An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
repost page 1 asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu, mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
Bismillahi Rahmanu Rahiim
GODIYA TA MUSAMMAN
Ina mai miƙa godiya ta ga Allah Madaukakin Sarki, Mahalicci, Mai Rahama, Mai Jinƙai. Shi ne ya bani ikon rubuta wannan littafi, ya azurta ni da hikima da basira, ya kuma ba ni kwanciyar hankali da natsuwa har na iya kaiwa ga wannan matsayi.
Ina roƙonSa cikin rahamarSa da girmanSa, da ya ci gaba da tsare ni daga sharri, sharri daga mahassada, daga makirci, daga shaidan da kuma dukkan fitintinu na duniya da lahira. Allah Ka sa ni cikin kariyarka, Ka kare ni da wannan rubutun nawa, Ka kuma sa ya zama alheri a gare ni da duk mai karantawa.
Godiya ga Manzon Rahma, Annabi Muhammadu (SAW), wanda shi ne mafificin abin koyi, mai cika da hikima da adalci. Allah Ka kara masa salati da aminci har abada.
GODIYATA GA IYAYENA, 'YAN UWANA, ABOKAN ARZIKI, DA MASOYANA
Ina miƙa godiya ta musamman ga iyayena masu daraja ku ne ginshiƙina na rayuwa. Kun raine ni cikin ƙauna, kun bani tarbiyya da kulawa har na kai ga wannan matakin. Allah ya saka muku da mafificin lada, ya tsawaita rayuwarku cikin ƙoshin lafiya da nutsuwa. Ya gafarta muku dukkan kura-kuranku, ya albarkaci zuri’a da al’amuranku. Amin.
Ga ‘yan uwana na jini kun kasance tare da ni a lokutan farin ciki da bakin ciki. Ina godiya da ƙaunarku da haɗin kan da kuke bani. Allah ya daɗa haɗa zukatanmu da soyayya da fahimta, ya wanke zukatanmu daga hassada da ƙiyayya, ya sa mu haɗu da juna a Aljannah.
Abokan arzikina da dukkan masoyana ba zan iya ƙirga irin goyon bayan da kuka bani ba. Da addu’arku, da karfafa gwiwa, da kulawa. Ina roƙon Allah ya biya muku buƙatunku na alheri, ya tsaida ku a kan hanya madaidaiciya, ya ƙara muku daraja a duniya da lahira.
Kowa da kowa da ya taɓa zama silar kwanciyar hankalina ko ci gaban rayuwata ku sani, kuna cikin addu’ata kullum. Allah ya ƙara mana soyayya da fahimta, ya kare mu daga fitina da sharri.
Amin.
SADAUKARWA
Wannan littafi na musamman na sadaukarwa ne ga matasa da ’yan mata na wannan ƙasa mai albarka Najeriya. Ku ne gatanmu, ku ne makomar ƙasa. Ina roƙon Allah ya ba ku basira, juriyya, da jajircewa wajen cimma burin rayuwa cikin gaskiya, kamala, da tsoron Allah.
Ga shuwagabannin mu, waɗanda ke da nauyin jagorantar al’umma cikin gaskiya da adalci wannan littafi yana mai tunatar da mu cewa jagoranci amana ne, kuma tarihinku zai ci gaba da rayuwa a zukatan jama’a muddin duniya na numfashi.
Ina fatan wannan littafi zai zama tamkar haske mai haskaka zukata, ya zaburar da masu karatu su yi rayuwa cikin nagarta, tsantseni da tunani mai zurfi.
Allah ya sa wannan rubutu ya zama sanadin canji mai kyau a zukatan al’umma.
Amin....
BOOK ONE page 1 to 2
______________________________________
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Kullum da safe Amal tana fita wurin aiki da tsohuwar rigar ƴan jarida da take alfahari da ita, duk da cewa ta daɗe tana amfani da ita..
Zata fita cikin murmushi tana yi wa Inna fatan alkhairi cikin ƙwanciyar hankali tare faɗin
“Inna, ki yi min addu’a yau ma dai kada wata tambaya ta fi karfina.”
Inna kuwa ba ta taɓa gajiya da addu’a ba ta ce
“Allah ya taimake ki Amal, ki yi ƙoƙari kamar kullum.”..
Amal, wacce ake ƙira da "Amal Voice" a kafafen sada zumunta, ta shahara da muryarta a tashar RAYUWA FM. Kowanne lokaci idan ta fara shirin “Labari da Muryar Rai”, gari kan lafa, motoci kan tsaya, kowa kan ji daɗin muryarta mai sanyaya zuciya.
A Instagram da TikTok, shafin ta ya cika da shahararrun faifan bidiyo, inda take bayar da labaran soyayya, dariya da tausayi. Idan ta yi dariya, sai zuciyar masu saurare ta natsu, idan ta yi kuka cikin labarin, mutane kan ji kamar su ma su zubar da ƙwalla.
Duk da shahararta, Amal tana rayuwa a gidan laka tare da Kakar ta, Inna, wacce ke tsananin ƙaunar ta. Albashin Amal bai fi dubu ashirin ba a wata, amma bata taɓa ƙorafi ba, tana son aikin ta, kuma tana ganin ba komai ne a rayuwa kan zama silar farin cikin wasu ba..
★★★★★
...Wata rana a cikin babban falon sa mai ƙayatarwa da shimfiɗar furanni na ƙasar waje, Maleekh Cashbank hamshaƙin saurayin nan da ke tafiya akan iska irin ta masu kuɗi yana zaune yana shan coffee, yana busar hayaƙin shisha kamar wanda ke ƙoƙarin goge ƙiyayya daga zuciyar sa, Fuskar sa a ɗaure kamar bai taɓa yin dariya ba tun da aka haife shi.
A gefe escort ɗin sa tsaye tamkar dutse, baya motsi kamar wanda aka shuka don kare masa kwanciyar hankali, sai kawai TV ɗin da ke gefe ya ƙara sauti da kansa, kamar yana da ikon sanin lokacin da wani abu zai ja hankalin mai kallon sa.
A cikin TV:
Amal sanye da rigar journalist, tana zaune cikin nutsuwa a cikin gidan rediyon RAYUWA FM, tana gabatar da shirin tattaunawa mai taken
“Girman kai..."
Muryarta ne ya shiga kunnuwansa kamar ƙaran sauti daga wata duniya. kalamanta suna da nauyi da natsuwa, tana faɗan maganganun da babu wanda ke iya furtawa cikin rashin tsoro, bata jin tsoron kowa, bata nemi jin daɗi daga wurin kowa ba.
Maleekh yana zauna ya kafe TV da ido, fuskarsa ɗauke da alamun mamaki duk da bai bar zuƙar shishar ba.
A TV da internet da labarai, kowa ya fara magana akan Amal. Shafukan sada zumunta sun cika da faifan bidiyonta. An fara rubuce-rubuce masu taken:
“Wacece Amal Voice?”
“Muryar Kaduna da ta girgiza girman kai.”
Maleekh ɗaukar wayarsa ya yi yana magana da ƙarfi kamar wanda bashi da lokacin komai yana faɗin
“Akwai wata yarinya a Nigeria, garin Kaduna. Sunanta Amal. Tana aiki a wani gidan rediyo, RAYUWA FM. Inaso ka nemomin bayanenta. Ina so in san komai game da ita, asalinta, rayuwarta, da dalilin da yasa mutane ke yawan magana akanta.”
Fuskar Maleekh ba ta sauya ba ko ɗigon dariya babu. Yana ɗaure da fuska kamar dutsen da aka ajiye a rana. yana tunanin cewa wata 'yar talakawa na ƙasar da ya baro, tana iya maganar da zata ja hankalin duniya?.
Amal bata san cewa yanzu haka wani idanun duniya na kallon ta ba. Kuma Maleek ba irin mazan da ake wasa da su bane. Ya shirya domin jin meye sirrin Amal, sannan ya tabbatar mata cewa girman kai ba laifi bane idan ka san darajarka....
Washegari da safe.........
Cikin ofishin Maleekh Cashbank dake England, babban ofishi komai a tsare sai ƙamshi da shishar hayaƙi da ke cika dakin.
Maleekh yana zaune, yana duba laptop ɗinsa, fuska ɗaure kamar wani shugaban ƙasa. Kamar bai taɓa kallon kowa ba, kamar duniyar gaba ɗaya tana ƙasansa.
Security yana tsaye cikin ladabi, hannuwansa a gaba Ya ce
"Sir... na kammala binciken kamar yadda ka umarta."..
Maleekh ba tare da ya ɗago ba, yana zuƙan shisha tare da latsar mouse ya jinjina kai ba tare da ya furta komai ba...
Security ya ci gaba da cewa:
"Sunan ta Amal Abdulsamaad. Tana matakin Diploma. Tana zaune da Kakarta a wani yankin talakawa. Ba su da wani gata ko arziki, sai ilimi da basira. An ce yarinyar bata jure raini, amma tana iya sarrafa magana mai ƙayatarwa. Wayayyiya ce, sai dai..."
Maleekh ne ya ɗaga masa hannu, tare da katse shi, muryarsa cikin ƙarfin izza Ya ce
"Stop right there! Kai, dallah dakata! Bance ka kawo min yabon ta ba. Domin ba ita nake buƙata ba. Ka samu number gidan rediyon su?"
Security yana dukar da kai cikin girmamawa Ya ce
"Na samu, sir....."
Maleekh ya ja tsaki tare da ɗora kafar hagu akan dama Ya ce:
"Inaso in tattauna da ita... a cikin gidan rediyo... ta hanyar voice call, yanda kowa zai ji. Ba sirri bane saboda bata kai matsayin da zan ɓoye maganata da ita ba."
Maleekh ya ɗau wayarsa, ya jefa wa security Ya ce
"Ka ƙira min su yanzu."
[RAYUWA FM Kaduna, Nigeria]
Amal tana zaune a cikin studio, ta gama karanta wani rubutu akan gaskiya da mutunci, muryarta cike da natsuwa, tana tafe da lafazi mai daɗi..
Sai aka katsar da ita tare da nuna mata ƙira daga waje.
Producer ne ya girgiza kai yana faɗin:
“international call.”
Amal ta ɗaga ƙiran da murya mai taushi Ta ce:
"Hello, wa ke kan layi? Fatan mai sauraro yana jin mu lafiya?"
Shiru akayi ba tare da an furta komai ba sai da aka ɗau tsawon mintuna biyu kafin muryar Maleekh ta bayyana cikin izza, babu girmamawa, kamar yana magana da ƙasa ba mutum ba, kamar bazai yi magana ba ya furta:
"Amal Abdulsamaad, ko ke ce? ki saurara da kyau, kada ki katse ni, ba wai ina son jin tarihin ki bane ko jin daɗin muryarki, ina da tambaya guda ɗaya."
Amal ta ɗan yi shiru sannan ta dai daita murya cikin nutsuwa Ta ce
"To, ina sauraron ka, amma a nan tashar muke, abin da za ka faɗa zai shiga kunnuwan jama'a."
Maleekh cikin murya mai sanyi da tsawa ya furta
“Ke ƙaramar yar jarida ce… kina magana akan girman kai? kin taɓa sanin me ake nufi da asalin darajar mutum kuwa? ko dai kina magana ne saboda baki da komai?”
[Live broadcast ke gudana... kowa a Kaduna yana sauraron su...]
A cikin studio, Amal ta zaro ido na ɗan wani lokaci. Sai da ta yi shiru kamar mai nazarin wani abu kafin ta gyara zama, ta dai daita mic, ta fara magana a hankali cikin fara’a da natsuwa, muryarta na kaɗawa cikin ilimi da wayo...
Ta ce:
"Tambayar ka mai ƙayatarwa ce, kuma na gode da samun damar jin irin wannan ra’ayi daga wurinka."
Tana ɗan murmushi cikin nutsuwa, muryarta na kwarara kamar ruwan sanyi akan dutse mai zafi, ta kuma cewa
"Ina ganin girman kai abu ne mai faɗi sosai, idan mutum ya san darajarsa, ya mutunta kansa, yana kare mutuncinsa wannan ana ƙiran sa ne da kamala.
Amma idan girman kai ya hana ka ganin kowa, ya hana ka sauraron gaskiya daga bakin talaka, ya hana zuciyarka karɓar nasiha daga inda baka zata ba to wannan ba girman kai ba ne, hakan rashin fahimta ne da kuma tsoron gaskiya.
Mutane da yawa suna ɓoye rauni da fushinsu a ƙarƙashin girman kai. Amma zuciyar da take da hankali tana karɓar gaskiya ko daga bakin mahaukaci ne...."
*Reaction daga sauraro a garin Kaduna, har da online comments*
“Kai amma yarinyar nan Amal wayayyiya ce gaskiya. Ta ba shi amsa cikin nutsuwa!”
“Wai wanene wannan mutumin da yake nuna raini haka?”
“Kalli yadda ta yi magana cikin ladabi da kuma hikima! Lallai Amal Voice!”
Duk waɗannan maganganun mabiyan bayan Amal Voice ne ke mita akai, sai kuma Online Comments da suke ta shigo wa, kowa da maganar da yake tofawa.....
A cikin ofishin Maleekh a England
Maleekh yana kallonta ta cikin laptop ya yin da suke voice call, yana sauraron amsar ta, ya ja dogon numfashi, wannan karon ya tsaya bai ce komai ba, fuskar sa ta nuna kamar wani abu ya tsaya masa a zuciya, amma saboda nuna ƙwarewar sa ya buƙaci ƙara turowa da wata magana.
Maleekh Ya ce:
"Kina magana kamar wacce kika kware, amma ai ilimi da bakin magana ba su isa su sauya duniya ba, Ke fa ƴar talakawa ce, Ina ke, ina mafita?"
Amal, ba tare da ɓata lokaci ba, ta amsa cikin kulawa tare da faɗin
"Ni ƴar talakawa ce, hakane. Amma talauci ba cuta ba ne, kuma mafita ba a cikin kuɗi kawai take ba, akwai waɗanda suke da dukiya amma basu da kwanciyar hankali, akwai wanda yake da iyakar ilimi, amma baya jin daɗin zaman duniya.
Ni bana so in sauya duniya, amma ina so in fara da mutum ɗaya wanda zai saurari muryar gaskiya ba tare da tambayar daga inda ta fito ba."
[More Comments from listeners]
“Ina ma ace duk ƴan Najeriya suna da nutsuwar Amal.”
“Kamar dai wannan mutumin yana jin wani abu a zuciyar sa yanzu…”
“Gaskiya wannan mutumin ya shiga uku… Amal dai bata da sauƙi amma tana da mutunci.”
★
Maleekh shiru ya yi na wasu sakanni tare da lumshe ido sannan
Ya ce
"Ke fa kina magana akan girman kai, amma kin san ma’anarsa kuwa? Ko kina faɗa ne kawai dan baki taɓa sanin matsayin da zai sa mutum ya yi girman kai ba?"
Amal ba tare da fargaba ko tsoro ba cikin nutsuwa ta ce
“Girman kai ba ya auna kuɗi ko motar da kake hawa. Girman kai na gaske shi ne lokacin da kake girmama kowa, koda kuwa kana da ikon wulakanta shi, kai dai kana da kuɗi, amma daraja? Hakan akwai bambanci.”
Shiru ya yi, saboda kalamanta sun yi masa nauyi fiye da duk wani kuɗi da ke cikin aljihunsa.
A fusace ya kashe ƙiran..
Security na gefe na kallon sa ba tare da ya ce komai ba.
Security a hankali ya furta
"Sir, should I follow up?"
Maleekh ba tare da ya kalli yanda yake ba, ya furta a hankali:
"Kar a sake min magana da ita... amma ku cigaba da sauraron shirin ta... kullum.".......
Asmeetah writer ✍️
*TAƘABBALALLAHU MINNA WA MINKUM...*
*EID MUBARAK KHARIM....*
*INA YIWA ƳAN UWANA BARKA DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA🙏🙏🙏*
*WANNAN FARKON PAGE ƊIN LITTAFIN AMALEEK SHINE BARKA DA SALLAH NA, UNSUSPECTING NEW BOOK ON FRIDAY....*
*The Eid al-Adha Prayer for Animal Sacrifice in the Year 2025*.....
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
__BOOK ONE___page__3 to 4_______________________
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
A daren nan bayan Amal ta gama aiki, ta koma gida... cikin ƙanƙanin lokaci Kaduna ta ɗauki zafi da magana game da tattaunawarta da wani mutumin England da bai bayyana sunansa ba, sai dai magana ta yaɗu sosai, ta fara zama trending a X, Instagram, da Facebook...
A gida, gidan laka, cikin ɗaki mai ɗauke da ƙamshin turare...
Amal ta shiga ciki tare da cire hijab, ta zauna a gaban Inna da take ta yankan alayyahu,
Inna cike da jin daɗi take faɗin
"Yau kin ƙara burge ni Amal, ai har ni da na ke nan na tsaya na saurari tattaunawarki da mutumin England, ina tunanin cewa da gaske wannan yarinyar da ke maganar ce jikata? ina mai ƙara alfahari da ke Amatullah..."
Inna tana murmushi da kwarjininta na dattijai....
Amal ta kwantar da kanta akan cinyar Inna, cikin nuna gajiya Ta ce:
"Inna, dole idan kana irin wannan aiki ka samu maƙiya, wasu ba don su fahimce ka suke saurare ba, sai don suna neman wata hanya su durƙusad da kai."
Inna Ta ce:
"Na san haka... kuma kin yi magana cikin hankali, da kuma Allah ya baki hikima, baki mayar masa da martani ta yanda ya zo miki ba, da kin biye masa da mutane sun ga rashin tarbiyyar ki...."
Amal ta murmusa da jin wani ƙarfin gwiwa Ta ce:
"Amma Inna kin ji irin muryar sa? wani irin girman kai ne da shi, kamar shi kaɗai ya ke da kuɗin duniya... yana so ya ƙaskantar da ni a idon masu sauraro, amma gaskiya da taimakon Allah na cinye wannan jarabawar...."
Inna ta dafa kafaɗarta a hankali Ta ce:
"Amal, idan Allah yana tare da ke babu wanda zai iya hana ki kai matsayinki, sai dai kiyi addua, kuma kar ki bari wannan abu ya rikita miki zuciya, shi da kansa zai dawo da hannu biyu yana roƙon ki, idan bai bayyana a fili ba to zai bayyana a ɓoye...."
Meanwhile a England...
Maleekh ya na zaune yana kallon clip ɗin hirar da aka yanke a social media wani video ne da aka ɗora:
"WACE CE AMAL? WATA ƴAR NIGERIA TA BA WA HAMSHAƘIN MAI KUƊI AMSA CIKIN HIKIMA!"
yanda ake ta comment
“Kalli wannan yarinyar da ta girgiza wani saurayi mai ji da kansa a rediyo!”
#AmalVoice #KadunaPride #WisdomNotWealth
Maleekh ya matse bakinsa. ya ƙura wa allon laptop ido ba tare da ya motsa ba, sai dai yana jin kamar wata ƙaramar guguwa tana ɗan kaɗawa a cikin zuciyarsa...
RAYUWA FM. Amal on Air
Amal a wurin aikin ta.
Sauti ya cika ɗakin rediyo. Murya ce mai raunana zuciya cike da karyewar rai da hawaye da ke kunno kai daga karshen ma'koshi. Amal tana kan microphone, hannunta na girgiza, idonta cike da hawaye amma zuciyarta ɗauke da ƙwarin gwiwa.
Amal cikin sassanyar murya da tausayawa ta furta
“Yau labari zan bayar, ba don na gigita ku ba, sai don zuciyarmu ta koyi darasi.
Wannan labarin na Hadiza da Fahad ne.
Masoya ne, ba don kuɗi suke son juna ba, ba kuma don nasaba da cancanta ba ko shahara,
sai don zuciya, zuciya mai gaskiya, zuciya mai tsarki.”
Amal ta lumshe ido tana jan numfashi da kyar, kamar tana kallon su a gabanta
Her voice trembling with emotion.
Anan ta bada labarin wasu masoya biyu waɗanda aka kashe su ba tare da sun ci hakkin kowa ba, kuma har ila yau an kasa ɗaukan mataki akai...
Ta kawo ƙarshen labarin cikin harshen turanci..
Amal ta share hawayen ta da tissue, tana matuƙar kame kanta, tana kuka, ta kammala bada labarin masoya biyu kuma Aminan ta...
Ta kuma cewa.
“Rest well, Hadiza and Fahad.
The world failed you but history will remember your truth.”
Sautin slow instrumental piano ya shiga a bayyane yayin da kukan jama'a ke tashi a comments da wayoyi da messages da ke shigowa kai tsaye a tashar RAYUWAR FM.
England Maleekh’s Private Apartment
Maleekh yana zaune a kan white leather couch ɗinsa, sanye da 3-quarter da singlet, ƙafa ɗaya a ɗore kan ɗaya, hannunsa yana riƙe da remote amma idanuwansa ba sa ko motsi daga laptop ɗin gaban sa, Amal ce akan Screen ɗin laptop cike da hikima, da harshen turanci mai girgiza zuciya, tana kuka tana magana...
Maleekh tsaki ya ja cikin jin haushin Amal, ya furta:
"Look at her...
What kind of manipulation is this?
So this is the game now? Make the world cry so they forget your status?"
Ya miƙe tsaye ƙirar jikinsa kamar basamude domin ko ina a jikinsa a cike yake, full built, jikinsa fari tas kamar madara, yana motsa kai kamar wanda ke buƙatar tashi daga wani irin mafarki...
Maleekh yana son kashe laptop amma ya kasa, tsayar da hand ɗin sa ya yi ba tare da ya motsa ba, fuska a yamutse, gira a haɗe sai faman huci yake, cikin muryar tsawa yake faɗin:
"This is nonsense, absolute nonsense,
Why... why is she still echoing in my head?"
Ya sunkuyar da kansa yana hargutsa gashin kansa da hannu daya, ya girgiza kai a hankali
yana magana kamar yana ƙoƙarin tsoratar da zuciyarsa
Ya ce:
"She's nothing, Just a radio girl, A local girl, A nobody.
How dare she touch the part of me I buried years ago?"
Kwantar da kansa ya yi a jikin bango, yana numfashi da ƙarfi, ba tare da ya san me ke tafiya a ransa ba, ya tuna kalmomin Amal da take cewa
“You are heard, you deserve better...”
Wani abu yana girgiza a cikin zuciyarsa... Amma Maleekh ya ƙi amincewa da cewa wani abu daga maganganunta ya taɓa wani yanki a zuciyar sa..
Yayin da labarin Amal ke ƙara karɓuwa a faɗin ƙasar, wani fitaccen dan jarida mai suna Rikky Blaze, wanda ke da shahararren podcast ɗin “Nigerian Voices Unfiltered”, ya kalli clip din Amal daga RAYUWA FM. Hankalinsa ya koma kanta nan take.
Rikky Blaze yana magana da PA ɗinsa cewa:
“Wannan yarinyar... Amal... tana da murya, tana da harshe mai daɗin saurare, she speaks from pain and depth.
I want her on the next episode! live from Abuja!
Arrange it, komai da komai, tikitin jirgi, hotel, VIP treatment. Kaduna is too small for that kind of voice.”
Da daddare Amal na zaune tana karanta littafin journalism cikin fitilar lantarki mai launi, Inna na kan sallaya tana jan carbi,
wayar Amal ne ya yi ƙara saƙon email ya iso...
Amal cike da mamaki ta ce:
“Inna... kinga sun ce wani shahararren podcast daga Abuja yana so in zo tattaunawa kai tsaye, sun ce ba tare da na kashe kuɗina ba, hatta jirgi da hotel sun riga sun shirya komai...”
Inna ta ɗaga gira tare da faɗin:
“Lah! To wa ke bibiyar ki haka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 62