Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wayo! Ki je gobe amma ki saka idanu kamar likita. Kada ki yarda ki zauna da shi kaɗai. Kuma wallahi, ki saka hijabinki sosai ki nuna masa ke cikin ƴar halak ce..." Amal ta ce "Inna, ni ma zanyi taka tsantsan. Amma wani abu ya daɗe yana damuna..." Inna ta ce "Wane ne?" Amal ta ce "Maleekh … ba kamar sauran mazan ne ba. Zuciyarsa na daban ne. Na lura da yadda yake kallona... ba wai kallon sha'awa kawai ba, kamar kallon tambaya ne... ko ƙiyayya..." Inna ta tsare ta da ido sannan ta ce "Amal, ki ji tsoro da irin kallon nan. Wani lokaci mugun mutum yana jin yana ƙaunar mutumin da zai ɓata. Ki kiyaye. Ki bari Allah ya fitar da ke da mutunci." Wuraren dare misalin ƙarfe 10 Maleekh da Baba Londo suna cikin wani VIP lounge a cikin wani babban hotel tal. Wuta mai launin purple da blue tana ta walƙiya, kuma ana rawa a gefe. Amma su suna zaune suna cin nama da lemon shayi... Baba Londo ya ce "Kana ganin zata zo?" Maleekh yana dariya ya ce "Wai don tana kare kanta ne zaka ce ba zata zo ba? Duk mace tana da buɗaɗɗen lungu. Sai dai kai ka samu hanyar da zaka shiga da sirri." Baba Londo ya ɗan runtsa sannan ya ce "To amma ka tuna... akwai wasu mata da ba sa fallasuwa, sai dai ka ɓata kanka. Idan wannan yarinyar ce ɗaya daga cikinsu..." Maleekh yana hura hayakin shisha sannan ya ce *"To zan bata ƙaunar da zata rikita ta, sai dai idan zuciyarta dutse ce. Amma idan ta ƙi da gaske..." ya ɗan langaɓe ya ƙarisa da cewa: "Zan mata abu ɗaya wato hukunci. A daina wasa da ni, ni ba wanda ake wulakanta wa ba ne." A wannan ranar Amal ƙin zuwa wurin tayi, har suka gaji da jiran ta, ran MALEEKH ya ɓaci amma sai dai Baba London ya bashi shawarar kada ya nuna mata ɓacin ransa.... Washegari da safe, Amal ta iso cikin kayan aiki masu kamala, hijabinta tsaf, fuska cike da kwanciyar hankali amma zuciya cike da damuwa. Tayi sallama, PA ɗinta Amira ta nuna mata za ta iya shiga.... A cikin ofis, Maleekh na zaune yana faman latsa laptop, yana kallonta da ɓoyayyen mugunta. Bayan ta zauna, ya fara magana cikin wani salo, ba kamar Maleekh ɗin jiya ba... Maleekh yana murmushi ya ce: "Yanzu Amal, na ƙira ki ne saboda na lura kina da basira sosai. Muna da wata sabuwar shirin nuni mai taken “Rayuwar Gaskiya” – kuma ina so ki zama presenter ɗinsa." Amal cike da mamaki ta ce: "Ni? A matsayina na ƴar kwangila kawai?" Maleekh ya lumshe ido tare da faɗin: "Kwarai kuwa. Sai dai akwai wasu abubuwa da zamu gwada. Na tsara zamu je location ɗin wani shooting gobe a resort da ke wajen gari." Amal ta ɗaure fuska ta ce: "Wajen gari? Da kai ko da tawaga?" Maleekh ya yi murmushi tare da hura shisha ya ce: "Ni da ke za mu fara don gwaji ne. Sai mu tantance style ɗin ki kafin a haɗa da crew." Amal ta ji wani abu ya motsa a zuciyarta. Duk da salon maganar sa, akwai wata muguwar niyya da ta ji tana tashi. Sai ta miƙe cikin nutsuwa ta ce: "Zan buƙaci takardar umarnin tafiyar da kuma cikakken bayani a rubuce. Ina kuma so Ogah na ya sani da kansa...." Maleekh ya ɗan daure, domin zuciyarsa tafasa take, ya ce: "Yanzu dai ki zauna mu gama magana. Bayan nan sai mu shirya komai." Amal ya ce: "A'a sir, ba komai da yafi tsari. Aikin da babu sahihanci ko rubuce-rubuce, ba ni da wani hannu a ciki." Maleekh ya kafe ta da ido, sai dai maganarta ta nuna masa ita ba yar wasa ba ce. Amma ya kame kansa Ya ce: *"Alright. I respect that. Za a rubuta komai." Amma cikin zuciyarsa yana cewa: "Zaki ga shirin da zan yi miki, yarinya!" Bayan Amal ta tafi, Shima fita ya yi tare da shiga motarsa ya nufi gidan Baba Londo. Bayan sun gaisa da dariyar sheɗanci.. Maleekh cikin ɓacin rai yake faɗin: "Plan A bai ci ba. Tana da wayo sosai. Amma zamu juyar da plan B." Baba Londo yana shan taba ya ce: "Ka shigar da wata yarinya cikin lamarin. Wacce zata shirya yin bidiyo da rigimarsu kamar suna faɗa... ko faɗa kan mijin aure... sai Amal ta fito kamar mai masifa, hakan zai baka damar ɗaukar ta a video ka tura cewa ƴar rigima ce bazaka iya aiki da mafaɗaciya ba...." Maleekh ya ce: "Za mu saka hidden camera a ofishina. Zan sa wata yarinya daga cikin ƴan nuni ta zo cikin shirin faɗa gobe ta tinkari Amal yanda zata biye mata suyi rigama tare, zan ɗauki Amal da camera cikin faɗa, zamu sa suna faɗa ne akan makullin sirrin ƙofar dukiyar al'umma, suna tsara yanda zasu yi su kwamushe kuɗaɗen ne, ɓarauniya ba zata iya wakiltar kamfani ba." Baba Londo ya ce: "Kai, wannan zai jefa ta cikin matsala! Ba za su sake yarda da ita ba. Daga nan zata roƙi gafara... kai kuma ka bata sharaɗi kafin ka yafe." Maleekh ya ce "Game on, Amal." Washegari da safe, Amal ta shirya cikin kayan aiki masu kyau rigar atamfa cikin tsabta da hijabi mai ƙyalli, amma a zuciyarta ta riga ta ɗauki matakin tsaro. Tayi addu’a kafin ta fita. Tana zuwa ofis, wata sabuwar mace tana zaune a cikin ofishin taro tana duba waya. Ita ce 'yar wasan da Maleek ya ɗauka don ya kunna rikici.. Amal ta gaishe da masu tsaro, ta nuna ID ɗinta, sannan ta shigo office ɗin Maleekh... Maleekh yana murmushi ya ce: "Amal, good morning. Kin iso da wuri. Mu jira ‘yar uwar da zamu yi rehearsals tare da ita. Akwai script ɗin faɗa ne zamu gwada." Amal cikin nutsuwa ta ce: "Toh, amma ina so in karanta script ɗin kafin a fara komai. Ina so in ga abinda zan faɗa da abinda nake nufi da shi." Maleekh ya ce: "Ai improvisation ne wato ki yi da kanki. Ki yi acting kamar da gaske." Amal ta yi murmushi mai kaifi tare da faɗin: "Haka kuwa? Amma wannan ba ya cikin tsarin aikin da aka tsara ni a kai. Kuma... ni presenter ce, ba actress ba." Maleekh ya yi dariya kamar ba komai a ransa ya ce: "Ki bar komai a hannuna, Amal. Daga nan zamu iya ɗaukar ki full time. Zaki daina zama ƴar hanya, kuma... wataƙila har ki samu gida a city." Amal ta gane ya na ƙoƙarin cin mutuncinta cikin zance. Ta ce: *"Sir, kamar yadda kace ni presenter ce. Kuma ni bana barin mutunci na ya zube akan gatan talauci." Ta miƙe tsaye cikin ladabi ta ce: "Nagode da gayyata, amma ba zan iya cigaba da wannan wasan ba. Ina da girman kai na halal." Ta juya zata fita, sai ga wata yarinya ta shigo ta fara acting kamar faɗa... Yarinyar ta fara faɗin: "Ke wacece da kike tunanin ke kaɗai kika iya wannan aikin! Marasa asali ba su da kunya! Kuma nasan cewa kina ƙoƙarin buɗe ɗakin tsaro na kuɗaɗe, kina so ki nuna mana cewa ke ɓarauniya ce? ina key ɗin da kika sata?..... " Camera ta kunna daga gefe, Maleekh yana dariya a cikin ransa.... Amal ta tsaya, ta juyo da fuska cikin sanyi rai, fito da ƙaramin recorder daga jakar ta tayi tana kallon Maleekh domin bata da lokacin yarinyar balle ta mayar mata da martani... Amal tana murmushi ta ce: *"Da fatan za ku cigaba da recording amma yanzu zaku ji cewa tun jiya da dare, na san shirin ku." Ta kunna recorder ɗin da ke ɗauke da muryar Maleekh da Baba Londo suna shirya plan A da B.... Amal ta ce: "Na san kuna so ku dauƙi bidiyon karya, ku ɓata mini suna. Amma Allah baya barin mai gaskiya. Recorder ɗin nan zai isa wajen shugaban network ɗin mu. Haka kuma, lauyana zai tuntubi kamfanin ku." Maleekh ya firgita, ya kasa tashi. Yarinyar da aka kawo acting ta fice da sauri. Amal ta nufi ƙofa cikin ɗaukaka kamar sarauniya... Kafin ta fita ta juyo tana kallon sa tare da faɗin: "Mutunci ba shi da farashi, Sir. Amma rashin mutunci yana da sakamako.....na yanke shawaran bazan cigaba da aiki anan ba, tin farko inda nasan cewa kaine shugaban wannan kamfanin da bazan kusanci yanda kake ba, zan koma asalin tushen da na fito wato aikin gidan rediyo.....' Tana kaiwa nan ta fice... A ruɗe Maleekh ya buga table ɗin gaban sa cikin ɓacin rai yana huci.... yana hura shisha cikin takaici, yana jin kamar Amal ta maida shi ɗan iska a zuciyarta. maimakon ya gane laifinsa, sai ƙiyayya ta mamaye shi... Maleekh a cikin zuciyarsa yana faɗin: "Wannan yarinya... zata gane waye ni. Duk da wayonta, ba zata tsira ba. Zanyi mata abinda ba zata taɓa mantawa da shi ba..." Cikin dare a cikin masaukin alfarma, Maleek yana zaune da Baba Londo da wasu abokansa guda biyu masu kuɗi, suna shan shisha. Idonsa jajir, zuciyarsa cike da haushi. Maleekh yana faɗa cikin murya mai ƙarfi... "Wannan yarinya Amal... ta ɓata min suna a ofishina. Ta kuma raina ni a gaban mutane. Wannan ba abinda za a barshi haka ba." Baba Londo ya ce: "Sai ka lalata mata suna gaba ɗaya. Babu mace da zata tsira da karfi idan ka shigar da police ko kafafen yaɗa labarai." Abokin Maleekh wato Nasir ya ce: "Ai akwai hanya mafi sauƙi. Muna da aboki a CID unit. Sai ka shirya cewa Amal tana zargin ku da cin zarafi ne saboda baka amsa mata soyayya ba, ka jujjuya lamarin. Da sunan tana cutar da kai. A kama ta, a tsare ta, ko a duba gidan ta da sharri." Maleekh yana murmushi mai cike da mugunta ya ce: "Perfect... Zamu rubuta ƙarar karya, mu ce tana amfani da kafar rediyo wajen tada ƙiyayya da fitina a tsakanin manya. Zamu ƙara cewa tana da haɗin guiwa da wani NGO mai kalubalantar gwamnati." Baba Londo ya ce: "Wannan zai hana ta aiki a kowanne channel. Zata durƙusa ta roƙe ka." SASHEN AMAL A washegari Amal ta tafi aiki cikin natsuwa. Ogan ta ya ƙira ta ofis yana faɗin: "Amal, akwai wata ƙara da aka kawo daga babban kamfani na kasuwa. Sun ce kina amfani da kafar rediyo wajen tayar da ƙiyayya da jita-jita. Wannan abu yana da nauyi sosai." Amal ta ɗan razana, amma sai ta daure ta ce: "Sir, wannan ƙarya ne. Sai dai na san daga inda yake fitowa..." Ogah ya ce: "Ba zamu yanke hukunci yanzu ba. Amma ina ba ki shawara ki tura duk wani hujja da ke hannunki. Kuma ki lura da matakan aikin, Wannan ana iya kai shi kotu." Amal ta fito daga ofis din cikin nutsuwa amma zuciyarta a ɓace take, Tana tsaye a bakin ofis sai wata mace daga HR ta zo da saƙo. Ta ce: "Amal, anyi suspend ɗinki daga aiki har sai an kammala bincike." Amal ba tare da ta ji wata damuwa ba ta amsa, domin tasan tana da gaskiya .... Da dare, Amal na zaune a cikin ɗaki tana kuka a gefen gado. Inna na shafa bayanta tana lallashi. Bayan sun yi addu’a, Amal ta ƙira wata ƙawatarta da take aiki a cikin wata NGO “Voice of Justice.” Amal ta ce: "Na shiga matsala, Hafsa. Sun kulle ni daga aiki saboda sharri. Kuma na san Maleekh ne. Ya jujjuya gaskiya zuwa ƙarya." Hafsa a waya ta ce: "Kar ki damu. Zamu turo da lawyer kuma zamu shiga tsakani da hujjoji. Amma kina da audio recording da suka shirya sharri tun daga farko, ko?" Amal ta ce: "Ina da shi. Kuma zan tura muku gobe da safe." Hafsa ta ce: "Amal... yanzu wannan ya wuce shari’ar aiki. Zai iya zama babban case defamation da false accusation. Wannan karon... Maleekh zai san kina da garkuwa mai kyau!" A cikin wani shahararren club na Kaduna, Nasir da Baba Londo suna zaune suna jiran Maleekh, amma Maleekh bai zo ba. Nasir ya yanka masa message ba tare da samun reply ba... Nasir ya ce "Wannan Maleekh yana ƙara fita hayyacinsa. Ko ya manta cewa ba duniya ce ke karkata saboda kuɗi ba ne. Wannan karyar da yayi wa Amal zai dawo masa da baƙar aniya..." Baba Londo ya ce: "Kai Nasir, me ya dame ka? Kai fa shi ne ya fitar da kai daga matsakaicin rayuwa. Yanzu kana da mota, kana da suite, kana shan shisha duk saboda shi. Kada ka fara goyon bayan waccan yarinyar." Nasir cikin jin haushin gorin da Baba Londo ya yi masa, ya ce: "Na lura da wani abu game da Amal. She's smart. She's classy. Kuma ba irin matan da zasu zube saboda kwaɗayi ba ce. She reminds me of my late sister… kuma Maleekh ya fara wuce gona da iri." Baba Londo ya ce: "Toh me kake nufi?" Nasir ya ce: "Ina nufin zan fara kare kaina kafin abin ya shafe ni. Na tattara abubuwa da yawa da Maleekh ke yi, ciki har da audios ɗin da ya shirya domin ɓata wa Amal suna. Kuma yanzu na fara tuntubar wani babban ɗan jarida a Abuja." Baba Londo a firgice ya ce: "Kana da hankali kuwa?! Wannan abu zai rushe Maleekh, ya kuma iya jawo mana matsala!" Nasir yana juyawa da murmushi mai cike da nufi ya ce: "Ko da zai rushe shi, zai wanke wata rayuwa. Zai wanke Amal. Kuma a duniya karshen mugunta ba shine girma ba." Washegari da safe, Amal na gida tare da Inna. Tana duba waya, sai ga saƙo daga wani lamba da bata sani ba. Ta buɗe ta karanta... Message: “Ki daina tsoro. Na fara ganin gaskiya. Zaki ji wani abu nan bada daɗewa ba. Kada ki yarda da kowa a work ɗin su duka. Daga wanda ke ganin haske a cikin duhu.” Amal ta karanta saƙon sau biyu kafin ta kalli Inna ta ce: "Inna, wani da nake zaton Abokin Maleekh ne ya aiko min da saƙo. Yace zai tallafa min, cewa zai tona gaskiya." Inna ta harari wayar tare da faɗin: "Toh Allah ya tabbatar da alheri. Amma ki yi hankali. Kada ki shiga jikinsa da sauri. Duk mai cece-ki a duhu, akwai dalili." Amal ta ce: "Inna, zan saurara. Amma na fara jin cewa wannan yaƙin, ba ni kaɗai ce ke cikin sa ba..." A wani café na sirri, Nasir ya gana da ɗan jarida mai suna Faruk, wanda ke aiki da wata jarida mai zaman kanta. Faruk ya ce: "Kai abokin Maleekh me kake da shi?" Nasir ya miƙa masa flash drive ya ce: "Gaskiya da shaidun shirye-shiryen da Maleekh yayi domin ɓata suna da cutar da wata mace mai gaskiya. Wannan shi ne bugun farko. Sai dai ka tsaya da gaskiya, kada a saye ka da kudi." Faruk ya ce: "In da gaske ne wannan abubuwan da ke ciki, to kuwa... gobe Nigeria za ta san wanda Maleekh yake neman tozarta wa ta musamman ce......" asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE. page 7 to 8 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Washegari da safe, an farka da labari mai firgitarwa... “Ɗan Minister Maleekh ya yi Amfani da Ƙarfin Mulki da Kuɗi Wajen Cin Zarafin Ma’aikaciya A Gidan Rediyo.” A ƙasan labarin: An samu shaidu daga sahihan majiyoyi da faifan sauti da ke nuna yadda Mr. Maleekh, ɗan Minister Kaduna ya shirya ƙaryar shigar da ƙara domin tozarta wata yarinya ƴar ƙaramar gida mai suna Amal, wanda saboda ta ƙi amincewa da soyayyarsa ne yasa ya ci mutuncinsa a wurin aiki...” “Bincikenmu ya nuna cewa Maleekh ya tura saƙonni, ya haɗa magana da wasu jami’an tsaro, da nufin ƙaryata sunan Amal a idon duniya. Amma wasu daga cikin abokansa sun tona sirrin, suna goyon bayan gaskiya.” SASHEN MALEEKH.... Maleekh yana tsaye a falon gidan mahaifinsa lokacin da ya ga hotonsa da taken labari a babban plasma TV. Minister ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, ya sa Maleekh a gaba sai faɗa yake ta masa tare da faɗin "Maleekh... me wannan yake nufi? Wannan ai rushewar gida ne. Ka manta da kujerar da nake kai ne? Wannan ai zargin cin mutunci ne, da amfani da iko!"..... Maleekh yana ƙoƙarin kare kansa da cewa: "Dad, waɗannan maganganun duk ƙarya ne. Amal da abokinta ne suka shirya wannan domin su ɓata mun suna. Kawai saboda na ƙi su!"... Minister Ya ce "Enough! Sai an fara bincike. Kuma har a gama ba zamu so ka fito bainar jama’a ba. Zaka koma England kwanan nan. Kuma ka daina shiga harkokin gwamnati." Maleekh Idonsa ne ya yi jajir yana nuna ɓacin ransa, tare da tunanin hukuncin da zai yiwa Nasir da Amal... Bayan fitan mahaifinsa, maganar zuci ya fara yana faɗin "Na rantse da Allah, bazan bar Amal ta tsira ba. Zan tabbatar da cewa zata nemi gafara a idon duniya, kuma sai na sa an ɗaure Nasir, sai naga abinda za'a mun ..." SASHEN AMAL Amal tana zaune a ofishin lauya da Faruk ya haɗa ta da ita. Faruk ya nuna mata duk wasu hujjoji... Faruk ya ce da Amal: "Kinga? Wannan ba ƙaramin girgiza bane. Na fitar da labarin amma hakan zai sa Maleekh ɗaukan hukunci, domin ya shiga kololuwar ɓacin rai. Ki cigaba da saka ID card da recording a jikin ko’ina." Lawyer Ta ce "Zamu kai ƙara. Suna, aikinki, lafiyarki duk sun ci karo da sharri. Zamu nemi compensation da public apology." Amal cikin tsantsar natsuwa ta ce "A shirye nake. Amma ban so a ci mutuncin Maleekh ba, ina so ya san illar abinda yayi. Ya tuba, ya fahimta cewa ba kowa ne talaka bane marar daraja ...." Faruk yana murmushi ya ce "Wannan shine bambancinki da shi. Kin fi shi zurfin tunani da tarbiyya da daraja." SASHEN BABA LONDON A cikin gidan rawa, Baba Londo yana karanta jaridar yana karkarwa, gaba ɗaya ya gama tsorata ganin yanda ake ta maganar Maleekh... Baba Londo Ya ce "Na shiga uku... Nasir ya jan yo mana masifa! Maleekh zai iya fallasa ni idan ya gano ni ma na taimaka wajen shirya ƙaryar. In kuwa Amal ta kai ƙara, shikenam kashi na ya bushe, gwara Maleekh yana da gata amma Ni babu mai duba Ni ....." Ya latsa wayarsa, bugu ɗaya aka ɗauka, Baba London ya ce "Hello Nasir... Dan Allah, muyi magana da gaggawa." Nasir ya ce "Faɗan bada kai bane da maleekh ne don haka ka kwantar da hankalin ka...." A gaban ofishin gidan rediyo, Amal ta fito daga mota, tana sanye da doguwar riga mai kyan gani da hijabinta, Tana tafiya cikin nutsuwa, sai taga ƴan jarida suna ta ɗaukar hoto da tambayoyi..... Ɗan jarida 1: "Miss Amal, ya kike ji yanzu da gaskiyar ki ta fara bayyana? Kinyi sanyi a cikin rikicin da yawa ..." Ɗan jarida 2: "Shin akwai wani abu da kike so ki faɗa ga sauran mata da suke fama da cin zarafi a wuraren aiki?" Amal ta tsaya, ta kalli Faruk, wanda ke tsaye a bayanta, sai kuma ta fuskanci Camera... Tana faɗin: "Ina so duk wata mace ta sani ba dole bane ki ɗaga murya cikin tsawa domin a saurare ki. Ilimi da nutsuwa suna da ƙarfi fiye da hayaniya. Kuma ki yarda da kanki ko da duniya ba ta ganinki....." Ɗan jarida na 3 ya fashe da sowan farin ciki yana faɗin "Powerful words! Wannan ce jarumar Kaduna!" A kafar TikTok da Twitter, hoton Amal yana yawo tare da kalmarta: “Ilimi da nutsuwa suna da ƙarfi fiye da hayaniya.” Ana reposting da tags kamar #JarumarRayuwa #MaceMaiDaraja #NotAllHeroesWearSuits. Wata matashiya a bidiyo ta ce: "Ni Amal ce a cikin raina. Yarinya marar dukiya amma tana da wayewar zamani, Muna tare da ke!" ★★★★★ Maleekh na zaune a ofis ɗinsa a Abuja, yana kallon TV da bidiyon Amal ke yawo. Yana ji ana yi mata ƙirari ana cewa “Jarumar da ta kare martabarta ba tare da zagi ko cin mutunci ba...." Maleekh yana dafe da goshinsa a zabure ya ɓuga tebur gabansa da hannunsa, yana huci yana faɗin: “Amal! Sai kin dawo kin nemi gafara ta ko da dole ne!” A cikin ofishinta, Amal tana zaune ta samu ƙira daga babban lamba: “Office of the Governor” Governor yana wayar da murya mai sanyi, bayan Amal ta je ƙiran ya karɓe ta cikin darajawa tare da faɗin: "Amal, kin bamu mamaki. Kin ɗaukaka darajar mace a cikin al’umma. Ina so mu haɗu da ke domin baki wani kyauta ta musamman, na baki kyautar Gida da mota bisa jajircewa, domin na ji daɗin irin hali da tunaninki. .." Amal ta dafa ƙirjinta cikin mamaki ta ce: "Na gode Your Excellency. Na ji daɗin wannan kyautar...." Amal ta ƙara sa tare da sharar hawayen farin ciki... Kafin ka ce mai ko ina ya baza cewa Governor ya yi wa Amal kyauta ta musamman gida da mota da wasu kuɗaɗe... Bayan Amal ta koma gida itama Inna har da kukan farin ciki, tana farin cikin sun yi kuɗi su ma... Amal ta ce "Inna mun yi kuɗi amma bana taɓawa bane..." Cike da mamaki Inna take kallon ta sannan ta ce "to uban me zamu yi da ƙudin in ba taɓa wa ba? Haka kawai sai mu zuba musu ido muyi ta kallon su kamar madubi?....." Amal tayi murmushi sannan ta ce "Inna idan muka bar su zuwa gaba zasu yi amfani, zamu cigaba da zama a yanda muke yanzu...." Inna ta turo baki tare da kawar da fuska gefe ba tare da ta furta komai ba... Amal da ta fahimci haka, ta sa hannu a jaka ta ciro 50k ta bawa Inna tana faɗin "Ga shi Inna, dubu hamsin ya yi miki ko? nasan ba wani abun kirki zaki saya ba...." Inna da sauri ta juyo tare da sa hannu ta karɓa tana faɗin "ba ni! ba ni!! zasu mun amfani nikam a yanzu, kuɗin haram nake gudu bana halal ba, ato...." Murmushi Amal ta yi tare da kwantar da kanta akan cinyar Inna.... Wata daga cikin ma'aikatan gidan rediyo wanda suke tare da Amal.. mai suna Zulaihat tana zaune tana ƙiran waya cikin fushi, ta kasa ɓoye damuwar ta duk da bata bayyanar abinda ke damunta ba. Zulaihat fitacciyar ce da ake yiwa kallon jaruma mai class a gidan rediyon a shekarun baya kafin zuwan Amal, amma tin zuwan Amal tana ganin kamar ana barinta baya, shafin ta ya rufe, taurarinta suka daina haskawa dake bata kai Amal jarumta da tsayar da magana ɗaya ba... Zulaihat tana waya cikin hawaye take faɗin: "Look, Amal tana ta ɗaukaka ne kamar wata waliyyar Allah, alhalin ni na fara sanuwa kafin ita, Na san me zanyi da ita, za mu ga wanda zai ƙara reposting bayan wannan."... Cikin zafin rai ta kashe wayar sannan ta fara duba laptop dinta tana shirya wata ƙarya da za ta farfaɗo da wani scandal akan Amal tana hada hoton jabu na Amal da wani tsohon saurayi da ta taɓa yi masa hira a gidan rediyo, tana fassara hoton da kalmomin soyayya da cin amanar aiki..... Washegari da dare, wani asusun bogi (@_ExposedGistNG) ya wallafa hoton Amal da rubutun cewa: “Shin wannan ce jarumar da kuke yi wa ƙirari? Ga hoton Amal da wani babban ɗan siyasa suna soyayya cikin sirri a lokacin da take aiki... Kuɗin wane ne ke ɗaga ta?” #Scandal #AmalExposed #ƳarTakiJaruma A cikin awa ɗaya, comments sun fara zuwa da zagi da tambayoyi. Wasu na goyon bayanta, wasu kuma sun fara baza magana da zargi. Amma Amal bata ce komai ba tukun na amma ta ga duk abubuwan da suke faruwa, sai dai ta ɗauki hakan a matsayin jarabawa.... Amal tana zaune a ofishinta na gidan rediyo tana karanta comments cike da raɗaɗi.... Faruk da lawyer suna kallonta cikin tausayawa. Faruk Ya ce "Ki ce komai mana, Amal! Maza suna ta rubuce-rubuce, wasu sun fara janye goyon baya." Amal cikin nutsuwa Ta ce: "Faruk... Idan ina da gaskiya, ba zan buƙaci in ɗaga murya ba. Amma wannan karon zan maida martani. Amma ba da zagi ba ko cin mutunci ba, domin ba hali na bane...." Lawyer Ta ce: "Kiyi shirye-shiryen rubuta statement. Kuma mu fara gano waye ya wallafa wannan,

Chapter 4 of 62