kenan. Tunda mahaifiyarki da mahaifinki sun rasu, mu ne iyayenki yanzu. Kuma wannan aure dole ne ayi shi."
Maleekh ya tashi daga inda yake zaune, ya tsaya a tsakiyar falo, idanunsa sun canza launi kamar wanda ya daɗe da rashin bacci...cikin fusata ya ce:
"Ba za a yi ba! Ba za a taɓa ɗaura mata aure da wani ba, tunda ina raye!"
Zainabu ta ce cikin tsoro:
"Subhanallah! Wannan yaro fa yana da zuciya kamar wuta. Waye kai da zaka hana aure da doka ta tabbatar?"
Kabiru ya miƙe shima yana kallon Maleekh da fushi ya ce:
"Wato kai ne kake hana auren? To ka sani, ko kai waye, ni dai bazan haƙura da Amal ba. Na ɗauki alkawari, gobe da safe za’a ɗaura auren nan, sai meye?"
Maleekh ya yi murmushi mai sanyi, idanunsa sun cika da fushi ya ce:
"Za’a ɗaura aure a kan matata? Kai,(yana nuna Kabiru) sannan yace "ka shirya, saboda idan aka yi hakan wallahi a ranar sai dai a zubar da jini!"
Amal a zabure ta miƙe ta riƙe hannunsa cikin kuka ta ce:
"Dan Allah Maleekh ka tsaya, ka bari muji me Abbah zai ce..."
Abbah ya miƙe da kansa, yana duba duka fuskokinsu cikin girmamawa da ƙasaita ya ce:
"Na fahimci akwai son juna a tsakaninku. Amma Maleekh, ka saurare ni. Amal yanzu tana ƙarƙashin ikon waɗannan, kuma aure a musulunci yana bin hanya da izinin iyaye. Na roƙeka ka haƙura har sai an samu mafita. Kada ka yi abu da zaka yi nadama."
Maleekh ya juyo da idonsa yana kallon Abbah, hawaye suka taru masa a fuska ya ce:
"Abbah, meye amfanin doka idan zuciya tafi ƙarfin dokar? Ni bana son wata mace face ita, Amal ce rayuwata!"
Abbah ya sauƙe ajiyar zuciya, ya ce a hankali:
"Zan nemi hanyar da zata daidaita wannan lamarin, amma ban yarda da tashin hankali ba. Bari mu bar wannan maganar zuwa gobe da safe."
Inna ta harare su ta ce:
"Ni dai babu wanda zai shawarce ni! Aure za’a yi, gobe sai an ɗaura. Sai dai idan wannan saurayin yazo ya tarwatsa mana gidan!"
Maleekh ya juyo yana kallon Amal cikin murya mai rauni:
"Idan har gobe suka ɗaura auren nan Amal, wallahi ba zan taɓa ƙyale kowa a nan cikin lafiya ba."
Amal ta rufe fuskarta tana kuka sosai, tana faɗin:
"Ya Allah, ina zan saka kaina yanzu...?"
Abbah ya kalli Amal, ya ce da nutsuwa:
"Ki kwantar da hankalinki, komai zai daidaita, amma ki bar komai hannun Allah. Ki yi addu’a kawai."
Falonnan ya cika da shiru. Sai ƙarar bugun zuciya da ajiyar rai kawai ke tashi..
Kabiru ya sake magana cikin daga murya ya ce.
"Gobe da safe Aure, ba wata tattaunawar da za'ayi..."
Maleekh a fusace ya juyo yana kallonsa, fuska a murtuke yake nuna Kabiru da yatsa ya ce...
"Kai ƙazamin ƙauye, ka iya harshenka, domin idan ka cigaba da ɗaga mun murya zan daddatse maka harshe, ko nasa ayi kidnapping ɗinka, inada iko akan hakan..."
Zainabu ta riƙe Kabiru tana faɗin
"A'a Kabiru ka daina jayayya da wannan domin zai iya yin komai aradu.. Ka kiyaye shi ba sa'arka bane.."
Malam Yawale shima kallon Kabiru yayi tare da girgiza masa kai akan yayi shiru kada su rasa shi...
Maleekh ya ce:
"Bana wasa da kai..."
Abbah ne ya bubbuga kafaɗar Maleekh yana rarrashinsa...
“Yaron kirki ka zauna. Wannan ba wurin hayaniya ba ne. Mu raba hankali, mu tattauna.”...
Abbah ganin Maleekh ya kasa kwantar da hankalinsa yasa shi kallonsa ya kuma kalli Amal ya ce.
"Auren nan an dakatar da shi, Amal da Maleekh ta dace, saboda haka kowa yayi hak'uri a bar maganar auren nan, idan lokaci yayi za'a ɗaura auren Maleekh da Amal..."
Sai yanzu Maleekh ya ɗan yi murmushi yana kallon Amal..
Sannan Abbah ya ce da su.
"Amal--Maleekh yanzu ku tashi ku tafi an gama da ku..."
Suka tashi suka fita cikin kwarin gwiwa..
Daga bisani Abbah ya kalli su Malam Yawale ya ce da su.
"Ku kwantar da hankalinku, kamar yanda kuke so ku haɗa auren zumunci insha Allahu zaku yi, babu abunda zai fasa auren Amal da Kabiru gobe, ku cigaba da shirin ku...ina tare da ku, nayi hakan ne saboda yaran su kwantar da hankalinsu..."
Kabiru ya ce
"Sai yanzu naji zuciyata tayi sanyi..."
♡♡♡♡♡♡
▪︎▪︎▪︎▪︎▪︎▪︎
Washegari da safe, Abbah yana sanye da manyan kaya da gariya, ya sanya farin glass akan idonsa yana zaune yana tunanin yanda zaiyi da Maleekh, ga shi yanzu duk sunyi shirin tafiya ɗaurin aure ba tare da sanin Maleekh ba, yana so ya ɓoye masa maganar ɗaurin auren..
Sai ga Ammy ta shigo falon ta zauna kusa da Abbah, ta ce
"Lafiya kuwa?.."
Abbah ya ce
"Tunani nake yanda zan tsare Maleekh daga batun auren Amal da wancan yaron, nayi masa alƙawarin an janye auren, alhalin za'ayi babu fashi..."
Ammy ta ja dogon numfashi sannan ta ce
"Kar ka damu da wannan zan san yanda zanyi da shi, bazai je wurin ɗaurin auren ba balle ya ta da rigima.."
Abbah ya ce
"Taya zaki dakatar da shi?..."
Ammy ta ce
"Kai dai kawai ka zuba ido, za'a je a ɗaura aure lafiya a dawo lafiya, yanzu ya riga da ya kwantar da hankali akan a fasa..."
Abbah ya ce
"Shikenan, ku ma zaku je ne?.."
Ammy ta ce
"Eh, zan je naga ɗaurin auren Amal, zanyi farin ciki da hakan domin hankalin kowa ya kwanta..."
Abbah yayi shiru ba tare da ya furta komai ba, shima kansa yana son Amal da Maleekh...
A part ɗin Maleekh kuwa..
Yana zaune a bakin gadonsa, yana sanye da farar t-shirt, idonsa jawur kamar wanda bai kwanta ba tsawon dare.
Har yanzu maganganun jiya suna dawo masa, musamman yadda aka nemi tilasta masa barin Amal.
Ya jingina da bangon gado yana sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi, ta wani ɓangare yana jin daɗin dakatar da auren da akayi...
Sai ga ƙarar ƙofar falo ta buɗe, sannan aka ƙara turo ƙofar bedroom da sallama..
Ammy ce ta shigo a hankali, hannunta riƙe da tray ɗin da ke ɗauke da lemo da cup.
Tayi murmushi, ta zauna kusa da shi.
Ammy tana murmushi ta ce:
“Maleekh... ka rage tunani, kaji? Abbah ya magance komai. Ba wani aure da za’a ɗaura wa Amal, komai ya ƙare.”
Ta miƙa masa lemo.
Ya ɗauka, ya shanye a hankali.
Ta ƙara da cewa,
“Ka kwantar da hankalinka ɗana, komai zai gyaru.”
Sai dai cikin lemun da ta zuba, akwai maganin bacci mai ƙarfi — 24 hours.
Domin ba za su taɓa iya ɗaura auren Amal ba idan Maleekh yana cikin hayyacinsa.
Bayan mintuna kaɗan, idanunsa suka fara lumshewa.
Ya jingina da jikin gadon, sannan a hankali ya kwanta, numfashinsa ya daidaita.
Ammy ta miƙe, ta ɗan murmusa da ƙarfin hali tana faɗin:
“Ka huta ɗana... komai zai kasance yanda nake so.”
🌤️ A gefe guda...
A gidansu Amal kuwa, ana ta shiri kamar ana shagalin sarauta.
An kafa tent a waje, an kawata da farin balloon da golden ribbon.
Muryar tana tashi ƙaramar wakar soyayya, mutane na ta dariya da murna.
Malaman ɗaurin aure sun iso, an shimfiɗa manyan tabarmai da kujeru....
Abbah ya shirya cikin babbar riga da hularsa, ya gyara ɗan farin gemunsa, fuskarsa da annuri, sai dai idanunsa sun ɗan nuna gajiya da damuwa.
Zayd ma ya fito cikin shadda navy blue, yana takawa cikin nutsuwa, amma zuciyarsa kamar ana hura masa wuta.
A yau dai, za’a ɗaura auren Amal da Kabiru..
👰 A ɗakin amarya Amal...
Tana zaune a gaban madubi, idonta a kumbure saboda kuka.
Ƴan mata suna shirya ta, amma ita babu walwala.
Hannunta na rawa, idonta na zubar da hawaye kamar ruwan sama.
Amal cikin kuka ta ce:
“Allah ya sani... bana son wannan aure, bana son shi... Maleekh ne kaɗai a raina.”
Inna tana tsaye a gefe tana share zufa tana faɗin,
“Shiyasa nace kar a bar ki da wancan Maliku, kinji yadda yake ruɗar da ke yanzu...”
Amal tayi saurin durƙusa wa ta kama ƙafarta tana faɗin,
“Inna ki taimaka ki sanar musu, wallahi bana so...”
Inna ta girgiza kai.
“Magana ta gama tsaruwa, aure ake yi yau.”..
A wajen ɗaurin aure...
Mutane sun taru sosai.
Ƙarar “Allahu Akbar!” da “barka da war haka” na tashi daga ko’ina.
Malaman aure sun zauna da takardunsu, ana jiran kawai a shafa fatiha.
Kabiru na gefen malam yawale cikin farin shadda, yana murmushi da sanyi a zuciya.
Abbah yana gefe, yana ƙoƙarin riƙe nutsuwarsa..
Kabiru ya sanar da cewa "Ya amince da auren Amal" Abbah shine mai karɓan auren Amatullah Abdulsamaad bisa sadaki dubu ɗari biyar...
Cikin farin ciki ana ƙoƙarin shafa fatiha...kowa ya ɗaga hannu..
Sai kawai aka ji ƙarar mota a wajen.
“Vruuuuuum!!!”
Wani irin danna burki akayi har sai da mutane suka tsorata, wasu na ƙoƙarin guduwa...
Motar tayi brake a fusace har ƙura ta tashi.
Kowa ya juya yana kallon motar...
A nan ne aka ga Maleekh ya fito daga cikin motar sanye da white t-shirt da 3quater, idonsa jajur kamar wuta, fuskar sa a rikice.
Shiru ya mamaye wurin.
Kowa ya tsaya, malamai suka tsaya da takardunsu.
Kabiru shima ya kasa motsawa..
Maleekh ya ɗago hannunsa da wuƙar da ke hannunsa, yana tafiya a hankali cikin natsuwa mai firgitarwa.
Yana zuwa ya tsaya a bayan Kabiru, ya ɗora masa wuƙa a wuya...
Maleekh cikin tsawa yake furta:
“Ana shafa fatiha da sunansa... wallahi zan yanke masa makogoro!
In ya sake sunansa ya fito daga bakinku a matsayin mijin Amal, to zan jira ta yi takaba — sannan na aureta!”
Jikin Kabiru ya fara rawa.
Yana jijjiga hannunsa yana ihu, tare da faɗin
“Don Allah kar ka yanka ni! Na fasa! Ku dakata da ɗaurin auren!”.
Jin hayaniya yasa mata daga cikin gida suka firfito gaba ɗaya..
Zainabu ta ɗauki ihu tana neman taimako,
“Wayyo Allah, a taimake ni! Maleekh zai kashe ɗana!!”
Malam yawale ya durƙusa yana kuka,
“Don Allah malamai ku dakata! Kada ku ɗaura aure, don Allah!”
Abbah ya nufi gaba yana faɗin,
“Maleekh! Ka ajiye wukar nan, please yarona! Ka saurare ni!”..
Amma Maleekh ya rufe ido ya ɗaga masa hannu yana huci, ya ce:
“Abbah kada ka matso mun! Idan har aka ɗaura, jini zai zuba ne!”
Wasu daga cikin jama’a suka soma gudu, wasu kuma sun ɗauka ya haukace.
Hayaniya ta tashi, mata sun fito daga cikin gida da hijab a hannu..
Inna ta durƙusa tana kuka tana cewa,
“Wannan wani irin al’amari ne haka? Ya Allah ka kare mu da jarabar nan!”
Amal da gudu ta fito daga cikin gida, rigarta tana ja a ƙasa, idonta cike da hawaye.
Ta nufi wurin, ta kama hannunsa tana kuka,
“Maleekh dan Allah ka ajiye wukar nan! Ka saurare ni, bana son auren nan nima!”
Sai lokacin ya saki wuƙar a hankali, ya kama Amal da hannu biyu ya rungumeta kamar zai haɗiyeta, yana huci cikin kuka..
“Bazan taɓa bari su raba mu ba Amal... wallahi bazan bari wani ya aure ki ba.”
Kowa ya tsaya yana kallon su, shiru ya mamaye wurin.
Kamar film ɗin da aka tsaya a tsakiyar zafi...
Wurin ɗaurin aure ya tarwatse.
Malaman aure suka tashi suka tafi.
Kabiru da iyayensa suka ɓuya don guje wa rigima.
Abbah ya rasa kalmar da zai ce.
Ammy kuwa ta rikice, hawaye na zubo mata.
Zayd ya janye gefe yana faɗin,
“Daman wannan mutumin ne a zuciyarta... mu dai wasa ne gareta.”
Amal ta kalli Maleekh cikin hawaye, tana murmushi da zafin da zuciyarta ke ji,
“Na san zaka zo... ban taɓa yarda zaka bari su ɗaura aure na da wani ba.”
Maleekh ya girgiza kai,
“Ba rabuwa a tsakanina da ke, har sai rai ya fita daga jikina.”....
Abbah ya rufe fuskarsa da tafin hannu yana sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi. Ammy ta kasa magana, ta kalli ɗanta da kallo mai ɗauke da mamaki, fushi, da ɗan tsoron irin yadda zuciyar Maleekh ta iya rikicewa saboda soyayya.
Malam Yawale kuwa ya kamo ɗansa Kabiru da hannunsa yana faɗin:
"Kai Kabiru, mu tafi gida kafin wani abu ya sake faruwa. Kaddarar da ba ta zama taka ba, ka bari ta tafi. Allah zai baka rabonka kaima..."
Zainabu tana kuka ta biyo bayansu, ita ma tsoron abin da ta gani bai bari ta zauna ba. Halima ƙaramar ’yar su kuwa ta manne jikin mahaifiyarta tana faɗin cikin rawar murya:
"Umma wannan mutumin fa mahaukaci ne wallahi..."
Amal ta tsaya tana kallonsa, zuciyarta ta cika da farin ciki da tsoro a lokaci guda. Tana jan numfashi a hankali, sannan ta ɗan murmusa cikin hawaye:
"Na san baka son rabuwa da ni, Maleekh. Amma da ace baka zo yau ba, da na zama mallakin wani. Na gode Allah da ya kawo ka akan lokaci..."
Maleekh ya ɗan murmusa, murmushi mai haɗe da zafi da nutsuwa.
Ya ɗora hannunsa a kafaɗarta, yana faɗin:
"Kada ki sake bari wani ya kusance ki ko ya sake shirin aure dake. Koda ni ban gani ba, soyayyata zata gani.".
Daga nan ya juya ya nufi motarsa zai tafi...
Yana tafiya kamar basaraken sarki...
Amal ta saki dariya mai sanyi, ta share hawayenta tana kallon yadda yake fita daga cikin taron da mutanen da suka rage ke bin sa da ido.
A gefe, Zayd yana tsaye yana kallon su daga nesa, ransa a ɓace, yana faɗin cikin haushi:
"To yanzu meye nake jira? Tabbas dole ne na samu Pretty, ko da kuwa dole sai na bi ta hanyar da ba kowa yake so ba..."
Sai ya juya ya bar wurin da sauri, yana cike da nufin da ba kowa zai gane ba.......
NEXT NEXT NEXT
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 57 to 58
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
A falon babban gidan Abbah da Ammy zaune a kan kujera, Maleekh kuma yana tsaye a gaban su kamar yaro da ya aikata babban laifi. Idanunsa sun kumbura saboda fushi da gajiya, yayin da hannunsa ke ƙasa yana karkarwa.
Abbah na daka masa tsawa cikin murya mai nauyi:
“Maleekh! Ka san abinda kayi kuwa?! Ka san irin abin kunyar da kayi mana a gaban jama’a? Ka san irin abin da hakan zai iya haifarwa ga sunanmu da matsayina a idon mutane?!”
Maleekh ya sunkuyar da kai, idonsa ya kaɗa yayi ja saboda tsananin zafi da baƙin ciki.
MALEEKH a raunane ya ce:
“Abbah… bazan iya haƙura ba. Bazan iya kallo ana ɗaura auren Amal da wani namiji ba. Na tabbata da ban shiga tsakani ba, da yanzu—”
AMMY ta katse shi da tsawa tana faɗin:
“Da yanzu me?! Da yanzu ka kashe mutum?! Kai ba ka da hankali ne Maleekh?! Wannan soyayya ta Amal zata kaika ga hallaka ne! Wallahi bazan taɓa yarda ka auri waccan matsiyaciyar yarinyar nan ba!”
Ta zabura ta miƙe tsaye, hannunta na rawa, idonta cike da hawaye.
AMMY ta cigaba cikin fushi:
“Kai ɗan gata ne, ɗan gwamnati, ɗan masu daraja! Amma yanzu ka juya saboda matsiyaciyar yarinyar can? Ƴar talakawa? Yarinyar da babu ko asalinta mai daraja? Kai baka ganin yadda take wulaƙanta mu?”
Maleekh ya ɗago kansa a hankali, murya a karye:
“Ammy, karki ci gaba da cewa haka. Amal bata da laifi… bata taɓa cutar da kowa ba. Ita ce rayuwata… idan har ba ita ba, to babu wacce zata iya maye gurbin ta a zuciyata.”
Abbah ya hura iska cikin takaici, ya juyo da murya mai taushi da ƙarfi yana faɗin:
“Maleekh! Ka saurare ni sosai… ba haka rayuwa take ba. Idan ma soyayya kake, akwai iyaka. Kai ɗan manya ne, ka san irin matsayi da nake dashi a ido al’umma. Ba zamu iya bari ka zubar mana da mutunci saboda mace ba.”
Maleekh ya matso kusa da su, muryarsa na rawa ya ce:
“Abbah, wallahi bana neman abin duniya. Bana neman gadonku. Abinda nake nema kawai shine ita. Ita ce nake so. Kuma idan wani ya sake ƙoƙarin ɗaura mata aure, wallahi sai dai a mayar da wurin, gurin jana’iza!”
Ammy ta rintse ido cikin fushi, ta ɗaga hannu tana nuna masa ƙofa:
“To sai ka fice daga wannan gida! Idan soyayyar Amal tafi iyayenka, tafi martabarka, to fita ka koma wajenta! Amma wallahi a wannan gidan, baza ka taɓa auren ta ba. Na rantse da Allah!”
Shiru ya ratsa ɗakin. Sai numfashin Maleekh da ya tsananta.
Abbah ya kalli Ammy ya ce
"Kin ga, ɗauko mun ruwan sanyi, makogorona ya bushe..."
A fusace Ammy ta bar falon kai tsaye frig ta nufa...
Abbah cikin murya mai sanyi ya ce:
"Maleekh... kai da nake ganin ka fi kowa nutsuwa, sai ka zama abin mamaki? Shin wannan aikin da ka aikata daidai kake ganin yayi ne? Gidan mutane ka shiga da wuƙa a hannu, ka firgita jama'a, ka tozarta sunan iyayenka?"
Maleekh ya kasa ɗaga kai. Idanunsa sun kumbura, a hankali ya furta:
"Abbah… ba zan iya kallon Amal tana auren wani ba… wallahi ba zan iya ba."
Abbah ya girgiza kai cikin takaici. Ya ce
"Amal mace ce, kuma auren nan addini ne, ba hauka ba. Kana so mutane su ce ɗana ya haukace saboda mace?"
Kafin ya ƙarasa, Ammy ta shigo cikin falon da sauri. Tana ɗauke da tray da jug ɗin ruwan sanyi da cups kananu, tana harararsa cikin fushi...
Ta ajiye glass ɗin ruwan da ƙarfi a tebur..
Ta cigaba da faɗa tana faɗin:
"Bazan taɓa yarda ka auri yarinyar nan ba! Wacce bata da asali, bata da daraja. Kai ɗana ne, ɗan mutunci da ƙima — ba zaka lalata rayuwarka saboda ita ba!"
Maleekh ya ɗaga kai cikin zafi, hawaye na zubo masa, murya na rawa ya ce:
"Ki faɗi duk abinda kike so, Ammy… Amma wallahi bazan iya rayuwa babu Amal ba. Ko dai ta zama matata, ko kuma ni na bar wannan duniyar gaba ɗaya!"
Ammy ta ɗaga hannu cikin mamaki da haushi, ta ce:
"Inna lillahi! Ka fara hauka kenan Maleekh?! saboda mace?"
ABBAH a tausashe ya ce:
“Daina faɗin haka ɗana. Ka bar wannan fushin. Idan har kaddara ta ce ita ce taka, babu wanda zai iya hanaka. Amma yanzu, ka kwantar da hankali. Ka barni da wannan maganar.”
Maleekh ya girgiza kai, hawaye suka zubo masa a kunci.
Ya ce:
“Abbah, ko da me zai faru, bazan taɓa bari a raba ni da ita ba. Babu wanda zai iya raba zuciyata da Amal. Koda hakan zai zama ajali na…”
Abbah cikin murya mai ƙarfi, yana ɗaga hannu ya ce:
"Is enough! Ku daina wannan maganar a gaban na.. Maleekh, wannan abun da kayi ba daidai bane. Amma yanzu… kayi shiru. Idan har kana son kiyayewa da wannan yarinya, to sai ka nutsu. Ka bar min maganar. Amma ka sani —"
Ya ɗan ja numfashi.
"Duk wanda ya kuskura ya sake jawo irin wannan tashin hankali, sai hukunci ya ziyarce shi. Amma, idan soyayyarka gaskiya ce, zan bincika wannan al’amari."
Maleekh ya zube a ƙasi yana share hawaye, yana kallon Abbah kamar ɗan da yake neman gafara. Ya ce
"Abbah, wallahi bana neman komai… burina ka bari Amal ta zama tawa. Zan iya fuskantar komai saboda ita."
Abbah a hankali, yana kallon shi da tausayi ya ce:
"Ka tashi ka je ka huta. Zan yi magana da Inna Delu… amma idan har na sake jin wani tashin hankali, ka sani wannan karon ba zan tsaya ba."
Maleekh ya tsaya tsayin daka yana kallon ƙasi. Ammy ta tsaya tana kallonsa da mamaki, ganin hawaye suna zubo masa...
Maleekh ya ce:
"Ko me zaku yi, ba zan bar Amal ba. Soyayya ce, ba son zuciya ba."
Ammy ta yatsina fuska ta ce:
"To mu gani… wane ƙarfin soyayya ne zai doke ikon uwa da ɗanta."
Yayi shiru yana kallon su, ya juya a hankali, ya fice daga falon cikin nutsuwa amma a zuciyarsa wuta ce take ci.
Abbah ya bishi da ido cikin damuwa, ya sauƙe numfashi.
Ammy ta zauna ta dafe kai, tana faɗin:
“Allah Ya shirya mana wannan yaro… saboda ina tsoron abin da soyayyar nan zata haifar.”
Falon ya koma shiru kamar ba kowa...
☆☆☆☆☆
Washegari da safe, zuciyar Abbah cike take da nauyi. Duk daren jiya bai runtsa ba. Kalaman Maleekh, duk suna masa yawo a cikin zuciyarsa. Yasan yanzu lokaci ne da ya kamata ya ɗauki mataki mai kyau domin rikicin ya kai matakin da idan bai shiga tsakani ba, zai iya lalata komai.
Ya shirya cikin farin babban riga, ya ɗauki hularsa ya fita da nufin gidansu Amal.
Lokacin da ya isa, gidan yana cike da natsuwa. Inna na zaune a falo tana lissafin kuɗin da aka kashe wajen shirye-shiryen auren da aka wargaza. Ganin Abbah yasa ta ɗan firgita ta tashi da girmamawa.
Ta ce da murmushi mai nauyi,
“Alhaji, sannu da zuwa, ai bamu tsammanin ganinka yau ba.”
Abbah ya gyara zama, ya ɗan shafa gemunsa cikin natsuwa, sannan ya ce:
“Inna Delu, na zo da magana ta hankali. Akwai abubuwa da suka kai yanzu dole sai an fahimta.”
Inna ta girgiza kai, ta ce:
“To ai yanzu duk duniya ta ji abin da ɗanka yayi jiya. Wani irin abin kunya wallahi. Idan ba don kai mutum ne mai mutunci ba, da na fadi abinda zuciyata ke ji.”
Abbah ya sauƙe ajiyar zuciya. Ya ce
“Inna, wallahi abin ya bani haushi fiye da kowa. Amma ki fahimci abu guda — ɗana yana cikin soyayya, kuma soyayyar da ta kai mutum ya yi wauta irin waccan… ba ƙaramin abu bane.”
Inna ta saki dariyar takaici,
“Soyayya fa kake cewa, Alhaji? Wannan hauka ce, ba soyayya ba. Kasan irin abinda ya aikata a gaban jama’a kuwa? Ya ɓata mun suna, ya ɓata sunanku. Yaronka fa ya ɗora wuƙa a wuyan ɗan mutane!”
Abbah ya ɗan lumshe ido, yana magana cikin tausasawa,
“Inna, na fahimci damuwarki. Amma ki saurare ni — ni a matsayina na uba, bana son wannan auren Amal da Kabiru, domin hakan ba zai kawo mata farin ciki ba. Maleekh ya fi ƙarfin da kike tunani, kuma soyayyarsa ta kai matakin da idan kika ƙi, zai iya lalacewa gaba ɗaya.”
Inna ta jinjina kai da takaici,
“To ai wannan ba dalili bane da zai sa a mayar da abin da ya aikata kamar wasa. Ko a ƙauyensu waɗancan ma da mutum yayi haka da wuƙa, ai tuni an ɗaure shi.”
Abbah ya ce cikin natsuwa,
“Na sani, amma yanzu ina so mu duba gaba. Ki faɗa min gaskiya Inna — Amal, har yanzu tana son Maleekh?”
Inna ta ɗan yi shiru, sannan ta ce,
“Wallahi ina ganin tana son shi. Duk da kuka da ƙuncin da tayi, tun jiya bata ci abinci ba, bata yi bacci ba. Amma ni ban yarda da shi ba, tunda mahaifiyarsa ta riga da ta nuna bata son ‘yar talakawa kamar mu.”
Abbah ya sauƙe numfashi a hankali, ya ce:
“Inna, ni zan daidaita komai. Zan je na zauna da Uwar yaron da kaina. Idan Allah ya yarda, zamu warware komai cikin mutunci. Ba a son ta auri wanda bata so. Kuma ni a matsayina na uba, bana son wulakanta ɗiyar da nake ganin kamar ‘yata ce.”
Inna ta ɗan share hawaye tana murmushi,
“Alhaji, Allah ya saka da alheri. Idan har zaka iya daidaita wannan, to ni na yafe masa. Amma fa, ka gaya wa matarka ta kiyayi yi wa Amal rashin mutunci.”
Abbah ya miƙe, ya ce da nutsuwa,
“Zan gaya mata. Na yi alkawari. Insha Allah wannan soyayyar bazata zama jaraba ba, sai dai rahama.”.
Ya ciro damin kuɗin wanda zai kai 300k ya bata akan ta rage asara..
Inna tana washe baki ta fara godiya, ta durƙusa har ƙasa tana masa albarka...
Suka yi sallama da nutsuwa.
Abbah ya fita yana tunani “Yanzu lokaci ne da zan fuskanci Maryam. Amma da yaushe zata fahimci cewa zuciyar ɗa ba a mulkinta?”
✨ Inna tana kallon ƙofar da Abbah ya fita tana faɗin cikin zuci:
“Allah ka shirya wannan al’amari. Kada a sake jefa Amal cikin wani tashin hankali…”
A daren yau..
A cikin babban falon gidan Abbah, ƙarshen daren ranar da ya dawo daga gidansu Amal.
Wurin ya cika da nutsuwa, sai ƙamshin turaren oud da aka kunna. Abbah yana zaune a kujerar fata yana sosa gashin kansa cikin gajiya. A gefe kuwa Ammy ta shigo da sauri, tana sanye da rigar babu da ya lulluɓe jikinta, idonta kuwa cike da fushi...
Ammy cikin ɗaga murya ta ce:
"Alhaji! To ka dawo ko? Ashe gidan su waccan yarinyar Amal ka je?
Abbah: cikin natsuwa, yana ɗan sauƙe numfashi ya ce:
"Na tafi ne saboda neman lafiya, Maryam.. Na je ne in fahimci gaskiyar abin da ke faruwa tsakanin Amal da ɗanmu Maleekh..."
Ammy ta taka zuwa gabansa ta ce:
"To meye abunda zaka faɗa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 38 Chapter of 62