hanci in gina gida na alfarma, in mallaki motocin da mutane ke mafarki amma hakan zai nufe ni da sayar da gaskiyata, na sayar da zuciyata.
Rayuwata ta ginu ne bisa gaskiya.
Kuma gaskiya ba ta da tsada amma ta fi kuɗi daraja.”
(Wani sassa na taron ya fara da tafi. MC ya kalli Amal cikin girmamawa.)
Ya ce
“Tabbas, abin burgewa ne.
To Amal, zamu so ki gaya mana me ya ja hankalinki kika shiga aikin jarida? Kuma me ya sa kika zaɓi ki dinga faɗa da ƴan siyasa maimakon ki nutsu da aikinki?”
(Amal ta dafe mic kamar wacce ke maganar zuciya.)
Sannan ta ce
“Na shiga aikin jarida ne domin rayuwa ba ta bani damar yin shiru ba.
Na ga abinda ake yiwa talakawa.
Na rasa iyayena saboda tsagwaron karyar siyasa.
Su da ba su da laifi an hallaka su kawai don sun tsaya akan gaskiya. Wannan shi ya haifi ƙiyayyata da ƙarya, ya sa na rantse zan yi amfani da muryata wajen ƙwato wa marasa murya haƙkinsu.
Ina faɗa da ‘yan siyasa ne domin yawancinsu ba su da gaskiya.
Suna cin zarafin al’umma, suna karkatar da dukiyar ƙasa kuma ba wanda ke cewa a’a.
Na yarda da Allah, na yarda da mutuncina kuma idan muryata zata mutu saboda gaskiya, to inaso ta mutu cikin daraja.”
(Wani sashi na jama’a suka ce “Allah sarki!” Tafi ta kaure.)
MC ya gyara murya cikin salo ya ce
“To Amal, ba za mu bar ki da duka tambayoyin zuciya ba yanzu me zaki ce: kina soyayya?”
Taron ya ƙara kankama. Kowa yana jiran amsa. Amal ta murmusa kaɗan ta sauƙe idonta kafin ta dago ta ce
“Bana soyayya.”
MC ya ce
“A’a kenan, amma akwai wanda ya furta miki soyayya kuwa?”
Amal ta ɗan yi dariya sannan ta ce
“Eh, akwai su da yawa. Amma ni soyayya ina kallonta a matsayin shashanci ne..
Ina tunanin yawancin waɗanda ke soyayya yanzu suna soyayya da abin da suke gani, ba abin da suke ji ba. Ina buƙatar soyayyar da zata gina ni, ba wacce zata rushe ni ba.”
MC yana murmushi ya ce
“Toh... toh... toh!
Amma akwai jita-jita. Amal da Maleekh Cashbank kuna soyayya ko a’a?”
Amal ta ɗan dakata. Taron ya koma cikin natsuwa. Kowa na jiran ta ce “eh” ko “a’a.”
Ta juyo cikin natsuwa ta ce
“Ban san zancen ba.”
MC ya taɓe baki sannan ya ce
“To ba zaki mana bayani ba kenan?”
Amal ta ce
“Na san mutane da yawa na jin labarai, na ga bidiyo, na ji maganganu…
Amma a gaskiya, ni kaina har yanzu ban fahimci me Maleekh yake nufi da rayuwata ba.
Ni ba na jin kalmomi, na fi karanta hali.
Idan ya zo da gaskiya, lokaci zai bayyana.
Amma har yanzu, ina da damuwa da tambaya ɗaya: shin yana da gaskiya ko kuma yana wasa da wuta ne?”
Taro ya kaure da tafi, wasu ma sai da suka taso tsaye. Haka shafin ya ƙare cikin nishaɗi, lulluɓe da mahangar gaskiya da jarumta..
Amal na ƙoƙarin janye jikinta cikin ladabi domin komawa kujera, tana ƙoƙarin tserewa hasken idon mutane. Sai kwatsam… ƙafarta ta zame! Ta ɗagu sama tana shirin faɗuwa ƙasi amma kafin ta faɗo hannuwan Maleekh suka riƙo ta!...
Riƙe shi ta yi da ƙarfi kamar mai neman mafaka. Ta kama wuyansa, idonta cikin nashi. Shi kuwa ya riƙe kunkumin ta da hannunsa ya manne ta sosai a jikinsa, yana kallon ta da idon da babu wata magana da ya fi dacewa da shi sai shiru mai sa bugun zuciya..
Wurin ya ɗau tsit. Kowa ya tsaya, kowa ya zuba musu idanu, daga manyan baki zuwa ƙanana, daga masu kirga numfashinsu zuwa masu ɗaukar bidiyo. Har sai da wani daga cikin manyan bak’i ya katse shiru da faɗin
“Soyayya phone storee!!!”
Wurin ya kaure da dariya da tafi. Ihu da nishaɗi suka mamaye ɗakin taron. Kamar abin da mutane ke jira kenan. Wasu suna cewa
“babu shakka Amal da Maleekh soyayya ce”, wasu suna ɗaukar video suna turawa kai tsaye. Har Amarya A’isha da angonta suna dariya cikin farin ciki da tafawa.
Amal jin yanda ya ɗora hannunsa akan boob ɗin ta, sannan mannuwan da suka yi ba ƙaramin mannuwa bane domin tana jin yanda take gogan banana bananansa 🍌🫣.
Ƙirjinta ne yake wani irin dukan uku uku..
Ganin yanda ta firgita ne yasa ya ɗaga ta yayi mata ɗaukan lud'a kamar karamar yarinya, yana kallon ta da murmushin da ta rasa fassara. Ya kai ta kujera, ya zaunar da ita a hankali..
Amal cikin jin kunya ta sunkuyar da fuskar ta, miƙa mata mayafinta yayi da ya zame ƙasi, dasauri ta karɓa tare da rufe fuskarta da shi..
Haka hawaye yake gangaro mata tsabar tsananin kunya da baƙin ciki...
MC ya kalli Maleekh yana dariya ya ce
“Toh toh toh! Toh yanzu daga ‘phone store’ zuwa ‘heart store’…
Yallabai, ka iso nan. Kai ma akwai tambayoyi da ke jiran ka!”
Tafi da dariya suka sake kaurewa yayin da Maleekh ya ɗan goge gefen rigarsa ya ƙaraso ya tsaya a gaban mic. Ya sauƙe bakinsa yana kallon Amal da har yanzu take kokarin ɓoye kunyar ta.
MC cikin murmushi ya ce
“Maleekh, kafin mu fara tambayoyi da gaske wannan rikewa ce ta gaggawa, ko kuwa da shiri aka zo da ita?”
Jama’a suka yi dariya. Maleekh ya ɗan yi murmushi ya jinjina kai, ya ɗauki mic, murya cike da kwanciyar hankali ya ce
“Da ace shiri ne da na tabbata zuciyarta tuni ta bar jikinta.
Amal fa ba mace bace da zaka shirya wasa da ita..."
MC ya ce
"Toh wane hali kake ciki yanzu, ganin yadda duniya ke alakanta ka da Amal, gashi nan kun rungumi juna a bainar jama’a, kana ɗaukar ta kamar amaryarka...”
Maleekh ya ɗan yi shiru. Sannan ya ce cikin nutsuwa, yana kallon inda Amal take ya ce
“Abin da ke faruwa tsakanin ni da Amal ba ni ke da ikon fassara shi ba, ita ce zata iya fassara shi.
Ni dai na san abu ɗaya: duk lokacin da take kusa da ni, nakan ji kamar zan manta da duniya gaba ɗaya.
Idan soyayya ne wannan to ban isa na musanta ba.
Amma har yanzu, ina jiran zuciyarta ta yarda da ni ba saboda bidiyo ko taro ba sai saboda gaskiya.”
Wurin taron ya sake kaurewa da ihu da tafi. Amal ta juyo a hankali ta kalle shi. Ya kalle cikin murmushi mai ƙayatarwa. Cikin shiru suka ci gaba da kallon juna… wanda bai da fassara..
Bayan mutanen wurin sun kaure da dariya, tafi, da ihu, MC ya ƙara miƙa mic ga Maleekh yana faɗin.
“Toh yanzu da ka furta cewa ‘ina jiran zuciyarta ta yarda da ni ba saboda bidiyo ko taro ba sai saboda gaskiya’… kana nufin kana sonta ne?”
Shiru ya sake ɗaukar wurin. Amal ta ƙara boye fuskarta da mayafi. Har MC ya ɗan cije leɓensa yana jawo kulawa sosai.
Maleekh cikin bugawar zuciya, wanda bai san fassara haka ba, ba tare da yasan abunda zai furta ba ya ce
“Ina son ta.”
Yayi shiru, sannan ya ƙara da wani muryar da ta cika taron kamar ana wasa da zuciya.
“Ba saboda kowa ya ce mun dace ba, ba saboda bidiyo ba, ba saboda ta shahara ba...
Sai dai saboda wata nutsuwa da nake samu idan ina kallon idonta.
Ina son ta kamar yadda ake son zuciya a ɓoye, cikin daɗi da tsoro.”
Ya ƙarasa kalaman idonsa akan ta..
Wurin ya ɓarke da ihu. Wasu na cewa "Allah ya kaimu biki!" wasu suna ɗaukar bidiyo suna cewa “Wannan speech ɗin yafi na proposal!” Amal kuwa... hawaye ne kawai ke gangarowa a gefen fuskarta, tana kallon ƙasa amma zuciyarta na motsi da wata sabuwar jin daɗi da tsoro...
MC ya ɗauki mic ya ce:
“Maleekh, muna godiya da ka tsaya tare da mu a wannan liyafa duk da irin girman matsayin ka. Amma akwai wasu ‘yan tambayoyi daga al’umma, suna so su ƙara tabbatar wa...”
Maleekh ya gyara tsayuwa cikin kwanciyar hankali, yana duba inda Amal take zaune, har yanzu tana rufe da fuskarta da mayafinta.
MC ya cigaba da cewa
“Tambaya ta farko daga jama’a: Maleekh, me ya ja hankalinka zuwa wurin wannan bikin da aka san yana da matuƙar zaman lafiya da mutane masu sauƙi kamar mu?”
Maleekh ya murmusa, ya ɗauki mic sannan ya ce
“Wannan ba ɓoyayyen al'amari bane, kusan kowa a wurin nan yasan cewa A'isha ƙanwata ce ta jini, wacce muke uba ɗaya..."
Amal ta ɗago tana kallonsa bata taɓa tunanin Maleekh da Aisha suna da wata alaƙa ba, ashe ma alaƙa ta kusa ne sosai, ta fara tunanin meyasa A'isha take supporting ɗin ta akan ɗan uwanta..."
MC ya katse mata tunani da cewa.
“Mun gode. Tambaya ta biyu, shin kai da Amal kuna soyayya ne? Duk da ka sanar cewa kana sonta, amma munaso mu ƙara tabbatar wa...”
Maleekh ya fara tunanin cewa ashe dai a fili ya furta cewa 'yana son Amal...'
Jama’a suka kaure da dariya da ihu ‘eeeeeeeeh!’
Maleekh ya ɗan yi shiru sannan ya ce:
“Ban san inda soyayya take zuwa ba, amma zan iya faɗa da amincewa cewa Amal ita ce mace ta farko da ta sauya min tunani akan duniyar nan. Ita ce mace ta farko da ta bar ni ina tambayar kaina ko ina rayuwa cikin gaskiya ne. Ban san ko soyayya ce ba, amma na san tana da wani ɓangare a zuciyata da ban taɓa bari kowa ya shiga ba.”
MC ya ce
“Hmmm… gaskiya ka ɓata zukatan mata da yawa yanzu!”
(Jama’a suka sake dariya)
MC ya kuma cewa
“Amal ta tsaya ta faɗi cewa ba ta soyayya, kuma tana ganin soyayya shashanci ne. Shin ka shirya ka gwabza da hakan?”
Maleekh ya ce:
“Idan wannan shashanci ne, to ni zan zamo babban shashi a gare ta. Saboda rayuwa ba komai bace face gaskiya, da mutunci, da jarumta irin na Amal.”
MC ya ce
“To Amal... kin ji da kunnen ki.
Zaki bashi damar ya gwada miki gaskiyar zuciyarsa, ko dai har yanzu dai soyayya shashanci ce?”
Amal ta ɗago a hankali, ta dawo filin wurin ta tsaya tana kallon Maleekh, sannan ta ɗauki mic tana murya ta na ɗan rawa ta ce
“Ba wai bana son a so ni bane...
Na ƙi soyayya ne saboda ta riga ta ƙone min zuciya tun kafin in gane me take nufi.
Na sha wahala da yawa har na rasa iyayena...
Har aka ƙi bani aikin da nake so, aka yi ƙoƙarin halaka ni… duk saboda rashin gaskiyar mutane.”
Ta kalli Maleekh, idonta cike da ƙwalla ta ce
“Amma kai...
Kana daga cikin waɗanda suke so su rushe ni. Amma duk da haka ba ka tsaya kallon bidiyo ba, ka tsaya kallon zuciyata.
Zan iya cewa: ka na kusa da samun amincewa daga zuciyata… amma ban gama yarda da duniya ba tukuna.”
Taro ya sake kaurewa da tafi. Wasu na cewa "Alhamdulillah!" wasu suna ɗaga poster “Amaleekh Forever!” MC kuwa ya ja dogon “Wooooow!”...
Bayan jawabin, wurin ya kaure da tafi da dariya, wasu daga cikin mutane sun riga sun fara ɗaukar bidiyon Maleekh suna cewa:
"From business to feelings Maleekh in love!"
"Amal and Maleekh: Nigeria’s realest power couple."
Amal kuwa ta koma gefe bayan jawabinta, tana shaƙar numfashi, zuciyarta na bugawa cikin nauyin kalmomin ta...
MC ya ce
“To! Bari dai mu bar soyayya mu koma taro…”
Yayin da suka koma wurin zama, Maleekh ya zauna gefen Amal. Sai ya ɗago wayarsa yana rubuta..
"A shirye nake na jira shekaru, idan hakan ne zai tabbatar miki da gaskiyata.."
Amal ta karanta saƙon daga cikin wayarta. Sai kawai ta saki murmushi. Wannan karon, ba ta ɓoye ba...
A lokacin da aka rufe liyafar da addu’a, mutane sun fara watsewa. MC da masu shirya biki suka zo wurin Amal suna ƙara gode mata, suna cewa jawabin da ta yi da kuma jarumtar ta ya sa mutane da yawa sun ji ƙwarin gwiwa..
Amal tana ƙoƙarin fita daga wurin taron ne sai taga PA ɗin Maleekh ya ƙaraso da girmamawa ya ce:
“Zaki iya zuwa mu ga oga Maleekh, yana tsaye a garden. Yana son ya ce miki kalma biyu kafin ku watse.”
Amal ta ɗan yi shiru, tana jiran amsar da zuciyarta zai bata, sai kawai zuciyarta ya bata cewa
“Ki je ki ji abinda zai ce. Idan ba haka ba, zaki dinga rayuwa da tambaya a zuciyarki.”
Gyaɗa kai kawai tayi, ta bi bayan PA ɗin Maleekh zuwa waje inda Maleekh ke tsaye, yana kallon sararin sama, ganin Amal yasa ya cire glass ɗin kan idonsa..
Amal ta tsaya daga gefe, sai yace da ita
“Na san nayi abubuwa da yawa da suka ɓata miki rai. Kuma ban zo nan saboda izza ba. Na zo ne saboda zuciyata ta buga lokacin da kika ce... ‘soyayya shashanci ne’.”
Amal ta ɗan murmusa kaɗan, ba tare da ta ce komai ba..
Ya cigaba da cewa
“Zan iya zama duk abinda kika ɗauka na kasancewa mai iko, mai kuɗi, ɗan siyasa... amma a gaban ki, bana da komai face zuciyata. Kuma idan akwai matsayi da zaki iya yarda da ni daga shi, to ina so na tsaya a matsayin wanda zai kare ki, ba wanda zai yi amfani da ke ba.”
Amal ta ce da shi a hankali:
“Ka san me ya fi komai tsorata ni game da kai?”
Maleekh ya ce “Menene?”
Ta ce
“Kai mai iko ne. kallo ɗaya ya ishe ka ka lalata rayuwar mace ko ka ɗaukaka ta. Kuma ba kai nake tsoro ba... sai zuciyata. Saboda tana iya faɗa maka duk abinda yazo rai, amma a yanzu zuciyata na cewa 'a’a' bazata amince dakai ba...”
Maleekh ya kalle ta a hankali sannan ya ce
“To bari na tsaya daga nan. Idan zuciyarki ta shirya... sai ki kirani.”
Ya miƙa mata wata ƙaramar katin waya: a ciki sunan sa kawai ne da private line number. Bai ce komai ba, ya juya ya bar wurin....
《☆☆☆☆☆☆》
Bayan Amal ta koma gida, ta sanar wa Inna yanda suka yi da Maleekh a wurin taron bikin, Inna farin ciki ta shiga yi domin kullum addu’ar ta shine Allah ya kawo musu sauyi..
Inna ta ce
"To Amal yanzu me kika yanke a ranki? shin kema kina son sa ne?..."
Amal ta sauƙe numfashi ta ce
"Haba Inna sai kace daman abunda zuciyata take jira kenan? ni ba haka nake ba, ban taɓa jin inason Maleekh ba, kuma wannan al'amarin ban san yanda zan ƙira shi ba, mutane sun riga sun haɗa ni da Maleekh..."
Inna cikin jin haushi ta ce
"To banda abin ki yaron nan ya dawo bayanki fa, kiyi soyayya da shi mana ko dan kuɗin sa..."
Amal yatsina fuska tayi tana kallon Inna.
Ta ce
"Inna yaushe kika dawo haka?..."
Inna a fusace ta ce
"Ya bazan zamo haka ba? So kike na mutu cikin talauci? alhalin ga dama yazo mana hannu, to wollahi sai kin so Maleekh..."
Amal ba tare da ta furta komai ba, ta shige ɗakin ta... Tana shiga ta zauna a bakin katifar ta tana hawaye, da sauri ta ɗauko jakarta, ta ciro wani ƙaramin hoto, hoton wani yaro ne yana sanye da uniform a jikinsa, ga kuma ita kanta Amal ta rungume da yaron suna dariya aka ɗauki hoton....lokacin bazata wuce shekara biyu zuwa uku ba, tin iyayenta suna raye....
Amal tana hawaye a fili take furta
"Maleekh ban sani ba ko kana raye ko ka mutu, ban san aina kake ba, na sanu a kafafen sada zumunta da television da sunana ɗaya Amal Abdulsamaad, sunan da ka sanni dashi tin muna yara amma hakan bai sa ka nemi yanda nake ba, meyasa?, kai ka kasance abokina na musamman sannan me bani shawara, yanzu inaso ka bani shawara akan wani kulallen lamari..."
Amal tana kallon yaron jikin hoton ta ce
"Akwai wani matashin saurayi mai ji da kansa, mai girman kai amma a yanzu ya sauƙe girman kansa a gabana, yana bayyana mun saƙon zuciyarsa..."
Ta ja dogon numfashi sannan ta ce
"Kasan wani irin saƙo ne? Saƙon Soyayya, kuma kasan meye sunan sa? to sunansa Maleekh..."
Tayi murmushi sannan ta ce
"Irin sunanka gare shi, ina matuƙar girmama masu irin sunanka Maleekh, yanzu gaya mun zan amshi saƙon soyayyar sa ko kuma na sharar da shi kawai?...."
Ta ɗago hoton saitin kunnenta tana sauraron abinda yaron jikin hoton zai ce mata, ba tare da taji komai ba ta tintsire da dariya tana faɗin
"Gaskiya Abokina ka haɗu, wato ka bani shawara mai kyau, kada na nuna masa soyayya yanzu sai ya sha wahala, zan rinƙa juya masa baya, ina wahalar da shi, idan da gaske ne soyayyarsa to zai cigaba da bibiyata, idan kuma bada gaske bane zai ja baya dani, good hakan yayi yanzu wasan zai fara..."
Ta mayar da hoton cikin jakarta...
《☆☆☆☆☆》
A Bangaren Maleekh kuwa yana zaune a office ɗinsa, dake nan Kaduna, kamfanin Cashbank....sai ga PA ɗinsa ya shigo, ya ce
"Boss! Lamarin ka da Amal yana ta baza duniya akan cewa kuna soyayya, har an fara buga banner hotonka dana Amal, taken banner shine 'AMALEEKH LOVE NEVER END' shin me ka shirya a lamarin, ga shi Amal ta ƙi amince da kai..."
Murmushi Maleekh yayi yana zuƙar shisha ya ce
"Hakane, ta ƙi amincewa a gaba na amma ta amince a idon duniya, kuskuren ta kenam, bazata taɓa goge wannan ba, yanzu ne zan fara buga ball ɗina, ta nuna mun tsananin taurin kai, tayi amfani da mic wurin tozarta ni, ta wulakanta ni to zan nuna mata cewa Maleekh ba sa'an buga ball ɗinta bane, zanyi amfani da zuciyarta wurin buga wasa na.....zan fito mata a Maleekh mai karyayyen zuciya, zan nuna mata tsananin so da ƙauna, zan bada kulawa na gaskiya, zan shayar da ita ruwan zuma amma duk na wucin gadi ne, idan kanaso ka cika burinka to sai ka sauƙe girman kan ka, zan juri duk wulakancin da zata mu amma da zaran ta kamu da matsanancin sona, wanda idan bata sameni ba zata iya mutuwa, ni kuma a lokacin yi break up da ita, saina tawarwatsa mata zuciya..."
PA ne ya jinjina kai sannan ya ce
"Boss ni daman nayi mamakin sauyawarka lokaci guda akan yarinyar nan, ashe akwai kullin da kake mata, idan baka ɗauki fansa ba, bazaka taɓa samun kwanciyar hankali ba...."
Maleekh ya ce "hakane..."
《☆》 Daga wannan lokacin ne Maleekh ya fara shishige wa Amal, akoda yaushe yana kan bayyana mata zuciyarsa, cikin kalar tausayi yake zuwa mata ya nuna mata cewa 'ta sauyar da shi kuma bazai taɓa mantawa da ita ba..."
Yau da misalin ƙarfe 5 na yamma Maleekh ne ya sauƙa a gidan su Amal, bayan ya Parker motarsa a ƙofar gidan, haka yake ƙare gidan da wani irin kallon up and down domin yana tunanin abun tozarci ne ya rinƙa shigowa unguwar balle har cikin gidan...
Bayan ya shiga gidan da murmushi akan fuskarsa, yayi sallama cikin ƙwarin gwiwa...
Inna tana zaune ganin Maleekh yasa ta fara washe baki, tana masa sannu da zuwa..
A tabarma Maleekh ya zauna suka gaisa da Inna, daga baya sai ga wasu mutane sun fara shigo da buhuhhunan kayan abinci, da wasu kayayyaki na abinci da zannuwa manya a Inna...
Sai wani ƙaton akwati wanda yake cike da kayayyakin sakawa masu tsada, ya kawo su a Amal..
Maleekh yana zaune tare da Inna suna shan hirar su akan Amal, Inna tana bashi tarihin rayuwar Amal da irin taurin kai da take da shi tin tana ƙarama, sai jin sallama suka yi...
Inna ce ta ɗago tana amsa wa tare da faɗin
"Yawwa gata nan ta dawo ƴar albarka ta Amatullah..."
Amal tana sanye da dogon hijab har ƙasi da littafin Al'kur'ani mai girma ta dawo daga hadda...
Tin a waje ta ga motar Maleekh, a fusace ta shigo gidan fuska a haɗe domin bata son yana zuwa musu gida...
Amal haka take bin kayayyakin abinci da aka ajiye su da kallo sannan ta maida kanta kan akwati, still eyes ɗinta suka sake sauƙa akan manyan atamfofi guda biyar...
Amal fuska ba annuri ta ce
"Wannan fa? wa ya kawo su?..."
Inna ta ce "bakya ganin Maleekh a zaune ne?..."
Amal ta ce "Na ganshi mana, meye sa ya kawo kayayyakin nan?..."
Inna ta ce "saboda soyayya mana, yana son ki shiyasa ya fara miki ihsani, kinsan soyayya da kyautatawa yana ƙara dankon soyayya..."
Amal tana kallon Inna ta ce
"Ki ai bai samu soyayyan ba tukun, kuma ki sanar masa cewa bazai taɓa samun soyayyata ba..."
Inna turo baki tayi tana hararar Amal, sai ji tayi Maleekh ya ce
"Inna! Ki sanar mata cewa soyayyarta zai kashe ni, Inna idan bata soni ba zan iya mutuwa..."
Amal ta ce
"Inna! Ki sanar masa cewa bana son jin wannan tatsuniyarsa, Amal bazata taɓa amincewa da shi ba, sannan ki sanar masa cewa dubu ya shi waɗanda suka mutu a soyayya, don haka idan ya mutu bai dame ni ba..."
Maleekh ya ce
"Inna meyasa bazaki sanar mata irin matsalar da zan shiga saboda ita ba?..."
Amal ta runtse idonta sannan ta ce
"Inna ki sanar masa cewa yabar gidan nan..."
Maleekh ya ce "Inna kice mata bazan bar gidan nan ba, har sai ta ce tana sona..."
Amal a fusace tayi waje ta je ƙiran mutanensa da suka shigo da kayayyakin, sai gasu sun shigo gidan, cikin masifa Amal take nuna su da yatsa tare da sanar musu...
"Duk kayayyakin da ku ka shigo dashi inaso yanzu a fitar mun dasu daga gidan nan, bana buƙata..."
Inna wacce kanta ya gama ruɗe wa sai yanzu tayi magana tana faɗin
"Kina da hankali kuwa Amal? kin san cewa bamu da komai a gidan nan yanzu kuma Allah ya kawo mana kice bakya so? to in bakya so ni inaso..."
Amal ta ce "bana ƙaunar ganin kayayyakin nan, a fitar mun dasu ko na cinna musu wuta..."
Maleekh ne ya dakatar dasu da cewa.
"Bana kyauta sannan a maida mun da kyauta baya, wannan dabi'ar matsiyata ne, amma asalin mai arziki baya karɓan kyautar da ya bayar...don haka bazan maida abinda ya fito daga hannuna ba...."
Cikin fushi Amal ta ce "ko ma ina zaka kai, ka kai amma ni bana so..."
Ganin Maleekh bashi da niyyar aiwatar da abinda take so ne yasa ta fita ta ƙira matasan ungunwar da mata akan su tattara kayan ta basu kyau, su je su raba, sannan ta ɗauki akwatin ta bayar wa matan cewa su ɗauka ta bar musu, tazo zata tattari zannuwan Inna, da gudu Inna ta durƙusa ta rungumi zannuwan sosai, amma duk da haka sai da Amal ta karɓe su da ƙarfi daga hannun Inna sannan ta bayar da su....Inna tana ihu a bata kayan ta amma tass saida Amal ta rabar...
Maleekh yana tsaye ya ji Amal ta ci kwalar rigarsa tare da finciko shi, tana riƙe da kwalar sa ta ja shi zuwa waje, suna fita ta ture shi tana nuna shi da yatsa ta ce
"Warning na ƙarshe, kada ka sake kawo mana wani naka domin mu ba mabukata bane, akwai masu neman taimako da yawa meyasa baza kaje ka tallafa musu ba? to bari kaji idan na ƙara ganin ƙafarka a cikin gidan nan saina karya ƙafar..."
Daga nan ta shige gida ta barshi a tsaye, daga baya ya girgiza kai shima ya shiga motarsa, sai wani mota daban wannan security sa ne a ciki, haka suka ja mota suka tafi...
Amal tana shiga ta tarar da Inna a durƙushe sai kuka take tayi...
Amal ta zauna a gabanta ta ce
"Kiyi haƙuri Inna, kiyi ta addu'a Allah ya buɗa mun zan miki abinda kike so, har makkah zan kai ki..."
Amal bata iddasa maganar ta ba taji Inna ta rufe ta da duka, tana kuka tana faɗin
"Ai kekam bazamu taɓa yin abin arziki ba, da talaucin mu zamu cigaba da rayuwa, baki da shi amma kin samu hanyar samu shine baza kiyi amfani da damar ki ba, da haka kike cewa zaki kai ni makkah? ..."
Haka Inna take jibgar ta kamar ta samu flawa, Amal miƙe wa tayi tana ƙoƙarin kare kanta...
Inna ganin dukan bazaiyi ba yasa ta kafa haƙoran ta a saitin dantsen Amal ta garzaya mata cizo..
Amal wani ƙara tasau tare da ruga wa cikin ɗaki da gudu, tayi saurin rufe ƙofa tare da danna sakata...
Inna ci gaba da ihu take kamar wanda aka aiko mata da saƙon mutuwar wani jininta..
Tana cikin ihun idanunta suka sauƙa akan wani ɗan envelope, ɗauka tayi tare da buɗe wa, tayi kici6us da ƴan dubu-dubu sun kai ɗari...
Washe baki tayi wanda duk goro ya dafar mata da haƙora...da sauri ta cusa envelope a cikin aljihun rigarta, tana faɗin
"Allah sarki yaron kirki, Allah yayi albarka ai daman nasan bazaka bar ni haka ba....wannan hegiyar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 62