Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
“Zayd! Lafiya kuwa? Meyasa zaka shigo mun haka ba sallama?” Kafin ta ƙara cewa komai Zayd ya zabga mata mari. “PATTT!” Muryar mari ta cika falon, blanket ɗin da ke jikinta ya faɗi ƙasa, daga ita sai kananan kaya short jeans da best... Amal ta riƙe fuskarta, idonta suka cika da hawaye da mamaki... “Zayd… yau ni ka mara? Ni?!” Zayd a fusace ya ce: “Abinda yafi mari ma zan miki idan baki gyara kuskurenki ba, Amal! Kin wulakanta ‘yar uwata, kin sa an kai Farha gidan yari! Duk son da nake miki, yanzu ya zama ƙiyayya! Indai baki sa Maleekh ya ciro mun ƙanwata ba, ki manta da zaman lafiya!” Amal ta matso kusa da shi cikin kuka, tana girgiza kai: “Zayd… nice fa Pretty ɗinka… wannan maganar shin ba'a cikin mafarki kake yin sa ba kuwa?” Zayd ya murtuke fuska tare da faɗin “Pretty ɗin banza! Idan kina son ki huta, je ki samu Maleekh ya fitar da Farha daga gidan yari. Idan ya ƙi, to ki rabu da shi. Idan ya ga kun rabu, zai yi abinda kike so!” Amal cikin kuka ta ce "na rabu da shi kuma?..." Ya ce "Kwarai kuwa, in ba haka ba zai cigaba da buga wasan sa akan soyayyarki, Maleekh ba sonki yake ba, domin inda yana sonki da gaske to da zaiyi abin da zai sa kiyi farin jini a wurin ƴan uwansa ba wai kiyi baƙin jini ba, yanzu kowa ya tsane ki a kaff dangi. Babu mai goyon bayan akan Maleekh ya aure ki, ki auna ki gani, Maleekh yau yayi wa ƴar uwarsa wannan tozarci to gobe kuma a ke zaiyi wa, kiyi hankali da shi domin yana can yana cikin farin ciki ke kuma ya barki da tashin hankali, abun nan da yayi ba laifinsa ake gani ba duk ya ɗora miki laifin ne saboda haka Maleekh ba masoyinki bane na kwarai..." Daga nan ya juya ya fice daga falon yana fizgar ƙofar da ƙarfi... Amal ta tsaya da hawayenta, zuciyarta kamar za ta faso ƙirjinta. “Zayd… kai ma…? Duk duniya babu wanda ya fahimce ni…” Ta share hawayenta da bayan hannu, ta ɗauki hijabinta, ta fita da sauri, ta shiga motarta.... In the Evening Gidan na cike da natsuwa, an saka turaren wuta, ƙarar kiɗa mai natsuwa na tashi a hankali daga parlour. Amal ta shigo da sauri, tana jin bugun zuciyarta. Ta tsaya a tsakiyar falon ayayinda ta tarar da Ammy a zaune, tana kallon wani fashion show a TV. Ammy ta ɗaga kai a hankali, idanunta suka haɗu da Amal. Ta miƙe, tana ɗaure fuska, ta ɗauke kai tana cewa. “Lafiya? Me ya kawo ki nan, bayan haukar da kika sashi yayi akan ‘yar uwarsa? Kinsa ya kai Farha gidan yari! To yanzu me kika zo yi? Kin zo neman afuwa ko neman cigaba da cusa masa hauka?” Amal ta share hawayenta, tana murmushi cikin nutsuwa da nauyin zuciya: “Ban zo faɗa ba, Ammy. Nazo ganin Maleekh ne kawai.” Ammy ta kwaɓe baki ta ce: “Wai ganin Maleekh? Bayan kin jefa shi cikin bala’i da sunan soyayya? Ashe baki da kunya ban sani ba? Ƴar matsiyata..!” Amal ta kasa magana, hawaye suka fara zuba. Ta juyo da niyyar fita sai ta ji muryarsa. Maleekh daga sama ya furta: “Beb? Me ke faruwa ne nan?” Ya sauƙo daga upstairs sanye da farin shirt da wando mai duhu, yana kallon Amal da mamaki da damuwa. Sai dai kafin ya ƙaraso, Amal ta juya gare shi da fuska cike da zafi da rauni. "Ina so ka gaya mun, me kake nufi da wannan hukuncin? Ka kai ‘yar uwarka kotu saboda ni, hakane ko? Kuma haka danginka ke cewa, Duk da cewa ban so haka ba? Kasa danginka sun tsane ni, suna zagina, cin mutunci ba kalar wanda ba'a mun..! Shin hakane soyayya?..” Maleekh cikin nutsuwa da ɓacin rai ya ce: “Na yi hakan ne don kare mutuncinki, Amal. Ba zan bari a ci zarafinki ba!” Amal tana kuka ta ce: “To ni ban so! Ni ban ce ka kai Farha kotu ba! Ni na yafe mata tuni… Me yasa baza ka saurare ni ba, Maleekh?” Ammy ta tsaya gefe tana kallon su da ɓoyayyen murmushi tana jin daɗin rabuwar da take gani ta fara tasowa... Maleekh cikin ɗaga murya shima ya ce: “Ke Amal, kina bani umarni ne? For what? Ki tsaya ki ji, ba zaki faɗa mun abinda zan yi ba! Na yanke hukunci ne saboda gaskiya, ba don son rai ba!” Amal itama cikin ɗaga murya ta ce: “Gaskiya? Gaskiyar me? Wacce ta sa ni cikin baƙin ciki? Idan ka fi kowa sanin adalci, me yasa kake cutar da zuciyata? Idan har kana sona da gaske inaso ka aure ni a yau, aure ni nace Maleekh...” Cikin fusata sosai ya ce: “Stop it Amal! Don’t talk to me like that!” Tana hawaye ta ce: “Na gaji da wannan soyayyar, Maleekh. Soyayyar da ba aure, hauka ne, soyayyar da sam ba'a ganin mutuncin ta, kuma bata da kariya daga danginka. Idan haka kake so, ka riƙe soyayyarka da su, ni na yafe komai!” Maleekh ya tsaya kallonta, idonsa ya canza launi saboda ɓacin rai. Cikin fusata ya ɗaga hannu ya zabga mata mari. “PAATTT!” Shiru ya cika falon na wani ɗan lokaci... Amal ta tsaya cikin rawar jiki, tana kallonsa cikin girgiza kai, hannunta na kan kumatunta. “Ni ka mara, Maleekh? Bayan duk wannan soyayyar?” Maleekh cikin nauyayyen murya ya ce: “Na mare ki. So what? Zaki rama ne?” Hawaye na zubo mata sosai, zuciyarta na tafarfasa. Tana riƙe da key ɗin mota, ta furta cikin rawar murya: “Shikenan. Tunda haka kake so, daga yau ba kai, ba ni. Ba zan tsaya ɓata lokaci na akan soyayyar da nake wulakanta ba.!” Maleekh ya yi dariyar takaici tare da faɗin: “So what idan kin tafi? Oya Go. Go get out!” Ta ɗago tana nuna shi da yatsa “Stay away from me!” Maleekh a fusace, ya riƙo hannunta: “Zo na taimaka miki ki fita! Daga yau bazaki sake ganin fuskar Maleekh ba! Zan koma England inda babu irin ki!” Ya ja ta da ƙarfi zuwa ƙofar harabar gidan. Amal tana kuka tana ƙoƙarin kwacewa, amma zuciyar Maleekh ta rufe da fushi. Yana fitar da ita ya wurga ta gefe. “Out! OUT!” Amal ta zauna ƙasa tana kuka mai ƙarfi, a lokacin ruwan sama ya fara zuba a hankali kamar sama na tausaya mata... Wani irin harara ya wurga mata tare da juya wa cikin gidan.. Ammy tana tsaye bakin ƙofa da murmushin mugunta.. A hankali ta furta: “Da kyau, ɗana. Wannan karon, ka faranta mun sosai.” Maleekh ya hau sama da sauri, ko tsaya kula Ammy da ƙannensa bai yi ba. Ya shiga ɗakinsa, ya buɗe akwati yana haɗa kaya cikin fushi da tashin hankali. “Ba za ta sake raina ni ba… Ba wata Amal a rayuwata daga yau.”.. Amal a waje tana cikin ruwan sama, tana kuka, tana faɗin cikin sanyi: “Ya Allah… idan wannan soyayyar ta zama hukunci, ka bani ƙarfin yin haƙuri…” A hankali ta miƙe da ƙyar ta shiga motarta, ta ja a hankali cikin ruwan, idonta cike da hawaye.. Gidansu Amal yayi shiru kamar ba kowa. Kukan ta ya cika falon amma babu wanda yake nan. Zuciyarta na bugawa da nauyin kalmomin Maleekh da suka tsaya a kunnenta kamar ƙaho. "Daga yau bazaki sake ganin fuskar Maleekh ba! Zan koma England inda babu irin ki!”.. Tayi murmushi cikin hawaye tana faɗin, “Ni kuma babu kai babu rayuwata…” Sai ta share hawayenta ta hau sama zuwa ɗakinta, tana ji kamar gabanta na faɗuwa. Ta sa hannu ta buɗe ƙofar ɗakin, wani sanyi da tsoro suka ratsa ta... Ganin Zayd a tsaye, ga duhu ya fara shiga, yana kallonta da idanu masu cike da nufin da ba a iya fassara shi... Amal ta ja baya tana faɗin cikin firgici: “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un… Zayd? Me kake yi a ɗakina haka?” Zayd ya saki murmushi marar daɗi, yana matsowa kusa da ita, “Na zo karɓar abinda zaisa in mallake ki, tunda kin rabu da masoyin ki… yanzu ni zan zama sabon masoyin.” Amal ta dafe ƙirji, murya na rawa, “Zayd, me kake faɗi haka? Wane irin hauka ne wannan?” A take ya cafke hannunta ya ja ta kusa da shi, yana shakar ƙamshin jikinta kamar wanda ya haukace. “Wani irin kamshi kike da shi, Amal… kin manta ni ne nake son ki tun farko?” “Ka sake ni! Zayd don Allah ka sake ni!” ta faɗa tana ƙoƙarin kwacewa, amma ƙarfin sa ya rinjaye ta... Ya jefa ta kan gado, tare da binta da sauri yana shashshafa jikinta cikin tsananin sha’awa da mugunta. Amal tana ƙoƙarin tura shi, ta buɗe baki zata yi ihu yayi saurin toshe mata baki da nasa, yana sumbatar ta da ƙarfi. Hawaye da gumi suka gama gauraye jikinta gaba ɗaya. Cikin wannan lokacin, zuciyarta ta cika da addu’a, “Ya Allah, ka ceci ni daga wannan azaba…” Yayinda Zayd ke ƙoƙarin cire mata rigarta, sai suka ji ƙarar ƙofa ta turo da ƙarfi...! Zayd a zabure ya tashi daga kanta yana kallon bakin ƙofar! Amal ta ja blanket da sauri ta rufe jikinta tana kuka. Idanunta suka haɗu da na Maleekh, wanda ke tsaye bakin ƙofa, hannunsa riƙe da takardar da ya zo bata. Idanunsa sun kumbura, zuciyarsa na harbawa da jin zafi fiye da rauni. Ya kalli Amal, ya kalli Zayd, sannan ya yi dariya mai ciwo. “Toh... dalilin rabuwar kenan?.. har gida kike kawo ‘visitor’? Har cikin ɗaki? Har kan gado?” Amal ta ɗaga murya tana kuka, tana son yin bayani amma muryarta ta kasa fita... “Maleekh... ba haka bane wallahi...” Zayd yana riƙe da rigarsa da yake kokarin sa, yana faɗi cikin ƙarfin murya, “Amma kai ɗan iska ne Maleekh! Ka turo mana ƙofa ba sallama, shin kai maigidanta ne...?” Maleekh ya yi wani murmushi mai haɗe da zafi da raini... “Ba sai na zama maigida ba don in gane ƙazanta. Na gani da idona kuma hakan ya wadatar...” Amal ta yi sauri katse wa da cewa, “Wallahi Zayd bai—” Kafin ta ƙarasa, Maleekh ya juya. Idanunsa sun cika da hawaye, zuciyarsa ta cika da ɓacin rai da rauni. Ya matse envelope ɗin da yake riƙe da shi, sannan ya jefa shi ƙasa...Yana furta “Kin gama da ni, Amal. Daga yau bana buƙatar ganin fuskarki. Kina da wanda yafi ni... ai kin same shi.” Yana faɗin haka ya fice daga ɗakin. Ƙarar rufewar ƙofa ta ƙara girgiza jikinta, ta durƙusa ƙasa tana kuka, tana faɗin: “Ya Allah! Ina zan saka kaina? Me yasa rayuwa take min haka? Na rasa soyayya, na rasa mutunci a idon wanda nake so…” Zayd ya tsaya bakin ƙofa yana kallonta, sai da ya gama sa rigarsa kafin ya fita yana wani irin murmushi.... Jiragen sama suna tashi da ƙarar da ke shiga kunne, amma a zuciyar Maleekh, ba ƙarar jirgi yake ji ba, ƙarar bugun zuciyarsa kawai yake ji. Ya tsaya bakin glass window yana kallon hasken titin jirgin, fuskarsa ta kumbura da damuwa, idanunsa sun yi ja kamar wanda bai kwanta ba kwana biyu. A hannunsa akwai boarding pass, amma a zuciyarsa akwai rashin natsuwa. Ya furta a hankali kamar yana magana da kansa: “Yanzu duk abinda nayi mata da abin da zata sakamun kenan? Duk da kaunar da nake mata, ta iya wannan abin? Amal?...” Ya jinjina kai, hawayen da yake ƙoƙarin boyewa suka zubo da kansu. Ya share da hannu, yana ƙoƙarin daurewa ya zama namiji, amma zafin ya fi ƙarfinsa... Wani mutum ya wuce kusa da shi yana riƙe da hannun matarsa, suna dariya cikin farin ciki. Maleekh ya bi su da kallo, sannan ya murmusa cikin ciwo. “A lokacin da nake ganin soyayya aljannar duniya ce... ban san cewa ta fi jahannama zafi ba.” Ya juya, ya nufi chair ya zauna. A gefe, wayarsa ta yi ƙara, Ammy ce ke ƙira. Ya ɗaga cikin kasala. “Hello Son, ka tafi ne? Ina gida ina yi maka addu’a Allah ya tsare ka. Kada ka damu da waccan yarinyar nan, Allah zai baka wadda tafi ta komai.” Maleekh da kasalalliyar murya ya ce: “Na riga na manta da ita, Mom. Na riga na manta da ita...” Ammy ta ce: “Hakan nake so. Kar ka juya baya, idan jirgin ya tashi ka bar komai a nan.” Ya kashe wayar, ya jingina da kujera, amma zuciyarsa ta ƙi yin shiru. Duk yadda yake ƙoƙarin tuna ƙiyayya, sai tunanin so ke dawowa. Yana tuno ranar farko da suka haɗu a office acan Kaduna, yadda Amal ta tsaya a gaban ofishinsa tana faɗin: “Ni ba’a raina ni saboda talaucina.” Da yadda yake kallonta yana ganin wata irin nutsuwa da bai taɓa gani a wata mace ba. Sai zuciyarsa ta soma bugawa da sauri. Ya matse hannunsa cikin fushi, “Amal... me yasa kika bani dalilin tsanarki bayan na fi so in mutu saboda ke?” Sai wani announcement ya cika hall ɗin: “All passengers traveling to London Heathrow, please proceed to gate 6…” Maleekh ya miƙe a hankali, ya ɗauki hand luggage ɗinsa, amma kafin ya taka ƙasa zuwa gate ɗin sai ya tsaya. Idanunsa suna masa raɗaɗi, jikinsa ya ɗan yi sanyi. Wata murya a zuciyarsa ta furta masa: “Ka tafi, amma soyayyar nan zata dawo maka. Ka tafi, amma ba za ka taɓa mantawa da ita ba.” Ya ɗan murmusa cikin raɗaɗi, “Toh, insha Allahu zan manta da ita kafin ta manta da ni.” Ya nufi hanyar gate, yana tafiya a hankali, kamar mai gudu daga wani abu da yake binsa a zuciya. Jirgin ya tashi amma a ƙasan duniya, akwai Amal da ke neman rai cikin hawaye da nadama..... NEXT NEXT NEXT... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 63 to 64 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Bayan Amal ta gama shan kukan ta idonta ya sauƙa akan envelope dake ya she a ƙasi... Da sauri ta sauƙa daga kan gado ta ɗauka. Ta buɗe letter hannu na rawa.. "Ban san yadda zan fara ba… sai dai kawai zan faɗa miki gaskiyar cewa zan tafi, kuma bana son ki ƙara gani na a gajeren zango. Rayuwa ta rikice, zuciyata ta gaji da yaƙi da soyayyar da take ban wahala. Na tafi ba don na gaji da ganinki ba, ba kuma dan na tsaneki ba, zan tafi ne don kawai na bar zuciyata ta huta daga tunaninki. Kullum idan na rufe ido, ke nake gani amma kin kasa fahimtar halin zuciyata, baza mu taɓa kasancewa tare ba indai baki koyi zama dani ba.... Please Idan kika tuna da ni, kar ki yi kuka. Ki yi addu’a kawai, domin duk inda nake, sunanki yana rayuwa cikin zuciyata. Maleekh 💔..." Tana kammala wa ta fashe da kuka, tana furta cikin rawar murya: “Wayyo Allah, meyasa zaka tafi ka barni inda gaske kake kana sona? Meyasa na bashi dalilin tsanata?… Amma ban fa yi komai ba! Me yasa rayuwa bata bani dama in bayyana gaskiyar zuciyata ba?” Ta share hawayen, ta miƙe a zabure. Ta zura rigar jikinta da hanzari, ta ɗauki key ɗin motarta, tana hawaye tana furta: “Zan same shi! Ko da kuwa a bakin jirgi ne, zan gaya masa gaskiya kafin ya bar ni.” Tana fita daga gida sai ta ja motar cikin gudu, tayoyi na rawa tsabar gudu... Fitilar gari ta zama hazo a idanunta saboda hawayen da suka hana ta gani sosai. “Ya Allah ka tsare ni… kar in isa jirgin ya tashi kafin in gan shi…” Tana isa gate na tashar jirgi, ta tsaya cak ganin motoci da mutane da yawa suna barin wurin. Da gudu ta shige cikin tashar, tana share hawaye, tana tambayar ma’aikacin tsaro: “Don Allah, jirgin London… jirgin London Heathrow, ya tashi ne?” Ma’aikacin ya duba agogonsa, sannan ya ce: “Madam, jirgin ya tashi mintuna goma da suka wuce.” Amal ta tsaya kamar an zuba mata ruwan sanyi. Hannunta ya saki key ɗin motar da take riƙe, ya faɗi ƙasa. Tana kallon taga mai nuni da jiragen da ke tashi a sararin sama, sai hawayen da sake gangarowa cikin zafi.. Ta durƙusa ƙasa ta fara ihu kamar zuciyarta zata tsage: “MALEEKH! Don Allah ka tsaya ka saurare ni! Wallahi ba haka bane, ban ci amanarka ba!!” Wata mata dake wucewa ta tsaya tana kallonta cike da tausayi, amma Amal bata ma lura da ita ba. Tana kuka tana faɗin: “Na rasa shi... Na rasa shi... Allah Ya sani ban yi masa laifi ba, amma bai tsaya ya saurare ni ba…” Ta durƙusa sosai, ta tallafi kanta da hannu guda tana kuka kamar ranta zai fita. Jikin ta na rawa, murya na dusashe wa. A hankali ta ɗaga idanunta ta kalli sama, tana faɗin a fili: “Allah, idan akwai adalci a duniya, ka tabbatar gaskiyata ta bayyana... kar Maleekh ya rayu cikin ƙarya... kar ya rayu yana tsanata da abin da ban aikata ba…” Hawayenta suna zuba gaba ɗaya ta jiƙe gaban rigar abayar ta, ta rufe fuska da tafukan hannayenta tana kuka. Wani sanyi ya ratsa jikinta, kamar an busa iska mai ƙarfi. Tayi shiru na ɗan lokaci, sai ta ɗaga kanta cikin tashin hankali: “Idan soyayyata ta ƙare da Maleekh, to ni ma zan kare daga rayuwar nan…” Sai ta tashi a hankali, ta fice daga tashar, tana tafiya kamar mai neman hanya cikin duhu, zuciyarta na bugawa... Haka ta shiga mota ta tafi jiki ba ƙwari.. Kwana Biyar Bayan Tafiyar Maleekh... Tunaninsa bai taɓa barin Amal ba. Tun ranar da ta dawo daga airport da kuka, babu rana da ta tashi ba tare da ta ƙira lambar sa ba. Kowane lokaci da ta danna “call”, sai ta tsaya tana sauraron sautin “number you are calling is switched off…” sautin da ya zama kamar wuƙa a zuciyarta. Tana zaune a gaban window, ta jingina kai a jikin gilashi, tana kallon ruwan sama da yake sauƙa cikin nutsuwa. Wayarta a hannu, idonta a kumbure, jiki duk ya rame. Tana faɗa cikin disasshen muryar : “Maleekh… har yanzu baka dawo ba? Ko baka ji ƙiran zuciyata ba?... Kai nake nema, Allah yasa kana lafiya.” Sau da yawa tana duba WhatsApp, babu last seen. Instagram shiru. Email babu amsa. Kamar ya ɓace daga doron ƙasa... Amal ta kasa cin abinci. Idan ta ɗauki cokali, sai hawaye su gangaro. Inna tayi iya ƙoƙarin lallashinta, amma ita kanta ta gane cewa ciwon soyayya ya fi kowanne ciwo ciwo. Da daddare Amal takan tashi tsakar dare, tana tunanin ko ya ci abinci, ko yana lafiya. Ta ɗauki wayarta ta kunna voice recorder, tana magana kamar yana gabanta: “Maleekh… ni ce Amal. Ka tuna mun yi alƙawarin cewa babu rabuwa a tsakaninmu, ko?” “Zan jira ka, har sai lokacin da ka dawo min da murmushi ɗaya daga cikin naka.” Ta dinga faɗin haka cikin kuka, tana maida numfashi a hankali. Da asuba, ta tashi ta shiga bathroom, tayi brush sannan tayi wanka tare da ɗauro alwala, ta saka hijab ɗinta ta tsaida sallah... Bayan tayi sallah tare da addu’o'i, ta tashi cikin ƙarfin hali tana faɗin. “Uhmmm, ban isa in mutu saboda ciwon soyayya ba. Zanyi aiki, zanyi rayuwa har sai lokacin da Allah Ya dawo min da shi.”... Da wannan niyyar, ta shirya ranar ta biyar, ta saka suit skirt da rigar office, ta ɗaure tie ɗinta a wuya, ta ɗauki handbag ta nufi falo, a wannan ranar ta dage tayi breakfast, daga nan ta shiga ɗakin Inna suka gaisa sannan ta wuce company. Lokacin da ta shiga reception, murmushi marar zurfi ne ya bayyana a fuskarta, murmushin wacce ta sha kuka amma ta nuna ƙarfin hali... Sai nan ne ma’aikatan suka yi mata sannu da dawowa, tare da gaisheta... Sai kuma Zayd ya bayyana da kalmar nan “My pretty…” Amma wannan karon, mari ya riga da ya sauƙa kan fuskarsa kafin kalmar ta gama fita daga bakinsa... Zayd ya tsaya dafe da kuncinsa, kowa a reception ya tsaya shiru. Sai sautukan takalman Amal da take taku cikin ƙasaita.. Idonta cike da zafi da hawaye, amma ta tsaya a gabansa kamar shugabar da ya kama wani da laifi... “Kayi farin ciki, ko? Ka rabani da mutumin da zuciyata ke numfashi dashi! Ka ɓata min suna a gabansa, kayi amfani dani wurin cimma burinka…Ba tare da nayi wani tunani ba na biye maka, wallahi ban yafe maka ba Zayd..." Zayd ya yi ƙoƙarin murmushi, amma muryarsa ta nuna gurbatacciyar niyya. “Eh, gaskiya ne. Ni nake sonki shiyasa nayi haka, na daɗe ina jiran wannan damar. Maleekh ya tafi, yanzu ba wanda zai tsaya tsakanina da ke. Wannan itace gaskiya, Amal.” Ta matso kusa da shi, tana kallon sa da idanunta masu cike da hawaye da tsantsar tsana ta ce. “Burinka bai cika ba, Zayd. Ba zaka iya maye gurbin Maleekh ba. Jininmu ya riga da ya haɗu, ba a cikin jikina kawai ba, har cikin ruhi da numfashina. Ka ji da kyau: ko ka kawar da ni, ko ka kawar da shi, ƙauna bata da kabari.” Tana kaiwa ta juya da ɗan huci. Ma’aikatan suka ba ta hanya, babu wanda ya iya magana. Ta shiga elevator, ƙamshin turarenta ya ci gaba da yawo cikin reception... Bayan ta hau saman bene na takwas, ta fito tare da shige office ɗinta ta rufe ƙofa. Ta jingina da ƙofar, hawaye suka fara sauƙa kamar ruwan sama. Ta zame a ƙasa ta durƙusa, tana riƙe da kanta tana faɗin “Ya Allah... har yaushe zai waiwaito ni? Ko da gaske ya tafi ne har abada? Maleekh, don Allah ka amsa ƙiran da nake yi maka…” Ta lalubo wayarta daga jaka, ta sake ƙira. number you are calling is switched off. Ta saki wayar ta faɗi gefe, ta lumshe ido tana kuka kamar ranta zai fita. A cikin office ɗin akwai hotonsu su biyu da Maleekh a kan tebur, lokacin da suka yi launching na sabon project ɗin CashTalk FM. Ta miƙa hannu ta ɗauka, ta kalli hoton, ta shafi fuskar sa a hankali tana faɗin. “Ka faɗa min cewa ba zaka taɓa yin nesa dani ba… ka faɗa min cewa zaka kasance dani har abada…” Sai ta ji kanta na sarawa. Tana numfashi da sauri, zuciyarta na bugawa da kyar. Ta tashi ta nufi window, tana kallon sararin sama, tana jin kamar ta ƙira sunan sa cikin iska... “Maleekh…” Sautin sunan ya fito da ƙarfi, yana haɗuwa da hawayen da suka zubo kamar ruwan sama daga idonta. Tana nan tsaye har sai da hasken rana ya fāɗi, sannan ta zauna a kujera, ta riƙe kai tana murmushi cikin hawaye: “Ba zan daina jiranka ba. Ko ka bar ni, zan ci gaba da yi maka addu’a.”.. A wannan ranar Amal bata samu ƙarfin gudanar da aiki ba.... Tafiyar da aka yi shi cikin fushi, bata taɓa sa ran zama makamin hallaka kamar haka ba... Maleekh ya bar Najeriya da zuciya mai raɗaɗi, fushi da ƙaunar Amal suka haɗu suka zama wuta a ƙirjinsa. A hannunsa akwai jakar da ya ɗauko kai tsaye daga cikin motarsa wanda yana tunanin nashi ne domin sak irin jakarsa ce, tunani ya dabaibaye kwakwalwarsa, yana tunanin komai lafiya. Bai san cikin jakar akwai abinda zai iya ruguza rayuwarsa gaba ɗaya ba.... Yana shiga jirgin. Ko wayar Amal da ke ta ƙira, bai amsa ba. Ya kashe komai, yana son mantawa da komai amma ba zai taɓa iya mantawa da yadda ya ga Amal cikin ɗakin nan tare da Zayd ba. Lokacin da jirgi ya sauƙa a Heathrow, tsaftataccen iska mai sanyi ya daki fuskarsa... Ya sauƙo cikin natsuwa, hannunsa na riƙe da pasport ɗinsa, sai kawai ya ji murya daga gefe ta ce: “Sir, can we have your luggage, please?” Ya miƙa musu cikin nutsuwa. Amma kafin ya ankara, sai ya ga wasu ma’aikatan tsaro biyu sun tsaya a bayansa, suka ɗauki jakar nan da suka saka a scanner. Cikin mintuna biyu, komai ya canja, hasken da ke kan fuskar screen ya yi ja, wani ɗaya daga cikin su ya ɗago da murya mai tsanani.

Chapter 42 of 62