kyau, tana gyara wasu takardu. Wata ma’aikaciyar FM ta shigo da hanzarin ta
Ma’aikaciya ta ce,:
“Amal, akwai wani mutum daga Abuja... ya ce sunansa Maleekh Cashbank, ya ce ke ya zo nema.”
Zuciyar Amal ne ta buga da ƙarfi. Ta ɗago kai da mamaki da tausayi a lokaci guda.
Amal Tayi shiru na ɗan lokaci sannan ta ce...
“Shigo da shi.”
Bayan ýan seconni.
Ƙofar ce ta buɗu, sai ga Maleekh ya shigo sanye da suit mai kyan gaske da tsada, yana ɗauke da tabarau. yana mata kallon sama da ƙasa kamar wanda ya zo yi wa ƙasa gadin mulki. Yana dubanta cikin raini,
kamar bai san darajarta ba. Ya zauna a kujera yana ƙare ta da kallo daga sama har ƙasa, sannan ya murmusa da wulakanci ya ce:
“Toh, ke ce Amal? Ashe ba da microphone kawai kike da ƙarfi ba... a zahiri sai na gane ke ‘yar talakawa ce dai dai misali.”
Ya yi mata magana ba tare da ya nuna ya santa ba, kamar bai taɓa sanin ta ba haka yake ta yatsina fuska...
Amal na zaune ba tare da ta yi motsi ba, tana kallonsa ido cikin ido.
cikin ladabi ta ce:
“Na gode da ziyara. Wannan gidan rediyo ne na kowa da kowa....
Maleekh ya ce:
"So... kece Amal da ake ta surutu a social media? Muryar marasa gata... ƴar talakawa da take firfitar da batun siyasa kamar wata jagora?"
Amal ta kalli agogo sannan ta kalle shi cikin kulawa ba tare da damuwa ba Ta ce:
“Ni ce. Barka da zuwa Rayuwa FM, gidan da yake sauraren kowa, ba tare da fifita darajar mutum bisa dukiya ba.”
Maleekh yana dariyar raini ya ce:
“Kina da ƙwarewa, zan ba ki hakan. Amma kuɗi basu tare da ƙwarewa a Nigeria. Na zo ne in ba ki wata dama. Ki bar wannan gidan rediyo mai ɗan ƙaramin tasiri, ki zo CashTalk FM tashar da zata fi Rayuwa FM nesa da gani.”
Amal ta saki murmushi cikin nutsuwa ta ce:
“Dama tana iya zama mai kyau, amma ba kowacce dama ce ta dace da kowane mutum ba. Rayuwa FM ba ta ciyar da ni kuɗi amma ta ciyar da ni gaskiya da ƙaunar talakawa.”
Maleekh ya ce:
“Kina nufin ba kya son ƙaruwa? Kina son ki zauna da ƴan talakawa har abada? Kina gudun cika mafarkin ki ne? ko kina jin tsoron canji?”
Amal ta ce:
“Ina son ƙaruwa. Amma ba zan sayar da zuciyata ba saboda hakan. Na fi son in bar tarihi da murya mai amfani fiye da na bar makudan kuɗaɗe da aka samu ta hanyar wulaƙanci.”
Maleekh ya daka tsaki, yana ƙare ta da kallo Ya ce:
“You talk too much for someone who is replaceable. Don’t forget, I can build a station, create a voice louder than yours, and bury your name in days.”
Amal ta gyara zama, ta ɗaga kai cikin murya mai sassauci ta ce:
“To bury someone’s name, dole ne ka goge, yadda sunan tasa wasu suka tashi domin binne ta. Kuma Maleekh murya ba ta girma da speakers, son samu ta girma da gaskiya.”...
Shiru ne ya ratsa ofishin. Maleekh ya kasa ce wa komai. Ya kalle ta da wani irin kallon ƙiyayya da mamaki....
Maleekh a hankali ya furta
“Hmm... interesting.”
Ya juya ya fita ba tare da sallama ba. Amal ta lumshe ido, ta ce a ranta...
“Da wuya babban mutum ya yarda da ƙaramin murya, sai dai idan muryar tana da gaskiya.”.....
Yayin da Maleekh ya shigo ofishinta a Rayuwa FM, Amal ta riga ta kunna ƙaramar mic recorder da ke haɗe da tsarin studio ɗin su. Ba mic ɗin da ake gani ba ne, amma yana da ƙarfin ɗaukar duk wata magana da ta faru a cikin ɗakin.
A zuciyar Amal tana faɗin:
"Zan bar duniya ta saurara da idanuwanta. Zasu ga wanda suke ƙira ‘jagoran zamani’ da ainihin halayensa."
📻 'ON AIR' BA SANI BA SABO!!!!
Tattaunawarsu da suka cika da wulakanci, kaskanci da rainin hankali daga ɓangaren Maleekh ta cigaba kamar yadda muka tsara a baya. Amma wannan karon duk maganganun suna tafiya kai tsaye zuwa wani system na backup audio a cikin ofishin Amal, kuma daga baya wani technician ya yanke hukuncin ya ɗora su a shafin YouTube da X (Twitter).
Bayan awa guda Maleekh ya bar FM, recording sautin yanda ya ƙasƙantar da Amal ya bazu kamar gobara! Mutane sun fara posting da hotunan fuskarsa da sautuka na yanda yake cewa:
“Ke ƴar talakawa ce kawai... ki gode da na zo…”
“I can bury your name in days!”
👇
(Zan binne sunan ki cikin ƴan kwanaki...)
“CashTalk FM za ta maye gurbin wannan ƙaramar tashar ku...”
🔥 Comments a social media suka fara tashi kamar haka:
@ArewaRight: “Shin wannan ne shugaban da zai kafa sabon gidan rediyo? Me ya sa yake wulakanta mace mai gaskiya?”
@NaijaWoke: “Yadda Amal ta ba shi amsa cikin nutsuwa ya nishadantar...
Maleekh ya ci karo da ƙaramar mace mai girman zuciya.”
@TalakawanVoice: “Idan yana da gaskiya, me ya sa yazo da barazana da cin mutunci? Kuɗi ba su da daraja idan babu mutunci.”
Haka maganganu suka rinƙa yaɗuwa ....
MALEEK CASHBANK NA FUSKANTAR RIKICI
A daren nan, PR team ɗinsa a London da England da Abuja sun shiga tashin hankali. Yana kallo a gida, yana shan coffee, sai ya ga trending topic:
#WhoIsMaleekCashbank
#IStandWithAmal
#TalakawaMukaNe
Ya finciki remote ya buɗe rikodin yana sauraro da ido wujiga-wujiga...
Maleekh cikin zafin rai
Ya ce:
"Taya wannan sirrin ya fito fili?!"..
Ya jefa kofin coffee ƙasa da karfi. Kunnensa yana ƙara kamar sauro. yana faɗin:
“She played me... she outsmarted me!”
(Ta yaudare ni… ta fi ni wayo!").
Washegari, kafafen yaɗa labarai sun fara ɗaukar labarin. Wasu suna gaya wa Amal "kin farka mana idanunmu", wasu kuwa suna tambayar:
"Shin Maleekh da yake shirin kafa rediyo, haka zai kula da ma’aikatansa?"
Rayuwa FM ta samu karɓuwa sosai. Amal ta koma bakin aikinta kamar ba abun da ya faru, amma ƙarfin ta ya ninka nasa sau ɗari.
A labarai ana sanar da labarin MALEEKH...
Maleekh Cashbank ɗaya daga cikin attajirai mafiya ƙarfi a Najeriya, ɗan asalin Kaduna ne, amma mahaifinsa babban ɗan siyasa ne mai tarin dukiya wanda ke zaune a Abuja. Shi kuma Maleekh ya kwashe rayuwarsa a ƙasar Ingila yana gudanar da wasu kasuwanci kafin ya dawo don kula da sabon tashar rediyon sa CashTalk FM da ke Abuja.
Maleekh ba ƙaramin fusata ya yi ba, ya yanke hukuncin komawa tashar rediyo inda Amal take aiki...
A cikin motar sa mai tsada, yana sanye da farin suit, baƙin glass, da ƙamshi mai ƙayatarwa. Yana tunanin tashar rediyo Rayuwa FM da ke Kaduna inda Amal ke aiki...
Bayan isar sa ko tsayawa bai yi anyi mata sallama cewa ya zo ba, kai tsaye ya kutsa ciki...
Da ƙarfi ya buɗe ƙofar office ɗin ta har sai da ta tsorata, tsaya wa ya yi yana kallon ta cikin takaici...
Itama miƙe wa tayi tsaye ganin Maleekh...
Yana da niyyar tattaunawa da ita a fili, amma ba tare da sanin cewa Amal ta ƙara kunna mic ba domin duk abinda zai faɗa ya isa kunnuwan al’umma kai tsaye.
Maleekh yana kallon Amal daga sama zuwa ƙasa
Ya ce:
“To me kike tunani da har kike yawo kina faɗin magana kamar ke ce mai kula da rayuwar al’umma? Me kika sani game da siyasa da iko? Kin taɓa ganin naira miliyan ɗaya da idon ki kuwa?”
Maleekh tsabar kansa ya ɗau zafi bai san wani magana yake yi akai ba, haka zuciyar sa take harbawa tana bugawa da ƙarfin gaske...
Amal ta ƙyalkyale da dariya cikin kwanciyar hankali ta ce:
“A'a, ban taɓa gani ba. Amma na taɓa jin yunwa, na taɓa zama da kakata da safe ba tare da mun ci abincin rana ba. Na kuma san cewa duk wanda bai ji zafin talauci ba, bazai iya jin raɗaɗin talaka ba.”
Maleekh yana girgiza kai ya ce:
“That’s why you’ll always be poor. Ke da kika yi tashin baƙin ciki, me zai canza? Wannan shine dalilin da yasa CashTalk FM zai ɗauki ragamar rediyo a Nigeria. Ku dai Rayuwa FM sai ku ci gaba da sauraron kan ku ...”
Amal cikin nutsuwa, ba tare da ɗaga murya ba ta ce:
“Mu dai ba mu da ruwa da kuɗin ku. Amma muna da murya. Muryar da zata faɗi gaskiya koman zafi. Kuma wallahi, idan muryar talaka ba zata kai ga wayar da kai ba, me zata yi?”
A lokacin jama’a da dama sun fara bibiyar shirin a wayoyinsu da rediyoyi. Sun fara rubuce-rubuce a social media:
"Shin wannan Maleekh Cashbank mai yake nema ne?"
"Wai da gaske yana ƙasƙantar da 'yan Najeriya haka?"
"Amal tana da gaskiya! Muryarta tana buɗe mana ido."
Maleekh a hankali, ya fara lura da cewa tattaunawarsu ta na fita kai tsaye. Ba shakka wannan sauyi ne da zai fara tayar masa da hankali a fagen da ya raina muryar talakawa.....
NEXT NEXT NEXTT
*MASU KARATU BANA GANIN ZAFAFAN COMMENT ƊIN KU, IN BAKWA TSOMA BAKI CIKIN RIKICIN AMAL DA MALEEKH TAYA ZAN SAN CEWA CAKWAKIYAR NA TAFIYA YANDA AKA TSARA ? PLEASE A DAGE DA COMMENT, SANNAN INASON GANIN YAWAN ÝAN TEAM ƊIN AMAL DA MALEEKH....*
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE. page 9 to 10
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Maleekh na tsaye gaban Amal, yana ƙoƙarin tursasa nata ra'ayi da tsoran kuɗi, amma ba tare da sanin cewa mic na kunne ba. Amal kuwa a zuciyarta akwai kuzari da jarumtar da ba a iya siye da kuɗi.
Amal.ta miƙe cikin nutsuwa, idonta cikin na Maleekh
Ta ce:
"Ba na buƙatar kuɗin da zai sa inyi shiru akan gaskiya. Ka duba mu a matsayin ƴan ƙasa, sannan ka duba kanku a matsayin sama da dokar ƙasa. To ka sani Allah yana sama da dukanmu, kuma kowanne ran mutum yana ƙidaye."
Maleekh ya saki dariyar yaƙe tare da faɗin:
"Wai ke da wannan muryar za ki canza duniya? Ke da babu ko rigar kwana guda mai kyau a jikin ki?... Ki tsaya lafiya Amal, domin wannan duniya ba ta talaka ba ce."
Amal ta juyo tana kallon mic da wayar laptop ɗin dake kusa ta ce:
"To ka tambayi duniya, daga yau... wacece Amal? Kuma wane ne Maleekh?"
Kafin Maleekh ya farga, ɗaya daga cikin ma’aikatan Rayuwa FM ya shigo da hanzari yana nuna masa wani bidiyo dake yawo a internet, duk maganganun Maleekh da zagin da yayi sun riga sun bazu....
Ma’aikacin ya ce:
"Sir, the whole of Nigeria is listening. Hashtag
‘#AmalTheVoice’ is trending number one.
Your brandCashTalk FM is under fire."
Maleekh ya tsaya cak! Yana kallon bidiyon kansa da Amal, yana jin yanda jama’a ke commenting:
"Wannan ba magana bace daga mai hankali."
"Maleekh ya nuna mana irin tsanar da attajirai ke yi wa talaka."
"Ina tare da Amal. Muryarta tana wakiltar miliyoyin da ke cikin shiru."
Cikin daƙilalliyar zuciya Maleekh ya haɗe tafin hannunsa yana kallon Amal wacce ta zamo wata alama ta ƙarfi da jarumta ba tare da ta buƙaci ƙarfi ko asali ba.
Amal ta ce cikin ƙasa da murya...
"Mu da kuke gani ba komai bane. Amma idan aka buɗe mana hanya, zamu ɗauki makamai da basira ba bindiga ba, sai ilimi."...
Maleekh cikin ƙosawa da fushi yana furta a hankali
"This is not over. You will regret this."
Amal ta kalle shi kai tsaye cikin idanu sannan ta ce:
"To ka dawo lokacin da za ka zama ɗan adam kafin ka zama ɗan siyasa ko ɗan kasuwa."
A lokacin da labarin ganawar Maleekh da Amal ya karaɗe gari a karo na biyu, mutane da dama sun fara jin juyayi da mamaki bisa irin rashin mutuncin da Maleekh ya nuna a cikin gidan rediyo. Sai dai shi bai sani ba cewa Amal ta kunna mic ɗin rediyo a ɓoye kafin ya fara magana. Kowane harshensa da ra'ayinsa na ƙasƙantar da 'yan talakawa da ɗaga kai kan kuɗinsa da sunan mahaifinsa da siyasa ya bayyana fili ga jama’a.
Jama’a sun ɗauki zafi
Mutane sun fara tambaya da zargin cewa
"Shin wannan shi ne wanda ake cewa matashin shugaba a Abuja?"
"Wai irin wannan mutunci ne zai kawo mana cigaba?"
"Ƴar talakawa bata da wani ƙarfi sai muryarta da gaskiyar ta, meyasa za’a ci mutuncinta haka kawai?"
Comments sun cika social media suna goyon bayan Amal, suna yabon hikimarta da ladabinta, duk da ƙasƙanci da cin mutuncin da Maleekh ya jefo mata.
A Bangaren Maleekh kuma...
Bayan ya bar gidan rediyo, ya fara samun rahotanni daga PR ɗinsa cewa abubuwan da ya faɗa an ji su a watsa shirye-shiryen gari, kuma hakan yana janyo rashin kyau ga kamfaninsa CashTalk FM. Amma Maleekh cikin jin isa ya kalle su ya ce:
"Ko gwamnati ba za ta iya tambayata ba. Kun san dalili? Saboda sun san wanene mahaifina. Idan tana tunanin zata iya kunyata ni da Muryar ta, zan nuna mata yadda iko ke aiki a Najeriya."....
Kai tsaye Abuja ya wuce...
Bayan isar sa cikin ɓacin rai ya zauna a cikin babban falonsa dake Abuja, yana kallo a kan plasma TV, yayin da Amal ke ci gaba da samun goyon bayan jama’a. Sai ya furta:
“Na ce miki I’ll crush you. No one messes with Maleekh Cashbank and walks free.”
Ƙarfin iko da mulkin kuɗi
Gwamnati da hukumomi basu iya tsoma baki ba, domin kowa ya san ƙarfin Maleekh da iyayensa. Ana kallon Amal tamkar ƙaramar yarinya marar mafita. Har wasu 'yan siyasa na Abuja suna cewa:
“Yarinyar nan bata san abinda take yi ba. Tana wasa da wuta. Tana jawo hankalin wasu da bazasu iya kareta ba.”
Amma Amal, duk da tsoron da ke kewaye da ita, ba ta ja da baya ba. Ta ƙudiri niyyar za ta tsaya da gaskiya, har sai an ji murya ɗaya da ke goyon bayan talakawa...
A cikin babban ofishin CashTalk FM dake tsakiyar Abuja, Maleekh ya kalli PA ɗinsa, Idris, da kallo mai cike da ƙorafi. Fuskar Maleekh na nuna gajiya da damuwa, amma har yanzu girman kai yana kansa, yana zaune a babban kujera da kafarsa ɗaya bisa ɗayan, yana motsa kofin coffee a hannunsa.
PA Idris sai da ya daidaita nutsuwar sa sannan ya ce:
"Mun gwada amfani da ƙarfi amma ya dawo mana da illa. Yanzu mutane suna tausaya wa Amal. Kafafen yaɗa labarai suna juya komai. Amma ina da wata sabuwar dabara..."....
Maleek ya ɗago kai da ɗan murɗaɗɗen fuska ya ce:
“I’m listening.”
PA ya ce:
"Mu sauya salon mu. Ba tare da barazana ba, sai da tausasawa. Za mu yi mata tayin da ba za ta iya ƙin karɓa ba. Misali… naira biliyan ɗari. Za mu gana da ita a wani villa mai zaman kansa, ba a gidan rediyo ba, ba a idon jama’a ba. Za mu sayi muryarta, mu sayi hotonta. Za mu mai da ita fuskar sabuwar CashTalk FM, tare da Rikky Blaze da ƙawayenmu na ƙetare. Sir, da zarar ta koma gefenmu, jama’a za su yi shiru."
Maleekh ya ɗan juya bakin sa, yana lumshe ido. Ya yi shiru na ƴan dakiku kafin ya ce:
“You think she’ll accept the money?”
Idris ya ɗan murmusa tare da faɗin
"Kowane rai yana da farashi, Sir. Ita ma dai tana kwaɓe ne kawai. Da zarar ta ga yawan kuɗin, za ta manta da duk wannan gwagwarmayar da take yi."...
Maleekh ya ɗan kaɗa kai yana murmushi da raɗa a zuciyarsa yana faɗin
“Idan ta karɓa, zata zama tamkar ɗan yatsa a hannuna. And if she refuses... then she’ll see the true meaning of regret.”
Bangaren Amal
A gida Amal na zaune cikin natsuwa, tana rubuta sabon rubutu na shirin rediyo da zai kawo sauyi. Fuskar ta cike damuwa, amma zuciyarta na cike da ƙarfi. Tana jin wata zuciya tana gaya mata kada ki ja da baya.
Sai kuwa ta samu saƙon gaggawa a wayarta daga wani lamba marar suna:
“We want to offer you a new life. One conversation, one hundred billion naira. No cameras, no mics. Private location. Just you and the future you deserve.”
Amal ta kalli saƙon, sannan ta ce cikin zuciyarta:
“Wannan shine yunƙurin da ke nuna irin su Maleekh sun fara jin tsoron gaskiya. Amma ni ba zan sayar da murya ta ba.”
An shirya komai. Wani babban villa da ke gefen Asokoro, cikin duhun dare, aka kai Amal. Gidajen tsaro a kofar villa sun tabbatar da ba wani na waje da zai iya shigowa. Amal ta iso ne bisa ƙa’ida ba tare da mic ko recording ba, ta zaɓi ta fuskanci wannan ƙalubale kai tsaye, cike da jarumta.
Ta shiga cikin babban falon da aka ƙawatar da fitilun da suke ɗaukan hankali. A gaban wata babban glass table ne Maleekh ke zaune, rik’e da cup na red wine, Rikky Blaze yana gefensa, sai wasu turawa biyu daga kamfanin Wave Broadcast International.
Maleekh ya yi murmushi mai cike da zafi da mugunta, sannan ya ce:
“Miss Amal... welcome. Please sit down.
Wannan ba barazana ba ne, kyauta ce. Kina da murya mai haske… da zuciya mai ƙin jin magana...."
Amal ta zauna cikin nutsuwa, har yanzu zuciyarta tana da matuƙar ƙarfi. Ta ce da muryarta mai nutsuwa:
"Faɗi abin da kake da niyyar faɗa. Na zo nan ne domin gaskiya, ba domin jin daɗi ba."
Maleekh ya lumshe ido, ya ɗauki wani babban envelope, ya saka a gabanta yana faɗin:
"A cikin wannan akwai takardar check naira biliyan ɗari. Za ki bar wannan Rayuwa FM mai fama da ƙalubale… ki koma CashTalk FM. Muryarki za ta karaɗe duk faɗin Afirka. Ba za ki yi aiki ƙarƙashin kowa ba sai ni. Abin da muke nema kawai shi ne: ki daina sukar gwamnati da 'yan siyasa. Ki mayar da hankalinki kan nishaɗi. Babu sauran ‘gaskiya kuma’."
Turawan suka ce:
“You’ll also represent us globally. Ambassador of media. All travel expenses covered. No more poverty.”
(Za ki wakilce mu a matakin duniya. Jakadiyar kafafen yaɗa labarai. Za mu ɗauki duk kuɗin tafiya da alƙaluma. Ba za ki ƙara sanin talauci ba.")
Amal ta kalle su duka. Ta daɗe tana kallon Maleekh cikin idonta. itama cikin nutsuwa ta ce
"Bari in fayyace maka abu guda… Muryata baza ta taɓa zama abin sayarwa ba. Ba za a iya sayen raina ba. Ina magana ne domin waɗanda ba su da murya kuma shi ya sa kuke tsorata da ni. Ni ba matalauciya bace, ni mai arziki ce da ƙarfin hali, da manufa mai ƙarfi. Kuma idan kana tunanin zan bar jama’ata saboda check… to, ba ka san komai game da ni ba....
Kana tunanin kai ne kake da Najeriya. Amma ƙarfin gaskiya Shi ne ƙarfin da ya fi komai. Kuma ba za ku iya kashe shi ba, ba da bindiga ba, ba da biliyoyi ba, ba da PA mai surutu ko turawa masu jajayen kunnuwa ba..."
Rikky Blaze ya tintsire da dariya, amma Maleekh ya ƙafe ta da ido. Wannan karon, zuciyarsa ta girgiza.
Ya ce da ita:
"To ki shirya. Kin ƙirƙiri abokan gaba da ba sa mantuwa."
Amal ta tashi tsaye. Ta ce:
"Ban taɓa roƙon a kare ni ba, abin da na roƙa kawai shi ne in kasance a kan gaskiya. Kuma zan ci gaba da magana… ko da mutanen cikin duniya sun zamo kurmaye."...
Ta juya ta bar su da mamaki. Kowa ya yi shiru a falon, turawan sun yi shiru, Rikky ya daina dariya, Maleekh ya kame bakin sa kamar wanda ya rasa hanyar tunani.
Washegari da safe.
Kafin kowa ya iso ofis, Amal ta riga ta buɗe mic ɗinta a Rayuwa FM. Bata faɗa wa kowa abinda ya faru da ita ba, Tana zaune a cikin studio, kafafunta a ƙasa, hannunta riƙe da mic, idonta a lumshe. Muryarta mai sanyi da natsuwa ta cika dukkanin filin.
AMAL:
“Assalamu Alaikum 'yan uwa. Ina so ku saurare ni da buɗaɗɗiyar zuciya. Ina magana da ku ba a matsayin mai gabatar da shirye-shirye ba, ina magana ne a matsayin 'yar Najeriya, mace, 'yar talaka, wacce ba ta da komai face gaskiya.”
Ta lumshe ido kafin ta cigaba, tana fuskantar mic kamar dai duniya tana kallonta kai tsaye.
“A daren jiya na zauna da wani babban ɗan kasuwa, mai girman kai, wanda ya ɗauki duniya da faɗi, kuma zai iya sayen mutunci kamar cin abinci a restaurant. Ya bani kuɗi, ya mun alƙawaruka, ya gaya min zan iya canza rayuwa ta da kuɗi. Amma amsar da na bashi shine "A'a.”
Domin rayuwa bata tsaya akan dukiya ba, sai dai akan amana da gaskiya. Na gaya masa: Ni ba zan iya haɗa baki da ƙeta ba. Ba zan iya cin abincin da na san yana zubar da jinin mutane ba. Ba zan yi aiki da waɗanda suka mayar da talaka kamar ƙwari ba.”
Ta ɗan dakata tana sauƙe numfashi, daga baya ta ci gaba da cewa
"Kafin su akwai waɗanda Suka ce zan iya mutuwa idan ban haɗa baki da su ba. Amma na ce musu: Wanda ya tsani gaskiya, to ya shirya zaman damuwa. Domin gaskiya, ko da an kashe ta, to zata bar ƙura a zuciyar duniya har abada."
Ta ƙara yin shiru na daƙiƙu, kafin ta ci gaba da magana
"An bani kuɗi. An bani iko. An bani suna. Amma suna da iko ba shine gaskiya ba. Na ga mutanen da suka zauna a kujerun gwamnati suna dariya akan hawayen talaka. Na ji kalmomin da suka ce min, kamar ni ƙura ce da za’a shafe da ƙafa. Kuma zan sake ce musu: NI BA NA SAYAR DA RAI DA RA'AYI NA.....
"Sun ce zasu bani biliyoyi, amma a cikin bil’adama, me kake da shi idan ka rasa gaskiya?"
Ta lumshe ido tana jiyo sautin numfashinta da sautin zuciyar ta.
"Ina magana da duk matasa maza da mata. Kada ku bari a saye ku. Kada ku bar wanda yake da kuɗi yayi muku shiru da kuɗi. Idan munyi shiru yau, gobe su ne za su zagi ƙwaƙwalwarmu."
"I met the kind of men that run Nigeria and they are scared of only one thing: THE TRUTH. So let's give it to them. Not with violence… but with courage."
A waje, mutane sun fara taruwa a kofar Rayuwa FM. Wasu suna jin kukan Amal a cikin radio, wasu suna kallon live stream ɗinta.
AMAL ta cigaba da cewa:
"Inna, idan kina jina yanzu, ki sani... jikar ki ba zata tsaya ba. Kuma ba zata ji tsoro ba. Zuciyarki tana cikin zuciyata. Kuma koda wata rana su yi nasara da jikina... maganata zata rayu a kunnuwan mutane!"
Muryarta ne ta karye da kuka amma bata daina magana ba:
Sai ta cigaba da magana da harshen Turanci domin duka Nigeria da duniya su fahimta:
"They wanted to silence me with wealth. They offered me power, fame, billions... But I looked them in the eyes and said, I am not for sale."
"Sun so su rufe mun baki da dukiya. Sun miƙa mun iko, suna, da biliyoyi... Amma na kalle su cikin idanu na ce: Ba na sayuwa."
Ga dukkan matasa a waje, iyaye maza da mata masu fama, samarin titi, da ’yan mata, ina tsaye a nan saboda ku. Ba domin ina da ƙarfi ba, sai dai domin na san gaskiya ta fi harsashi ƙarfi, ta fi kuɗin jini tsabta."
"Ga waɗanda suka sace ni... na yafe muku. Amma ku sani: idan na mutu yau, miliyoyi za su tashi. Domin wannan murya ba tawa ce kaɗai ba, tamu ce."
"Kuma ga waɗanda suka sace ni... na ga fuskokinku. Yanzu kuwa, duniya na ganin tawa. Kun ji tsoro ba saboda kalmomina ba, saboda waɗanda ke sauraro na..."
Ta dafe mic, tana kallon glass ɗin gaban ta, tana fadin:
"This is not just about Amal. This is about every girl that has been told she's too small to speak, too poor to matter, too weak to fight. I speak for them now. And I will never stop."
Ta gama jawabi tana hawaye,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 62