Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
cak. Wannan gida ya bambanta da duk wanda ta taɓa gani. Tsari ne na alfarma, gininsa na zamani, duk an zagaye gidan da tsararrun tiles, da manyan trees masu kyau da burgewa a cikin harabar. Tana dafe da kirji, ta juya tana kallonsa da mamaki: Cikin rawar murya ta ce "Nan ɗin wani gida ne? Nifa so nake na koma Kaduna… nabar Inna ita kaɗai. Ka kuma ce za ka kai ni tashar mota…" Maleekh bai ce mata komai ba, sai ya kashe motar, ya fito. Ya zagaya ya buɗe mata ƙofar jikinsa cike da ƙarfi da izza, sannan ya riƙe hannunta. Tana tsaye a inda take kamar an dasa ta, ya ja ta cikin ƙarfin ikon da yake da shi a kanta. Maleekh da muryarsa da na cika da iko ya ce "Ki tsayar da tambayoyin ki..." Ya shigar da ita ciki. Gidan ya cika da tsari irin na masu kuɗi. Dogayen glass windows suna kyalli da hasken, lambu mai kyau ya zagaye shi, flowers masu launi suna ta kaɗawa da iska, sai kamshin fresh roses da ya gauraye da iska. Amal ta tsaya tana kallon kowane ɓangare, zuciyarta na wani irin bugawa... Da haka ya shigar da ita ciki, wani tsararren falo ne mai girma, ya tsaru sosai.. Maleekh ne ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon, Amal cikin ɓacin rai take kallon Maleekh kamar zata yi kuka ta ce "Wai me kake shirin aikata wa haka? na ce ina buƙatar komawa Kaduna, shine ka kawo ni wannan gidan? me kake nufi dani Maleekh? kana so aita zargi nane? baka ji abinda mahaifiyarka take faɗi akaina ba?.." Tana cikin wannan masifar ne sai ga sautin takun ƙafafu daga sama. Amal ta ɗago ido tana kallon stairs ɗin dake zagaye da golden railing. A hankali wata dattijuwa ta bayyana daga upstairs, Tana sanye da dankararren less mai launin shuɗi da silver, an yi mata ɗaurin ɗan kwali mai kyau wanda ya ƙara mata ƙima, duk da tsufarta. Amal ta tsaya cak. Zuciyarta ta buga. Ido ya sauƙa kan fuskarta da ta shafe shekaru tana gani, amma a yanzu ta canza ganinta a irin wannan gidan... Cikin rawar murya ta furta: "Inna?... Innaaaaaa!" Ta ruga da gudu kamar yarinya, ta rungumi Inna gam a jikinta, hawayenta na zuba kamar fanfo... Amal cike da mamaki da kuka take faɗin "Inna! Taya kika zo nan Abuja? me yasa kika baro Kaduna?..." Inna ta shafa kanta da hannunta mai sanyi. Ta yi murmushi, sai kawai ta ce: "Ki tambayi Maliku mana..." Amal ta janye jikinta kaɗan tana kallon Inna cikin mamaki. Inna ta ci gaba da magana cikin natsuwa: "Kin dai san tsufa baya barin mutum yayi surutu sosai. Amma ki sani wannan Maliku ɗin mutumin kirki ne. Tunda kika tafi Abuja, yasa can Kaduna ana kula dani: abinci mai kyau, ruwan sha mai kyau, sutura masu tsada. Jiya Jiya yasa aka kawo ni nan Abuja aka ajiye ni a cikin wannan gida. Yace gidan nan na mu ne…" Amal ta juya a ruɗe tana kallon Maleekh da hawaye a idonta... Maleekh ya miƙe daga kujerar da yake zaune, ya matso kusa da ita cikin natsuwa. Ya ce "Amal… ba wai na ajiye ki a gidan mu ba ne kawai. Na yi haka ne saboda gidan da nake gina muku bai kammalu ba sai jiya. Aka kammala shi. Shi yasa na sa aka kawo Inna nan gidan domin nan gidan sadaukarwa ne. Hallak mallak naku ne. Ko da a misali mun rabu, kada ki taɓa tunanin za ki mayar mun da gidan nan." Ya saka hannu cikin aljihunsa, ya fitar da wasu takardu. Ya miƙa mata da hannunsa cikin kulawa. Sannan ya ci gaba da faɗin "Ga takardun gidan. An rubuta shi da sunanki, Amal Abdulsamaad." Amal kamar zata haɗiyi ranta tsabar farin ciki, haka take tsalle tana farin ciki haɗe da kukan farin ciki, kamar zata rungume shi domin sauran kaɗan ta rungume shi sai kawo ta juya ta sake rungumar Inna... Tana faɗin "Ya Allah! Na gode, na gode..! Inna! Inna! Wannan duk ya faru saboda soyayya ne?!..." Inna ta shafa kanta tana murmushi. A wannan lokacin suka ji motsin mutane. Sai ga wasu dattijan mata biyu sun bayyana daga cikin corridor. Suna sanye da uniform masu tsabta, kowannensu da nutsuwa a fuska. Maleekh ya nuna su da hannu. Yana faɗin "Waɗannan su ne masu aikin gidan gaba ɗaya. Su zasu kasance tare da ku, ki ɗauke su kamar uwaye." Amal ta kalle su cikin mamaki da farin ciki. Idonta ya sake cicciko da hawaye. A zuciyarta ta ce: "Wannan Maleekh… ni kaina ban san me zan ce game dashi ba. Allah ya sani…" Da sallama da girmamawa, dattijan mata biyun masu aikin gidan suka ƙaraso kusa da Amal. Dukansu suna ɗauke da murmushi irin na masu hidima masu gaskiya. Ɗaya daga cikinsu mai ƙiba kaɗan ta yi gaisuwa cikin ladabi: "Sannu da zuwa, Hajiya Amal. Munji daɗin zuwan ki. Daga yau za ki ɗauke mu tamkar ‘yan uwa. Ba aikin gidan kawai muke ba, muna nan ne don mu kula da ku da gaskiya da zuciya ɗaya." Ɗayar itama ta ɗora da cewa: "Ni sunana Goggo Rabi, ita kuwa wannan ita ce Goggo Hauwa. Mun daɗe muna hidima a gidajen manyan masu kuɗi a Abuja, amma yau wannan shi ne karon farko da muke jin daɗin zama gidan da ya dace sosai. Zamu kula da ke da Inna kamar iyayen mu. Ki kwantar da hankalinki." Amal ta kasa boye farin cikinta. hawayenta na zuba cikin murmushi. Amal ta ce "Na gode sosai, Allah ya saka muku da alheri. Wallahi ban san yaya zan nuna godiyata ba… Amma zan ɗauke ku kamar iyaye na..." Maleekh da ya tsaya gefe yana kallon ikon Allah, murmushi kawai ya yi. Bai ce komai ba sai ya ƙara jin daɗin ganin Amal cikin farin ciki. Bayan sun zauna na ɗan wani lokaci, Amal ta fara nuna sha’awar ta ga dukkan tsararren gidan. Maleekh ya lura da hakan, ya miƙa hannu yana kallonta cikin kulawa: "Zo, Amal. Bari na nuna miki gidan ki daga yau." Ta yi dariya mai cike da kunya, ta miƙe ta kama hannunsa cikin nutsuwa. Suka fara zagaye cikin gidan. → Babban Falon Gida: Babban falo ne mai faɗi da tsayi. An ƙawata shi da luxury Italian sofas, an jera su a geometric design. Babban chandelier mai sheƙi yana rataye a rufin sama mai tsawo, yana haskawa tamkar rana ta sauƙo. TV mai faɗin bango yana manne a gaban su tare da sound system mai cike da ƙarfi. Amal ta tsaya tana girgiza kai cikin mamaki. Amal cikin zuciyarta ta ce "Wannan gidan da kaɗan gidan su Maleekh ya fishi tsaruwa..." → Kitchen: Kitchen ɗin kuma tsararre ne irin na zamani. Granite countertops, microwave, oven, coffee machine da duk wasu kayan girki na zamani suna cikin tsafta da tsari. Goggo Hauwa ta nuna mata kowanne bangare, tana cewa: “Nan ne gidan ki, duk abinda kike buƙata yana nan.” → Upstairs: Suka haura bene, Amal tana jin ƙamshin flowers da aka tanadar a cikin hallway. A gefen hagu akwai guest rooms guda uku, kowanne da toilet. A dama kuwa akwai library mai ɗauke da littattafai daga turai har da na larabci, sai ɗakin hutawa da ya sha kayan alatu.. → Bedroom ɗinta da aka tanadar. A ƙarshe suka isa wani ɗaki mai kama da ɗakin sarauta. Bed ɗin king-size ne, an yi masa canopy da curtains masu siliki. Ɗakin ya sha kyawawan paintings, sai wardrobe na glass da aka shirya mata kayan da aka siya daga supermarket... Amal ta tsaya tana rufe da fuska cikin farin ciki, hawaye na bin kuncinta cikin murmushi. Ta ce "Wannan duk saboda ni ne, ya Allah!..." Inna ta shigo daga baya tana dariya, ta ce: "Ki gode wa Allah, ki gode wa Maliku. Wannan duk bai yi miki komai ba idan kika cigaba da kasancewa mai kirki da biyayya." Amal ta juya tana kallon Maleekh. Idonsu suka haɗu. Numfashinta ya tsaya cak. Taji kamar ta ce masa: “Kai ne Leekh ɗina.” Amma ta daure, ta janye idonta cikin kunya. Maleekh kuwa ya juya da murmushi mai cike da ɓoyayyen nufi. A zuciyarsa ya ce: "Kada ki manta, Amal… duk wannan kyautar, akwai fansa a bayan sa.".... NEXT NEXT NEXT... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 25 to 26 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Bayan ya tabbatar da cewa Amal da Inna sun zauna lafiya a cikin sabon gidan da ya mallaka musu, Maleekh ya juya ya koma gida. Zuciyar Ammy har yanzu cike take da nauyin bacin rai. Da ya shiga falo ya tarar da ita zaune akan sofas tana fuskantar plasman. Sai da ya zauna a gefenta ya kama hannunta cikin ladabi sannan ya furta: “Mom, ki yafe mun. Na ga halin da kika shiga saboda Amal, amma na tabbatar da cewa daga yau ba zan sake sa ki cikin kunci saboda ita ba..” Ammy ta ɗago ido ta kalle shi, tana nazarin maganarsa. “Kana nufin ba za ka sake ɗora ta a kan zuciyarka ba, Maleekh?” Ya jinjina kai cikin nutsuwa, muryarsa na fita da yanayin rarrashi. “Ina bada mahimmanci a soyayyarki Mom, wannan karon na yi abin da ya dace. Amma ki fahimce ni, ba zan iya rabuwa da ita ba. Ko da me zai faru, zuciyata ta amince da ita.” Shiru ya ratsa tsakanin su. A zuciyar Ammy, akwai sassaucin rai, amma tunanin alƙawarin da tayi wa Farha na Aura mata shi sun riga sun yi katutu. Duk da haka ta ce da ƙasa-ƙasa: “To shikenan, Allah Ya kyauta. Amma ka sani, idan ta ci amanarka… ba zan taɓa yafewa ba, tin da ka nuna ban isa na rabaka da Amal ba amma inaso ka sani cewa bazaka ƙi Auran Farha ba..." Maleekh ba yanda ya iya haka ya tashi ya nufi part ɗinsa... 🌹 Tun daga wannan rana, soyayya mai zafi ta shiga tsakanin Amal da Maleekh. Amal ta fara samun kwanciyar hankali, zuciyarta ta ji sabuwar rayuwa ta buɗe gare ta. Idan Maleekh bai zo ba, to tabbas za su yi waya har zuwa ƙarfe sha biyu na dare... Sai dai… duk da wannan kulawa da gaskiyar soyayya da yake nuna mata, a zuciyar Maleekh akwai wani abu da ba ya iya fadar wa kowa. Duk lokacin da ya rungumu Amal cikin ƙauna, sai wani muryar zuciya ta yi masa ƙira: “Ka tuna, wannan soyayya ba ta kawar da manufarka ba. Fansar ka har yanzu tana nan.”.. Bayan cika wata guda da zamansu a Abuja, soyayya ta fara ƙara ƙarfi tsakanin Amal da Maleekh. Duk da cewa akwai sirrin gida da bai bayyana ba, har yanzu babu wanda yasan Maleekh ya siya wa Amal gida... A yau kuwa, Maleekh yana cikin ofishinsa, yana jingina da kujerar executive, yana kallon files a gaban laptop ɗinsa. Da Bluetooth a kunnensa yana waya da Amal, muryarsa cike da kasala ya ce: “Amal, yau kam na wuni ofishin nan. Tun safe har yanzu ban motsa ba. Kuma fa yunwa kamar zata kashe ni.” Amal ta yi dariya a ɗayan ɓangaren wayar, ta furta cikin shagwaɓar soyayya: “Tin da kai baka iya jiran girkin wata mace sai nawa. To ka kwantar da hankalinka, bari na haɗa maka delicious food da hannuna, zan kawo maka yanzu.” Maleekh ya rufe ido da murmushi, zuciyarsa na bugawa da farin ciki. Daman haka yake son ji domin yana son cin girkin Amal mai daɗin gaske... “Yawwa tawan wallahi wannan shi ne burina. Ina jiran ki.” Wayar ta yanke, shi kuma ya cigaba da kallon agogo, yana jiran zuwanta kamar wani yaro mai jiran a sauƙe abinci... Bayan lokaci mai tsawo, sai yaji knocking a ƙofar office ɗin. Da kasala ya ce: “Yes, come in.” Ƙofar ta buɗe a hankali, sai ga Farha ta shigo cikin shigar riga da wandon jeans na kanty, ta sha kwalliya tana ɗauke da basket ɗin kulolin abinci. Ta yi kyau matuƙa, sai ƙamshin turare take... Maleekh da ganinta sai ya miƙe tsaye, fuskarsa cike da mamaki da rashin jin daɗi. “Farha? Me ya kawo ki nan?” Farha ta ɗan bubbuga ƙafafunta, kamar wata yarinya mai jin daɗin shagwaɓa, sannan ta ce: “Kai Ya Maleekh, kenam ba zan iya zuwa inda kake ba? Naga tun safe baka dawo gida ba, na ƙira PA ɗinka yace har yanzu kana office. Na san yunwa kake ji, shiyasa na haɗo maka girki na kawo.” Ta miƙa basket ɗin tana murmushi. Maleekh ya kawar da fuska gefe, zuciyarsa na tafarfasa ya ce “Farha, ki koma da abincinki. Ni dai na ƙoshi. Kuma ban ce ki kawo min girki ba. Wane irin abu ne haka?” Farha ta matso kusa, idonta cike da hawaye na shagwaɓa ta ce “Haba Ya Maleekh, kasan ina sonka sosai. Ba zan bari ka zauna da yunwa ba.” Maleekh ya dafe kansa da ɓacin rai ya ce “Na ce ki koma da abincin nan! Ko yau na saba kaiwa wannan lokacin ban koma gida ba? Don Allah Farha ki daina tada mun hankali. Please join yourself.” Ya ƙarasa yana ɗaga muryarsa... Kafin rigimar ta lafa, sai suka ji ƙofa ta turo da sauri. Security ɗin ofishin ya shigo cikin ladabi ya ce “Sir, akwai baƙuwa a waje. Ta ce tana da appointment da kai.” Da zarar Maleekh ya ji haka, zuciyarsa ta yi tsalle, ya san Amal ce. Ya ɗaga hannu yana nuna Farha da basket ɗinta. “Daga yau ku daina bari kowa ya shigo mun office haka ba tare da izini ba. Ko wannan (ya nuna Farha), ko kuma waccan. Idan na ce ku bari ne za ku bari. Otherwise, kar ku sake.” Security ya gyaɗa kai cikin girmamawa, sannan ya juya. Sai ga Amal ta bayyana a ƙofar ofishin, hannunta ɗauke da kulolin abinci, da murmushi a fuskarta. “Assalamu alaikum.” Cikin nutsuwa ta shigo, amma tana ɗaga kai ta kalli Farha tsaye, tana riƙe da basket ɗinta. Amal ta dakata cak, zuciyarta ta ɗan buga, tana kallon Farha da mamaki da tsoro a lokaci guda. Farha ta haɗiye miyau, ta furta cikin ƙiyayya: “Kai kai kai! Ashe wannan yarinyar bata koma inda ta fito ba? Wannan matsiyaciyar ƴar gari, ubanta me take a Abuja? Kenan Ya Maleekh har gida ka kama mata a nan Abuja?” Amal ta runtse ido da ƙarfi, kafin ta buɗe baki, Maleekh ya furta. “Farha, wannan bai shafe ki ba. Don Allah ki fita daga ofishina yanzu.” Ya nufi Amal da murmushi, yana karɓar basket ɗin hannunta. “You’re welcome abar ƙauna. Fatan kin haɗa min wannan girkin da ɗanɗanon ki.” Amal ta yi murmushi a hankali, muryarta cike da soyayya: “Na kawo maka irin wanda kafi so. Fatan zaka ci da ɗanɗano.” Farha ta ƙara haɗiye zuciya, idonta cike da ƙiyayya. Amal kuma ta juya tana kallonta da tsananin kishi, ganin yanda Farha take ta harararta yasa itama ta mayar mata da martanin hararar sannan ta ce “Ki sani, yanzu ba a gidan ku nake zaune ba. Ki kama kanki, domin Amal bata rasa abin faɗi. Tambayi kowa ki ji wacece Amal Voice.” Farha ta yi ƙoƙarin danne fushinta, a hargitse tazo wuce ta bugi kafaɗar Amal da ƙarfin tsiya sannan ta buɗe ƙofar da ƙarfi ta fice. Ƙamshin turarenta ya bi bayanta.. Amal ta juya tana kallon Maleekh, da murmushi a fuskarta, duk da cewa zuciyarta tana tsalle-tsalle da kishi. Shi kuma ya tsaya yana kallonta, zuciyarsa ta ji daɗin ganin yadda ta tsaya kai tsaye ta kare kanta a gaban Farha. Bayan Farha ta fice daga ofishin cikin ƙiyayya, wurin ya dawo da nutsuwa. Maleekh ya saki ajiyar zuciya, sannan ya ɗauki basket ɗin abincin da Amal ta kawo, yana murmushi yana kallonta ya ce “Na saba da irin fitinun Farha. Amma yau na ji daɗin yadda kika tsaya ki ka bata amsa. Amal, kin burge ni sosai.” Amal ta lumshe ido, fuskarta cike da jin kunya da farin ciki ta ce. “Ni dai bana son ta ci gaba da shiga tsakanina da kai. Na san kai mutum ne da kowa ke so, amma ni bazan yarda a raina ni ba..” Maleekh ya ɗan matsa kusa da ita, yana kallon idonta kai tsaye. Hannunsa yasa yana buɗe kulolin abinci ɗaya bayan ɗaya. Ƙamshin miyan taushe ya cika ɗakin... Maleekh ya ce “Masha Allah… girkin nan da kanki kika haɗa shi? Na rantse, wannan shi ne mafi daɗin gift da aka taɓa kawo mun.” Ya ɗauki spoon, ya ɗan ɗibo tuwo da miyar taushe mai kyau, ya miƙa mata kai tsaye yana faɗin “Come on, open your mouth. I want to be the first to taste this with you.” Amal ta yi murmushi tana girgiza kai. Ta ce “A’a, kai dai ka fara. Ni ba zan iya cin abinci haka a ofishinka ba, idan wani ya shigo fa?” Maleekh ya yi dariya, yana ɗan danna spoon ɗin a gaban bakinta. Yana faɗin “Ba wanda zai shigo. Kuma idan suka shigo, sai su ga yadda masoyiyata ta fi kowacce mace a duniya.” Cikin jin kunya da sanyi, Amal ta buɗe baki a hankali, ya saka mata spoon ɗin. Yana kallonta sosai har sai da ta haɗiye. Lumshe ido tayi tana faɗin “Hmmm… ai na ce maka zaka ji daɗin sa. Amma ya Maleekh, ka dena irin wannan magana da kake yi, zuciyata tana tsalle kamar zata fito daga kirjina.” Maleekh ya yi dariya cikin tsantsar shauƙi, sannan shi ma ya ɗauki spoon ya ci. Ya lumshe ido yana jin ɗanɗanon abincin. “Wallahi Amal, da za a bani damar zaɓen abincin duniya, sai dai na zaɓi wanda kika girka. This is heavenly.” Ya furta yana santy.. Amal ta ɗan sunkuyar da kanta, tana murmushi. Ta ji wani irin ƙarfi a zuciyarta, tana jin soyayyar Maleekh ta wuce dukkan tunaninta. Suka ci gaba da cin abincin tare. Wani lokaci shi ke feeding ɗinta, wani lokaci kuma ita ke ɗaukar spoon ta miƙa masa. Suna hira mai daɗi da tsokanan junansu... A ƙarshe, bayan sun gama, Maleekh ya jingina da kujera yana kallonta. Ya furta “Amal, kin san me yasa nake so in kasance kusa da ke kullum? Domin idan na kasance tare da ke, komai na duniya ya zama kamar baya da muhimmanci. Ni da ke kaɗai nake gani.” Idon Amal ya kaɗa da hawaye, ta ji kamar ta rungume shi a nan take, amma ta danne kanta. Ta ce cikin murya mai sanyi: “Ni ma haka nake ji. Ina jin kamar duk duniya babu abinda nake so face kasancewa tare da kai.” Shiru ya ratsa tsakaninsu, sai kukan zuciya da bugun numfashi. Amma dukansu biyu sun san cewa soyayyar da ke tsakaninsu ta fara shiga wani sabon matsayi da ba zata taɓa komawa baya ba… Cikin wannan lokaci zuciyar Maleekh ta fara sauya salo. Duk da akwai wani sirri a boye a ƙirjinsa, sai dai soyayya ta fara hura wutar da bai taɓa zato ba. Ya fahimci cewa kasancewar Amal kusa da shi na sa zuciyarsa ta huce, duk da cewa har yanzu yana da wani ƙuduri na ɓoye a cikin ransa. Amal kuwa ta fara jin wani irin nishaɗi da kwanciyar hankali fiye da da. A lokuta da bai samu ya zo gidan nata ba, sai wayar su ta ɗauki dare suna hira da dariya kamar sabbin masoya da suka yi asarar shekaru da dama ba tare da sanin juna ba... Da safe idan Amal ta farka, zuciyarta kan cika da farin ciki, ta ji kamar komai na duniyar ya tsaya cak domin jin muryar Maleekh. Haka shi ma idan ya shige cikin aiki, bai da sukuni har sai ya ji labarinta. Wannan kusanci ya zama tamkar sabon babi a rayuwarsu. Amma akwai wani zazzafan ƙuduri da Maleekh ke ɓoyewa, wanda shi kaɗai ya san yadda zai bayyana nan gaba. Farha tana komawa gida ta fara ihu, tayi wurgi da basket ɗin kulolin abincin da ta kawo, suka watse a ƙasa. Ammy ce ta fito da gaggawa tana tambayarta cikin tashin hankali: “Farha meya faru haka? Me yasa kike ihu kamar wacce aka ci zarafi?” Farha tana kuka tana sheshsheka tace: “Ya Maleekh bai yi mun adalci ba Ammy, ya fifita wata a kaina? To wallahi bazan yadda ba!” Ammy ta ɗan runtsa idanu kafin tace: “Wace yarinya ya fifita a kanki? Ki faɗa min gaskiya.” Farha tana huci tana share hawaye ta ce “Wacece inba wancan matsiyaciya ba?” Ammy ta ɗaga gira a rikice ta ce “Wa kuma?!” Farha ta tura baki cikin jin haushi tace: “Amal ƴar jarida. Ya nema mata gida anan Abuja Ammy! Kuma kullum take kai masa abinci office…” Ammy ta dafa ƙirjinta da hannu biyu, fuskarta ta nuna firgici, ta furta da ƙarfi: “Meeeeee? Ya nema mata gida? Shi Maleekh ɗin? Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Abun da zai yi mun kenan? Yau sai ya dawo ya same ni, sai nayi maganinsa!” A wancan ɓangaren kuma, Maleekh bayan sun gama lunch da Amal, sun sha soyayyarsu cikin annashuwa, sai suka fita tare. Shi ya kaita har gida da motarsa. Sai da ya shiga ya gaishe da Inna cikin ladabi kafin ya juya gida da daddare, misalin ƙarfe 8 na dare lokacin da bai saba komawa ba... A falo kuwa Ammy ce take zaman jiran dawowarsa, zuciyarta da ƙuna.. Da ya shigo da motarsa ya ajiye a wurin parking, sannan ya nufi compound ɗin gidan, ya shiga falo da sallama yana riƙe da jakar office ɗinsa... Ammy tana jin sallamar tasa, tayi saurin miƙewa, ta tsaya cak tana kallonsa kafin ta fara masifa: “Wato Maleekh ban isa na faɗa maka ba kenan? Ashe duk ladabin da kake nuna min ƙarya ne? Meye ya zaunar da Amal a garin nan? Har tana kai maka abinci? Shikenan ta zamo dadironka?” Maleekh ya ja numfashi, daman yasan dole Farha zata sanar mata. Ya dubeta a hankali yace: “Mom, ba zaman dadiro nake da ita ba. Kin fi kowa sanin ɗanki, ba manemin mata bane. Kar ki ɗora min wannan shaidar, dan Allah.” Ammy ta girgiza kai cikin tsawa: “Oh to me yasa ka nema mata gida anan Abuja?!” Maleekh ya sauƙe numfashi mai nauyi sannan yace: “Na siya musu gida ne ita da kakarta.” A ruɗe Ammy ta ɗaga murya: “Ka siya musu gida? Maleekh kasan me kake faɗi kuwa? Anan Abuja har kayi kyautar gida?” Maleekh ya kalli gefen bango kafin ya mayar da kallonshi gareta: “To Ammy, meye amfanin dukiyar da bazaka kyautar da ita ba, sannan bazaka sadakar da ita ba? Amal marainiya ce, bata da iyaye. Daga ita sai kakarta. Gidan da suke ciki a Kaduna gidan haya ne. Please Mom, ki bar ni na taimaki waɗanda basu da ƙarfi.” Ammy ta tafa hannu cikin huci: “To idan kana son kyautar gida, sai a nan Abuja? Meyasa bazata cigaba da zama a Kaduna ba? Ko dole sai ita zaka yiwa kyautar?” Maleekh ya girgiza kai da sanyin murya ya ce “Ina kyautata ga duk wanda na ga dama Mom. Kafin Amal, nayi kyautar dukiya fiye da adadi. Ba abinda ya ragu a hannuna. Allah bai bani arziki don in sa a gaba naita kallo ba. Ki yi haƙuri, biyayya zan ci gaba da yi miki a matsayin mahaifiyata. Amma kada ki shiga hurumin abinda zan kyautar da shi cikin dukiyata. Ni ba bin mata nake da dukiyata ba. Ba shaye-shaye nake ba. Ba gidan club nake zuwa ba. Ba safarar miyagun kwayoyi nake yi ba. Shiyasa kullum Allah bai hanani ba. Kuma dukiyata kullum ƙaruwa suke, ba raguwa ba.” Sai ya ɗan ɗaga murya cikin ƙarfin hali: “Zan yi kyauta, zan yi sadaka, zan yi zakka. Duk garin da na zagaya naga basuda masallaci zan gina musu. Zan tono rijiya ko in saka fanfoo. Lokacin layya waɗanda basu da hali zan raba musu. Duk ba saboda riya ba. Kuma ba kowa yasan irin abubuwan da nake yi ba, ko ke baki sani ba sai yanzu da nake gaya miki. Gida kuwa, ba Amal kaɗai ba, duk wanda nayi niyyar taimaka masa da gida zan yi. Ko a England ne, indai inada hali zan yi. Saboda haka ku gani kawai ku yi shiru.” Ammy tana huci kamar zata yi kuka tace: “Uhmmm! Amma Amal dai saboda soyayya kayi mata.” Maleekh ya murmusa cikin ƙarfin hali: “Kusan haka. Abinda nake so dole na kyautata masa. And so what idan ina

Chapter 17 of 62