a wannan ranar.
Maleekh bai san meke faruwa ba dake ya kulle ƙofarsa ya hana koma shigo masa..
Sai a yanzu da ya fita a ruɗe...
Kuma har wannan lokacin kowa yana falo, sai dai su ɗin ma kallon television suke, kan labarin Amal...
Wannan ya ƙara ɓacin rai ga Farha, amma duk da haka tana jin daɗin sharri da ta kitsa wa Amal.
Maleekh ya isa club ɗin da gudu, zuciyarsa kamar za ta faso ƙirjinsa. Ya shiga cikin cunkoson mutane. Ƴan sanda na son dakatar da shi amma ya ture su gefe.
Ya ga Amal kwance, ga jini a jikinta, ga wayoyi a sama suna ɗaukar hotuna. Idanunsa suka cika da hawaye.
Ya faɗi a kanta ya riƙe hannunta:
“Amal! Ki tashi, ki dubeni, don Allah kar ki barni haka. Ba zan bari su lalata miki suna ba. Zan gano wanda ya yi wannan sharri, kuma sai na ɗauki mataki akan hakan..!”
Ƴan jarida suka yi wuf da kyamarori suna ɗaukar hotonsa da ita...
“Amal! Amal! Open your eyes, please! Don’t leave me… Wallahi ba zan bari ki tafi ba!”
Haka Maleekh yake ta jijjiga ta amma ko motsi..
Mutane suka tsaya kallonsa, ƴan jarida suka ɗauki hoton shi yana kuka a kan Amal. Ɗaya daga cikinsu ya ce da sauti:
“Shin wannan ba shi ne Maleekh, babban ɗanbusiness, wanda a yau aka shirya aurensa da wata ba?”
Kowa ya fara raɗa: “To yaya ake ciki kenan? Ai Amal ita ce budurwarsa ta asali...”
Zuciyarsa ce ta fara masa wani irin zogi. Yana tuna kalaman Ammy da cewa ba ɗanta ba ne, yanzu kuma Amal tana shan mugun zargi..
Ya riƙo haɓarta da rawar hannu yana faɗin:
“Na rantse da Allah, zan binciko gaskiya. Zan wanke ki daga wannan sharri! Duk wanda ya yi miki wannan sharrin zai biya kuɗinsa da rayuwarsa…”
A lokacin, ƴan sanda suka nufe shi da nufin ɗaukar Amal. Amma Maleekh ya ɗaga Amal ya nufi ƙofar waje...
A wannan daren, duniya ta tsaya ga Amal da Maleekh.
Cikin hanzari Maleekh ya ɗauke Amal a hannuwansa, yana daka tsawa ga ƴan jarida:
“Kafin safe duk posting ɗin da kuka yi game da Amal ku share shi! Duk hotunan da kuka saka ku cire su yanzu! Idan kuwa wani ɗan jarida ya sake taɓa wannan magana, sai na tabbatar an kamashi, kuma bai sake ganin hasken waje ba sai ya mutu a prison!”
Ƴan jarida suka tsaya a tsorace, wasu suka fara sharewa nan take. Ƴan sanda suka matsa kusa, amma Maleekh ya ɗaga musu hannu da cewa:
“Ku kuma! Ba ruwanku da wannan case. Ku ja baya ku barta a hannuna!”
Ya fito da Amal cikin karfi, yana riƙe da ita kamar zai cinye duk wanda ya kusance ta...
Haka ya nufi hospital da ita...
A asibiti
Amal an kwantar da ita a kan gado, da drip a hannunta. Maleekh ya zauna kusa da ita har dare, bai runtsa ba. Idonsa cike da hawaye, zuciyarsa cike da tsoro da damuwa.
Anan duk suka kwana....
_Washegari_
Da safe, Inna ta shigo tana kuka, tana riƙe da mayafi tana jijjiga kai.
Cikin rawar murya take cewa:
“Na ji labarin… Amal tana asibiti? Amma me ya faru da ita ne? Me aka yi mata haka?”
Maleekh bai ce komai ba, ya riƙe hannun Amal yana kallon fuskar ta da hawaye.
Doctor’s Office
Doctor yana zaune a office ya gama rubuta result akan Amal..
Knocking aka yi masa, ya bada izinin shigo wa...
Farha ce ta shigo. Ta zauna tana facing Doctor, ta zaro wata babbar jaka mai cike da kuɗi.
Tayi murmushi mai cike da mugunta sannan ta ce
“Kasan nan ɗin nawa ne?”
Doctor ya kalli jakar yana firfito da ido waje, a ruɗe ya ce:
“A’a… gaskiya ban sani ba.”
Farha ta ce
“Kimani ne 2 billion dollars ne. Kuma duk naka ne idan ka yi min abu ɗaya kawai.”
Doctor ya miƙe a zabure, zuciyarsa ta rikice.
Cikin rawar murya ya ce:
“Subhanallah! Hajiya, me kike so ayi?”
Farha tayi dariyar mugunta sannan ta ce:
“Yarinyar da aka kawo jiya da daddare Amal. Nasani result ya nuna ba ciki a jikinta, kuma bata sha maganin zubar da ciki ba, kawai maye ne ya yi mata. Dama haka ne ko?”
Doctor da sauri, yana jinjina kai ya ce
“Hakane, wallahi kuwa.”
Farha ta ce
“Toh, ina so ka canza result ɗin. Ka rubuta cewa Amal ta zubar da cikin wata huɗu. Ka tabbatar labarin ya zama ainihi, babu wanda zai iya ƙaryatawa.”
Doctor ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya dubi jakar kuɗin da idanuwansa suka ciko da jarumta na ɗanɗano kuɗi ya ce
“Indai wannan ne aikin, ki tafi lafiya. Zan shirya result ɗin yanzu.”
Farha ta miƙe da murmushin mugunta, ta bar masa kuɗin sannan ta fice daga office ba tare da kowa ya lura ba...
A ɗakin Amal, Maleekh da Inna suna zaune kusa da ita. Amal har yanzu bata farfaɗo ba.
Doctor ya shigo da takardu a hannunsa. Maleekh ya miƙe da sauri, zuciyarsa na bugawa.
Maleekh a tsanake, cikin tashin hankali ya ce:
“Doctor… meke damun Amal? Ka faɗa min gaskiya.”
Doctor ya ɗan gyara tsayuwarsa, sannan ya ce da nutsuwa:
“Result ɗin ya nuna cewa Amal ta zubar da ciki… cikin wata huɗu ne ya fita.”
Wani irin shock ya shaƙe jikin Maleekh. Ya riƙe takardar, idanuwansa suka ciko da hawaye. Ya kalli Amal da hawaye suna zuba a fuskarsa.
A hankali ya furta
“Ciki… Amal?? Har na wata huɗu? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…”
Inna ta zabura ta miƙe a tsorace.
Ta ce
“Meeeee?? Amal ta yi ciki??”
Girgiza kai Maleekh ya yi tare da faɗin:
“Amal ta cuce ni. Amal ta gama da rayuwata. Ta rusa soyayyata. Ta bani kunya. Fuska biyu gare ta? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!”
Inna ta fashe da kuka, tana jijjiga kai.
Cikin baƙin ciki ta ce:
“Ko da ta zubar da cikin, ta riga ta zubar da tarbiyyarta! Ta zubar da mutuncinta! Iyayenta suna kwance a kabari, ita kuma ta janyo musu abun kunya. Jikata ce ita, amma ta janyo mun abun kunya!”
Maleekh ya miƙa wa Inna result ɗin da hannunsa na rawa, ya fita daga ɗakin cikin baƙin ciki.
Doctor ma ya fice, zuciyarsa cike da natsuwa cewa ya gama da aikinsa da aka saka shi.
Amal kuwa, tana kwance cikin rashin sani, bata san halin da ake ciki ba......
*_NEXT! NEXT!! NEXT!!!_*
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇 domin samun akai-akai har zuwa complete.
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 39 to 40
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Farfaɗowar Amal.
Ta buɗe idanunta a hankali, tana jin nauyin kanta. Sai ta yi mamakin ganin kanta a asibiti. Idonta ya sauka kan Inna wacce ke zaune gefe tana juya mata baya, idonta cike da hawaye, murya na rawa ta ce:
"Inna… me ya kawo ni asibiti? Me ya same ni haka? Ni dai ban gane komai ba. Na manta… na manta yanda na shigo nan…"
Inna ta juyo da huci ta ce:
"Ke baki da kunya wallahi Amatu! Ashe haka kika lalace? Ashe ashe cikin shege kike ɗauke dashi, har ya zube a gidan rawa na ‘yan iska?!"
Amal ta zabura, ta riƙe kanta sakamakon ciwon da yake tana girgiza kai a ruɗe ta ce:
"Ciki kuma Inna? A jikina? Inna shin ana iya ɗaukar ciki haka kawai? Kodai a ruwa ake sha? Wallahi ban taɓa sanin haka ba…!"
Inna ta daka tsawa, ta miƙe a fusace tare da faɗin
"Kar ki raina mun hankali Amatu! Ba abinda zaki ce mun yanzu! Me ya kaiki club ɗin ‘yan iska? Me kike nema a can? Sai dai ki karɓi sakamakon sharrin ki!"
Amal ta fashe da kuka, tana jin kamar duniya ta juya mata..
_Gidansu Maleekh_
A falo kuwa, Abbah yana zaune da Ammy da iyayenta (Grands). Fuskokinsu cike da baƙin ciki.
Grandmother (na bangaren Ammy) ta daka tsawa tana faɗi
"Ke Maryam! (Ammy) Ashe har yanzu baki canza ba? Tun kina yarinya kike ɗaga kai, baki taɓa bin umarninmu ba. Shi yasa yau ɗanki ya koma haka! Duk sakamakon halinki ne!"
Grandfather shima ya ce:
"Mun ja miki kunne a baya! Mun gaya miki rashin biyayya ga iyaye bala’i ne. Yanzu kin ga sakamakon! Ki kalli yaronki, ya koma halin da ba’a taɓa tsammani ba."
Islam cikin kuka ta ce:
"Ammy ta tsine wa Ya Maleekh jiya. Ta ce shi ba ɗanta bane! Ta ce ba daga jikinta ya fito ba!"
Abbah ya girgiza kai da tsananin takaici ya ce:
"Maryam, wannan wane irin rashin hankali ne? Wane irin baki ne ya fita daga bakinki? Kin shirya Auren ɗana ba tare da sanar da ni ba, hakan ma kin tsine masa?!"
Ammy ta fashe da kuka tana kare kanta da cewa:
"To ku gani fa a TV jiya! Yarinyar da yake so, ta zubar da ciki a gidan rawa! Ni zan aura masa irin wannan ‘yar iskar?!"
Abbah a fusace ya daka tsawa yana faɗin
"Duk abinda ɗana yake so shi za’ayi! Ba za ki kashe min yaro da damuwa ba!"
Cikin wannan hayaniya ne sai ga Maleekh ya shigo daga waje, yana jan ƙafa da ƙyar, kamar ba jini a jikinsa. Fuskarshi ba annuri, idonsa sun ƙanƙance kamar wanda yake shirin mutuwa. Bai kalli kowa ba, ya nufi sama.
Abbah da sauri ya miƙe tare da zuwa ya riƙe shi, yana faɗin:
"Yaron kirki, an soke maganar auren da baka so. Ka kwantar da hankalinka. Yanzu ka gaya min, mu je mu nema maka auren Amal ne?"
Maleekh ya tsaya yana kallonsa da idanu masu cike da hawaye, daga bisani ya furta cikin sanyin murya:
"Bana ƙaunar kowace mace yanzu! Na tsani mata gaba ɗaya! Gaba gaba gaba gaba ɗayaaaa…!"
A lokacin ya yi luuu, zai faɗi ƙasa.
Abbah ya yi saurin tare shi a rikice, cikin ɗaga murya ya ƙira sunansa:
"Maleekh!!"
Ammy ta nufo da gudu tana kuka tana faɗin:
"Maleekh ɗana, don Allah ka tashi! Wallahi ina sonka, wallahi kai ɗana ne, taya mahaifiya zata ƙi ɗanta?!"
Islam da Arfat suka ruga suna kuka, suna riƙe da hannun Maleekh.
Tsofin suka miƙe tsaye a firgice suna cewa:
"Akai shi asibiti yanzu! Kada lokaci ya kure!"
Abbah ya ɗaga ɗansa ya rungume shi da ƙarfi, su Islam suka riƙe ɗayan ɓangaren suka nufi waje, suka fice cikin hanzari.
Farha da gudu ta bi bayansu...
Security suna ganin haka suka yi saurin karɓar Maleekh tare da shigar da shi motar, kai tsaye sai hospital...
_Asibiti – Emergency Room_
An shigar da Maleekh cikin emergency room. Nurses da likitoci suka zagaye shi da hanzari.
Doctor cikin tsawa yake faɗin:
"Quick! Prepare oxygen mask! Bring the defibrillator, now!"
Nurse ta ɗaura masa oxygen, wani ya saka drip a hannunsa. Domin numfashinsa ne ya tsaya cak...
Doctor yana ɗaga murya a gaggauce ya ce:
"We’re losing him! Start CPR, now!"
Wani likita ya fara bugun ƙirjinsa da hannu (chest compression), wani kuma ya saka oxygen da karfi..
Babban Doctor ya ce:
"Charge defibrillator to 200! Everyone clear!"
Suka ɗaga hannuwa daga jikinsa, aka kwantar da shi. Aka buga shock na farko, jikinsa ya motsa ya tashi, amma monitor ɗin ya nuna flatline.
Doctor ya kuma cewa:
"Again! 300! Everyone clear!"
Aka sake bugawa, monitor ɗin ya yi tsalle ɗaya ya dawo flat...
Nurses suna kallon juna da hawaye a idonsu. Islam tana waje tana ihu tare da faɗin:
"Yaya Maleekh, don Allah kada ka mutu! Ka dawo mana…!"
Doctor ne ya sake ɗaga murya ya ce:
"Increase to 360! This is our last chance! Clear!"
Aka buga na uku sai beep beep beep ya dawo kan monitor. Numfashinsa ya fara dawowa a hankali.
Doctor ya sauƙe numfashi mai nauyi:
"Alhamdulillah! We got him back. Keep monitoring his vitals!"
Nurses suka fara farin ciki, suka fara jona masa magunguna da drip..
Waje kuwa, Abbah ya jingina da bango yana hawaye. Ammy tana kuka tana faɗin:
"Allah na tuba, kar ka ɗauke mun ɗana! Kar ka ɗauke mun Maleekh…"
Islam ta durƙusa tana addu’a da roƙon addu’a, tana kuka kamar za ta mutu..
(Ikon Allah, masu kuɗi kenam, da zarar Allah ya jarabce su da jinya sai su ɗauka mutum mutuwa zai yi🤔 amma mu ƴaƴan talakawa da zaran babu lafiya muna langwa6ewa sai ace lalaci ne, a baka kaje chemist ka haɗo magani )...
Doctor bayan ya fito daga Emergency room, ya tadda Abbah da Ammy da Grandma da sauran iyali a tsaye cikin tashin hankali.
Doctor ya kalli Abbah a hankali sannan ya ce da murya mai sanyi:
"Alhaji... ba zan ɓoye muku ba. Yaronku yana cikin matsananciyar halin gaggawa. Heartbeat ɗinsa na tafiya da sauƙi sosai, a wasu lokutan har yana tsaya wa cak. Mun sha wahala wajen dawo da numfashinsa… yanzu haka injin na taimaka masa. Idan har ya tsira daga wannan, zai buƙaci kulawa sosai da kuma kwantar da hankali domin zuciyarsa tana da rauni mai tsanani."
Ammy ta fashe da kuka, Grandma ta dafe kirji tana ambaton "Innalillahi wa inna ilaihirraji’un."
Doctor ya ɗauki numfashi kafin ya ƙara cewa:
"Alhaji, ya kamata ku sani, damuwar da yaron nan yake ciki tafi ƙarfin jikinsa. Duk wani raɗaɗi da kuke ji a jiki, shi zuciyar sa take ɗauka kai tsaye. Idan ba'a yi hankali ba, Allah kadai yasan yadda zai kasance."
☆☆☆☆☆
An kwana biyu babu motsi daga Maleekh.
Yana kwance a gadon asibiti, komai na'ura ce ke yi masa. Abbah kullum yana zaune kusa da shi, Islam ta kasa barin asibitin tin da aka kawo shi, kullum tana kuka tana riƙe da hannunsa tana faɗin:
"Yaya, dan Allah ka tashi ka duba ni. Ka tuna kace baza ka taɓa barina ni kaɗai ba… don Allah ka tashi."
Ammy kuwa ta rikice gaba ɗaya, kullum sai dai ta yi kuka tana tunanin kalaman da ta faɗa masa, ta tsinewa ɗan da ta haifa da kanta.
A gefe guda kuma Amal…
An sallame ta daga asibiti, sun dawo gida. Amma Inna ta ƙi kulata gaba ɗaya.
Ko zama kusa da ita Inna bata yi, balle ta duba yanayin jikinta..
Ko wani lokaci Amal na tambayarta tana hawaye:
"Inna… don Allah ki gaya min, me ya faru da ni? Me yasa na tashi a asibiti? Taya aka ce ina da ciki…?"
Inna ta daka mata tsawa cikin tsananin fushi:
"Kar ki raina min hankali Amatu! Ke baki san me kika aikata ba? Kina can gidan rawa na ƴan iska kina tozarta kanki! Doctor ne ya ce kin zubar da ciki sakamakon iskanci! Har kike cewa baki sani ba?"
Amal ta zaro ido tana mamaki sosai, ta fara shafa cikinta tana girgiza kai da kuka ta ce:
"Inna wai haka kawai mace zata iya samun ciki ne? Ko a ruwa ake sha ne? Inna don Allah ki yarda dani, ban san komai ba, ban taɓa yin wannan abun ba!"
Inna ta yi tsaki, ta juya mata baya cike da ƙiyayya ta ce:
"Ni dai ban san komai ba, Amatu. Duk abinda kika aikata, ki ɗauki alhakin kanki. Ni ba ruwana! Na gaji da wahalar ki, na gaji da tozarci da kunyar ki. Idan kika ga dama ki je ki nemi uban cikin nan ki kawo mun shi a gabana. Ni ba zan raba miki shimfiɗa da shi ba!"
Amal ta fashe da kuka tana dafe da cikinta da mamaki da tsoro, gaba ɗaya ta shiga cikin tashin hankali mai tsanani....
*_Day 1_*
Duk daren nan Abbah bai runtsa ba. Ya zauna a gefen gadon ɗan nasa, ya riƙe hannunsa da karfi yana ta ambaton:
"Allah ka dawo min da ɗana…kada ka raba ni da shi. Ya Allah ka dawo da shi cikin rayuwa."
Islam kuwa ta kwanta a ƙasa kusa da gadon, ta ƙi tafiya ko da minti ɗaya. Idonta ya kumbura saboda kuka. Duk lokacin da injin ɗin da ke jona numfashin Maleekh ya yi sautin gargaɗi, sai ta firgita ta nufi ƙofar ta ƙira nurse.
Ammy ta kasa shigowa ɗakin. Duk lokacin da ta kawo ƙafafunta wajen ƙofar, sai ta tuna kalamanta: “Kai ba ɗana bane.” Sai ta ja da baya ta fashe da kuka. Grandma ta riƙe ta sosai tana faɗin:
"Kije ki riƙe hannun ɗanki, shin ba addu’ar nakin bane zai dawo da shi ba?"
Ammy ta fashe da kuka tana girgiza kai ta ce:
"Na tsine masa da bakina, ke kina so in ƙarasa kashe shi kenan?…"
*_Day 2_*
Doctor ya ƙira Abbah da Ammy ofis ɗinsa. Ya ce da su:
"Alhaji, gaskiya mu dai likitoci mun yi iya bakin ƙoƙarin mu. Wannan na'ura ce kawai ke riƙe da shi yanzu. Amma ku sani, yaron nan yana cikin koma mai tsanani. Sai dai Allah ya ɗora masa rayuwa."
Ya ɗan yi shiru, ya kalli Abbah cikin tausayawa:
"Kar ku daina addu’a, saboda zuciyarsa tana fama da nauyin damuwa da tashin hankali. Idan ba’a cire masa wannan nauyi daga zuciya ba, duk magunguna ba zasu wadatar ba."
Abbah ya dafe kansa yana hawayen maza...
Ammy ta durƙusa a gaban Doctor tana kuka sosai tana faɗin:
"Doctor, akwai wata hanya da za ku iya yi? Ko zaku cire mun zuciya ku saka masa, wallahi ku yi!"
Doctor ya girgiza kai ya ce cikin tausayawa:
"Allah ne kaɗai zai iya yin hakan, Hajiya."
Islam dake zaune da Maleekh a ɗakin..sai kuka take tayi tana faɗin:
"Yaya, wallahi ba zaka mutu ba. Ka tashi ka duba ni don Allah…"
Waje daban kuma… Amal a gida.
Amal ta kasa cin abinci, ta kasa runtsawa. Inna ta ƙi kulata, ko da tambayarta abu zata yi sai dai ta yi mata tsawa. Amal tana zaune ita kaɗai cikin ɗaki tana shafa cikinta da hawaye tana cewa:
"Allah ka sani ban san komai ba… Na tashi a asibiti ne kawai. Shin ni ƴar iska ce? Da wannan rayuwar gwara mutuwa ta, Allah ka bani gaskiya…"
☆Daren kwana na uku☆
Injin numfashin yana ta bugawa a hankali. Abbah yana zaune a gefensa kamar yadda ya saba, ya riƙe hannunsa yana karanta Qur’ani. Islam ta kwantar da kanta a gefen gado tana bacci da kuka a idonta. Ammy kuwa ta jingina da bango tana hawaye cikin shiru...
Iya su uku ne a zaune da Maleekh..
Sai a hankali yatsun hannun Maleekh suka motsa...
Abbah ya ji motsin ya kalli hannun cikin sauri, zuciyarsa tana bugawa. Ya matsa kusa ya ƙira cikin rawar murya:
"Maleekh… ɗana, kana jin Abbah?"
Kamar wanda aka ɗago daga zurfin rami, Maleekh ya ɗan motsa bakinsa a wahalce...
Bai iya magana sosai ba, sai dai wani irin numfashi mai nauyi ya fito daga bakinsa.
Islam ta farka da sauri ta ce:
"Yaya! Yaya ya motsa! Abbah, Yaya ya motsa wallahi!"
Ammy itama taso wa tayi daga jikin bango cikin rawar jiki ta durƙusa a kusa da shi, tana riƙe da hannunsa cikin hawaye ta ce:
"Maleekh ɗana… don Allah ka tashi ka kalle ni, na rantse ban tsaneka ba, na yi kuskure. Nasan ni ce na jefa ka a wannan hali, ni ce na cutar da kai… Amma ina ƙaunarka fiye da komai."
Likitan da nurse suka shigo da gudu, suka fara duba injin.
Likitan ya ce cikin farin ciki:
"Alhamdulillah, yana nuna alamun farkawa. Ku ci gaba da ƙiran sunansa, wannan yana taimaka masa sosai."
Maleekh ya yi wani irin gunji kamar yana ƙoƙarin magana.
Abbah ya sunkuya sosai ya ce:
"Ka yi ƙoƙari ɗana. Ka dawo mana, muna jiranka. Babu aure da za a tilasta maka, babu wanda zai cutar da kai, ka kwantar da hankalinka."
Sai a hankali idanuwan Maleekh suka fara ƙoƙarin buɗewa, dishi-dishi kamar mai ganin haske bayan dogon duhu.
Islam ta yi ihu da murna tana cewa:
"Ya buɗe ido! Wallahi ya buɗe ido!"
Ammy ta fashe da kuka tana rungume da hannunsa ta ce:
"Na gode Allah, na gode! Maleekh ɗana, sakacina ne ya jawo haka, amma wallahi ina sonka. Ka gafarta mini…"
Likitan ya yi murmushi ya ce:
"Alhamdulillah, hakan yana nuna zuciyarsa tana dawowa a hankali. Amma kada ku dame shi da surutu mai yawa yanzu. Yana bukatar nutsuwa."
bayan ya buɗe ido a karo na farko
Ɗakin ya ɗau shiru, sai ƙarar injin numfashi da ɗan motsin nurse dake gyara drip. Abbah da Ammy sun zuba ido suna jiran wani kalami daga gare shi. Islam kuwa tana riƙe hannunsa tana kuka da murmushi lokaci guda.
Maleekh ya buɗe bakinsa a wahalce, muryarsa na fita ƙasa-ƙasa kamar fitar rai ya ce:
"Ab…bah…"
Abbah ya matsa kusa cikin sauri ya ce:
"Na’am ɗana, ina nan, ina jinka. Kar ka damu, Abbah naka yana nan a tare da kai."
Sai ya ɗau dogon numfashi a wahalce, ya sake cewa:
"Am…my…"
Ammy ta sunkuya tana hawaye, zuciyarta kamar zata tarwatse ta ce:
"Eh Maleekh, Ammy ce, ɗana. Na’am… ka faɗi abinda kake ji."
Idanuwansa suka cicciko da hawaye, ya ɗago da ƙyar yana kallon fuskarta ya ce:
"Me… yasa… kika ce… ni..ba ɗanki… bane…?"
Ammy ta fashe da kuka tana girgiza kai:
"Na yi kuskure, wallahi ba da nufin zuciyata ba. Na ce haka a cikin fushi ne, amma kai jinin jikina ne, Maleekh ɗana. Don Allah ka yafe min…"
Maleekh ya runtse idanu yana sauƙe numfashi da ƙyar. Sai ya buɗe su a hankali, muryarsa ta sake yin rauni ya ce:
"Na gaji… da rayuwa… Na gaji… da soyayya… Ba na son kowa… sai ku…"
Islam ta rushe da kuka ta rungume hannunsa tare da faɗin:
"Dan Allah kar ka sake faɗin haka Yaya. Kana da mu, kai rayuwarmu ne…"
Abbah ya share hawayensa ya ce:
"Ka kwantar da hankalinka, ɗana. Zamu tsaya a tare da kai har sai ka farfaɗo gaba ɗaya. Babu wanda zai sake cutar da kai."
Maleekh ya lumshe idanu, hawaye na sauƙa daga gefen kumatunsa, sannan ya furta cikin rauni:
"Ina… so… na huta…"
Sai ya sake lumshe idanu yana shaƙar numfashi a hankali, ya koma shiru.
Doctor ya matsa kusa da Abbah da Ammy. Ya da fa kafaɗar Abbah cikin girmamawa, sannan ya dubi Ammy da ido mai cike da gargaɗi.
Sannan ya ce:
"Don Allah ku kula da kalamanku a gabansa. Zuciyarsa tana da rauni sosai yanzu, duk wata magana da zata tada masa hankali na iya sake rikita bugun zuciyarsa. Wannan halin da yake ciki ya samo asali ne daga tashin hankali da damuwa mai tsanani. Idan kuna so ya warke, to ku tabbatar komai da yake ji daga gareku yana da sauƙi, babu zafi, babu fushi."
Abbah ya jinjina kai cikin nauyi ya ce:
"Insha Allah, zamu kiyaye. Wannan yaron mu ne gaba ɗaya."
Ammy ta share hawayenta da sauri ta ce:
"Doctor, wallahi zan riƙe alƙawari. Ba zan ƙara masa ciwo ba, sai dai farin ciki."
Doctor ya dube ta yana faɗin:
"Ki tabbata kin aikata hakan. Wannan ba wai maganin asibiti kaɗai bane, soyayya da kwantar da hankali suna cikin maganin sa."
Scene ɗin Amal...
Tun daga daren da ta dawo daga asibiti, kullum ƙoƙari take ta ƙira Maleekh amma wayarsa a switch off. Hankalinta ya fara tashi.
A daren nan ta ɗauki wayarta ta ƙira PA ɗin Maleekh, wanda shine manager ɗinsa a campany.
Amal cikin damuwa ta kara wayar a kunne bayan ya ɗaga ta ce:
"Hello… don Allah, ina Yaya Maleekh ne? Na kirashi tun kwanaki amma wayarsa a kashe. Ko yana lafiya ne?"
Manager ɗin ya yi shiru na wasu sakanni kafin ya amsa da wata murya mai nauyi:
"Eh… Madam Amal, gaskiya akwai wani hali da yake ciki. Yana asibiti yanzu, tun kwanaki biyu kenan yana kwance."
Amal a firgice ta ce:
"Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Hospital kuma? Amma me ya same shi?!"
Manager ya ce:
"Ni ma ban san cikakkun bayanai ba. Amma dai likitoci suna ƙoƙarin ganin ya warke. Ki kwantar da hankalinki…"
A ruɗe ta kashe wayar tare da rufe baki da tafin hannunta, hawaye suna zubo mata ta ce:
"Ya Allah… Maleekh a asibiti kuma ni ban sani ba…!"
Sai zuciyarta ta ƙara tsinkewa lokacin da ta ga results ɗin asibiti nata da aka kawo mata a envelop.
Ta buɗe da hannu mai rawa… idonta ya sauƙa akan rubutu:
“Evidence of miscarriage, 4 months pregnancy.”
Amal ta zaro ido tana kallon saƙon, jikinta ya ɗau rawa. Sai ta riƙe cikinta a gigice tana magana da kanta:
"Ciki kuma? Wai a jikina? Na rasa gane komai amma ina aka ɗauko wannan sakamakon? Shin Maleekh ya sani?.."
Sai ta rushe da kuka tana riƙe da ƙirjinta.
Bayan ta gama shan kukan ta.
A ruɗe ta ɗauki gyale ta yafa, ta sauƙa down stairs a falo ta tarar da Inna..
Wani irin kallo Inna ta yi mata..
Amal a ruɗe take faɗin
"Inna Maleekh yana hospital ba lafiya inaso zanje na dubo shi.."
Inna ta kawar da kai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 62