ta ce,
“Alhaji… dan Allah kuyi haƙuri. Ku aura masa Amal.
Mahainfinta ya yi alkawarinta ga shi tun tuni, ka sani. Kuma hakan ya zama wasiyya”
Abbah ya yi shiru… yana tunani.
Maganar Ammy ta kama shi sosai, domin alkawari ne. Amma kuma ba zai yi wa Amal dole ba.
Ya juyo a hankali yana kallon Amal.
“Amatu… ga shi nan. Maleekh yayi miki rashin adalci, amma kin ga matsayin alƙawari, kin ga matsayin zuciyarsa.
Kin ga yadda yake nan a gaban jama’a saboda ke…
To yanzu ki faɗa da bakinki:
Kin yafe masa za ki aure shi?”
Duk wurin ya yi shiru.
Ko kukan jariri babu.
Kowa ya zuba ido yana jiran amsar Amal.
Ta ɗago kai a hankali, hawaye na kwance kan fuskarta. Ta ce da muryar da ke rawar zuciya:
“To Zayd fa?..”
Abbah ya shafa gemunsa, ya juyo da natsuwa:
“Zayd zai yi haƙuri.
Shi ma ya san aure kaddara ce.
Tunda dama bai yi tsammanin zai same ki ba.”
Amal ta riƙe zuciyarta tana huci cikin tausayi da baƙin cikin abin da Maleekh yayi mata..
Amal ta ce,
“Shi Maleekh ɗin zai yi haƙuri… domin ya rasa ‘Amal’ har abada.
Na yafe masa… amma bazai taɓa samun aurena ba.”
Wannan kalaman sun yi masa tasiri fiye da harbi.
Maleekh ya yi saurin matsowa ya rikice, ya kama ƙafarta yana kuka kamar wanda aka yanke masa hukuncin kisa:
“Amal dan Allah! Dan Allah ki karɓeni… dan Allah ki bani dama…
Ki aure ni… ki taimakeni… ki ceci rayuwata…”
Amal ta janye ƙafar, hawaye na gangarowa, bata ko dube shi ba.
Abbah ya kama kafaɗar Maleekh ya ɗaga shi tsaye da ƙarfi. Yana cewa.
“Kayi haƙuri ka je ka nemo wata.
Ba zan yi mata dole ba.
Ka fita… ka bar mutane nu nutsu.
Malamai na yin wa’azi.”
Maleekh ya so magana, amma Abbah ya dakatar da shi da hannu.
Ya ƙira securities biyu da ke bakin ƙofa..
"Ku fita dashi. Ana karatun kur'ani..."
Ya furta tare da juyawa..
Securities suka tasa shi a gaba, suna jansa suna tura shi.
Shi kuwa sai kuka yake, muryarsa na karyewa:
“Amal! Amal please! Kar ki min haka!
I love you Amal!
I love you wallahi!
You are my life… my everything…
Amal please!!!”
Suka fice da shi har waje, muryarsa na ƙara nisa da su… har ya ɓace...
Amal kuwa zuciyarta ta rikice.
Kaman numfashinta ya tsaya..
Soyayyar da take ɓoyewa ta taso da ƙarfi, amma dama ta riga ta yanke hukunci.
Ta zauna tana kuka, Inna ta rungume ta.
Kowa ya zazzauna zuciya cike da girgiza.
An cigaba da wa’azi a hankali, malamai suka soma karanta ayoyi da hadisan aure.
An fara raba kayan ci da sha.
Sautin ƙira'a ya cika wurin, yana sanyaya zukata.
Bayan haka aka fara ɗaukan hotuna.
Amal na tsaye amma ba ta cikin duniyar nan, tunaninta gaba ɗaya yana wurin. Maleekh.
Ana hotuna ciki walwala.
Ita kuwa zuciyarta na can a rikice..
Islam da Arfat sam basu ji daɗin wannan al'amarin ba.
Farha duk da Zayd ɗan uwanta ne amma tafi son Amal da Maleekh...
Ammy ma bata cikin walwala.
Iyayen Zayd kuwa suna farin ciki ne saboda zasu samu dama akan Amal..
Abbah, Ammy, da Amal suka ɗauki hotuna masu kyau a tare..
Sai kuma suka ji ƙarar engine mai ƙarfi daga waje:
FWMMMMMM!!!
Kowa ya dakata da hoton da yake yi.
Engine ɗin ya ƙara kusantowa da gudu!
Gabanin kowa ya gama juyawa..
TAAASHHH!!!
Gilashin ƙofar da aka kawata ya FASHE ya tarwatse!
Superbike mai sheƙi ya bankaɗo ta ciki cikin gudun wuta!
“Wayyo Allah!!”
Mutane suka firfita suna ja da baya.
Wanda yazo kan Superbike ɗin yana rufe da helmet, babu wanda ya gane ko wanene ko mai ya zo yi..
Ya shigo tamkar tauraron fim!
Ya yi sufa ɗaya zuwa tsakiyar taron.
Kafin a ce .U. ya yi wani irin juyi da kwarewa, ya miƙa hannu ɗaya ya cafke Amal!
Kamar iska ya ɗaga ta sama tamkar ba ta da nauyi ko kaɗan!
Kafin kowa ya ankara, ya ɗora ta a gaban Superbike ɗin, ya danne throttle…
FWMMMMMMMM!!!
Hayaƙi ya turnuke wurin!
Mutane suka watse!
Kafin a iya rufe baki
SUN ƁACE!
Kamar wuta a cikin iska.
Wanda ya ɗauke Amal cikin mintuna kaɗan ya ratsa titin Abuja ta baya.
Amal na ta bugun ƙirjinsa, zuciyarta na huci cikin tsoro da fargaba.
Cikin kuka da rawar murya take faɗin..
“Waye ne kai…kai ɗin waye? Kodai Maleekh ne ya ƙara turowa a sace ni?…”
Bayan sun bar cikin garin gaba ɗaya, mutumin ya buɗe fuskarsa..
Ya cire hular helmet, sai ga fuskar Maleekh tana sheƙi da annashuwa...
Amal, ganin Maleekh, sai ta buɗe baki tana kallonsa.
Idanunta cike da hawayen farin ciki da tsoro.
Amal cikin kuka, ta daki ƙirjinsa da ƙarfi.
“Maleekh… kai ne…!”
Ta zagayo da hannayenta ta rungume shi sosai, ta kifar da kanta akan ƙirjinsa.
Maleekh kuwa sai dariya yake, cike da nasarar karɓe fiancée ɗinsa a ƙarƙashin ikon wani...
Suna tafiya cikin daji mai tsanani.
A wani tsauni, Maleekh ya tsayar da machine ɗin, domin wurin babu kowa.
Kukan tsuntsaye kawai ke yawo, dajin babu mai shiga...
Ya sauƙe Amal a ƙasa.
Amal ta tsaya kallon wurin cike da tsoro, zuciyarta na huci.
Cikin rawar murya da tsoro ta ce.
“Maleekh… ina ne nam?
Ina ka kawo ni?
Nan fa kamar ba Nigeria ba ne… wannan… wannan daji ne kawai…”
Maleekh ya murmusa, ya ɗaga kai, idonsa na sheƙi da annashuwa.
Cikin muryar natsuwa, cike da ƙarfin zuciya ya ce,
“Idan muka ƙara tafiya kaɗan, zamu iske ruwan Maliya…”
Amal ta buɗe baki sosai, tsoro ya cika zuciyarta.
Hawayen mamaki da fargaba suka zubo a fuskarta.
Cikin rawar murya ta ce:
“Akan iska kake tafe ne?
Na ga akan machine muke… har mu bar Abuja… mu isa kusa da Maliyaaa???”
Maleekh ya yi murmushi mai sanyi, ya riƙe hannunta cikin nasa.
Ya matso kusa da ita, ya rungume ta sosai, yana jin fiancée ɗinsa a ransa gaba ɗaya.
Cikin ƙarfi zuciya ya ce.
“This machine is not like any other… it can take us anywhere we want safely.”
Amal ta tsaya kallonsa, hawaye na kwance a idanunta, zuciyarta na bugawa da sauri.
Maleekh ya matsa kusa da ita, yana riƙe kunkuminta tare da manna ta a jikinsa, yana jin farin ciki na mamaye shi...
Yana murmushi ya ce
"Wasa nake miki bamu zo red sea ba, Maliya ai ba'a Nigeria take ba..."
Cikin shagwaɓa ta ce
"To inane nam?.."
Ya ce "har yanzu bamu fita daga Abuja ba, kawai na ratso ta daji ne..."
Ya rungume ta sosai, hannayensa na zagaye da kunkuminta, yana jin zuciyarta na bugawa da sauri a ƙarƙashin ƙirjinsa.
Dajin da ke kewaye da su, kukan tsuntsaye da numfashin iska mai sanyi yana ƙara musu nutsuwa.
Amal cikin muryar tsoro ta ce,
“Maleekh… wannan wurin… yana lafiya kuwa? Please Ina ka kawo ni?”
Maleekh cikin murmushi, idonsa na sheƙi ya ce,
“Ki kwantar da hankali, fiancée ɗina… wannan wuri na musamman ne. da iska mai sanyi, babu kowa da zai cutar da ke. Wannan machine ɗin na musamman ne, ba kamar sauran ba… zai kai mu ko ina lafiya.”
Amal ta ɗora hannunta akan ƙirjinsa, zuciyarta cike da haɗuwa da tsoro da farin ciki.
Hawayen farin ciki suna zubo a fuskarta.
Cikin rawar murya, tana kallon Maleekh ta ce.
“Maleekh… idan har kana tare da ni, zan iya amincewa da komai… amma ina son sanin komai a bayyane.”
Maleekh ya ɗago kai, yana kallonta da ɗumin zuciya.
Ya ɗan sumbace ta akan goshi, yana riƙe da ita sosai.
Ya hau machine ɗin sannan ya ce "hau..."
Ta ce "Ina muka nufa daga nan?.."
Ya ce "Zamu ƙara gaba, nan ba tsaro, koda yaushe za'a iya afko mana..."
Ta hau bayan machine tare da zagayo hannayenta ta gabansa ta riƙe shi sosai, kanta a kwance kan bayansa..
Suka ci gaba da tafiya da machine ɗin zuwa wani ɓangare na daji, bakin ruwa ya bayyana a gabansu, ruwan yana da haske sosai..
Anan suka sauƙa domin hutawa..
Amal ta tsaya, ta ɗaga hannunta, ta taɓa ruwan, tana jin sanyinsa mai daɗi.
Amal cikin murmushi ta ce.
“Maleekh… wannan wurin… yana da kyau sosai… kamar wani aljanna duniya...”
Maleekh cikin dariya ya ce.
“Duk wannan wuri na musamman ne, saboda ke. Na kawo ki nan domin ki ga cewa babu wani da zai iya ɗaukar ki daga gare ni. Wannan wuri shine tsaro da zaman lafiya, musamman ga fiancée ɗina.”
Amal ta rungume shi sosai, ta sauƙe kanta cikin ƙirjinsa.
Hawayenta sun haɗu da dariyar farin ciki, zuciyarta na cikewa da jin daɗi.
Amal cikin annashuwa ta ce,
“Maleekh… yanzu na fahimci cewa, komai da ya faru a baya… kuskure nane. Kuma kaine kafi cancanta da na kasance dakai...”
Maleekh ya ɗaga kansa yana kallonta, ya ƙara matsa kusa da ita, yana jin fiancée ɗinsa na ɗaukaka a ransa...
Suka zauna a bakin ruwa ga duhu ya shiga sosai domin dare yayi...
Yana zaune ita kuwa tana kwance ta ɗora kansa saman cinyarsa..
Maleekh cikin tsantsar so yana shafa sumar kanta ya ce,
“Amal, ki sani, ba zan bar ki ga kowa ba. Ko da menene ya faru a baya, yanzu ni da ke ne… rayuwa ɗaya, soyayya ɗaya. Zan yi komai don kiyaye fiancée ɗina.”
Suna zaune a bakin ruwa, suna kallon hasken wata a sararin sama...
Kowane numfashi, kowane motsi, ya kasance mai haɗa su da juna.
Daji da iska da ruwa sun kasance kamar shaidar soyayya da tsaro..
Ƙafafunsu na cikin ruwan suna wasa da ruwan..
Dare ne sosai domin yanzu misalin ƙarfe 11 ne.
Da wayan Maleekh suke ganin haske amma sai dai ba network kwata-kwata balle a dame su da ƙira...Sai power bank ɗinsa da yake chargy.
Ita kuwa Amal bata tafo da waya ba..
Cikin lokaci ƙanƙani bacci ya ɗauke Amal..
Shi kuwa yana zaune yana shafa gashinta a hankali,
Haka suka zauna a bakin ruwa, suna jin daɗin zaman lafiya da soyayya..
A wannan dare, dajin da ruwan sun zama alamar soyayya, tsaro, da alkawari tsakanin Maleekh da Amal...
Maleekh haka ya kwana a zaune, Amal a kwance kan cinyarsa har lokacin asuba yayi..
Duba wayarsa yayi yaga ƙarfe biyar, dake ba masallaci balle su ji ƙiran sallah...
Tasar da Amal yayi ta hanyar sumbatar bakinta.
Jin ana tsotsar lips ɗinta ne yasa ta farka..
Tana lumshe ido a hankali.
A hankali ya furta
"Beb! Time to pray, daga nan sai mu hau kan hanya..."
Ta furta tana lumshe ido
"Sai ina?.."
Ya ce "Sai gaba..."
Haka suka tafi sukayi alwala da ruwan kogin.
Sannan suka tsayar da sallah..
Bayan nan suka hau kan machine.
A tsawon hanyar, babu motsi face ƙarar tayar mota. Sun shigo cikin jihar Taraba ta gefe, hanyar ta fara canzawa, bishiyoyi sun rufe hasken rana..
Tafiya sosai suka yi har suka shiga gindin dajin Mayogwo, sai suka tsaya anan...
Babu wani alamar mutum ko ƙauye.
Babban daji ne sosai..
A gefen su kuma, kogi ne a kwarare kamar yana bacci. Ruwa mai duhu, mai sanyi, mai zurfin da ba za ka iya ganin ƙasa ba. A saman ruwan ana iya ganin yadda ganyen bishiya ke sauƙa su narke a hankali.
Masoyan suka tsaya suna sauraron dajin.
Wani irin shiru ne ba irin na wancan ba wanda suka bari, shiru ne da yake cike da sirri, da fargaba, da kuma wani abu mai ban tsoro...
Suna tsaye a bakin kogin inda ƙasan kasa yake da launin toka...
Ga wani irin sanyi mai ratsa jiki..
Wani iska ne ta ratsa ta, gashin kanta na kaɗawa, ta lumshe ido tana sauƙe numfashi mai nauyi...
Maleekh ganin yanda take ta kakkarwar sanyi ne yasa ya cire rigar sweter ɗinsa, ya ɗora mata, shi kuwa ya tsaya da farar singlet ɗinsa..
Ya ce mata,
“Ba wanda zai same mu a nan… mu kaɗai ne.”
Ta kalle shi, idonta cike da hawaye da fargaba ta ce,
“Ka tabbata za mu iya kwana a nan?”
Ya kama hannunta, ya ɗan matsa yana jin yatsunta sun yi sanyi.
“Inasonki… kuma zan kare ki. Wannan dajin… yau tamu ne.”
Da suke magana, kogin ya yi wani ƙaramar ƙara kamar yana magana da su. Dajin ya yi wani irin motsin iska wanda ya sa jikin su ya yi sanyi, amma a lokaci guda ya ƙara haɗa su wuri guda.
Suka zaɓi wani ƙaramin fili a kusa da babban dutse, gefe da kogin. Suka kunna ƙaramin wuta, hayaƙin yana tashi sama yana ɓacewa cikin duhun bishiyoyi..
Dare bai wani yi sosai ba domin ƙarfe 6 na yamma ne, amma tsabar bishiyoyin da suka rufe sararin sama yasa dajin yayi duhu ƙirin..
A wannan wurin.
Babu wanda zai san inda suke.
Duhu mai zurfi ya lulluɓe komai. Wutar da masoya suka kunna ta fara ƙara tash,tash,tash… tsatsatsa…
Iska ta yi sanyi...
Dajin ya ƙara yin shiru.
Sai kukan kogin da suke ta ji..
Suka zauna gefe da juna, begensu ya haɗu, hannunsu riƙe da na juna kamar kar su sake...
🌬️
Ta lumshe ido zata yi magana sai ta tsaya cak.
Tana jin wani sautin iska.
Fiiuuuuuuuuuuuu…
Fiiuuuuuu… fiiuuuu…
Kamar iska ce ke kiran wani abu a ciki.
Ta matsar jikinta kusa da shi.
“Ka ji motsi kuwa?” ta tambaya da wata murya mai kunshe da tsoro.
Ya kalleta.
Ya ɗan murmusa, duk da shi ma jikinsa ya ɗauki sanyi.
“Ki kwantar da hankalinki. Dajin ne yake motsi da dare. Nan babu mutane… babu mai cutar da mu.”
Amma kafin ya gama, guuuuuummmm wani irin sauti ya ƙara a cikin dajin. Kamar wata bushashshiyar bishiya ce ta faɗi, ko kukan wata dabba.
Ya tsuke baki.
Ita kuwa ta riƙe wuyansa kamar zata shige cikin zuciyarsa.
Wani tsuntsu ya yi tsalle daga reshe, yana yi masu kuka: Krrr… krrr… krrr…
Sai kuma ya tashi da sauri kamar yana gudun wani abu.
Daga can cikin inuwa, ana jin ruffa-ruffa na ganyayyaki kamar mutum yana tafiya cikin hankali, yana takowa a sannu, yana ƙoƙarin kada su gane shi.
Cikin tsoro ta ce,
“Wani yana nan?”
“Ba mutum bane… dabba ce.”
A cewar Maleekh..
“Wacce dabba ce zata yi tafiya kamar mutum?”
Ta ƙarasa tana zazzaro ido waje..
Shiru yayi..
Ita ma ta gane shiru ɗin nasa akwai alamun wani abu.
Kogin ya yi bugun ruwa mai ƙarfi, kamar wani abu ya faɗa ciki ko ya taso daga ciki.
Sai jikin su ya tsaya.
Tana girgiza kafa cikin tsoro ya ce.
“Ina tsoron wannan wurin… wallahi ina ji kamar wani na kallo na.”
Ya janyo ta jikinsa sosai, ya jinginar da kansa da nata.
“Ki saurara… komai lafiya. Wannan dare anan zai zama sirrin mu. Da safe zamu fita mu nemo wani wuri mafi kyau.”
🔥
Wutar na haskaka su, tana bayyana farin idonta da motsin hawaye. Suka zauna suna jin ɗumin wutan..
Tana rufe da rigarsa ta jingina kanta a kirjinsa.
Numfashin su biyu na gauraye cikin iska mai sanyi.
A cikin wannan duhu mai tsoro, soyayya ta ƙaru.
Ta kama hannunsa, tana ɗan matsawa a hankali.
“Ka tabbata ba za ka bar ni ba?”
Ya ce mata da murya mai taushi.
“Ba a barin mace a daji… musamman wacce nake so.”
Sannan… wani abu ya tunkaro su.
Daga cikin duhun dajin, daga can inda kogin yake, an fara jin wata ƙara mai sanyi:
Hooooooo… hooooooo…
Kamar dai mutum ne...
Wani lokaci kamar dabba ce, wani lokaci kamar iska ce, amma da ƙarfi… tana matsowa a hankali.
Ta ɗago da sauri, idonta ya cika da tsoro.
“Kai… wannan kamar tsuntsu. Kamar dabba. Kuma wannan… kamar—”
Ya miƙe tsaye a hankali, ya kamo hannunta.
“Ki tsaya a baya na… kada ki yi magana.”
Wutar ta yi ƙara, kogin ya yi bul-bul-bul kamar yana jan wani abu.
Daga nesa, an fara ganin inuwa tana motsawa tana kusantowa…
_NEXT NEXT NEXT_
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 81 to 82
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Inuwar nan tana tafe a hankali, amma tabbas ba irin tafiyar dabba ba ce.
Ba ta da sautin ƙafa.
Ba ta da nauyi.
Kawai tana shawagi… tana matsowa kamar iska mai rai.
Wutar gabansu ta fara ja da baya kamar tana tsoron ta.
Kogin kuwa ya yi wani irin bulk-bulk-bulk kamar wani abu ya taso daga ƙasan sa.
Ta riƙe hannunsa sosai yatsunta suna rawa..
“Wannan… wannan aljani ne?”
Muryarta ta kaɗe kamar na yarinya
Ya ɗaga mata hannu ya ce ƙasa-ƙasa
“Ki yi shiru…”
Daga cikin duhu, shafan iska ya fito, ya buɗe hanya ga inuwar da take matsowa… har ta bayyana.
Fuskarta ta fara bayyana… ba mutum ba ce, ba kuma dabba ba…
Da fari abin ya yi kama da mace.
Doguwar mace.
Siril, ba ta taka kasa ba.
Gashinta yana shawagi kamar yana cikin ruwa.
Idanuwanta kuwa… farare tsaf, babu ƙwayar ido.
Jikinta smokin haske ne, ba ta da nauyi, tsayin ta daidai yake da reshen bishiya.
Ta tsaya ƙarshen wutar su, tana kallon su ba tare da motsi ba.
Kamar ba ta numfashi...
Lokaci guda ta yi magana… ta cikin iska ba ta baki ba.
Fiiuuuuuuuuuu… har kun zo…???
A zuciyarsu suka ji muryar, ba a kunne ba...
Ta durƙusa a hankali, ba tare da ta taɓa ƙasa ba, ta ƙarasa zuwa bakin wutar…
Amal idonta cike da hawaye, ta ce a hankali:
“Kai… wacece wannan?”
Abin ya juya kai yana kallon su duka biyun, kamar yana nazarin su.
Sai ta ɗaga hannunta mai tsawo, siriri kamar kara, ta nuna su:
“Ba ku kamata ku kasance a nan ba…
ku biyu kun karya doka…
kun shiga hannu…”
Ta ja iska.
Tana yawo a cikin iska.
“…kun shiga dajin da ba’a bijirewa… dajin Tsakar-Malmai.”
Maleekh ya matso gaban ta, yana kare masoyiyarsa Amal ya ce,
“Me kike nufi? Ba mu zo domin cuta ba. Muna neman mafaka ne kawai.”
Sai ta yi murmushi, murmushi marar rai.
“Mafaka?” ta ce.
“A dajin Malmai… mafaka ba ya zuwa da mutane.
Sai dai tsoro.
Shan wahala…
ko kuma… fatan fansa.”
Ta matsa kusan su. Tana shirin kai hannunta kusa da fuskar Amal.
Amal ta ja baya da sauri.
Inuwar ta tsaya cak.
Ta sauya launin ido daga fari zuwa duhu.
“Na daɗe ina jira…
Kujerar ku biyu… tun kafin a haife ku…
an rubuta cewa zaku zo wannan dajin a daren yau.”
Suka kalli juna cikin tsoro.
Wani irin bugu zuciyar Maleekh yayi..
“Me ake nufi? Wane ne ya rubuta haka?”
Sai iska ta buga cikin dajin, ganyayyaki suka fara kaɗawa kamar ana tsawa.
Inuwar ta juyo da sauri ta kalle shi.
Idanuwanta sun yi ja kaɗan.
“Wanda yake sane da komai.
Mahafinku ya taɓa kawo sunanku nan…
shekaru dubu da suka wuce.”
Amal ta zaro ido waje ta ce,
"Kaii shekaru dubu ai ba'a halicci Nigeria ba ko?.."
Aljanar ta ɗaga hannun ta.
Wutar ta mutu..
Daji ya zama baƙi ƙirin...
Kogin ya yi ihu kamar mutum ya faɗa ciki...
Sai fitacciyar inuwar ta ƙarasa da wani zafi ta ce:
“Ku biyoni.
Ko ku mutu.”
Da zarar halittar nan ta ce “Ku biyoni ko ku mutu,” idanuwan Maleekh suka kaɗa....
Zuciyarsa ta fashe da tsoro.
Jininsa ya hau sama...
Ya kamo hannun Amal da ƙarfi kamar kada ta zame.
“Mu gudu! Kada ki kalli baya!”
Ba ta ko yi tambaya ba, tsoron da yake fuskarta ya isa ya gaya mata cewa wannan ba lokacin maganganu ba ne.
Suka yi tsalle suka fice daga wajen ruwan kogin, suka kutsa cikin kauraye ganyayyakin da suka rufe hanya.
Suka isa wajen da suka ajiye machine ɗinsu, Superbike.
Ya hau da sauri
Ya ɗaga mata hannunta ya ɗora ta a bayan sa
Ta rungume shi tana rawar jiki
Kanta a bayan wuyansa
Hawaye suna zubowa saboda tsananin tsoro.
“Ka kunna! Ka kunna! Ka kunna da hanzari!” ta furta, muryarta na rawa.
Ya buɗe choke
Ya danna
Machine ɗin ya yi fummmm–wummmm–wummmmmm!
Dajin ya yi duhu sosai.
Bishiyoyi suna bugun gefen su, wasu rassan suna shafan jikinsu kamar hannun mutum.
Sauti ɗaya rak ya biyo bayan su:
“Hooooooooooooo…”
Bai yi kama da ihu na dabba ba.
Bai yi kama da iska ba.
Kamar an haɗa muryar aljanar da kukan tsuntsaye tare zuwa sautin da ya fi ƙarfin kunne...
Amal ta matse shi sosai, hawaye suna fita ba tare da numfashi ba.
“Maleekh! Wannan sautin ya na biye da mu! Ya na tahowa!”
Ya ce da ita cikin tsananin murya.
“Ki rufe kunne! Kada ki saurari komai! Ina nan… ba zan bari mu hallaka ba!”
Machine ya na tsalle-tsalle akan ƙasa mai cike da duwatsu, wani lokaci yana ɗaguwa sama, kamar zai faɗi, amma bai tsaya ba.
A bayan su, wani farin haske yana shawagi a sama, yana bin su cikin sauri kamar hazo..
Ba ya tangalewa.
Ba ya tsayawa. Sannan ba ya gajiyawa.
Dajin ya yi sanyi sosai.
Amal tana ihu, tare da faɗin
“Wayyo! Innalillahi! Tana kusa! Wallahi ta kusan iso mu!!”
Ya jawo handle ya yi wani irin mugun zaro da machine ɗin:
“Hold me tight!”
Suka ƙara gudu ta hanyar mutuwa ko rayuwa..
Ya ce:
“Mun kusan fita daga ɓangaren dajin! Ki daure!”
A gefe kuwa, muryar halittar ta sake cika sama:
“Kuuuuuuuuuuu… ba ku tsere ba…”
Amal ta fashe da kuka...
🏍️💨
Machine ya shige cikin wasu manyan duwatsun, hayaƙi tana fitowa cikin duhu, duwatsun suna gogan jikinsu saboda matsin wurin..
Suka fita kai tsaye daga cikin duhun.
Sai iska ta buso su.
Dajin ya yi haske wato sun wuce ɓangaren da halitta ke iya fakewa..
Machine ya tsaya da ƙyar saboda zafin gudun.
Maleekh ya yi numfashi mai nauyi.
Amal ta faɗa jikinsa tana kuka, tana rawar tsoro.
“Ka… ka ceci ni…” ta furta cikin kuka.
Ya rungume ta sosai, yana jin hucin numfashinta a kan kirjinsa.
“Ba komai… kin ji? Ba zan taba barin ki ba.”
Amma… kafin su samu nutsuwa…
Sai suka ji ƙara daga cikin dajin da suka baro, wanda iyakarsu sai an ratsa ta cikin manyan duwatsu..
“Babu inda za ku je… zamu sake haɗuwa.”
Daga dajin da suka tsere, suka koma wani daji daban, ba duhu sai nau’in tsoro daban...
A nan, akwai ƙaramin gari a cikin daji, ba a gani daga nesa saboda bishiyoyi sun rufe shi.
Mutanen garin kuwa… mafarauta ne masu ƙarfi, masu jini a jikinsu, masu kamannin daji.
Suna amfani da wuƙaƙe, kibiyoyi, gatura, da makaman gargajiya.
Jikinsu ba kaya sai ganyayyaki da ƙugiya ɗin da sahon farautarsu ke rataye a wuyansu.
Da suka shigo cikin dajin, kafin su fahimci komai sai suka ji “Ffff! Ffff! Ffff!”
Wuƙaƙe suna miko musu hari daga kowane ƙarshen bishiya..
Maleekh yana riƙe da hannunta haka suke sunsunkuya.
Kafin su yi magana, mutane goma sha biyu suka fito suka kewaye su.
Dukkansu babu kaya, sai ganyayyaki da ke rufe da ƙugunansu..
Ganin mutane kewaye dasu yasa suka durƙusa cikin tsoro, domin fuskokin mutanen sun sha baƙin fenti..
Suka karɓe su da wuƙaƙe a hannu, sannan suka ɗauke machine ɗin..
Shugaban su, Babban Mafarauci, ya yi gaba..
Idonsa jajir, kan sa yana rufe da fatar bauna..
Ya kalle su sama da ƙasa ya ce da muryar da ta cika daji:
“Me ke tafe da ku? Wa ya ce ku shigo dajinmu?”
Maleekh ya yi saurin ɗago wa yana kallonsa, saboda jin tsananin muryarsa.
Amal ta riƙe hannunsa tana kuka..
Ya ce cikin tsananin tsoro:
“Hanya ce ta kawo mu nan… mun tsere… wallahi ba mu zo cutar da kowa ba.”
Mafarautan ne suka fara magana ta tsawa:
“Ƙarya ne! Duk wanda ya shigo dajinmu sai an yanka shi! An ci naman sa! Wannan dokar kakanninmu ce!”
Amal ta fashe da kuka, tana rawar jiki.
Ta durƙusa gaba ɗaya, ta ɗago kai, tana roƙonsu.
“Dan Allah… kada ku kashe mu… ba mu da laifi…
Ni da shi masoya ne… aure za a ɗaura min da wani wanda bana so…
Shine muka gudu… don mu tsira…”
Dajin ya yi shiru.
Mafarautan suka kalli juna.
Wasu suka yi shewa:
“Ahhh! Masoya!!”
“Aure! Aure!!”
“A yayanka su! A ci naman su tun kafin su yi aure!”...
Matar shugaban mafarautan ce ta fito.
Babbar mace ce, mai taushi fiye da mijinta.
Ta duba Amal sosai ta hango tsoron gaske a idanunta.
Ta ce da muryar mace mai hangen zuciya.
“Kada a yanka su.
Masoya da suka gudu don juna ba a kashe su.
Wannan al'ada ce ta tsohuwar mahaifiyata…
A bar su… a kula da su.”
Mafarautan suka yi shewar daji..
Shugaban mafarautan ya ɗaga hannu, ya ce:
“To! Idan wannan ne hukuncin mata…”
Ya juya ya kalle su, idonsa na haske.
“Za mu ɗaura muku aure a nan… yanzun nan… domin wannan shi ne tsawon zaman dajinmu.”..
Duk mutanen suka fara tsalle!
Suna shewa!
Suna rawa!
Suka fara busa ƙaho da ƙarfi domin shugaba ya yi magana..
A nan cikin dajin, a tsakanin ganyayyaki da wutar da aka kunna da rassan itatuwa, aka kafa da'ira.
Mutanen gari sun yi tsaf, suna tsatstsaye.
An sa Amal a tsakiyar da'irar.
Maleekh kuma a gefe.
An ɗaure su da igiyar reshe.
Shugaban ya yi rantsuwa cikin harshen daji, ya ɗaga wuƙa sama, ya ce:
“An ɗaura aurenku da dokar daji, da dokar ruwa, da dokar mafarauta.
Daga yau… ku biyu miji da mata ne.”
Mafarautan duk suka yi ihu:
“Auuuuuuuuuuuuuuuuuuu!!!!”
Amal tana kuka.
Ba kukan farin ciki ba sai na tsantsar razana...
Maleekh ya riƙe hannunta, ya ji hannayenta sunyi sanyi kamar kankara..
Ya ce cikin ƙasa da murya:
“Ki da kiji tsoro… ki sani… ina nan tare da ke.”
Mafarautan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 52 Chapter of 62