zan tafi..."
Inna ta ɗaga hannu tana maimaita:
"Allah ya tsare ki Amatullah, Allah ya miki jagora."
A haka Amal ta nufi tashar mota, zuciyarta cike da tsoro da bege, kamar mace da ke barin ƙauye zuwa wani sabon duniyar da bata san menene ke jira a ciki ba.
A tashar mota mutane suna ta cunkoso, kowa da kayansa, kowa da nufinsa. Amal ta tsaya gefe da jaka ɗaya a hannunta tana jiran direban ya cika mota. Wani irin sanyi na ratsa jikinta...
Direba ne ya fara ƙwala ƙira: "Abuja! Abuja! Azo a tafi! Ku shigo mu tafi!" sai ta matso a hankali ta shiga, ta zauna a gefen taga.
Motar ta tashi, Amal ta jingina kanta da gilashin taga, idonta na kallon gari da nisan da yake raguwa a bayanta. A zuciyarta kuwa, tunani na kai komo kamar ruwan sama.
"Shin Maleekh zai karɓe ni? Shin zai ji daɗin gani na? Ko kuwa fushinsa zai ƙara muni?... Amma duk da haka ba zan iya jure wannan rabuwa ba."
Tana rufe ido sai ta ji muryar Inna na sake dawo mata:
"Allah ya tsare ki Amatullah…"
Wannan kalma ta Inna ta ba ta ƙarfin zuciya, sai ta ɗan yi murmushi da hawaye a idonta.
Hanyar Kaduna zuwa Abuja ta yi tsawo a gare ta fiye da yadda ta taɓa yi. A duk lokacin da direban ya taka birki ko motar ta yi tsalle, zuciyarta sai ta buga da ƙarfi, tana addu’ar Allah ya kai ta lafiya.
Ƴan mata biyu a motar suna hira da dariya a kusa da ita, amma ita gaba ɗaya zuciyarta nesa take can wurin Maleekh. Tana jin kamar kowane irin abu ne zai iya faruwa da ita muddin ta same shi.
Lokacin da suka fara shiga cikin birnin Abuja, hasken manyan fitilun tituna da ginin gine-ginen birnin suka bayyana a gaban Amal. Ta zaro ido tana kallon birnin, cike da bege.. domin zuwan ta Abuja na farko bata tsaya kalle-kalle ba, domin tin lokacin da Rikky Blaze ya gayyato ta zuwa podcast ɗin su, nan ma daga jirgi ne zuwa airport, anan kuma ta shiga mota sai hotel, daga hotel sai podcast, har ta koma bata wani zagaya Abuja ba...
A hankali ta furta.
"Ashe haka Abuja take... Duniyar manyan mutane, duniyar da zan yi gwagwarmaya domin zuciyata ta huta."
Ta dafe kirjinta, tana jin bugun zuciyarta na ƙaruwa.
"Maleekh... na iso."
Ta furta a hankali...
Tana sauƙa daga mota anan Amal ta fara tsorata, domin bata san ina zata je ba, shin idan ta hau napep ina za'a kaita? haka take zuru-zuru da ido...
Tambaya ta fara yi tana faɗin.
"Dan Allah aina zan samu Maleekh?..."
Gaba ɗaya kwakwalwarta ya toshe da inkiyar sunan Maleekh 'Maleekh Cashbank...' sannan ya toshe da sanin shi ɗin ɗan gidan Minister ne, but Minister meye? tinda ba iya Minister guda ɗaya bane...
Amma inda tayi kwatance da 'Maleekh ɗan gidan Minister Alhaji Abdul-majeed' zai fi sauƙi...
Amma gaba ɗaya sunan mahaifinsa ya kwanta mata a rai, ta rasa yanda zata yi..
Duk wanda tace
"Dan Allah ina neman Maleekh..." Sai dai a bata amsar da ba'a san shi ba...
Kuma a yankin da take a Abujan ba nan ne yanki masu kuɗin ba, domin yankin unguwar gomnoni da shugaban ƙasa da ministoci da chairmomi da sauran su babu wanda yake shiga yankin sai da izini...
Har dare ya fara yi Amal bata samu mafita ba, ga number Maleekh baya shiga kwata-kwata..
Dare yayi sosai. Tana zaune a bakin wani babban supermarket, hannunta na riƙe da ƙaramin jakarta. Ta gaji sosai ga yunwa na neman cinye ta gaba ɗaya, sai dai zuciyarta ta ƙi ba ta damar yin barci. Duk inda ta juyo, babu Maleekh, babu labarinsa.
Wayarsa kuwa koda ta ƙira sau nawa, sai dai ta ji muryar machine ɗin waya na cewa
“The number you are trying to call is switched off.”
Kifa kanta tayi a kan gwiwowinta tana huci da ƙarfin gajiya. Har gari ya waye, motoci suka fara cunkoso, mutane suka fara kai-komo, amma ita nan take zaune, idonta ya kumbura saboda rashin barci ga kukan da take sha...
Da ta ga babu wata mafita, sai ta yanke shawarar ta ƙira A’isha.
Lalumo lambar A'isha tayi bugu ɗaya kacal A’isha ta ɗauka, kamar daman wayar a hannunta yake..
Amal ta yi sallama cikin raunanniyar murya..
A’isha ta amsa, ta ce:
"Amal? Me meya faru kika ƙira da sanyin safiyar nan?"
Amal ta gyara zama sannan ta ce cikin rawar murya
"Ni yanzu haka ina Abuja A’isha... na zo neman Maleekh tun jiya, amma har yanzu ban same shi ba. Dan Allah ki taimaka ki turo min lambar da yake amfani da ita yanzu."
A’isha ta zaro ido kamar za ta fasa wayar, ta ce cikin mamaki:
"Abuja kuma Amal? So kike ki ɓatar da kanki? Ni fa wallahi lambar Yaya Maleekh yanzu ba ta shiga kwata-kwata...."
Amal ta fashe da kuka, ta ce:
"Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un..."
A’isha ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ce:
"Sai dai wata hanya ɗaya zan iya turo miki lambar ɗaya daga cikin ƙannensa, zasu iya kwatanta miki gidansu, ki neme shi ki ji ainihin inda yake..."
Amal ta girgiza kamar wacce take gabanta, ta ce da sauri:
"Gidansu kuma? A’a... ba zan iya zuwa gidansu haka ba."
A’isha ta ɗan yi dariya mai ɗaci, sannan ta ce:
"To shikenan, idan haka ne ki nufi Kamfaninsa, CashTalk. Ai sananne ne a nan Abuja. Idan kika je, sai ki ce a kai ki can. Wannan shi ne mafi sauƙi."
Sai yanzu Amal ta tuna. Ta share hawayenta, ta ce da ƙarfin zuciya:
"Eh, I remember... CashTalk. Zan tafi can."
Da wannan suka kashe wayar, zuciyar Amal na dukan uku-uku...
Bakin hanya ta nufa da ƴar jakarta a hannu, ta tari mai napep, tana cewa 'akai ta kamfanin CashTalk, mai napep ya amsa mata, amma sai wurin yana da nisa sosai, iya kuɗin jikinta kenam ta bashi gaba ɗaya, nan ma saida ta bashi haƙuri akan ya taimaka mata domin kuɗin basu kai ba....
Suna zuwa daga nesa-nesa ta fara ganin tsayin kamfanin, da irin tsaruwar kamfanin, ko wani ƙofa glass ne amma baka iya ganin wanda yake ciki, amma na cikin zai iya ganin abinda ke faruwa a waje...
Mai Napep ne ya ajiye ta a wurin...
Amal tana kallon bakin get ta ga security sun fi goma suna tsatstsaye dake mashigar get d'in biyu ne, akwai bangaren dama da hagun...
Abun da ta lura da tsarin shine..
Idan zaka shiga cikin kamfanin get ɗin shiga da ban yake, kuma akwai security masu duba mai shiga...
Sanna ɓangaren ɗayan get kuma idan za'a fito daga cikin kamfanin, nan ma kawai security masu duba waɗanda zasu fita...
A tsorace ce Amal ta nufi wurin, gaba ɗaya tayi wujiga-wujiga da ita, tana zuwa suka tare ta...
Cikin rawar murya da yunwa yaci ƙarfinta take faɗin
"Maleekh nake nema?..."
Ɗaga daga cikin security cikin tsawa ya ce
"Wani Maleekh?..."
Amal kamar zata yi kuka ta ce "Maleekh dai..."
Ɗaya daga cikin su ne ya ce
"Wannan fa! Boss take magana akai..."
Bata ankara ba taji security na gabanta ya ɗauke ta da mari tare da zazzaro mata ido yana cewa.
"Baki da hankali ne, cikin rashin respect zaki ambaci sunan sa kai tsaye? to bari kiji shine mai wannan kamfani gaba ɗaya...."
Security yayi magana yana nuna girman kamfanin da hannunsa, sannan ya cigaba da cewa
"Duk mu ɗin nan da kike gani shi yake mulkan mu, a ƙarƙashin sa muke..."
Wani daga cikin security ne ya ce
"Haba dallah, har sai ka tsaya kana ɓata yawun bakin ka wurin mata explain... ta je bamu san shi ba..."
Amal tana kuka tana riƙe da fuskarta da ta sha mari ta ce
"Dan Allah ku taimaka wallahi saboda Maleekh nazo garin nan..."
Security cikin tsawa ya ce
"In baki gyara wannan sunan ba sai mun karairaya ki a wurin nan..."
Cikin kuka ta ce
"To Yalla6ai Maleekh..."
Wani irin ran'kwashi security gabanta yayi mata a tsakiyar kanta yana faɗin
"To dole sai kin furta Maleekh ɗin ne a gaba?...."
Amal 6are baki tayi tana kuka hannunta a tsakiyar kai tanashafawa ta ce
"Ya Y YA Yalla6aiiiiiiii...."
Security ya ce
"To bai zo ba, sai ki jira zuwa jumawa, kije can ki zauna ki jira shi..."
Amal ta juya tana kuka hannu a tsakiyar kai yana mulmula wurin rankwashin... hannu ɗaya kuma na riƙe da jaka...
Amal ta zauna a ƙarƙashin inuwa a wajen nesa da get sosai, jikinta ya yi sanyi saboda yunwa da gajiya, ta zauna a gefe tana kallon yadda ma’aikata ke shige da ficen kamfanin CashTalk...
Ta juma sosai, tin safe har yanzu misalin ƙarfe 12 na rana.
Tana zaune kawai sai taga wata babbar mota mai haske white color, ta shawo kwana da gudu.
Motar ta tsaya a gaban gate, sai ga security suka ruga da gudu, suna buɗe masa get cikin ladabi da girmamawa.
Motar ta shige cikin harabar kamfanin, aka rufe gate. Amal ta runtse idanu da sauri, zuciyarta na bugu da ƙarfi: “Shine kenan... Maleekh ɗin da nake nema, Alhamdulillah.”
Cikin ƙasaita da izza ya fito daga motar, farin suit ne a jikinsa da gilashi akan dara-daran idanunsa. A mashigar kamfanin ma wasu security ne, yana shiga kai tsaye ya nufi ginin babban office ɗinsa da ke saman bene, ko kallon gefe baya yi, sai kamshin turarensa da ya cika sararin wajen. Duk ma'aikata sai gaishe shi suke, da haka ya nufi can upstairs...
Amal ta miƙe a zabure, zuciyarta kamar za ta fito ta hancinta.
Ta nufi security da gudu ta ce
"Dan Allah naga ya zo, inason ganinsa... ku sanar masa ina nan."
Security ɗin suka kalle ta da mamaki, ɗayan ya ce:
"Ashe baki tafi ba har yanzu? Mun manta ma kina nan."
Sai suka kalli juna, daga bisani ɗaya ya ɗaga wayarsa ya ƙira office ɗin sama...
A cikin ofis kuwa, Maleekh yana zaune a kujerarsa mai juyawa, yana duba wasu takardu. Telephone kan table ta fara ringing, ya yi shiru bai ɗauka ba har sai da ta jima tana ruri. Daga ƙarshe ya ɗauka a gajiye...
Muryar da ke can ta ce:
"Sir, akwai ba'kuwa tana son ganinka a ƙasa."
Maleekh ya ɗan yi shiru, bai ma tambaya ko wacece ba, sai kawai ya ce da gajeriyar murya:
"Let her in."
Bayan ya sauƙe wayar, sai ga knocking.
Ya bada izini, wata ma’aikaciyar kamfanin ta shigo da takardu. Bayan ta gaishe shi, ta fara bayani cikin nutsuwa:
"Sir, wannan ne jadawalin ribar da muka samu cikin sati, da kuma matsalolin da muke fuskanta a kasuwa..."
Suna cikin wannan tattaunawa sai ga wani knocking a ƙofa. Maleekh ya ɗan tsuke fuska, ya ce:
"Come in."
Security ne ya shigo, sai kuma Amal ce ta biyo bayansa...
A hankali Maleekh ya ɗago kai ya kalli bakin ƙofa, sai kawai eyes ɗinsa suka sauƙa akan kaɗaɗden fuskar Amal, wacce ta sha wahala, fuskar tayi fari ƙal kamar ba jini a jikinta...
Ji yayi duniyar kamar ta tsaya cak.
Ya zazzaro da idanunsa kamar wanda aka fizge shi daga mafarki...
"Amal...?!" ya faɗa a zabure, ya miƙe tsaye da sauri daga kujerarsa.
Amal ta tsaya a bakin ƙofa, hawaye na zuba daga idonta, zuciyarta cike da farin cikin ganin sa.
Shi kuma zuciyarsa ta buga da ƙarfin gaske tsakanin ƙiyayya da soyayya da mamakin zuwanta Abuja...
*NEXT NEXT NEXT....*
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 19 to 20
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Ofishin ya yi shiru, sai ƙarar AC da ƙaramin turirin shishan da ya fara fita daga gefe..
Maleekh ya tsaya cike da mamaki, hannayensa a dafe saman tableɗingabansa, yana kallon Amal kamar zai cinye ta. Amal kuwa ta kasa magana, sai hawayen da ke bin kuncinta.
Cikin ƙasa da murya ta ce:
"Na zo ne... don na ganka."
Maleekh kallon ma'aikaciyarsa yayi sannan yayi mata nuni da ta basu wuri, shi kuwa Security yana kawo ta ya juya...
Maleekh ya yi dariya mai cike da ciwo, ya dafe ƙirji yana kallonta.
"Kin zo Abuja... bayan abinda kika yi mun? Bayan wulakancin da kika yi a bainar jama’a, kike da ƙarfin halin tsayawa a gabana?"
Amal ta ɗan runtse ido, zuciyarta na tsananta bugawa ta ce
"Ban zo in yi faɗa ba, Maleekh... ban zo in tuna da baya ba. Na zo ne saboda zuciyata bata iya haƙuri da rashin ka ba."
Ya matsa kusa da ita, yana hura numfashi mai ƙona zuciya ya ce
"Rashi na? Haba Amal! Ni kike faɗa wa haka? Kin manta da marin da kika mun a bainar jama’a? Kin manta da wulakanci? Kin manta da mutuncin da kika zubar mun?"
Amal ta share hawayen fuskarta da sauri, tana mayar da ƙarfin hali ta ce
"Eh, na tuna da duk abinda ya faru. Amma ni mace ce... zuciyata baza ta taɓa ƙin ka ba. Ina sonka Maleekh, amma ban yarda da kai ba har yanzu. Ina son in ga gaskiyar zuciyarka."
Maleekh ya tsaya cak, ya ɗan ja numfashi da ƙarfi, sannan ya yi murmushi mai sauti, murmushin da ya ɓoye muguwar manufa.
"Kin zo Abuja don ki tabbatar da zuciyata? To, Amal... zan nuna miki zuciyata. Amma ki shirya... soyayyata ba zata zo miki a sauƙaƙe ba."
Ya juya da sauri ya koma kujerarsa, ya zauna yana juyawa da kujerar, ya buga table da ƙarfi sannan ya ce
"Amal, ke ce kika sa na zubda hawayen baƙinciki. Zan sa ki biya duk abinda kika yi... ta hanyar soyayya."
Amal ta kalle shi da idanu masu cike da fargaba da soyayya a lokaci guda, zuciyarta na bugawa a hankali ta furta
“Shin so ne ko fansa yake nufi?”
Maleekh ne ya ɗago yana kallonta, lokaci guda ya saki murmushi sannan ya taso ya zo front ɗinta tare da riƙo hannun ta a hankali, yana kallon fuskarta cikin nuna kalar tausayi ya ce
"Akwai kalmar da kika faɗa… Amal. Ina son ki maimaita mun."
Amal ta runtse idonta, hawaye na tsiyaya a fuskarta, sannan cikin rauni ta furta:
"Ina sonka Maleekh…"
A hankali ya saki ajiyar zuciya, ya zaro murmushi wanda ya gauraye da jin daɗi da wata muguwar manufa ya ce
"Kin san me Amal? Duk soyayyar da za ki nuna mun… bazata kai wanda nake miki ba. Ni na riga na nutse a cikin sonki fiye da yanda kike zato. Kin zo Abuja saboda ni, and I appreciate you for that."
Amal ta share hawayenta da hannunta tana kallon shi cikin tsantsar gaskiya ta ce
"Ban iya zaman kadaici ba… nayi gwagwarmaya da kaina, amma zuciyata ta kasa daina tunaninka."
Ya matso sosai, ya kamo fuskarta da hannunsa, yana shafar gefen kuncinta da yatsa ya ce
"Kin tabbatar min da matsayina a zuciyarki… matsayi wanda babu wanda ya isa ya kwace. Ki kwantar da hankalinki Amal, Maleekh bazai taɓa gujenki ba. Na yi nesa da ganin ki, amma a zuciyata… kina kusa da ni kullum."
Amal ta yi ɗan dariya mai sauti, cikin hawaye tana jin kamar an sauƙe mata nauyin da take ɗauka tun tsawon lokaci.
Ta yi saurin faɗowa jikinsa, ta jingina kanta a faffadar kirjinsa, tana shakar ƙamshin turarensa da ke ƙara narkar da ita.
Shi kuwa ya zagaye ta da hannuwansa, yana bubbuga bayanta a hankali tamkar yana rarrashin yaro.
a hankali cikin kunnenta ya ce
"Shhh… komai zai yi kyau…"
Amal ta runtse idonta, ta yi murmushi cikin hawaye, tana jin ɗumin soyayyarsa ya lull6ube ta.
Sai dai a cikin zuciyar Maleekh, wani murmushin gefen baki ya bayyana. Wannan farin ciki da yake ji ba wai saboda soyayya ba ne, saboda nasarar matakin farko na ɗaukan fansa ne.
Yana maganar zuci
"Zan barta ta nutse sosai cikin soyayya… zan barta ta saba da ni har ta daina iya numfashi ba tare da ni ba. Daga baya… sai na karye zuciyarta. Zai fi komai daɗi in ga Amal da kanta tana neman Maleekh, amma Maleekh yana juya mata baya."
Sai ya lumshe ido, ya jingina habarsa saman gashinta, yana ci gaba da dariya a zuciyarsa.
Ita kuwa Amal tana jin zuciyarta ta samu wurin hutu, tana hawayen farin ciki a kan kirjinsa.
Bayan suka gama rungumar juna a office ɗinsa, Maleekh ya ɗan ja Amal da hannunta cikin natsuwa ya ce
"Na san yunwa ta galabaita mun da ke… bari mu fita restaurant, kin sha wahala daga jiya har yau."
Amal ta yi ƙoƙarin share ragowar hawaye a fuskarta tana ɗan murmushi ta ce
"Wallahi gaskiya ne, ban ci komai ba tun jiya…"
Maleekh ya ƙara sakin murmushi, yana kallonta da wani irin yanayi da zai sa kowace mace jin daɗi. Ya ce
"To shikenan, yau ni zan ciyar da masoyiyata."
A haka suka fita yana riƙe da hannunta, suna fita harabar kamfanin wurin parking motoci suka nufa, yana zuwa ya buɗe murfin gaba ta shige, sannan ya zaga yo driver side ya shiga shima, a ɗari suka bar kamfanin....
Security da suka mata wulakanci ganin yanda ta samu matsayi yasa suka shiga mamaki, har suna faɗin
"Yarinyar da muka raina wa wayo ashe ba ƙarama bace, cabbb Allah ya taimake mu kada ta sanar wa Boss abinda muka mata..."
Haka suka gama mitar su...
Maleekh da Amal ne suka nufi wani babban restaurant mai kyau. Amal tana zaune tana dube-duben ƙawataccen wurin. Maleekh kuwa yana ta duba menu yana zaɓa mata abinci da ruwan sha.
Bayan sun ci abinci sosai, ya ɗan jingina ya na kallonta da murmushi. Ya ce
"Na san kin gaji sosai… bari mu wuce gida ki huta."
Amal ta ɗago kai tana kallonsa da sauri ta ce
"Gida kuma? Wane gida kake nufi?..."
Maleekh ya ce
"Gidana da nake hutawa. Ba komai a can sai nutsuwa. Zaki huta, zaki sha iska ki samu kwanciyar hankali."
Amal ta girgiza kai da sauri tare da faɗin
"A’a, Maleekh… bazan iya zama a gidanka ba. Na san kai mutum ne mai daraja, amma idan mace da namiji suka haɗu a wuri ɗaya da babu kowa, shaidan ne na ukun su. Ka nema mun gidan wata matar aure kawai, zan kwana acan."
Maleekh ya tsaya yana kallonta, sai ya yi dariya mai taushi. Ya ce
"Amal… kina da imani da tsoron Allah sosai. Wannan shi ya sa nake ƙaunarki. Amma idan hakan ke damunki, to shikenan… zan kai ki gidan mu."
Amal ta zaro ido da mamaki. Ta ce
"Gidan ku kuma? Kai… ina tsoron iyayenka. Me zasu yi tunani idan suka ganni?..."
Maleekh ya ɗan jingina ya na kallonta da ido mai cike da sirri ya ce
"Kar ki damu da wannan, masoyiyata. Ni na fi kowa sanin iyayena. Zan gabatar da ke da kwarin gwiwa, domin ni ban zan taɓa ɓoye ki ba."
Amal ta kasa ɗauke idonta daga nasa. Zuciyarta ta cika da farin ciki. Ta furta cikin natsuwa..
"Ka tabbata babu matsala?..."
Ya jinjina kai cikin tabbaci. Yana faɗin
"Ba matsala… ki kwantar da hankalinki."
Wannan maganar ta ƙara narkar da Amal, domin a zuciyarta ta tabbatar da cewa Maleekh da gaske yake sonta.
"Toh kenan… wannan shi ne soyayya ta gaskiya," ta faɗa a zuciyarta.
Shi kuwa a ransa murmushin gefen baki ya sake bayyana. Wani sashe na zuciyarsa yana jin kamar ya ci nasara sosai domin ya san zai fi sauƙi ya karya ta idan ya riga ya gabatar da ita da iyayensa....
Bayan sun kammala gidansu, Maleekh ya nufa da ita..
Arfat da Islam suna zaune a babban falon gidan suna hira da dariya, kowannensu da waya a hannu. Cikin ɗan lokaci sai suka ji ƙarar motar da ta shigo harabar gidan.
Da sauri suka leƙa daga window, suka gane motar Yayan su ce. Duk suka koma zaune cikin shirin tarbarshi.
Sai ga Maleekh ya shigo cikin falon da sallama mai ƙarfi.
Arfat & Islam cikin fara’a suka ce
“Sannu da dawowa Yaya!”
Maleekh yana amsa musu cikin natsuwa, ya ce
“Yawwa, sannu… .”
Kafin su sake tambayar wani abu, sai ga Amal a bayansa ta shigo cikin gidan da sallama a ranta, tana sunkuyar da kai saboda jin kunya.
Arfat da Islam suka zaro ido suna kallonta da mamaki. Sai ga Farha ta sauƙo daga upstairs, alamar daga ɗakinta ta fito, tana riƙe da glass cup a hannunta mai ɗauke da lemon juice, cikin falon ta shigo ba tare da ta kalli kowa ba, ta zauna tana sha a hankali... ɗago kai tayi zata yi wa Maleekh magana, idonta ne ya sauƙa akan Amal, a zabure ta miƙe da sauri kamar wacce aka mintsina..
Farha cikin ɗaga murya ta ce
“Wacece wannan kuma?…”
Maleekh ya tsaya cak, fuskarshi babu alamar wasa. Ya ce
“Amal ce… matar da zan aura.”
Fuskar Farha ta ƙara canzawa, ta ɗaga muryarta cikin kishi da takaici tana faɗin
“Amal kuma? A cikin wannan gidan?…”
Arfat da Islam ne suka miƙe tsaye
Arfat ta ce
“Amal wannan matsiyaciyar yarinyar nan?”
Islam itama ta ce
“Wallahi Yaya, ka rasa macen da zaka so sai wannan ‘yar talaka?”
Maleekh ya daka musu tsawa har sai da suka razana, ba iya su kaɗai ba hatta Amal dake bayansa sai da ta tsorata,
har suka tsaya cak cikin tsoro..
Maleekh cikin ɗaga murya ya ce
“Ku dakata mun! Shin ina wasa da ku ne?…”
Arfat da Islam suka yi tsumu, zuciyarsu na harbawa saboda sun san Yayan nasu idan ya ɗaga murya, ba mai iya tankwarar da shi...
Farha kuwa ta matse baki cike da kishi, ta kuma furta cikin masifa:
“Ƴar talakawa ce mana! Ka rasa mata sai wannan jakar matsiyaciya zaka kawo mana gida? Ni ɗin meye aibu na?…”
Maleekh yana zazzaro mata ido cikin tsananin ɓacin rai ya ce
“Farha! Gidan ubana ne ko gidan ubanki? Idan kuma baki da amsa, ki yi shiru kafin ki tashi min hankalin da zai sa na kakkarya ki a gidan nan...!”
Arfat da gudu ta haura stairs, zuciyarta na ɓari, ta je ta ƙira Ammy da gaggawa.
Ba a jima ba sai ga Ammy ta fito daga ɗaki da hanzari ta sauƙo falo, fuskar ta cike da masifa da mamaki. kallo ɗaya tayi wa Amal tayi saurin kawar da kanta tana kallon Maleekh..
cikin ɓacin rai ta ce
“ Maleekh saboda ka raina mutane yanzu abun naka har ya kai ka kawo mana wannan matsiyaciya gidan nan? Wato duk duniya ka rasa mace sai wannan jakar marar mutunci?…”
Amal ta sunkuyar da kanta, ta kasa cewa komai, hawaye na taruwa a idonta.
Maleekh kuwa yana kallon Ammy ya ce
“Ammy, ki saurare ni da kyau. Duk masifar da za ki yi, na yanke hukuncina. Dole Amal ta zauna a gidan nan, babu wanda zai hanata. Kuma wanda ya wulakanta ta tamkar ya wulakanta ni ne.”
Falon ya ɗauki shiru. Arfat da Islam suka shiga tsoron kallon Yayan nasu, suna taɓa juna da alamun tsoro.
Maleekh ya juya ya kalli Islam da idon da yasa ta firgita.. Ya ce
“Islam, tashi ki je ki gyara mata ɗaki. Ina so ta samu wurin kwana mai kyau.”
Islam ta tsaya cak tana kallon Ammy, amma saboda tsananin tsoron Yayan natan yasa ta juya cikin jin haushi ta tafi ɗakin domin shirya wurin....
Ammy ta cije lebenta, amma babu yanda ta iya domin ta san halin ɗanta idan ya tsaya akan abu mai mai dakatar da shi sai Abbansa...
Maleekh ya juyo ya kamo hannun Amal, ya zaunar da ita a kan babban sofa, ya furta cikin natsuwa da izza
“Ki zauna a nan, ki kwantar da hankalinki. Ana kammala gyara miki ɗaki sai ki shiga ki huta. Kin ji?”
Amal ta ɗaga kai a hankali, zuciyarta cike da tsoro da kunya, amma kuma tana jin wani farin ciki na musamman cewa Maleekh ya tsaya tsayin daka saboda ita.
Farha kuwa ta kasa zama. Kishi ya rufe mata ido, tana ta hararar Amal kamar idanunta za su faɗo. Zuciyarta na karyewa, tana jin kamar duniya ta tsaya mata saboda yadda Maleekh ya fito fili ya kare Amal a gaban kowa.
Bayan Islam ta gyara ɗakin da ƙyar saboda tsoron Yayan ta, Maleekh ya kai Amal da kansa...
Cikin tausasawa ya ce
“Kin ga! Ki kwantar da hankalinki, ki huta sosai. Ni zan koma part ɗina. Idan kin buƙaci wani abu, ki sanar.”
Amal ta gyaɗa kai cikin kunya, ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 62