Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Hawaye na ci gaba da zuba amma sai ta yi ƙoƙarin ƙara daidaituwa, ta ce: “Maleekh… wannan ba abu ne mai sauƙi ba na sani. Abinda ka aikata… bazan manta ba. Amma… zan saurare ka. Zan saurare ka har sai na ga gaskiya.” Maleekh ya lallashi Mahaifiyarsa ta sigar lallami ba tare da ta haƙura akan batun Amal ba, ya wuce part ɗinsa... Daga baya Farha ta nufi part ɗinsa da kwalliya a fuska tana tafiya tana rangwad'a... Farha ta tsaya a bakin ƙofar falon Maleekh, zuciyarta na bugawa cikin sauri. Tana knocking, tana jan numfashi, tana tunanin yadda zata iya shawo kansa. Maleekh, yana zaune a kan kujera, ya ɗaga kai ya kalli ƙofar. "Come in," ya faɗa murya cike da fushi. Farha ta turo ƙofa a hankali, ta shigo falon, idonta na ƙasa, durƙusa wa ta yi tana gaishe shi irin na nutsuwa, fuska cike da murmushi, Duk da akwai wani shiri a cikin ranta, ta shirya tarko domin Amal, ta sa Maleekh ya ji zuciyarsa ta tsani Amal sosai. Maleekh ya harare ta da idanunsa masu tsanani, sannan ya ce cikin murya mai kaifi: "Bana son wannan shirme, kar ki raina mun hankali na, Farha. Kuma kada ki yi tunanin zan yadda dake. Idan na tsani mutum, to bana taɓa sonsa." Farha, tana ƙoƙarin riƙe hawaye, ta tambaya cikin kuka: "To, me na maka? Me yasa ka tsaneni, Yaya Maleekh?" Maleekh, cike da fushi, ya ce: "Rashin nutsuwa da naci. Na ce bana sonki, amma kin nace. Har kina haɗa ni da mahaifiyata, mahaifiyata tana yawan fushi dani. Taya zan so ki? Kuma yanzu kin nuna halinki na shaye-shaye. Babu mace mai tarbiyya da zata rinƙa shaye-shaye, babu kuma mutum mai hankali da zai auri ƴar shaye-shaye, koda mata sun ƙare a duniya..." Farha tana kuka, tana ɗaga murya ta ce "Zan daina, wallahi zan daina..." Maleekh ya girgiza kai tare da faɗin: "Da ki daina, da kar ki daina wannan ya rage naki. Kuma kada ki sake zuwa gidansu Amal. Idan na ji wani abu ya faru da ita, ki yi kuka da kanki." Ya ɗaga kai ya kalleta, sannan ya tambaya: "Wai me yasa iyayenki basu ɗauke ki sun tafi dake ba?" Farha, cikin kuka, ta ce: "Ya Maleekh, kayi haƙuri. Wallahi ina sonka. Ni na yarda ka haɗa mu ni da Amal ka aura..." Maleekh ya girgiza kai, fuskarsa cike da tsanani, ya ce: "God forbid. Please leave my room. I don’t want to see your face." Farha ta buɗe baki zata ƙara magana, amma Maleekh ya riƙo hannunta, ya ja ta waje, ya wurgata kamar kayan wanki, ya rufe ƙofar falonsa da key. Kai tsaye ya nufi bedroom ɗinsa, yana cire kayan jikinsa ya shiga bathroom domin yin wanka. Farha kuwa, cikin kuka da damuwa, ta miƙe da gudu, ta sauƙa zuwa ƙasa, kai tsaye ta nufi ɗakinta. A falon, Islam ce kawai take zaune, ta jingina kai, da murmushi a fuska mai cike da tausayi... "Kin haɗu da aiki, ƴar wahala… Nidai, Yayana Maleekh nake supported akan Amal. Bana goyon bayan ya aure ki," Islam ta faɗa a cikin ranta.. NEXT NEXT NEXT.... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 33 to 34 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Weekend Driving Lesson Ranar Asabar ce, rana mai haske, iska na kaɗa wa a garin Abuja. Maleekh ya ɗauki Amal da mota zuwa wani driving school mai suna “Skyline Driving Academy”, wuri mai faɗi da filin parking mai kyau, da alamomin hanya sosai, cike da tsaro da tsari, wanda ya dace da masu koyon tuƙi.. Amal ta shiga mota da ɗan tsoro a zuciya, tana kallon Maleekh da ido mai cike da sha’awa da jin tsoro a lokaci guda. Maleekh cikin nutsuwa yake zaune gefen ta, yana zaune a driver's seat. “Ok, Amal, yau zan koya miki yadda za ki iya *_tuƙi_* a hankali. Kada ki ji tsoro, ni a gefen ki zan kasance.” Amal ta ɗaga kai, idanunta suna haske da ƙarfin soyayya da bege ya ce “Yaya Maleekh, ni dai ban taɓa tuƙin mota ba, amma zan yi ƙoƙari.” Maleekh ya murmusa, ya ce: “Ni zan tabbatar kin koya cikin sauƙi, amma ina so ki mai da hankali sosai. Wannan ba wasa ba ne.” Ya fara koya mata yadda ake adjusting seat, mirrors, da kuma starting the engine. Amal tana bin dukkan umarninsa cikin natsuwa, duk da tana ɗan tsoro. “Yanzu danna clutch da hannun dama, sannan ki kunna gear ɗin farko. Kada ki yi gaggawa,” Maleekh ya faɗa. Amal ta yi daidai, sai dai tana ɗan razane saboda jin zuciyarta na bugawa da sauri. Maleekh ya riƙe hannunta dake kusa da gear, yana murmushi: “Kar ki ɗaga hankali, Amal. Kada ki damu. Ni zan kasance tare da ke.” A hankali suka fara tuƙi a open parking lot, jere da alamomin tsayuwa, juye, da canza gear. Amal tana farin ciki, idanunta na kallon Maleekh lokaci zuwa lokaci. Maleekh yana kallonta yana murmushi: “Kin ga, ba ruwan ki da tsoro ko matsala, abin da kike buƙata shine nutsuwa.” Amal ta ɗaga kai, idonta cike da farin ciki da ɗan ban tsoro ta ce: “Yaya Maleekh… wannan yana da wahala, amma ina jin daɗin kasancewa tare da kai.” Maleekh ya motsa gefenta, ya ɗan matsa kusa da ita yayin da suke tuƙi a hankali, cikin murya mai laushi ya ce: “Amal, ina son ganin murmushin ki yayin da kike jin tsoro. Wannan shi ne abin da nake so.” Amal ta yi murmushi mai ɗan kunya, hannunta na ɗauke da clutch, amma zuciyarta na bugawa cikin sauri saboda ƙarfin soyayya da take ji.. Maleekh ya ɗaga hannunsa, ya taɓa hannunta a hankali: “Kin san, ba na son kina jin tsoro. Ina son ki amince da ni.” Amal ta danna brakes ɗin hannu kaɗan, tana kallon fuskar sa ta ce: “Na amince, Yaya Maleekh. Na amince.” Suka tsaya kaɗan a gefen filin, suna kallon juna. Rana ta haske su sosai, iska na busa wa, kuma zuciyarsu tana bugawa da sauri saboda soyayya... Maleekh ya ce, da murmushi a fuskarsa: “Yau ne farkon zamaninmu tare, a matsayin malaminki Amal. Zan koya miki tuƙi, amma zan koya miki yadda za ki kula da zuciyarki ma.” Amal ta ɗan yi murmushi, sannan ta yi murmushi mai ɗauke da ɓoyayyen tsoro da sha’awa.... “Yaya Maleekh… kai ne mutum na musamman.” Suka cigaba da tuƙi a hankali a filin Skyline Driving Academy, suna dariyar farin ciki, suna jin farin ciki a zuciyarsu, har rana ta fara sauƙa, hasken rana ta sauya launi, alamu a saman filin tuƙi alamun yamma tayi sosai... Sun tsaya bayan wani lokaci, Maleekh ya kalli Amal, sannan ya ce: “Kin yi kyau sosai a yau. Ina alfahari da ke.” Amal ta kalli Maleekh, idonta na cike da farin ciki ta ce: “Na gode, Yaya Maleekh… Kai ne malamina na musamman.” A wannan lokacin, zuciyarsu ta haɗu cikin wani irin romance mai ɗumi, soyayya da kulawa, a tsakiyar filin Skyline Driving Academy, inda sun fara wani sabon babi na rayuwarsu... Evening Return Home Rana ta fara raguwa, hasken duhu na sauƙa, Amal da Maleekh sun gama driving session ɗinsu, duka cike da nishaɗi da dariya. Maleekh ya tsaya gefen mota, ya juya fuska ya kalli Amal: sannan ya kuma cewa: “Amal, yau kin yi kyau sosai. Ina alfahari da ke.” Amal ta kuma yin murmushi ta ce: “Na gode, Yaya Maleekh. Ban taba jin nishaɗi haka ba a driving lesson kafin yanzu.” Maleekh ya miƙe hannunsa ya taimaka mata ta fita daga mota. Sun tsaya kaɗan suna kallon junansu a ƙarƙashin hasken rana mai raguwa. “Kin shirya mu tafi gida?” Maleekh ya tambaya, fuska cike da kulawa. “Eh, ina shirye,” Amal ta amsa, tana ɗan jin kunya amma zuciyarta na cike da farin ciki. Maleekh ya tuƙa su zuwa gidan Amal.. hanya cike da nishaɗi da light conversation: “Yau na ga kin koya sosai, Amma ki tuna kada ki manta da nutsuwa idan kina tuƙin ki kada ki yi sauri kuma tinda farko ne.” Amal ta yi dariya sannan ta ce: “Ni mai hankali ce yanzu, Yaya Maleekh. Zan tuna duk abin da ka koya min.” A gidan Amal, Maleekh ya tsaya a bakin ƙofar. Ya fito sannan ya zagaya ya buɗe mata, Ya miƙa hannunsa, ya sauƙe ta daga motar yana faɗin “Sai da safe, Amal. Na gode da kasancewa tare da ni yau.” Amal ta yi murmushi, murmushi mai ɓoyayyen shauƙi ta ce: “Na gode, Yaya Maleekh. Sai da Safe, Allah ya kai ka gida lafiya.” Maleekh ya ƙara murmushi, yana kallon ta: “Zan jira gobe Sunday mu sake haɗuwa, domin weekend ba za ta ƙare ba har sai mun ci gaba da wannan nishaɗi.” Amal ta ɗaga kai, idonta cike da farin ciki: “Zan kasance a shirye, Yaya Maleekh.” Maleekh ya juya baya, ya shiga mota ya wuce gida. Zuciyarsa cike da happiness da nishaɗi, yana tunanin yanda ya fi jin daɗi lokacin da Amal ke tare da shi. Amal ta shiga gida, ta shiga falonta tana murmushi mai ɓoyayyen farin ciki da soyayya. Ta zauna a kan sofa ta duba wayarta, tana ƙaunar tunanin ranar da suka yi driving lesson tare, zuciyarta na bugawa da sauri saboda soyayya da kulawa daga Maleekh. A gefen Maleekh kuwa, ya isa gida cikin residence, ya shiga falonsa cike da nishaɗi da contentment, yana tunanin Amal, yana jin farin ciki cewa yana da wani wanda zai raba lokacinsa da shi cikin nishaɗi da soyayya. _Washegari da safe_ Sunday Morning Driving Lesson.. Rana ta fara haskakawa alamun gari ya waye sosai. Gidan su Maleekh duk sun hallaru a dining area cike da murmushi da haɗin kan iyalai, kowa ya hallaru, Abbah, Ammy, Maleekh, Arfat, Islam, da Farha duk sun zauna suna breakfast... Maleekh yana tafiyar da breakfast cikin sauri, yana duba lokaci lokaci, yana tabbatar komai na tafiya lafiya. Abbah ya kalle shi, fuska cike da mamaki ya ce: "Ina zakaje ne my son da safen nan, yau weekend ne ba aiki amma naga kanata sauri.." Maleekh ya ɗaga kai, yayi murmushi kaɗan sannan ya ce: "Wallahi Abbah, na fara koya wa Amal mota ne tun jiya, shiyasa nakeso muna fita da sassafe. Inaso ta koya sosai cikin satin nan." Ammy ta wurga masa harara tare da jan dogon tsaki, fuskarta cike da rashin jin daɗi. Maleekh kuwa bai ce komai ba, ya san halin mahaifiyarsa bazata taɓa son Amal ba. Farha kuwa tana zaune, fuska cike da raunin kishi, zuciyarta kamar ana hura wuta, amma ba ta nuna komai ba.. Bayan sun kammala breakfast, Maleekh ne ya ɗauki wayarsa ya fice daga gidan, ba tare da ya tsaya ba sai a kofar gidan Amal. Amal tana tsaye a ƙofar gidan tana jiran shi. Yana ganin ta ya sau murmushi tare da faɗin "Sorry Beb, na ɓata miki lokaci koh?" Amal ta murmushi, idonta na shining ta ce "Ai kai baka laifi, saboda kar na ɓata maka lokaci ne yasa na kammala shirina tun sallar asuba." Maleekh ya murmusa, ya buɗe motarsa, suka shiga cikin nishaɗi. Hanya ta kasance shiru amma cike da yanayin soyayya kowa jin kansa yake cikin farin ciki, dake motar Amal acan school ake barin ta, su na zuwa zasu fara.. Bayan sun isa Skyline Driving Academy, babban fili mai faɗi a Abuja, Maleekh ya tsayar da motarsa a gefen filin. Sai Motar Amal da aka fito da ita na zamani, Mercedes-Benz GLE 2025, kyakkyawa, mai amfani sosai ga sabon mai koyan tuƙi... Maleekh ya juya fuska ya ce: "Amal, yau za mu fara da basic. Zan fara nuna miki yadda ake jan motar da kanki, sannan daga nan sai mu shiga real driving." Amal ta yi murmushi mai cike da nishaɗi, ta ce "Na shirya, Yaya Maleekh. Zan koya sosai, kada ka damu." Maleekh ya fara shiryawa, ya tabbatar da seat, mirrors da steering wheel sun yi daidai. Ya tsaya a gefe yana kallonta ya ce "Ki da ki ji tsoro, sannan ki yi a hankali sosai. Nayi miki wannan kyauta saboda ina son ki koya yadda ake tuƙi lafiya da kuma zuwa yanda kike so ba tare da kin sha wahala ba, ba wai kawai nishaɗi ba." Amal ta ɗora hannunta a steering wheel, zuciyarta cike da farin ciki da jin daɗi.. "Ina godiya sosai, Yaya Maleekh. Zan yi iya ƙoƙarina." Maleekh ya tsaya a gefe, idonsa na kallonta, yana tabbatar da cewa tana fahimta. A hankali ya barta ta ja motar da kanta a filin, suna dariya da tsokanar junansu lokaci-lokaci, soyayyar su na bayyana a cikin kowane murmushi, kowane dariya da ƙaramar kulawa. Skyline Driving Academy ta cika da nishaɗi da jin daɗi a tsakanin su, har lokacin da rana ta fara sauƙa, suna cikin jin daɗi da soyayya, suna ci gaba da lesson ɗinsu... Bayan sati guda na koyarwa a Skyline Driving Academy, Amal ta koyi motar sosai, har yanzu duk wani mota zata iya ja ba tare da jin tsoro ko shakka ba. Kowace rana Maleekh da Amal suna fita da safe, suna tuƙi a filin driving academy, har sai da Amal ta koyi basics sosai, daga ja da kanta, gear changes, parking, har zuwa driving cikin traffic simulation a cikin academy. Maleekh ya tsaya gefenta, yana kallonta, idonsa na haske da alfahari ya ce: "Amal, kin yi kokarin sosai, kin koyi abin da ya kawo mu cikin mako guda... Ina matukar alfahari da ke. Ba kowa ke iya jan mota haka a wannan lokaci kaɗan ba." Amal ta yi murmushi, zuciyarta na cike da farin ciki ta ce: "Na gode sosai Yaya Maleekh. Ba zan taɓa manta wannan lesson ɗin ba. Ina jin kamar yanzu ko wacce mota zan iya ja da kaina." Maleekh ya yi dariya kaɗan, ya ja ta kusa da motar, ya nuna mata kyautar da ya shirya mata, yana faɗin "Don nuna min girmamawa akan yadda kika yi ƙoƙari, na bawa masoyiyata kyauta ta musamman certificate na iya mota, award ɗin ‘Best Driver of the Week’ a Skyline Academy." Amal ta ɗaga ido, mamaki ya bayyana a fuska: "Seriously? Wannan nawa ne? Ina matukar farin ciki Yaya Maleekh!" Maleekh ya miƙa mata award ɗin, ya ɗaga hannu, yana murmushi: "Na san wannan ba kawai kyauta bane, amma shaida ce cewa kina iya jan mota ba tare da tsoro ba. Ina alfahari da ke sosai." Amal ta ɗauki award ɗin da hannu biyu, tana jinjina masa da murmushi ta ce: "Na gode sosai, Yaya Maleekh. Wannan zai zama tunawa mai kyau ga zuciyata." Maleekh ya yi murmushi, ya ce: "Kuma ki sani, wannan bai tsaya nan ba, yau kin koyi mota sosai, kuma na san kina iya tuƙi sosai a kowane lokaci, koda a real traffic na Abuja. Ina matuƙar alfahari da ke." Amal ta ji wani irin nishaɗi, zuciyarta cike da farin ciki, yayin da Maleekh ya rungume ta kaɗan, suna dariya tare. A cikin driving academy, sauran instructors da students sun jinjina mata saboda yadda ta koyi driving a cikin sati guda, kuma award ɗin ya ƙara mata kwarin gwiwa sosai... Daga wannan rana, Amal ta zama cikakkiyar mai iya tuƙi ba tare da jin tsoro ko shakka ba, kuma soyayyar Maleekh da ita na karfi, suna cikin nishaɗi da jin daɗi, suna shirya tarurruka na driving sessions.. Bayan Amal ta samu cikakken kwarin gwiwa a Skyline Driving Academy, Maleekh ya yanke shawarar yau ita za ta tuƙa motarsu. Sun fita daga gidan da safe, rana tana haskakawa cikin annashuwa. Maleekh ya miƙe hannunsa a kan seat na passenger, yana kallon Amal da idanuwan cike da alfahari ya ce: "Amal, yau ke za ki tuƙa mu, ba zan shiga driving ba. Ina son ganin yadda kika koya, zamu zagaya cikin gari har wajen gari shiyasa na fito da safe..." Amal ta yi murmushi mai cike da jin daɗi, ta sa hannu a kan gear, ta kunna motar, sannan ta fara ja a hankali. Motar ta motsa cikin santsi, Maleekh yana kallonta yana murmushi: "Wow… ki kalli wannan smooth driving! Ina alfahari da ke sosai." Amal ta juya kanta kaɗan, tana dariya ta ce: "To fa, Yaya Maleekh, yanzu ka tsaya a gefena kana son ganin kwarewa ta kenam." Duk dariya suka yi tare da jan mota suka tafi a slow... Sun fara zagaye Lugbe Road, suna hawa zuwa Jabi Lake Mall da Central Business District na Abuja. Amal tana tuƙi cikin hankali, tana canza gears ba tare da wata tsoro ba. Maleekh yana ta dariya, yana tsokanar ta: "Ba zan taɓa mantawa da ranar da kika fara koyon driving ba… yanzu ga ki, kamar gogaggen driver..!" Amal ta yi dariya tare da tsokanar shi da cewa: "Eh! Kada kayi tunanin zan zauna haka kana driving ɗina. Domin na fi ka ƙwarewa yanzu." Maleekh ya yi dariya, ya riƙe hannun ta kaɗan: "Eh… wannan gaskiya ne. Ina ganin zan bari ki zama official driver ɗina." Suka wuce Millennium Park... motarsu tana tafiya a hankali, suna jin iska mai sanyaya jiki. Amal ta yi parking na ɗan lokaci a gefen titi, suka fito daga motar, suna kallon shimfidar birnin Abuja daga saman titi, Maleekh yana kallon Amal cike da soyayya ya ce "Amal, kina da kyau sosai a kowace rana, amma a yau, ganin ki kina tuƙi, na ga kin samu cikakken iko da komai… Ina matuƙar son ki." Amal ta yi murmushi tana riƙe da hannun shi ta ce: "Yau na ga soyayya cikin motsin mota da nishaɗin birni, Yaya Maleekh.".. Bayan sun gama hutawa.. Suka koma cikin motar, Amal ta ci gaba da driving zuwa Wuse Market da Garki, suna yawon shakatawa, suna hira da dariya a kan titi. Maleekh yana ta godewa Amal a zuciyarsa, yana ganin yadda ta koyi motar da kyau, yana jin ƙaunar ta ta ƙaru da kowace rana. Daga karshe, suka dawo gida bayan zagaye birni, Maleekh yana jinjina kai cikin alfahari ya ce "Na san yau kina jin daɗin driving sosai, kuma na ga kin cancanci duk girmamawa da kyaututtuka. Ina matuƙar alfahari da ke." Amal ta yi murmushi mai cike da jin daɗi, zuciyarta na cike da farin ciki, tana jin cewa soyayya da Maleekh ta girma sosai yayin da suke cikin nishaɗi a kan titi. Cikin begen juna suka yi sallama Maleekh ya koma gida, yanzu burinsa ya cika Amal ta iya mota yanzu sauran fara aiki a kamfaninsa.... _Bayan Sati, ranar Monday_ .. Amal Starts Work at CashTalk Yau da safe Amal ta fito daga gidan ta cikin sabuwar motarta, jeep mai kyau, wacce Maleekh ya bata, tana tuƙi kamar gogaggen driver. Hasken safe na yi mata kyalli, kowa a unguwar yana kallonta kamar tauraruwa. Yanzu itama ta shigo sahun masu kuɗi, dake unguwar da take duk masu kuɗi ne.. Tana zuwa CashTalk FM, gate security suka hango motarta. Sai da suka buɗe gate tare da gaishe ta cikin ladabi: "Good morning, Madam Amal," ɗaya daga cikin masu tsaro yace, idanuwansu na cike da mamaki. Duk ma’aikatan da suka hango Amal, sun tsaya cike da mamaki. Yarinyar da suka daɗe suna ganin a matsayin talaka matsiyaciya yanzu ta bayyana cikin ƙyakkyawan tsari da ƙwarewa: Black glass yana rufe akan golden eyes ɗinta, yana ƙara mata sirri da kwarjini. Tana sanye da Abaya mai milk color da stones a gaba, gyalen rigar ya ɗan yi masa highlights, yana bayyana kyan ta... Handbag ɗinta da wayarta a hannunta guda. Takalmanta mai tsini yana ƙara mata kwarjini a kowace mataki. Kowanne ma’aikaci yana kallonta, zuciyoyinsu cike da sha’awa da mamaki. Mata da maza, duka suna mamakin wannan canji: daga ƙaramar matsiyaciya zuwa mataimakiyar babban attajiri. Maleekh kuwa daga ofishinsa dake saman building stairs yana tsaye a glass office da ke zagaye da windows, yana kallonta yayin da yake shan coffee daga glass cup ɗinsa: "Ahh… wannan ita ce nawa… babu shakka, ta cancanci duk wani yabo," ya ce cikin ransa, yana murmushi. Amal tana motsi a hankali cikin compound ɗin kamfanin, tana lura da kowace matsala da takalmanta mai tudu zai iya janyo... tunani ta fara yi shin wata hanya zata bi don haura wa sama yanda Offince ɗin Maleekh yake... Tunani tayi gwara kawai ta shiga elevator ya kaita har sama ba tare da ta sha wahala ba.. Wani ma'aikacin saurayi ne ya nuna mata hanyar elevator, domin ta kauce wa stairs ɗin da zai kawo mata cikass da takalminta... Tana shiga elevator, ta tsaya cikin kwarjini, zuciyarta cike da farin ciki da ɗan tsoro. Ta san wannan rana zata fara aiki a CashTalk, a matsayin mataimakiyar Maleekh, wanda hakan zai ƙara mata ƙwarewa da girmamawa a gaba... Maleekh ya dan yi murmushi, zuciyarsa cike da alfahari yake faɗin "Yau za ta fara aikinta… ina fatan zata ba da kyakkyawan hoto ga kamfanin." Elevator ya tsaya a floor na 18 na ƙarshe ƙarshe... Amal ta fito cikin nutsuwa, tana shirya handbag ɗinta, tana duba ma’aikata da murmushi. Duk wanda ya hango wannan sabon fuskarta, sai zuciyarsa ta narke, domin Amal ba karamar kyakkyawa bace ta asali.. "Good morning, everyone," Amal ta ce cikin ladabi da nutsuwa, kowa ya miƙe ya amsa gaisuwa, suna kallonta cike da mamaki da yabon kwarjinta... Kai tsaye Office ɗin Maleekh ta nufa, tana zuwa tayi knocking, daga ciki ya ce: "come in." Ta shiga da Murmushin ta, bayan sun gaisa ta zauna akan kujerar dake facing ɗinsa.. Maleekh ya ɗan ɗaga kofi ɗinsa yana zuƙar juice, yana murmushi ya ce: "Amal… I knew you would shine today," ya faɗi a ransa, cike da jin daɗin ganin yadda yarinyarsa ta girma cikin kwarjini... A wannan lokacin yasa aka ƙira masa duk ma'aikacin dake aiki a wannan kamfani, za'a gudanar da meeting a office ɗin taro na musamman.. First Official Meeting at CashTalk FM Kowa ya hallaru a babban ofishin CashTalk FM, babban ɗakin taro wanda yake na zamani, da dogon table a tsakiyar room, gefen table an jera kujeru masu yawa ga ma’aikata. Hawa hawan bene na wannan kamfani sun kai goma sha takwas, kuma babu wanda zai iya zuwa floor na sama sai da elevator ko escalator. Gida ne na kamfani mai girma a Abuja, wanda babu wanda bai san shi ba. Maleekh ya tsaya a ƙarshen dogon table, kujerarsa tafi ta kowa girma, yana fuskantar dukkan ma’aikata da suka zauna a jerin kujeru a gefen table, ciki har da Amal. Ofishin yana cike da haske, tare da kyawawan kayan ofis da technology na zamani. Maleekh ya ɗaga hannu, dukkan ma’aikata suka nutsu, suna sauraren shugaban su. Maleekh ya fara magana: "Good morning everyone, I hope you all had a productive week. Today, we are here not only to discuss our weekly operations but also to welcome a new member to our team." Duk tafi suka fara yi.. Daga nan sai ya juya fuska zuwa ga Amal ya furta: "Amal Abdulsamaad will be joining us as my Assistant. I trust she will bring fresh energy and perspective to CashTalk.".. Nan ma aka kaure da tafi.. Amal ta miƙe, tana murmushi, tana gaisawa da dukkan ma’aikata, ta ce: "Good morning everyone. I’m very honored to be here. My name is Amal Abdulsamaad. Many of you may know me from my work as a journalist across different states, but today, I’m here to serve as Assistant to the CEO, Maleekh Abdul-Majeed, and I hope to contribute positively to the success of this company." Duk ma’aikata suka fara tashi tsaye suna gabatar da kansu, suna nuna ladabi da professional attitude: "I’m Ahmed, Head of Marketing." "I’m Fatima, Finance Department." "I’m Chike, IT Coordinator." PA ɗinsa shima yana daga ciki ya miƙe tare da gabatar da kansa da cewa: "I'm Ibrahim, The Manager." Bayan kowa ya gabatar da kansa, Maleekh ya ɗaga hannu tare da faɗin: "Thank you all. I’m proud of the team we’ve built here. CashTalk is not just a company; it’s a family. Every week we achieve milestones, but we also face challenges. Our goal is to continue expanding, innovate in broadcasting, and maintain our position as the leading media company in Abuja." Ya ɗan ɗauki lokaci yana kallon dukkan ma’aikata, sannan ya ƙara: "I encourage open communication, professionalism, and teamwork. Amal will be assisting me directly, so I expect everyone to support her as she transitions into this role." Amal ta zauna bayan wannan jawabi, tana jin ɗan tsoro amma kuma cikin fargaba da excitement saboda wannan shine babban mataki a rayuwarta. Duk wanda ya kalli Maleekh da Amal a

Chapter 23 of 62