Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ciki ne ai Maleekh za a zarga, domin ban taɓa kula wani ba sai shi. To wallahi ya isheki, Inna.... Kuma shi Maleekh ɗin, idan akwai hukunci a kaina, ya rage nasa, tunda shi ya san gaskiyar Amal ɗinsa.” Inna ta miƙe cikin masifa tana zaginta, itama Amal ta ƙara ƙarfafa murya cikin zafi ta ce: “Inna, ko tsine mun kikayi, wallahi bazai kamfani ba. Domin ba ke kika haifeni ba. Mahaifina kika haifa, ba ni ba. Shi ya mutu balle… Ni jikarki ce, amma ba ƴarki ba!” Kalmar ta girgiza Inna, ta tsaya tana haki tana kallonta da mamaki da fushi. Amal kuwa bata tsaya ba, ta juya cikin isa ta bar falon... Tana fita ta shiga motarta kai tsaye ta nufi company, zuciyarta cike da haushin rayuwa amma ta daure ta sanya fuskar izza domin ta san yanzu dole ta tsaya ta kare matsayin da Maleekh ya bari a hannunta. Motar Amal ta tsaya a bakin harabar CashTalk Empire. Security da receptionists suka yi saurin tashi da girmamawa, kowannensu na zuba mata ido. Sun ji tsoro da mamakin irin labarin da ya bazu akan Amal cewa ta zubar da ciki a gidan rawa. Amma babu wanda ya furta komai, saboda sun san matsayin ta: Assistant CEO. Amal ta fito daga motarta a hankali, dogayen takalmin da ta saka na ɗaukar hankali. Gyalen da ta ɗora ya ɗan zame gefe yana ƙara fito da tsantsar kamalarta. Idanuwanta da farin glass ya lullube suka bada wani irin izza da basira. Kowa da yake kallonta ya ɗan sunkuyar da kai, suna yin gaisuwa cikin ladabi. Ma’aikata suka miƙa gaisuwa da cewa: “Good morning, Madam Amal.” Amal ta ɗan ɗaga hannu a hankali, muryarta a nutse ta ce: “Morning.” Ta wuce kai tsaye zuwa elevator, kafafuwanta na yin taka-tsantsan kamar sarauniya. Duk inda ta bi sai kallonta ake yi, amma babu wanda ya ƙara magana. Wasu ma’aikatan mata suka yi shiru suna bin ta da ido cike da hassada da kuma mamaki. Bayan ta shiga office ɗinta, ta rufe ƙofar da ƙarfi ta jingina da ita. Ta runtse idanuwanta tana jan numfashi mai nauyi. Zuciyarta tana tuna zagin Inna, kalaman Ammy, da kuma yanda Maleekh ya nuna mata baya son ta. Sai dai ta girgiza kai, ta tafi ta zauna a kan kujerar executive chair mai juyawa. A gabanta akwai takardun contracts, files masu yawa da suke jiran signature ɗin Maleekh. A hankali ta fara ɗauka ɗaya bayan ɗaya, tana nazari sosai. Amal a cikin zuciyarta ta ce: “Ba zan bari mutanen nan su raina ni ba saboda abinda suka ji. Ni Amal ce Assistant CEO. Kuma na san kowa a nan da yake aiki yana jiran ganin ikon da zan nuna.” Ta ɗaga wayarta ta ƙira secretary. Amal ta ce: “Kawo min dukkan reports na kwana biyun nan da na yau. Ina son ganin komai kafin ƙarfe goma. Kuma ka sanar da managers ɗin departments su shigo da briefing yanzu.” Secretary ya bada amsa da cewa: “Yes, Madam.” Bayan ‘yan mintoci kaɗan, manyan ma’aikata da managers suka shiga office ɗinta cikin ladabi. Sun tarar da ita zaune, ta cire glasses tana kallon files a gabanta. Amal ta ɗago da idanu masu kaifi ta ce: “Ku zauna. Ina so in ji matsayin kowane department yanzu. Maleekh baya nan, amma aiki bai tsaya ba. Ku tuna, company ba ta tsaya wa akan mutum guda sai dai akan tsarin aiki da jajircewa.” Managers suka kalli juna, kowanne yana girmama ƙarfin halinta. Duk da ƙazafin da ake mata, ta zauna a matsayin shugaba mai cikakken iko. A lokacin, ɗaya daga cikin managers ɗin ya ɗan gyara murya cikin girmamawa ya ce: “Madam, gaskiya muna mamakin yadda kika zo da ƙarfi haka. Mun san komai da ake magana a waje, amma yanzu mun ga da idonmu kin fi ƙarfin duk wata jita-jita. Zamu ba ki haɗin kai.” Amal ta ɗan murmusa, murmushin da ya cika da takaici da izza a lokaci guda.....ta ce: “Kyakkyawan aiki shine amsar da zan bawa maƙiyi. Babu wanda zai ce Amal ba ta da daraja. Ni zan tabbatar da haka.” Sai ta ɗora hannunta akan files ɗin gaban ta ta fara briefing, tana ƙiran department ɗaya bayan ɗaya. Duk da zuciyarta na ta ƙuna da zafin kaunar Maleekh, a wajen aiki ta bayyana kamar wadda babu wata damuwa da ta taɓa zuciyarta. Bayan ta kammala meeting ɗin managers, Amal ta koma office ɗinta. Duk wani aikin da aka kawo mata ta duba shi da tsantsar hankali, ta sanya signature inda ya dace. Duk da gajiyar zuciya da ke cin jikinta, ta tsaya daram ta tabbatar da babu wani abu da zai tsaya a gaba saboda rashin Maleekh. Sai dai lokacin da ta kalli agogo ta ga ƙarfe 3:30 na rana. Zuciyarta ta fara bugu da ƙarfi. Ta san akwai wurin da zuciyarta ke jan ta: Office ɗin Maleekh. Da sauri ta miƙe, ta ɗauki glass ɗinta ta ɗora, ta ɗauki jakarta ta fita daga office ɗinta. Bata tsaya sauraron kallon da ma’aikata ke mata ba, ta nufi babban office ɗin CEO.... (Oh ko ina dai sai ka samu magulmata..). Bayan ta isa bakin ƙofar, zuciyarta ta buga sau uku kamar zata fito. Ta jingina da ƙofar tana jan numfashi mai nauyi. A hankali ta murɗa handle ɗin ta shiga ciki. Office ɗin na Maleekh ba kowa a ciki. Sai duhu, sai shiru, sai kuma ƙamshin turarensa da ya lulluɓe ɗakin gaba ɗaya. Amal ta tsaya cak a bakin ƙofa. Idanuwanta suka rufe, zuciyarta ta fara rawa. Kamar Maleekh yana zaune a kan kujerarsa yana mata kallon ƙauna. Ta ja ƙafar ta a hankali ta ƙarasa zuwa kujerar executive chair ɗinsa. Ta taɓa bayan kujerar da hannunta, hawaye suka zubo mata. Amal a cikin ranta ta ce: “Oh Maleekh… har yanzu ƙamshinka yana nan. Har yanzu zuciyata ta ƙi yarda da cewa baka sona. Me yasa kake min haka bayan dukkan so da ka nuna mun?…” Ta zauna a kujerarsa, ta jingina da kujerar tana runtse idanu. Hannunta ta ɗora akan teburinsa tana shafa wani pen da yake ɗauke da rubutunsa. A hankali ta ɗauki hotonsa da ke kan teburin wanda aka ɗauka lokacin award ɗinsa na CEO of the Year. Ta ɗauki hoton ta kalle shi sosai, hawaye na zuba. Amal a hankali da murya mai rawa ta ce: “Ko da duniya ta juya mun baya, ko da iyayenka basu fahimce ni ba, na rantse ba zan taɓa daina sonka ba. Koda kuwa ka tsane ni…” Sai ta ɗora hoton akan ƙirjinta, ta rufe idanu tana jin tsantsar ƙauna da zafi a zuciyarta. A waje kuwa, wasu daga cikin staff sun hango Amal na fita daga office ɗin CEO ɗin daga baya, suka kalli juna cikin mamaki. Wata daga cikinsu ta ce da sannu-sannu: “Lallai wannan yarinyar akwai ƙarfin hali… Da ace ni ce a irin halinta, wallahi ba zan iya zuwa ko kusa da wannan campany ba. Amma ita, har tana iya shiga ta zauna.” Staff ɗin namiji ya ce: “Shi ne bambancin mace mai kishin zuciya da ƙuduri. Ko da kuwa duniyar bata yinta, sai ta tsaya tsayin daka akan abinda take so.” Amal ta fito daga cikin office ɗin Maleekh, ta nufi ƙofar fita daga campany. Sai dai a tsakar corridor ta hangi wasu ma’aikata mata biyu suna ta magana da dariya, suna kallonta a ɓoye. Da ta matsa kusa ta ji da kunnenta suna faɗin: “Ko kunya bata da ita wallahi. Kin manta irin yadda aka ɗauke ta a cikin jini daga gidan club? Ai magungunan zubar da ciki ta sha...” Ɗayar ta ce: “Haka fa. Amma yanzu gashi tana tafe da wani isa kamar ba ita ake nunawa a TV ba. Wallahi akwai wauta a rayuwa.” Amal ta tsaya cak! Ta ja numfashi ta juyo a hankali. Da glass a idonta, fuska cike da izza, ta taka cikin tafiya mai natsuwa zuwa wajen reception. Sai ta tsaya a tsakiyar hall ɗin inda ma’aikata suke cike. Ta ɗaga hannunta sama ta ce da murya mai ƙarfi: “Ina son waɗanda na jiyo suna gulmata su fito nan yanzu. A gaban kowa. Ku fito!” Sai aka yi shiru, kowa ya kalli juna. Su biyun da suka yi maganar suka fara rawar jiki suka fito a kunyace. Amal ta juya da kafaɗarta, ta cire glass ɗin daga idonta a hankali, ta dafa tebur ta ɗan jingina, sannan ta ce da murya mai kaushi: “Kun ce bani da kunya? Kun ce an ɗauke ni cikin jini daga club? Kun ce magungunan zubar da ciki ne suka kaini can? To ku saurara! Ƙaddara bata san gidan kowa ba. Wallahi idan wata rana irin wannan ta same ku, da kun san babu abinda ya fi shiru da adalci a rayuwa. Amma saboda ƙarancin tunani, ku kaɗai kun fake kuna munafurci, wawaye kawai, marasa kishin kai...” Sai ta kalli sauran ma’aikata gaba ɗaya, ta ɗaga hannu tana girgiza musu yatsa ta ce: “Ina so a san wannan a matsayin gargaɗi. Duk wanda na sake jin ya tsoma baki cikin rayuwata ko kuma ya kuskura ya sake ambaton wannan batu a bakin sa, wallahi zan rubuta masa takardar kora a nan take. Na rantse da ikon Allah zan tabbatar da ya bar wannan campany ba tare da second chance ba!” Ta ɗan ɗaga kai cikin izza ta ƙara da cewa: “Kar ku manta, ko da ban mallaki kujerar CEO ba, yanzu ni ce assistant CEO. Kuma ikon ɗaukar hukunci a hannuna yake. Don haka kowa ya kashe wutar gabansa, ya kula da aikinsa. Ku tuna..." Ta maida kallonta kan matan da ta kama tana cewa: "Mata ne ku, ba ku san irin makomar da Allah ya tanadar ba. Kada ku yi min hukunci da sharri, domin yau ni ce, gobe wata ce.” Ta ɗora glass ɗinta a idonta, ta juyo cikin izza ta nufi ƙofar fita. Takunta na ƙara amo a cikin shiru da kowa ya yi. Sai ta ce kafin ta fita: “Na gama magana. Ku tuna da abinda na faɗa.” Ta fice ta nufi motarta. Gaba ɗaya ma’aikatan suka tsaya shiru, suna kallonta cike da mamaki. Wasu suka lumshe ido suna cewa: “Wallahi wannan yarinya ƙarfin hali gareta sosai. Duk da kuwa an yi mata sharri, sai ta tsaya ta kare kanta.” Wani ya ce: “Eh… wannan izza da kwarin gwiwa ba kowa ke da shi ba.” Bayan Amal ta fice daga cikin campany cikin izza, harabar ofishin ta yi shiru kamar wuta ta mutu. Duk ma’aikatan kowa da abinda yake tunani, babu wanda ya iya sake yin magana. Sai PA ɗin Maleekh, ya fito daga cikin corridor. Shi ya shaida komai tun lokacin da Amal ta tsaya ta tara ma’aikatan. Ya tsaya yana kallon fuskar ma’aikatan da suka yi ƙasa da kai cikin kunya. Ya ɗan gyara murya ya ce: “Kun ga wannan abin da ya faru yau? Wannan yarinya ta nuna muku cewa bata da rauni a zuciyarta. Duk wani sharri da za ku ƙirƙira mata, wallahi za ta iya fuskantarsa da ƙarfin hali. Idan har tana iya tsaya ta kare kanta haka, to ta cancanci a ƙira ta shugaba.” Sai ya ɗan yi shiru ya kalli su biyun da Amal ta fallasa a gaban kowa. Ya ce: “Kuma ku, ku ji tsoron Allah. Wannan abu da kuka yi ba magana bace ta office. Aikin ku ne ya kawo ku nan, ba rayuwar wani ba. Ku ma ku iya tunanin kanku, me zai faru idan wata rana aka yi muku sharri irin wannan? Kada ku kuskura ku kuma.” Daga nan ya ɗan juya yana kallon sauran ma’aikatan gaba ɗaya: PA ɗin Maleekh ya ce: “Na ga yawanku kunyi shiru, kun girgiza kai. Wannan darasi ne. Kar ku manta duk wanda ya ƙi yin aiki da hankali da mutunci, wallahi Amal ba zata taɓa bari ya lalata campany ba. Kuma ni kaina zan tsaya a bayanta.” Ya jinjina kai ya ce a hankali: “Ko da kuwa Maleekh baya nan, Amal ta riga ta tabbatar da kanta a matsayin mai ikon ɗaukar hukunci. Ku kiyaye.” Sai ya juya ya koma cikin office ɗinsa, barin ma’aikatan da ke jinjina da cewa Amal ta nuna ƙarfin hali da cikakken iko. Da dare bayan kowa ya watse daga campany, PA ɗin Maleekh ya ɗauki waya ya ƙira ɗakin asibitin da yake kwance. Bayan sallama da gaisuwa, aka miƙa masa wayar zuwa Maleekh... PA ya ce: “Boss, ina fatan jikinka ya ɗan sauƙa?” Maleekh Ya ɗan murmusa da rauni sannan ya ce: “Muna nan, Allah na tare damu… Amma ka fadamin gaskiya, me yake faruwa a campany? Na ga har yanzu baku kawo mun daily report ba.” PA Ya yi gyaran murya, zuciyarsa cike da damuwa ya ce: “Hakane Boss… Amma akwai abu da na ga ya kamata ka sani kai tsaye. Yau bayan Madam Amal ta kammala aikinta, ta fito ta iske wasu daga cikin ma’aikatan suna gulmarta… suna cewa wai ‘yar club ce, da kuma zancen zubar da ciki. Boss, wallahi duk ma’aikata sun tsaya suna ji.” Maleekh ya runtse ido, zuciyarsa ta sake raɗaɗi, amma ya ce a hankali: “To, me tayi?” PA ya ce: “Wallahi, ta tsaya a gabansu cikin izza. Ta tara su gaba ɗaya, ta fallasa waɗanda suka fara gulmar, ta wulakanta su a gaban jama’a, sannan ta gargaɗi dukkanin ma’aikata cewa idan har wani ya sake taɓo wannan batun, zai fuskanci takardar kora. Boss, komai ta yi cikin natsuwa da ƙarfin hali.” Shiru ya cika ɗakin, Maleekh yana maida numfashi da nauyi. Duk da jin haushin Amal da yake yi tun daga asibiti, zuciyarsa ta girgiza da jin irin tsayuwar da ta yi a kan mutuncinta... Ya ɗago kai yana kallon PA ɗin da yake cikin call ya ce: “Duk wanda ya sake gulmar Amal a campany, kai da kanka zaka rubuta mun sunansa. Ba zan yarda wani ma ya wulakanta ta a ofishin nan ba. Kowane mutum yana da kurakurai, amma wannan ba dalili bane da zai sa a raina assistant CEO. Kaji ko?” PA da murmushi cikin girmamawa ya ce: “Na ji sir. Zan tabbatar babu wanda ya kuma.” Maleekh ya lumshe ido, zuciyarsa ta kumbura da abubuwa biyu: haushin Amal saboda sakamakon zubar da ciki da yake tunani, da kuma ƙarfin hali da ta nuna a bainar jama’a. Ya ja numfashi a hankali ya furta: “Amal… kin zame min raɗaɗi...” Bayan PA ya katse wayar, Maleekh ya jingina da filo yana rufe idanuwansa. Zuciyarsa na juyawa tsakanin soyayya da ƙiyayya. Sai ga Ammy ta shigo ɗakin da tray a hannu, ta kawo masa tea. Ta zauna kusa da shi tana tambayar: “Ya jikinka ɗana? Har yanzu kana ɗauke da damuwa ne?” Maleekh da murmushi ya ce: “Alhamdulillah Ammy, jikina ya ɗan sauƙa sosai.” Ammy ta ce: “Toh Allah ya ƙara lafiya. Campany fa? Ban ji kana magana akai ba yau. Wane irin labari kake samu daga can?” Maleekh ya buɗe ido ya dubeta, ya ɗan yi shiru kamar yana tunani. Sai ya ƙara gyara kwanciya, ya ɗan yi murmushi ya ce: “Komai lafiya. Ayyuka suna tafiya yadda ya dace. PA yana kula da komai, babu wani rikici.” Ammy ta gyaɗa kai cike da gamsuwa ta ce: “Toh madallah. Kar ka damu da komai sai lafiyar ka. Ni dai har yanzu bana jin daɗin ganin waccan yarinyar (Amal) tana zagaye ofis ɗinka. Amma dai idan har kana bukatar hakan, zan tsaya a gefe tunda Doctor ya ce a bar ka cikin natsuwa.” Maleekh ya ɗan saki murmushi marar sauti, zuciyarsa na motsi. Bai ce komai ba sai cewa da yayi: “Na gode Ammy… komai zai zo daidai da iznin Allah.” Ya rufe maganar da wannan, bai taɓa bari ta ji labarin abinda Amal ta fuskanta a ofishinsa ba. Ya ƙuduri aniyar boye komai daga iyayensa, saboda baya so wani ya ƙara wulakanta Amal a gabansa even da yake shi ma yana jin haushinta a zuciyarsa. Sai dai zuciyarsa ta furta a ransa: “Amal… duk da na tsane ki, bana son wani ya tauye mutuncinki.”.... _NEXT! NEXT!! NEXT!!!_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 43 to 44 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Bayan tattaunawar da yayi da Ammy, an bar shi shi kaɗai a ɗakin. Ya jingina da filo yana sauƙe ajiyar zuciya. Kalaman PA suna yawo a kunnensa: “Madam Amal ta tsayar da ma’aikata gaba ɗaya, ta nuna musu ƙarfi da izza… ta gargaɗe su cewa idan aka sake maganar ta, zata kori kowa.” Maleekh ya lumshe ido, zuciyarsa ta haɗu da soyayya da haushi. Ya tuna result ɗin Amal, ya tuna rashin gaskiyar da yake zargin ta da shi, sannan kuma sai ya tuna irin ƙarfin zuciyar da ta nuna a campany, tana kare mutuncinta da mutuncin sa kai tsaye. Hawayen takaici suka tsaya masa a ido, ya furta cikin zuciyarsa: “Amal… me yasa kika zama min tamkar dafin da nake sha kullum? Duk da ina zargin ki, ban so wani ya kalle ki a matsayin marar mutunci.” Sai ya runtse ido, yana jin ciwon zuciya da soyayya suna rikici a ransa. Amal kuwa ta dawo da mota gida, ta shiga falon. Inna na zaune tana duba TV, tana kallonta da idon da ya cika da zargi. Amal da sallama cikin ladabi ta ce: “Inna sannu da hutawa…” Inna ta kawar da kai, da dariyar raini ta ce: “Kin dawo kenan? Ko daga aiki kike, ko daga club ɗinki! Domin ai ban ga bambanci ba.” Amal ta tsaya cak tana kallonta. Ta ji kamar zuciyarta zata fashe, amma ta daure cikin nutsuwa ta ce “Inna, na dawo daga aiki ne, ina wakiltar Maleekh a campany. Ni ba ‘yar club bace.” Inna ta buga hannu a kujera cikin tsawa ta ce: “Ke da aka ɗauke ki cikin jini daga club, da likitoci suka tabbatar kin zubar da ciki… kina da bakin cewa ba ‘yar club bace? Ke ce bala’in rayuwar Maliku!” Amal ta matse hawayenta, tana girgiza kai. Sai ta taka kusa da Inna, ta ce da murya mai rauni mai cike da gaskiya: “Inna, wallahi ban taɓa bin wani namiji ba banda Maleekh. Kaddara ce kawai ta jawo abin da ya faru, amma da zuciya ta zan shaida miki ni ba ‘yar iska bace. Ni masoyiyarsa ce, shi kuma masoyina ne. Komai ya faru, Allah zai fitar da gaskiya.” Inna ta ja tsaki tare da faɗin: “Sai dai ki ci gaba da mafarki, domin Maliku yanzu ba ya son ki! Kuma bana so ki kara zancen shi a gabana.” Amal ta kalli Inna da idanuwan da suka cika da hawaye, amma ta ƙara murya da ƙarfin hali cewa: “Inna, ko da duniya ta ƙi ni, zan ci gaba da tsayawa da gaskiya. Domin soyayya tsakanina da Maleekh, ƙaddara ce. Ba wanda zai iya goge abin da aka rubuta.” Ta juya tana hawaye, ta haura sama kai tsaye ɗakinta, ta faɗi kan gado tana kuka... Bata ankara ba ta ji an turo ƙofar ɗaki da ƙarfi.. Inna ta shigo ɗakin Amal da masifa, tana huci kamar wuta.. Ta dafa bango tare da faɗin: “Ni dai wallahi Amal, baki isa ki tozarta ni ba. Ke kika jawo abin kunyar nan, yanzu za ki zo kina min gadara a gidan nan? Wacece ke a nan gidan?” Amal ta miƙe a fusace, idonta akan Inna tana zazzaro ido ta ce: “Inna kin wuce gona da iri! Me na yi miki da kike ta zagina kullum? Ko kin manta ni jikarki ce? Idan kika ci gaba da mun haka wallahi zan wurgar da ke daga wannan gidan, sai dai ki koma can Kaduna ki ci gaba da masifa a can! Wannan gidan gida na ne, da sunana a rubuce a jikin takardun gidan nan..!” Inna ta zaburo, ta kama ƙugu tana jijjiga kamar wacce zata yi dambe ta ce: “Au? Gidanki? To sai naga ‘yar iskar da zata bani umarni a gidan nan. Kina so in koma Kaduna saboda ki kawo tsinannun samarin club ɗinki gidan nan koh? To ki ji tsoron Allah Amal, bazan taɓa barin gidan nan ba wallahi, kuma zan nuna miki ni na fi ki bariki, karuwa kawai!”.. Amal ta sau murmushin takaici sannan ta ce: “Inna, na ga baki ɗauke ni a mazannin jika ba, meyasa bazaki kyale ni naji da abin da ke da mu na ba? Can ba sauƙi, nan ma ba sauƙi shin ya ku ke so nayi da raina? Ko kina so na mutu ne?..." Inna cikin ɗaga murya ta ce: "To ki mutu manaaaa, da wannan abun kunyar da kika jawo mana ai gwara mutuwar ki..." Amal ta ɗaga muryarta sosai, tana cewa: “Kafin ki ga mutuwata bari na wurgar dake tukun! Ki ji! Jarababbiyar tsohuwa kawai, kin mayar da gidannan gidan masifa! Daga yau, babu ruwanki da ni, babu ruwanki da Maleekh!” Amal ta riƙo hannun Inna da ƙarfi ta jawo ta. Inna tana ihu tana cewa: “Ki sakeni munafuka! Ke ba kya ji tsoron Allah?! Ni kike ja kamar yarinya?!” Amal bata saurare ta ba, ta ja ta har bakin ƙofa. Sai da ta ture ta waje gaba ɗaya, ta rufe ƙofa da ƙarfi “paahhhtttt!!” sannan ta saka key tana huci... Amal ta jingina da ƙofar tana huci, zuciyarta na bugawa da ƙarfi, Inna kuma tana waje tana ci gaba da tsinewa da masifa kamar zata tarwatse... Zuwa ta yi ta kwanta kib da ciki tare da lumshe ido...tana tunani har bacci ɓarawo ya ɗauke ta.. 🤦‍♀️🧞‍♀️ Amal tana zaune a kan kujerarta, biro a hannu amma gaba ɗaya zuciyarta ta tattare ne da damuwar Maleekh. Zuciyarta ta tsinke, idonta ya rinƙa lumshewa da nauyin tunani. Kwatsam krrriiiin ta ji an turo ƙofar office ɗinta a hankali. Bata san lokacin da ta ɗago kai ba, sai idonta ya sauƙa akan Maleekh!.. Sanye da fararen suit, farar riga, farin wando, farin tie duk ya haɗu tamkar mala’ika ya sauƙo. Fuskar sa cike da annuri, murmushi ya mamaye kyakkyawar fuskarsa, idanuwansa masu tsananin haske suka zuba kai tsaye cikin nata. Amal ta tsaya cak! Jikinta ya ɗauki rawa. “Ya Maleekh…” ta furta a hankali cikin ruɗani. Shi kuwa ya ɗan daga hannu alamar “zo nan”. Amal ta tsaya naƙe-naƙe kamar mai mafarki, amma ƙarshe ta miƙe, da sauri ta nufi inda yake. Da zarar ta isa ƙofar office ɗinta sai ya juyar da kai ya fita. Ita kuwa tana biye dashi a guje. Ƙafafuwansu suna ɗaukar sauti a kan tsalelakun bene suna hawa beni can sama-sama har sai da suka kai top floor na company, beni mafi tsayi wanda daga nan idan ka leƙo ƙasa za ka ga mutane kamar ƙwari. Sai da zuciyar Amal ta tsaya lokacin da ta ga inda Maleekh ya tsaya, bakin gefen building, inda babu komai sai sararin sama a samansa da kuma tsalelakun ƙasa a gaban sa. Ya juyo yana murmushi mai cike da annuri akan fuskarsa. Ya ɗaga hannayensa biyu yana buɗewa kamar yana ce mata “shigo ki faɗa jikina”. Amal ta furta cikin kuka: “Ya Maleekh… wallahi na yi kewarka… wallahi ina sonka!” Tayi gudu da karfi ta nufi inda yake domin rungume shi. Sai dai kafin hannunta ya rufe kirjinsa - battt!- ya ɓace kamar hayaki. Amal kuwa ta yi gaba! Hannayenta suna a buɗe, ƙafafunta suka zame ta faɗa cikin sararin ƙasa daga tsayin beni! Ta ware hannaye tana kukan tsoro cikin iska ta ce: “Yaaa Maleeeekh…!!!” Iskar sama na kaɗawa a kunnenta, zuciyarta ta riga ta amince cewa mutuwa ta iso. Idanunta sun kulle suna jiran ƙarshen faɗuwa... Sai kawai Amal ta farka a razane! 😱 Tana kan gadonta, jikinta na rawa, zufa ya wanke fuskarta. Numfashinta na fita da ƙyar kamar wacce ta yi tsere. Ta dafe kirjinta tana hawaye tare da faɗin: “Ya Allah… ashe mafarki ne… Ya Maleekh! Me yasa kake min haka a mafarki?…” Ta kwanta ta sake lumshe ido amma tsoron da ya mamaye ta bai bari ta sake samun nutsuwa ba... Amal tana kan gadonta amma har yanzu hawayen mafarkin na gangarowa. Hannunta na rikicewa akan kirjinta tana ji kamar zuciyarta zata tsage. Ta ce cikin rawar murya: “Ya Allah… me yasa mafarkina kullum akan Maleekh ne? Me yasa zuciyata ta kasa kwanciya sai na ganshi? Shin wannan ƙauna zata hallaka ni ne?…” Ta rufe fuska da hannuwanta, numfashinta na fita da ƙarfi. Cikin zuciyarta ta fara addu’a, tana roƙon Allah ya yaye mata wannan ƙunci. Amma ko da take addu’a, hoton Maleekh ɗin nan da murmushinsa mai ɗauke da annuri bai

Chapter 30 of 62