Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Amma haka ya haƙura suka yi jana’izarta sannan aka kaita gidanta na gaskiya. ​Zayd kam ba bakin magana, idonsa yayi jawur domin sai da ya zauna a kabarinta ya yi mata addu’a da kuka gaba ɗaya. Da ƙyar Maleekh ya ɗago shi suka dawo gida. ​Bayan an dawo, Alhaji Wadata ne ya shiga gidan. Ya tarar da mata sun cika a babban falo. Hajiya Sa’adatu itama ta farfaɗowo amma da wani irin bala’in kuka ta tashi, ta kasa yiwa kowa magana sai kuka. ​A lokacin da Wadata ya shigo, bai dubi kowa ba ya fara maganar: ​ “Saboda rashin mutunci yarinyata ta mutu amma a kasa sanar mun a lokacin? Nine fa ubanta kuma ina gari!” ​Sai a lokacin Hajiya Sa’adatu ta miƙe tazo gabansa, kai tsaye ta ɗauki hannu ta zabga masa lafiyayyen mari! ​Alhaji Wadata yana zazzaro ido cike da mamaki yace, “Ni kika mara Sa’adatu?!” ​Hajiya Sa’adatu ta ce, “Ban taɓa marinka ba tun da nake sai yau, kuma yanzu ma idan bakayi wasa ba zan ƙara maka! Marar mutunci kawai! Wallahi nayi danasanin aurenka domin da kai da babu duk ɗaya ne, na auri mijin da zai kashe mun ƴa da hannunsa! Tirrr!” ​Mutane haka suka tsaya kallonsu cike da mamaki. ​Tana kuka tana faɗin “Allah ya isa tsakani na da kai jahili kawai!” “Sa’adatu nine jahili?!” ​Hajiya Sa’adatu ta ce, cikin kuka “Na faɗa jahili, dabba, tsinanne, ɗan jahannama!” ​Amal tana zaune tana kallonsa, ji take kamar ta tashi ta murɗe masa wuya. ​Suna cikin wannan hayaniya kawai Alhaji Wadata yaji an kwaɗa masa katako a tsakiyar kansa. ​Yana waiwayawa yaga Inna ce da katako a hannunta tana kuka. Nan ta cigaba da kwaɗa masa tana tsine masa: ​ “Allah ya isa na Wadata tsinanne! Daman ina jiran wannan ranar da farin cikinka zai ƙare har abada! Ka kashe mun ɗana ɗaya tilo da matarsa saboda rashin imani sannan kazo kana neman rayuwar jikata! To ta Allah ba taka baaa!” ​Alhaji Wadata ne ya riƙe katakon da Inna take kwaɗa masa. Inna ta rungumoshi ta fara cizonsa a ta ko ina. Haka take jan naman fatarsa da ƙarfi. Ta kama naman wuyansa ta ja da ƙarfi sai da fatar ta ɗage. ​Da ƙyar ya karɓe kansa ya ruga da gudu ya fito. A sama sama ya gaggaisa da mutanen da basu san me ke faruwa ba, da sauri ya shiga motarsa ya ja a ɗari ya tafi... Bayan kwana uku da rasuwar Farha, an gama ta'aziyya. ​Alhaji Wadata da abokinsa Alhaji Gusau suna zaune a falon gidan Wadata. Hajiya Sa’adatu da Zayd suna can gidansu Maleekh. ​Wadata da Gusau suna zaune suna shirya neman mafita domin sun san asirinsu ya tonu. Suna shirya barin ƙasar gaba ɗaya ta wata hanyar sirri. ​Sai suka ji an turo ƙofar falon ba tare da neman izini ba. Maleekh ne ya fara shigowa sai Zayd da kuma Jami’an Tsaro sanye da kayan aiki. ​Maleekh ya tsaya yana kallonsu da idanun baƙin ciki da fushi.. ​Maleekh ya furta cikin ɓacin rai “Uhmm, rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai kaya! Ba tare da ɓata yawun bakina ba, anzo tafiya da ku…” ​Alhaji Wadata ya ce, “Zuwa ina?…” “Kotu!” a cewar Maleekh ​Alhaji Wadata da Alhaji Gusau suka kalli juna a tsorace. ​Wani irin tsawa Maleekh ya daka musu, yana fitar da ikon iko “Ku miƙe mana!” ​Alhaji Wadata ya ce, “Kai Maleekh! Laifin me mukayi haka?…” ​Maleekh ya matso kusa da su, yana kallon su cikin kaskanci. ​**“Kar ku raina mana wayo! Laifuka da dama! ​Laifin kashe tsohon babban gwamna (Mahaifin Amal) da matarsa. ​Laifin cin dukiyarsa ta hanyar juyar da kadarori da asusu. ​Laifin ɗora wa marar laifi sharri na kisa (Alhaji Abdul-Majeed). ​Laifin kai farmaki don ɗaukan ran wacce bata ji ba bata gani ba ta hanyar hatsarin mota tun da farko. ​Sannan laifin kai mata farmakin ɗaukan ranta bayan iyayenta da ka kashe. ​Na ƙarshe, laifin kashe ɗiyar ka daka haifa a wurin shagalin bikinta, wacce ta mutu saboda rashin tausayin ka da miyyatun zuciyarka!”** ​Zayd ya ƙara da cewa: ​“Yau ranar ku ta farin ciki ya ƙare! Yau ka kashe ɗiyarka Farha, gobe kuma akaina harin zai tsaya!” ​Wasu jami’ai ne suka zo zasu sa musu handcuffs. Wadata da Gusau suka miƙe tare da dakatar da su suna so su nuna girman su. ​A fusace, Maleekh ya karɓi handcuffs ya sanya musu da kansa yana nuna mallaka da ikon fansa. Sannan ya turasu gaba da ƙarfi. ​Alhaji Gusau ne yake faɗin: “Ku tsaya, hulata!”. ​Cikin zafin rai, Maleekh ya ɗago hannu ya kai masa wani irin mari akan ƙeyarsa da ya sha askin maluuu sai sheƙi yake kamar mirror. ​Sai wani paattttt!!! Ƙarar mari mai tsanani... ​Alhaji Gusau ya durƙusa saboda zafin marin kuma goshinsa ya bugi ƙasa da ƙarfi, ga shi ƙato dashi ga tunbin ciki kamar wanda ake hurawa kullum... ​Haka aka ja su waje. Sun nemi alfarmar zasu shiga cikin motocinsu su je kotun don guje wa kaskanci, amma samm Maleekh ya ƙi amince wa. Ya sa suka hau motar ƴan sanda ta baya yanda kowa zai gansu a cikin jama’a yayin da ake wuce wa dasu... ​Bayan an kama Alhaji Wadata da Alhaji Gusau, Maleekh ya dawo gida tare da Zayd. Gidan ya cika da nutsuwa da baƙin ciki. ​Maleekh ya nufi ɗakin Amal, inda ta ke zaune tana rungume da jariranta, amma hawaye na zuba a fuskarta. Tana tunawa da furucin Farha kafin ta rasu. ​Maleekh ya zauna kusa da ita, ya ɗauki Arhaan ya rungume shi, yana shafa kan Amal a hankali. ​A hankali ya furta “Amalina... Yanzu komai ya wuce. An kama waɗanda suka aikata laifin kuma an tona asirinsu. Farha ta rasu tana mai daraja, kuma ba zata taɓa mantuwa ba.” ​Amal ta jingina kanta a kafaɗarsa tana kuka mara sauti. ​“Ya Maleekh… gaskiya ne? Iyayen Farha ne? Sune suka kashe Mamana da Baba na? Sune suka ɗora wa abbah sharri? Kuma sune suka sanya ni cikin hatsari?… Farha ta gaya min…” ​Maleekh ya ɗora ɗan yatsansa a kan leɓɓan ta don ta yi shiru. ​Ya ce, “Gaskiya ne, my love. Amma Farha jaruma ce kuma ta sanar da ke gaskiya saboda ta nuna soyayyar gaske. Ba ta so ki rayu da ƙarya. Kuma ba ta so ki mutu a hannun su. Sun shirya miki farmaki a wurin bikin... saboda sun san zaki kawo musu cikass... ​Tun farko, auren Farha dabara ce. Na sanya mata mic a cikin sumar kanta don in ji duk abin da suke shirin yi da sirrin da suke ɓoyewa. Na gano cewa layar rufe bakin da ke kan Zayd tana rage ƙarfin ta idan an faɗi gaskiya a gefe. Don haka, na saka Farha ta zama wakiliyar mu ba tare da ta sani ba, har sai da ta gano mic ɗin kuma ta yanke shawarar taimaka mana da kanta... ​Iyayen Farha sun ɗauki Abban mu a matsayin katangar kariya. Sun sani cewa idan Abba ya shiga kurkuku, ba mai neman su saboda Abba yana da ƙarfi da tasiri. Sun tilasta wa mahaifin ki ya furta cewa Abba ne ya kashe su kafin su kashe shi. Sannan Abba bai san komai ba, duk makircinsu ne..." Amal ta fashe da wani irin kuka na jin daɗi da na yafe wa kai. Ta rungume Maleekh da ƙarfi, ta ji nauyin shekaru ya sauka a kanta.. ​ “Nagode, Ya Maleekh. Ina sonka! Kuma na yafe wa Farha gaba ɗaya! Yanzu Abba kawai zan so ganin sa! Kuma zan so ka kula da Hajiya Sa’adatu saboda ta rasa ɗiyar ta kuma ta rasa mijinta ta hanyar gaskiya.” ​Maleekh ya ce, “Za mu kula da ita. Zayd yana tare da ita yanzu. Kuma yanzu da gaskiya ta fito, lokaci yayi da zan ɗauko Abbah...” Bayan Maleekh ya kwantar da hankalin ta, Ta tashi ya nufi wani side ɗin wardrobe ɗinta inda take ajiye wasu takardun... ​Ta kalli Maleekh ta furta “Ya Maleekh, kadarorin Babana da kudin gado gaba daya Alhaji Wadata ya cinye su ta hanyar juyar da sunayen bankuna da shaidun kwangila. Sai wasu ƙananan kadarori ne kawai suka rage a bankin da na canza sunan su, bayan rasuwar Farha wani ya kawo mun wai Farha ce ta bashi ajiye cewar nawa ne. Me za mu yi?” ​Maleekh ya duba takardun kadarorin da kyau. Wannan kaddarori sun haɗa da gidaje da filaye da kuma manyan asusun banki da ke da alaƙa da gwamnati da ƙasashen waje. ​Ya kuma furta, “Kada ki damu, my love. Tun kafin in tafi, na riga na tsara komai. Waɗannan ƙananan kadarori da kika canza sunan su, sune katangar kariya ta farko. Zan sanya laoyoyin mu su daskarar da dukiyar Wadata da Gusau nan take a dukkanin bankuna na gida da na waje, tare da shaidar Zayd. Kuma za mu neme su a ƙarƙashin laifin cinikin ƙasa (money laundering) da kisan kai.” “Kada ki taɓa komai har sai na dawo. Kula da yara kuma ki kwantar da hankalin ki. Gobe da asuba zan kama jirgi zuwa Ethiopia don dawo da Abbana gida. Ina sonki!” ​Maleekh ya rungume ta da ƙarfi, ya sumbaci yaran sa gaba ɗaya, sannan ya fita don kammala shirin farko. ​Maleekh ya tafi zuwa sashen Zayd inda yake tare da Hajiya Sa’adatu (Mommy) a wani babban daki. Haj. Sa’adatu ta yi kuka mai yawa don rasuwar Farha da kuma tonuwar asirin mijinta. ​Maleekh ya shiga sannan ya ce “Mommy, kar ki damu. Zayd zai kula da ke kuma ku kula da kanku. Bari inyi magana da Zayd a waje.” ​Suka fita waje. ​Maleekh ya ce, “Zayd, tuni na sanya laoyoyin mu sun fara daskarar da kadarorin Daddynka da Gusau gaba daya. Yanzu aikin ka ne ka yi magana da Mommy yadda za ta ba da haɗin kai ga DPO da kuma manyan Lauyoyin mu.” ​Zayd ya ce, “Amma Mommy tana jin tsoron gidan yari!” ​Maleekh ya ce, “Ba zata shiga gidan yari ba muddin ta ba da dukkanin takardun da Daddynka ya ɓoye da kuma takardun shaida na asirin su. Ka gaya mata ta yi hakan don ceton kan ta da kuma girmamawar Farha. Idan ta ki, ba zan iya kare ta ba a gaban shari’a.” ​Zayd ya koma falon, ya yi doguwar magana da Mommy. Bayan awa ɗaya, Mammy ta yarda! ​Zayd ya kira Maleekh a waya. ​“Ta yarda! Ta gaya min inda Daddy ya ɓoye dukkanin kadarorin Gwamna da kuma makudan kuɗi da ya ciyo ta hanyar siya da sayarwa. Ta kuma gaya min sunayen bankuna da kamfanoni da ke ƙasashen waje.” ​Maleekh ya ce, “Haka nake son ji! Yanzu zan kira DPO ya zo da Lauyoyin mu kai tsaye! Ka kiyaye da Mammy har sai na dawo! Sannan ku shirya sirrukan domin su zama shaida a kotu na gobe! Sai na dawo.” ​Maleekh ya kira DPO jami'in ‘yan sanda ya gaya masa dukkanin shaidun da Mommy ta bayar, kuma DPO ya zo tare da lauyoyi don kama kadarorin nan take. ​Yayin da Maleekh ke shirya jirginsa na Ethiopia, a kotun babban birnin tarayya, an gabatar da Alhaji Wadata da Alhaji Gusau gaban babban alkali. ​Wadata da Gusau sun shigo sanye da ancuffs a hannunsu, kuma jama’a sun cika kotun. ​Lauyoyin Maleekh da DPO sun gabatar da shaida ta farko ga alkali. ​Lauyan Gwamnati ya ce, “Mai girma Alkali! Muna gabatar da su a gaban kotun ka a kan laifukan kashe-kashe ciki har da na Gwamna da Matarsa da kuma na Farha, cin dukiyar Gwamnati, cinikin ƙasa (money laundering), kuma ɗora wa mutumin ƙwarai sharri (wato Alhaji Abdul-Majeed).” ​Wadata da Gusau sun yi ƙoƙarin musantawa da nuna iko, amma hannun jami’ai ya dannesu. ​Alkali Cikin zafin rai, bayan ya karanta shaidar da ke cike da sunan Maleekh da Farha da Zayd da kuma Sa’adatu “An tabbatar da cewa akwai shaidu masu ƙarfi da kuma haɗin kai daga waɗanda suke kusa da ku. Wannan kotu ta yanke hukuncin tsare ku a gidan gyara halin na musamman (maximum security prison) har sai an kammala bincike!” ​Wadata ya kalli Gusau da ido cike da tsoro da baƙin ciki. Sun san cewa sun faɗi a wani rami da Maleekh ya haƙa musu. ​An fitar da su daga kotu cikin kaskanci, inda aka sanya su a motar yansanda ta baya a gaban mutane da talabijin yanda kowa zai gansu. Maleekh ya nufi Ethiopia a jirginsa mai zaman kansa (private jet). Ya isa asibitin da ke Ethiopia inda Abban sa (Alhaji Abdul-Majeed) yake kwance. ​Maleekh ya tarar da Abbansa ya farfaɗo daga doguwar sumar da ya shiga. Yana iya aiki sosai da jikinsa amma sai dai tafiya tana ɗan masa wahala kuma yana saurin gajiya saboda yana fama da hawan jini (hypertension) da kuma mummunar rauni na zuciya da ya shiga... ​Alhaji Abdul-Majeed Muryarsa a ɗan raunane, ya ce, “Maleekh! Na san ba ka ci amanata ba wurin kula da Amatu! Na san gaskiya za ta yi nasara! Ina jinjina maka ɗana!” ​Maleekh ya furta. “Haba Abba! Ai gaskiya ta fito! Yanzu Wadata da Gusau suna hannu! Kuma kotu tana buƙatar ka don share sunanka a filin siyasa! A yau zamu tafi.” ​Kasancewar kotu tana buƙatar ganin Abbah, hakan yasa aka bashi keken zama (wheelchair), irin wanda ake tura waɗanda basa iya tafiya. Likita ya ba su takardar shaidar lafiya da kuma izinin tafiya. ​Bayan ƴan awanni a sama, Maleekh da Abba sun dawo gida. Kowa yayi farin cikin dawowar Abbah ciki lafiya. ​A falon gida, Islam da Arfat suka rungumi Abbah suna kuka da murna. ​Amal ta kasa fitowa saboda kunyar haɗa ido take da Abbah saboda yardar da tayi akan shi ya kashe iyayenta tun da farko. ​Alhaji Abdul-Majeed yana zaune a keken sa na zama, kuma ƴan biyu Arhaan da Lihaam Abbah yana riƙe dasu da hannu biyu. Abbah ya ce, “Ina daughter take? Ina Amal? Ku kira min ita yarinya mai juriya!” ​Kowa sai zuwa yake yana gaishe da Abbah. ​Abbah ma yaji mutuwar Farha sosai ya shiga baƙin ciki, sannan ya sha mamakin jin abin da su Alhaji Wadata suka aikata. ​Maleekh ne ya samu Amal a ɗaki, ya rungumeta daga bayanta. ​ Yana faɗin “Ƙaunata, me kike yi a nan? Abba yana son ganinki! Yana son ki fito yaga daughtersa!” ​Amal ta ce, “Kunyarsa nake ji, Ya Maleekh! Ban san me zan ce masa ba! Na zarge shi akan abun da bai aikata ba! Na yi masa laifin da ba zan taɓa mantawa ba! Bana so in fita.” ​Maleekh ya furta. “Bai san kinyi masa haka ba Amal. Ba ya ganin laifin ki! Yana ganin jahilcin makiya ne! Ki fito don farin cikin sa! Sannan don ki girmama shi!” ​Maleekh ya rarrasheta ya bata baki akan ta fito kar taji komai. Ya ɗago fuskarta ya fara shafa mata leɓenta a hankali. ​ “Ki yarda dani, idan kika fito kin nuna tsarki na zuciya! Ki nuna wa Abba cewa yar sa ce ke! I Love You.” Maleekh ya sumbace ta da doguwar sumba wacce ta kwashe duk wani tsoro da kunya a zuciyar Amal. Suka rungume juna da ƙarfi, Maleekh ya bar numfashinsa a jikinta har sai da ta tuna da abubuwan farin ciki da suka faru a baya. Daga nan ya riko hannunta suka fita falon. ​Suna fitowa, Abbah yana kallon ƙofar da murmushi. Ganin Maleekh da Amal sun fito hannu da hannu, ya miƙe duk da wahalar tafiyar, ya ajiye ƴan biyu a kan cinyar Ammy. ​Amal ta gane irin halin da Abbah yake ciki. Ta yi gaggawa ta durƙusa a gabansa da hawaye na gaske.. ​Cikin kuka mai zafi take faɗin “Abbah! Don Allah ka yafe ni! Nayi maka mugun laifi! Na zarge ka akan abinda baka aikata ba! Ka yafe ni! Ina rokonka alfarma!” ​Abbah ya ɗago ta da ƙarfi, ya rungumeta a jikinsa yana faɗin. “Ban taɓa ɗaukar ki a matsayin mai laifi ba! Ke jaruma ce! Ke ƴata ce! Kuma Maleekh ya cika alƙawari! Na yafe miki tun da farko! Yanzu ki daina kuka kuma ki kula da Maleekh da zuriyar ku!..” NEXT NEXT NEXT asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* Asmeetah writer Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 Anan ne labarin Amaleekh ya kawo ƙarshensa. Nagode da kasancewarki/ka a wannan tafiya tun daga farkonta har zuwa nan. Wasu labarai ba sa ƙarewa a shafi na ƙarshe; suna ci gaba ne a cikin zuciyar mai karatu. — END OF AMALEEKH — Nagode da karantawa. 101 to 102 An shirya zaman kotu na biyu don yanke hukunci a kan Alhaji Wadata da Alhaji Gusau. An ɗauki matakan tsaro masu ƙarfi. ​ Abbah ya zo a kekensa na zama tare da Ammy da Maleekh a gefensa. Zayd da Hajiya Sa’adatu sun kasance a gefen Lauyoyin Gwamnati domin bada hujjoji a kan su Wadata da Gusau. Amal tana nan itama sai Islam da Arfat da suke riƙe da ƴan biyu (Arhaan da Liiham)... ​Zayd ya yi doguwar shaida mai raɗaɗi game da shigar da aka yi masa da kuma laifin iyayensa. Hajiya Sa’adatu kuma ta fallasa dukkanin takardun da Wadata ya ɓoye game da kadarorin Gwamna da kuma yadda aka yi kisan kai. ​Alkali ya yanke hukunci, bayan ya saurari dukkanin ɓangarorin: ​Hukuncin alƙali shine. “Saboda kisan kai da aka yi wa Gwamna da matarsa, da kisan kai na Farha, da kuma cin dukiyar al'umma, wannan kotu ta yanke hukuncin zama gidan yari na tsawon shekara 10 ga Alhaji Wadata da Alhaji Gusau, kafin a sake nazari a kan hukuncin da ya dace dasu a matsayinsu na masheƙa!” ​An yi ihun murna a gefe. ​Bayan an fito daga zama kotu, yayin da ake kama su Wadata da Gusau don a kai su gidan yari.. ​Alhaji Gusau ya tsaya a kusan Amal da wani ɗan sanda yana riƙe dashi. Gusau yana mata wani dariya na izgilanci tare da faɗin: ​“Indai kuɗi na aiki to nan da sati biyu zaki ganmu muna yawo a gari a cikin maka-makan motocinmu… Iyayenki mu muka kashe su har lahira! Mahaifiyarki bayan mun sumar da ita muka sa bindiga muka fasa mata ƙwaƙwalwa! Sannan mahaifinki yana ihu a cikin wuta yana neman taimako babu! Har wuta yayi ƙurmus da shi sai ƙwarangwal ɗinsa! Hahahahhh…” ​Amal ta tsaya mutum-mutumi, zuciyarta ta daina bugawa saboda tsananin zafin maganar da ya yi mata. Daga nan ɗan sandan ya ja shi da ƙarfi ganin zai ɓata musu lokaci. ​Amal tana kuka cikin fushi da damuwa. Ba tare da tunani ba, ta saka hannunta a aljihun wani Police da ke kusa da ita ta ciro ƙaramin bindiga (gun). ​Ta saita Alhaji Gusau da hannu bibbiyu take riƙe da bindigar. ​Ta fara harbi! Bullet bai sauƙa a ko ina ba sai a bayan Alh. Gusau. Haka take ta jero harbi a jejjere kafin a dakatar da ita. ​Har ta harba masa harsashi sun yi biyar a jikinsa: ​Wannan bullet a bayan ƙeyarsa. ​Wannan a wuyansa. ​Wannan a bayansa ta saitin tumbinsa. ​Da sauran biyu. ​Maleekh da gudu ya nufo kanta da wasu ƴan sanda. Da sauri aka karɓe bindigar a hannunta. ​Ta faɗa saman ƙirjin Maleekh tana kuka mai tsananin gaske. Daga nan ta zame ƙasa ta kafa gwiwowinta ta shiga tsananin gigita. ​Nan take ƴan jarida har sun mamaye wurin suna ɗaukar hotuna da bidiyo na wannan mummunan yanayi na kisan kai a kofar kotu. ​Shi kuwa Alhaji Gusau har ya gama shure-shurensa ya mutu nan take.. ​Abbah da Ammy da Inna kowa ya tsorata ganin yanda Amal ta ɗauki hukunci a hannunta.. ​An gama da Alhaji Gusau ta hanyar ɗaukar fansa kai tsaye daga Amal. Bayan Amal ta faɗi ƙasa cikin gigita bayan ta kashe Alhaji Gusau a gaban kotu, Maleekh ya rungume ta da ƙarfi. Jami’an tsaro sun kewaye su, kuma ‘yan jarida sun yi rikici wajen ɗaukar hotuna na wannan abin al’ajabi da ya faru. ​An kama Amal nan take saboda kisan kai a fili. A take aka yanke hukuncin kaita gidan gyaran hali itama amma kafin suyi hakan Maleekh ya shiga tsakani tare da Lauyoyinsa masu daraja... ​Maleekh ya rungume ta sosai yana faɗin “Ba za ku iya tafiya da ita ba! Wannan kisan kai ne na kare kai (self-defense) saboda Gusau ya tsoratar da ita da maganganun wulakanci da kisan iyayenta! Zuciyarta ta buga saboda tsananin zafin da ya faɗa! Lauyoyina suna nan kuma za mu yi garanti na beli nan take! Ba zata shiga kurkuku ba!” ​Lauyoyin Maleekh sun yi gaggawa suka yi amfani da hujjoji na cewa Amal ta kasance wacce aka zalunta kuma tabbataccen bayanin kisan da Gusau ya bayar a gaban ta ya haifar mata da gigita ta kwakwalwa (acute psychological trauma), wanda ya sa ta rasa ikon sarrafa kanta. ​An kafa shari’a ta gaggawa don Amal a kan kisan kai. ​A zauren shari’a, Maleekh da Lauyoyinsa sun yi bincike mai zurfi a kan laifukan Gusau da kuma yanayin taɓin hankali da Amal take ciki. ​Lauyan Maleekh ya gabatar da hujjoji guda uku: ​Laifin Gusau, ya tabbatar da cewa shi ne ya kashe iyayen Amal a gaban ta, wanda ya haifar mata da tsananin zafin zuciya. ​Kare Rayuwa, Amal ta ga bindiga kuma ta ɗauka cewa Gusau yana shirin kashe ta... ​Shaidar Likita, Likitan Maleekh ya tabbatar da cewa Amal tana cikin mummunan tashin hankali tun daga rasuwar Farha da kuma gaskiyar da ta ji. ​Alkali ya yanke hukunci: ​ “Duba da laifukan da aka tabbatar na mamacin Alh. Gusau, da kuma hujjojin taɓin hankali da aka kawo na Amal, wannan kotu ba za ta yanke mata hukuncin ɗauri ba... ​Amma dole a yi hukunci saboda an aikata kisan kai a fili. Wannan kotu ta umarci Amal ta shiga cikin kulawar likita (psychological rehabilitation) na tsawon shekara biyu..." ​Maleekh ya yi murna sosai. Ya ceto matarsa daga shiga kurkuku. An daskare dukiyar Wadata, kuma an tabbatar da cewa Wadata zai rayu a gidan yari har abada. ​An kammala shari’a! An gyara wa Alhaji Abdul-majeed sunan sa, an dawo da kadarorin Amal gaba ɗaya, kuma Hajiya Sa’adatu ta yi nadama ta cigaba da zama a gidan Abbah har Allah ya fito mata da miji nagari tunda ba wuce aure tayi ba.. ​Bayan shekara biyu na kulawa da likitoci, Amal ta warke gaba ɗaya daga raunin zuciya. ​Maleekh da Amal sun ci gaba da rayuwa cikin farin ciki da soyayya. Suna kula da yaran su. Suna yawaita ziyartar kabarin Farha don girmama sadaukarwar ta. Yanzu shekaru sun shuɗe. Maleekh da Amal da yaransu Arhaan da Lihaam sun koma gidansu na Maleekh na kansa. Yara sun girma suna da shekara uku-uku yanzu, suna zuwa makaranta cikin gata da kuɗin uba da na uwa... ​Zayd da Islam su ma suna can gidansu, soyayya iya soyayya suna shanta. Islam ma ta haihu, ta haifi mace kyakkyawa a inda ta samu sunan Ammy wato Maryam Inkiya Ummul Khair.. ​A yau an sha hidimar bikin Arfat itama, ta auri Manager Maleekh. Sun sha hidima sosai. A yayinda ita da angonta suka fita Honeymoon can ƙasar Indian. Zayd da Islam da yarinyarsu su ma sun fita yawon shakatawa ƙasar London... ​Maleekh da Amal suna fita aikinsu a tare bayan sun sauƙe yaransu a School, su kuma sai su wuce babban kamfaninsu wanda ya haɓaka sosai... Suna shan soyayya na gaske, kuma babu wani damuwar komai a rayuwarsu. ​❤️ ​Kamar yau da ya kasance ranar weekend, an kai twins can gidan Abbah ziyara. Iya su biyu suka kasance a gida, lokacin bawa soyayya muhimmanci. ​Suna kwance akan gado (King size bed) a babban ɗakin su mai cike da tsarin zamani da kayan alatu da kuma hasken rana mai launi da ke shiga ta madubin ɗakin. ​Maleekh yana kwance yana rungume da Amal ta bayan ta. Ta sanya kanta a kan hannunsa tana jin numfashinsa mai ɗumi. ​Cikin muryar shagala da kasala ta ce, “Hubby na... na gode wa Allah da ya sanya ni cikin rayuwar farin cikinka… bayan dukkanin abin da ya faru…” ​Ya sumbaci gashinta a hankali “Ni ne ya kamata inyi godiya! Ke ce jarumar rayuwata! Kin yi haƙuri da ni lokacin da ba ki san gaskiya ba! Kuma kin yarda dani a lokacin da kowa ya juyamin baya… Ina sonki Amal! Karshen soyayyar ki shine Farin Cikina.” ​Maleekh ya juyar da ita a kan gadon tana fuskantarsa. Ya sanya hannunsa yana shafa fuskarta da siraran leɓenta masu kyau. ​Ya furta a hankali “Har yanzu ina son ki fiye da yadda nake yi tun farko! Soyayyarki ta ƙare mun damuwa! Ki rufe idon ki…” ​Ta rufe idonta cikin gamsuwa da yarda. Ya sunkuya ya fara sumbatar ta a hankali, yana watsa mata kalmomin soyayya a kunnenta. ​ “You are my Queen, my salvation! I Love You... I Love You... I Love You…” ​Ta kankame shi

Chapter 61 of 62