Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
su a kan rauninsa da rigansa da ya yage. ​Maleekh ya fito da kansa gabaɗaya daga dajin, ya fara tafiya zuwa bakin ruwa da ya bari, yana jan ƙafarsa da take ciwo. Burinsa shine ya tarar da wata hanyar da zai iya ƙetare ruwan. Ya san cewa idan har Amal ta tsira, dole ne ya yi haka... A wannan ranar a bakin ruwa ya kwana.. Yana shan iska da sanyin wurin.. Asubar fari duk da bai san lokacin sallah ba a wurin haka ya yi alwala da ruwan sannan ya tsaida sallah. Yana cikin sallah sai ga wasu daga cikin mutanen sun afko masa. Yana jin yanda suke ta ihu suna ɗaga makamansu sama amma haka ya ci gaba da sallah. Wasu ne suka fara kwaɗa masa sanda a baya ga raunin kibiya. Haka yake daure wa sai da ya kammala sallarsa yayi sallama sannan ya ɗaga hannu sama yana addu'a.. Wani ne ya kwaɗa masa a tsakiyar kai sai a lokacin ne ya riƙe kansa tare da sakin ihu... Wani irin ƙarfi ne ya ziyarce shi a take ya riƙe ya riƙe hannun wani daga ciki wanda ya kawo masa sara da adda. Wani irin zulluya yayi ya miƙe ya murɗe addar, cikin fusata yake kai musu sara da addar.. ​Maleekh, duk da raunukan da ya ke fama da su amma jarumtarsa ta ƙaru. Kuma haka ya ci gaba da sararsu, har sai da ya kashe su duk yawansu. ​Bayan ya gama da su, ya fara jin ihun wasu mutane da suke tahowa da gudu, kuma suna da yawa. Maleekh ya jefar da addar, jini na zuba daga raunukan da ya ji. Yana jin ihun sababbin mafarauta suna tahowa. Ya san cewa duk da nasarar da ya samu a kan waɗannan mutanen, ba zai iya sake fuskantar taron mutane ba tare da ya mutu ba. Dafin kibiyar da kuma raunin faɗa sun yi masa nauyi.. ​Ya tattara ragowar ƙarfin da ya rage, ya juya, ya fara gudu cikin zurfin daji inda duhu ya mamaye ko'ina, duk da yanzu ba dare bane. ​ Maleekh yana gudu ne da ƙafa ɗaya mai rauni, raunukan da ya ji a faɗan suna ci gaba da buɗewa, yana zubar da jini a kowane mataki. ​Ya yi ta tuntuɓe a kan kwalabai da sassanyan bishiyoyi, duk yana roƙon Allah ya ba shi ƙarfin da zai ci gaba. Amma ganinsa ya fara rufe wa. ​ Ya tsallake wani rami mai zurfi da duhu. Bai gane ba, saboda duhun ya yi masa katanga. ​Ya faɗa cikin ramin da ƙarfi mai ban tsoro. amma sa'ar ta juya lokacin da kansa ya bugu da wani ƙaton dutse mai kaifi. A take, ya sume a cikin ramin... Mutanen dajin sun isa wurin faɗan. Sun ga gawarwakin 'yan'uwansu a warwatse. Fushin su ya ƙaru. ​“Ya kashe su! Wannan yaron ba mutum ba ne! Ruhu ne na daji!” wani ya yi ihu cikin mamaki da tsoro. ​Suka bi sawun jinin Maleekh. Suna ta ihu, suna ta nemansa, amma duhun ya ba shi kariya. ​Sun zo bakin ramin, amma rami ne mai zurfi da duhu ya rufe shi. Jininsa ya tsaya a bakin ramin, amma ba su ga faɗuwar tasa ba. ​“Babu shi! Ya gudu! Ko kuma duniya ta haɗiye shi! Ku cigaba da nema! Ba za mu koma ba tare da shi ba!” Sun ci gaba da nemansa har tsawon dare, ganin basu same shi ba yasa suka koma yanda suke da safe ba tare da nasara ba. Doka ta ce dole ne a rama mutuwar 'yan'uwansu, kuma sun sanya farashin duk wanda ya nemo Maleekh.... ​Ita kuwa Amal bayan ta tsallake ruwa, tana tafiya a can gefen ruwa, ta fara jin wani irin hajijiya saboda ƙaton ruwan tekun da ta shiga. Anan ta faɗi itama ta suma. ​Sai da ta kwana a wurin. Da sassafe, wasu matasa Fulani suka tsince ta. Mutanen Fulani ne, da matansu da yara. Suka kaita wata ruga. Anan aka fara mata jinya. Amal ta farka daga sumewar wahala da hargitsin jiki da ta samu sakamakon tafiya mai tsawo a ruwa. Ta fara jin ƙamshin madara da hayaƙi. ​Tana buɗe idanunta, ta ga wata mata Fulani tana sanye da kayan fillo farare, tana gauraya wani abu a cikin ƙaramin tukunya.. ​“Sannu da zuwa, 'yar gida,” matar ta furta “Mun same ki a bakin ruwa. Jikinki duk ya yi sanyi.” ​Amal ta yi ƙoƙarin tashi, amma rauninta da hajijiyar da ta shiga sun hana ta. Ta ji kamar ta shiga wata sabuwar duniya. ​Matan Fulani sun yi mata jinya ta gargajiya. Sun yi amfani da ganyen magani da man shanu don shafa mata a jiki. Sun ba ta madara mai zafi da nono don dawo da ƙarfinta. ​A rugarsu akwai zaman lafiya da tsafi. ​Amal ta kwashe kwanaki tana murmurewa. Ta ƙudurce cewa ba za ta faɗa musu cikakken labarinta ba tukuna, don tsoron kada su gane ta kuma su mayar da ita. Ta dai faɗi musu cewa ta rasa iyayenta ne a cikin ruwa. Amal ta koyi zaman gida da kuma yadda Fulani suke mu’amala. ​A cikin zuciyarta, Maleekh shine burinta.. Tunaninta kullum akan Maleekh. 《》《》《》《》《》《》 Tashin hankalin a ya mamaye Abuja. Mutane ba su san inda Amal da Maleekh suka shiga ba tun bayan sace Amal da Maleekh ya yi ta hanyar Superbike a wurin walimar aure.. ​Inna ta shiga cikin tsananin tashin hankali da baƙin ciki. Tana zaune a cikin falonta mai tsada, amma babu wani abu da yake da daraja a idonta face Amal. ​Inna tana kuka tana faɗin “Na rasa Ɗana (mahaifin Amal), yanzu kuma ga Amal ta shiga cikin haɗari! Ina Maleekh ya kaita? Me yasa zai raba ta da mutuncinta har haka?” ​Abbah shima ya shiga gigicewa. Yana jin laifin rashin kulawa, da kuma laifin ɗansa da ya kawo masa ci da baƙin ciki a idon abokinsa (mahaifin Amal) da ya mutu. Abbah ya yi amfani da dukkan hanyoyin jami'an tsaro da kuɗi da yake da su don neman yaran. Ya san cewa idan ba a gansu ba, za a iya zargin Maleekh da sace mutum (kidnapping), duk da cewa an san suna soyayya. ​‘Yan sanda sun fara bincike a duk manyan hanyoyin fita daga Abuja, suna neman motosar Superbike ɗin Maleekh.. ​Hotunansu sun bazama a shafukan sada zumunta da kuma gidajen rediyo, amma babu wani shaida mai ƙarfi da aka samu. Zayd kuwa daman yasan aurensa da Amal ba mai yu wa bane kawai ya amince ne... Domin yasan Maleekh bazai taɓa bari ba.. ​Babban Sufeto mai kula da case ɗin neman yaran, wanda ke da hankali da gogewa, ya gano wasu bayanai masu mahimmanci: ​ Binciken Sufeto ya sanar cewa “Wannan ba sace mutum ba ne na tashin hankali. Wannan guduwa ce ta masoya. Amma gudunsu ya yi nisa sosai har muka rasa sawun su. Ga alama, sun shiga wani wuri ne da ba shi da hanyoyin sadarwa.” ​Ya gano cewa Abbah ya riga ya ajiye wasu tsare-tsare na gano su, ta hanyar satellites da kuma wasu ƙwararrun masu binciken sirri. Ana zargin cewa sun shiga yankin daji ne saboda Motosar Superbike ba za ta iya tafiya nesa a kan hanya ba tare da shan mai ba. ​Bayan kwanaki da yawa na bincike mai tsanani, wata ƙwararriya a fannin fasahar sadarwa ta gano wata yar ƙaramar siginar waya da ta fito daga wani wurin da ba a sani ba a wani wuri mai nisa da Abuja, kusa da wani babban dajin da aka sani da haɗari. ​Sifeto ya fahimci cewa wannan siginar na iya zama wayar Amal ko ta Maleekh, ko kuma wani tsarin sadarwa da suka yi amfani da shi kafin a gano su. ​Ya ƙira Abbah ya sanar da shi cewa, “Muna da wani wuri. Ga alama sun shiga cikin wani babban daji mai haɗari. Dole mu tura ƙwararrun mutane su shiga nan da nan.” Duk da irin bincike mai tsanani da jami’an tsaro da masu neman sirri na Abbah suka yi, binciken ya kasance a banza. An shiga dukkan kwa-kwa da rassa na dajin, amma babu wanda ya ga ko wani alamar Amal ko Maleekh. ​Hakan ya faru ne saboda basu da wata wayar hannu da za a iya bin sawunta (tracking), Maleekh kuma yana kwance sumamme a cikin rami mai duhu, ita kuma Amal tana cikin ruga mai nisa inda hatta mutanen rugar gaba ɗaya basu da wayoyin sadarwa.. 《》《》《》《》《》《》《》《》 ​Bayan tsawon watanni shida na neman da aka yi ba dare ba rana, an haƙura da neman. An ba da sanarwar cewa watakila yaran sun shiga tekun haɗari ko kuma sun rasa rayukansu a cikin daji. Inna ta fita daga hayyacinta, shima Abbah ya shiga cikin baƙin ciki da nadama mai tsanani. Ga an rufe shari’ar... ​Amal ta samu kulawa ta musamman a cikin Rugar Fulani. Ta yi amfani da nutsuwar wurin da magungunan gargajiya don warkewa daga wahalar da ta sha a dajin. ​Bayan tsawon watanni, Amal ta fahimci cewa ikon Allah ya ɗaura mata juna biyu a cikin ɗan kankanin lokacin da suka yi tare da Maleekh a wurin mafarauta. Sun sadu da juna har kwana biyu, a rana ta uku ne suka gudu. A yanzu, tana ɗauke da ciki na tsawon watanni shida. ​Wannan ciki ya zama shaidar soyayyarsu da kuma sadaukarwarsu a ƙarƙashin barazanar rayuwa. ​Amal ta tattara ƙarfin hali ta gaya wa Fulani gaskiyar labarinta daga soyayyarta da Maleekh, zuwa ga sace ta, zuwa ga auren da aka ɗaura musu a daji, har zuwa ga gudun tsira. ​Mutanen Fulani, da yake mutane ne masu tausayi da mutunta rayuwa, sun karɓe ta da hannu biyu. Sun ɗauke ta a matsayin ɗiyarsu ta gaskiya kuma suka yi alkawarin kare ta har sai ta haihu. Cikinta ya zama alamar bege a cikin wannan ruga mai nisa... Duk da a yanzu mutanen rugar basu zauna ba, suna nema mata hanyar da zata bi don ta koma gida.. ​Shi kuwa Maleekh, bayan tsawon wata ɗaya a kwance a cikin ramin da ya faɗa, wasu Sojoji sun tsince shi. Sojojin sun shigo yankin ne domin gudanar da aiki na yaƙi (military operation), kuma sun same shi cikin jini, sumamme a cikin rami mai zurfi. ​Sojojin sun ɗauke shi, sun fara bashi kulawa ta musamman (medical treatment) a sansanin su na ɗan lokaci. ​Bayan wata ɗaya da ya yi a hannun su, ya farfaɗo. Sai dai mamaki da firgici suka lulluɓe Sojojin. ​Maleekh bai san inda yake ba. Ba ya gane fuskarsa ko hannuwansa. Saboda tsananin buguwar da ya yi a kansa lokacin da ya faɗi a cikin rami ya bugu da dutse, kwakwalwarsa ta juye. Ya shiga cikin cikakken mantuwa (Amnesia). ​ Bai san sunansa ba. Ya manta da wata Amal. Sannan a yanzu ya manta da Mahaifinsa. Bai san yadda ya fito daga cikin wayewar gari ba. ​Sojoji sun riƙe shi, suna bashi kulawa sosai har tsawon watanni shida suna jiran farfaɗowar ƙwaƙwalwarsa. Amma shiru. Babu wanda ya sanshi a wurin, kuma Maleekh bai iya bayar da ko wani bayani game da kansa ba. Sun sanya masa wani suna na wucin gadi a cikin sansanin.... _NEXT NEXT NEXT_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 85 to 86 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 ​A cikin ruga, kwatsam, wani matashi ɗan Fulani wanda ya shiga birnin Suleja don kasuwanci ya dawo da wani labari mai zafi. Ya samo wata jarida wadda ke nuna hotunan Amal da Maleekh, kuma ana neman su. ​Labarin ya nuna cewa: Ana neman Amal da Maleekh waɗanda suka ɓata. Akwai kyauta mai tsoka wadda za ta wadata mai ba da labari har karshen rayuwarsa. Haka kuma, an saka lambar waya don tuntuɓa. ​Nan da nan, matashin ya koma rugar da wata ƙaramar waya (torchlight phone). Ya sanar da mutanen rugarsu abin da ke wakana. Duk da cewa watanni shida sun shige, wannan wata dama ce ta zinare don bayyana Amal ga iyayenta. ​Amal ta ji labarin, sai farin ciki da tashin hankali suka shige ta lokaci guda. Ta matsu da ta je ta ga Innanta. Amma sai mutumin ya sanar mata da cewa tsakaninsu da Suleja da kuma Abuja nesa ce sosai. ​Sai dai, basu yi ƙasa a gwiwa ba. Suka ƙira lambar wayar da ke jikin jaridar. Lambar jami'in tsaro ce mai kula da binciken tun farko. Mutumin Fulani ya gaya masa duk abin da ya faru. ​Jami'in ya ƙira Abbah a waya, yana sanar masa cewa: "An samu Amal, a wani yankin ƙauye mai nisa." ​Abbah ya kasance tare da Inna a lokacin. Inna ta yi farin ciki sosai har ta miƙe, tana godiya ga Allah tana kuka. ​A wannan ranar, an tayar da jirgi mai saukar ungulu (Helicopter). Abbah da wasu jami’ai suka shiga cikin jirgin. Sun riga sun yi amfani da fasaha (tracking) don gano wurin da aka ƙira su, saboda haka basu buƙaci wani ƙarin bayani ba. ​Nan da nan, sai ga su a sararin rugar Fulani. Mutanen ruga sun yi mamaki sosai sai ganin Elekwabta sukayi yana shirin saukowa a tsakiyar daji! ​Abbah da Jami'an suka sauƙo. ​Jami'i Yana magana da ƙaramar waya "Mun iso. Muna kan bakin rugarku." ​Matashin Fulani Yana duban jirgin sama da mamaki ya je yanda suke yana faɗin, "Na ganku! Ga ni nan! Ku biyo ni!" ​Anan matashin Fulani ya sanar musu wurinda Amal take. Suka fara tafiya da sauri, sai ga su a gidan Fulani inda Amal take zaune. ​Amal tana zaune a ƙasa, da tsohon ciki, wata mata Fulani tana bata nono don ta sha. ​Abbah muryarsa cike da tausayi, ya kusan fashewa da kuka ganin Amal. “Daughter?… My daughter?” ​Amal ta ɗago da sauri a zabure. Ta kalli mutumin da ya zama uba a gareta. ​Amal cikin kuka, muryarta a raunane ta ce “Abbah!…” ​Ta miƙe da gudu duk da nauyin cikinta, ta nufe shi, ta rungume shi da ƙarfi. Shima Abbah ya kasa riƙe hawayensa, ya fara kuka. Abbah ya rungume ta, yana shafa bayan ta, “Alhamdu Lillah! Ƴata, na gode wa Allah! Na gode wa Allah da ya nuna min ke. Na yi zaton na rasa ki har abada!...” Amal tana kuka ta ce, “Abbah, na shiga wahala! Na yi kewar ku! Na yi kewar Inna! Allah ya ceci rayuwata, Abbah!” Jami'i yana motsa Abbah a hankali ya ce “Ranka ya daɗe, ya kamata mu rage kukan nan. Muna buƙatar mu tafi nan da nan. Tana buƙatar kulawa ta musamman.” Abbah ya saki Amal, yana riƙe da hannunta, ya kalli cikin nata ya ce “Wannan… me ya faru? Wannan… Maleekh ne?” Amal ta sunkuyar da kai cike da kunya ta ce, “Eh, Abbah. Auren da suka ɗaura mana ne a dajin… Amma Abbah, Maleekh ya ceci rayuwata. Bai bar ni ba. Muna son juna.” Abbah ya numfasa da wani dogon numfashi, ya shafa cikinta ya ce, “Allah ya muku albarka, rayuwarku tafi komai muhimmanci … Ba komai, ƴata. Wannan tsari ne na Allah. Yanzu dai mu tafi.” Bayan haɗuwar, Abbah bai manta da kyautatawa da mutuntawa ba. Ya yi wa dukkan mutanen ruga babban alkhairi. An raba musu makudan kuɗaɗe, amma gidan da Amal ta zauna da kuma matashin da ya sanar musu sun fi samun alheri da arziki sosai. An cika musu alkawarin kyauta. ​Ba a jira wani abu ba. Suka ɗauki Amal. ​Amal tana kuka tana yi wa matan Fulani da suka riƙe ta bankwana. Sun shaku sosai, kuma sun yi mata alkawarin addu'a da kuma fatan samun lafiya. ​A lokacin da suka shiga cikin Helicopter, Abbah ya tambayi Amal: “Ina Maleekh? Ba ku tare ne?” ​Amal cikin hawaye ta ce, “Na barshi ne a bakin ruwa… An harbe shi, Abbah, ya yi ta jini. Ya bani tayar na gudu… Ban san yanzu yana ina ba.” ​Ganin cewa babu wanda ya san inda Maleekh yake kuma yana cikin matsanancin haɗari, suka yanke shawarar wucewa gida tare da Amal don a ba ta kulawa ta musamman.. Bayan Jirgin Helikwafta ya sauƙa a Abuja, gidauniyarsu ta cika da mutane. Kowa yana cikin mamaki da tsananin alhini. ​Abu na farko da kowa ya lura da shi shine cikin Amal. Sai dai, abin da ya fi muhimmanci a idon kowa shine tambaya ɗaya: “Ina Maleekh? Yana ina shi?” ​Ammy ta rungumi Amal cike da kewa da tausayi. Amma hankalinta ya tashi, ganin cewa ba a samu Maleekh ba, kuma Amal ta tabbatar da cewa an harbe shi a gaban idonta. ​Nan take, Ammy ta durƙusa, ta fara kuka sosai. Muryarta na fita da ƙarfi, tana nuna tsantsar ciwon zuciya da rashin bege na rasa ɗanta. ​Abbah ya numfasa, cike da damuwa, amma yana ƙoƙarin nuna ƙarfin hali: “Ban ga amfanin ihun ba, Maryam. Tunda har aka samu Amatu shima Maleekh za a same shi. Ku kwantar da hankalinku, ina da yakini.” ​Ƙannen Maleekh, Islam da Arfat, suma haka suke kuka na rashin ɗan uwansu. Gidan ya kasance ba annuri tun watanni shida. ​Inna da Amal suka rungumi juna sosai, suna kuka.. ​Inna cikin kuka take cewa, “Duk laifinki ne, Amatu! Da a lokacin kin amince da Maliku, da hakan bata faru ba! Ya baki haƙuri a lokacin! Da kin amince da an fasa aurenki da wancan, an ɗaura da Maliku, da yanzu kuna zaman farin ciki!” ​Amal tana kuka tana shafa cikinta ta ce, “Inna, kaddararmu ce haka. Allah ya nufa hakan zai faru. Ga wannan cikin na Maleekh ne, amma ba ta hanyar alfasha ba. An ɗaura mana aure ne bisa dokar Musulunci… a cikin dajin.” ​Amal ta basu labarin abin da Mafarauta suka yanke musu: Cewa idan Maleekh bai yi mata ciki ba a cikin kwana uku, za su kashe shi su jefa shi cikin tekunsu mai zurfi, sannan kuma ita za su aura mata maza biyu a cikin mafarautan. ​Wannan labari ya sanya tausayi ya lulluɓe kowa. Sun fahimci cewa gudunsu ba wai don sha’awa ba ne, gudun tsira ne. An yi alhini sosai a cikin gidan. ​Nan take, aka ƙira likita aka duba lafiyar Amal da kuma ɗan da ke cikinta. ​Likita yana murmushi ya ce, “Dukkan su suna lafiya, amma dole ne ki rage yawan damuwa. Ki ci abinci mai gina jiki. Ki manta da abin da ya faru. Yanzu kin dawo gida lafiya.” ​Daga nan, aka fara ba Amal kulawa ta musamman, tare da abincin ƙara jini da na lafiya. ​Tana zaune a gidan Abbah don ta fi samun kulawa sosai daga Ammy da Inna. An ma buƙaci Inna ta ci gaba da zama a gidan, yayin da aka kulle gidansu na can. ​Yanzu Amal ta zama cibiyar tausayi ga kowa. ’Yan uwa da abokan arziki sun dinga zuwa duba ta. ​Farha, wacce yanzu ta ɗauki Amal a matsayin ƙawa, kullum sai tazo duba ta. ​Hatta Zayd shima ya zo ya ganta. Ya shigo cikin falo da fuska cike da fushi saboda kunya.. ​Zayd ya goya hannayensa, yana dubanta sama da ƙasa a yayin da babu kowa a falon sai su kaɗai. “Daman kun shirya guduwa ne? In ba haka ba, me zai kawo ciki? Ko ba komai, kun zubar da mutuncinku. Da farko kowa yana tunanin Maleekh sace ki yayi, amma yanzu ganin ciki ya sa kowa ya yarda guduwa kuka yi.” ​Amal, ta dube shi da kyau, ta yi wani murmushi na izgilanci fiye da nasa. ​muryarta a sanyaye ta ce, **“Daman na taɓa cewa ina sonka ne, Zayd? Dalilin da yasa zan aureka, saboda na musguna wa Maleekh ne. Amma kowa ya san cewa Amal da Maleekh su suka fi dacewa da juna. Kuma ga babyn Maleekh a jikina. Kaga kuwa soyayya tayi rana!” ​Zayd yana huci. Ya harare ta da wani mugun kallo sannan ya fita da sauri. Domin ba shi da ta cewa. ​Ammy tana ci gaba da ba Amal kulawa ta musamman har ta shiga watan haihuwarta. ​Kowa yana cikin farin ciki da jiran haihuwar, amma kuma cikin alhini na rashin Maleekh. ​Har zuwa yanzu, babu wani labarin Maleekh. Cikin dare, duk da cewa an rage mata damuwa, cikin Amal ya fara murɗa wa. Ta riƙe cikinta sosai, tana juyawa a kan gado. Ita kaɗai ce a cikin babban ɗakin kwananta da aka tanadar mata don kada a takura mata. ​Ta fara jin zafin nakuda mai tsanani. Ga kuma jini da ruwa suna bin ƙafarta. Ta fahimci cewa lokacin zuwan jaririn Maleekh ya yi. ​Ganin cewa ba za ta iya jurewa ba, kuma tana tsananin wahala, sai ta yi wani ihu mai rauni wanda ya ratsa cikin gidan. ​Ammy da Abbah suna ɗakinsu a upstairs suka ji ihun. Nan da nan suka sauƙo cikin tsananin firgici da gaggawa. A falon ƙasa, suka tarar da Inna da Islam da Arfat duk sun tashi daga barci. ​Dukansu suka nufi ɗakin Amal. Suka sameta a ƙasa, tana kuka riƙe da ciki. Nan da nan aka ɗauke ta da gaggawa zuwa Asibiti domin ba ta taimako. ​An garzaya da Amal zuwa asibitin masu kuɗi kuma mai daraja a Abuja. Asibiti ne da aka gina shi da kayatattun kayan gini, inda nutsuwa da tsafta suka mamaye kowane lungu da sako. ​An shigar da Amal cikin ɗakin aji Biyu (VIP Room) wanda ya yi kama da ƙaramin gida mai cin kansa, maimakon ɗakin asibiti. Bango ne da aka yi da launin zinare da creamy white, tare da fitilu masu laushi da ke ƙara annuri ga wurin. Gadon Amal tsararren gado ne, mai girma, tare da farin zannuwan gado masu taushi. Babban talabijin ne rataye a jikin bango, kuma akwai sofa masu taushi don waɗanda suka zo duba ta. Akwai ƙaramin falo a cikin ɗakin inda Abbah da Ammy suke zaune, yana nuna tsararren rayuwa da kuɗi suke bayarwa.. ​A cikin wannan ɗaki ne Amal ta sha wahalar nakuda har na tsawon dare. An mata allurai don rage mata zafi, amma ta ƙi, tana son ta ji tsananin zafi na haihuwar ɗan Maleekh... ​Da asubar farko, bayan tsananin wahala da jajircewa, Amal ta haifi ɗan namiji. Kafin a gama shirya jaririn, ta sake nakuɗa ta biyu cikin sauri, kuma ta haifi kyakkyawar yarinya mace. ​Amal ta samu Tagwaye (Twins) kyawawa! ​Jariran sun ɗauko kyawun gaskiya daga iyayensu, Maleekh da Amal, waɗanda tun asali kyawawa ne. Jariran manyan-manya ne, kuma fatar jikinsu fari tas mai haske, kamar farar fata ta Indian. ​Dukansu suna da suma mai kauri da dogon gashi a kansu, wanda ya yi kama da gashin al’adun Indiya. Ga ​idanuwansu farare, kuma suna da wani tsantsar annuri a fuskarsu wanda yake nuna cewa sun zo duniya da sa’a. ​Duk ma’aikatan asibitin sun yi mamakin kyawun jariran. ​Bayan an gama shirya jariran, ma’aikaciyar asibitin ta fito cikin farin ciki ta sanar da su Abbah da Ammy da suke jira a Compound (babban falon jira na asibiti). ​Ma’aikaciyar Asibiti tana murmushi ta ce da su, “Alhamdu Lillah! Muna taya ku murna! Allah ya sauƙe ta lafiya! Ba ɗaya ba, ba biyu ba… An samu Tagwaye! Namiji da Mace!” ​Dukansu sun cika da farin ciki sosai har suka yi sallama mai ƙarfi, suka gode wa Allah. ​An basu damar shiga ɗakin Amal domin ganin jariran. ​Suka shiga cikin tsananin farin ciki da kuma tausayi.. Uwar kuwa ta tafi dogon bacci sakamakon wahalar da ta sha da kuma alluran da aka mata don ta huta. ​Suna tsaye kowa ya kasa zama, suna kallon tagwayen da suka zama alama ta Maleekh a duniya.. ​Ammy tana kuka da murna, tana shafa kan jikokinta ta ce, “Maleekh… Maleekh na. Ga ‘ya’yanka sun zo duniya. Ina muku addu’a, Allah ya dawo da Abbansu!” 《》《》《》《》《》《》《》《》《》 Maleekh ya manta da komai a rayuwarsa, amma hakan bai hana shi saba da sabuwar rayuwarsa ba. Ya saba da Sojoji masu kula da shi, kuma kullum suna cikin wasa da dariya. ​Sojojin sun ba shi suna na musamman 'Lion'. Wannan sunan ya biyo bayan wata rana da suka shiga daji don motsa jiki, suka ci karo da wani zaki mai tsananin haɗari. Sojojin sun gudu, domin babu wanda ya taho da

Chapter 54 of 62