ci gaba da clicking iPad d'in dake gefensa.
A b'angaren Inno kuwa lokacin data isa gida har time d'in a firgice take da lamarin Yarima saboda tsabar fargabar dake addabarta har ta shiga d'aki ta kulle kanta bata sani ba,tsantsar mamakin da yak'i barin ranta a wannan lokacin kuwa baya rasa nasaba da yadda Yariman yasa aka kyaleta ba tare da anyi mata komai ba,al'halin shi d'in da kansa ya kamata kuma da idanunsa ya ganta tana kan k'ok'arin abducting d'an cikinsa,ba wani ya bashi labarin ba,,tana cikin wannan halin kiran JIBO ya sake fad'owa wayan,jikinta duka babu isashen nd yadda wayan ke vibrates itama haka take kamar wacce aka jonawa shocking k'wari dan haka har wayan ya katse bata iya samun damar fito da ita daga jikinta ba,ci gaba akayi da kiranta amma sam ta kasa ko da kwakwaran motsi bare ta d'auka,sai a karo na uku sannan ne tayi k'arfin hali bayan tarin fargaba ta d'auki wayan ta kashe ta gaba d'aya,a gefen JIBO kuwa dai² lokacin da yake kiran Inno tarin b'acin rai ne ya had'e masa bayan tarin haushi na irin kiran da yayi ta mata tun dare ba'a d'auka ba yanzunma yana kan kira amma yaga alamun kamar tana son raina musu hankali,sai da ya kira yafi a lissafawa a kira na kusan k'arshe sai ya tsinto baturiyar company tana shaida masa wai wayan tana kashe,wani uban ashar ya dunk'ule ya milmilo,tsabar masifa ya hau fad'ar duk abunda yazo bakinsa kamar wacce yake yi dominta tana gabansa,after ya kirata bai samu ba sai ya shiga kiran number uwargijiyar tasa,abunda ya sake k'arawa JIBO haushi a lokacin shine itanma wayar tata tana tafiya kamar yadda yayi a daren jiya sai dai ank'i answering call d'in,wannan b'acin ran shi ya haddasa masa fizgar motan da yake ciki ya bar wajen babu shiri.
Ga Yarima kuwa duk kiran da akewa Inno da number yana ganin kiran sai dai ya kasa fahimtar abunda ke shirin faruwa da har ya janyo Inno ta k'i answering,cikin nutsuwa bayan an gama kiran bata d'auka ba,ya sake turawa Bilal number daya kirata yanzun ta text yace ya masa hacking nata itama,ko kafin bilal ya kira shi ya sanar da shi tunani yadda zai b'illowa lamarin na Inno yake,coz a wannan halin ko kad'an baya so yayi wani abu akanta da zai janyo masa tsayawar duk wani plan d'in daya shirya,besides kuma yana zargin akwai wasu mutanen a bayan case d'in nasu shi yasa ma tun a ranar da abun ya faru yasa suka sake ta ba tare daya bada damar a tambayeta ba,dan yadda yake tunanin akan Inno baya tsammanin tunaninta ya kai ta iya shirya wannan badak'alar,dole ne ko da ace tana da hannu a ciki ya zama ba ita kad'ai bace akan lamarin,ya jima yana wannan tunanin sai dai har zuwa lokacin bai gama tabbatar da zarginsa ba akan hakan hundred %,moving yake a tsakanin walls d'in bedroom d'in daga nan zuwa can,hannayensa goye a bayansa yana sake zurfafa tunanin sa,sai dai duk da hakan sam ya kasa fahimtar komai akan lamarin,saman resting chair ya koma ya zauna a fili ya furta
"It's necessitates na samu Inno nayi magana da ita,ya zama dole ta amsa min duk tambayoyina nd ta bani had'in kai,if tak'i amincewa kuma dole ne na nuna mata zan sanar da kowa abunda tayi.!"
Shiru ya d'anyi cike da tunani,zuwa can kuma ya furta
"Nooo! Sa mata ido ya kamata a fara yi,kafin ayi wani abu kuma.."
Haka yaita tunani iri daban² idan yace wannan sai ya soke yana ganin duk ba hakan ya kamata yayi ba,ya jima a wannaan yanayin har zuwa sanda yaji zuciyarsa tafi karkata akan su sa mata idon,ajiye tunaninsa yayi kan zai tura guards d'in nasa su fara bibiyar ta kafin ace ya tunkareta da wani batun,wannan shawaran itace ta d'an soma bashi nutsuwa,daga nan sai ya nemi number d'aya a cikin guards d'in ya kira had'e da shaida masa yana son kawai su bibiyi matar da suka saka a d'azun amma suyi komai cikin nutsuwa baya son su bar duk wani hanya/shaida da zaisa ayi saurin gano shirin su,amsa masa yayi cike da girmamawa sannan Yarima ya ajiye wayan yana sakin ajiyar zuciya mai k'arfi.
A b'angaren Inno kuwa tun daga ranar da abun ya faru gaba d'aya sai ta fara jin tsoron fita,hatta da bayan gida idan zata zaga a tsorace take shigarsa ta fito,sai dai ko da ganin har yau babu wani batu data ji yana yawo daga gurin wani sai ta fara sakin jikinta har tana niyyan fita ta shiga cikin gida a yau d'in,sai dai duka a hakan tana jim nauyin mutanen masarautar wanda yasa ta fara jin kamar kada taje,yayi da a wani sashin kuma na zuciyarta nan ya shiga shaida mata taje d'in kawai babu abunda zai faru,lokacin data gama shiryawa ta fito a gidan sai data gama kallon hanya kafin ta fara tafiya cikin tsoron bata san da waye zata had'u ba,a haka har taje gidan ta gama abunda za tayi ta kuma kamo hanyar dawowa babu wanda yace mata k'ala haka nan babu da wanda ta had'u bare yayi mata barazana,dan haka ko data fahimci hakan sai bata tada hankalinta ba,dama da farkon tayi tsammanin ko Yarima ya sanar da iyayensa ne kan batun amma sai taga babu wanda ya tada mata maganar,ko da ganin haka sai itanma ta saki ranta tayi abunda ya kawota ba tare data nuna musu akwai damuwa ba.
Shi kuwa Yarima a nasa gefen duk wannan abun dake faruwa a b'angaren Inno kawai ya zuba mata ido ne badon komai ba sai dan saboda Jeeddah,a nasa tunanin yana ganin bai kamata ace yasa a tozartar da ita ba kasancewarta mahaifiya ga matar daya fi k'auna a duniyarsa kuma yake aure,ko ba komai a cewarsa tunda har ta haifa masa mata ya kamata ace shima ya gwada mata hallaci,nd wannan shine uzurin farko daya kamata ace yayi mata a matsayin surukarsa,kasancewar wannan shi ne laifi na farko data tab'a masa duk da munin abunda tayi masan,wanda yaji shi a ransa,amma sai ya tsinci kansa da son yayi mata wannan alfarmar,kuma wannan dalilin shi ne yasa tun ranar da abun ya faru ya kasa koda yin tari a gaban idanunta,buh duk da haka bawai ya kyaleta bane kawai dai yana shirin yaga abunda zai sake biyo baya ne.
A lokacin da Inno ta zo cikin gidan a yau duk babu abunda bai sani ba coz duk akan idanunsa komai ke wakana tun daga fitowarta a gida har kawo lokacin data shiga apartment d'in Umma'nsa tayi duk abunda za tayi ta tafi duk yana ankare da ita,yanayin reactions d'inta kad'ai yake dad'a sawa ido yana kuma sake karantar ta,ganin babu wani abu da tayi attempt tayi a cikin gidan har ta tafi yasa shi dad'a fahimtar lallai akwai wani b'oyayyen al'amari a tare da ita da bata son a sani,buh ya barwa ransa son bincikarta da gano duk wani abun da take son boy'ewa.
Around 9:00pm yayi shiri kamar wanda zashi wani guri mai muhimmanci ya fita bayan ya nunawa Jeeddah akwai inda zashi,addu'ar fatan alkhairi ta bishi da ita,sanda ya fice kuwa direct tsohon apartment d'in da aka kaita rannan ya nufa ba tare da sanin kowa ba,lokacin daya karaso bakin apartment d'in nan ya iske guards d'insa suna shawagi da sake bawa gidan tsaro,wucewa yayi zuwa ciki dan gabatar da abunda ya kawo shi coz baya son b'ata lokaci har wani ya kawo zargin akwai abunda yake k'ok'arin aikatawa a boy'e,coz cikin iyayensa ko YASEER bai sanar da ko wanne ba,da shigarsa cikin gidan nan ya iske Inno a wannan d'akin dai da aka sata kwanakin da suka gabata,yauma d'in saman kujeran ya zauna yana kallonta da jinjina kai cike da al'ajabi,in a serious tune kuma cikin lallami ya fara magana
"Inno..! Nasan za kiyi mamakin yadda akayi muka dawo dake bayan mun riga mun sake ki.."
Bata iya d'agowa ba bare ta had'a ido da shi ba dan tun daga ranar kawo yanzun da take zaune a gabansa har wani nauyin had'uwa take da shi,shima d'in bai damu data amsa ba yaci gaba da magana
"I knew duk abunda ya faru a wannan ranar babu laifin ki a ciki,coz na tabbatar wa raina babu yadda za'ayi yadda kike matsayin mahaifiya ga JEEDDAH ace kiyi trying na sace d'an data haifa kuma jikanki,,shin mene ma ribar da zaisa ki aikata aiki irin wannan..?? Buh i pleaded u for the sake of Allah ki duba girmansa sannan ki tuna wani lokaci duk zamu riske shi,duk iya adadin abunda muka aikata da sannu akwai ranar da zamu girbe,Inno ina rok'on kiyi min wannan alfarmar ko badon ni ba ina so ki duba jikanki ki sanar dani abunda yake faruwa,ko da ace wani yayi miki barazana ne akan lallai sai kin aikata hakan,I promise u zanyi iya k'ok'arina na baki kariya,matuk'ar kika sanar dani zanyi duk wani k'ok'arin dana san zan iya akai na ganin na fitar dake,buh sai idan har kin sanar dani gaskiyan yadda AL'AMARIN ya kasance..!"
Shiru ya d'anyi yana kallonta dabin reactions d'inta,har ta bud'e baki kamar za tayi magana nan take Yarima ya fara hamdala da godiya ga Allah coz yana tunanin da zaran ta fad'a masa komai zai sake zuwa masa da sauk'i,ga Inno kuwa lokacin har ta bud'e baki kamar zata yi magana ko mene ta tuna kuma sai kawai taja bakinta tayi shiru,duk motsinta akan idanunsa yana kallonta,ko da yaga tak'i cewa komai har tsayin lokaci sai bai hak'ura ba yaci gaba da kalamanceta da dad'in baki a tunanin sa duk hakan zai sa tayi k'ok'arin fad'a masan,amma saboda tsabar taurin kai irin na Inno saima tak'i yin magana gaba d'aya,iya jin haushi da b'acin rai Yarima yaji haushinta a lokacin,dan yadda gaba d'aya ya gama ayyanawa a ransa da zaran ta shaida masa ba zaiyi sanyata ba har sai yaga masu laifin sun shiga hannu sannan zai saurara,ko da hakkaan ya faru nan take ya fara tunanin a ransa cewa da wani ne ba ita ba yau yayi masa wannan ta'addancin da tuni ya jima da sawa a tafasa masa jiki,sai dai duk da haka itanma kawai dai yana mata kawaici ne badon kowa ba sai don d'ansa da kuma Jeeddah,amma bayan wad'annan da ace babu su a tsakanin daya jima da kifar da ita a gurin,duk girman kusancinsu kuwa.Ko da yaga sam bata shirya sanar da shi abunda yake da buk'ata ba cike da sanyin jiki ya kalle ta yana fad'in
"Shi kenan Inno kiyi hak'uri da takuraki da muka yi,,in sha Allah komai ya wuce daga yau,babu wanda zai sake saki a gaba,mun gode sosai..!"
Daga haka bai ko sake kallonta ba ya fice yana cewa guards d'in
"Ku tabbatar kun maida ita inda kuka d'auko ta ba tare da wani abu ya saketa ba."
Yana fad'in haka yasa kai ya fice a cikin gidan gaba d'aya cike da tsantsar jin haushinta a ransa.
A b'angaren Jeeddah kuwa duk wannan badak'alar dake kan faruwa ko d'aya bata san dasu ba haka bata da labari,nd ko kad'an shima a b'angaren Yarima bai bata fuskar da zata sani d'in ba,sai dai itan a cikin kwanakin ta kula da yadda yake yawan zaman shiru ko kuma taga yana aiki da iPad d'insa,wanda a kwanakin bayan kam tun da suka dawo daga wanka ta san yana iya k'ok'arin sa wajen kulawa da su sosai sab'anim yanzun da duk ta kasa fahimtar inda ya nufa,dan haka itama duk sai ta zuba masa ido tana jiran taji yace mata wani abu amma har yanzun bai nemi da su yi wani magana makamancin wanda take tsammanin ba,wannan dalilin kuwa yasa itanma sai ta d'an janye masa iya karta da shi a yanzun cin abunci tare sai ko idan yana buk'atar wani abu daga gareta ko kuma lokacin bacci yayi,nan ne kad'ai take ganin tana da amfani a gurinsa,buh duk da hakan sai bata sa hakan a ranta ba ta dai ci gaba da addu'ah kan lamuranta da shi.
Inno kuwa koda ta samu wad'annan askarawan na Yarima suka dawo da ita k'ofar gida,nan hankalin ta ya d'an kwanta,lokacin data tsinci kanta kuwa a cikin uwar d'akanta,tunani ita kanta ta shiha akan lamarin tun daga farkon fara afkuwarsa har kawo yanzun da take tsaye a d'akin da ta kasa tab'uka komai,haka nan tun bayan da suka rabu da su Yarima da yasa guards d'in su dawo da ita gida nan ta shiga tunanin anya kuwa ta kyauta kan abunda tayiwa Yariman..?? Yadda yayi ta lallab'ata akan ta sanar masa da abunda yake faruwa sam bai kamata ace ta saka masa da kwatankwacin abunda tayi a yanzun ba,matuk'ar ace kamarta zata yi irin wannan d'anyen aikin akan son nata rayuwar shin yaya rayuwar yarinyanta zata kasance,besides kuma idan har ace tayi haka ne saboda mutuwa ko gudun wahala to what about rayuwar jariri kamar AHYAN..?? Shin hakan shi ne abunda ya kamata ace ta aikata a matsayinta na uwa kuma kaka..??
Wannan tunanukan sune suka shiga kwakwalwarta har suka janyo ta fara ji a ranta ya zama dole akanta ta aikata wani abun kirki da zaisa ayi alfahari da ita a matsayin surukar data dace a jinjina mata,,,kamar wacce aka tsikara tayi zumbur ta mik'e had'e da fara bincikar tsohuwar adakarta dake k'asan gado,wayarta data kashe tun a ranar da AL'AMARIN ya faru ta d'auko sannan ta kunna,still ta isketa da alamun kira akai na tun ranar,nam dai ta lallab'a tayi flashing sannan ta nemi guri ta zauna a k'asa tana mai buga tagumi da duka hannayenta biyu,mintuna kad'an sai gashi an kirata,kasancewar dama jira take yasa ko bari wayan tayi cikakkcen ring bata iya ba tayi caraf ta d'auka,daga can gefen JIBO daya kira cike da tsantsar b'acin rai ya fara masifa
"Wato saboda kin maida mu wad'anda basu san abunda suke yiba shi yasa kika k'i d'aukan kiran da muke miki..?? Ko kuwa dan kina tunanin abunda muka fad'a bazai mu aikata bane..??"
Jikin Inno na b'ari had'e da bakinta ta furta
"Ba haka bane Yallab'ai,kayi hak'uri dan Allah..wallahi matsala aka samu ne shi yasa ban iya na d'auki wayar ba tun a lokacin da kake kiran nawa,,,yanzunma haka so nake na shaida maka ina son ka d'an sake bani lokaci nayi nazarin yadda ya kamata ace munyi wajen sato yaron nan,tabbas idan har muka ce ta hanyar daka fad'a ne,ina mai tabbatar maka lallai ne za'a iya kamamu saboda tsananin taron dake gidan,amma kayi tunanin maganata dole ne mu k'ara lokaci.."
Wani uwar tsawa ya buga mata dan yadda yake ganin kamar tana son raina masa hankali ne kawai,amma yadda yaji tana kwantar da kai sai ya sassauta mata,har ya kuma yarda da maganar da take kan tsara masa na k'arin lokacin data ce ya matan,da wannan maganar su duka suka yanke magamar,Inno ta ajiye wayar tana sakin ajiyar zuciya,shima d'in kwatankwacin abunda yayi a nasa gefen kenab.
A b'angaren Yarima kuwa dai² lokacin da Inno ta kira number duk yana sane,dan haka koda yaga number ta kitara back sai ya sake nutsuwa bayan da yaga kira daga number ya fad'o wayan Inno'n,kaf hiran da suka yi da maganarsu kan lamarin babu wanda bai jiba har zuwa lokacin da suka ajiye wayan dukansu,wani kayataccen murmushin jin dad'i ya saki sanda yaji yadda Inno tana tsarga zance da yayi sannadiyyar bayyana farin cikinsa a fili,coz ya fara hangen nasara a cikin kalamanta,besides kuma yasan ko babu komai a yanzun ya sake samun wani shaidan daya tabbatar masa da anyi threw na Inno ne kawai a case d'in ba don komai ba sai saboda cimma buri,dan haka shima take yaci k'udurin koma su waye kuma ko mene ne zai faru lallai ne sai ya binciko su a duk inda suka boy'e had'e da bawa y'ar dattijuwar kariya.
Ita kuwa Inno baiwar Allah lokacin da suka gama wayan da JIBO wani gawurtaccen nutsuwa ne ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 50 Chapter of 63