za'a ce cikinsu babu wanda yaji abunda yake shukawa,sai bayan daya tabbatar sun shige sannan yaja k'afarsa ya bar gurin yana sake sakin ajiyar zuciya mai k'arfi,direct hanyan ficewa a hospital d'in ya kama gaba d'aya,bai zame ko ina ba a time d'in sai Beirut road,latest phone ya nema ya siya,bayan wasu awanni ya aza sims d'insa,yana tafiya a napep yana clicking wayan kafin ya karata a kunnensa,kusan mintuna biyu sannan ya fara magana k'asa²
"Hello...ranki ya dad'e..!"
"Haba JIBO..wane irin wulaka'anci ne wannan ka kashemin waya ina magana.??"
Dai² yana sauka a napep d'in ya sallama mai napep d'in sannan ya juya yaci gaba da tafiya cikin unguwar dake shiru,hakan ne ya sake bani damar jiyo abunda na d'ayan gefen ke fad'a saboda yadda murya ke amsawa kamar an sa wayan a hands free
"Afuwaan ranki ya dad'e..amma bada niyyane hakan ya faru ba.."
Shiru akayi a d'ayan side d'in kafin aka furta
"Me ya faru ne kake k'ok'arin b'oyemin..??"
Ajiyar zuciya ya saki sannan ya fara magana
"Wollahi ranki ya dad'e da kyar na tsallake rijiya da baya.."
Saurin taron numfashin sa aka yi
"Wai meye ne ya faru kake ta wane dojewa..??"
"Ranki ya dad'e Allah dai ya tak'aita wahala.. Amma saura kad'an fa YARIMA yaji maganar da muke d'azun.."
"Whattt...??"
Ta fad'a cikin k'araji
"Ka tabbatar bai jinba ne..??"
"Kwarai ranki ya dad'e,,,amma fa na tsorata sosai lokacin dana juya na ganshi a gabana.."
Labarin yadda suka yi da Yarima kaf ya bata,sai data gama jin labarin sannan ta saki ajiyar zuciya tana sake cewa
"JIBO let's talk later...yanzun akwai abunda zanyi mai muhimmanci.."
Daga haka suka yi sallama,ya ajiye wayan dai² yana tsaiwa gaban wani madaidaicin gida..
^^^^^
Kwanaki biyar da haihuwan amma a kullum saboda yawan bak'in da ake y'an zuwa barka kama daga dangi zuwa abokan arziki sai yasa mutum yayi tunanin yau ne aka yi haihuwan,a b'angaren Yarima kuwa shiri sosai yake yi akan taron suna coz yace lokacin aurensa babu wani mythology da akayi,dan haka yanzun kam zai nunawa duniya tsantsar farin cikin da yake ciki bisa kyautar da rabb yayi masa na abubuwa da dama.
Kasancewar kullum apartment d'in Ummi na a cike yasa yanzun basu cika samun damar zuwa ba,sai dai da safe kafin su fice,amma da dare kam babu hali saboda wasu cikin bakin sukan kai dare ko hadimai dake zirga²,itanma kuma Jeeddah a nata b'angaren tun data haihu sai bata cika zama a parlor ba sai dai ko wane lokaci tana d'aki,yau kam suna shigowa a apartment d'in Ummi suka yada zango,sai dai da zuwansun suka iske har Ummi'n ta shiga turakarta kasancewar dare ya d'an fara yi,a parlor ya bar YASEER ya nufi d'akin da Jeeddah take ba tare daya bi takan wadu hadiman Ummi ba coz wasu lokutan dama da suke zuwa ganin Ummi ke sawa ya dakatar,yau kam sai ya samu har ta shige,lokacin daya shiga d'akin da take a kwance ya tarar da ita ta juyama k'ofa baya baby'nsun kuma na gabanta da alamun baccin nasu duka basu shirya masa ba yayi gaba dasu,a bakin bed d'in ya d'an zauna yana kallonsu da murmushi a saman fuskarsa,a hankali yadda bazai tashi baby'n ba ya d'auko shi yana masa addu'ah,sai daya gama tofe shi kafin ya d'an shafi kanta itama yana sakin kayataccen murmushin sa kamar ance masa idanunta biyu,addu'ah ya sake musu duka yayi pecking nasu sannan ya fice yana ja musu k'ofa.
Washe gari kam tun da sassafe gidan gaba d'aya a kacame yake,tako ina ka duba jama'a ne wannan yana wane wannan cikin kwalliyar da kowa yake ganin kansa shi wani ne kuma idan zab'a za'ayi shi ne number 1,fitowar Yarima a dai² lokacin itane yasa hankula komawa kansa dan kuwa cikin wani diecaprie exclusive suit ya fito mai launin bak'i haka ma takalmin dake saye a kafafunsa,tie d'in wuyarsa ne kad'ai aka d'an samu ratsin pink,sosai ya matuk'ar d'aukan numfashin y'an matan dake farfajiyar gidan,amma gare shi shikam ko kad'an basa a gabansa,hasalima shi gimbiyarsa kad'ai yake da muradin gani a dai² lokacin,can a tsakiyar jama'a ya hangota dan haka ya shiga ratsawa tamkar baiga kowa a gurin ba sai ita d'aya ya nufeta kai tsaye,cikin wani arnen net gown pink color mara hannu take,daga sama wajen cikinta daf da k'irjinta a d'an kama rigan had'e da yi mata ado da silver,yayin da can saman rigan ya zama na net d'in zalla daya kasance har yana d'an showing albarkar k'irjinta,sosai kanta ya sha gyara,yayin da ta gaban goshinta ya kasance ya d'an yi tudu saboda yanayin gyaran da aka mata da kuma bread din dake mak'ale wanda aka d'aure shi daga tsakiya,sannan ta kowane side na fuskarta an d'an sak'o gashin bayan adon da aka masa like twist yana lilo har wajen chest d'inta,sauran kuma da aka kama ta baya ya sauka a bayanta,tafiya yake idanunsa duka akanta saboda kyaun da tayi cikin shigan,hannunsa d'aya zube cikin aljihun suit d'insa,kasancewar ta bashi baya lokacin tana kan gaisawa da jama'a shi yasa sam bata ga tahowarsa ba har saida ya k'araso yasa hannunsa d'ayan a dai² waist d'inta yana kuma zaro d'ayan ya aza ta d'ayan side na waist d'in tan,saurin d'agowa tayi tana d'an juyar da kanta zuwa kallonsa,koda taga shine lumshe iso tayi tab'a d'an mutsu² alamun ya saketa amma ina yak'i still suna kan kallon juna,hakan da suka yi sosai ya bada wani style daya asalin fallasa k'aunar da sukema juna,ABEELA ce tayi caraf tana kallonsu da murmushi kwance a fuskarta na tsantsar farin ciki ta d'an kalli yayan nata da suka lula duniyar k'auna tana cewa
"Yah Prince..! Pleasee dan Allah ku tsaya a haka..let's me give u some snapshot...Pleasee..!"
Murmusawa yake shi kam ba tare daya san me take fad'a ba,yana d'an lumshe mata ido ya kuma rausayar da kai gefe take hakan yasa tayi tunanin ya bata permission ne,har ta saita zata d'auka YASEER da suka iso tare yayi hanzarin jonama Jeeddah wani rose daya kasance green mai ratsin fari,daga tsakiyansa kuma da d'an kalar pink,hannayensa akan waist d'inta yayin da ita kuma tayi holding furenta da hannu biyun kamar tasan da zamansa a hannun suna kallon juna.Ba iya kad'ai ABEELA ba duka jama'ar gurin ji suka yi sun matuk'ar burge su dan haka jama'a duka sai kowa yayi kansu kowa na burin d'aukansu,kan kace me tuni ruwan flashes kad'ai ke motsawa daga kowane edge.Hasken ne ya ankarar dasu duka dan yadda abun nasu ke neman wuce hankali sannan ya d'an mata rad'a a kunne yana barin gurin,bayansa tabi da kallo ta d'an murmusa itama sannan taci gaba da gaisawa da jama'ar da basu gaisa ba,yinin ranar abunda aka yi ta faman yi kenan kamar baza'a daina ba.
Da dare kam tun misalin k'arfe 8:00pm motoci suka fara haramar tafiya dinner,kafin kace me gidan tuni har ya d'auki shiru kowa ya kama hanyar zuwa PAP's,gaskiya gurin babu k'arya ko ni na shaida da wannan,iya had'uwa ya tsaru,ko ga yanayin haske kad'ai dake gurin idan mutim ya gani tamkar rana ne ba dare ba,cool music sai tashi yake a gurin a yayin da jama'a ke rak'ashewa abunsu,wasuma ni dana hangosu har sai da nayi mamaki coz banyi tsammani ba,tawagar y'an *WANI AL'AMARIN FAN'S* suna fara hangowa coz ko su kad'ai ma sun isa abun kallo a gurin bare kuma a k'aro da sauran groups² na whatsapp,Facebook harma da na wattpad,abun dai sai wanda yaje,masoyan Yarima YAZEED da Jeeddah kuwa cewa sukai ranar tasu ce dan haka dole a basu guri.
To 9pm wani sabo dal d'in ash color na delta toyota mini cruiser ya faka a gurin,glasses d'inta duk masu haske dan haka babu abunda ke iya b'oyewa mutum,Yarima ne da Jeeddah a ciki,ko daya gama daidaita parking shi da kansa ya fito yana sanye cikin wani suit na tuxedo ceremonial suit mai launin grey nd black,curtly hair d'insa nan kuwa da yake bak'i ya sha gyara sai kyalli yake zubawa haka mustache d'insa ma,cikin nutsuwa ya zagayo side d'inta ya bud'e mata k'ofan ta fito,hannunta d'aya ya rik'e a cikin nasa sannan suka fara takawa cike da tsantsar k'auna suna sakarma juna murmushi mai burgewa while d'ayan hannun nata rik'e da cunkon fure,tana sanye cikin wani white gown mai long hand,wannan karon gyara kanta a tsakiya yake sai d'an kad'an da aka d'an yanko ta gefen fuskarta mara tsayi,bread d'in kanta a wannan lokacin fari ne da aka mak'ale d'an wani Vail fari na net a jikin kantan hakan sai ya sake bada gudun mawa na sake k'awatata aidanun al'umma ta fito stamkar wata QUEEN,wannan karon kam zan iya cewa har tafi d'azun kyau Mesa ba kusa ba,dan yadda kayan suka matuk'ar amsar ta abunda dai sai wanda ya gani,sai a lokacin su YASEER suka samu damar karasowa lokacin kuma tuni har sun d'anyi nisa da inda motansu yake,a gabansu YASEER yayi parking ko dan ya dakatar dasu ya fito da sauri
"Haba Man..! Wannan ai tsaban black stomach ne,,kaida zaka bari mu k'araso shi ne zaka ja matarka ku wuce ba tare da kun jira mu ba.."
Wani kallon k'asan ido Yarima ya masa yana tab'e baki
"Kai ka san wannan..ni kam daka matsaminma a hanya dan ba jerawa zamuyi da ku ba,coz ur era already passes..so mene naka na damuwa dan mun wuce bamu jira kuba..??"
Drama sosai suka tsaya yi wa junansu,ganin haka yasa ABEELA ta d'an ja hannun Jeeddah dake gefen Yarima tana sauke kai k'asa suka matsa jikin motan da suka zo da shi,back seat na motansu dake tsaye wajen tayi saurin bud'ewa tana fad'in
"Sisi Pleasee..! Lemme give u one snapshot."
Murmushi ta mata hakan yasa ta d'an sake janta,dan haka itama Jeeddan sai ta d'an zauna kad'an kafin ogannin nasu su gama tsiyan da suke ma juna,yanayin zaman da tayi sai yayi kamar dai² lokacin zata fito a motan her left hand side ta rik'e murfin motan da shi,while right hand d'in kuma tayi holding rose d'inta mai launin green da ratsin white ta tsakiya ta d'an d'ago shi fuskarta cike da fara'a,nan fa ABEELA ta shiga sauke mata ruwan hotuna har sai da Yarima yaji haushi yazo ya janyeta,dcoz yaga abun na ABEELA kamar bazai k'are ba,sune kan gaba sai YASEER da ABEELA dake biye dasu a baya cikin shigan alfarma ta zallar kalar fari,suka ratso k'ofar shiga hall d'in daya matuk'ar tsaruwa,nan fa salon kid'a ya chanja saboda shigowarsu ta bambanta da saura a haka suka ratsa ta tsakiya har wajen zaman su.
Tun kafin su kaiga zama tuni MC ya nemi da su tsaya tsakiyan deck d'in,sai daya gama janyo jawabinsa na taya murna sannan ya d'ora da fad'in tunda suka sa jama'a jira har na tsawon awa guda wasuma sun wuce haka tofa babu su babu zama until sunyi abunda zaisa zuciyoyin al'umman da suka taru dominsu sunyi sanyi,murmushi kawai Yarima yake zubawa yana watsa idanunsa akanta,yayin da ita kuma duka ganin jama'a yasa ta duk ta nemi rikice masa,a hankali ya dad'a matsowa da ita jikinsa yana rik'e waist d'intan da hannu d'aya yana mata rad'a,faruwar hakan ke da wuya nan take MC ya shiga kirari ga Yarima saboda burgeshi da yayi,gurin kuwa banda ihun jama'a da sowarsu babu abunda yake tashi,dan babu wanda basu burge ba,cikin mick ya shiga sanar da DJ ya bashi latest song da zai tada tsumi ga duk wasu Masoyan dake cikin maye,da begen junan su like thus couples dake tsaye gabansu,nan kuwa bada b'ata lokaci ba a hankali taken ya fara tashi kafin sautin wak'an ya bayyana,dukansu suna tsaye kamar wad'anda aka dasa a gurin,nan MC yake fad'in shifa ba shi zasu kunyata ba,al'umman dake kallonsu zasu kunyata,amma ina ita Jeeddah ma jikinta wani rawa ya hau yi a time d'in coz bata saba tsintar kanta a irin wannan gurin ba,surutun MC d'in shi ne yayi ta cika musu kunnensa har ta kai ga ya ingiza Yarima,nan take ya sake matsarta sosai had'e da kamo hannunta d'aya ya rik'e yana sanar mata kiss,fuskarta a d'an karkace tana kallonsa ta lumshe ido saboda bak'on yanayin da suka tsinci kawunansu a ciki,a hankali kuma ya juyota zuwa gabansa yana d'ora hannuntan da yake rik'e cikin nasa a saman shoulder sa d'aya while shi kuma yasa nasa a dai² waist d'inta,kansa ya sa ta d'ayan side na fuskarta yana mata rad'an ta d'an dunga motsawa saboda ya kula da yanayin da take ciki,sannu a hankali suka fara d'an takawa suna juyi,kafin kuce me ai tuni sautin kid'a ya ratsa Yarima tun suna rawan a d'an fuska sai gasu sun zange wanda k'arshe da rawa yayi rawa sai ga Yarima ya sauke blazer saman ya bada rik'o................
*😱😱😱 Tofa...! Fan's kunga ikon Allah gurin Yarima... Harda su cire riga kuma a bada rik'o..?? Gaskiya da mamaki,anya kuwa Yariman dana sani ne wannan..??🤔*
#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
💠💠💠💠💠
*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*
بسم الله الرحمن الر حيم.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
_Thank u does not seem enough.Thank u a million times over,i love it *UMMUFAREED,KHADIJA ALIYU ADAM & CHASHEEN* real smasher loves u more n more.🌹_
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 29.*
^^^^^^^^
*#The plan*
Yanayin yadda suke rawa a gurin kamar wasu Indians,sosai yasa suka ja hankulan jama'a,nanfa al'umma suka ce dawa Allah ya gamamu,nan take asken flashes ya ci gaba da tashi a kansu,su kam gare su sun mance da kowa da komai dake gurin,abu d'aya ne kad'ai yayi musu saura a tare da su wanda shi ne tsantsar k'aunar su ga junansu,sun jima suna rawa saman deck d'in sannan MC ya dakatar dasu had'e da jinjinawa namijin k'ok'arin da suka yi,tafi da shewar al'umman gurin ne da suka burge ya maye gurbin sautin cool music dake tashi,a hankali MC ya kalli jama'a yana dariya mai cike da gamsuwa yana kuma tambayansu shin sun k'ayatar dasu ko kuwa,jama'a duka kamar had'in baki suka ce sun k'ayatar dasu too premise ma kuwa,dariya ya sake yi sannan ya basu permission na zama,a matuk'ar gajiye Jeeddah ta d'an rausayar da idanu tana d'an kad'a k'afafunta dake saman wani fresh pump white heels,kafin ta fara d'an tafiya a hankali cike da tsananin gajiya coz tunda suka zo basu zauna ba,waist d'inta yasa hannu ya rik'o dai² suna tafiya a saman deck d'in suna d'an hira abunsu,har suka isa saman seat da aka tanada dominsu,YASEER da ABEELA ma ba'a barsu a baya ba,dan kuwa sune mutum na farko bayan su Yarima da suka sake bud'e filin,suma kam sun zubar da nasu salon k'aunar a wannan gurin wanda suma ba k'aramin burge jama'a suka yi ba,haka taro yaci gaba da tafiya har zuwa lokacin tashi,wanda basu suka tashi a gurin ba ba sai misalin k'arfe 11pm bayan kowa ya kama hanya,suma suka nufo gida cike da gajiya.
Cikin mota suna tafiya a hanyar su na dawowa ta d'an kwantar da kanta saboda tsabar laushin da tayi ko maganama da kyar take iya d'agowa ta amsa duk da bawai suna hira bane amma yakan d'an tambayeta,a ranta kam sai yanzun take murna da godiya ga Allah da yasa tun farko Ummi ta hana tafiya da Muhammad AHYAN (Abu YAZEED name sake) gurin dinner,can k'asan zuciyarta ta furta
"Waiii! Allah ya taimakeni daya ce shima sai an tafi da shi yau daya zanji a saman wannan tuntumemen takalmin..??"
Kallonta ya d'an waiwayar da kai yayi lokacin yana gyaran parking yana kuma sake kallon yadda ta wani narke fuskarta duk a yamutse,murmushi ya d'an sake kafin ya zare nasa seatbelt d'in ya nufo ta duk ba tare data san me yake shirin yiba,light kiss ya d'ora mata a saman lips d'inta,da sauri ta bud'e idanunta tana diriricewa da ganinsa closer to her sai rud'ewar ta nemi ta wuce ta farkon sanda yayi mata kiss d'in,lips d'inta ya tsurawa idanu yana murmushin da shi kad'ai ya san ma'anar sa,itanma shi take kallo da idanunta kamar mara gaskiya ko mai gudun faruwar wani abun,cikin rashin gaskiya ta fara k'ok'arin matsawa,yannaa kallonta har sanda ta gama komawa jikin murfin motan kamar zata shige cikinsa ta b'illa waje,kallonta ya sake yi sai yanzun nema daya nutsu ya gano duk iya adadin firgicewar da tayi,bakinsa kad'ai ya d'an tab'e kafin ya sake matsota,wannan karon kam idanunta kad'ai ta iya samun damar runtsewa,yadda ta k'ank'ame idanunta ya sashi kallonta kafin yasa hannu ya zare seatbelt d'in dake jikinta,komawa yayi mazauninsa yana sakar mata kallon da shi kad'ai yasan ma'anar sa,a hankali jin babu abunda yayi mata ta shiga bud'e idanunta,har ta gama waresu sannan ta juya ta kalle shi,b'ata fuskar da yayi yasa ta d'an kauda kai gefe
"Muje ko sarauniyar tsoro.."
Ya fad'a can k'asan mak'oshi,sarai ta jishi sai dai tayi ignoring nasa coz bata san mene zai biyo bayan maganarta ba idan har ta tanka masa,shi ya fara fita sannan ya zagaya ya bud'e mata yana jira ta fito,da kyar ta iya motsawa a gurin saboda irin kallon da yake binta da shi,tana nok'ewa tana komai ta sako k'afarta waje da niyyan fitowa sai wani yauk'i take zuba masa,yadda take jan aji gurin kamar bata son motsawa shi kuma Yarima abunda yake sake dilmiya zuciyarsa kenan,almost 3-5 minutes da bud'e mata motan amma har yanzun iya k'afarta kad'ai ce a waje,matsowa yayi gabanta kafin tayi tunanin abunda zai biyo baya tuni har ya kamo hannunta ya mik'ar da ita tsaye,ba tare daya bata ko wane irin space da zata iya wucewa ba ya sake matsarta yana curbing hanyan da duka hannayensa had'e da sauke mata narkakkun idanunsa dake cike da zallar k'aunarta,ita kam jin yadda ya matseta ne ga numfashin su dake mingling yasa duka ta kasa sakewa a gurin saboda wani bugu da zuciyarta take cike da wani mahaukacin feelings dake taso mata tun daga cikin b'argonta besides kuma ga fargabar kada wani ya gansu kasancewar parking lot ne na gidan duka a hakan da suke tsaye kuma sai hanya take lek'e,hannunsa daya d'ora saman fuskarta ne yasa ta juyowa da sauri tana kallonsa zuwa lokacin gaba d'aya tayi asalin firgicewa saboda hasken motan su YASEER dake tunkaro gurin,tunma kafin ta kaiga yin wani tunanin tuni ya bud'e wani wagon mai duhun glasses dake kusa da su ya sata cikin back seat shima ya shige,dan haka koda su YASEER d'in suka k'araso babu kowa a gurin nd dama bawai sun hango su bane,yana gama daidaita parking kuma suka fito,tana kallonsu zasu wuce ta kalleshi ya wani haye samanta ga idanunsa cikin nata ya zuba mata su,jira kawai yake su YASEER su bar gurin,ai kuwa ilai duk kallon da yake mata tun kafin su YASEER d'in su wuce ta kalleshi tana fad'in
"Yallab'ai.. Let's..!"
Bakinsa ya d'ora saman nata gently nd calmly ya shiga sucking lips d'inta ba tare daya bata damar k'arasa maganar da tayi niyyan ba,daman kuma kallon da yake mata kenan na kada tayi magana,amma shi ne tun ba'a je ko ina ba tana neman tona musu asiri,sai daya tsotse duk lipstick da aka samata wajen makeup sannan ya d'ago jajayen idanunsa yana kallon yadda ita kanta tayi laushi a wajen,idanunta duka a kulle tana son yin magana amma tana tsoro cos bata san mene zai kuma biyowa baya ba,resuming back yayi da abunda yake yi,sam Yarima ya manta da cewar har lokacin tana kan jego dan yadda ya fice a hayyacinsa,itanma kuma ta kasa bud'e baki ta sanar masa,sai da taji yana neman b'allo mata ruwa sannan ta rik'e hannunsa a firgice idanunta taf da tsoron abunda ke shirin faruwa,kallonta yake yadda ta wani k'ank'ance idanu a kansa cike da wani irin yanayin tana rausayar da kai
"What's happen KHUSHI..?? Don't tortured me..Pleasee.!"
Ya fad'a cikin muryansa mai kama da rad'a yana kuma kallonta,wannan karon har da wasu munafukan hawaye kwance cikin idanunta ta turo masa baki gaba cike da tab'ara
"Nifa ba wai na gama bane..!"
Da mamaki yake kallonta yana tambayar kansa "mene kuma bata gama ba..?? Is it what he ask..?" duk hankalinsa a tashe dan yadda yake jin yakai mak'ura a buk'atar ta
"Mene ne baki gama ba KHUSHI..??"
Ya tambaya a hargitse cos ya kasa ganowa da kansa,gashi sai wani kare jikinta tame,sai data sake tura masa baki gaba can k'asan mak'oshi ta ce
"Shi d'in.."
Gaba d'aya shi kam a lokacin ta gama d'aure masa kai,duk wani kalamanta ba fahimtar su yake ba bare ya iya gano abunda take nufi
"KHUSHI speak ur mind,,,i can't even understand..What do u mean..??"
Sai data boy'e fuskarta a jikinsa sannan ta furta
"Nifa ce maka nayi ban gama ba,shi ne abun wahala..??"
D'agota yayi yana kallon fuskarta a hargitse
"Pleasee KHUSHI talk mana,explain it to me..I didn't get it right.."
"Shifa nake nufi..ni wane bayanin zanyi maka bayan u knew about it.."
D'an kad'an ya kuma tab'e baki kafin ya ce
"Ke kika sani.."
Yana fad'a ya sake immersing kan abunda ke gabansa,ba tare daya sake sauraronta ba,sanda ya sake kai hannu zaiyi k'asa da pant d'inta ta sakar masa wani irin kuka,slender crack yaja na b'acin ran abunda ke neman faruwa,a fusace ya mik'e yana gyara zaman trouser sa,duk yadda yake ji a hakan ya fara k'ok'arin saita nutsuwarsa,jin ya d'agata ne yasa ta fara k'ok'arin mik'ewa tana kokawar gyara nata jikin dan gaba d'aya abunda ya rage Yarima yayi mata tsirara a motan bashi da yawa,ta gefe yake kallonta sanda take saita zaman boobs d'inta a cikin riga kamar da gayya take wani d'ago masa su,ajiyar zuciya yayi yana kulle idonsa had'e da jingina kansa da seat yana kuma rarrashin zuciyarsa,ita kam ko da taga ta kammala shiryawa kallonsa ta d'anyi cike da tsoron shirun da yayi ta furta
"I am through..!"
Bai ko kalli inda take ba saboda haushin abunda ta masa yace
"U can go..!"
Bai ko sake motsawa ba ya sake yin shiru,waiwayawa tayi ta cikin glasses d'in tana kallon gurin,ko ba dare ba aka ce tazo nan ita d'aya bazata tab'a iyawa ba,bare ita kad'ai yanzun da wannan daren yace wai ta tafi,itama shiru tayi tana sunkuyar da kai k'asa dan yadda k'irjinta ke bugawa da k'arfi,shirun da yaji bata fita ba yasa shi d'an kallon gefensa sai ya ganta har lokacin bata ko motsa ba ya kalleta yana had'e rai
"What are u still waiting for..??"
A d'an tsorace ta kalleshi tana marairaicewa
"Am scared.. Ni kad'ai zan tafi..??"
Yadda tayi magana kamar za tayi kuka yasa shi kautar da fuskarsa gefe
"Da tare da waye kike tunanin zaki tafi..??"
Kallonsa tayi saurin yi tana matsowa jikinsa
"Pleasee
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 47 Chapter of 63