Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ce cikin murya mai rauni “Nagode sosai Yaya Maleekh. Allah ya saka da alheri..” Maleekh ya dafa kanta ya yi mata murmushi, sannan ya fita daga ɗakin ya nufi part ɗinsa. Amal ta rufe ƙofar a hankali, ta kwanta a kan gadon. Da hawayen farin ciki da kuma tsoro, ta rinƙa farta addu’o'i a ranta: “Ya Allah, kai ka san zuciyata da gaskiyata. Kada ka jarabceni da wulakanci. Ka kare min mutuncina, ka tabbatar min da soyayyar da nake gani a fuskar Maleekh…” Ta rufe idonta, hawaye suka fara silalewa akan kuncinta, zuciyarta na tsaka da farin ciki da tsoro a lokaci guda... Ba a jima ba sai ƙofar ɗakin ta buɗe da ƙarfi, Amal dake kwance a firgice ta tashi daga kwancen da take. Farha ce ta shigo, fuska cike da ƙiyayya da kishi, tana tafiya a hankali kamar maciji, tsaya cikin izza tana furta.. “Ke! Tashi ki fuskance ni kafin na tashi miki hankali.” Amal ta tsaya tana kallonta cikin tsoro, ta kasa cewa komai. Farha ta ƙara matsowa ta cigaba da faɗin “Kin ji abin da na faɗa ko? Wannan ɗakin ba naki bane, wannan gidan ba naki bane, wannan namijin da kike mafarki da shi ba naki bane! Ni ce wacce zai aura Farha, cikakkiyar yarinya daga gidan masu kuɗi, mai kima da daraja.” Ta kwaikwayi Amal tana girgiza kai cikin raini ta kuma cewa “Ke kuwa? Babu abin da kike dashi face tsiya! Ƴar talakawa marar gata, ke da kika rasa komai sai kukan banza. Ki fita daga rayuwar Maleekh kafin ki ga tashin hankali a hannuna.” Amal ta runtse idonta, hawaye suka cika mata ido. Ta ce cikin rawar murya “Ni banzo nan domin in karɓe shi daga kowa ba. Soyayya ce ta haɗa mu, kuma shi da kansa ya ce…” Farha ta dakatar da ita da dariyar rainin hankali ta ce “Soyayya? Ke da Yaya Maleekh? Haba! Soyayya ce ta makantar dake har kina tunanin zaki zauna a matsayin Amaryar sa? To bari in gaya miki gaskiya wannan gidan zai zubar miki da mutunci ne, idan baki fice da kanki ba.” Amal ta yi shiru tana kallonta, zuciyarta tana bugawa da sauri. Ba ta so a yi hayaniya ba, amma kalaman Farha sun shiga zuciyarta sosai. Amal cikin rauni ta ce “Me yasa za ki ce haka? Ni ban zo nan da niyyar karɓar wanda ba nawa ba. Idan Maleekh ya yanke shawara akanki, ai ni ba zan taɓa tsaya masa a gaba ba.” Farha ta matso kusa da ita, ta ɗaga gira da isa ta ce “Kin yi kyau wajen wasa da magana, amma ki sani, ni ba zan bari ki tsaya a tsakanin mu ba. Idan baki fita da kanki ba, to zan tabbatar kin fita da kunya.” A part d'in Maleekh kuwa, yana zuwa ya shige bathroom domin watsa ruwa, bai san abinda yake wakana ba acan area Amal. Kunna shower yayi mai ɗauke da ruwan ɗumi...Ruwa na sauƙa akan sa, zuciyarsa na tunanin yadda Amal ta zo Abuja saboda shi.... A hankali ya furta cikin mugun murmushi... “Amal, zaki sha soyayyata sosai… har sai na cika miki zuciya da soyayyata. Amma a ƙarshe zan nuna miki bana taɓa yafewa....” Ya lumshe idanu yana dariyar mugunta, amma a waje yana shirin fito da murmushin soyayya.... Part ɗin Amal... Amal ta yi shiru na ɗan lokaci tana ƙoƙarin ɗaure zuciyarta kada ta fashe da kuka. Ta san cewa idan ta nuna rauni, Farha za ta ɗauka cewa ta yi nasara. Sai ta ɗaga kanta, ta dubi Farha da idanu masu ɗauke da nutsuwa... Ta ce “kin ga, ba ni na gayyaci Maleekh cikin rayuwata ba, shi da kansa ne ya zo. Ni ban zo nan da faɗa ba, kuma ba na buƙatar maƙiyi. Amma ki sani, gaskiya ba ta ɓoye kanta. Wanda Allah ya rubuta miki shi zai kasance naki, to ba makawa zaki mallake shi, amma wanda ba naki ba ne, ba za ki taɓa riƙe shi ba.” Farha ta taɓe baki, ta juya kamar za ta fita, sai kuma ta sake juyowa ta kalle ta... “Kada ki sake ce mun 'Kin ga' sunana Farha, sannan Kina da wayo sosai, amma wayon ki ba zai hana ni zama matar Maleekh ba. Ki dai jira ki gani.” Ta bar ɗakin tana kwaɓe baki.. Amal kuwa tana zaune akan gadon da zuciyarta cike da ƙuna. Ta tashi ta shige bathroom domin dauro alwala, tana fito wa ta zura hijabinta ta rufe jikinta sosai, sannan ta tsada sallah akan sallayar da yake a shimfiɗeyi, bayan ta idar ta fara addu’a a cikin ranta “Ya Allah, ka bani ikon jure wannan jarabawa. Ka kare min mutuncina da amincina.” A bangaren Maleekh kuwa, ruwa ne ya tsaya a bathroom, Maleekh ya fito da tawul yana goge kansa. sai murmushi kawai yake yi, zuciyarsa cike da shirin komawa wajen Amal domin su ci abinci tare... Maleekh ya fito daga bedroom ɗinsa cikin shigar rigar barci, Ya nufi ɗakin da Amal take.. Da ya buɗe ƙofar, ya same ta zaune gefen gado akan sallaya, kanta a sunkuye, hannuwanta cikin hijabi kamar wacce ke cikin tunani mai nauyi... Sai da ya tsaya na ɗan lokaci yana kallonta, fuskar ta nuna cewa tana ɓoye wani abu... Cikin murya mai taushi ya ce "Amal… ya naga fuskar ki haka? Ko dai akwai damuwa ne?" Amal ta ɗago kanta a hankali, ta yi murmushin ƙarya, tana ƙoƙarin ɓoye hawayen da suka taru a idonta. Ta ce "A’a, ba komai… kawai gajiya ce." Maleekh ya matso kusa da ita ya zauna a bakin gado, yana dubanta sosai. Ya ce "Karki ɓoye min wani abu, Amal. Na fi kowa sanin idanuwanki. Idan kina cikin damuwa, zan gane." Amal ta ɗan ja numfashi, ta yi shiru tana kallon hannayenta. Ta yi ƙoƙarin guje wa magana game da Farha saboda kar ta zama dalilin tashin hankali. Ta ce "Wallahi ba komai, Yaya Maleekh. Zan yi ƙoƙari na saba da sabuwar muhalli kawai." Sai ya kama hannunta ya riƙe da ƙarfi, yana kallonta cikin idanu. Ya ce "Kin san ba zan taɓa barin wani ya cutar da ke ba, ko Amal? Na kawo ki gidan mu, kuma wannan gida naki ne. Karki ji tsoro, ina tare dake." Amal ta ɗan murmusa, hawaye suka zubo mata ba tare da ta shirya ba. Ta ce "Nagode, Yaya Maleekh… nagode sosai." Ya share mata hawayen da yatsansa, sannan ya miƙe yana faɗin: "Taso mu je cin abinci..." Amal ta tashi a hankali ta bi shi, zuciyarta tana ƙara tabbatarwa cewa duk da ƙiyayyar da gidan ke nuna mata, Maleekh na tare da ita. Amal da Maleekh suka fito daga ɗakin da aka tanadar mata. Amal na tafiya a hankali gefen Maleekh, kamar wacce take jin nauyin ƙasar da take takawa. Maleekh kuwa ya kama hannunta yana jagoranta har suka ƙarasa dining area. A can kuwa, Ammy tana zaune a kujera tana sanye da eyes glass tana nuna rashin jin daɗi a fuskarta, Farha kuwa ta jingina da kujera, ganin Maleekh da Amal yasa ta kama kugu tana kallon Amal cikin kiyayya. Islam da Arfat suna gefe suna washe baki kamar suna jiran rikici ya tashi. Ammy ganin su yasa ta buɗe baki cikin masifa ta ce "Kai Maleekh, baka da hankali ne? har da ita zaka kawota wajen cin abincin mu? Wannan gidan na talakawa ne? Ko kuwa ka manta gidan uban ka ne?!" Maleekh bai zauna ba, ya tsaya yana duban Ammy da mamaki ya ce "Ammy, ki kula da kalamanki. Ki tuna Amal baƙuwa ce kuma sannan ita ce matar da zan aura. Kuma ban kawo ta nan domin ku wulakanta ta ba." Farha ta tintsire da dariyar baƙin ciki tana tafa hannu ta ce "Matar da zaka aura? Hmmm… da kuwa ka nuna wa duniya cewa iyayenka basu da matsayi! Wannan matsiyaciyar ce zaka zaɓa a matsayin matarka? Wallahi bazan yarda ba!" Amal ta sunkuyar da kanta, zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Maleekh ne ya matsa kusa da ita, ya zaro kujerar dining ya zaunar da ita da kansa... Sannan ya juyo yana duban Farha da Ammy ya ce "Ko ku yarda, ko ba ku yarda ba, Amal za ta ci abinci anan, kuma zata zauna a wannan gida cikin mutunci. Na faɗa, kuma na gama." Arfat da Islam suka yi shiru, suka kallon juna, suna jin tsoron yadda fuskar Yayan nasu ta sauya, kamar ba shi ba... Ammy ta daka tsawa, tare da miƙewa tsaye ta ce "Maleekh! Ka raina ni kenan? Ni mahaifiyarka ce! Kuma ba zan taɓa amincewa da wannan abinda kake shiryawa ba. Wannan yarinya ba zata taɓa zama surukata ba, ka ji ni da kyau!" Maleekh ya goya hannuwansa a ƙirji, yana kallonta cike da mamaki.. Ya ce "Ammy, tabbas ke mahaifiyata ce kuma kinada matsayi na musamman a cikin zuciyata, matsayin da ba kowa zai iske shi ba, amma kada ki ɗauke ni a matsayin ƙaramin yaro yanzu. Domin na girma, ina kuma da ra’ayi, kuma ra’ayina shi ne Amal. Na kawo ta cikin wannan gida saboda ina so ta saba da ku, amma idan kun ci gaba da wulakanta ta…" Ya ɗan dakata, ya sauƙe numfashi mai nauyi sannan ya ce "…to wallahi zan ɗauketa mu bar wannan gidan gaba ɗaya." Jikin kowa ya yi sanyi. Amal kuwa ta ji hawaye na tsiyaya a idonta, tana tunanin wannan ƙuduri da Maleekh ya ɗauka saboda ita. Farha kuwa kaɗa kai tayi cikin takaici, zuciyarta na ƙuna saboda rashin nasarar da ta yi wajen dakatar da Maleekh... Farha tana jin maganar Maleekh sai jikinta ya ɗauki rawa saboda takaici. Ta kalli Ammy, ta d'addage gira kamar zata fashe da kuka ta juya da gudu ta nufi ɗakinta cikin fushi... Bayan ta shiga ɗakinta ta rufe ƙofar ɗakin da ƙarfi, ta fashe da wani irin ihu mai cike da tsananin kishi. Ta ɗauki kwalbar turare ta buga a jikin glass mirror ya tarwatse gaba ɗaya... Cikin zafin rai take faɗin "Wallahi Amal! Sai kin gane wacece ni! Kin shiga tsakanina da Maleekh? To kuwa ba za ki taɓa cin nasara a kaina ba!" Ta fara yawo cikin ɗakin tana shirin haɗa plan... Cikin murmushin mugunta ta kuma cewa "Hmm… yanzu dai Maleekh ya ɗauki ta a matsayin mai tsarki, mai gaskiya… Ai babu matsala. Zan nemo hanyar da zan zubar masa da ita, zan nuna masa ainihin Amal da yake so. Sai na jawo masu ƙiyayya ta asali a tsakanin su..." Ta ɗauki wayarta ta fara duba hotunan Amal a shafinta na social media. Tana dariyar mugunta..tare da faɗin "Yar ƙaramar talaka ce kawai, mai kalar da za a iya amfani da ita a jefar da ita. Zan jawo mata mummunar asara, sai Maleekh ya tsane ta da kansa." Ta tsaya a gaban madubin da ya farfashe tana kallo cikin ido da yake yabe wa biyu, tana tafa hannuwa cikin shakku da mugun nufi ta kuma cewa "Zan fara da Ammy, sai ta ƙara tsanar Amal, daga nan zan samu wasu bayanai na karya domin in nuna musu ita ba budurwa ba ce… ko da kuwa karya ce. Wannan ne kawai zai karya Maleekh. Zan ci gaba da amfani da sharrin magana da dabaru. Sai Amal ta gudu da kanta daga gidan nan!" Ta fashe da dariya mai ɗauke da ƙiyayya, tana jin daɗin tunanin yadda zata ɓata sunan Amal a idon iyayensu da mutanen duniya gaba ɗaya... Da dare bayan Maleekh ya koma part ɗinsa, Amal tana kwance a ɗakin da aka gyara mata. Amma zuciyarta ta kasa samun natsuwa. Duk kalaman da Farha ta faɗa mata suna yawo a cikin kunnenta. "Ni ce matar da Maleekh zai aura, ke ba kya da komai sai talauci… ki fita daga rayuwarsa…" Amal ta ɗauki pillow ta rungume shi, hawaye suna sauka daga idonta. A cikin ranta take faɗin "Wayyo Allah na, shin gaskiya ne? Shin da gaske za su ƙi ni saboda halin da nake ciki? Ko kuwa Maleekh zai iya tsayawa dani? Amma idan ya canza ra'ayi fa… idan ya amince da Farha fa…?" Ƙirjinta ya buga da ƙarfi, tana jin tsoron kar soyayyar da take riƙewa da zuciya ɗaya ta zame mata bala’i. Sai ta tuna lokacin da Maleekh ya kamo hannunta a ofis dinsa, lokacin da yace “Maleekh bazai taɓa gujanki ba…” Amal ta ƙara fashewa da kuka. Cikin rawar murya take faɗin "Na biyo shi zuwa Abuja saboda soyayya, amma yanzu na fara jin tsoron makomata. Idan suka wulakanta ni fa? Idan iyayensa suka ƙi karɓata fa? Idan Maleekh ya gaji da ni ya juya mun baya fa…?" Kuka mai ƙarfi ya ci gaba da kwace mata. Ta miƙe tsaye a jikin window tana kallon waje, tana jin daɗin iska mai sanyi. Amal a hankali ta furta "Ya Allah, idan wannan soyayyar ce ƙaddara ta, ka tabbatar mun da ita. Amma idan zata zame min wulakanci da tozarci, ka fitar da ni cikin ruwan sanyi kafin zuciyata ta karye gaba ɗaya…" Ta durƙusa a sallaya, tana roƙon Allah cikin hawaye, zuciyarta na cike da ruɗani da shakku.... ☆☆☆☆ Washegari da safe, tun kafin kowa ya tashi Amal ta farka, ta yi sallah. Amma duk da haka idanunta sun kumbura saboda kuka... Misalin ƙarfe takwas, Farha ta shigo ɗakin Amal da wani ƙamshi na turare. Tana riƙe da cup ɗin coffee a hannu, tana tafe a hankali kamar sarauniya... Tana murmushin raini ta ce "Yar talaka, ina kwana? Kin tashi lafiya kuwa a gidan da bai dace dake ba?" Amal ta sunkuyar da kanta, bata ce komai ba. Farha ta ƙaraso kusa da ita, ta tsaya a gabanta ta ce "Kin ji ko? Wannan gidan ba wurinki zaman ki bane. Maleekh kuwa… Maleekh nawa ne, ba naki ba. Kin ji kuwa? Ni ce matar da zai aura, ba ke ba." Amal cikin sanyin murya ta ce: "Ki daina faɗar haka, don Allah ki barni da masoyina…" Farha ta kyalkyale da dariya mai cike da raini. Ta ce "Masoyinki? Haba Amal. Kina ganin wannan gidan na alfarma, wannan iyalai masu daraja, zasu zaɓi mace irin ki? Matsiyaciya mai lalatacciyar rayuwa? Ki duba kanki, ki duba ni?" Ta ɗaga hannayenta tana nuna rigarta mai tsada, da sarƙa a wuyanta mai kayan da ta sha kwalliya... Farha cikin ɗaga murya ta ce "Ni ce nagarta, ni ce mai kyau, ni ce mai kuɗi, ni ce mai daraja. Ke kuwa… ba kya da komai! Ki fita daga rayuwar Maleekh, ki barshi gare ni kafin ki ga abinda yafi ƙarfin ki!" Amal ta fashe da kuka tana faɗin: "Wallahi ina son Maleekh da gaske, ba wai saboda kuɗinsa ko darajarsa ba…" Farha cikin tsananin kishi, tana zaro ido ta ce "Ke da gaske kike son shi? To bari ki gani. Zan nuna miki wacece ni, zan tabbatar da kin bar rayuwarsa da kanki!" Ta juya cikin masifa ta bar ɗakin, ƙamshin turarenta ya biyo bayanta... Amal kuwa ta durƙusa a ƙasa tana kuka, zuciyarta na cike da tsoro da ruɗani. Jin alamu mutum ta nufo ɗakin ta kuma ƙamshin turaren ya nuna cewa Maleekh ne.. Da sauri ta goggoge hawayen fuskar ta, ta zauna silently.. Maleekh ne ya shigo cikin shirinsa zai tafi Office na tafiya Office... Bayan sun gaisa ta nuna masa ba wani damuwa.. Amal tace dashi "Yaya Maleekh dan Allah inaso zan koma Kaduna, na bar Inna ita kaɗai.." Maleekh yace "bazaki koma yanzu ba Amal, Inna kuwa nasa a kula da ita acan..." Amal tace "sai yaushe to? Nifa da niyyar kwana ɗaya zanyi na koma..." Maleekh ya karkada kai sannan yace. "Taso muje muyi breakfast.." Haka ya ja hannun Amal suka fita. Dinning suka je ana suka tarar da sauran yan gidan. Ammy da Abbah wato mahaifinsu da kannensa biyu Arfat da Islam, sai wacce take masifar sonsa wato Farha... Kowa yana zaune akan kujerun cin abinci. Amal ta shigo a hankali tare da Maleekh, hannunsa riƙe da nata. A zuciyarta tana jin nauyin ganin iyayensa, musamman yadda ta fahimci Ammy ba ta sonta. Amal ce ta durƙusa ƙasi tana gaishe su, Ammy ko kallon yanda take bata yi ba, sai Abba da ya kalleta yana murmushi ya amsa mata....ba tare da ya tambaya ko ita wacece ba ya ci gaba da breakfast ɗinsa, domin duk wanda yazo gidansa yana mai farin ciki, domin masoyinka ne zai zo yanda kake, shiyasa bai wani damu da sanin ko ita wacece ba.... Bayan sun zauna, Ammy ta kalli Abbah da tsananin damuwa. Ta ce da shi "Ka gani ko? Ga shi nan abinda nake ta faɗa maka tun jiya. Maleekh ya kawo mana matsala gida. Wannan matsiyaciyar yarinya ce, wacce ta zubar masa da mutunci a bainar jama’a, ta mare shi, ta wulakanta shi, kuma har yanzu ya kasa kawar da ita daga rayuwarsa. Wannan abin kunya ne gare mu!" Abbah ya juyo yana duban Maleekh. cikin nutsuwa ya ce "Maleekh, me hakan yake nufi?" Maleekh ya riƙe hannun Amal yana kallon mahaifinsa ya ce "Abbah, gaskiya Amal ta zo Abuja ne don ta bani haƙuri akan abin da ya faru a Kaduna. Ba ta da wurin zama anan, shi yasa na kawo ta gida a matsayin mace. Ba zai yiwu in bar ta a waje ba. Kuma gaskiya… ina sonta." Abbah ya gyara zama, yana jin daɗin yadda ɗansa ya faɗi gaskiya... Abbah ya ce "Shikenan, ba komai. Idan kai ka fahimci dalilin ta, na fahimta nima. Ba laifi bane ta zo ta nemi sulhu." Ammy ta buga hannayenta akan tebur cike da mamaki da takaici. Tana masifa "Au, kai ma? Ka ce shikenan? Kana ganin wannan yarinyar, yar matsiyaciya zata shafa mana kashin kaji, kuma ita ka ce shikenan? Yarinyar da zata jawo mutane su ƙi mu? To wallahi, muddin ina da rai, bazan bar ɗana ya aure ta ba. Farha ce ta dace da shi, ita nake so, kuma ita zai aura dole!" Amal ta sunkuyar da kanta, hawaye suna neman zubo mata saboda kalaman Ammy. Abbah ya juyo cikin nutsuwa da karfin murya ya ce "Maryam, ki saurara da kyau. Abinda ɗana yake so shi zan yi. Ba ni zan zauna masa da mata ba, shi ne zai zauna da ita. Idan Farha ya zaɓa, zan yi farin ciki. Idan kuma wannan yarinyar da kike kiran matsiyaciya ce ya zaɓa, to ni na amince. Kin gane?" Ammy ta dafe kirji tana girgiza kai cikin takaici ta ce "Wato kai kake goya masa baya akan raina ni koh? To wallahi ba zan taɓa amincewa da wannan auren ba!" Maleekh ya dubi Ammy yana murmushi ya ce "Ammy, ki sani wannan ba wasa bane. Ni Amal ce nake so, kuma babu wanda zai hana ni. Duk soyayyar da nake nuna mata da gaske ne. Tin da na zaɓe ta, to babu wanda zai hana ni auran ta." Abbah ya ɗaga hannu alamar sulhu ya ce "Shikenan, ku daina ɗaga hankalin ku akan wannan magana. Ku bar shi ya yi abinda zuciyarsa ta zaɓa." Ammy ta yi shiru, tana huci cike da takaici. Farha kuwa ta ɗaure fuska kamar zata fashe da kuka. Maleekh ne shima ya zauna kusa da Amal, yana ƙoƙarin rarrashinta. Suka fara cin breakfast tare, duk da cewa Amal bata iya ɗaga kai sosai saboda kunya da nauyin kalaman da ta ji daga Ammy. Haka suke cin abinci, gidan ya ɗauki shiru, Amma idan aka kalli fuskar Farha, cike take da kishi da takaici. Farha kasa cin komai tayi, ta ɗago tana dariyar mugunta ta ce "Hmm… wallahi mamaki yake bani. Yarinyar da ta mare shi a bainar jama’a, yau ga shi tana nan zaune a gidanmu tana cin abinci da mu. Kenam wannan ce masoyiyar gidan?" Islam ta runtse idanu tana kallon Amal da ta tsinci kanta cikin kunya... Farha ta ɗora da gori tana faɗin "Kin kyauta Amal. Ke da ƙaramar rigar jikinki da tsiyarki, yau kin samu wurin zama a gidan da ba kowace yarinya ke kaiwa ba. Amma ki sani wannan abinci da kike ci, ina ganin ya fi ƙarfin ki. Kuma idan har za a zaɓi wacce za ta zama matar Maleekh, ni ce, ba ke ba!" Abbah yayi kamar bai ji ba ya ci gaba da cin abincin sa... Farha ta kalli Maleekh kai tsaye tana ƙara murya da cewa. "Ya Maleekh, kowa yasan ni ce aka zaɓa maka. Wannan matsiyaciya ba zata tsaya da kai a duk inda ka je ba. Ita yar gari ce kawai, ni ce ta dace da kai. Kai ka duba ka ganni fa, na haɗu sosai..." Amal ta tsaya cak, ta kasa ɗaga cokali. Idanuwanta suka cika da hawaye amma ta nace ta yi shiru saboda kada ta kawo gardama a gaban iyayen Maleekh. Maleekh ya ajiye cokalin hannunsa a fusace, ya yi wani irin tsawar da yasa kowa ya dakata... Maleekh cikin ɗaga murya yake faɗin "Farha! Ki rufe bakinki kafin na nuna miki ina matsayin ki yake. Amal ce zaɓi na, kuma duk wanda ya kuskura ya wulakanta ta to ni ya wulakanta. Ki ji tsoron kalaman ki." Farha ta ɗaga gira tana kallonsa da hawaye cikin fushi, amma bata iya cewa komai ba. Abbah ya ɗan ɗaga kai ya ce cikin natsuwa: "Ku daina wannan hayaniya. Idan aka gama ci kowa sai ya kama abun yi. Amal baƙuwa ce a gidan nan, ku girmamata." Ammy ta yi ƙasa da ido, tana huci da baƙin ciki, Farha kuwa ta share hawayenta da ƙyalle tana jin haushin yanda Maleekh yake nuna kulawarsa a Amal. Maleekh ya jawo Amal kusa da shi yana nuna mata cewa babu ruwanta da wannan masifa, sannan suka ci gaba da breakfast cikin nauyin zuciya da shiru. Bayan sun kammala, Abbah ne yayi wa Ammy sallama cewa zai wuce Kaduna wurin ɗayar matarsa wato uwar su A'isha ƙawar Amal... AMAL jin haka yasa ta sau murmushi tana duban Ammy taga wani irin reaction ne zai bayyana a fuskar ta... A tsawace Ammy ta ce "To ina ruwana, idan ka je kada ka taɓa dawowa gidan nan, tin da zuwa take lasa maka a baki, kada ka ƙara mun sallama in zaka tafi wurin wancan mahaukaciyar matar takan.." Abbah yana duban ta ya ce "To sai bayan kwana biyu kuma..." Ammy tana huci ta ce "Kayi shekara ɗari idan ka ga dama..." Da haka Abbah ya tafi tare da Maleekh suka fice... Amal tana zaune akan sopa tana fuskarta plasman da dariyar Ammy akan fuskarta... Arfat ganin yanda Amal take da murmushi kamar bata da wani damuwa, yasa ta je gabanta tana faɗin "Ke wai kin manta inda kika fito ne? Ƴar talaka kawai, kin samu damar shigowa gidan mu shine kina ji da kai... In ba don Yaya bane ya kawo ki, da tunin an kore ki daga nan!" Amal ta kalle ta cikin nutsuwa ta ce: "Arfat, ban zo nan don mu yi takaddama ba. Ban kuma zo neman girma ba. Allah ne ya kawo ni, kuma duk wanda Allah ya ɗaukaka, babu wanda zai iya wulakanta shi." Islam kuwa, tana zaune gefen kujera, ta ce a hankali cikin taushin murya: "Ku daina mana....." Islam tana kallon Arfat ta ce "Amma fa, ba haka ake yi ba. Tinda Yaya Maleekh ne ya kawo ta gidan nan, to akwai dalili, kuma bai dace a wulaƙanta ta ba." Ammy ta ɗan zaro ido tana kallon Islam, dake itace mai ɗan sauƙi ta ce "Ke ma kin fara nuna wa wannan matsiyaciya goyon baya kenan? To ki kalle ni da kyau, ba zan taɓa yarda ta zama surukata ba!" Farha ta sake matsowa kusa da Amal cikin harara ta ce "Kin ji dai? Ni ce matar da Maleekh zai aura. Ki fita daga gaban mu, ki daina ƙoƙarin shiga tsakaninmu... Kafin ki gane da ruwa ake shayi, ki duba yadda gidan nan yake buƙatata, ba ke ba!" Amal ta ɗan murmusa cikin taurin zuciya, ta dubi Farha idon cikin ido sannan ta ce "Farha, mijin da Allah bai rubuta miki ba, ba ki isa ki riƙe shi ba. Kuma mijin da Allah ya rubuta miki, babu wanda zai iya kwace shi daga gare ki. Don haka ki daina jin tsoro ko ƙiyayya a kaina." Farha ta ƙara tunzura tana huci... Ammy ta daka mata tsawa tana faɗin. "Ni ba zan ɗauki wannan abun kunya ba! Ki jira Maleekh ya dawo, yau sai dai ya zaɓa, ni ko ke, wato har kin samu bakin mayar wa koh?!" Farha cikin jin nasara ta tsaya a gefe tana dariya tana tafa hannuwa, tana faɗin "Amal, ki shirya tafiya, domin nan ba wurinki bane!" Ammy cikin fushi ta wurga wa Amal harara tare da faɗin "Wai tsaya,, Ke ɗin wacece?..." Amal tayi murmushi sannan tace "ni ƙawar A'isha ce, ƴar kishiyarki dake kaduna..." Ammy cikin fushi ta zabga wa Amal mari tare da faɗin "Aikin banza kawai, to uwar A'isha ma dan buro ubanta ba komai ne a wurina ba balle A'isha, balle ke ƙawar Aisha, saboda kin raina mun wayo shine zaki bani wannan amsar koh?..." Farha tana dariya tace "ƙawar ƴar kishiyar Ammy? Lallai da kalan dangi kike kam, kenam Aisha ce ta haɗa ki da Maleekh koh?.." Amal

Chapter 13 of 62