Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ko kallonta bata yi ba. Amal har zata tafi ta juyo tana kallo Inna, tace "Inna anyi auren Maleekh kuwa?.." Nan ma Inna bata kula ta ba. Ganin inna bazata kulata ba yasa ta girgiza kai zata tafi... Inna ta daka mata tsawa da cewa "Bayan ke kikayi silar kwanciyarsa jinya shine yanzu zakije ki ƙarasa kashe shi koh?.." A firgice Amal ta juya tana kallo Inna. Muryarta na rawa tace "inna ni kuma?.." Inna ta ce "Mutumin da yake burin aurenki, yazo yaji cewa kin zubar da cikin wata huɗu ya kenam? Kowa ya sani, an tallata ki a tv da ko ina, ke ko kunyar fita bazaki ji ba?..." Amal ta ja dogon numfashi sannan ta ce "Koma menene tinda ina da gaskiya, zanje, zan tabbatar shin Maleekh baya sona yanzu ko kuma har yanzu yana sona.." Inna taja tsaki tare da kawar da kai.. Amal ta fice, kai tsaye motarta ta shiga tare da fita daga gidan... Amal ta hau mota jikinta yana kyarma, zuciyarta kamar zata fito daga ƙirji. Hannunta a kan sitiyari sai rawar sanyi yake, idanuwanta sun cika da hawaye amma ta share su da bayan hannunta tana faɗin: "Ya Allah, idan da gaske Maleekh yana sona, ka haɗa ni da shi cikin alheri… kar ma'kiya su rabamu da ƙiyayya. Kar cutar zuciyata ta zama gaskiya..." Yayin da ta ƙarasa bakin asibitin, motarta ta tsaya cak a bakin gate. Security ya matsa kusa yana tambaya, kafin ta ce komai sai ta nuna musu sunanta da sunan Maleekh. Nan take aka buɗe mata hanya. Cikin tsoro da ruɗu ta shige cikin babban building ɗin, ƙafafunta kamar ba ya jikinta. Tana shiga cikin reception ta ce da rawar murya: "Excuse me… ina wajen da aka kwantar da patient ɗin nan, Mr. Maleekh?" Nurse ɗin ta dube ta da mamaki tace: "Kin shigo da ɗan ɗaukar rai ne… ke ce Amal?" Amal ta kasa amsa sai da ta ɗaga kai kawai, zuciyarta ta cika da tsoro. Nurse ɗin ta nuna mata hanyar ward. A hankali Amal ta nufi hanyar, ƙafafuwanta suna jijjiga, hawaye suna tsiyaya a fuskarta. A zuciyarta kalmomi ɗaya ke maimaituwa: "Ya Allah kar ya ƙi ni… kar ya ƙi ni…" Da ta isa bakin ƙofar ɗakin, sai zuciyarta ta tsinke kamar zata tsaya. Hannunta ya tsaya cak a kan handle ɗin ƙofar. Ta ɗauki numfashi tana kuka a ranta: "Ko zai ƙi ni, zan sani yau… zan ji da bakinsa. Tinda Inna ta ce ni ne silar ciwonsa, bari ya gaya min da kansa…" A hankali ta murɗa ƙofar ta shiga... Sai idonta ya sauƙa a kan Maleekh, kwance a gadon asibiti, gaba ɗaya ya rame, yana sanye da oxygen pipe a hancinsa. Amal ta dafe ƙirji tana sauƙe kuka mai ƙarfi. Cikin zuciya ta ce: "Wayyo Allah na, ciwon har ya kai haka? Innalillahiwa’innailaihirraji’un, Ya Maleekh dan Allah kada kace nine silar rashin lafiyarka.." Ta ƙarasa kusa da shi da rawar jiki, ta durƙusa a gefen gadon, ta riƙe hannunsa. Hannu mai sanyi da rauni.. A hankali, kamar wanda yake jin muryar da zuciyarsa ta fi so fiye da komai, Maleekh ya motsa idanunsa. Suka buɗe a hankali, yana lumshe su a slow, sannan suka tsaya kan Amal... Shiru ya cika ɗakin. Na’urar heartbeat yana beep beep beep a hankali. Sai Maleekh ya ɗan motsa leɓensa. Muryarsa ƙasa sosai, amma kalmomin suna ɗan fitowa... "Amal… kina nan?" Amal ta fashe da kuka mai ƙarfi tana faɗin: "Eh, ni ce… ni ce My bee. Na zo… na zo duba ka…" Sai Maleekh ya ƙara lumshe idanuwansa, yana ƙoƙarin yin murmushi mai rauni, ya ce "Ban taɓa daina sonki ba…" Amal ta durƙusa tana riƙe da hannunsa, idanuwanta na cike da hawaye, ta ce: "Ka daina kuka Ya Maleekh, don Allah… ka tsaya ka dubeni, ni ce… ban taɓa daina sonka ba nima..." Sai dai Maleekh ya lumshe idanunsa gaba ɗaya, zuciyarsa na bugawa da sauri. A ƙwaƙwalwarsa sai muryar Doctor ta dawo yanda yake faɗin: "Mr. Maleekh, result ɗin ya nuna cewa Amal ta zubar da cikin wata huɗu…" Zuciyarsa ta ƙara karye wa! Wani irin raɗaɗi ya shige shi fiye da duk wani ciwon jiki da yake ji. Numfashinsa ya ƙara sarkewa, idanunsa suka ƙumbura da hawaye masu zafi.. A cikin ransa ya ke faɗin: “Na yarda da ita… na amince da ita… yanzu kuwa?” Sai hawaye suka kwaranyo masa, ya girgiza kai yana ta faman zubar su. Amal ta firgita, ta miƙe tana share masa fuska tare da faɗin: "Wayyo Allah! Me yasa kake kuka haka? Na baka tsoro ne? Ko jikinka ne ke maka zafi?!" Maleekh ya zame hannunsa daga nata da ƙarfin da ba’a zata zai iya ba. Idanunsa suka canza, suka cika da huci da tsanar da take neman cinye shi. Ya ɗan motsa bakinsa da ƙarfi ya ce: "Ke… me kika yi min? Ke wacece Amal?!" Amal ta tsaya cak, jikinta ya ɗauki rawa ta ce: "Ni? Ni na yi maka me, Maleekh?" Ya lumshe idanuwansa yana ƙoƙarin tattara ƙarfin magana.. "Na ji… na sani… asibiti… result ɗin ki… kin zubar da ciki na wata huɗu! Me kike nufi da wannan? Wane namiji kika aura da har kika yi masa ciki, kika zubar?!" Amal ta durƙusa tana rikicewa ta ce: "Subhanallah! Maleekh, ni fa ba haka bane! Wallahi ba haka bane! Ka yarda da ni… ba gaskiya bane wannan…" Amma Maleekh ya juyo da fuskarsa gefe, hawaye na zuba, zuciyarsa ta cika da haushi da kishi mai ban tsoro. A cikin ransa kalma ɗaya ce ke maimaituwa: "Ta ci amanata… ta ci amanata…" Sai muryarsa mai rauni da tsawa a lokaci guda yana cewa: "Ki fita! Ki fita daga ɗakin nan kafin ki kashe ni da ƙaryar da kike zubawa! KI FITA!!!" Amal ta fashe da kuka, ta juyo da rawar murya tana faɗin: "Na rantse da Allah, ni ba haka bane! Ka yarda da ni Maleekh, wallahi ban ci amanarka ba!..." Ta miƙe da kuka, amma zuciyarta ta kasa barin ɗakin. Ta tsaya a gefen gadon tana kallon shi yana cigaba da zubar da hawaye cikin raɗaɗi, zuciyarta ta karye fiye da tunanin kowa. A daidai lokacin da muryar Maleekh ke ƙara ɗaga ɗaki yana tsawatawa da ƙarfin da bai kamata ba, ƙofar emergency ɗin ta buɗe da sauri. Doctor ɗin ya shigo da nurses biyu a ruɗe. Doctor ya daka-tsawa tare da faɗin: "What is going on here?! Waye ya saka shi magana haka?!" Ya matsa kusa da gadon da sauri, yana riƙe da stethoscope ɗinsa, ya duba hancin Maleekh da kirjinshi. Sai ya juyo yana hararar Amal da fushi ya ce: "Young lady, baki fahimci halin da marar lafiya yake ciki bane?! Zuciyarsa tana a critical stage! Koda kaɗan ba zai iya ɗaukar tashin hankali ba. Idan kika cigaba da tayar masa da hankali, zai iya mutu nan take! Kina son hakan ya faru?!" Amal ta zabura da rawar jiki, ta saki kuka tana girgiza kai ta ce: "Wallahi ban nufin cutar da shi ba, Doctor… ban nufin haka ba…" Doctor ya tsawata mata da ƙarfi cewa: "Sai dai ke kika jawo wannan! Ki fita daga ɗakin nan yanzu! Lafiyar marar lafiya ce a gaba, ba damuwar zuciyarki ba!" Nurses suka matsa kusa da Amal, suka riƙe hannunta cikin tausayawa, suka fitar da ita.. Amal tana cewa cikin kuka mai ƙarfi: "Na rantse da Allah, ban ci amanarka ba Maleekh… Wallahi sai gaskiya ta tabbata, sai Allah ya saka min…!" Ta juya da gudu cikin kuka, ta bar wurin, ƙafafuwanta na jijjiga kamar zata faɗi. Doctor ya kalli Maleekh da idanu masu ƙarfi ya ce da shi: "Ka saurare ni, Mr. Maleekh. Idan baka kwantar da hankalinka ba, zuciyarka zata iya tsaya maka. Ka tuna kai babban mutum ne da rayuwarka take da daraja a gaban iyayenka da jama’a. Idan kana son mutum to ka kiyaye lafiyar ka, idan kuma baka so, ka kwantar da zuciyarka..... Idan baka so ka rayu saboda kanka, to ka rayu saboda waɗanda suke ƙaunarka." Ya nuna nurse ɗaya ya ce da ita: "Ku saka masa oxygen sosai, sannan ku duba ECG. Na ce babu wanda zai sake shiga ɗakin nan sai na bayar da izini!" Nurses suka amsa: "Yes Doctor." Doctor ya sake kallon Maleekh cikin tausayawa ya ce: "Don’t waste your life on anger. Heart is too delicate for that." Ya juya ya fice daga ɗakin, nurses suka cigaba da gyara masa kayan da aka jona. Maleekh ya lumshe idanu yana sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi, amma hawaye na ci gaba da gudana. A zuciyarsa kalma ɗaya ce ke murɗawa: "Na so ta fiye da komai… amma ta ci amanata…". _NEXT! NEXT!! NEXT!!!_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 41 to 42 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 A corridor ɗin hospital Amal ke tafiya tana kuka, hawaye na sauƙa kamar ruwan sama. Gyalen jikinta ta ɗora akan fuska gaba ɗaya, ta kasa ganin inda take nufa. Sakamakon hakan ta buge wani babban mutum da ke tsaye yana waya, takardun da ke hannunsa suka watse ƙasa. Amal a firgice ta dafa ƙirji, ta durƙusa da sauri tana tattara takardun: "Innalillahi! Na shiga uku, don Allah ranka ya daɗe kayi haƙuri wallahi ban lura ba…" Hannunta na rawar sanyi tana miƙa masa takardun cikin ladabi. Shi kuwa mutumin, Abbansu Maleekh ya ɗago yana dubanta. Yana kallon yadda take kuka kamar mara galihu, fuska cike da hawaye, zuciyarsa ta ji tausayinta duk da bai san wacece ba... Abba ya karɓi takardunsa, sannan ya sa hannunsa ya ɗagota a tausashe: "Tashi ki tsaya yarinya, babu laifi. Amma meyasa kike kuka haka?. Me ya same ki haka?.." Amal ta share hawaye cikin ƙaryar ƙarfin hali, tayi murmushi mai ciwo tare da faɗin: "Ba komai wallahi… wata ƙaddara ce kawai. Na gode sosai." Abba ya girgiza kai yana kallonta cikin tausayawa ya ce: "Kada ki yarda damuwa ta raunana miki zuciya. Rayuwa ba ta wuce gwaji ba. Ki roƙi Allah ya kawo miki mafita, domin shi ne mai iko akan zuciya da ƙaddara." Kalamansa sun shige jikin Amal kamar wutar lantarki. Ta ɗan lumshe ido tana jin sanyi a ranta, kamar an shafa mata magani. Ta kasa cewa komai sai dai ta yi masa godiya tana murmushi cikin hawaye: "Na gode ranka ya daɗe, Allah ya saka da alheri." Ta yi gaba tana fita daga corridor ɗin. Abba ya bita da kallo, zuciyarsa na tambaya “Wacece wannan yarinya mai ɗauke da baƙin ciki haka?” Sai ya juya ya nufi ɗakin da Maleekh yake. A harabar hospital, Amal na tafiya a hanzari zuwa motarta. Amma kafin ta isa, sai ta yi kucuɓus da Ammy, Farha, Arfat, da Islam waɗanda yanzu suka shigo asibitin. Ammy ta tsaya cak tana harararta, muryarta cike da izza ta ce: "Me ya kawo ki asibiti? Shin baki ji na yi muku iyaka ba? Ko kina so ki kashe ɗana da hannunki?!" Farha ta haɗe fuska, ta turo baki cikin raini ta ce: "Eh mana! Ai yanzu Yaya Maleekh ya daina ƙaunarki. Ba zai taɓa mu’amala da karuwa ba, don karuwai kawai suke zubar da ciki a club!" Amal ta tsaya kyam, sai ta saki murmushin takaici. Ta juya kai a hankali ta dubi Farha da idanu masu ƙarfi sannan ta ce: "Haka kuma ba zai taɓa mu’amala da yar shaye-shaye ba." Farha ta ɗaga hannu cikin hargowa za ta mari Amal. Cikin zafin nama Amal ta cafke hannunta da sauri, tana murɗawa kaɗan har sai da Farha ta ji zafi. Idanunta sun canza launi zuwa ƙiyayya, muryarta a tsanake take faɗin: "Kada ki sake taɓa ni Farha. Idan kika kuskura, sai nayi gutsi-gutsi da yatsun ki nan take." Arfat ta ɗan ja da baya tana kallon Amal da mamaki. Islam kuwa ta runtse baki tana ƙoƙarin boye murmushinta. Ammy ta katse su da tsawa: "Enough! Warning na ƙarshe nake baki Amal, ki fita daga rayuwar ɗana. Bana son sake ganin ki kusa da shi!" Amal ta ja dogon numfashi, ta ɗan yi shiru kamar wacce ke tunani. Sannan ta ɗaga ƙafa ta taka gaba, ta tsaya a gabansu cikin ƙarfin hali, muryarta na rawar zuciya cike da tabbaci take faɗin: "Ammy, sai dai idan Maleekh ne ya mutu, ko ni na mutu, amma ƙaddara ta riga ta haɗa mu. Kuma ƙaddara ba a goge ta da kalma, a rubuce take a littafin Ubangiji." Ta wuce su kai tsaye, ta buɗe motarta, ta shiga. Ta kunna engine, a ɗari ta bar hospital ɗin ba tare da ta sake waiwayen su ba. Ammy ta tsaya kallonta da tsananin haushi, har sai da motar ta ɓace daga gani. Farha ta harare Amal cikin ƙiyayya tana turo baki, tana huci ta ce: "Tabbas dole mu kawar da wannan yarinya daga rayuwar Ya Maleekh, kafin ta kashe shi da hannunta." Islam kuwa ta kasa ɓoye murmushi, ta yi gaba ta bar su a tsaye. ☆☆☆☆ Abba yana shiga cikin hospital, zuciyarsa na tunani akan yarinyar da ya gani a corridor. Ya ji kamar akwai wani abu a tattare da ita, baƙin cikin da yake ɗauke da shi ya ratsa shi sosai. Yana shigowa ɗakin Maleekh ya tarar da shi kwance, har yanzu bai farfaɗo da kyau ba, idanu a lumshe, numfashi a sarƙe. Likitoci sun fito daga emergency room sun ce a barshi ya samu hutu. Abba ya zauna a gefen gadonsa, ya riƙe hannunsa da ɗumin ƙauna. Idanunsa suka kaɗa da hawaye, sai ya ce cikin sanyi: "Yaro na… Maleekh. Ka tashi ka ga yadda kake jefa mu cikin tashin hankali. Ni mahaifinka ne, kuma na rantse da Allah, ba zan taɓa bari a tilasta maka abin da ba ka so ba. Duk yarinyar da kake so, zan tsaya a bayanka." Ya yi shiru, ya goge idonsa. Sai kuma ya sake magana cikin tausayi: "Ka san meye ɗana? yanzu na haɗu da wata yarinya a corridor. Na ji tausayinta. Amma ban san wacece ba. Sai kawai zuciyata ta ce, wannan yarinyar akwai wani abu mai girma a ranta. Kamar ƙaddarar rayuwarka tana haɗe da ita… Amma Allah ne masani..." Maleekh ya motsa a hankali, kamar yana jin maganganun. Ya ɗan buɗe ido kaɗan, hawaye suka gangaro masa, amma bai iya magana ba. Abba ya matse hannunsa da ƙarfi ya ce: "Ka kwantar da hankalinka ɗana, Allah zai baka mafita. Na fasa, babu wata yarinyar da zan saka ka aura. Babu tilas. Zan tsaya a bayanka da gaskiya." Ya ji motsin ƙofa. Sai ga Ammy ta shigo tare da iyalanta. Ammy ta tsaya cak, ta hango Abba yana riƙe da hannun Maleekh. Fuskar Abba ta nuna rashin jituwa. Abba ya dubeta da ido cike da gargaɗi ya ce: "Kina ji ko? Na ce babu tilas ga ɗana. Na gaji da wannan mulkin da kike yi na rashin hankali. Ki bar wannan doka taki, saboda wannan ɗan ba naki bane ke kaɗai. Shi ɗana ne, kuma rayuwarsa ba abar wasa ba ce." Ammy ta fashe da kuka tana cewa: "Kana gani ko? Kana gani fa? Wannan yarinya karuwa ce, ta zubar da ciki a club! Shin wannan ce kake so ta zama matar ɗanmu?.." Abba ya daka mata tsawa cikin bacin rai ya ce: "Shiru!! Ba ki da ikon yanke hukunci akan rayuwar ɗana. Ni ne uba, kuma na yarda da abin da zai zaɓa. Duk abinda ya so, shi ne za’ayi. Kuma wallahi, bana son sake jin ki da sunan karuwanci ko zubar da ciki a gaban ɗana! Idan kin kasa gane magana, zan tabbatar iyayenki sun koya miki darasi." Tsofaffin iyayen Ammy wanda shigowarsu kenam, basu koma garin da suke ba suna jiran tashin Maleekh, jin tattaunawarsu yasa suka gyaɗa kai, suka ce da ita cikin tsawa: "Ai ke kika ja wannan bala’in da rashin biyayya da bijirewa tunda kina yarinya. Ki ci gaba da ganin sakamakon dabi’arki yanzu." Ammy ta saki kuka tana girgiza kai, amma babu wanda ya tausaya mata. Maleekh a gefe yana sauraron wannan maganganu, hawaye na fita daga idonsa. Zuciyarsa ta ƙara rikicewa, ƙaunar Amal, tsanar Amal, da soyayyar iyayensa da kuma tsanar Farha duk sun gauraye cikin zuciyarsa. A ɗakin, shiru ya mamaye bayan hayaniyar Ammy da iyayenta ta lafa. Kowa ya fita, aka bar Maleekh a kan gadonsa, da Farha a gefen gado tana kuka. Farha ta tsuguna ƙasa, tana riƙe da hannayensa cikin rawar jiki. Idonta ya cicciko da hawaye, muryarta na rawa tace: “Yaya Maleekh… wallahi ina matuƙar kaunarka. Ka sani ko? Shi ya sa kake ganin ina abubuwa marasa kyau. Ni ba wai saboda mugunta nake ba, kawai burina shi ne na mallake ka a matsayin mijina.” Ta kalli fuskarsa, amma ba amsa. Sai ta ƙara fashewa da kuka mai ƙarfi: “Amma tinda baka sona… shikenan. Ni ba zan tilasta kaina a gareka ba. Ka huta kawai, ka manta da ni.” Ta saki hannuwansa ta rufe fuskarta a cikin tafin hannunta tana kuka sosai. Maleekh ya juyo da kyar, idanunsa sun cika da hawaye, ya dube ta na ɗan lokaci. Sai zuciyarsa ta motsa da tausayin kalmarta. Wani abu ya shige shi, ƙaunar, soyayya duk ya watsar da su gaba ɗaya, amma jinin ɗan’uwantaka ya motsa... Cikin rauni, muryarsa ƙasa ƙasa sosai, ya furta “Farha… kin cancanci a so ki… amma ni… na haƙura da soyayya gaba ɗaya. Na haƙura da ita har abada. Ke, ko Amal… babu wanda zai sake samun zuciyata.” Ya lumshe idonsa, hawaye suka zubo daga gefe yana ƙara cewa cikin rauni: “Zan rayu ba tare da mace ba… tunda babu komai a soyayya sai ciwo kawai.” Farha ta yi ƙara cikin kuka ta riƙe gadon, tana faɗin: “Wayyo Allah naaa! Yaya Maleekh kada ka ce haka. Ni bazan iya jurewa ba.” Ya rufe ido gaba ɗaya, bai sake magana ba.. Farha tana kuka tana jingina da gefen gadon, sai taga Maleekh ya rufe idonsa gaba ɗaya. Kafin ta sake magana sai ga ƙarar buɗe ƙofa. Doctor ya shigo da file a hannunsa, yana takowa har kusa da gadon. Idonsa ya sauƙa kan Farha da ke tsugunne a ƙasa, sannan ya duba fuskar Maleekh da ke lumshe ido, hawaye na zuba masa a gefe. Doctor ya ɗan tsaya yana nazari kafin ya yi magana da tausasawa da ƙarfi ya ce: “Hajiya, kiyi hakuri, amma yanzu dole ne ki bar ɗakin. Yana cikin damuwa sosai. Idan kina ƙara saka shi cikin kuka ko tashin hankali, hakan na iya cutar da lafiyarsa fiye da jinyar da muke yi masa.” Farha ta ɗago kai cikin kuka, ta dubi Doctor da idanunta jawur ta ce: “Ni ba wai son tashin hankalinshi nake so ba Doctor… wallahi ni ina ƙoƙarin kwantar masa da hankali ne.” Doctor ya girgiza kai cikin ladabi, ya ɗan sauƙe numfashi sannan yace: “Na fahimta, amma yanzu ba wannan lokacin bane. Lafiyarsa tafi buƙatar kwanciyar hankali. Ki bari ki fita ki barshi ya huta. Zaki iya dawowa daga baya idan ya samu sauƙi.” Sai ya matsa kusa da ita cikin tausayawa, yana nuna mata ƙofa da hannu. Farha ta share hawayenta, zuciyarta na karyewa, ta dubi Maleekh da bai buɗe ido ba. Ta miƙe a hankali, tana jin jikinta ya yi nauyi, kafin ta fice daga ɗakin cike da ƙunci. Doctor ya juya ya duba Maleekh, ya ɗan murmusa da tausayawa a gefen baki, yana rubuta wani abu a takarda. ☆☆☆ Amal ta shigo gida da hawayen da ta kasa dakatawa, duk jikinta yana rawa saboda nauyin damuwa da tashin hankali. Hannunta a rufe akan fuska da gyale, ta shige falo ba tare da ta wa Inna kallon kirki ba. Inna tana zaune a kujerar falo, tana zare ido tana haɗa rai. Da sauri ta daga murya cikin yanayin tsawa: “Can miki dai! Ki ƙarata sama ki zauna. Wawiya kawai! Kin tsaya kina rawar jiki saboda wani namiji da ya watsar dake? Taya kike tunanin Maliku zai sake kallonki bayan wannan abun kunyar da kika aikata? Kin tozarta kanki kin tozarta mu gaba ɗaya!” Kalmar “tozarta” ta shiga kunne Amal kamar wuƙa, ta ƙara ratsa zuciyarta da raɗaɗi. Bata tsaya sauraren ƙarin magana ba, ta wuce da gudu zuwa sama. Da ta shiga ɗaki, ta rufe ƙofa da ƙarfi, sannan ta faɗa akan gadonta. Ta dunƙule jikinta kamar ƙaramar yarinya, hawaye suna tsiyaya tamkar ruwan sama. “Ya Allah… me yasa zuciyata ke son shi haka? Me yasa Maleekh ya zame min kamar rai na? Duk inda na juya, shi kawai nake gani…” ta furta cikin shessheƙar kuka. Tsanannin kaunar Maleekh ya yi mata nauyi kamar dutse mai murƙushe zuciya. Zuciyarta na neman hallaka, jikinta gaba ɗaya na rawa da sanyi. Ta matse pillow tana goge hawayen da basu daina zuba ba. Duk da kalaman Inna sun ɗora mata raɗaɗi, amma ƙaunar Maleekh ta mamaye duk wani tunani nata. A zuciyarta, ta yi addu’a cikin rawar murya: “Ya Allah, idan wannan soyayya zata zama abun da zai hallaka ni, ka bani ƙarfin zuciya in jure. Amma idan ƙaddara ce ta haɗa mu, to ka sauƙaƙa min… ka dawo min da shi…” Darenta ya yi tsawo kamar shekara. Amal ta juya ta baya, ta juya ta gaba, amma idanunta sun ƙi rufuwa. Kallon ceiling ɗakin kawai take yi, amma abin da zuciyarta ke gani daban ne – fuskar Maleekh ce kawai a cikin idanunta. Hawayen da suka gama bushewa sai suka sake sabunta. Duk lokacin da ta lumshe idanu, sai zuciyarta ta cika da muryarsa, yadda yake kiranta “Amal” cikin salo na musamman da babu wanda zai iya kwaikwayo. Sai a hankali barci mai nauyin damuwa ya ɗauke ta. A cikin mafarki ta tsinci kanta a cikin wani fili mai yalwa, duk wurin fari ne kamar ƙasar hazo. A can gaba kuwa, ta hangi Maleekh tsaye cikin farin kaya, yana mata murmushi irin na da. Da gudu ta nufi wurinsa tana cewa: “Ya Maleekh! Ka dawo gare ni, ka ce baza ka barni ba…” Amma kafin ta kai shi, sai fili ya fara rikicewa. Maleekh ya fara ja da baya, kamar wani ƙarfin duhu ke jansa daga gareta. “Amal… bazan iya zuwa gare ki ba… kin ci amanata…” muryarsa ta fito kamar wuƙa, tana yankan zuciyarta... Amal ta durƙusa cikin kuka tana ƙiran sunansa, tana miƙa masa hannaye amma ya ƙi kamo su. Hazo ya lulluɓe shi gaba ɗaya, ya ɓace daga ganinta “A’a! Maleekh, wallahi ban ci amanarka ba! Ka saurare ni, ka dawo! Don Allah ka dawo!” A firgice ta farka daga barcin, tana tsalle daga gadon kamar wacce aka jefa a wuta. Kafafunta suna rawa, jikinta duk ya jike da zufa. Ta dafe ƙirji tana kuka mai tsanani, zuciyarta kamar zata tarwatse. “Wayyo Allah! Har mafarki ya koma azaba saboda Maleekh… Ni me nayi ne haka? Ina ruwana da wannan ƙaddara? Wayyo Allah …” A daren, Amal bata sake iya rufe ido ba. Ta zauna tana kallo cikin duhun ɗakin, tana jin soyayyar Maleekh na hura mata wuta a ƙirji tamkar ana zuba gishiri cikin raunannen zuciyarta. Washegari bayan sallar asuba, Amal ta zauna a kan sallaya, idanuwanta sun kumbura saboda kukan daren jiya. Kafin ta miƙe, wayarta ta fara ringing. Ta ɗauka cikin sanyin murya. “Hello…” Manager ya ce: “Madam Amal, mun jiki shiru daga gare ki. Kema baki zo company ba. A matsayinki na assistant CEO, yanzu da oga Maleekh ba shi da lafiya, ya kamata ki tsaya ki wakilce shi. Ayyuka sun yi mana yawa sosai…” Amal ta rufe idanunta tana jan numfashi mai nauyi. Kalaman sun bugi zuciyarta domin har yanzu tana cikin baƙin ciki, amma bata so ta nuna raunin ta.. Ta ce: “Kar ku damu. Zan dawo aiki yau.” Suka yi sallama, ta kashe wayar. Ta shiga bathroom ta watsa ruwa, sannan ta sha kwalliya kamar wata sarauniya. Ta shafe fuskarta da makeup, ta sanya Atamfa riga da skirt da suka matse jikinta sosai, sun fito da surar jikinta. Ta sanya takalmi masu tudu a ƙafarta, ta ɗan yafa gyale a kafaɗa gefe guda, sannan ta ɗauki farin glass siriri ta ɗora a idonta. Sai ƙamshin turare masu sanyi da daɗi suka mamaye jikinta. Ta ɗauki handbag da wayarta ta fito. A falo ta tarar da Inna zaune. Ta yi mata sallama cikin ladabi, amma Inna ta kawar da kai kamar bata ji ba. Ta kuma cewa: “Ni zan tafi wurin aiki.” Inna ta kalleta da ido mai cike da tsana ta ce: “Ai idan kin ga dama ki wuce wurin club ɗin ma. Domin na tabbata nan ne wurin samarinki.” Amal ta tsaya cak, sai murmushin da ta yi sannan cikin takaici ta ce: *“Inna, idan har tunaninki bai gushe ba, gaya min. Da wa kika taɓa ganina tunda kike? Eh, gaya mun? Idan

Chapter 29 of 62