ta ce "Allah ne ya haɗa ni da Maleekh..."
Farha ce ta kawo hannu zata mari Amal, Amal tayi saurin riƙe hannunta tare da faɗin
"Kada ki kuskura ki mare ni, koda wasa...idan ita Ammy ta mare ni tasha to ke baki isa ba..."
Ammy cikin tsawa tace "to ko nima zaki rama ne?..."
Amal tace
"ke Mahaifiyar Maleekh ne, Mahaifiyarsa kuma tamkar Mahaifiyata ce, ina girmama ki..."
Kafin Amal ta ƙarasa Ammy tayi saurin dakatar da ita, tana faɗin
"kull....Kada ki kuskura ki ɗauke ni a matsayin mahaifiyarki domin ni ban haifi matsiyaci ba..."
Farha ta ce
"saboda rashin kunya har da riƙe mun hannu na kawo miki mari koh? To bari kiji nafi karfinki, kuma ko kasheki nayi a gidan nan babu abinda za'a mun...Sai dai ƙarin matsayi..."
Arfat itama ta fara mata, tana mata wulakanci, tare da kwatanta ta da "yar kasuwa marar galihu...".
Islam, wacce tunda farko bata ce komai ba, ta shiga tsakaninsu tana faɗin
"Don Allah ku daina. Wannan da kuke yi babu amfani, sai dai ku ɓata wa Yayana Maleekh rai."
Ammy ta ɗaga hannu tana girgiza kai cikin tsawa:
"Wallahi yau sai Maleekh ya zaɓa a tsakani ni da ke! Ni ba zan zauna da ke a matsayin suruka ba!"
Farha ta yi dariya tana tafa hannuwa ta ce
"Ki shirya tafiya Amal. Wannan gida ba naki bane, ni ce uwargida a nan!"
Amal ta kalle ta cikin bacin rai, ta ce:
"Farha, mijin da Allah bai rubuta miki ba, ba zaki taɓa samu ba. Kuma mijin da Allah ya rubuta a gare ki, babu wanda zai iya kwace shi. Zan jira Maleekh ya dawo domin bazan cigaba da zama a gidan nan ba, ku kwantar da hankalin ku..."
Daga nan ta wuce ɗakin da aka ajiye ta.....
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 21 to 22
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
A cikin babban office nasa mai yalwa da haske, Maleekh yana zaune akan kujerarsa ta Executive, yana juyawa a hankali tare da zuƙar shisha, yana wani mugun murmushi ta gefen baki. A gabansa kuwa akwai manyan screens guda biyu, ɗaya yana nuna masa graphs na business ɗinsa, ɗaya kuma live CCTV footage na gidan su.
Sai ga PA ɗinsa ya shigo da takardu a hannu. Yana kallon boss ɗinsa cikin mamaki, saboda murmushin da yake yi.
PA Ya ce
“Boss, yau naga kamar kana cikin farin ciki… ko akwai wani sabon deal?”
Maleekh yana jinjina kai, ya ɗan ja shisha sannan ya ce
“Eh, akwai deal mafi girma fiye da kowanne. Amal ta zo Abuja, ta nemi sulhu, ta kuma amince da soyayyata. Yanzu haka tana gidan mu.”
PA cike da damuwa ya ce
“Amma Boss, kasan fa cewa Hajiya da Farha da sauran ’yan gidan basa ƙaunar ta. Za su iya yi mata duka ko wulakanci. Ka tabbatar da hakan?”
Maleekh yana dariya marar sauti, ya ɗan zazzaro ido ya ce
“Na tabbatar. Shi yasa na kaita gidan. Inaso suyi kaca-kaca da ita. Hajiyata fa ba kanwar lasa bace, Farha kuma ta fi kowa kishin banza. Arfat kuwa, rashin kunya ne sunanta. Sai dai Islam… ita kaɗai ce mai tausayin abin da nake so. Amma da tasan abinda ke cikin raina na tsanar Amal, da ita ma zata tsane ta.”
Ya ɗan matsar da kujerarsa gaba, ya danno wani button, footage na Amal tana tsaye a falon gida tare da Arfat da Farha suka bayyana akan screen. Ana jiyo su suna mata masifa. Maleekh ya kalli PA yana murmushi ya ce
“Ka gani? Wannan shi nake so. Ina so su gasa ta da wulakanci, sai dai ni in fito a gabanta a matsayin mai kare ta. A haka zata ƙara manne mun ɗari bisa ɗari. Daga baya kuma in jefa ta cikin wuta, in buga wasan ball ɗina da ita. Wannan shine plan ɗina.”
PA ya lumshe ido yana jinjina kai tare da faɗin
“Boss… wallahi ka fi kowa wayo. Amma fa ta yi babban kuskure da ta dawo wurinka. Yanzu dole ne ta gane babu gudu babu ja da baya.”
Maleekh yana kallonsa tare da jan kunne ya ce
“Karka manta, babu wanda yasan wannan game sai ni da kai. Idan wani ya ji wannan sirri daga bakinka… uhmm! zaka iya tuna yadda na gama da abokin nan nawa wancan shekarar?”
PA ya girgiza kai da sauri, jikin sa har ya ɗan ɗauki karkarwa ya ce
“A’a Boss! Babu wanda zai ji daga bakina. Kai kaɗai ne boss ɗina har abada.”
Maleekh ya sake yin la’anannen murmushi, yana juyi akan kujerarsa, shisha a hannu, footage na Amal a gaban sa.
Maleekh a hankali, kamar yana magana da kansa ya furta
“Amal zata ji soyayyata a fili… amma a ɓoye, zan jefa ta cikin wuta har sai ta zama abinda nake so.”
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Amal in her Room
Amal tana zaune a ɗakin da aka tanadar mata. Ɗakin kuwa ba wani mai yalwa ba ne idan aka kwatanta da sauran d'akunan gidan, amma ya fi mata komai tunda tana cikin ƙasaitaccen gida....
Tana zaune akan gadonta ta jingina kanta jikin bango, idanunta sun kumbura saboda kuka. Hannunta na riƙe da hijab ɗinta domin bata fiye cire shi ba, kullum yana jikinta, tana murza gefensa kamar zata samu nutsuwa daga hakan...
Amal muryarta a hankali, tana magana da kanta...
“Me yasa kowa a gidan nan baya sona? Ko Ammy bata tausaya mun… Farha kuma sai kishi dani. Arfat kuma sai rashin kunya. Wayyo Allah na, na shiga gidan da ba kowa ke so na ba.”
Ta ɗan ɗaga ido tana kallon sama, hawaye na zubo mata ta ci gaba da faɗin .
“Amma ban da Maleekh. Shi kaɗai ne ya tsaya mun, yake kare ni. Duk da abinda ya faru a baya, yanzu nake tabbatarwa cewa yana sona da gaske. Da babu shi a gefena, da tuni zuciyata ta fashe da baƙin ciki.”
Ta ɗan kwantar da kanta bisa filo, tana tuna lokacin da Maleekh ya rungume ta a falon ofishinsa, ya ce ba zai gujeta ba. Wani ɗan murmushi ya bayyana a fuskar Amal duk da cewa tana cikin hawaye.
“Zan jure komai saboda shi. Ko wane irin wulakanci suka min, ina da tabbacin Maleekh zai tsaya a bayana. Shi ne hasken zuciyata.”
A haka ta lumshe ido tana kuka a hankali, zuciyarta cike da soyayya da amincewa ba tare da ta san cewa wanda take ganin mai tsaronta ne babban mai jefa ta cikin ramin wulakanci ba.
In the Corridor
A waje kusa da ƙofar ɗakin Amal, Farha tana jingine da bango hannunta riƙe da glass cup ɗin drink, tana sauraron maganganun Amal da take yin su a fili cikin kuka...
Farha ta lumshe ido tana saurare, wani mungun murmushi ya bayyana a fuskarta.
A hankali, tana magana da kanta ta ce
“Haka nake so… ki fara jin zafin da gidan nan zai miki. Wannan ba wai farkon ba ne, Amal! nan ne asalin azabarki. Ni kuwa sai na tabbatar kin gudu kin bar min Maleekh gaba ɗaya.”
Ta ɗan ja numfashi, sannan ta juya da isa da gadara kamar wata sarauniya, ta nufi sashen ta...
Bayan dawowar Maleekh daga Office da yamma, ya ƙaraso gidan cikin nutsuwa. Ganin bai tarar da kowa a falo ba yasa ya nufi sashen Amal, knocking yayi tare da tura ƙofar a lokaci guda, bai tsaya jiran bada izini ba, yana shiga ya tarar da ita zaune a kan gado, kanta lullube da pillow tana sharar kuka kamar ƙaramar yarinya...
Cikin dabara ya ɗan tsaya a bakin ƙofa yana kallonta, murmushin mugunta ya wuce a zuciyarsa kafin ya daidaita fuskar sa ya saka annuri. Ya shiga a hankali yana faɗin:
“Amal… kina kuka kuma? Waye ya taɓa min ke a gidan nan?”
Amal ta ɗago da idonta da suka yi jawur saboda kuka, ta share hawayenta da sauri...
Cikin raunanniyar muryar ta ce
“Ban iya jurewa ba, Maleekh. Gaba ɗaya suna kallona da mungun nufi, suna nuna min cewa ban dace da kai ba. Har suna ƙira na da matsiyaciya…”
Sai hawaye suka sake zubo mata.
Maleekh ya ƙaraso kusa da ita ya zauna, ya ɗauki hannunta ya riƙe sosai, yana kallonta ya ce
“Kin san abinda zan faɗa miki? Bazan bar kowa ya hana ni soyayyata ba. Ki daina sauraren su, ki tsaya a kan kalmar da kika faɗa min jiya cewa kina sona. Idan har kina sona Amal, babu wanda zai iya raba mu.”
Amal ta girgiza kai tana hawaye ta ce
“Ina sonka, Maleekh… amma tsoron iyayenka nake ji. Tsoron kar su raba ni da kai.”
Maleekh ya ɗan murmusa, ya matso da ita sosai har ta jingina da ƙirjinsa ya ce
“Babu wanda zai iya rabani dake. Ki tabbatar da wannan. Ki ɗauki zuciyata tamkar garkuwarki. Har abada, ni ne zan kare ki.”
Ya ɗora hannunsa a kanta yana bubbuga bayanta cikin rarrashi. Amal kuwa ta sake fashewa da kuka na farin ciki, tana jin kamar wannan kalaman sun share mata duk wata damuwa...
A zuciyar Maleekh kuwa, yana wani irin dariyar mugunta tare da maganar zuci.
“Haka nake so, Amal. Ki miƙa min zuciyarki gaba ɗaya. Lokaci yana zuwa da zaki gane ni ba abin da kike zato ba.”
Sai ya share fuskar da murmushi mai taushi, yana ci gaba da rarrashin ta kamar masoyin gaskiya.
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Washegari da safe, Maleekh ya shirya cikin shigar alfarma mai kyau. Yana tare da Amal a room ɗinta, cikin sassanyar murya ya ce da ita.
“Amal, yau ba na so ki zauna a gida. Zamu fita tare, mu sha iska, mu ci abinci mai daɗi a waje.”
Amal da farko ta yi shiru tana tunanin ko hakan ba zai fusata iyayensa ba. Amma ganin irin rarrashi da tsananin kulawa a fuskarsa, sai ta amince.
Sun fita da wata motarsa mai kyan gaske, suka je wani babban restaurant mai ɗauke da haske da kiɗa mai laushi. A wajen Amal ta ji daɗin kasancewa tare da shi. Har ta manta da tsangwamar iyayensa.
Maleekh yana murmushi, yana saka ta dariya. Yana tsokanar ta da kalmomi masu daɗi, har sai da zuciyar Amal ta sake gaba ɗaya.
Maleekh cikin murmushi yake faɗin
“Kin ga yadda dariya yake bala'in miki kyau? Wannan dariyar ce ta ɗauke mun hankali. Idan kina kusa da ni, babu wani abu da zai dame ni.”
Amal tana dariya cikin jin kunya ta ce
“Ni dai ina jin daɗin kasancewa tare da kai. Amma gaskiya ban saba irin wannan wuri ba.”
Maleekh ya dafa hannunta akan teburin restaurant, yana kallon ta ido cikin ido ya ce
“Wannan rayuwa tamu ce. Zan koya miki komai a hankali. Ki daina jin tsoro.”
Amal ta yi murmushi cikin hawaye na farin ciki...
Bayan nan suka nufi babban supermarket yayi mata siyayya kala-kala, da dogwayen riguna, da takalma da kayan kwalliya, har da su pants da breziyass da komai abinda ya shafi mata..
Maleekh ganin Amal ta ɗauki sinƙin wani abu kamar dozen ne a ninninke ya sa hannu yana taɓa wa cike da mamaki ya ce.
"Amal ke ɗin me zaki yi da sinƙin bread haka..?.."
Amal tayi dariya tare da faɗin
"Ba fa bread bane, mata ne kawai masu amfani dashi..."
Ya ce. "Kamar ya? Shi ɗin meye ne kenam?.."
Amal ganin yana so ya takurata da wannan question ne yasa ta miƙa masa ba tare da ta furta komai ba...
Ya karɓa yana faɗin
"Yawwa ban na duba koma menene..."
Karanta rubutun jikin yayi sannan ya saki murmushi yana faɗin.
"O hoooo, sai ki ce mun abun ku na taran makwararin jini ne..."
Amal da sauri ta karɓe cikin jin kunya tayi saurin yin gaba, domin akwai wasu matasa har sun juyo suna dariya...
Da haka suka kammala siyayya, Maleekh ya biya duk kayan da suka ɗauka...
Bayan sun dawo gida, Amal ta ji nutsuwa sosai saboda kulawar Maleekh. Amma tun da suka shigo gidan taji wani bugun zuciya...
Ita kaɗai ta shigo falo ta tarar da mutanen gidan a falo...
Ammy wani irin harara ta wurga mata cike da baƙin ciki ta ce
“Kin yi ta yawon banza da shi ko? Wannan dai shine aikin ki, jan ɗana ya manta da iyayensa...”
Farha, wacce zuciyarta ke cike da kishi, ta miƙe tsaye tana kallon Amal da tsantsar tsanarta ta ce
“Ni kam ban san wace irin jaraba ce ke da Maleekh ba. Kin ɗauka soyayyar da yake miki za ta kare ki ne? Ki sani, ni ce wacce za ta zama matar Maleekh, ba ke ba. Ke dai matsiyaciya ce kawai, marar gata.”
Arfat ta ɗan goyi bayan su
tana cewa:
“Amal, kin san wannan gidan ba naku bane. Ki shirya komawa inda kika fito, kafin mu kore ki da kanmu.”
Amal ta yi shiru tana sauraronsu. Amma zuciyarta tana karfafa mata da cewa
“Ina da Maleekh. Shi kaɗai zan dogara da shi.”
Islam dai ta tsaya gefe tana tausayawa Amal, amma bata ce komai ba saboda tana tsoron ɓacin ran mahaifiyarta...
♡
Maleekh ne ya shigo yana riƙe da jakunkuna na siyayya masu alfarma, waɗanda duk wanda ya gansu ya san ba a ƙaramin kasafi aka saya ba. Har lokacin murmushi yake yi, zuciyarsa cike da nishaɗin yadda zai faranta wa Amal rai da sabbin kayayyakin da ya siya mata.
Da ya taka cikin babban falon, abin da idonsa ya tarar da shi ya karyar da farin cikinsa. Amal ce tsaye a tsakiyar falo, Ammy da Farha sun zagaye ta da kalaman wulakanci, yayin da Arfat kanwarsa ke ɗaga hannu cikin tsananin bacin rai, alamar ta kusa kaima Amal duka. Amal kuwa tana tsaye, hannunta a gefe tana ƙoƙarin tattara ƙarfin guiwa, kodayake idanunta sun kaɗa saboda tsananin zafin cin fuska. Islam ce kaɗai ke gefe, shiru kamar wacce ba ta da ikon magana.
Maleekh ya dakata da sauri, idanunsa suka sauya kala. A fusace ya isa tsakiyar falon yana ɗaga murya cikin faɗa:
“What the hell is going on here?!”
Dukansu suka kalle shi. Amal ta juya idanunta suka haɗu da na Maleekh, sai ta sauƙe numfashi mai nauyi, alamun jin daɗin ganin shi.
Farha ce ta fara tsaki tana turo baki ta ce
“Oh, har mata siyayyar kayayyaki koh? Wato wannan ce yanzu har ta zama special?…”
Ammy ta tsunduma cikin magana tana kallon jakunkunan hannunsa cikin ɓacin rai ta ce
“Kai Maleekh, Kana da hankali kuwa? Ka dawo gida da wannan ‘yar banza, har da mata siyayyar kaya masu tsada? Ka manta kai ɗan gidan masu kuɗi ne, ba ɗan gidan talauci ba? Wataƙila ta shirya maka wani laya ne da take shirin mallake ka, to wallahi bokanta bazai taɓa yin aiki a gidan nan ba…”
Amal ta kasa jurewa, zuciyarta ta buga da ƙarfi jin an kwatanta ta da boka, amma kafin ta buɗe baki Maleekh yayi saurin faɗin:
“Enough, Mom! Enough! bazan bari ku wulakanta min ita ba. Amal ba matsiyaciya bace kamar yadda kuke ƙiran ta. Duk wani abu da nake mata daga zuciyata yake fitowa. Kuma ki sani Mom, duk wanda ya ɗaga mata hannu, tamkar ya ɗaga mun hannu ne!”
Ammy ta ce
"And so what idan an ɗaga maka hannun? Ubanka ma ai bai fi ƙarfin a ɗaga masa hannu ba balle kai, to ka kiyaye ni..."
Maleekh ya kawar da fuska gefe ba tare da ya furta komai ba,
Ya kama hannun Amal yana ƙoƙarin jan ta ya nufi saman upstairs da ita...
Arfat ce tayi dariya tana faɗin
“Wow, lallai Amal, kin yi nasara! Amma ki sani ba wannan ke nufin za ki ji daɗin zama a gidan nan ba. Ki jira ki gani…”
Maleekh ne ya juyo a fusace ya zabga mata mari daman a gefensa take...
Arfat tinin ta riƙe fuska tana zunduma ihu...
Farha ce ta riƙe ta tana shafa mata wurin marin, tare da faɗin
"Yanzu saboda wannan matsiyaciyar zaka raunana ƙanwarka?..."
Islam kuwa hannu tasa ta toshe baki tana gusar da dariyar marin da Arfat ta sha...
Ammy kuwa dariya ta yi cikin tsaki tana girgiza kai ta ce
“Maleekh, wallahi baka da hankali. Ka je sama ka ci gaba da wawantarka, amma ka sani wannan ƴar jarida ba zata taɓa zama ‘yar gidan nan da daraja ba. Ni ce mahaifiyarka, na fi sanin abin da ya fi dacewa da kai.”
Maleekh ya juyo yana ƙoƙarin haɗiye zuciyarsa ya ce
“Mom, idan kina son darajata, to ki fara daraja ni ta hanyar daraja wacce nake so. Wannan shine karshen raini da cin fuska akan Amal a gidan nan. I won’t take it anymore.”
Ya ɗauki jakunkunan siyayya, sannan ya ja hannun Amal da ƙarfin gaske ba tare da ya sake kallon kowa ba, Maleekh ya ja Amal suka nufi sama, a wannan lokacin part ɗinsa suka nufa tare...
matakan gilashin beni mai walƙiya suna bayyana tsantsar tsadar gidan. Amal idonta akan glass ɗin benin, gani take kamar zai fashe, just a tsorace take takawa...
Kowa yana kallonsu cike da bacin rai da tsananin kishi, musamman Farha da idonta ya kaɗa saboda tsananin baƙin ciki.
✨ Part ɗin Maleekh’s Area
Bayan sun haura upstairs, Amal ta tarar da wani sashe mai faɗi wanda ya bambanta da sauran wurare na gidan. Wannan part ɗin na Maleekh yana da private sitting room (falo na musamman), wanda aka yi wa ado da farin paint da fitilun chandelier masu launin haske. A gefen falon akwai glass table mai ƙyalli, sofas masu launin grey da cushions masu taushi.
Daga gefen hagu, akwai ƙofar da ke kaiwa master bedroom ɗinsa, wanda shima ke da king-sized bed, bedsheet ɗinsa mai launin fari da launin navy blue mai kyan gaske..
A cikin bedroom ɗin akwai side ɗin walk-in closet mai cikakken shelves na tufafi da takalma da dabam..
A gefen dama kuma akwai ƙofa da ke kaiwa private bathroom, wanda aka gina da tiles masu sheƙi, jacuzzi mai faɗi, da gilashin shower room mai tsada. AC ɗin ɗakin yana busar da sanyi mai ɗaukar hankali, yana haifar da kwanciyar hankali da nishaɗi...
Da suka shigo cikin falon nasa, Maleekh ya ajiye jakunkunan akan glass table, Amal kuwa ta zauna a gefen sofa cikin nutsuwa. Duk da kukan zuciyarta da takaicin wulakancin da ta sha daga Ammy da Farha, sai ta yi murmushi mai rauni tana kallon Maleekh.
Shi kuma ya nufi bedroom ɗinsa domin rage kayan jikinsa. Tunaninsa ya cika da damuwa da fushi, amma ya daddage domin kar Amal ta ji wani tashin hankali.
Yana cikin bedroom ɗin yana sauya kaya, sai ya fito da t-shirt mai sauƙi da trouser. Amma da ya fito, sai ya tsaya cak. Amal ce akan sofa, tana kwance idanunta a rufe gaba ɗaya. Ta miƙe akan kujera tana sharar bacci cikin nutsuwa, gashin kanta ya warware duk ya zubo akan kafaɗarta...
Maleekh ya tsaya yana kallonta, Sanyin AC ɗakin ya lulluɓe ta gaba ɗaya, har take bacci cikin nutsuwa, ba tare da ta damu da komai ba...
Ajiyar zuciya ya sauƙe, ya sunkuya ya ɗauke ta a hankali cikin hannayensa kamar jaririya. Numfashinta mai sanyi yana bugan wuyansa...motsi ta fara yi tana ƙoƙarin gyara kanta a saman kafaɗarsa. A hankali ya shiga cikin bedroom ɗinsa...
Maleekh ya isa kusa da gadon ya kwantar da Amal a hankali, tamkar bai son ta tashi daga baccinta. Ya ja blanket mai laushi ya lulluɓe jikinta gaba ɗaya. Duk da haka, idanunsa ba su iya barin fuskarta ba.
Ya tsaya a tsaye gefen gadon, hannuwansa a aljihunsa, yana kallonta da irin kallon da mutum ke yi wa abu mai daraja wanda bai taɓa tsammanin zai mallaka ba.
A zuciyarsa akwai tarin ƙiyayya, amma a wannan lokacin wani sabon abu ya taso masa, abin da bai iya fahimta ba. Idanunsa suna biye da kowanne ɓangare na fuskarta:
Farar fatar ta mai ɗaukar ido, wacce take da laushi kamar auduga.
Idanunta duk da a rufe suke, girman su da tsawon gashinsu na sa mutum ya ji tamkar za su yi magana koda ba ta buɗe su ba.
Ƙaramin bakinta, tare da launin lips ɗinta mai color ja tamkar sabuwar pomegranate, suna yi masa wani irin kallo koda ba ta motsa su ba.
Gashin girarta mai kauri mai siffar natural, wanda ya yi kyau daidai da surar fuskarta.
Tsayin hancinta madaidaiciya..
Idanunsa suka sauƙa ƙasa, suka tsaya a kan kirjin ta. Breast ɗinta a cike masu girma suna lulluɓe da blanket, amma shaid'an ya shiga masa rai. Da sauri ya ɗauke kansa cikin ƙarfin hali, zuciyarsa tana wani mummunan bugawa...
Shape ɗin hips ɗinta da ya bayyana cikin lulluɓin blanket ya sa shi ƙara yin shiru yana danne zuciyarsa.
Kyakkyawar surarta ta zarce misali, irin kyan da yake haɗe da na Indian beauty...
Maleekh ya ja numfashi mai nauyi. Ƙila zuciyarsa ta fara karkata gareta....girgiza kai yayi tare da matsawa daga jikin gadon, yana jin kamar idan ya ƙara tsayawa kusa da ita, zai rasa ikon kansa...
“Ba yanzu ba… fansa ta fi wannan muhimmanci.” Ya furta a zuciyarsa.
Sai dai, idanunsa sun ƙi barin jikinta...
Maleekh ya tsaya gefen gadon, yana kallon Amal da ta yi nisa a baccin ta. Numfashinta mai sauƙi yana fita cikin nutsuwa, tamkar ba ta taɓa shiga cikin wahala ko tashin hankali ba.
A zuciyarsa ya fara magana da kansa:
“Amal… ke ce mace ta farko da ta taɓa tsallake iyakokina, ta mare ni, ta wulakanta ni a bainar jama’a. Na rantse cewa ranar fansa ta ba zata wuce ba. Amma yau… ga shi kina kwance a kan gadona, kina baccin nutsuwa kamar wata sarauniya.”
Ya lumshe ido, ya haɗa hannuwansa ya goya akan kirjinsa..Ya ci gaba da faɗin
“Kina da kyau fiye da misali… farin fatarki, idanuwan nan masu girma, bakin ki mai ɗaukar hankali… komai naki abin sha’awa ne. Amma, Amal… wannan kyau ba zai hana ki biyan fansar da kika jarabtar da ni da ita ba.”
Ya ƙara matsawa kusa, idanunsa suka tsaya kan blanket ɗin da ya lulluɓeta, yana iya hango siffar jikinta a ƙarƙashin sa.
“Na san duk wani namiji da zai ganki a wannan yanayi zai ruɗu ya manta da komai, amma ni… Maleekh… ban saba barin mace ta ci karfina ba. Sai dai gaskiya Amal, yau na kasa ɗauke idona daga gare ki. Kamar wanda kika mun sihiri?.”
Ya jinjina kai, ya yi murmushin gefen baki, mai ɗauke da duhu da alamar mugun shiri...
“Zan nuna miki soyayya, zan lulluɓe ki da alheri da kariya… amma duk a fuska ne. A ɓoye kuwa, zan jefa ki cikin wuta. Ki ɗanɗana wahalar da ta fi marin da kika yi min sau dubu.”
Ya yi shiru na ɗan lokaci, yana lumshe idanuwansa cikin nutsuwa, sai daga baya ya furta a hankali, tamkar yana magana da ita amma ba ta jin sa:
“Amal… kiyi bacci, ki huta a kan gadona… domin wannan hutu zai zama farkon hanyarki zuwa cikin azabar da nake shiryawa a zuciya ta.”
Ya ja blanket ɗin da ta ɗan zame, ya rufe ta sosai, sannan ya juya ya fice daga ɗakin da wani irin nauyi a zuciyarsa, nauyin soyayya da yake ƙoƙarin hana shigar sa cikin zuciyarsa, da kuma nauyin mungun fansa da yake ran sa...
Yanayin tsarin bedroom ɗin gwanin burgewa, domin bedroom ɗin ba kawai ɗaki bane, mazauni ne na sarki...
Katafaren gadon king size bed ne, mai frame ɗin Italian mahogany wood wanda aka yi masa zane a gefuna. Headboard ɗinsa an yi shi da leather quilted design mai taushi, wanda fitilar gefen gado (bedside lamp) ke haskawa yana fitar da walwali.
Blanket ɗin farar fata ce mai ɗauke da silk embroidery, pillows kuwa sun cika gadon, manya-manyan masu taushi da ƙananun masu launi daban-daban, suna sa gadon yayi kamar wani gado na princess..
Bangon ɗakin an yi masa marble wall panels na farin dutse, sannan a tsakiyar bangon da gadon ya jingina aka saka babban frame mai ɗauke da painting na art ɗin ocean view.
An yi hidden lighting a saman bangon (ceiling) wanda yake bada hasken mai laushi, yana sa ɗakin yayi romantic.
Ƙasa kuwa Persian carpet ce mai launin ruwan haske, ta rufe tsakiyar ɗakin, yayin da sauran ƙasan Italian marble tiles ne masu kyalli.
An saka manyan windows masu gilashin tempered glass, sai dai an rufe da long
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 62