ke. Ko da me zata yi, ko da me zata faɗa… you’re the only one.”
Sai ya ji jikinta ya yi sanyi a jikinsa, tana ɗan fashewa da kuka a hankali, zuciyarta na narkewa da kalaman nasa.
Bayan shiru mai ɗaukar lokaci, Maleekh ya saki ajiyar zuciya sannan ya ɗan raba jikinsa da nata, yana kallonta cikin lumsasshen ido. Ya ce
“Come on… zo mu je falo. Kina buƙatar kwanciyar hankali, sannan kuma kina buƙatar cin abinci.”
Ya kama hannunta a tausashe ya ja ta zuwa falo, kai tsaye zuwa dinning area ɗinsa da ya jera kulolin abinci a kai. Amal tana tafiya a hankali, tana jin yadda hannunsa ke riƙe da nata tamkar kada ya sake.
Bayan suka isa, ya zame kujerar dinning ɗaya ya ja ya zaunar da ita, sannan ya zauna a gefenta. Kulolin abinci masu ƙanshi ya buɗe, ƙamshi ya gauraye wajen.
Sai ya ɗauki cokali ya zuba mata cikin faranti, yana murmushin da bai saba yi ba. Idonsa na lumshewa kamar na wanda ya shafe dare bai huta ba.
Amal tana kallon sa ta ce
“Maleekh… ka dai bari ni zan ci da kaina.”
Ya girgiza kai cikin izza da taushin murya ya ce
“No, Amal… tonight ba zan bari ki yi komai da kanki ba. Ki huta kawai, ni zan kula dake.”
Ya ɗauki spoon ɗin ya ɗebo abinci ya kai mata baki. Amal ta tsaya kallonsa, zuciyarta na rawa da wani irin zafi mai daɗi. A hankali ta buɗe baki ta karɓa.
Maleekh ya kasa cire idonsa daga fuskarta yayin da take taunawa. Hannunsa da ya riƙe spoon ɗin ya tsaya cak, yana jin tamkar lokaci ya tsaya a wurin.
Maleekh a hankali kamar yana furta a ransa ya ce
“Allah ya sani… kina da wani abu a jikinki da ke rikita ni…”
Amal ta ɗaga ido ta kalle shi, idanuwansu suka haɗu, suka tsaya suna kallon juna cikin nutsuwa.
Sai ya sake ɗaukar wani ya sake bata, yana murmushin da ya fi na baya taushi.
Amal cikin ƙanƙanin murya ta ce
“Na gode… Maleekh.”
Sai kawai ya sa hannunsa ɗaya ya dafa ƙaramar fuskarta, yana shafa gefen kumatunta mai taushi, sannan ya kai spoon ɗin gaba cikin kulawa.
Har abincin ya ƙare, suka ci cikin natsuwa. Duk da kulawar da Maleekh ya nuna mata, Amal zuciyarta na karyewa...
Maleekh ya sanar mata cewa su shiga cikin ta kwanta...
Ta san idan har ta kwana a part ɗinsa, idanun gidan gaba ɗaya za su sauƙa akan ta da wata mummunar fahimta. Amma a lokaci guda, ta kasa faɗa masa kai tsaye...
Bayan sunci abinci ya ja hannunta zuwa bedroom ɗinsa. Katafaren gadon yana shimfiɗe da blanket mai laushi, sannan ya jawo ta a hankali ya kwantar da ita..
Maleekh da saukin murya, yana kallonta daga tsaye ya ce
“Amal… ki kwantar da hankalinki. Babu wanda zai cutar dake a nan… babu wanda zan bari ya tsawata miki. Ki huta kawai.”
Ya gyara mata lulluɓa da hannunsa, har ta ji sanyin girmamawa fiye da yadda ta zata. Ya ɗan tsaya kallonta kamar zai sake magana, amma sai ya sauƙe ajiyar zuciya, ya juya..
A zuciyar Amal, soyyaya da tsoro suna rikici. Soyayyar da take jin tana ratsa zuciyarta saboda Maleekh, da kuma tsoron abin da zai biyo baya idan gidan ya sake samun labarin kasancewar ta a ɗakinsa.
Maleekh kuwa fita daga bedroom ɗin yayi ya nufi falonsa. Sofas ɗin falon ya shimfiɗa blanket, ya kwanta yana kallon ceiling ɗin falon..
Zuciyarsa cike da tunanin abin da ya ji a lokacin da ya rungume Amal, yadda numfashinta ya rikita shi, yadda idanunta suka ja shi tamkar ruhi. Amma duk da haka, bai bari ya kauce daga burinsa ba. A zuciyarsa yana nan da niyyar fansar da zai ɗauka akan Amal, duk da cewa wani sabon yanayi na soyayya yana rarrafe shi ba tare da saninsa ba.
Amal ta juyar da kanta a kan gadon, tana kallon hasken ɗakin da ya rage a kunne. Ta zuba ido a jikin kofar bedroom ɗin da Maleekh ya fita, zuciyarta na ta faman bugawa.
A ranta take faɗin
“Allah ka kare ni daga wannan soyayyar da zan iya rasa rayuwata a dalilinta…”
Sai ta runtse ido cikin damuwa, tana jin ƙamshinsa ya gauraye har cikin gadon da take kwance.
Amal tana kwance a kan katafaren gadon Maleekh, zuciyarta ta kasa samun nutsuwa. Sai ta rufe idanu tana ƙoƙarin yin bacci, amma tunanin ya fi karfin zuciyarta.
A zuciyarta kalmomin da Maleekh ya faɗa mata na ci gaba da maimaituwa:
“Ki kwantar da hankalinki… babu wanda zai cutar dake a nan.”
Sai ta sau ƙanƙanin murmushi mai ɗaci.
“Taya zan kwantar da hankali, alhalin idanu da yawa na kallona da ƙiyayya? Kuma ina jin tsananin ƙaunarsa tana ƙara ɗaure mun zuciya…”
Ta jawo pillow ta rungume shi kamar shi ne Maleekh ɗin, tana jin daɗin ƙamshin turarensa da ya gauraye gadon. Sai wani irin shauƙi ya taso mata, da wata shakka mai haɗawa da tsoro.
Lokaci guda bacci mai nauyi ya ɗauke ta, sai kuma ta fara mafarki...
mafarkin kanta a matsayin matar auren Maleekh, tana tafiya da shi cikin taro cikin farin ciki, kowa yana kallonsu da girmamawa. Tana sanye cikin fararen kaya na Aure, Maleekh kuma yana riƙe da hannunta, yana nuna ta ga kowa a matsayin “matata”. Ta ji daɗi fiye da kowane lokaci.
Amma kafin ta gama jin daɗin mafarkin, sai hoto ya sauya, Ammy da Farha sun shigo cikin mafarkin, suna tura ta daga jikin Maleekh, suna ƙiran ta “wawiya, matsiyaciya, ƴar tasha da ba ta cancanci zama matar mai daraja ba.” Haka suka riƙa caccakarta, suna dariya, suna ƙasƙantar da ita. A lokacin ta farka da tsananin firgici, tana jin hawayenta na zubo mata ba tare da saninta ba.
Sai ta lumshe ido ta sake yin wani irin mafarki. A wannan karon, ta ga Maleekh ya rungume ta sosai, yana shaƙar ƙamshinta, yana furta kalmomi da suka daɗe suna ɓuya a zuciyarta:
“Amal… kin zama nawa gaba ɗaya. Babu wanda zai rabani dake.”
Sai numfashinta ya rikice har cikin baccinta. Ta miƙe a hankali ta zauna akan gadon, ta dafe kirjinta, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa kamar zai tsage mata ƙirji.
Amal a ranta ta ce
“Ko wannan soyayyar zata hallaka ni… amma wallahi ba zan iya tserewa daga gare shi ba. Kamar an ɗaure ni da Maleekh tamkar igiyar da ba zata taɓa yankewa ba.”
Sai ta sake kwanciya, tana rufe fuska da bargo, tana jin kuka da dariya suna haɗuwa mata lokaci guda.
A falon waje kuwa, Maleekh ya kwanta amma bacci ya gagare shi. Duk da cewa ya ɗaura kan fansa, yana jin wani sashi na zuciyarsa na tura shi ga ƙaunar Amal fiye da kowane lokaci.
Ƙarar ƙiran sallar asuba ta ne ya daki dodon kunnensa, sautin muryar mai ƙiran sallah yana ratsa zuciya cikin nutsuwa.
Maleekh ne ya fara tashi, ya buɗe idonsa a hankali yana kallon hasken fitilar ɗakin da bai mutu gaba ɗaya ba. Ya miƙe daga kan sofas ɗin falonsa, ya nufi bedroom ɗinsa domin duban Amal.
Da ya buɗe ƙofar, sai ya ganta a kwance, idonta a lumshe kamar wacce bacci ya yi nisa. Amma a zahiri ba bacci take ba tana jin shigowarsa sosai, zuciyarta kuwa haka yake tsalle-tsalle tamkar zata ƙwace daga kirjinta.
Maleekh bai nuna ya gane hakan ba, sai kawai ya wuce kai tsaye cikin bathroom domin ɗauro alwala. Murmushin ƙaramin ƙarfi ne ya bayyana a fuskarsa, wanda shi kaɗai yasan ma’anarsa.
Bayan ƴan mintuna ya fito, tare da zura farar jallabiyarsa, ya matsa kusa da Amal, ya bubbuga kanta a hankali da tafin hannunsa cikin natsuwa.
“Ki tashi, lokaci yayi na yin sallah.”
Amal ta buɗe idonta a hankali, ta ɗaga kanta daga kan pillow tana kallonsa. Ba tare da wata magana ba ta miƙe, ta shiga bathroom don yin alwala. Ita kanta zuciyarta ta cika da mamaki tausayin irin nutsuwar da ta gani a fuskar Maleekh lokacin da yake cikin fararen kaya ya tsunduma mata a rai sosai.
Shi kuwa, bayan ya kammala shirinsa, ya fice gaba ɗaya daga part ɗinsa. Kai tsaye masallaci ya nufa tare da wasu daga cikin maza masu aiki a gidan.
Amal ta fito daga bathroom ɗin, ta shimfiɗa dadduma a tsakiyar bedroom. Ta tsai da sallah, zuciyarta cike da nauyi da addu’o’i. Duk da yanayin da take ciki, ta ji sallar ta mata daɗi sosai, zuciyarta ta ji wani irin sauƙi kamar an wanke mata damuwa da tsoron da ya rufe ta tun jiya.
Da ta idar, ta zauna akan daddumar tana jera tasbihi. Numfashinta ya sauya zuwa na kwanciyar hankali. Sai dai duk da haka, a zuciyarta tana maimaita addu’a guda ɗaya:
“Ya Allah, idan soyayyarsa alheri ne gare ni, ka daɗa mana kusanci. Idan kuwa sharri ne, ka raba ni da shi cikin sauƙi kafin zuciyata ta hallaka da ƙauna.”
Bayan an idar da sallah a masallaci, Maleekh ya dawo cikin natsuwa...kafin ya haura part ɗinsa sai da ya bi da ɗakin Ammy ya yi mata knock kamar yandq ya saba kullum, yakan je ya tashe ta idan Abbansu baya nan, koda kuwa ta tashi, bayan ta buɗe sai da ya durƙusa sannan ya gaisheta kamar kullum, Ammy a sama sama ta amsa masa sannan ta juya ba tare da ta ce mishi komai ba, Amal ganin ba haka Ammy take masa ba idan yazo da asuba yasa hankalinsa tashi, amma haka ya daure ya bar part ɗinta, sai da yabi ɗakin ƙannensa sannan ya tayar dasu suma, sannan ya sanar musu akan su je ɗakin Farha su tashe ta itama... daga nan ya nufi part ɗinsa...
Bayan ya shi ga falonsa kai tsaye buɗe ƙofar bedroom ɗinsa yayi, sai idonsa ya sauƙa akan Amal da take zaune har yanzu a kan daddumar sallah.. hannunta kuma na riƙe da sibha tana jera tasbihi cikin kwanciyar hankali.
Ya tsaya cak yana kallonta. A zuciyarsa wani abu ya motsa, ba wai ƙauna ba ce kai tsaye, amma akwai wani irin nutsuwa da ya gani a cikin yanayinta da ya ɗan ɗaga masa hankali.
Amal kuwa, da ta lura da shigowarsa, ta ɗan saki murmushi, ta ajiye sibha a gefe sannan ta ce cikin muryar kasaita.
“Ina kwana, fatan antashi lafiya..”
Maleekh ya ƙaraso a hankali, ya tsuguna a gabanta tare da faɗin
“Lafiya klau Alhamdulillah. Amma wannan nutsuwar da nake gani a fuskarki, yau kin bambanta. Kin fi jiya kwanciyar hankali.”
Amal ta ɗan sunkuyar da kanta, tana wasa da yatsun hannunta a kan dadduma.
“Ka san dalili? Addu’a ce ta ba ni wannan sauƙin zuciya. Na roƙi Allah ya yanke hukuncin da ya fi alheri a tsakaninmu.”
Kalmar “a tsakaninmu” ta ɗauki zuciyar Maleekh. Ya danne murmushin gefen baki da yazo masa, ya zauna kusa da ita, yana ɗaga gira yana dubanta. Ya ce
“To me kike nufa da wannan addu’ar? Kina son ki tabbatar da soyayyata ce alheri gare ki ne, ko kina addu’ar Allah ya cire ni a zuciyarki gaba ɗaya?”
Amal ta ɗan yi shiru, sannan ta ce cikin nutsuwa:
“Na barwa Allah komai. Ni dai na fi ƙarfi wajen sanin wanda ya fi dacewa da ni. Amma ka sani Maleekh, soyayya ba abin wasa ba ce. Bata wuce zuciya ba, amma zata iya ruguza zuciya idan ta tafi kan hanya marar kyau.”
Maleekh ya ɗan jinjina kai, yana ɗaga hannunsa ya shafi gashin kansa cikin yanayin mai nazari. A zuciyarsa kuwa ya yi dariya, yana cewa:
“Ki kwantar da hankalinki Amal. Wutar da na fara kunna miki ba zata mutu ba. Sai na tabbatar kin kamu gaba ɗaya kafin wasan ya fara.”
Amma a fili ya nuna mata kulawa, ya ce:
“Na fahimta. Amma kin san wani abu? Bana son ki yi tunani mai wahalar da ke. Duk wani abu da kike ji, ki faɗa mun kai tsaye. Ni ina tare da ke.”
Ya miƙa mata hannu kamar yana son ya ɗaga ta daga kan daddumar.
“Taso, ki je ki ɗan kwanta. Kin yi salla, kin yi tasbihi, yanzu lokaci ne na hutu kafin kowa a gidan ya farka...”
Amal ta kalle shi na ɗan lokaci, zuciyarta tana tsalle, sannan ta miƙa hannu ta miƙe tare da shi. Har lokacin ta kasa fahimtar dalilin da yasa idan tana kusa da Maleekh take rasa ƙarfin taurin zuciyarta gaba ɗaya.
Knocking mai ƙarfi aka fara yi a ƙofar part ɗin Maleekh, har Amal ta firgita tana kallon hanyar ƙofar.
Maleekh ya fito daga bedroom ɗinsa cikin nutsuwa, ya nufi ƙofar falon ya buɗe, sai ga Islam tsaye fuskarta ɗauke da alamar damuwa.
Islam ta rusuna da ladabi, tana cewa:
“Yaya, Ammy na kiranka… kai da Amal… a babban falo.”
Maleekh ya ɗan taƙaita fuska ya ce:
“Lafiya kuwa da sassafen nan take ƙiran mu?…”
Islam ta ɗan kame baki kafin ta ce cikin siririyar murya:
“Ni ma ban san menene ba, amma naga kamar ranta a ɓace yake… bana wasa ba.”
Maleekh ya yi ɗan murmushi yana girgiza kai:
“Ita ai koda yaushe cikin ɓacin rai take. Kije kice muna zuwa.”
Islam ta jinjina kai ta juya ta tafi.
Da ƙyar Maleekh ya shawo kan Amal suka fito daga part ɗinsa. Kamar yadda ake tafiya zuwa kotu haka zuciyar Amal ke bugawa, ita kanta bata san me zata fuskanta ba...tsoron fuskantar su take, tana tunanin yau dole tabar gidan nan koda Maleekh baya so, domin a takure take, kuma sam bai dace ta zauna a gidansu ba kuma haka ma a ɗakin sa, hakan yasa take jin kunyar fuskantar mahaifiyarsa..
Da suka shigo babban falon gidan, suka tarar da Ammy zaune kan babban kujerar ta daidai tsakiyar falo, fuskarta ta cika da ɓacin rai. Farha tana gefenta cikin shegen kishi, yayin da Arfat ke jingine da kujera tana taɗa nails ɗinta, Islam kuma tana gefen su cikin natsuwa...
Amal tana isa ta durƙusa ta ce "ina kwana Mama..."
Ammy a fusace ta juyo tana mata wani irin kallo sannan ta ce
"Da ban kwana ba zaki ganni ne? wato ke marar kunya iskancin nakin har ya kai ki kwana a ɗakin sa? idan aka ce miki gantalalliya yanzu sai kiji haushi ko? To bari kiji baza kizo ki koya wa ɗana iskanci ba, yarona baya neman mata, yau ne na farko da yarona ya kusanci mace, ɗana bai taɓa aikata zina ba sai yau ata sanadiyyar ki..."
A ruɗe Amal ta ɗago tana kallonta ƙirjinta na wani irin bugawa da ƙarfi, bata san lokacin da ta furta
"INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN..."
Amal ta fashe da kuka tana faɗin
"Wallahi ba haka bane, kar kuyi irin wannan mummunan zargi a kaina, wallahi babu abinda ya faru..."
Ammy ta darara mata tsawa tare da faɗin
"Yi mun shiru karuwar banza, gantalalliya marar tarbiyya, ƴar tasha, kenan haka iyayenki suka ɗora ki akan wannan turba? cewa ki rinƙa bin saurayi yanda yake har kina kwana a ɗakinsa? tirrr da halin ki, wannan sam rashin kunya ne da tarbiyya, alamar ke jahila ce, Allah ya kiyaye na bar ɗana ya Aure ki, ban san maza nawa kika rabar wa kanki ba, haka kawai bazaki zo ki dasa wa ɗana cutar da bazai taɓa warkewa ba sai dai mutuwa, ɗana namiji ɗaya a duniya, wannan ya nuna cewa haka iyayenki suke ba tarbiyya balle su baki..."
Amal tana kuka ta ce.
"Kiyi haƙuri Mama iyayena suna kabari, basa raye..."
Ammy ta ce
"Au saboda basa raye sai akace ki rinƙa jawo musu zagi a kabari? Haka ya kamata ki saka musu? mai makon ki zauna ki nutsu kiyita musu addu'a sai ki fake da bin maza? Ke wata iriyar shashasha ne?..."
Amal ta ce
"Mama ki yi h....."
Ammy ta katseta da cewa.
"Kada ki sake ƙirana da Mama, domin ban haifi ƴar tasha ba kuma insha Allahu bazan taɓa haifan gantalallu kamar ke ba..."
Amal ta ce
"Yau zan tafi..."
Ammy ta ce
"Kada ma ki tafi kiga rashin mutuncin da zan miki, wallahi sawa zanyi karnukan gidan nan suyi fata-fata da naman jikinki, ba yau ba yanzu ma zaki bar gidan nan dan kutumar ubanki..."
Maleekh gaba ɗaya bai ji daɗin abinda Ammy tayi wa Amal ba...
Ya kalli Ammy sannan ya ce
"Mom laifi nane dana kawo ta..."
Ammy ta wurga masa hararar da yasa ya dakata..
Sannan ta ce.
"Ita kuma mahaukaciya ce da ta biyoka koh? ko kwaya ka bata ne ka kawo ta gidan nan ba tare da saninta ba?..."
Maleekh bai ma zauna ba yana tsaye a tsakiyar falon, Amal kuwa tana durƙushe a gefe kusa da shi tana kuka..
Ammy ce ta kuma yin magana tana kallon Maleekh ta ce
“Yanzu inaso ka zaɓa, Maleekh. Ni ko wannan yarinyar? Domin a yanzu nake so tabar gidan nan, ba zan lamunta a cigaba da zama a nan ba!”
Kalmar ta ratsa falon gaba ɗaya, ta cika kunne da nauyin da ya tsaya cak. Amal sai da jikinta ya ɗauki rawa, zuciyarta ta shiga bugu kamar ana buga ganga.
Hankalin Maleekh ya tashi matuƙa, duk da irin taurin zuciyar da yake da shi, wannan maganar Ammy ta bambanta da sauran kwanakin. Ya san halin mahaifiyarsa tana da ƙarfin mulki a gidan, kuma idan ta ɗauki mataki, lallai zai zame masa babban ƙalubale...
Ya yi ƙoƙarin buɗe baki cikin ladabi, ya fara cewa:
“Ammy ki kwantar da hankalinki, zan—”
Ammy tayi saurin katse shi da tsawa, ta ɗaga hannu tana huci:
“Ba lallashi nake so ba! Ina jiranka yanzu, ni da na haife ka, na kuma raine ka, inaso ka zaɓa ni… ko wannan matsiyaciyar yarinya da kuka haɗu a titi!”
Kalmar “haɗuwar titi” ta buga zuciyar Amal da ƙarfi, ta sunkuyar da kai hawaye na zubo mata....
Maleekh ya tsu'ke baki ya tsaya kamar gunki, ya kasa amsawa nan take. Fushin Ammy ya ƙara zafi, idanunta har sun canza launi tsabar ɓacin rai...
Maleekh ya jinjina kai cikin ladabi kamar ɗan da bai saba yin gardama da iyayensa ba, sai dai a zuciyarsa akwai tsananin ɓacin rai. Ya furta cikin sanyayyen murya..
"Shikenan zata tafi a yau, kar ki damu Mom… bana so na cigaba da ganin ɓacin ranki akaina. Idan hakan zai kawo miki nutsuwa, to na amince. Amma kiyi haƙuri, bana jin daɗin ganin ki cikin wannan yanayin."
A wannan lokacin zuciyar Farha ta cika da farin ciki, har wani ƙaramin murmushi ta saki tana jin nasara.
Sai ya juyo ya kalli Amal, idonsa ya cika da wani irin abu mai wuyar fassara, ƙauna da tsananin tausayinta a lokaci guda. Kamar yana so ya furta kalmomin da zuciyarsa ke ɓoyewa, amma sai ya jure ya maida numfashinsa.
Ya kama hannunta a hankali, ya ɗago ta muryarsa na rawa ya furta.
"Mu je, Amal. Mu shirya kayanki… bana son na ƙara ganin mahaifiyata cikin ƙunci saboda mu."
Amal ta zuba masa ido, zuciyarta na tafasa da zafi. Duk da ba ta ce komai ba, hawaye suka cicciko a idanunta. Ta ji hannunsa yana da dumi a nata hannun, amma zuciyarta ta karye da tunanin cewa wannan kusancin da suka gina cikin dare ɗaya zai rushe haka kawai, ta wani ɓangare tana farin cikin barin ta gidan..
A haka suka fice daga babban falon, inda dukkan idanu suka bi bayansu kamar suna musu kallon karshe.
Sun nufi part ɗin Maleekh, shiru ya lulluɓe su gaba ɗaya, babu wanda ya iya furta wata kalma.
A can cikin zuciyarsa, Maleekh yana tunanin:
"Taya zan sa6awa uwata akan matar da nake so na ɗauki fansa akan ta?..."
Bayan sun shiga ɗakin, Amal a iya falo ta zauna akan sofas, yayinda shi kuma Maleekh ya wuce cikin bedroom domin haɗa mata kayan da yayi mata siyayya, ya jera kayan a cikin akwatin da ya siya mata..
Amal tana sharar hawaye tana jiran fitowarsa, sai idonta ya sauƙa akan wani glass photo a jikin bango, an kewaye shi da kyawawan flowers. Ta tsaya cak, zuciyarta ta yi wani irin tsalle kamar an danna mata wuta. hoton da bata lura dashi ba sai yanzu..
Kirjinta ne ya buga lokaci guda ganin hoton yara biyu mace da namiji sanye da kayan makaranta..
Amma namijin kana ganinsa kasan ya girmi macen sosai sannan ya fita da class sosai..
Amal a ruɗe ta nufi wurin idonta akai, ganin hotonta tana ƙarama da abokinta wanda a halin yanzu bata san a yanda yake ba, domin tin suna yara suka rabu...
A hankali ta furta sunan yaron dake jikin hoton "My Leekh💝..
Maleekh wanda fitowarsa kenam daga bedroom yana jan akwatin ta jin kamar ta ambaci sunan da babu wanda yake ƙiran sa da shi sai fiance ɗin ta...
Da sauri ya ɗago, zuciyarsa ta tsaya cak. Kalmar da ya ji daga bakinta “My Leekh” ita ce kalmar da tin yana yaro babu wanda ya sake ƙiransa da ita sai abokiyar ƙuruciyarsa...
Ya juyo a rikice yana kallonta, idonsa ya sauya launi da mamaki.
Da sauri ya furta
“Me kika ce?…”
Amal ta yi saurin gyara kanta, tana son ɓoye damuwarta, tana nuna kamar hoton kawai ya burge ta ne ta ce
“Na ce naga hoton nan ya burge ni… su waye waɗannan yara?”
Ta nuna da yatsanta cikin rawar jiki, idonta na kan hoton amma zuciyarta na dukan tara-tara.
Maleekh ya tsaya kallon hoton na wasu daƙiƙu, sannan ya murmusa da wani irin murmushin da ke ɗauke da zafi da sirri.
Ya ce
“Wannan ita ce fiancée ɗina… tun muna yara muka rabu. Ban san a ina zan sake samunta ba. Na sha nemanta, domin ita ce ƙaunata ta farko, amma har yanzu ina riƙe da wannan hoton a zuciya.”
Sai kuma yayi shiru, ya ɗauki numfashi mai nauyi yana dubanta da ido kai tsaye, yana ji zuciyarsa na son faɗa mata gaskiya amma kalmomi sun makale...
Dakatawa yayi saboda kada taji haushi akan ya bayyana irin ƙaunar da yake yiwa fiancée ɗinsa...
Amal lumshe idonta tayi zuciyarta na bugawa, ganin Maleekh yana ƙoƙarin sanar mata cewa shine 'Leekh ɗinta..."
Sai ta ɗago idanunta a hankali, ta tsaya kallon shi, zuciyarta na cewa: “Shin zan iya furta masa cewa nine Fiancée ɗinka?…”
Muryar Maleekh ne ya katse ta da cewa.
"Yanzu zamu iya tafiya, amma ki sani… bazan taɓa barin ki ba, ko da duniyar nan ta ɗauka cewa mun rabu. Ki adana wannan magana a zuciyarki."
Amal ta kasa cewa komai, zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Sai kawai ta ɗan girgiza kai, idonta cike da hawayen farin ciki da tsoro lokaci guda.
Ya kamo hannunta, suka nufi falo tare.
Bayan sun shiga babban falo, sun tarar da su Ammy, Farha, Arfat da Islam.
Wani murmushi mai cike da fifiko da kishi ya bayyana a fuskar Farha..
Farha ta haɗe fuska, tana tsaki sannan ta ce..
" Tafiya zakiyi Amal?, to ai kuwa gwara ki tafi domin nan ba wurinki bane. Allah ya raka taki gona, sannan Allah ya baki miji ɗan tasha kamar ke, kuyi rayuwar ƙasƙanci irin na ƴan tasha, ya kuma baku ƴaƴa masu irin tarbiyyarku na ƴan tasha…"
Amal ta juyo tana kallon ta sannan tayi murmushi tare da mayar mata da amsar cewa..
"Amin ya Allah tinda gashi nan a gabana..."
Tayi maganar tana nuna Maleekh..
Farha ta wurga mata harara tare da haɗiye maganarta..ganin zata raina mata hankali...
Ammy idonta akan Maleekh cikin isa da gadara ta ce
"Na gode da ka fahimce ni, Maleekh. Wannan ce dama ɗaya da zan tabbatar da kai ɗana ne nagari. Amal… Allah ya raka ki lafiya."
Amal ta sunkuyar da kai cikin kunya, zuciyarta na bugawa domin Ammy na mata gwarjini, amma sai taji hannun Maleekh ya ƙara matse nata da ƙarfi...
Har zasu juya sai ga Arfar ta wurgo mata jakar kayanta da tazo dashi, tana faɗin
"Tsaya ki ɗauki tsiyarki nan, shin awa zaki bar wannan kazantar kayan ki?..."
Amal sunkuyawa tayi ta ɗauki jakar..
Maleekh kuwa nuni yayi wa Arfat cewa
"Zai dawo zata shiga hannunsa..."
Arfat kukan shagwaɓa ta fara yi tana kallon Ammy, da sauri taje ta faɗa jikin Ammy tana shishshige mata kamar zata koma ciki, dake ita ce ƙarama..kuma ƴar auta a wurin Ammy, domin a wurin Abbah akwai ƙaramar Arfat ƙanwar A'isha...
Ba tare da wani ƙarin magana ba, suka fita. Maleekh ya ja Amal da kansa har zuwa mota.
Ya buɗe mata ƙofa cikin kulawa, ta shiga, sannan shima ya zagaya ya zauna a kujerar driver.
A nan security ya buɗe musu gate, suka fita a ɗari daga gidan...
Sunyi tafiya sosai kafin su fita daga unguwar Maitama..
Suna tafiya akan titunan Abuja cikin nutsuwa. Dukansu babu wanda ya ce komai, amma zuciyoyinsu suna ta magana, kowannensu yana ji kamar ana rura musu wutar soyayya..
Doguwar tafiya suka yi, sai dai ba su fita daga Abuja ba. Amal na sa ran tashar mota zai nufa, domin ta koma Kaduna. Amma sai taga ya tsaya a bakin wani tsararren gida mai katanga babba, cike da tsaro, ya fara hon da mota.
Bai ɗauki lokaci ba maigadi ya buɗe musu gate. Maleekh ya shiga ciki da mota cikin nutsuwa..
Amal ta zaro ido, zuciyarta ta tsaya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 62