Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Maleekh ya sauƙa a Nigeria, motoci sun fi goma waɗanda suka zo ɗaukan sa a airport, iyayensa sun yi matuƙar farin ciki da ganinsa tsawon shekaru a ƙasar england, duk da su ma iyayen suna yawan zuwa ƙasashen waje har su ziyarce shi... Maleekh shine babban ɗa a wurin Minister Alhaji Abdul-Majeed. sai ƙannen sa mata biyu, bayan ya bawa iyayensa isasshen lokaci washegari da safe sai da ya ziyarci gidan rediyon sa mai suna CashTalk FM. ba ƙaramin kuɗi aka kashe a wurin ba, komai na musamman, duk ƙofofi da winduna na glass ne, upstairs mai hawa takwas ne a gidan rediyo, amma ba'a fara gudanar da aiki a cikin sa ba, wurin yana nan a tsare sai matakan tsaro da aka zuba da sojoji.... Yana gama wa da nan kai tsaye Kaduna ya nufa amma a wannan lokacin shi kaɗai yake tafe ba escort, domin idan ya isa akwai wasu security sa acan masu jiran sa... A gidan rediyo Rayuwa FM kuwa an sanar musu cewa zasu yi babban baƙo, an tanadar masa wuri na musamman..... Ya sanar wa mutanen sa cewa sai ya fara sauƙa a masauƙinsa dake GRA kafin ya zo gidan rediyo... Bodyguard's ne sun kai sha biyar waɗanda suka je gidan rediyo, suna tsaye da bindigu a hannayensu, kowa yasan cewa za'a yi babban baƙo kuma sun san ɗan hamshaƙin mai kuɗi ne, mai ji da kansa domin kaf Kaduna babu wanda bai san Maleekh cashbank ba da Mahaifinsa Alhaji Abdul-Majeed... Da wasu baƙi na musamman masu kuɗi kafin kace mai wurin ya cika da motoci masu bala'in tsada, domin kaf ƴaƴan masu kuɗi ne babu talaka a cikin su ko mai rufin asiri.. kafin zuwan Maleekh.. Director gidan rediyo ya sanar wa Amal ta waya cewa ta fito da wuri domin akwai hira ta musamman da zata jagoranci shirin..... ★★★★★ A cikin wata safiya mai ɗan sanyi a Kaduna, Amal ta tashi daga karamin ɗakin da ta ke tare da Inna, tsohuwar da ta raineta tun tana shekara biyar. Ta shirya cikin doguwar riga mai launin ruwan-saman madara ta ɗaura gyale a kai, sannan ta ɗauki jakar aikin gidan rediyo. Yau akwai wani shirin tattaunawa da za ta jagoranta, ba ta san cewa shi ne zai zama karo na farko da za ta haɗu da Maleekh ba. A gefe guda kuma, Maleekh ɗan gidan Minister yana sanye da rigar designer, agogon zinare a wuyan hannunsa ya fito daga sabon masauƙin sa a GRA, lokacin yanzu yana ɗokin bayyana sabbin manufofin da zai tallafa wa kamfaninsa. Manajan sa ya shirya masa hira da tashar rediyo domin ya yi tsegumi ga jama’a game da sabuwar kungiyar tallafawa al’umma da su ka kafa. Amma a zuciyarsa, hira ce kawai za ta ƙara masa sunayen jaridu, ba wai ya damu da jama’a ba. A Studio ɗin Rediyo Lokacin da Amal ta ga jerin baƙin da za su shiga shirin, ta ɗan murmusa, sunan Maleekh Cashbank ne a rubuce, a cikin ranta Ta ce: “Hmm, waɗannan ƴan manya ne da ke yawan ɗaukan iska,” ta furta a hankali. Ta gyara na’urorin sauti, ta ƙira editan shirin Ta ce: “Ku tabbatar an dai-daita mic ɗin babban baƙon, kar ya zo ya fara ƙorafin ‘voice quality.’ ” Ba a ɗauki lokaci ba, ƙofar studio ta buɗe. Shigowar Maleekh ta cika ɗakin da ƙamshin turarensa mai tsada, sannan yana wani ji da kai kamar shi kaɗai ne mai kuɗi a faɗin duniya, Ya kalli Amal daga sama zuwa ƙasa, kamar yana tantance ta. Maleekh a zuciyarsa yana faɗin " Haka kawai za a ce wannan ce mai jagorantar shirin? Wata ƴar diploma da ita...." Amal a zuciyarta Ta ce: "Tafiya ɗaya ne da yaro mai jin kansa, zan nuna masa ba duka za a wulaƙanta ba...." Amal ta yi masa sallama cikin ladabi da kwanciyar hankali. Ta nuna masa kujerar zama da microphone, sannan ta fara shirin da sallama ga masu sauraro. Sauti na kunna intro jingle… Amal cikin sassanyar murya Ta ce: “Assalamu alaikum warahmatullah. Masu sauraro barkan mu da warhaka daga tashar Rayuwa FM. Ni ce Amal Abdulsamaad, kuma yau muna da baƙo na musamman… ɗan siyasa, ɗan kasuwa, kuma ɗan gidan Minister, Malam Maleekh Abdul-Majeed. Barka da zuwa.” Maleekh cikin dariyar ƙasaita Ya ce: “Barkan ku Amal. Yana da kyau ganin yadda kuke ƙoƙari… duk da cewa studio ɗin nan da ku kanku sai kun ƙara tsabtace kan ku kaɗan...” Ya ƙare kallon ta daga sama. Amal cikin murmushin ladabi Ta ce: “Za mu yi la’akari da shawarar ka… mun gode. Za mu fara da tambaya: mene ne dalilin dawowar ka Najeriya bayan shekaru da dama a ƙasashen waje?” Maleekh Ya ce: “Hmm, kin sani, wasu daga cikinmu ba za su iya rayuwa da ƙalubalen waje ba. Ni dai na ɗauki digiri na acan, sannan na yi Masters ɗina a England, sannan na yanke shawarar cewa lokaci ya yi da zan taimaka wa ƙasata. Yana da wahala ki fahimta idan baki taɓa fita daga Najeriya ba.” Amal cikin sakin fuska Ta ce: “Wannan ra’ayi ne mai kyau. Amma na sani yawancinmu da muke nan cikin ƙasar muna iya bada gudummawa, koda ba mu taɓa fita ƙasashen waje ba.” Maleekh ya zaro ido, yana ɗan dariya sannan Ya ce: “Toh kenan Amal, idan zan tambaye ki a ina kika tsaya ne a karatun ki?” Amal Ta ce: “Na gama diploma a fannin sadarwa. Kuma ina ci gaba da karatu yanzu a matakin digiri.” Maleekh ya kwashe da dariya tare da faɗin: “Diploma? Subhanallah. Wannan ai kamar keke ne a gaban mota! Amma kinsan ba laifin ki ba ne, ai ba kowa ke da damar zuwa Cambridge ba.” Ya tafa hannayensa biyu yana dariyar raini yana faɗin: “Ku dai ƴan talakawa ku na jin kuna da ilimi, amma…” Ya kawar da fuskarsa gefe, sannan ya tofa yawu a gefe ɗaya kamar yana ƙyamar abin... Amal ta ɗaure fuska, tana danne zuciyar ta cikin kwanciyar hankali Ta ce: “Eh, gaskiya ne. Ba kowanne ne yake da damar zuwa Cambridge ba. Amma ba kowanne ɗan Cambridge ne ke da ilimi na ainihi ba. Wasu su na da takarda, amma babu tarbiyya. Wasu kuma suna da ƙwarewa da mutunci ko da suna da ‘diploma’.” Maleekh ya ɗan ɗaga gira cikin ɓacin rai Ya ce: “Oh, ke kina nufin kina da ƙwarewa a fannin rediyo kenan?” Amal Ta ce: “Eh. Kuma wannan ya fito fili. Hira ce kake yanzu da ni kuma jama’a suna sauraron ka. Za su iya auna nagarta, ba sai na gaya musu ba. Ilimi ba wai inda ka karanta shi ba ne kawai, har da yadda kake amfani da shi.” Maleekh yana ɗan harararta Ya ce: “Kin iya magana sosai. Amma ki sani, a wannan ƙasa, kuɗi da suna ne ke tafiyar da komai. Ba diploma ba.” Amal Ta ce: “Eh, amma a kowanne lokaci ƙasar da ke gina kanta kan kuɗi da girman kai faɗuwa ƙasi take Amma ƙasar da ke amincewa da kishi, basira da aiki tuƙuru tashi sama take....” Gaba ɗaya shiru suka yi cikin studio. Edita da sauran ma'aikata suna kallon juna. Kowa na sauraron tattaunawar.. Maleekh ɗan yatsina fuska ya yi, tare da ɓoye mamakin sa Ya ce: “…Wannan magana ce mai nauyi. To mu gani a ƙarshe, wanne ne zai fi ƙwaƙwalwa ko kuɗi?” Amal ta ɗan saki murmushi tare da faɗin: “Ko wanne yana da kyau a mallake su, zaman lafiya tsakanin su ne zai gina ƙasa. Ba raini ba.” Sauti yana ƙarewa da outro music... A karshe shirin ya kare, Amal ta yi godiya ga Maleekh, Da suka fito daga studio, Maleekh ya matsa kusa da ita yana faɗin: “Kin san dai baki yi min adalci ba, maganar ki ya yi yawa....” Amal ta sake murmushi ta ce: “To idan ka san kana son yabo, ka shirya tambayoyi kafin hira amma ni aikina na ke yi.” Kafin ya yi ƙarin magana, wata ƙiran gaggawa ta shigo wayarsa. Maleekh ya yi tsaki ya juya, ya tafi ba tare da sallama ba amma zuciyarsa ta fara tunanin wannan yarinya mai kuzari. Maleekh ya bar studio ɗin da zuciyar sa a ɓace, amma yana ɓoye baƙin cikin sa saboda mutanen da yake tare da su... . Amal ta dawo ofis cikin numfashi mai nauyi, amma tana jin daɗin yadda ta tsaya da mutuncinta. Wannan ya zama matakin farko na rikici, kuma watakila farkon juyawar tunanin Maleekh kenan ...… Bayan rana guda, wani bidiyo na shirin ya yi trending a social media. Masu sauraro sun yaba da yadda Amal ta ɗan yi masa “ƙwaɓe” cikin ladabi. A gefe guda, an fara sharhi kan girman kai da rashin natsuwar Maleekh. Wannan ya sa Maleekh ya ji ɓacin rai sosai amma kuma akwai wani abu a ransa: sha’awa da mamakin jarumtar Amal. ★★★★★ Amal ta dawo gida da yamma, ta jingina jakar ta gefe, ta cire gyalen kanta cikin gajiya. Fuskar ta cike da damuwa, amma tana ƙoƙarin ɓoye shi. Inna ta leƙo daga ɗaki ta ga a yanda Amal take kamar akwai damuwa, Ta ce: "Ke Amal, lafiya? Yau kin dawo kamar wadda aka buga da tukunya." Amal ta zauna a tabarma, ta sauƙe ajiyar zuciya sannan ta ce: "Inna... yau kam ban ji daɗin aikin ba. Na haɗu da wani mutumin da ba ni da kwarin gwiwar sake hira da shi....." Inna ta matsa kusa da ita Ta ce: "Waye kuma? kin san ke ba kya son hayaniya. Me ya faru?" Amal Ta ce: "Sunansa Maleekh… ɗan gidan Minister, shine wanda muka yi hira da shi daga England, An zo hira da shi a studio… amma ki san me Inna? Bai da kunya. Wai don na faɗi cewa na gama diploma, sai ya fara raina ni, yana cewa kamar na koyi keke ne a kan hanya, sai har ya tofa yawu yana nuna kyama." Inna ta ɗaga hannuwa tare da faɗin: "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Tofa! Yaro yazo studio don ya ɗaga kansa, amma sai ya saukar da kai da harshensa. Wane irin mutum ne haka?!" Amal ta ɗaure fuska tana faɗin: "Inna, ya ƙira ni yar talakawa a fakaice, yana dariyar raini. Amma ban bari ya raina ni ba. Na faɗa masa gaskiya cikin nutsuwa ko da kuwa yana sanye da agogo mai daraja." Ta ƙarasa maganar kamar irin sakalan yaran nan... Inna ta zaro ido Ta ce: "Amal wallahi maganar gaskiya Ni dai na tsani irin waɗannan samari. Masu kuɗi amma babu tarbiyya! Don Allah ki rabu da wannan yaron ni ma har zuciyata na tsane shi!" Amal ta furzar da iskar bakin ta tana faɗin: "Ni ma Inna. Wallahi na tsane shi. Idan ya sake bijiro min da wata magana, sai na taka wuyansa gaba ɗaya." Shiru ya ɗan biyo baya. Inna ta juyo ta kalle ta cikin tausayawa. Ta ce: "Amal... ki riƙe mutuncin ki kamar yadda na koya miki. Talauci ba laifi ba ne, amma girman kai babu aji a cikinsa. Idan ya dawo neman shahara a gaban ki to ki sa shi ya gane cewa 'yar diploma ta iya kafa duniya da ilimi fiye da takardar da babu hali a cikinta." Amal ta ƙyalkyale da dariyar taƙama cikin kwarin gwiwa Ta ce: "Hakan za ayi, Inna. Wallahi ba zan bari ya raina ni ba." Sashen Maleekh Maleekh na kwance a kan katafaren gadonsa mai launin azurfa, A.C yana busa iska mai sanyi. Ya juya gefe, ya kalli silin ɗin ɗakin, amma zuciyarsa cike da ɗaci. Wayarsa a gefe tana ring ging amma bai saurari ƙiran ba. Kawai maganar Amal na yawo cikin kwakwalwarsa kamar ƙaho ne ke bugawa. Maleekh a zuciyarsa yana faɗin: "Yar diploma… amma kalamanta kamar lecture. Ta ce: 'Wasu suna da takarda amma babu tarbiyya'... Aibanta kenan ko?" Ya juyo gefe yana huci. Maleekh a fili Ya ce: "Ni ɗan Minister wanda ya gama Cambridge yarinyar talakawa ta ƙira ni marar tarbiyya? Cikin rediyo? A gaban kowa?!" Ya miƙe zaune, ya ɗauki remote, tare da jefar da shi gefe... Maleekh cikin haushin ta yake faɗin: "Ta raina ni. Wallahi ta raina ni. Kuma in ba ta gane inda take ba zan nuna mata bambanci tsakanin gata da ƙasa. Ba zan bar wannan batun lafiya ba." Yayi shiru, yana jujjuya kalmarta a rai. A hankali, ya sauke murya... Cikin raunin zuciya Ya ce: "Amma fa ta iya magana... Ba kamar sauran ‘yan jaridu da ke jin tsoro ba. Ta tsaya da mutuncinta. Hakan ya… ya ɓata min rai sosai." Sai ya ɗan murmusa, yana jin baƙin ciki da nauyi a zuciyarsa. Ya cigaba da cewa: "Yanzu ni wanda ake ji da ni a birni, yarinya ‘yar unguwa ta ruguza min kwarin gwiwa? Sai na saka ta daina jin daɗin aikin nan. Sai ta daina jin kamar tana da ƙima." Yayi tsaki, ya kashe wutar ɗakin gaba ɗaya. Duhu ya mamaye ɗakin, amma zuciyarsa cike take da barazana... da tsantsar jaraba. ★★★★★ Bayan kwana uku, Maleekh ya gama siye Ogan gidan rediyo da kuɗaɗe kimanin five billions akan ya tura Amal cikin wayo da dabara ta fara aiki a kamfanin sa dake nan Kaduna, Ya nuna cewa anyi mata ƙarin matsayi ne daga gidan rediyo Rayuwa FM zuwa Kamfani CashTalk, dake Amal bata san waye mallakin wurin ba.... Washegari Shugaban gidan rediyo ne ya aiki Amal washegari da safe bayan taje wurin aiki, wai taje kamfani ta kai takardu a shugaban kamfanin, ya sanar mata cewa zata ɗan musu aiki a wurin na wani ɗan lokaci... Cikin mutunci da kulawa da kuma ganin girman shugaban nasun ta amsa cikin girmamawa.... Amal ta hau keke napep taje har kamfanin da aka aike ta dake yau ba da wanda zata tattauna a rediyo, Amal na fitowa daga napep, ta kalli ginin kamfanin mai beni hawa hawa mai sheƙi, sannan ta shiga cikin harabar. Bayan tambayoyin da ma'aikatan suka mata sai da ta nuna takardu, da ƙyar aka barta ta shiga cikin kamfanin kamar wata mai neman taimako. tana shiga ta tambayi office ɗin shugaban kamfanin aka nuna mata sai dai daƙer suka barta ta nufi office ɗin har sai da ta nuna musu ID card ɗinta tukun, tana zuwa bakin office Ta tsaya a bakin ƙofar office, ta kwankwasa a hankali. sai da ta ɓata lokaci kafin aka bata umarnin shiga ciki... Muryar daga ciki mai sanyi da kuma cike da izza ya furta "Shigo..." Amal ta buɗe ƙofar a hankali, da sallama a bakinta. "Assalamu alaikum..." Tana ɗaga kai, sai ta tsaya cak. Idonta ya sauƙa akan Maleekh, wanda ke zaune cikin kujera a matsayin shugaban kamfani. Sanye yake da farar riga mai kyau, hannunsa na ɗauke da shisha, yana hura hayaki a hankali. Ya ɗago kai yana kallonta daga ƙasa har sama cikin salon raini.. Maleekh yana hura hayaƙin shisha, cikin izzah ya furta: "Toh toh… ga yarinyar da bata gajiya da tunkarar manya. Wane saƙo ne kuma kika kawo yau? Ko kin zo ne ki ƙara mini 'lecture' kamar ranar?" Amal ta ɗaure fuska, zuciyarta cike da takaici. ta miƙa masa takardun da aka bata daga ofis. Sannan ta ce: "Wannan ne takardar da aka ce in kawo daga gidan rediyo. Nazo ne don isar da aiki." Maleekh ya karɓi takardar kamar bai damu ba, Ya ce: "Aiki kenan… Yar diploma, mai azama. Kina durƙusar da kai ne don ki nuna kina da hankali da ilimi ko kuwa?!" Amal cikin natsuwa, da murya mai taushi Ta ce: "Ba don nuna hankali nake ba. aiki kawai nake, kuma ina mutunta kowa ko da kowa bai mutunta ni ba." Maleekh ya saki dariya mai cike da izza tare da faɗin "Wannan muryar kamar mai wa’azi. Sai kace ke ce HR ta duniya. Kin ƙirani marar tarbiyya ko dai kin manta?" Amal ta saki murmushi mai kaifi sannan ta ce "Ban manta ba. Kuma ban faɗa da bakina ba. Idan kai ne ka karanta hakan a cikin kalmomi na, to hakan na nuna inda matsalar ya ke." Maleekh ya yi shiru na ƴan daƙiƙu. Ya kalleta sosai kallon da ke cike da mamaki da ƙyashi. Amma a can cikin zuciyarsa, kalmarta ta sake sosa shi... Maleekh Ya ce: "Toh tunda ke mai ilimi ce, menene burinki a rayuwa? Wani matsayi kike mafarkin kaiwa?" Amal cikin ƙarfin gwiwa Ta ce: "Burina shine in rayu cikin mutunci, in taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi, in yi amfani da harshena da ilimi na wajen tallafa wa al’umma. Ba wai kawai in ɗora ƙafa akan tebur in sha shisha ba." Maleekh ya riƙe murfin shisha sosai, idanunsa suka ɗan sauya launi amma bai nuna ba. Ya juyo gefe yana faɗin: "Hmmm… kamar dai wata ce ke jin haushin masu gata. Amma me yasa duk lokacin da na ganki, sai nake jin kina ƙoƙarin cewa ni ne matsala?" Amal Ta ce: "Saboda ka ɗauki kujerar gata, ka manta da nauyin da ke tare da ita. Ba kowa ke da damar zama babban mutum ba, wasu kawai manyan suna ne da ƙaramin hali." Shiru suka yi . Sai dai wannan karon Maleekh bai ce komai ba. Ya janyo wata takarda, ya sanya hannu kai tsaye sannan ya miƙa mata cikin sanyin murya Ya ce: "Zaki iya tafiya yanzu." Amal ta jinjina kai tare da faɗin "Nagode." Ta juya cikin kwanciyar hankali, ta fita daga ofishin. Amma a ƙirjinta, zuciyarta na harbawa ba don tsoro ba, sai don mamakin yadda kaddara ke juyawa. Shima Maleekh yana zaune shiru, yana kallon ƙofar da ta rufe bayan ta fita. Ya furzar da iskar bakin sa... Maleekh a zuciyarsa yake faɗin: "Wannan yarinyar… tana da zuciya. Kuma tana da baki. Amma sai ta gane ban faɗi kalmar ƙarshe ba tukuna." Amal ta fito daga ofishin, ta rufe ƙofar a hankali. Ta jinjina kai kamar wacce ta gama jarabawa mai wahala. Tana takawa zuwa ƙofar fita, amma zuciyarta cike da faɗuwa. Amal a zuciyarta take faɗin: "Me nake yi a duniyar masu kuɗi? Wannan mutumin dai… ya raina duk wanda bai kai sa ba. Amma wallahi… sai yaga cewa ba gata ke sa mutum zama nagari ba." A lokacin da ta ke fita harabar kamfanin, wata murya ta tsaya mata a baya. Muryar mace.. "Excuse me, ke ce Amal daga gidan rediyo?" Amal ta juyo, sai ta ga wata mace doguwa, fara, tana sanye da kaya na ofis masu kyau. Fuskar mace ce mai wayewa Amal Ta ce "Eh, nice. Lafiya?" Matar Ta ce: "Ni sunana Amira, ni ce Personal Assistant ɗin shugaban kamfanin. Na ji ɗan ƙaramin ɓangare na tattaunawarku daga ciki. Ki sani, ba kowa ke iya tsayawa gaban Maleekh har ya faɗa masa maganganu ba." Amal ta kalli Amira cikin mamaki ta ce "Ban gane ba..." Amira ta ce "Yana da zuciyar ƙyashi, amma idan mutum ya kasance da gaskiya da daraja, sai ya ƙyale jin haushi ya koma sha’awa. Ki kula da yanda kike magana da shi, sabo da idan mutum kamar shi ya fara jin haushin mutum... yakan rikice." Amal ta ɗan danne dariyarta, tana kallon Amira da murmushin tausayi ta ce "Ni bana kula mutane irin sa. Sai dai mutanen da ke da daraja a zuciyarsu, ba a kuɗinsu ba." Amira ta jinjina kai ta ce: "Na gane. Amma ki sani, akwai abinda ba ki sani ba. Maleekh yana da wani bala’i da baya so a ambata. Ya tsani wanda zai fallasa rauninsa." Amal ta ce "Idan yana da rauni, to bai kamata yana cutar da mutane ba. Duk da ina aiki a ƙarƙashinsa yanzu, bai cancanci mutum ya ba shi zuciya ba." Amira ta ce "Zan kula dake. Idan wani abu ya tashi, ki kira ni. Amma ki sani ke kin taso da ruɗani a zuciyar wanda ba’a saba masa ba." Amira ta juya ta bar Amal tsaye cikin ɗan mamaki da nauyin tunani. Maleekh yana tsaye a tagar ofishinsa yana kallon Amal tana fita. Yana zuƙar iska daga shishar sa, yana kallon ta cikin rashin natsuwa. Maleekh a zuciyarsa ya ce: "Yarinyar nan… bata da kuɗi, amma tana da daraja. Na tsani irin kalaman da take faɗa amma me yasa nake tunaninta? Me yasa kalmarta ke yawo a kunne na kamar ƙira?" Ɗaukar wayarsa ya yi ya ƙira wani Abokin sa mai suna Baba Dan London... Yana ɗaga ƙira Maleekh ya ce: "Baba Londo… kana free ne? Zo ofis ɗina yanzu. Muna da aiki akwai wata ƴar rediyo da nake so na koya mata darasi. Ta raina manya." Yana kammalawa ya kashe wayar... Maleekh yana zaune a ofis ɗinsa, gaban rigar sa ta buɗe sai ƙirji a waje, yana ta juya shisha da ƙasaita kamar basarake. Wayarsa ta yi ƙara sau ɗaya. Ya dubata. Maleekh yana murmushi ya ce: "Yo! Baba Londo ka shigo mana..." Kafin minti biyar su wuce, ƙofar ofishinsa ta buɗe. Sai ga wani saurayi mai yawo da kaya na zamani, sanye da tabarau a cikin ofis. Shine Baba Londo mashahurin ɗan yawo da gurɓataccen tunani, wanda ba ya gajiya da yaudarar mata. Baba Londo yana dariya ya ce: "Kai kai kai! Maleekh ɗan Minister! Gani nan! Wai kai ka ce akwai wata drama a nan?" Maleekh yana hura hayaƙin bakin sa ya ce: "Baba… wata yarinya ce daga gidan rediyo. Yar talakawa ce, amma fa kyan ta ya wuce misali, farar fata ce kamar farar larabawa. Amma fa... tana raina hankali na! Wai saboda ta karanci journalism shine take taƙama...." Baba Londo ya zauna a gefensa, yana gyara agogon hannunsa ya ce: "Kai ka bari. Talakawa da wayo sunfi wuƙa mai kaifi. Amma kai fa ba'a raina ka haka fa.... sai mu koya mata darasi." Maleekh ya ce "Kai nake jira. Gaya mini yadda zan danne mata girman kan nan cikin kwana biyu." Baba Londo ya matso kusa da shi tare da da rage murya ya ce: "Ka ji plan. Tunda tana aiki a ƙarƙashinka, zaka sa a ƙara mata aiki kullum... har sai ta gaji, Idan tayi kuskure, sai a nemi soke kwangilar ta ko a hana ta albashi." Maleekh yana jin hakan sai ya lumshe ido yana jin daɗin wulaƙancin da zai mata.. Maleekh ya ce: "Hmm... wannan ra'ayin ya fara birge ni." Baba Londo ya ce: "Daga nan sai ka fara jan hankali ka nuna kamar kana jin tausayinta. Ka shiga cikin lamarin ta, ka rinƙa bata kulawa da magana mai taushi. Sai zuciyarta ta fara rikicewa. Amma fa kada ka nuna mata zafin nama. Ka fi dacewa da wasanni da hankali." Maleekh yana dariyar mugunta ya ce: "Zaka ce ni ba master bane a wasan zuciya? Ni nake barin manyan ƴan ministoci suna jira, ga su nan beautiful model. Amma wannan 'yar diploma za ta ci kaina?" Baba Londo ya ce: "Wallahi ba zata ci ba. Amma kayi hankali irin wannan mata idan ka fallasa musu rauni, sai sun rikita rayuwarka." Maleekh ya ce: "Don haka zan koya mata darasi da hannuna. Ni ba zan so mace 'yar talaka ta ga girma na ta raina ni ba. Sai ta gane ban da sakarci nake yi, maye ne kawai ban fara ba." Sai suka yi dariyar mugunta tare. Maleekh ya kira PA ɗinsa ta waya. yana sanar mata cewa: "Amira… ina so a shirya meeting na gaggawa da Amal gobe da safe. Ki ce da ita, akwai wani 'special project' da zan so mu yi tare. Tell her it’s top priority." Yana kashe wayar, ya kalli Baba Londo da murmushin mugunta Ya ce: "Let the game begin." Amal ta dawo gida da yamma, jikin ta duk a gajiye amma zuciyarta na tafasa da tambayoyi. Tana shiga daƙin su, ta ajiye jakarta tana huci ƙasa ƙasa. Inna na zaune tana yanka kayan miya ta ɗago kai da kallon tambaya Ta ce: "Amal! Lafiya?..." Amal ta zauna a ƙasa, ta sauƙe ajiyar zuciya sannan ta ce: "Inna... kin san ofishin da aka aike ni yau?" Inna ta dafa goshi tare da faɗin " Wajen marar mutunci?" Amal ta ce: "Na sake samun gayyata can gobe. Wai shugaban kamfanin ya ce yana so mu yi special project tare. Kuma wai top priority ne..." Inna ta miƙe da sauri tana faɗin: "Subhanallah! Wannan ai ba aiki ba ne makirci ne! Kin san irin mazan nan Amal? Su suke fara da “project”, su ƙare da lalacewa!" Amal ta lumshe ido tare da faɗin "Ni ma ban gamsu da maganar ba, amma kuma Inna… aiki ne. Idan na ƙi zuwa, zasu ce ban bi umarnin su ba amma a zahiri bazan je ba..." Inna ta zauna tana faɗin "To ke ma ki zauna da

Chapter 3 of 62