Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Maleekh ya juya... Abbah cikin fushi ya ce, “Wawa! Mahaukaci! Ka ɗauki hoton da baka san asalin sa ba, kana wulakanta mutuncin ɗan Adam haka?, Kai da bakinka kake zargi yarinya da karuwanci? Waye ya tabbatar maka da gaskiya?” Kafin Maleekh ya maido da numfashi Abbah ya sake zabga masa wani mari na biyu. Falon ya yi tsit! Maleekh ya tsaya cak, yana dafe da gefen fuska. Inna ta rufe fuska da mayafi tana kuka, Amal tana ƙara volume kuka ta ce: “Abbah, dan Allah ka barshi... Allah zai nuna gaskiya.” Abbah ya kalli Amal cikin tausayawa, sannan ya kalli Maleekh cikin fushi ya ce, “Idan akwai Allah a cikin zuciya, wallahi gaskiya zata fito. Kuma idan karya kake, wallahi wannan muryar da kake da ita zata zama la’ana a gareka har ƙarshen rayuwa!” Abbah ya juya ya fice daga falon cikin ɓacin rai, yana huci. Kowa ya tsaya yana kallon Amal da ta durƙusa, tana kuka da rawar jiki. Wani irin shiru mai nauyi ya mamaye gidan, shiru da ke cike da zafi, kunci, da rashin gaskiya. Bayan fitar Abbah, ɗakin yayi shiru kamar ba a taɓa yin magana ba. Maleekh ya tsaya yana kallon Amal cike da jin nasara, yana ɗan murmushi irin wanda yake cike da mugunta da wulaƙanci. Sannan cikin sanyi da murya mai nauyi ya furta: “Ban kwana…” Ya juyo ya fita daga falon ba tare da ya waiwayo ba. Ammy ta bi bayansa tana jan Islam da Arfat. Sai Farha da Amal kawai suka rage a wurin. Amal ta juyo ta kalli Inna, idonta cike da hawaye da tambaya, tana shirin magana. Inna ta ɗaga hannu a hankali tana girgiza kai da cewa: “Ki tsaya, ki je ki huta, Amatu. A yanzu ba lokacin magana bane. Komai ya zama ruɗani… in gaskiya ce, to gaskiya zata fito. In ƙarya ce, itama zata bayyana. Don Allah kar ki takura ni, kar ki takura kanki.”** Ta ƙarashe cikin kuka... Farha ta kama Amal da ta riga ta zama kamar gawa, jikinta yana rawa saboda zazzabi, zuciyarta kuma kamar an ta da ta daga kabari. Ta rakata zuwa ɗakinta sama. Bayan sun shiga, Amal ta faɗa kan gadonta tana lulluɓe jikinta da bargo, tana rawar sanyi. Farha ta fara zagayawa ɗakin tana neman magani a drawers. Tana cikin dube-dube ne idonta ya sauƙa kan wani ƙaramin akwatin da yake haske, mai sheƙin azurfa. A hankali ta ɗauka, ta dubi Amal da take rufe da ido kamar marar numfashi. Farha ta buɗe akwatin... Sai ga hotuna kusan guda goma na Amal da Maleekh tun suna yara. Hotunan cike da annuri, murmushi, da ƙaunar juna. A gefe kuma akwai ƙaramin sarƙa da aka ɗaure da ribbon, sannan wata takarda da aka rubuta da turanci cikin salo: “A + M = Forever. Amal and Maleekh.” Farha ta tsaya, idonta ya cika da hawaye. Tana magana a cikin zuciyarta: “Amal, ki yafe ni… Na ɗauki alkawari cewa bazan bayyana sirrinku ba amma yanzu dole. Wannan cin mutuncin da yayi miki… da yasan kece fiancée ɗinsa, da yasan kece asalin wacce yake jira shekaru da yawa… da yasan kece, da bazai wulaƙanta ki ba.” Ta ja numfashi, ta rufe akwatin a hankali, sannan ta ɗauke shi ta saka cikin jaka. Ta fita daga ɗakin da niyyar tafiya kai tsaye wurin Maleekh... Amal kuwa ta cigaba da kwanciya cikin zazzabi, tana rawar sanyi, idonta lumshe, zuciyarta na tafasa da ƙunci da kukan da ya ƙi tsayuwa. Hawayenta suna bin kan kuncinta a hankali, tana faɗin cikin zuciya: “Ya Allah… kai ka san gaskiyar zuciyata. Ka bayyana ni daga ƙaryar da duniya ta min...” 🕯️ A lokacin da Abbah ya dawo gida, ya zauna cikin fushi da tunani. Bayan wasu mintuna, sai ga su Maleekh da Ammy suka shigo. Bayan sun shigo Abbah ya miƙe cikin ɓacin rai yana nuna Maleekh da yatsa: “Wallahi, wallahi, ka zubda damarka, Maleekh! Damar da ba zata dawo gareka ba har abada. Ka sani Amatu itace damar ka! Amma ka bari ta kuɓuce maka saboda jahilci da ƙiyayya. Nine yanzu madaurin aurenta, kuma na rantse da Allah, bazan taɓa aura maka ita ba!” Ya sauƙar da numfashi mai zafi sannan ya ci gaba: “Ka yi asarar abunda kake farauta. Ka daina tunanin zaka iya dawo da ita. Kayi asara mai girma, domin lokacin ka ya wuce time done go!” Ya kalli Ammy yana daga murya: “Ke kuma! Uwar asara. Ke kike zuga shi, ke kike juyar da zuciyarsa! To ki jira ranar da zaki dawo kina kuka kina cewa: ‘Da na sani…’” Ammy ta zazzaro ido da cewa, “Akan wannan matsiyaciyar? Wallahi babu ranar da zamu yi dana sani!” Abbah ya yi mata kallon da ya cika da tsana da fushi, ya juya ya haura saman part ɗinsa yana girgiza kai. Maleekh kuwa ya tsaya, zuciyarsa cike da ruɗani, bai fahimci cikakken ma’anar kalaman Abbah ba. Ya juyo yana kallon Ammy kamar wanda ya rasa hanya. Ammy ta dafa kafaɗarsa a hankali tana murmushi mai cike da mugunta: “Ka je, yarona. Ka tafi part ɗinka ka huta. Kada ka damu da maganganun tsoho. Gaba ɗaya duniya zata fahimci cewa kai baka da laifi.” Maleekh ya ɗan ɗaga kansa ya yi shiru, ya juya cikin sanyi ya tafi part ɗinsa, amma zuciyarsa tana bugu da tambayoyi masu nauyi, "me yasa Abbah yace na rasa damar rayuwata? Wace ce Amatu to? Bayan awanni da suka wuce, Farha ta iso harabar gidansu Maleekh. Tana shiga babban falon, ta tarar da Ammy a zaune cikin shigar alfarma tana kallo. Ammy ta ɗago idonta da murmushi mai ɗauke da ƙasaita ta ce: “Ha’a, Farha kece? Lallai yau ƙamshin soyayya ya cika gidan nan.” Farha ta tsaya cikin nutsuwa, tana riƙe da jakarta wanda ƙaramin akwatin da ta ɗauko daga ɗakin Amal ke ciki. Cikin murya mai daidaito ta ce: “Ammy… Ya Maleekh yana ciki ne?” Ammy ta ɗan kwaɓe fuska, tana murmushi ta ce, “Kinzo raya soyayyarki ne? Tunda kin san ina son ki, da zan fi kowa farin ciki idan kika same shi.” Farha ta ɗaga kai a hankali ta ce: “Ba wannan ne ya kawo ni ba, Ammy.” Kafin Ammy ta sake cewa komai, ta wuce kai tsaye zuwa saman part ɗin Maleekh. Tana isa ƙofar ɗakinsa, ta fara knocking da ƙarfi. Babu amsa. Sai ta sake bugu, ta danna kararrawar ƙofa, ding… ding… ding… A cikin ɗaki kuwa, Maleekh yana can kwance cikin baccin gajiya. Ƙarar kararrawar ta shiga kunnensa a hankali, yana jan numfashi cikin jin daɗin baccin da aka tarwatsa masa.. A gigin bacci, ya miƙe da ɗan fushi, yana tafiya da ƙyar har bakin ƙofa. Yana buɗewa sai ga Farha a tsaye tana kallonsa.. Ya ɗaga girarsa cikin gajiya, ya ce da ita. “Me ya kawo ki ke kuma?” Farha ta ce cikin kwanciyar hankali: “Nazo wurinka ne.” Ya juya yana komawa ciki tare da faɗin: “Ban da lokacin ki, Farha.” Ta bishi da kallo, sannan ta ce cikin izza, “Ai nasan baka da lokaci na amma ni ma ba wai nazo ganin kyan fuskarka bane ko surar jikinka.” Ya tsaya cak, ya juyo yana kallonta da ɗan murmushi mai ɗauke da raini: “Farha, na daɗe da gaya miki cewa tsakani na dake ba soyayya. Ni ba aurenki zanyi ba.” Farha ta ƙure shi da ido, sannan ta ce cikin ɗaga murya: “Ka ci amanar wacce kake so ma balle ni! Ni asu wa? Ido ba kwalli? Wacce kake yi akanta ma baka kyale ta ba balle wata Farha a gefe! Ni yanzu ba wannan ne ya kawo ni ba don bazan tsaya ɓata lokaci na akanka ba..." Maleekh ya ɗan motsa baki kamar yana son yin dariya, amma daga ƙarshe ya ce cikin taushin murya, “Ni kike gaya wa haka?” Ta ɗaga kai, ta ce: “Eh, kai nake gaya wa. Kar ka manta tsakani na da kai babu soyayya. Don haka kada ka ɗauki komai da zafi don na gaya maka haka..” Ta kai hannu cikin jaka, ta ɗauko ƙaramin akwatin azurfa, ta jefa masa a kirji cikin ƙarfi tana faɗin: “Ga saƙon Amal.” Maleekh ya kama akwatin da sauri, ya kalle shi, sannan ya ja dogon tsaki mai cike da raini: “Mtsssww… banda lokacin ta. Kuma ba abinda zanyi da wannan abun banza.” Farha ta ɗan jinjina kai, ta ce cikin nutsuwa: “Ai dama bata buƙatar lokacinka. Tunda yanzu haka tana kwance tana fama da zazzabi, tana raye ne kawai saboda Allah. Wannan box kuma baya buƙatar lokaci, Duk san da kayi niyyar kan ka zaka iya buɗe wa..." Bayan ta gama maganar, ta juya ta nufi ƙofa cikin nutsuwa ba tare da ta waiwaya ba. Maleekh ya tsaya yana kallonta har sai da ta ɓace daga gani, sannan ya rufe ƙofar yana mamakin ta... Ya koma cikin ɗaki yana faɗi da ƙaramin murya: “"bazan tsaya ganin wani shirme anan ba... nonsense.” Ya tura akwatin can karkashin gadonsa, ya koma ya kwanta, amma wannan karon baccin ya ƙaurace masa.. Yana tunanin meye a cikin box ɗin? Sai dai girman kai ya hana shi buɗewa. Ya rufe ido, amma hoton Amal ne yake yawo a cikin tunaninsa kamar fatalwar da ba za ta bar shi ba.... *_NEXT NEXT NEXT_* asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 75 to 76 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Washegari Amal ta tashi da ƙyar, kanta na mata wani irin mungun sarawa. Kamar wanda aka jefar da ita cikin duhu, haka take ji.. Da kyar ta nufi ƙofar ɗakin tana shirin saukowa daga beni, a yayin da take shirin sauƙo wa ne wani irin hajijiya ya ɗauke ta. Kafafuwanta suka zame daga kan benin. Ta kife akan stairs tana fara gangarowa, sai da ta zo ƙasi goshinta ya bugu da ƙasa, take goshinta ya ɗan fashe... A daidai lokacin Inna ta fito daga ɗakinta, ganin Amal a ƙasa ya sa ta nufar ta da gudu, tana salati. Ta durƙusa tana girgiza ta da rawar murya, “Amal! Amal! Subhanallah! Ina ƴan aiki suke?!” Ƴan aiki suka fito da gaggawa, suka ɗago Amal suka kwantar da ita a kujerar falo. Inna ta haɗiye kuka tana ƙoƙarin ƙiran Abbah da sauri ta sanar masa.. Yana ɗaga wa ta ce. “Don Allah ka turo likita gida. Ba za mu iya kaita asibiti ba, mutane sun ji labarin dawowarta, an riga an baza maganar cewa ta gudu ne a ranar bikinta...” Cikin mintuna ƙalilan Abbah ya turo likita. Shi ma daga baya ya iso. Suka tarar da ita a sume.. Likita ya duba jikinta, ya taɓa goshinta, ya girgiza kai. “Jikinta yayi zafi sosai, da damuwa. Zuciyarta da kanta suna buƙatar hutu.” Suka ɗaga ta zuwa saman ɗakinta, aka kwantar da ita akan gadonta. Aka ɗaura mata drip, likita ya mata allurai sannan ya fice. Abbah ya zauna a bakin gadon, yana kallonta cike da tausayi... Bayan lokaci kaɗan ta motsa, ta fara buɗe ido da ƙyar. Muryar Abbah mai taushi ta fara ji a kunnuwanta, “Alhamdulillah... daughter, kin farfaɗo. Ki daina saka damuwa a ranki..." Ya ɗago ta a hankali sannan ya ɗauki abincin da aka kawo mata. "Ki ci abinci, ko kaɗan ne. Damuwa bata gyara komai.” Da ƙyar ta iya buɗe baki tana ɗan ci, Abbah da kansa yake bata a hankali. Bayan ta ɗan huta, Abbah ya ce da ita cikin tausayi, “Ki kwantar da hankalinki Amal. Ki daina saka Maleekh a zuciyarki. Ki bar komai a hannun Allah.” Amal ta kalle shi cikin hawaye, ta ce da murya mai rauni, “Abbah... shine fa fiancé ɗina...” Abbah ya dan yi shiru, yana kallon idonta cikin tausayawa sannan ya ce, “And so what? Bayan shi akwai waɗanda suka fishi komai, halayya, mutunci, da soyayya. Kina da masoya da dama, har wasu sun zo wurina suna roƙon su aurenki, nace musu ai ni mahaifinki ne zan iya aurar dake ga duk wanda ya cancanta, sai dai ki yarda da wanda kika zaɓa. Ki kwantar da hankalinki. Allah zai baki wanda yafi shi sau dubu.” Amal ta share hawayenta, ta sauƙe numfashi cikin rauni. “Abbah... duk yadda ka yanke...” Abbah ya sa hannunsa ya shafi kanta yana murmushi, “Shikenan, daughter. Kar ki damu. Allah zai ba ki farin ciki dawwamammiya.” Bayan ya gama bata kulawa yasa ta ci abinci sosai, ya miƙe cikin nutsuwa, yana kallonta da idanu masu cike da ƙauna da tsoron kada ta shiga cikin halin da zai tarwatsa rayuwarta gaba ɗaya. Bayan Amal ta kwanta... Abbah ya tsaya cak a bakin ƙofar ɗakin yana kallonta, idonta a rufe tana shakar iska cikin rauni. Ya ɗan numfasa, ya fita a hankali. A falo ya tarar da Inna tana zaune da hijabi a jikinta, hannunta riƙe da tasbihi tana kan sallaya.. Abbah ya zauna kusa da ita, ta juyo tana kallonsa ta ce “Alhaji... ni kam zuciyata ta kasa kwanciya. Wannan yarinyar ta rame kamar wanda ake tsotse jininta. Idan ka kalle ta, ba kamar Amal ɗin da muka sani ba.” Abbah ya dafa kansa, ya girgiza kai. “Ni ma haka nake gani, Mama. Wannan abun da ya faru ya girgiza ta sosai. Amma tunda ta dawo gida, in sha Allah zan kula da ita da kaina. Zuciyarta tana buƙatar natsuwa, ba tambayoyi ko zargi ba.” Inna ta share hawayen idonta ta ce: “Allah Ya kyauta, amma ka dai lura. Wannan kukan zuciya da take boyewa yana da hatsari. Ko da yake ban san me ya faru da ita a lokacin da ta ɓace ba, amma akwai wani abu da ta ɗauko a ranta daga can.” Abbah ya ja numfashi mai nauyi, sannan ya ce, “Kin faɗi gaskiya. Har yanzu ban gane yadda ta ɓace ba, balle yadda ta dawo. Amma ko meye sirrin nan, lokaci ne kaɗai zai bayyana mana. Abin da nake so yanzu shi ne ta rayu lafiya...Shi kuma Maleekh zanyi maganinsa domin duk saboda shi ta kasa kwantar da hankalinta..” Ya ɗan yi shiru, yana kallon gefen sama kamar yana neman karfin gwiwa daga sama. “Mama, ki kula da ita sosai. Kada ta bar gida ko da minti ɗaya. Zan saka masu tsaro biyu su kula da ƙofar gida..” Inna ta gyada kai, ta ce. “Toh, Allah Ya taimake ka. Zan kula da ita kamar jaririya...” Suka yi shiru na ƴan dakikoki. Inna ta ɗan ce da muryar kuka. “Allah Ya dawo mana da jikata yadda take da…” Abbah ya amsa da “Amin” cikin murya mai sanyi da ƙasaita kamar wanda yake ƙoƙarin ɓoye wani abu a ransa. Sai ya miƙe, yana kallon beni inda ɗakinta yake. Wani irin shiru ya mamaye falon.. Cikin dare. Iskar sanyi tana kaɗawa daga taga, labulen ɗakin yana motsawa a hankali. Wutar ɗakin ta yi lumm, lamp mai green light dake gefen gado ce kaɗai ke bada haske, tana haskaka fuskar Amal da ta kwanta cikin shiru. Inna ta fito daga ɗakinta bayan ta idar da sallar tahajjud. Zuciyarta ta kasa samun natsuwa, saboda tunanin yarinyar nan da take can ɗakin ta.. Da taka-tsantsan ta ɗauki fitilar hannu sannan ta nufi sama. Ta tura ƙofar ɗakin Amal a hankali, ƙamshin turaren ɗakin ne ya buge ta. Ta tsaya a bakin ƙofa tana sauraron numfashinta. Sai kuma taji kamar Amal tana sambatu a hankali, tana magana cikin bacci. Da sauri Inna ta ƙaraso kusa da gadon, ta durƙusa, ta ji Amal tana faɗin cikin rawar murya: “Maleekh... dan Allah ka daina gudu na... kada ka cutar dani... na rantse... ka yarda dani, dan Allah ka yarda dani, wallahi inasonka...” Sai hawayenta suka fara gangarowa a kan pillow, tana juyi a gadon kamar wacce ke gudun mafarki mai ciwo. Inna ta dafa kafaɗarta a hankali tana lallashinta: “Shh... shh... ya isa Amatu...ki kwana lafiya, ki huta. Komai zai yi dai-daita in sha Allah.” Amal ta ɗan buɗe idonta, kamar wacce ta farfaɗo daga mafarki, amma sai ta sake runtse su, tana fitar da numfashi mai nauyi. Inna ta zauna gefen gadon, ta dafa kanta. Hawayen tausayi suka cika idonta. A hankali ta fara karanta mata surar Yasin, tana shafa kanta bayan kowace aya. Lokacin da ta gama, ta jingina da jikin gadon tana kallon Amal da ta koma bacci cikin shiru. A ranta ta ce, “Ya Allah, idan akwai gaskiya a cikin soyayyarsu, ka mayar musu da zaman lafiya. Ka tabbatar da adalci, ka kare jikata daga zafin ƙaddara.” Ta sake share hawayenta, ta miƙe cikin nutsuwa, ta rufe mata ƙofa, sannan ta fita a hankali tana ƙiran sunan Allah har ta sauƙo ƙasa. A cikin ɗakin, fitilar ɗaki ta cigaba da haskaka fuskar Amal, fuskar da hawaye suka shafe, amma a gefen leɓenta akwai ƙaramin murmushi kamar tana jin wani a zuciyarta… ☆☆☆☆☆ Cikin babban office ɗin Abbah, mai cike da kayan alfarma, framed certificates, tambarin ƙasa a bango, da ƙamshin turaren oud mai sanya nutsuwa. Abbah yana zaune a kan babban kujerarsa mai juyi, yana kallon wasu takardu.. A gefe guda, jami’in sa na tsaro ya kawo masa saƙon cewa Zayd ya iso. Abbah ya ɗaga kai kaɗan, ya ce da shi: “Ka shigo da shi ciki.” Bayan mintuna ƙofar ta buɗe, Zayd ya shiga cikin ladabi, yana sanye da suit mai kyau. Ya tsaya yana gaishe shi: “Assalamu alaikum, barka da aiki Abbah.” Abbah ya ɗaga kai kaɗan, ya amsa da murya mai ƙarfi: “Wa’alaikumus salam, Zayd. Zauna.” Zayd ya zauna da ɗan ɗoki, yana dafe ƙafarsa da hannunsa, kamar wanda ba ya jin daɗin zama a wuri ɗaya.. Abbah ya jingina da kujerarsa, ya ɗan dubi Zayd sama da ƙasa, sannan ya ce cikin nutsuwa da nauyin murya: “Ya Daddyn naku? Har yanzu yana kasar nan?” Zayd ya amsa cikin girmamawa: “A’a Abbah, ya koma London. Yanzu haka yana duba harkokin business ɗinsa can.” Abbah ya jinjina kai sannan ya ajiye takardun hannunsa gefe. Sai kuma ya ɗan yi shiru kafin ya ɗaga ido ya dubi Zayd kai tsaye: “To, bari muje kai tsaye. Ina tambayarka, meye tsakaninka da Amatu?” Zayd da yake zaune ya ji kirjin sa ya buga da karfi. Ya ɗan dafe ƙirjinsa, ya kasa kallon Abbah a ido. Sai kuma ya ce da sanyin murya, “Abbah, gaskiya tsakaninmu... wallahi ina sonta ne. Kuma wannan son ba na wasa ba ne, son gaskiya ne. Ba na neman cutar da ita.” Abbah ya kalle shi cikin tuhuma, sai kuma murya ta canza: “Kana sonta ne, sannan kake neman ta da lalata? Kake neman cin zarafinta?” Zayd ya sunkuyar da kansa, ya kasa cewa komai. Abbah ya ɗan tafa hannuwansa biyu cikin takaici. “Zayd! A duk lokacin da kake neman kusantar ta sai kayi hoto ka turawa Maleekh? Me yasa? Me kake nema?” Zayd ya girgiza kai: “Wallahi Abbah, banyi haka da niyyar cuta ba. Sau ɗaya ne, lokacin da muka haɗu a waje na rungumeta ta baya, sai wani daga nesa ya mana hoto... amma ban sake ba!” Abbah ya ce cikin ɓacin rai: “To wa ya je ya kwana da Amal a gadonta ba tare da ta sani ba? Waye?!” Zayd ya yi shiru, jikinsa ya soma rawa. Abbah ya daka masa tsawa da ƙarfi: “Ina tambayarka Zayd! Waye ya kwana da ita?!” Zayd ya ɗan girgiza kai cikin firgici: “Abbah... ni ne... amma wallahi bana nufin cutar da ita. Na tura wa Maleekh ne saboda ina son shiga tsakaninsu. Ina sonta ne Abbah, hakan yasa...” Abbah ya datse maganarsa da murya mai nauyi: “Kana sonta ne amma ka zubar mata da mutunci? Kasan hoton nan idan ya fita waje ya labarin zai kasance?. Ka san irin abin da kayi kuwa?” Zayd ya fara hawaye yana cewa: “Abbah dan Allah kayi haƙuri, kayi haƙuri...” Abbah ya ɗan jingina da kujera, ya runtse ido cikin takaici. “Saboda baka son aurenta da Maleekh ne ka sace ta, ko?” Zayd ya zabura da sauri yana girgiza kai: “Wallahi tallahi, Abbah, ban sace ta ba! Ban san inda ta je ba. Na rantse da Allah ban da hannu a ɓatanta ba!” Abbah ya ɗaga masa hannu sama da murya mai cike da iko: “To idan na gano kana da hannu fa, Zayd? Idan na tabbatar da kai ne fa?” Zayd ya share hawayensa yana cewa da rawar murya: “To Abbah kayi mun duk abinda ka ga dama. Kasa a harbe mun kwakwalwa, bana buƙatar jinƙai idan hakan gaskiya ce...” Abbah ya jinjina kai, sannan ya ce cikin sanyin murya. “To ka sani, daga yau na shiga tsakanin ka da Amal. Ba ka da izinin kusantar ta, ko ta hanyoyi, ko ta magana, ko ta waya. Ni zan kareta daga sharrinku.” Zayd ya sauƙe kansa, yana magana a ƙasa ƙasa: “Na fahimta Abbah... shikenan.” Ya miƙe, ya juya ya fita da sauri cikin wani yanayi na kunya da damuwa. Abbah ya bishi da ido har ya fice, sannan ya jingina da kujerarsa yana hura numfashi mai nauyi, ya ce a hankali: “Allah ya kare yarinyar nan daga sharri.. Son zuciya sai ya lalata ku saboda rashin hankalinku....” 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 Bayan sati biyu, Amal ta samu sauƙi daga ciwon jikinta, amma ba ta samu sauƙin zuciya ba. Da safen nan tana zaune a dinning area tare da Inna suna breakfast cikin natsuwa. Sai ga wayarta ta fara ringing. Ƙiran da ya bayyana a fuskar wayar ya sa jinin jikinta ya tsaya cak. “Maleekh…” ta furta a hankali da idanu a zazzare. Inna ta kalleta, ta ɗan ɗaga gira tace: “Meya faru ne, Amal? Waye ke kiranki haka duk hankalinki ya tashi?” Amal ta kalli Inna da fargaba, muryarta na rawa: “Maleekh ne Inna… wayarsa ce!” Inna ta ɗan ɗaure fuska: “To uban me zai miki? Kina jin tsoro saboda yau ya ƙira ki?” Amal ta ɗan girgiza kai, muryarta a sarke: “Ban sani ba Inna… amma kamar zuciyata na sanar min akwai wani abu…” Ta kasa ɗauka har wayar ta katse. Bai jima ba sai ta sake ringing karo na biyu. Ta ɗan matsa kusa da Inna, ta ce a tsorace: “Wallahi bana son ɗauka, Inna. Yanzu da yake ƙirana, ji nake kamar yana ƙirana zuwa mutuwata ne…” Inna ta miƙe ta ɗauki jug ɗin shayi tana zubawa a ƙaramin cup domin ƙarawa, ta furta, “To ki ɗaga ki ji mai zai ce. Ba kowa ke ƙiran mutum sai da dalili.” Amal ta lumshe idanu, ta ja numfashi mai nauyi sannan ta ɗaga wayar. Muryarsa ta fito daga can ƙasa, mai cike da iko: “Ina nemanki a office ɗina… yanzu.” Sai wayar ta yanke. Amal ta kalli Inna cike da mamaki: “Inna wai yana so naje campanynsa.” Inna ta ɗan ɗaga kai: “To ki je. Ki natsu, kar ki ji komai. Ki je ki fuskance shi kamar yadda kika saba.” Bayan breakfast, Amal ta shirya cikin kayan office masu sauƙi. Tana fita daga gida ta tare napep, saboda yanzu ba ta da mota a hannunta. Tafiyar ta ɗauki awa biyu kafin ta isa CashTalk. Bayan ta shiga, ma’aikata suka fara tarar ta da murmushi da girmamawa: “Good morning ma’am!” “Welcome back ma’am!” Ta mayar musu da sallama cikin ladabi, tana murmushin dole... Ta shiga reception, sannan ta shige elevator ya kai ta bene na takwas. A hankali ta nufi ƙofar office ɗin CEO Maleekh.. Tayi knocking sau biyu, daga ciki aka ce: “Come in.” Ta buɗe ta shiga. Ta gan shi zaune a kujerarsa, fuskarsa a ɗaure yana aikin danna computer, ba tare da ya kalleta ba. Ta tsaya a bakin ƙofa, ta ce cikin ladabi: “Gani…” Shiru. Ya cigaba da duba system ɗin kamar ba wanda ya shigo. Mintuna goma cif tana tsaye, jikinta har ya fara rawa domin har yanzu jinyar bai gama sakinta ba. Sai daga bisani ya furta cikin izza: “Baki iya gaisuwa bane?” Amal ta ɗan lumshe ido, ta ce a hankali: “Ina kwana…” Ya ɗan ɗaga kai, yana murmushin gefen baki: “A wannan company kin taɓa jin ana gaisuwa da Hausa?…” Ta ɗan ja numfashi: “Good morning, sir.” Ya amsa da gajeriyar kalma: “Fine.” Sai ya ɗaga kai daga system ɗin, yana kallonta kai tsaye: “A matsayinki na assistant CEO, me ya hanaki zuwa wurin aiki tsawon sati biyu bayan dawowarki daga yawon shalholiyarki?” Amal ta haɗiye yawu cikin rawar

Chapter 49 of 62