Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
amma fuskarta ta nuna nutsuwa da ɗan murmushi mai sa tsoro. Ta tsaya gabansa, sun tsaya fuskantar juna. Hannuwanta suka tafi kai tsaye ga wuyansa... kafin ya yi wani tunani, ta haɗe bakinta da nasa... Da farko Maleekh ya tsaya kamar an dasa shi. Idonsa ya zaro, zuciyarsa ta tsaya. Sai dai sannu a hankali jikin sa ya fara yin sanyi, ya fara narkewa a hannunta... Amal ta riƙe kansa sosai, ta zurfafa sumbatar. Ba sumbatar ƙauna bace kawai, sumbatar azaba ce, sumbatar ramuwar rai, sumbatar mace da zuciyarta ta kone. Hawayenta na gauraye da numfashinsa, tana sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi, kamar wacce ke sakin wani zafi da ta ɗauka shekaru. Mintuna suka shuɗe suna a haka. Kamar wanda aka tsayar da lokacin domin ya tsaya ne cakk. Numfashin Maleekh ya canza, hannunsa ya zame a hankali daga jikinta, jikin sa ya ɗau rauni, kamar wanda aka tsaga masa zuciya da yatsa. Amal ta dakata. Ta ja numfashi mai zurfi, ta ɗan matsa baya kaɗan tana kallonsa cikin ido. Sai ta saki wani murmushi mai taushi da ke ɓoye ciwo. “Na baka raunanniyar zuciyata…” ta ɗan numfasa “Na karɓi taka lafiyayya.” Ta ɗan jinjina kai, ta ƙara da murya mai ƙarfi kaɗan: “Je ka. Ka jira… abin da zai faru.” Kamar an soka masa wuƙa a cikin zuciya, Maleekh ya tsaya yana kallonta. Zare baƙin glass ɗinsa daga idonsa yayi, ya jingina kai, yana kallonta da idon da ke bayyana abu biyu lokaci guda, mamaki da ƙiyayya... Ya ɗan ja numfashi, ya juya ba tare da ya furta komai ba. Ƙarar takalminsa ta ɓace daga ɗakin a hankali... A lokacin, Amal ta faɗa kan gado, ta rufe fuska da hannaye tana numfashi cikin zafi, hawaye na sauƙa kamar ana wanke zuciya da jini. Bayan Maleekh ya fita daga gidan, sai Abbah da Inna suka shigo ɗakin da sauri, zuciyarsu cike da fargaba. Amal tana zaune a gefen gado, idonta na kallon ƙasa kamar wacce ke jiyo muryar zuciyarta. Abbah ya matsa kusa, ya furta cikin tausayi: “Daughter…” Amal ta ɗago a hankali, ta kalli Abbah da Inna, murya a sanyaye kamar wacce ta fito daga ƙasa ta ce: “Ina son ganin Zayd…” Kallon juna suka yi da mamaki, Inna ta dafa kafaɗarta cikin farin ciki da jin sauƙin zuciya ganin yanzu Amal tayi magana. Abbah ya murmusa, yana faɗin: “Alhamdulillah…! Yanzu kin yi magana kenan. To shikenan, kar ki damu, zan ƙira shi.” Ya miƙe ya fita da sauri, zuciyarsa cike da godiya ga Allah... ☀️ Washegari da safe. Zayd yana zaune a falo, cikin nutsuwa da ɗan damuwa. Ƙiran Abbah ne ya kawo shi, bai san me Amal zata gaya masa ba. A zuciyarsa, yana jin ƙaunar Amal kamar da gaske amma har yanzu yana jin kunyar abinda suka aikata tare da Maleekh. Sai ga Amal ta sauƙo daga beni. Takalminta na yin ƙaramar ƙara, kowane mataki yana jawo hankalin Zayd ya kasa motsawa. Ta tsaya a gaban kujera, ta zauna cikin kwanciyar hankali amma idonta na cike da nutsuwar da ke ɓoye wuta. “Duk nasan komai, Zayd. Duk shirye-shiryen da aka yi mun, daga photona har zuwa zubar da mutuncina duk shirin Maleekh ne.” Zayd ya yi shiru, ya kasa ɗago kai. ta ci gaba. “Kaima nasan baka da bambanci da shi, tinda duk ɗaya kuke wurin ɗaukar fansa. Amma ban tsaneka ba…” Zayd ya ɗago, ya ce cikin raunannen murya “Amal… kiyi haƙuri. Wallahi ba da niyyar cutarki nayi ba. Na biye masa ne saboda ina son ganin farin cikinsa amma daga baya, na gane… Na gane ke ce matar da nake so da gaske.” Amal ta ɗan saki murmushi sannan ta furta “Da gaske kake?” Zayd ya jinjina kai da sauri, idonsa cike da tabbaci: “Na rantse da Allah, ina sonki da gaske, kuma zan so ki har karshen raina.” Ta ɗan juyo gefe tana murmushi, ta ce cikin sanyin murya: “To in har da gaske kana sona to sai an tabbatar.” Ya kalleta cikin tambaya. “Ta yaya?” Amal ta ɗago idonta kai tsaye cikin nasa, ta ce da murya mai daɗin sauraro: “Ina so nan da sati ɗaya a ɗaura mana aure.” Zayd ya yi firgigit, amma murmushin farin ciki ya bayyana a fuskarsa. “Aure? Amal... kina nufin... muyi aure?” A taƙaice ta ce: “Eh. Auren gaskiya. Na riga na sanar da Abbah cewa kai nake so, kuma na tabbata ba zaka ƙi ni ba.” Zayd ya kasa boye farin cikinsa, zuciyarsa ta ɗau haske kamar ɗan ƙaramin yaro. “Insha Allahu! In har kin amince, ko gobe kika ce, zan ɗauka da hannu bibbiyu.” Amal ta ɗan kalli gefe, “To, next week ɗaurin aure, kai dai ka sanar da iyayenka, su zo su samu Abbah. Ni kuma zan fara shiri tun yau.” Zayd ya miƙe da murmushi yana faɗin: “Nagode Amal. Na rantse bazan taɓa cutar da ke ba.” Amal ta ɗan saki murmushi, “Na sani. Ka tafi lafiya.” Da farin ciki Zayd ya fita daga falon, yana jin kamar mafarki. Amal kuwa ta jingina kanta da kujera, ta lumshe ido, numfashinta ya yi nauyi. Sai ta ce a ranta, cikin zafi da ƙuduri: “Zaka sha mamaki Maleekh… Zan ga yadda zuciyarka zata yi lokacin da ka ji cewa zan auri Zayd.” Ta saki murmushi mai cike da zafi, murmushin mace da aka karya wa zuciya, amma yanzu ta zama wuta. 🔥 Washegari Mahaifin Zayd ya samu Abbah, suka yi magana akan auren Amal. An fara shirye-shiryen aure cikin gaggawa, ana ta walwala da cike da murna a gida, amma Amal dai kamar inuwar kanta bata runtsa ba, bata fara gyaran amare ba. Lokaci kawai take jira, ba saboda son aure ba, sai don burin zuciyarta... A gidansu Zayd. Farha ta riƙe hannun Zayd da murmushi ta ce, “Dan Allah Yaya, ka riƙe Amal da amana. Ta sha wahala sosai, kar ka ƙara mata ciwo.” Zayd ya jinjina kai cike da niyyar gaskiya. “Farha, wallahi zan kare ta. Zan ba ta farin cikin da ta rasa. Zan zama murya a lokacin da wani ya kasa jin nata.” Sai dai cikin zuciyarsa yasan, ƙaryewar zuciya ce kawai ta sa Amal ta amince da shi... A can wajen Maleekh, lokacin da labarin auren Amal da Zayd ya riske shi, sai kawai yayi murmushi, murmushin ƙarfin zuciya.. Sai kawai ya buge da cewa. “To tunda ta ce tana so, ai sai tayi. Ni kuma ban damu ba...” Ya faɗa yana shan shisharsa, amma a ransa akwai rikici da tambayoyi marasa amsa. 🌹🌹🌹 Ana saura kwana uku a ɗaura auren Amal da Zayd, Abbah ya ƙira iyalansa gaba ɗaya a babban falo. Yana zaune a kujerar tsakiyar falo, kowa yana kallonsa. Ammy, Maleekh, Islam, Arfat, da Zayd wanda zai auri Amal. A cikin nutsuwa Abbah ya gyara murya, yana murmushi. “Na tara ku saboda wani abu mai muhimmanci. Kuma maganar akan Maleekh ne.” Maleekh ya ɗago kai yana kallon mahaifinsa cikin rashin fahimta. “Ni kuma? Me ya faru, Abbah?” Abbah ya ɗan murmusa, sannan ya ce da ƙarfi mai nauyin gaskiya: “Saboda ina tausaya maka, Maleekh. Na san baka tausayin kanka, Ka ji auren Amal, ko? Toh, yanzu zaka ji sirrin da muka ɓoye a cikin wannan shekarar...” Ammy ta ɗan matsa kusa da shi ta ce, “Wani sirri ne haka Alhaji?” Abbah ya ɗaga mata hannu alamar ta dakata. “Zan gaya muku duka. Maleekh... waccan Amatu da ka bari a shekarun baya, wadda ka ɗauka ta mutu a gobarar gidan su... to itace Amal!” Falonsu ya ɗauki shiru na ɗan lokaci. Maleekh ya ɗago da sauri, yana kallon Abbah, zuciyarsa ta tsaya. “Me... me kake faɗa Abbah?” Abbah ya daure ya cigaba. “Ita ce fiancée ɗinka tun yarinta. Na faɗa maka labarin, ko? Gobarar gidan iyayenta? To, iyayenta ne suka mutu, ba ita ba. Kakarta Inna ce ta gudu da ita kafin gobarar ta ci gaba. Wannan dalilin yasa bata da wani a duniya face Inna.” Maleekh a rikice yake kallon Abbah yana girgiza kai tare da faɗin, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un... na wulakanta ta... ni na ci amanar wadda ta kasance fiancée ɗina tun yarinta...!?” Ammy ta riƙe kirjinta tana kallon Abbah da mamaki. “Kace Amal ɗiyar Hajiya Khadija ce? Ƴar gidan Babban Governor Alhaji Abdulsamaad Cash Maker?!” Abbah ya ce da karfi, “Itace! Itace ‘yar Alhaji Abdulsamaad babban abokina, wanda aka kashe da gobara a lokacin siyasarsa! Amma ga ɗiyarsa ka zalunce ta!” Maleekh yana riƙe da kansa yana faɗin, “Me yasa... me yasa ban gane ba? Me yasa ban bincika wacece ba? Sunanta ma Amal Abdulsamaad... ya kamata nayi tunani... amma na makance da ƙiyayyar fansa!” Zayd ya yi shiru yana kallon ƙasa, zuciyarsa na bugawa jin wannan al'amarin... Maleekh ya ɗago idonsa cikin hawaye ya kalli Abbah. “Abbah, me yasa baku gaya mun da wuri ba? Meyasa Amal ta ɓoye min alhalin tasan nine Leekh ɗinta?” Abbah ya ce da murya mai nauyi, “Saboda kai ka lalata komai. Daman burinta shi ne a daren farkonku ta sanar maka da gaskiya. Amma ka wulakanta ta, ka karya mata zuciya. Ka mayar da soyayyarta zafi da ciwo. To yanzu babu abin da zai iya dawo da wancan lokacin, aurenta da Zayd ba zai fasa ya ba.” Ammy ta ce cikin kuka, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Ashe wannan yarinyar ce Amatu? Ashe mu ne muka gaza?” Abbah ya kalleta, ya ce, “Kuma yanzu da ya sani, me zai canza? Rashin jin tausayin ɗan Adam shi ne ya jefa shi wannan halin...” Maleekh ya miƙe cikin ruɗani, hawaye na sauƙa daga idonsa, ya juya zuwa ɗakinsa. Yana zuwa, ya buga ƙofar da ƙarfi, ya shiga tare da durƙusa ƙasi yana ihu kamar ransa zai fita. “Na lalata komai! Na lalata komai Amal!!!” Sautin ihunsa ya fita zuwa falo. Ammy ta rufe fuska tana kuka. Abbah ya jingina yana kallon sama da murmushi mai ciwo, ya ce a hankali: “Ko mutuwa zakayi, yanzu Amal ba taka bace.” Sai ya juya ya dubi Zayd ya ce cikin kwanciyar hankali: “Je ka, ka cigaba da shirye-shiryenka. Jibi ɗaurin auren.” Ammy ta ɗago tana kallon Abbah da mamaki da ɗan tsoro a fuskarta. “Alhaji... kana nufin kace... Hajiya Umma itace Inna?” Abbah ya ɗan juya kansa a hankali yana kallonta da murmushi. “Da kika kasa ganeta ai shikenan.” Ammy ta ɗaga murya cike da rashin yarda. “Wallahi Alhaji, ban san ita bace! Gaba ɗaya ta canza mun! Hajiya Umma da na sani farar mata ce sosai, ga haƙoran Makkah, sannan tana da dirin jiki. Wayayyar tsohuwa ce, mai ƙamshi, mai kalar hutu. Amma wannan Inna da nake gani yau, ta tsufa sosai, ta yi baƙi, wasu haƙoranta ma sun cire, bata da dirin jiki kuma sai masifa! Wancan kuwa mai sanyi da nutsuwa ce, amma wannan kamar ba ita ba ce... gaba ɗaya ta sauya, Alhaji.” Abbah ya ɗan yi dariya mai zafi, yana jinjina kai. “Au ke da haka kike? Haka na auro ki? To ai lokaci tafiya yake, rayuwa bata tsaya a kalar jiki ko kamanni. Ita Inna ta sha wahala, ta rayu a cikin talauci. Shi yasa duk siffofinta suka canza. Amma ni kallo ɗaya na ganeta. Kuma ita ma ta gane ni. Ta sanadiyyarta ne ma yasa na gane Amatu.” Ammy ta ce cikin mamaki, “To ya akayi ni na kasa gane ta, Alhaji? Ni dai a ganina ba ita bace.” Abbah ya juyo yana dubanta da idanu masu cike da raini. “Ai daman ke da ɗan naki, duk kwakwalwarku a toshe take. Idan aka ce ku yi gabas, sai ku yi yamma.” Daga nan, Abbah ya ɗauki hularsa, ya tashi ya bar falon cikin ɓacin rai. Ammy ta tsaya kallon ƙofar da ya fita tana guntun murmushi mai cike da zafi. “Amatu... Amatu da na ɗauke ta tamkar ‘yar cikina, yau ita nake gava da ita? Amatu da a baya take yawan wasa a gidan nan har ta kwana, amma yau ita nake ƙi? Tir da rashin sani. Ashe ba talaka bace, ba matsiyaciya bace. Ashe ita ce ƴar gidan Babban Governor! Wayyo ni... kullum nake zaginta da talauci, nake cin zarafinta... ashe ni ce mai kaskanci!” Ta riƙe kanta tana kuka a hankali, hawaye na bin fuskarta. A can sama, Maleekh ya shiga tashin hankali. Gaba ɗaya ya hargitsa ɗakin. Duk ɗakin ya birkice, gilashe duk sun faffashe, takardu a yage, hotunan Amal da ya ɓoye a jaka ya baza su a carpet, hoto na yanzun ta. Yana cikin tashin hankali, ya janyo wani akwatin azurfa da Farha ta kawo masa a baya, akwatin Amal.. Ya buɗe shi hannu na rawa... Sai ga hotunansu tun suna yara shi da Amatu a lokacin suna sanye da kayan makaranta, suna dariya, hannunsa riƙe da nata a bakin wata bishiya. A ƙasan hoton akwai rubutu da ƙaramin salo da Amal ta rubuta: “My Leekh… my promise will never die.” Maleekh ya firgita, hoton ya faɗo daga hannunsa, idonsa suka rufe da hawaye. Yana riƙe da kansa yana faɗin: “Amatu... ashe kece? Ashe kece? Na lalata rayuwarki, na wulakanta ki...Dan Allah! Me yasa ba ki faɗa min ba? Me yasa kika bari har na zama abokin gavarki?” Ga hotunan akwatin duk ya baza su.. Ya zube ƙasa, yana dariya cikin hawaye, dariya mai ciwo, kamar wanda ya rasa hankali... “Na yi fansa a kan soyayyata... na kashe farin cikina da hannuna... yanzu menene ya saura gare ni?”... A ƙasa kuwa, Ammy ta zauna shiru, tana tunanin rayuwar da ta wuce, tana faɗin a zuciya: “Inna da Amatu sun dawo ne don su zama hasken da muka ƙi gani... amma yanzu babu haske, duhu kawai muka bari ya lulluɓe mu.” A wannan ranar Da daddare, misalin ƙarfe 8:00, Maleekh ya isa gidansu Amal. Shigarsa cikin falon ta zo da mamaki, ya tarar da ita zaune akan kujera tana hira cikin natsuwa da Zayd. Da ƙafe su da rinannun idanuwansa. Wani irin zafin takaici da haushi ya ratsa zuciyarsa. Ya ƙarasa cikin ruɗani, murya na rawa ya ƙira sunanta: “Amal…” Ta ɗago kai tana murmushi, kamar wadda babu komai a zuciya, ta ce cikin nutsuwa: “Sannu da zuwa…” Maleekh ya ɗan matsa, muryarsa cike da raɗaɗi da rashin fahimta, ya ce: “Meyasa zaki mun haka, Amal? Ashe ke ce fiancée ɗina kika wahalar dani wurin jinkirin jiranta? Ashe ke ce ita? Why Amal? You are part of everything in my life…” Amal ta tashi a hankali, tana murmushi, ta ce cikin kwanciyar hankali: “Maleekh, wannan shi ne Zayd, wanda zan aura.” Ta ƙarasa maganar tana nuna Zayd da hannunta cikin sanyi, amma kalmarta ya zame masa kamar kibiya. Maleekh ya yi gabanta yana faɗin cikin rawar murya. “Ki fahimce ni Amal…” Sai ta katse shi da murmushi, ta ce: “Maleekh, jibi ɗaurin aurenmu da Zayd. Amma gobe za’ayi shagalin walima fatan zaka halarta.” Maleekh ya dafe ƙirji kamar wanda aka soka masa wuƙa. Ya yi wani irin ihu da murya mai raɗaɗi: “Please, Amal! Ke ɗin rayuwata ce. Kar ki manta akwai alƙawarin aure a tsakaninmu. Ni ne Leekh ɗinki wanda zai iya bada rayuwarsa saboda ke!” Amal ta cigaba da murmushin da yake haɗe da zafin tausayi, ta matsa kusa da Zayd. Ta riƙo hannunsa cikin nata, ta ɗago shi tsaye sannan ta dafa kafaɗarsa, tana cewa: “Ga Zayd mijina na gobe kuma abin alfaharina.” Maleekh ya zaro idanu yana kallonta, muryarsa ta dushe cikin rawar murya: “Oh my God! Ina ruwana da wani Zayd? Ina miki magana ne akan rayuwarmu, Amal…” Ta ɗan ja numfashi, ta yi murmushi mai sanyi amma idonta ya nuna ƙarfin hali da yanke hukunci: “Rayuwata ai gashi nan…” Ta nuna Zayd da hannunta. Maleekh ya girgiza kai, hawaye na sauƙa daga idonsa kamar ruwa. Ba tare da ya sake cewa komai ba, ya juya da sauri, ya fice daga falon cikin fusata.. Kofar ta rufe da ƙarfi bayan fitarsa... Amal ta kalli Zayd sannan ta ce "Please Zayd kaje sai gobe zamu sake haɗuwa..." "A wurin shagali ko kuwa?..." Ya tambaya yana kallonta. Ta ce "A wurin shagali..." Daga nan ta zauna tare da ɗaukar cup tana shan lemon cikin. Shi kuwa Zayd sallama yayi mata ya fita... Wannan rana ta kasance daren da ya fi kowanne tsayi. Maleekh bai runtsa ba, sai zirga-zirga yake a cikin ɗakinsa kamar wanda yake gujewa tunaninsa. Zuciyarsa na bugawa da sauri, numfashinsa na fita cikin nauyi. Ya tsaya gaban madubi yana kallon kansa, yana tambayar kansa da murya mai raɗaɗi: “My fiancée zata auri wani ina ji ina gani? Me yasa ta iya furta mun haka kamar ban taɓa zama komai gareta ba?” Ya janye ido daga madubin, ya koma gefe da gadonsa duk hotunan Amal da su tun lokacin yarinta, suna nan a baje a kan gado. Wasu hoto tana dariya, wasu tana kuka, wasu kuma tana tare da shi lokacin da soyayyar su ta fara. Ya ɗauki ɗaya daga cikin hotunan da hannu mai rawa, ya ce cikin murya mai raɗaɗin ƙauna: “Amal… kina tuna wannan hoto? Ran da kika ce ni ne masoyin da ba zai iya rabuwa dake ba. To yau me ya faru, Amal?” Hawayen da yake ƙoƙarin ɓoye suka zubo. Ya ajiye hoton yana kama kansa da hannu biyu, yana tafiya gaba da baya kamar mai ciwon zuciya... Ya doku a gado yana kallon ceiling a hankali ya furta. “I thought I was enough for you… But maybe I was just a memory you wanted to forget.” Zuciyarsa ta matuƙar nauyi, jikinsa duk yayi sanyi. “Amal… zaki yi aure, ni kuma zan zauna da tunanin ki har abada?” _NEXT NEXT NEXT_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 79 to 80 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Da sassafe, kafin shagalin walima, Ammy ta nufi gidansu Amal cikin nauyin zuciya. Da ta shiga, ta tarar Inna zaune kan kujera, Amal na gefenta tana nuna mata akwatunan auren da za'a kawo a wayarta... Inna ta ce "Yanzu to ya zamu yi da lefen wurin Maliku? Ga su Abbanku yace 'abar miki su' ai zasu yi yawa kuma.." Amal ta murmusa sannan ta ce "Inna, ai kogi bai ƙi yayyafi ba.." Suna cikin tattaunawa sai suka ji buɗewar ƙofa. Tsaya kallon Ammy suka yi wacce ta shigo jiki a sanyaye. Ammy ta tsaya cak, hawaye suka taru a idonta. A hankali ta durƙusa a gaban Inna, kafin ta sa hannu biyu ta rungumeta tana kuka kamar ƙaramar yarinya. Ammy cikin kuka, ta ce. “Uma… ki yafe mun. Ki yafe wannan zuciya ta da ta kasa ganeki… Ki yafe ni Uma. Na wulakanta ku, na ƙyamace ku… wallahi ban san ke bace Hajiya Umma… Ki yafe ni, wallahi ban san ke bace ba!” Inna ta share hawayen fuskarta, ta dafa bayanta. Tare da faɗin, “Allah ya yafe ki, Maryama. Rayuwa tana canzawa, jiki yana canzawa. Ba laifinki bane, sai dai ki riƙe min jikata kuma ƴarki da amana.” Ammy ta juyo da sauri, ta rungumi Amal sosai kamar zata maido da shekarun da suka ɓace. Ammy ta ce, “Amatu… wayyo ‘yata… tun rasuwar mahaifiyarki na shiga kewar da ban taɓa fuskantaba. Wallahi ni ban san ke bace ‘yar Khadija ba… Ban san ke bace ‘yarta ba… Don Allah ki yafe min, ki yafe wannan zuciya ta da ta rufe saboda rashin sani…” Amal cikin kuka ta ce, “Na yafe miki, Ammy. Ni ban taɓa ɗaukar ki abokiyar gaba ba. Kullum ina roƙon Allah ya shirya zuciyarki saboda ni.” Suka rungume juna, kuka ya cika ɗakin. Farha da wasu mata suka shigo, suka tarar da su cikin kuka, kowa sai tausayin wannan rana ta mamaye zuciyarsa... A wannan ranar Ammy wuni tayi a gidan, domin ita ta shirya Amal domin tafiya wurin shagalin Walima.. An kawata wurin cikin natsuwa... wannan karon ba kiɗe-kiɗe, ba rawa. Malamai ne zaune a gaba suna wa’azi kan hikimar aure, zaman lafiya, hakuri da biyayya.. Domin Abbah ya sanar cewa yawan kiɗe-kiɗe ne yake kawo fitina da rashin zaman lafiya, domin shaidan yana fitsari a wurin... Wurin Amarya da Ango an gyara shi cikin kayatarwa, an jera furanni, an haxa fitilu masu launi. Amal na zaune cikin rigar walima, Zayd a gefenta cikin nutsuwa. Wurin cike yake da mutane sosai, ƴan uwa, abokan arziki, dattijoji, duk sun hallarta... Hajiya Sa’adatu wannan ranar, ranar baƙin cikinta ne domin ta sa ran za'ayi hidima sosai a bikin ɗanta na fari... amma sai aka fake da wa'azi da karatu.. Ana cikin wa'azi sai ga hayaniya a bakin ƙofar shiga.. Kafin a ce meye, Maleekh ya shigo… Cikin black jeans da white t-shirt, idonsa jawur kamar wanda bai runtsa ba. Hannunsa na riƙe da bindiga. Mutane suka miƙe cak! Amarya ta miƙe da sauri, zuciyarta na bugawa. Zayd ya miƙe da fargaba. Abbah ma ya taso.. Maleekh bai tsaya ba, ya haura kai-tsaye zuwa wurin Amal da Zayd. Kamar mahaukaci, ya ɗaga bindigar ya saita Amal. Muryarsa ta karye wa, hawaye na kwance kan fuskarsa.. Abbah cikin firgici ya ce, “Maleekh!! Kana hauka ne? Za ka kasheta ne?!” Maleekh cikin rawar murya, yana rikitar da bindiga ya ce, “Naje gidansu… nayi mata magana… akan dalilin da yasa ta ɓoye min cewa itace fiancée ɗina! Amma ta maida ni kamar mahaukaci! To yau zan nuna muku haukata! Bazan bari ta auri kowa ba… In ba ni ba, sai dai mutuwa! Ni da hannuna zan kashe ta… sannan na kashe kaina! Fiancée ɗina ba mallakin kowa bace sai ni!” Amal tana kuka, ta kasa motsi. Zayd ya yi baya yana jijjiga kai cikin tsoro. Maleekh ya kunna kunamar bindigar… Ya ɗora yatsa… Ya ɗaga hannun… Bindigar na gab da tashi… Kowa ya rufe ido cikin tsoro… Sai kawai ya kawar da bindigar. Ya jinjina kai, ya miƙa bindigar ga Amal, yana rawar jiki. “Bazan iya kashe ki ba… fiancée ɗina… rayuwata… Amma ga bindiga… don Allah ki harbe ni! Ki huce wannan baƙin cikin da na saka miki. Na jawo miki raɗaɗin da ba zan iya gyara ba… Ki kashe ni Amal… ki yi min adalci…” Amal ta karɓi bindigar da kuka mai ƙarfi. Ta ɗaga ta kai saman kanta, tana kallonsa. Murya na kakkarwa ta ce, “Na gode da bindigar da ka kawo min… Ka ce in huce, ko? To ga shi… mutuwa ta fi zaman da zanyi da wani ba kai ba… Ka bar ni lokacin da nake buƙatarka, ka wargaza min zuciya… Iyaye na sun mutu, nima mutuwa zanyi… Domin babu wani farin ciki a tattare da ni…” Ta rufe ido… Ta matse bindigar… Ta ɗan matsa kunamar Wani ƙara bindigar yayi na fitar bullet!!! Bullet ɗin ya yi karo da mirror da aka kafa don kwalliya ya tarwatse! Kowa ya fara ihu! A lokacin da ta matsa Maleekh yayi saurin karɓar bindigar lokacin kuma ya matsa... Ganin babu abinda ya same ta ne yasa hankali kowa kwanciya.. Inna da Ammy rufe idonsu sukayi zuciyoyinsu na bugawa da ƙarfi... Abbah ne ya je ya tsaya a tsakiyarsu cikin fushi yake kallon Maleekh tare da faɗin “Ka zo domin ka hallaka ta kenan?! Maleekh, shin ka rasa hankalinka ne!?.. Ko me zaka yi, ba zan taɓa aurar maka da Amatu ba! Ka rusa damarka da hannunka! Da ma na gaya maka duk wanda ya iya wargaza zuciyar mace bai cancanci soyayya ba! Ka tafi, ka je ka ƙare haukarka!” Maleekh ya yi ƙasa da bindigar, ya durƙusa ƙasa da gwiwowinsa, hawaye na gangarowa cikin mugun raɗaɗi. Ya fashe da kuka kamar yaro… Kowa a wurin ya tsaya yana kallonsu.. Maleekh yana durƙushe ƙasa, hannayensa a haɗe, idanu suna ciccike da hawaye kamar ruwan sama. Cikin kuka mai karyar da zuciya, ya ce. “Abbah… dan Allah… kar ayi auren nan. Amal da ni ta dace… ita ɗin rayuwata ce. Na gina burina da ita tun farko… har ƙarshen numfashina… Dan Allah ka taimake ni… ina ƙaunarta… wallahi ina ƙaunarta Abbah…” Abbah ya tsaya yana kallon ɗansa wanda ya rikice gaba ɗaya, fuskar sa cike da takaici... Abbah ya ce, “Ka ce kana ƙaunarta? Shi yasa ka wargaza mata rayuwa? Shi ne ka kawo mata bindiga don ta hallaka kanta? Hakan ce soyayyar taka?” Ammy da ta tsaya gefe tun farko, zuciyarta ta taɓu sosai da ganin ɗanta cikin kaskanci da kuka. Ta matso tana share hawayen

Chapter 51 of 62