Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
rai. ​“Ita ta sa wutar! Tayi babban laifi! Don haka ina umartar ku da ku tafi da ita can Station! Zaman prison ya wajaba a kanta! Ku ɗauke ta!” ​Ammy cikin kuka ta ce, “Maleekh! Me kake shirin aikatawa!?” ​Maleekh ya ɗaga mata hannu, ya hana ta magana: “Mom! Abinda ya dace nayi! A tafi da ita!” ​Amal tana kuka, bakinta ya rufe, ta kasa cewa komai. Jami’an ‘yan sanda suka kama ta! ​Maleekh ya juya, ya kalli gadon da Abbah yake kwance ido a rufe. ​ “Ba shiri! Za mu canza masa asibiti! Ko ma ƙasar waje za a fita dashi! Gobe zan kai shi Hospital Ethiopia!” a cewar Maleekh. ​Ya yanke hukuncin kamawa da fitar da Abbansa daga ƙasar a cikin tsananin fushi da baƙin ciki, yana mai cewa Amal ce ta yi hakan. Ba tare da yayi bincike ba kawai hukunci ya yanke. ​Washegari da asuba, shirin Maleekh na fitar da Abbah zuwa Ethiopia ya fara. Ammy ta kasa yarda da yadda Maleekh ya yi wa Amal rashin adalci, har ya yanke mata hukunci ba tare da sauraro ba. ​Ammy cikin kuka da damuwa ta ce, “Maleekh! Zaka bar ƙasar kuma Amal tana can a tsare! Kuma ga jariranta ko wata basu yi ba da haihuwa! Ya zakayi kayi haka? Wannan ba dabi’a mai kyau bace!…” ​Maleekh ya dubi Ammy. Zuciyarsa ta cika da tunanin cin amana da kisan kai wanda ya danganta wa Amal. Cikin tsaurin fuska da yanke hukunci ya ce, “Ba daɗe wa zanyi ba a can. Idan na kaishi, akwai manyan kwararrun likitoci a can da zasu kula dashi. Kwana biyu kawai zanyi na dawo. Kafin na tafi zan aiko wa yaran da madara mai kyau na jarirai. Ita kuma zata cigaba da zama a can cell!” ​Ammy ta sake faɗin damuwarta game da tagwayen da suke buƙatar nono na uwa. ​“Amma ai uwarsu tana raye, kuma suna da nono! Sai a rinƙa basu madara? Sun yi ƙanƙanta sosai!…” ​Maleekh ya girgiza kai, ya ƙuduri aniyar yin abin da ya yi “Kawai ki bar komai a hannu na! Kar ki damu! Amal daga Cell sai Prison na mata! Yara kuma ba yau ake haifan jarirai kuma mahaifiyarsu ta mutu ba! Zan siya musu madara mai inganci wanda zasu cigaba da sha! Innarta kuma zata dawo nan gidan saboda ta samu masu kula da ita! Ni yanzu zamu nufi Airport!” ​Ba tare da ɓata lokaci ba, Maleekh ya ɗauki Abbah cikin tsari mai kyau zuwa Filin Jirgi. An fita da Abbah a na'urar tallafin numfashi (life support), aka shiga jirgi mai zaman kansa (private jet) zuwa Hospital Ethiopia don kulawa ta musamman. ​Maleekh ya aika musu da madarar yara (Infant Formula) masu inganci da yawa don ci gaba da ciyar da tagwayen. ​Bayan Maleekh ya tafi, Inna ta dawo gidansu Maleekh kamar yadda ya umarta. ​Ammy ta tarbe ta da hannu bibbiyu.. An bata ɗaki na musamman.. ​Inna (A Zuciyarta) tana maganar cewa “Alhaji Wadata! Na san ka! Na san sirrinka! Yanzu Maleekh ya dawo, zan bashi dukkan abin da na gani a daren nan! Ba zan bari ka kuma hallaka wannan yaro marar laifi (Maleekh) ba!” ​Inna yanzu tana zaune tare da tagwayen da kannen Maleekh, tana jiran dawowar Maleekh don ta bayyana gaskiya... 🪸🪸🪸 Amal tana Station, inda aka sanya ta a cikin Cell (kurkuku na ɗan lokaci). Washegari antashi da hukunta Amal. ​ƴar Sanda cikin tsaurin fuska da baƙin ciki take faɗin “Ke! Har kina da ƙarfin hali zuwa asibiti! Ki nemi kashe mutumin kirki wanda ya ɗauke ki tamkar ɗiya! Ba zaki ga daɗi ba a hannun mu!” ​An yi wa Amal dukan tsiya! An horar da ita sosai saboda zargin kisan kai da kuma ƙona asibiti. ​Amal tana cikin azaba.. ​Alhaji Wadata ya ji labarin ƙonewar asibiti da kuma kamawar Amal a matsayin wacce ta kawo wuta. Yayi farin ciki sosai. ​Yana faɗin cewa, “Wannan shine tsari mafi sauƙi! Yanzu za a zarge ta da kisan kai da ƙonawa! Makarinta ma ya gujeta! Sun sauƙake mun aiki!” ​Ya kuma ji labarin cewa Maleekh ya tafi Ethiopia da Abbah.. Alhaji Wadata ya lura da tausayin Zayd da kuma yunkurinsa na son tona gaskiya. Ba tare da bata lokaci ba, ya sanya aka ɗaure Zayd a wani ɗaki na sirri a gidansa. A ɗakin sirri yake kallo Zayd tare da faɗin. “Ba za ka taɓa tona min asiri ba! Kai ma za ka shiga azaba har sai na gama da Maleekh da iyalansa!” Shiri na gaba Alhaji Wadata ya nemi Malaminsa (bokaye) ya bashi Laya (sihiri) don rufe bakin dukkan shaidu waɗanda za su iya tona sirrinsa. ​Malami ya bashi laya mai tsanani.... A gidansu Maleekh kuwa, Inna tana zaune ita kaɗai a ɗaki tana tunanin yanda zata gaya wa Maleekh gaskiyar lamarin.. A Zuciyarta take faɗin, “Za ni gaya wa Maleekh… Wadata ne!…” Ta yi ƙoƙarin buɗe baki “Mmm… mmm…” Bakinta ya kasa motsi!.. Bayan kwana biyu da dawowar Maleekh daga Ethiopia, ya yi amfani da ƙarfin ikonsa da kuma tasirinsa a cikin siyasa don shure ƙarar da ake tuhumar Abbansa da kisan kai. An rufe komai. ​Bayan ya huta a gida ya rungumi jariransa (waɗanda ke sanya shi cikin nishaɗi), ya nufi Station don ganin Amal... Bayan ya isa. ​Maleekh ya tsaya a bakin Cell, tare da ƴan sanda biyu a gefensa. Yana ganin Amal a ɗaure, ga tabon dukan da aka mata a fuska da jiki.. ​Maleekh cikin sanyin murya a tsanake ya ce, “Kun yi mata rauni sosai, hakan kuskure ne saboda macece! Amma abinda ta shuka, shi take girbewa! Ku ɗaga mata ƙafa saboda uwar ƴaƴana ce!” ​ƴan Sanda suka ce “Okay Sir, za a kiyaye.” ​Maleekh ya tambayi ko ta ci abinci, kuma aka ce A’a. Ya umarce su da su bata abinci nan take. ​Islam da Arfat sun zo tare da shi, riƙe da tagwaye. Sun tsaya a nesa don Amal ta ga jariranta daga nesa ba tare da an bata su ba. ​Ƴar sanda ta shiga ta ajiye mata kular abinci a ƙasa. Abincin shine farar shinkafa da mai da dakakken yaji, sai tattasai da attaruhu a roba daban mai zafi sosai. ​Amal tana zaune, ta dubi abincin sosai. Ta ɗago tana kallon Maleekh da rinannun idanuwanta (cike da azaba da jarumta). ​Cikin rashin kula da abincin, Amal ta miƙa hannu, ta ɗauki dogon tattasai mai tsananin zafi, ta kai bakinta tana taunawa a hankali! Sannan ta ɗauki attaruhu (hot chili pepper) tana ci. ​Islam da Arfat sun zaro ido suna kallonta! Ƴan sanda sun shiga mamaki! Duk abincin da aka bata tun kwana bakwai bata ci, amma yanzu tana cin kayan miya masu tsananin zafi! ​Ko zafi bata ji! Haka take cinye su, idonta akan Maleekh! ​Maleekh ya fahimci cewa Amal tana aiko masa da saƙon cewa tana da ƙarfin hali da jarumta, ba za ta rushe ba! ​Maleekh Ya yi murmushi a hankali sannan ya furta, “Dakyau! Jaruma! Irin wannan jarumtar ai ko nima zan iya!…” ​Ya kalli ɗaya daga cikin ƴan sanda: ​“Ku miƙo mun tattasan da attaruhun nan! Nima na kwada jarumtar!” ​Aka miƙo masa tattasai da attaruhu a hannu. Yana kallon ƙwayar idanun Amal da sukayi jawur, ya sa attaruhu a bakinsa yana taunawa! ​Da hanzari ya tofar da na bakinsa! Ya fara shishshitu! ​Cikin ruɗewa da gigicewa yake faɗin “Ku ban ruwa! Ku ban ruwa! Kuyi sauri!…” ​Aka bashi bottle na ruwan sanyi. Ya kafa kansa ya fara gwangwada! Sai da ya ga bayan bottle ɗin, duk da haka bai daina shishshutun ba! Sai zaro harshe yake kamar tsohon maye! ​Arfat tana riƙe da Lihaam, sai kunshe dariya take tana kallon Maleekh! Islam kuwa ta ƙafe idonta akan Amal saboda mamaki da ƙarfin hali irin nata! ​Amal ko kibta ido bata yi. Ta cinye tattasai da attaruhun nan tasss! ​A hankali, cikin tsokana ta furta, “Akwai ƙari ne?…” ​Duk zaro ido suka yi suna kallonta! Ko irin shishshitun da Maleekh ya yi bata yi ba! ​Maleekh ya jijina kai cikin mamaki da girmamawa ga jarumtar Amal (amma ya ci gaba da nuna hukunci a zahiri). ​Ya miƙa wa ƴan sanda takardar Kotu na tura Amal zuwa Prison (gidan yari) na mata, inda zata cigaba da zama acan. ​Daga nan, suka juya suka tafi, suka bar Amal a Cell... Bayan Maleekh ya dawo, ya yi amfani da ƙarfin ikonsa don sanyaya al’amarin zargin kisan kai a kan Abbah. A hukumance, an rufe ƙarar kuma Abbah ba ya cikin haɗari na kamawa a Kotu. ​A gida, Inna tana ƙoƙari sosai don gaya wa Maleekh gaskiya. Sau biyar kenan tana tare shi, amma sihirin Alhaji Wadata ya hana ta. ​Yau ma, kamar kullum, ta tsayar da shi zai wuce part ɗinsa. ​“Daman akwai maganar da nake so gaya maka dangane da wannan al’amarin…” ​Maleekh cike da mamaki ya ce, “Al’amarin ai biyu ne Inna. Akwai na Abbana, sannan akwai na Amal.” ​Inna ta ce, “Akan na Abbanka…” ​Ya ce, “To, ina jinki.” ​Inna ta tsaya, ta yi shiru. Ta kasa furta komai! ​Bayan dogon shiru ta ce. “Shikenam ma, ni na manta abinda zan ce ma…” ​Maleekh ya girgiza kai. Ya lura cewa sau biyar kenan tana masa haka. Ya rasa gane dalilin wannan mantuwar kwatsam.. ​Ya kalli Islam sannan ya ce, “Ku kawo mun yarana, ina son ganinsu.” ​Daga nan ya haura sama, inda ya kwanta a kan gadonsa. Islam da Arfat suka shigo da tagwaye, suka ɗora masa su a faffadan kirjinsa. Ya rungume su, yana lumshe ido cikin farin ciki. ​Bayan mintuna kaɗan, Farha ta shigo gidan da sallama. Bayan ta gaisa da Inna da Ammy, ta nufi ɗakin Maleekh. Ta danna ƙararrawa, jin shiru yasa ta murɗa handle ta shiga.. Tana shiga ta sake masa knocking a bedroom part ɗinsa, a hankali ya furta "come in.." Ta same shi kwance da jarirai a saman kirjinsa. ​Farha ta zauna a kujerar gefen gado. ​Idonsa a lumshe ya furta “Ya akayi?” ​Farha ta fara magana, tana bayyana nadamarta akan hukuncinsa.. ​“A lokacin da ka shigar da ni ƙara… nayi zaton ni kawai ka tsana… amma yanzu na tabbatar da cewa kai ɗin na Musamman ne, zaka iya ɗaukan hukunci akan kowa. Ban tabbatar ba sai da ka aiwatar akan masoyiyarka… amma abinda nake gani yanzu shine sam bai dace kayi mata wannan hukunci ba ko don saboda yaranta…” ​Maleekh ya dube ta sannan ya ce, “Shin ke bakya tunanin zakiyi aure ne? Idan kika haihu yaranki suka girma bazasu san cewa kin taɓa zaman prison ba? Ki fara duban kanki kafin ki dubeta!..." Farha ta ce, "Amma mutane sai magana suke..." "Bana duban mutane idan zan aiwatar da abinda ya dace, domin ba tsoron kowa nake ba a cikin mutane!” ​Sannan ya ƙara furta “Shin me ya kawo ki?” ​Farha ta ce akwai wata magana da ta kawo ta. “Kwana kusan uku kina ƙirana a kan zaki gaya mun wata magana amma kin kasa. Kina son raina mun wayo ne?” ​Farha ta girgiza kai ta ce, “Hakan yasa na tako nazo da kaina.” ​Ya ce, “Ina jinki.” ​Ta fara bayyana cewa, “Zargin kisa da ake yi wa Abbah ba gaskiya bane… akwai wata rana da na fara fitowa a prison har ka kawo ni gida… to, to, to, to, to, tooo, tooooo, toooo, toooo…” ​Maleekh ya katse ta saboda tsananin shirme da take yi. ​“To, to, to, ya isa haka! Bana son shirme fa!” ​Farha ta fara hawaye. Ta faɗi cewa ta manta abin da zata furta. ​Maleekh ya kalle ta, sai kuma Inna ta faɗo masa a rai! Itana tana son gaya masa magana amma sai mantuwa ya biyo baya, yana tunanin duk maganar ɗaya ce indai hakane...! ​A hankali ya furta “Kina nufin kice kinsan waɗanda suka shirya makircin nan? Kuma daga gidanku? To waye?…” ​Farha ta tsaya tana kallonsa, ta kasa cewa komai! ​ “It’s okay! Zan binciko komai da kaina! Tashi ki tafi!” ​Farha ta miƙe, jiki a sanyaye. Tana shirin barin ɗakin, sai ga wata kalma ta bugi dodôn kunnenta: ​ “Za ki aure ni?…” ​Kirjinta ya fara bugawa da ƙarfi! Ta juyo baya ido a zare tana kallonsa! ​Ya ƙara maimaitawa “Ki shirya! Next week ɗaurin aure! That’s it!” ​Farha ta sake baki tana kallonsa. Bata yi tsammanin haka ba! ​Maleekh ya kwantar da yaran a hankali. Ya miƙe, ya iso wurinta, ya rungume ta sosai. ​“Idan kinje, ki sanar wa iyayenki cewa zan kawo sadakin ki!” Ya ƙarasa yana shafa mata sumar gashi ta cikin gyalenta... ​Daga nan ya sake ta. Farha ta fice daga ɗakin tana mamakinsa! Bayan kwana biyu. ​A safiyar yau da za a wuce da Amal zuwa Prison, Maleekh ya shirya tsaf domin dashi za’a kaita. Kafin ya fita, ya shiga ɗakin Inna don yi mata bankwana da kuma bayyana ra’ayinsa. ​Maleekh ya zauna a gefen Inna bayan ya gaishe ta.. “Inna, kiyi haƙuri akan abin da nayi na hukunta Amal. Na san ranki bazai yi daɗi ba, amma nima ba yanda zan yi, ba’a son raina nayi hakan ba. Nayi hakan ne domin na samu salama. Zanyi bincike na yanda ya dace a tsare. Zaman ta zai iya bani cikass (clues opportunity to find the truth).” ​Inna ta girgiza kai, tana hawaye ta ce, “Baka yi laifi ba Maliku, abinda kayi daidai ne. Ta cancanci hakan! Wanda yake shirin aiwatar da kisan kai ai hukuncinsa shine gidan yari. Ko kaɗan Amatu ta rasa imaninta! Bata cancanci ta zama uwar ƴaƴanka ba!” ​Maleekh ya jinjina kai, sannan ya tashi ya fice... ​Maleekh ya nufi Station. Ya yi parking motarsa a bakin station, ya fito ya jingina bayansa a jikin motar, yana facing Station. Ya rufe idonsa da baƙin glasses ɗinsa. ​Bayan wasu mintuna, ƴan sanda suka fito da Amal, tana tafiyar wahala saboda dawa da dukan da aka yi mata. Aka kaita gaban Maleekh. ƴan sanda suka juya.. ​Maleekh ya ƙare ta da kallo ta cikin glass. Ya fara furta mata maganganu. "I can do anything for my father, no matter who he is. My father is very important in my life. If anything had happened to him at that time, I would have shot your brains out because you don't know the value of elders. You don't know the value of old age, you don't know the value of the person who loves you." Ya cigaba da faɗin "Rashin hankalinki da taurin kanki da nauyin bakinki yasa sauran kaɗan na kasheki har lahira... inda ace kece asalin wacce kika kai farmaki da kin ƙare rayuwarki a gidan Prison. Sa'arki ɗaya da na gano gaskiyar lamarin...".. ​A cikin rashin sanin kowa, Maleekh ya riga ya gano gaskiyar lamarin. ​An rufe case ɗin Amal saboda an gano gaskiya ta hanyar CCTV (na'urar tsaro) da ke wajen asibitin. An ga ainihin mutumin da ya wurga jarkar petur a gabanta. An kama shi! Yana tsare yanzu haka, amma ya kasa bayyanar da wanda ya turo shi. ​ ​Maleekh ya riƙo hannunta da ƙarfi, ya buɗe murfin motar shi ya wurgata ciki sannan ya rufe. ​Shima ya zagaya ya shiga. Ya ja motar a ɗari ya bar wurin. Maleekh ya sanya mic ɗin sirri a gashin Farha lokacin da ya rungume ta a ɗakinsa. Ta hanyar Bluetooth, ya saurari dukan maganganun da suka faru tsakanin Farha da iyayenta (Alhaji Wadata da Matarsa). ​Abubuwan da Maleekh Ya Ji. Ya tabbatar da cewa Alhaji Wadata ne ya tura ƴan daban don sa wuta a asibiti. ​Ya ji maganganu da ke nuna cewa Alhaji Wadata ne ainihin wanda ya kashe iyayen Amal tare da Alhaji Gusau, kuma sun yi wa Abbansa sharri ta hanyar bidiyo. Ya tabbatar da cewa Alhaji Wadata ya kulle ɗansa Zayd domin kada ya tona asiri.. ​Ya ji batun layar da Alhaji Wadata ya yi amfani da ita don rufe bakin shaidu.. ​A cikin kwana biyu, Maleekh ya san ainihin gaskiya da kuma makiyansa!... ​A cikin mota, Maleekh ya sanar da Amal hukuncinsa mai zafi. “Zanyi aure.” ​Amal ta razana, ta juyo tana kallonsa. Cikin kuka da azaba ta furta: ​“Amma kafin kayi ka tabbatar ka sake ni! Domin ba zan iya zama dakai da wata ba!…” ​Maleekh ya furta. “Whatever you said… Farha zan aura. Next week!” ​Amal ta ja wani irin numfashi mai zafi. Zuciyarta ta buga! Lokaci guda ta sume a kujerar motar. ​Maleekh kallo ɗaya yayi mata, ya cigaba da jan motarsa ba tare da ya damu ba. Ya sani cewa zai farfaɗo da ita a lokacin da ya dace... Kai tsaye gidansu Farha ya nufa. Amal ta farfaɗo a hanya, tana kuka mai zafi ba tare da ta san inda za su ba. Suna isa ƙofar gidan Alhaji Wadata, suka tsaya. ​Ya kalleta, cikin tsanaki ya ce, “Ki share hawayenki! Domin zamu shiga gidan sirikaina! Kar su fahimci kishi ne yasa ki kuka!” ​Amal ta wurga masa wani irin harara mai zafi. ​Ya sauƙa, sannan ya ce “Ta sauƙo!” ​Amal ta nuna ba za ta sauko ba. ​Ya ce, “Kinga irin taurin kan naki ko? Oya come out. Fito!” ​Ta fito jiki a sanyaye. Maigadin gidan ya buɗe musu. Suna shiga babban falo, suka tarar da Alhaji Wadata, Matarsa, da Farha suna breakfast (ƙarfe 12 na rana). ​Farha ta miƙe da tsananin mamaki da firgici ganin Amal a tare da Maleekh! ​Maleekh ya riƙo hannun Amal, ya zaunar da ita a kusa dashi. Amal tana harararsa ciki fushi... ​Ya ɗaga musu hannu da cewa. “Yaa ku zo mana! Ko bakuyi farin cikin ganina bane?” ​Suka nufo falon da mamaki da damuwa lokaci guda. Maleekh yana daga zaune ya furta. “Ina wuni Uncle, duk da naga yanzu kuke breakfast! Kuma nasan kunyi mamakin ganina duk da na sanar da yarinyarku cewa zan zo.” Ya kalli Farha ya ce “Ko ba haka bane?” ​Farha ta jinjina kai tare da fad'in “Hakane.” ​Amal ta wurga mata wani irin harara, tare da jan dogon tsaki! ​Maleekh ya kalle ta ya ce, “Ya haka? Baki san gidan sirikai na bane? Ke ba daga cell kika fito ba?!” ​Ya maida kallonsa kan Alhaji Wadata. ​ “Daman na wakilci Mahaifina zuwa neman aure na, don haka nazo nemawa kaina auren ƴarku Farha! Ko dan Uncle ai kaima mai nema mun aure ne, kaga tinda ƴar gida za’ayi, shikenam faɗuwa yazo dai-dai da zama!” ​Alhaji Wadata ya ce, “Ita matar takan ta amince ka auri Farha ne?” ​Maleekh ya ce. “Matata ai ni nake auranta ba ita take aure na ba! Don haka yasa ta rakoni zuwa neman aure yafi nazo ni kaɗai. Ma’ana itace wakiliya ta!” Ya kalle ta tare da rungumarta “Ko ba haka ba jarumata?”... "Aww! Ashe dai ke zaki nema mun aure nake ta ɓaɓatu, yanzu abin da zaki ce shine kice 'Ni Amatu, na zo nema wa mijina Maleekh auren ƴarku Farha..." Wani irin wurga masa kallo tayi, idonta har yayi jawur tana kallonsa.. Shima itan yake kallo ya ce "zaki faɗa ko a'a? ..." Haɗe gira tayi kai a sunkuye ta ce. "Ni Amatu, nazo nema wa mijina auren ɗiyarku Farha..." Maleekh ya dube ta ya ce. "Ahhhh! Haka ake neman aure daman? Fuska a murtuke? Ai za ki sa su kore mu kuma..." Yasa hannu ya ɗago da habarta ya ce "ki kalle su ki nema mun aure malama..." Wani irin yawu ta haɗiya sannan ta ɗan sake fuska ta ce, "Ni Amatu, na zo nema wa mijina Maleekh auren ɗiyarku Farha..." Maleekh yayi murmushi yana duban Alhaji Wadata sannan ya ce "To Alhaji gare ka fa, ana nema mun aure a wurinka, ka amince kawai..." Alhaji Wadata ya jinjina kai cikin ɓacin rai sannan ya ce "Shikenan na baku..." Maleekh yana dariya ya kalli Amal ya ce, "kiyi godiya mana an bamu mace..." Amal kai a sunkuye hawaye ya gama cika idon ta ce, "Mun gode..." ​Maleekh ya sa hannu ya ciro ɗamin kuɗi da zasu yi kimanin Dala miliyan 5 ($5,000,000). Ya ba Amal yana faɗin. ​“Wannan sadakin Farha ce! Ki karɓa, kije ki bawa mahaifinta! Yafi ni na bashi da hannuna, kinga ba mutunci ai. Don haka kiyi mun kara kije ki basu!” ​Amal tana turo baki kamar zata fashe da kuka, ta karɓa. Tana takawa a hankali, ta je gaban Alhaji Wadata ta tsaya tana ɗaga kai sama ta miƙa masa kuɗin... ​Alhaji Wadata ya karɓa yana kallon Maleekh. Amal kuwa ta je ta tsaya, ta kasa zama.. ​Shima Maleekh miƙewa yayi yana faɗin: ​“To mu zamu wuce.” Ya kalli Amal ya ce, “Jarumata, ni ya auren zai kasance ne? Wani rana ya kamata asa?” ​Amal ta yi wani irin jan tsaki, ta bar falon a fusace. Ta buɗe ƙofa ta fice. ​Maleekh kuwa ɗaga kafaɗa yayi ya dubi su Alhaji Wadata. ​ “Kuyi haƙuri fa kunsan halin mata, dole sai sun ɗan taɓa kishin nan. Yanzu dai bikin zai kasance ranar Asabat, sauran kwana biyar yanzu!” ​Daga nan ya fice shima. ​A mota, ya tarar da Amal zaune tana kuka. Shiga yayi yana shirin tada mota. ​Amal ta fara ɗaga murya tana kuka. “Ka cuceni Maleekh, kaci amanata wallahi, sannan ka wulakanta ni da kuma alakar dake tsakaninmu na ma’aurata... shin na cancanci kamun wannan wulakanci da cin fuska? Ai gwara ka barni na hallaka a prison akan wannan tozarcin daka mun!” ​Maleekh ya zaro ido tare da faɗin “Me kuma na miki?” ​Amal ta cigaba da faɗin “A tarihi a ina ka taɓa jin mace ta nema wa mijinta auren wata daban? Har ka ban kuɗin sadaki kace na basu? Wannan ai cin fuska ne bayan kasan inada kishi!” ​Maleekh cike da zolaya ya ce, “Au haba! Yanzu kina kishina? Ai ban san haka kike sona ba sai yanzu! Yanzu ana kishina! Ba kuma hakan zai hana a fasa auren ba!” ​Ya ja motar suka tafi, kai tsaye gida suka nufa dake unguwar Maitama... _NEXT NEXT NEXT_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 93 to 94 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Bayan sun bar gidan Alhaji Wadata, inda Maleekh ya yi amfani da Amal don wulakanta su tare da bayyana dabararsa ba tare da sun sani ba, kai tsaye suka nufi gidansu Maleekh a Maitama. ​Da suka isa gida, Amal ta fito daga motar tana kuka mai tsanani da tsananin fushi. Bayan ta shiga falo, Ammy da Inna suka tarbe su da mamaki ganin Amal a gida, ba a Prison ba. ​Amal ba ta ko kula da kowa ba. Ta tunkari Maleekh da tsawa a tsakiyar falon. ​Cikin kuka take faɗin “Maleekh! Ka yi zaton dabarunka sun yi nasara! Ka cuceni har sau biyu! Na farko da ka bar ni a cikin ƙazamar cell! Na biyu da ka yi mini wulakanci a gaban danginka! Ka ci amanar ƙaunata! Ka manta da yaranka! Me yasa za ka so ka azabtar da ni haka! Meyasa ka sa ni na je na nema maka auren wata! Ka sani cewa kai ba namijin kirki ba ne! Ni na cancanci mutuwa a Prison a kan na ga wannan cin amanar!” ​Maleekh ya tsaya cak, ya dube ta cikin tsaurin fuska. Ammy da Inna sun yi shiru cike da damuwa da rashin sanin abin da ke faruwa. ​Maleekh ya ɗauki Amal a hannunsa, ya haura da ita can saman Bedroom ɗinsa, ya rufe ƙofar da ƙarfi. ​Ya kwantar da ita a kan gado, sannan shima ya haura saman kanta yayi mata doki yana fuskantar ta. ​Ta buɗe baki zata yi magana, ya yi saurin toshe mata baki da nasa. Tana ƙoƙarin ture shi, ya haɗe hannayenta biyu ta sama ya riƙe da hannu ɗaya. Haka yake ta sumbatar ta ba kakkautawa. ​Jin yanayin ya fara ratsa jikinta ya sa ta fara lumshe ido. A hankali kamar ba zata iya ba take ɗan mayar masa da martani... A lokacin ta fara tuna zamansu a dajin mafarauta da yadda suka kasance.. ​Maleekh ya zamar da

Chapter 57 of 62