suka fara rawa.
Suna ɗaga wuta sama.
Ganyayyaki suna kaɗawa...
Auren da ba su taɓa mafarki ba yau an ɗaura musu...
A cikin daji.
A tsakanin mutane marasa kaya.
A ƙarƙashin hukuncin daji.
Akwai wata tsattsauran al'ada da dole su bi.
Shine zasu zauna anan.
An kafa wa Maleekh doka cewa dole ta samu ciki a cikin kwana uku.
Idan ba haka ba zasu jefa shi cikin babban tekun su.
Ita kuma Amal su aura mata maza biyu daga cikin mazan su.
Kuma a dokar su, maza biyu ne suke auran mace ɗaya domin mazansu sun ninka mata yawa...
Amal ta tsorata sosai.
An basu wani ɗaki wanda aka gina da itace.. wanda aka rufe da ganyayyaki..
Yana ta tunanin to kenam taya zai mata ciki a cikin kwana uku al'halin ba shine mai bada ciki ba..
Haka aka ajiye wannan dokar.
Idan kwana uku yayi akwai abinda suke gwadawa ya nuna musu mace ta samu ciki...
Da daddare, aka tura su cikin ƙaramin ɗakin da aka yi da itatuwa. Wurin yana ɗauke da ƙamshin ƙasa da ɗaci na hayaƙin wuta...
Amal ta zauna a kusurwar ɗakin tana rawar sanyi da tsoro, idanuwanta sun kumbura saboda kuka.
“Me zamu yi?” ta ce cikin murya mai rauni, tana kallon Maleekh da ya kasa zaune saboda damuwa.
Shima ya nufe ta ya durƙusa a gabanta.
“Ki saurare ni… ba zan bari su cutar dake ba. Wallahi ba zan bari ki shiga wannan muguwar al’ada ba.”
Sai kawai ta fashe da wani sabon kuka mai ƙarfi, tana tunanin yadda aka kakaba musu aure na dole, kuma yanzu ga wannan tsattsauran hukunci da ba zata iya tsallakewa ba.
A waje kuwa, ana ta busa wutar al’ada. Mazan mafarautan suna ta shirya manyan takubansu, kamar suna jiran ranar uku ta cika su aikata hukuncinsu. Matan kuma suna ta yi wa Amal siyayya ba don tausayi ba, sai don ta zama amarya ga mazansu idan saurayin ya gaza...
Maleekh yana ta tafiya a cikin ɗakin kamar zai haukace.
“Ya za mu yi ciki cikin kwanaki uku? Ni abun ya ɗaure mun kai… ba ni da damar…” ya tsaya, saboda ba zai iya faɗi gaba ɗaya ba...
Amal ta share hawaye ta ce,
“Suna cewa idan ban samu ciki ba… za su aurar da ni ga wani har biyu.. Kai kuma za su jefa ka cikin tekunansu. Kasan me hakan yake nufi?”
Shiru ya cika ɗakin.
A waje kuwa an kunna wuta suna rawar al’adarsu ta dare. Sautin ganguna ya ɗauki dajin da ihu na murna..
Duk suna ɗaki sun rasa abun yi, ya riƙe ta tare da zaunar da ita.
“Ni dai abu ɗaya nake so ki sani…” ya ce cikin muryar da ke rawa.
“Ko me ya faru, sai dai su kashe ni, amma ba zan bari su aurar ki ga wani ba.”
Ta kalle shi wannan maganar ta ƙara mata tsoro, amma kuma tanajin wani nau’in kwanciyar hankali a zuciya.
A wannan lokacin, matar shugaban mafarautan ta shigo ta ɗaga bargon ganyen.
“Ku shirya. Gobe da safe zamu fara bibiyar al’amuranku.”
Suka fita.
Amal ta kwanta a jikin Maleekh ta rungume shi saboda tsoro...
Da daren sun kwanta amma barci ya ƙi zuwa.
Gaskiya kawai ɗaya ce:
A cikin kwanaki uku ko dai su tsira…
ko kuma su rasa rayuwarsu.
Amal tana zaune tana murza yatsunta saboda tsoro da rashin tabbas. Maleekh kuwa ya tsaya a tsaye yana kallon ta, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi saboda nauyin abin da ake expects daga gare su.
“A yau ne daren farko…” ta faɗa cikin murya mai sanyi, tana kau da kai.
“Idan muka yi addu’a, ko Allah zai ba mu sa’a? Mu samu ciki kafin kwanaki uku?”
Ya zauna a gabanta a hankali,
“Ni ma haka nake fatan,” ya ce.
“Ba wai saboda dokarsu ba, don kawai saboda mu tsira. Kuma… saboda ina matuƙar jin ki a raina.”
Ta yi murmushi mai raɗaɗin tsoro.
“Ni ma ina sonka. Idan Allah ya rubuta a yau ne… toh shi kenan.”
Ya kamo hannunta, hannun yana rawa, nashi ma yana rawa. Babu wani wasa a al'amarin, sai zallar tsoro da soyayya, da fatan nasara a wurin Allah..
Suka durƙusa su biyun, suka ɗaga hannaye sama,
“Ya Allah, ka ba mu mafita.
Ka sanya mu samu abin da zai ceci rayuwarmu.
Ka kare mu daga wannan sharrin al’ada.
Ka sanya mu samu albarka a wannan daren.”
Hawaye ya zubo daga idon Amal saboda tashin hankali da addu’a a lokaci ɗaya.
Maleekh ya matsa kusa da ita.
“Ko da muna cikin tsoro… ni zan yi iya ƙoƙarina. Allah ya gani.”
Ta ɗaga kai, idonta cike da hawaye ta ce,
“Ni ma zan yi iya nawa. Ka tuna… muna da aure yanzu shine babban farin ciki, ba wai zina zamu aikata ba.”
Suka lumshe ido sannan suka rungumi juna, cikin nutsuwa da jin kunya da kulawa...
Babu hayaniya, babu rawar kai kawai nutsuwa, addu’a, da fatan cewa Allah zai basu ikon da zai ceci rayuwarsu..
Haka numfashinsu yake haɗuwa suna shakar ƙamshin jikinsu..
Cikin lokaci ƙanƙani suka haɗe bakinsu.... A hankali suke sumbatar juna, cike da ƙaunar juna da sha'awa lokaci guda..
Sun daɗe suna foreplay kafin a hau aiki 😅.
Haka take razana saboda tsananin zafi da raɗaɗi, a hankali ya furta mata a kunne.
"Sorry! Kar ki ji tsoro zafin na lokaci kaɗan ne......Zai shiga yanzu.....Zai shiga....Ki nutsu please..."
Haka take daure wa saboda kar mutanen waje su ji...
A waje ana ta busa ƙaho, alamar cewa mafarautan suna jiran sakamakon kwanaki uku....
☆☆☆☆☆
Bayan sun gama, suka rungume juna cikin shiru.
Ba wanda ya ce wani abu.
Kawai jin numfashin juna da fatan cewa Allah ya amsa addu’arsu.
Maleekh ya ce a hankali:
“Ina fatan wannan dare ya yi mana albarka.”
Ta jingina kanta a kirjinsa.
“Ni ma haka… gobe safe saura kwana biyu.”
Haka suka cigaba da zama, suna zaune rungume da juna cikin tsantsar gajiya da fargaba, sun sanya kayan jikinsu. Wurin ɗakin ya yi duhu, hasken fitilar wuta ta waje kawai ke shiga ta gefen ganyen da aka rufe..
Sai kawai suka ji ƙarar takun ƙafa, kafin ma su yi wani motsi, ɗan mafarauci ya bankaɗo kofar ɗakin da ƙarfi.
Ya shigo ba sallama, ba neman izini. Da wuƙa a hannunsa...
“Oh! Har yanzu kuna nan zaune? Baku yi komai ba kenan!” ya faɗi cikin tsawa yana huci...
Maleekh yana kallonsa cike da mamakin jahilci irin na wannan al'ada, ya ce.
“Yanzu muka gama...”
Mafaraucin ya zaro ido, yana matsowa kusa..
“Munafukai! Sai kun cire kayanku! Na rantse da dokar mu, sai na ga da idona.”
Maleekh ya girgiza kai ya ce,
“Yanzu muka gama fa. Kazo ka taɓa tabarmar nan zaka ji a jiƙe yake…”
Mafaraucin ya durƙusa ya taɓa tsakiyar tabarmar.
Sai kuma ya ɗaga kai ya yi ihu yana cewa.
“Ƙarya ne, ruwa kuka zuba! Kuna wasa dani ne? Sai kun cire kayan ku!”
Maleekh ya ce,
“Ta wahala sosai… ta gaji… ka bari—”
Kafin ya rufe baki, mafaraucin ya ɗago wuƙa sama, idonsa ya kaɗa da ja.
“Ƙarya kuke! Zaku yi yanzu! Ko sai nayi masa yankan damo..?”
Amal ta fashe da kuka, ta tashi a rikice tana marairaicewa:
“Dan Allah ka saurare mu! Zamu yi! Zamu yi! Amma ka fita. Bazai yu mu cire kayan mu a gabanka ba…”
Ta durƙusa tana roƙonsa, muryarta na rawa.
Amma mutumin ya girgiza kai:
“A'a! Sai an fara kafin na fita. Sai na tabbatar da gaskiya, domin turo ni akayi domin na duba.”
Haka ya tilasta su yin abin da yake so, sun tilasta kansu cire rigunansu bisa kunya, zuciya na rawa.
Sai da suka fara kusantar juna ba don sha’awa ba, sai don su tsiratar da kansu.
Sannan mafaraucin ya tintsire da dariya, ya juya ya fita.
Amma kafin ya tafi ya ce:
“Ku tabbatar na ji ihunta. Ko ba haka ba, gobe akwai hukunci.”
Ƙofar ta rufe da ƙarfi, ya bar su cikin yanayi, zafi, tsoro, da bugun zuciya.
Lokacin da su ka rage su kaɗai…
Amal ta fashe da kuka, hannunta na rawa kamar wacce aka jefa cikin wuta.
“Wallahi bana jin ƙarfin jikina… amma idan muka ƙi… za su kashe ka.”
Maleekh ya matso ya rungumeta a hankali:
“Ki yi haƙuri. Ba zan taɓa cutar da ke ba. Amma dole mu tsira. Ki bari mu yi abin da ya kamata, sannan mu yi abinda Allah ya sa a bisa aure.”
Suka yi addu’a cikin hawaye, sannan suka kusanci juna a hankali, cikin kwarin gwiwar auren da suke da shi...
Maleekh ya mara mata baya cikin sassauci, yana kwantar mata da hankali.
Ya zamar da rigarsa, tana jin bugun zuciyarsa kamar nata.
Sannan… suka shiga second round..
Na bar wannan bangaren cikin mutunci 🤭🙈
Amma a wannan karon Amal ta yi ihu...
Ihun
tsoro
raɗaɗi
nutsuwa
da kuma dalilin da za su tsira...
Ihun nata ya fita har wajen dajin.
Mafarautan suka ji.
Har an fara busa ƙaho, alamar sun gamsu da cewa “aikin daren” ya tabbata.
Wani dattijo a waje ya yi ihu yana faɗin.
“Sun yi! Sun yi! A gobe mu haɗa musu kayan ciye-ciye!”
Dajin ya cika da kiɗe-kiɗe da buge-buge..
A ciki kuma…
Amal na kwance a jikinsa tana kuka, shi kuwa yana shafa kanta:
“Ki yi haƙuri… ki yi haƙuri… duk da tsananin tsoro, Allah ya ga abinda ya faru.
Allah ya sani ba da son ranmu ba.”
Ta ce cikin rawar murya:
“Gobe sauran kwana biyu… idan ba ciki ba… zasu kashe ka…”
Shiru ya ratsa ɗakin.
Su biyun kawai, cikin duhu, cike da addu’a da fatan gobe zata kawo sabon numfashi ko kuma sabon bala’i…
💥
Asubar fari ya fara haskowa ta cikin ganyen da ke rufe rufin ɗakin itacen da aka basu.
Amal ta farka cikin firgici, tana rungume da jikinta kamar mai jin sanyi. Idonta ya kumbura saboda kuka..
Babu kaya a jikinta, haka ta lalumi kayan ta saka..Tana rawar sanyi..
Maleekh yana kwance sai baccin yake ta sha. Baccin gajiya..
A hankali ta tatta6a shi. Ya farga yana addu'a tare da lumshe ido..
Wani ƙaramin yaro ne ya leƙo cikin ɗakin, yana cewa:
“Shugaba ya ce ku fito. Akwai abubuwan da za a gwada yau.”
Dukkansu suka kalli juna da tsoro.
“Wane irin gwaji kuma?” Maleekh ya tambaya.
“Ba ni da ikon faɗi,” in ji yaron, ya gudu.
A Wajen Gari
Sun fito. Mafarauta suna tsaye a layi, tsirara daga sama zuwa ƙasa, sai ganyayyaki a jikin su. Da makamansu wuƙa, baka, kibau, sanda mai karan ƙarfe..
Mutanen gari sun yi shiru.
Shugabansu, dattijo mai dogon gemu da tabo a fuskarsa, ya ce:
“Yau kwana na biyu kenan. Dole mu tabbatar idan akwai ‘alamar ciki’ ko babu.”
Maleekh ya ji jikinsa ya sake, tsoro ya daki zuciyarsa.
“Wace alama kuke nema?” ya tambaya a hankali.
Shugaban ya ɗauko wani ƙaramin kwandon itace da ganye kore da farar laka a ciki.
“Zamu yi gwajin ganyen Takur-shi.
Idan matar nan ta zauna a kai, ganyen ya yi fari to ciki na nan.
Idan ya koma baƙi, to babu komai.
Idan babu komai kafin kwana uku, sai dai hukuncinmu.”
Amal ta jijjiga kai tana kuka:
“Don Allah, na gaji! Wannan abu ya yi min yawa…”
Sun ba ta ganyen.
Sai suka tafi su biyun zuwa wani yanki na dajin da babu mutane.
Sai wasu mata masu rakiya..
Suka isa wani wuri mai sanyi da bishiyoyi.
Suka zauna a ƙasa...
Amal na kuka kamar ranta zai fita.
Maleekh ya riƙe hannunta, yana jin zafin duniya a kansa.
“Ki yi haƙuri. Ki zauna a kai. Allah zai yi mana mafita…”
Ta zauna a hankali kan ganyen da ke cikin kwandon.
Suka jira. Shiru. Sai kukan tsuntsaye.
Mintuna suka wuce.
Maleekh ya ɗaga ta sannan ya duba ganyen a sannu…
Ya yi fari.
Amal ta yi ajiyar zuciya.
Amma shi ya gane wani abu…
Ba fari sosai ba ne, daidai tsakanin fari da launin baƙi yake..
“Wannan ba alamar fari bane.” ya faɗa a ransa.
Amma bai faɗa mata ba saboda tsoron ya ƙara rikita ta.
Ta yi murmushi kaɗan, cikin hawaye:
“Alhamdulillah… ka gani?”
Ya yi mata murmushin ƙarya:
“Na gani.”
Amma hankalinsa ya cika da tambaya:
“Idan suka ga ba fari sosai ba fa?”
Sai suka miƙe suka koma gari..
A GABAN MAFARAUTA
Shugaban ya karɓi ganyen ya kalla da kyau.
Mafarautan suka kange su a kewayen wuri gaba ɗaya.
Dattijon ya ce cikin murya mai nauyi:
“Ganyen ya nuna… ba cikakkiyar alama ba ce.
Wato… wataƙila ta fara, ko kuma babu komai.”
Wani matashi daga cikin mafarauta ya yi ihu:
“To mu jefa shi cikin tekun! Dokarmu ba wasa bane!”
Amal ta fashe da kuka tana riƙe da Maleekh sosai:
“Dan Allah ku ba mu zuwa gobe! Don Allah! Gobe ne kwana na uku! Don Allah!”
Matar shugaban wacce ta cece su jiya ta shiga tsakani:
“Ku bar su. Ba ku ga fari ba? A ajiye hukunci zuwa gobe.
Gobe ne rana na uku..."
Mafarautan suka yi gurnani da jin haushi, amma babu wanda ya ƙi umarnin matar shugaba.
Shugaban ya yi magana a tsawa ce:
“Kwana na uku zai yanke hukunci.
Ko ciki ko teku...!”
Maleekh ya lumshe ido, zuciyarsa na bugawa.
Amal ta riƙe hannunsa tana kuka...
“Ba za su kashe ka ba… ba zan bari ba…”
Amsar da ta fito daga bakinsa cikin muryar da ya yi ƙoƙarin ɓoye rawar kuka ita ce:
“Idan Allah bai kawo mu’ujiza ba… gobe zan ga ƙarshena.”
Daren ya gangaro da sauri a dajin. Ga wutar da mafarautan suka kunna a tsakiyar ƙauyen...
An mayar da su cikin ɗakin su na ganye da itace.
Kamar jiya, babu kofar rufe wa...
Sai da suka shiga suka zauna sannan suka ji zuciyoyinsu biyu suna bugawa da sauri.
Amal ta jingina da bango, hannunta na riƙe da ƙirji.
Maleekh ya zauna a gabanta cikin nutsuwa.
“Gobe shine ƙarshe… idan ba a samu cikakkiyar alama ba…”
Ya kasa finishing kalmar.
Ta ɗago kai cikin hawaye:
“Dan Allah kada ka faɗi hakan. Ka tuna da addu’a.”
Sai ta matso kusa da shi, ta jingina kanta a kafaɗarsa.
Zuciyarsa ta lafa kaɗan.
Saɓanin Jiya, A Yau Dajin Ya Yi Shiru
Babu sautin komai.
Kamar an dakatar da dukkan halittu saboda wani abu da zai faru.
Sai dai daga can nesa, suna iya jin:
Takk! Takk!
Kamar ana yanka itace.
Maleekh ya ɗaga kai da sauri.
“Ina jin kamar suna shirya wani abu…”
Amal ta matso kusa da shi sosai, muryarta na rawa:
“Ka riƙe ni… ban jin daɗi.”
Ya riƙe hannunta, yana shafa bayanta a hankali...
Daga can suka ji shigowar mutum yana matsowa cikin ganyen da ke rufe su.
Amal ta sa hannu ta rufe bakinta saboda tsoro kar ya ji motsi.
Maleekh ya riƙe ta sosai yana whispering:
“Shhh… ki zauna a baya… bari in wuce gaba.”
Ganin dajin babu wani abu da zai kare su sai Allah, ya matsa kusa da ƙofar itacen da aka ɗaure.
Wani irin bakanen mutum ne ya leƙo
gashinsa a ɗaure da igiya,
kuma ganyen da ya rufe jikinsa ya fi na sauran nauyi...
Ya yi magana a hankali kamar ba ya son wani ya ji:
“Ku kwana lafiya… amma ku sani akwai wasu da ba su yarda da ku ba.”
Maleekh ya tsaya daram:
“Wa ye kai? Ka zo ka cutar da mu ne?
Mutumin ya ce:
“Ba don cuta ba. Don gargaɗi.
Wasu maza sun ce gobe ba za su jira gwaji ko alama ba suna so su ɗauki matar nan.”
Amal ta fashe da kuka.
“Sun ce idan ba ka ba ta ciki ba, to zasu yi mata ‘tubani’ wato su raba ta gida biyu su bayar ga wasu...”
Maleekh ya ji jikinsa ya yi sanyi gaba ɗaya.
“Wannan ba adalci bane!”
Mutumin ya yi shiru na daƙiƙu kuma ya ce:
“Ni ɗin ba ni da iko. Na zo ne in sanar da ku.
Ku kwana a farke… ku yi addu’a.
Gobe ba zai yi sauƙi ba.”
Ya ɓace kafin su ce wani abu.
Bayan ya tafi
Suka zauna su biyun kamar kurame.
Maleekh ya zura ta cikin jikinsa ya rungume ta sosai, zuciyarsa tana bugawa kamar tambari.
Amal ta ce cikin kuka mai sanyi:
“In ba mu tsira ba fa? In gobe ta yi fa?”
Ya goge mata hawaye,
“To ki saurare ni. Idan suka zo gobe, ko me zai faru, ba zan bar ki ba.
Idan ni za su kashe to ki tabbatar kin gudu. Ki gudu ki kuɓuce...”
Ta girgiza kai da sauri:
“A’a! Ba zan bar ka ba!”
Ya kalli idonta cikin duhun ɗaki, ya shafi kumatunta:
“Kin riga kin zama matata. Kuma zan kare ki da rayuwata...”
Ta matsa jikin sa sosai, tana jin numfashinsa yana tafiya da sauri.
Daren ya yi tsawo, suna jin bugun zuciyar juna kawai.
Yau babu wani wanda ya kusanci su cikin ɗaki, amma tsoron gobe ya fi duk wani abu tsanani..
Amal ta yi magana cikin rauni:
“Ka yi addu’a ka sake rungumata… zuciyata na tsalle.”
Ya sake matseta a hankali, suna kallon fitilar daji ta waje tana ɗaukar ido.
Cikin sanyi da matsanancin tsoro, suka kwana suna rungume da juna har gari ya fara haske...
Gobe… gobe… ita ce ranar hukunci....
_NEXT NEXT NEXT_
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 83 to 84
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Da asuba, hasken farko ya shiga cikin dajin. Amal da Maleekh sun buƙaci a kaisu bakin ruwa domin wankan tsarki na janaba, kamar yadda addinin Musulunci ya tsara, duk da cewa mutanen dajin ba sa bin wannan dokar..
Maza biyu ne suka rakosu, masu gadinsu.
Bayan sun yi wankan tsarki, kusa da wurin ruwan, suka yi sallah. Domin wurin shine wurin da suke ganin yafi tsarki.
A lokacin da masu gadin suka juya bayansu don gudun ganin tsaraicinsu yayin da suke wanka, Maleekh ya fahimci cewa wannan ce damarsu ta ƙarshe. Ya riƙe hannun Amal da ƙarfi.
A hankali, ya furta ciki-ciki, “Mu gudu… ki riƙe hannuna, mu gudu…”
Amal ta dube shi cikin tsoro ta ce, “Machine ɗin yana hannunsu. Ba zamu iya tafiya ba!”
Ya ce, “In sha Allah zamu tsira, ba tare da machine ba. Allah yana tare da mu, zo mu tafi!”
Basu jira wani tunani ba. Suka ratsa wani wuri da masu gadin ba sa nan. Suka yi amfani da juyawar bayansu a matsayin kariya kuma suka fara gudu cikin dajin.
Can aka ji shiru. Masu gadin suka leƙa, sai suka ga ba su nan. Nan da nan aka hura ƙaho, kuma dukkan mutanen dajin suka bazama, suna neman su.
Suna gudu cikin dajin ba ji ba gani. Ba takalmi a ƙafafunsu, suna taka kwalabai da itace masu kaifi, amma basu tsayar da gudun ba.
Daga nesa, aka fara harbo kibiyoyi.
Cikin sa’a marar kyau, wata kibiya ta samu nasarar harba ƙafar Maleekh. Wata kuma ta shige shi a baya. Amma bai saki hannun Amal ba. Ya ci gaba da gudu, yana jan ƙafarsa da ƙyar.
Sun kai bakin wani babban ruwa wanda shi ne iyakar dajin da kuma mafarautar suke. Idan suka tsallaka, sun tsira.
Cikin sa’a, suka tarar da wani ƙaton taya a wurin. Maleekh ya ɗauko shi da sauri, domin mutanen sun kusan iso wa.
Ruwan yana da matuƙar zurfi.
Ya ɗora tayar a wuyan Amal, sannan ya jefa ta cikin ruwan, yana faɗin, “Ki riƙe tayar sosai. Kiyi ƙoƙarin tsallakewa. Ba zan bari a cutar da ke ba!”
Amal tana kuka tana faɗin, “Babu yanda zanje na barka! Kazo mu tafi tare!”
Tayar ce ke ta tafiya da ita, kamar jirgin ruwa.
Shi kuwa Maleekh, jini sai zuba yake a jikinsa. Kibiyar da ya ji a baya ta yi masa rauni, amma da saninsa ya yi ƙoƙarin tare kibiyoyin don kada su same ta. Dafin kibiyar ya fara ratsa shi.
Yana tsaye, sai da ya tabbatar da ta yi nisa, sannan shima ya juya, ya bi wata hanya daban, yana jan ƙafa da gudu da ƙyar...
Bayan Maleekh ya bar wurin, sai ga mafarautan dajin sun iso, suna ihu.
Suka tsaya a bakin ruwan, suna hango Amal ita kaɗai a tsakiyar ruwan, cikin tayar. Har ta kai tsakiya, ta bar yankinsu, ta shiga wani yanki daban.
Mutanen dajin suka firgita, da cewa
“Wannan yarinyar ce ita kaɗai ta tsere mana! Shin ina yaron? Duk yanda akayi yana cikin yankin nan!”
Suka ga yadda jinin Maleekh ya zuzzuba, ya zama kamar wani rubutu a ƙasa. “Ba zai yi nisa ba. Yana kusa…”
Suka durƙusa, suna laluben ƙasa. Suna biye da tabon jinin, wanda ya yi layi kamar zane. Suna binsa, kamar karnukan farauta.
Maleekh yana ci gaba da gudu, numfashinsa na fita. Kibiyar bayansa ta yi masa nauyi, dafin kibiyar yana ci gaba da cin jikinsa kamar wuta marar hayaƙi. Ya ji jikinsa yana sanyi, hannayensa suna rawa.
Ya ji ƙasa ta juya masa. Yayi tuntuɓe ya faɗi amma da haka ya miƙe da ƙyar, yana jan ƙafa ɗaya kamar gurgu.
Kamar daga sama ya ji muryar su daga bayan daji,
“Ga shi nan! Ga jinin nan yana tafe!” “Kada ku bari ya tsere! Ku kama shi kafin ya tsallake yankin mu!”
Hankalin Maleekh ya ƙara tashi. Gumi ne ke ta kwaranya a jikinsa, zuciyarsa tana bugawa kamar ƙaho “Kar na mutu kafin in tabbatar ta tsira… kar su kama ni domin bana so na hallaka a hannunsu.”
Da ƙyar ya rarrafa. Ya kama jikin wata bishiya mai kaifi, yana jan kansa gaba.
Har sai da ya ji ƙafarsa ta zame, ya faɗi ƙasa da ƙarfi. Kibiyar da ke bayansa ta makale sosai, ba ƙaramin shigarsa tayi ba..
Ya yi ihu kaɗan yana cije haƙoransa..
A lokacin ya ji ƙafafunsu sun kusanto.
“Ga shi nan!” ɗaya ya yi ihu. “Kada ku bari ya mutu nan! Ya kamata mu jefa shi cikin babban tekun nan, yadda doka ta ce!”
Ya kalli gaba, sai ya ga ƙaramin kwazazzabo a cikin ƙasa, ramin da ruwa ya tone...
“Wannan ce damar da ya rage…”
Maleekh ya tattara ƙarfin da bai san yana da shi ba. Ya nannarke jikinsa cikin ramin, yana ɓoye kansa da ƙasa..
A dai dai lokacin da suka iso, sai jinin da ya zuba ya tsaya a bakin ramin, amma babu alamun sa.
“Sai dai idan ƙasa ta haɗiye shi!”
"Amma babu yadda za'ayi ya shige ƙasa, dole yayi wani hanya daban..."
Suka ƙareshi maganarsu daga bisani suka ci gaba da bi, suna bazama cikin daji, suna ta ihu.
Maleekh kuwa yana ɓoye a ciki, kamar gawa. Numfashinsa na fita a hankali. Jikin sa yana rawa.
A hankali, ya furta cikin zafi.
“Allah… ka kare ta… ka kare ni…”
Ruwan rami ya fara cika wurin da yake kwance, saboda ruwan yana zuba daga sama. Yana jin jikinsa yana nutsewa.
Sai duhu ya mamaye shi.
Daga nesa, muryar mafarautan ta sake tashi da ƙarfi, “Mun rasa shi! Amma dole sai an same shi kafin dare! Mai cin dokar mu ba ya rayuwa!”
Maleekh ya shiga cikin duhu mai sanyi. Ruwan ramin yana ci gaba da cika, yana shigar masa hanci da baki. Dafin kibiyar yana aiki tukuru, yana kashe masa jijiyoyi, kuma zafin kibiyar da ta shige shi ya sanya jikinsa ya yi nauyi kamar guba. Ya ji kamar ruwan ya rufe shi gabaki ɗaya.
Amma a cikin wannan nutsuwar, wani ƙaramin abu ya haskaka a cikin zuciyarsa wato Amal.
“Kada in mutu kafin in tabbatar ta tsira…”
Wannan tunani ya zama ikon numfashinsa. Ko da yake numfashinsa yana raguwa, tunanin cewa idan ya mutu mutanen dajin za su dawo su nemo ta ya ba shi ƙarfin da ya tilasta masa buɗe idanunsa da suka rufe da ƙasa.
A hankali, Maleekh ya fito da yatsunsa daga cikin laka. Ya ɗaga kansa daƙyar, ruwan ramin ya kusan cikowa, ya zama kamar wani ƙaramin kogi mai ruwan laka. Ya ji motsi sama da shi, sautin tattaunawar mafarautan sun fara raguwa, alamun suna ta nisa. Suna ci gaba da bin sawun da basu samu ba.
Ya jira har sai da shiru ya sake mamaye daji. Dajin ya koma wurin tsoro.
Daƙyar ya fito daga cikin ramin. Jikinsa ya yi sanyi, ga zafi, ga zufa. Kibiyar ta shige shi sosai, kuma ya san cewa dole ne ya cire ta ko ya mutu..
Jikinsa duk taɓon ƙasa, haka ya rarrafa ya je ya wanke fuskarsa sannan ya jingina da wata bishiya mai kauri, ya tattara duk wani ƙarfi na ƙarshe.
Cire kibiya mai dafi na iya zama haɗari, amma Maleekh ya san cewa barin ta ma zai kashe shi.
Haka ya riƙe jikin kibiyar da ƙarfi, ya yi ihu marar sauti saboda zafin da bai taɓa ji irinsa ba, kuma ya ja ta da sauri. Jini ya sake ɓarkewa daga jikinsa, amma tare da shi wani nauyi da zafi ya ɗan ragu. Ya faɗi ƙasa yana huci, amma ya yi nasara.
Ya tattara wasu ganye waɗanda ya san suna da magani ya ɗaura
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 53 Chapter of 62