Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bindiga. Sai Maleekh da ya yi nasarar tinkarar zaki da tsananin ƙarfi har ya raunana masa ƙafa, wanda hakan ya sa zaki ya kasa ci gaba da binsu. Anan ne suka fara ƙiran shi 'Lion Man'. ​Sojojin sun fahimci cewa Maleekh yana da zafin rai (intensity), kuma babban mutum ne mai tsananin jarumta da basira. ​Maleekh ya zama cikakken Soja a cikin sansanin, domin aikin training ya ƙara masa jiki da ƙarfi. Ya zama masanin dabarun yaƙi duk da mantuwar da ya yi. ​ Daman yana da tsayi, kuma karfafan jikinsa ya cika da tsoka (muscle-bound), wanda yake nuna cewa mutum ne da yake aiki tuƙuru a harkar motsa jiki. ​ Hasken fatarsa mai laushi ya ƙaru, kuma kwantaccen sumar kansa mai baƙin gaske ya ƙara masa kyau. ​Ya ƙara kyau mai tsanani, wanda ya yi kama da tsararren Balarabe mai ƙarfi da kwarjini.... ​Yana zaune da Sojojin, yana basu training. ​Kwatsam, a yayin da suke tsaka da wani wasan dariya, Maleekh ya ji jikinsa ya yi sanyi sosai. Wani abu ne ya cije shi a zuciyarsa, wani jin daɗi da kuma firgici sun shige shi a lokaci guda. Ya riƙe ƙirjinsa, yana mamakin me ke faruwa da shi. Ya ji kamar yana buƙatar wani abu da yake da nutsuwa.. ​“Akwai buƙatar a ba ni madara in sha, nan take. Wani abu ne nake ji a jikina, amma ban san menene ba.” ​Wani soja ya dube shi da mamaki: “What? Lion! Ko ka fara tuna wani abu ne?” ​Maleekh ya girgiza kai cike da tausasawa ya ce, “Har yanzu dai, ban tuna ba. Amma jikina ya yi sanyi, da alamun akwai abinda ya faru. Kar ku damu, ina kan yin addu’a domin shine kaɗai ban manta ba. Wata rana, haske zai zo mun kuma zan gano kaina.” ​Sojojin sun fahimci cewa Lion yana da haɗin gwiwa na ruhi da wani abu mai mahimmanci a waje. Sun san cewa wannan jin sanyin na iya zama alamar farfaɗowa. Sun tafi da gaggawa domin su samo masa madarar da ya buƙata. 《》《》《》《》《》《》《》《》《》 ​A ɗakin asibiti mai tsada, Amal ta farka daga bacci mai zurfi. Ta ji ƙarfi da nutsuwa sun maye gurbin wahala. ​Ta fara buɗe idanunta a hankali, taci karo da kyawawan jariranta guda biyu. Wata nurse ce ke kula da su a gefen gadonta. ​Amal ta shiga farin ciki sosai. Ta yi kukan murna da godiya ga Allah. Nan da nan ta miƙa hannu, ta ɗauki ɗanta namiji wanda ya yi mata kama da ƙaramin Maleekh. ​Sai dai, duk da murnar, Maleekh yana cikin ranta da kuma zuciyarta. Ta sha alwashin cewa ba za ta taɓa dena kewarsa ba. ​🌟 ​Duk abokan arziki da ’yan uwa sun cika asibitin, domin sai ta samu hutu na musamman kafin su koma gida. Suna ta jiran ganin jariran. ​Amal tana kallon jariran ta yi tunani na musamman game da sadaukarwar Maleekh... ​Amal ta rungume ‘yan biyun, tana furta sunayensu a hankali: ​“Ke sunanki LIHAAM.. kai kuma AR'HAAN.. Ya’yan Maleekh, insha Allah Abbanku zai dawo ya ganku!” ​Ta rungume Ar’haan da Lihaam, tana musu addu’a da tunanin Maleekh a lokaci guda.... Duk mutanen da suka taru a asibiti sun yi mamakin sunayen da Amal ta sa wa jariran, waɗanda ba a taɓa jin su ba. Amma duk da haka, sun yi shiru don mutunta zaɓin uwar... ​Inna wacce ke zaune a gefe, ta kasa jurewa ta ce, “Ai na ɗauka sunan iyayenki da suka rasu za ki sanya musu! Me yasa kika manta da su?” ​Amal cikin ladabi ta ce, “A’a Inna, na tuna da su sosai.” ​Inna ta ce, “To kuwa sai ki sa Abdulsamaad da Khadija… ko kuma ki sa sunan Abbah Maleekh Abdul-Majeed da sunan mahaifiyarsa Maryama…” ​Abbah, yana murmushi, ya shiga tsakani da cewa, “A’a Umah, ki bari kawai. Sunan da tasa ya yi. Ai yanzu an daina yin masu suna domin zamani ya canza. Ki bar yaran su ci gaba da zamani.” ​Inna ta ɗaure fuska ta ce, “To ni ya za a yi da ni? Ni da ban iya faɗin sunayensu ba! Yanzu yaya zan ƙira su?” Islam tana dariya, ta ce: “Inna, zaki iya! Faɗi sunan yaron mu ji!” ​Inna ta motsa baki da ƙyar, ta dage kamar za ta iya furta shi yadda ya dace. Sai ta ce da tsananin murya: “A-ra-ha…” ​Duk suka kwashe da dariya! ​Suka ce, “To Inna, faɗi sunan yarinyar!” ​Nan ma Inna ta daure, ta ce “Haam-ma-ta!” ​Amal ta zaro ido, ta rufe baki, tana dariya: “Inna! Hammata kuma? Ni wallahi kar ki ɓata mun sunan yara!” ​Inna ta ce, “Dan kaniyarki! Haka na iya faɗi, kuma zan rinƙa faɗi! Daga yau haka sunayen suke!” ​Amal ta ce, “To tsaya! Ga inkiyar sunayen masu sauƙi ne. AR'HAAN inkiyarsa shine: ‘Ar’y’. Ita kuma LIHAAM inkiyarta shine: ‘Lii’y’.” ​Inna cikin murna ta ce, “Tooo! Gwanda inkiyar! Zan iya faɗi: Ari da Lili!” ​Amal ta dafe goshi, domin Inna tana shirin sa mata ciwon kai da waɗannan ƙagaggun sunayen nata... ​Abbah yana dariya cikin farin ciki ya ce, “To Daughter, ko za ki gaya mata ma’anar sunayen, da kuma dalilin da kika sanya musu? Wataƙila hakan zai sa ta gane su.” ​Amal ta yi murmushi, wanda ya nuna zurfin tunani da soyayya ta ce, “Shikenan Abbah, ni nasani.” ​Ta fara fayyace musu ma’anar sunayen da kuma dalilin da ya sa ta zaɓe su, tana kallo jariran nata ta ce, ​“Na sanya wa ɗana namiji sunan AR’HAAN saboda yana nufin ‘Jagora’ (The Ruler). Maleekh ya mutu ne domin ya ceci rayuwata, ya sadaukar da kansa don in rayu. Ya zama ‘Jagora’ a cikin wannan faɗan. Na sanya masa wannan sunan don ya tuna min cewa ɗansa dole ne ya zama jarumi kuma mai Gaba-gaba a rayuwarsa, kamar mahaifinsa. Zai zama Mai Jagorantar Rayuwarmu.” ​Ta ɗauki Lihaam, tana ci gaba da furta, ​“Ita kuma Lihaam, sunan yana nufin ‘Girmamawa’ da kuma ‘Tausayi’ (Respect and Compassion). Rayuwarmu ta kasance cikin wulakanci da ƙasƙanci a wajen mutanen dajin. Wannan yarinya za ta kawo mana ‘Girmamawa’ da ‘Tausayi’ a cikin iyalinmu. Kuma zan koyar da ita ta mutunta maza kamar yadda Maleekh ya mutunta rayuwata har ya ceci ni.” ​Kowa ya saurari bayanin Amal da tsananin tausayi da girmamawa. Sun fahimci cewa wannan ba wai zaɓin zamani ba ne kawai, wasiyyar Maleekh ce ta hanyar sunayen jariran.... NEXT NEXT NEXT Allah ya raya mana jikoki wato Ar'haan da Lihaam. 'Ar'y' and 'Lii’y' 🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 87 to 88 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Bayan sun shafe kwanaki a asibiti, Amal da jariranta masu kyau, Ar’haan da Lihaam, sun samu damar komawa gida. An yi musu cikakkiyar kulawa a asibitin. ​Komawarsu gida ya cika da faranta rai da mamaki. An yi wa gidan Abbah ado da balloons da kyaun launi don tarbarsu. ​Ammy da Inna ne suka jagoranci tarbar jariran. ​Inna har rige-rige take don ta ɗauki 'Ari' da 'Lili' (kamar yadda ta ke kiran su).. ​Islam da Arfat sun cika da murna, suna ta daukar hoto da kuma bidiyo na jariran. ​An zaunar da Amal a wani wuri na musamman a cikin babban falon gidan, inda take samun isasshen hutu da kulawa. Bayan mako guda. ​Nan take, aka fara shirye-shiryen hidimar suna. Abbah ya yanke shawarar cewa wannan hidimar za ta kasance babbar hidima don nuna godiya ga Allah. ​“Dole ne mu nuna wa duniya cewa ko da Maleekh ya ɓace, mutuncinsa da abin da ya bari suna da daraja. Wannan suna zai zama bikin Maleekh ne!” ​An ƙira manyan masu shirya biki anan Abuja. ​An tanadi abinci mai yawa na zamani da na gargajiya. An nemi shahararrun masu dafa abinci don su dafa. ​An gina tantuna a babban filin gidan, an yi musu ado da kayatattun kayan alatu da fitilu masu haske. ​ An aika da gayyata ga dukkan manyan abokan arziki, ’yan uwa, da kuma manyan jami’ai a Abuja. Wannan ya zama taron da kowa yake magana a kai. ​Amma a duk cikin farin cikin shirin suna, tambaya ɗaya ce ke ta yawo a zuciyar kowa: “Ina Maleekh?” ​Amal ta yi amfani da lokacinta wajen ba wa jariranta madara da kuma yi musu addu’a. Tana da yakinin cewa Maleekh yana raye, kuma ceton da ta samu ya zama tsanaki cewa Maleekh zai dawo.. ​Amal A Zuciyarta take faɗin, “Zan fara shirin nemanka Maleekh. Ba zan bari ɗana da ‘yata su taso ba tare da sanin Abbansu ba. Wannan bikin suna shine farkon neman dawo da kai.” An yi bikin sunan tagwaye Ar’haan da Lihaam a cikin tsari mai kayatarwa wanda ya dace da darajar iyalan gida. ​An shirya wajen taron da kyakkyawan ado, an kawo manyan makada don nishadantarwa, kuma manyan jama'a sun hallara don taya Abbah murna da kuma nuna girmamawa.. ​A cikin taron, Zayd ya hallara duk da cewa yana cikin fushi.. Hakan nan iyayensa sun hallara su ma. ​A wurin bikin, bayan an gama gabatar da jawabai da kuma kyaututtuka ga Amal da jarirai, an buɗe fili don kowa ya gabatar da murnarsa a gaban taro. ​Zayd ya miƙe. Kowa ya yi shiru, yana tsammanin ko zai faɗi wani abu na cin zarafi ko ɓata rai, kamar yadda ya saba yi wa Amal. ​Zayd ya nufo microphone cikin natsuwa da kwarjini. Ya fara magana da murya mai taushi da girmamawa: ​“Assalamu Alaikum. Ni ne Zayd, Ɗa ga wannan families mai albarka, kuma wanda ya kamata in auri Amal. Na zo nan ne don in nuna girmamawa ta ga Maleekh da kuma iyalai. Na yi farin ciki sosai da Allah Ya ceci Amal kuma Ya ba ta waɗannan kyawawan tagwaye, Ar’haan da Lihaam. A matsayina na dan uwa kuma aboki, ina taya ku murna.” ​Duk mutanen taron sun yi mamaki da wannan juyin magana da ya yi.. ​ Zayd ya juya kansa, ya kalli inda Islam take zaune kusa da Ammy. Ganin Islam ya ƙara masa ƙarfin hali. ​Ya cigaba da maganarsa kamar haka “A ƙarshe, ina so in yi amfani da wannan wuri mai albarka, a gaban duk ‘yan uwa da abokan arziki, don in furta wani abu da yake cikin zuciyata tun lokaci mai tsawo.” ​Ya ɗauki numfashi mai zurfi, ya kalli Abbah da Ammy cikin ladabi, sannan ya koma kan Islam. ​“Yanzu da na fahimci cewa soyayya ta gaskiya tana da wurinta a kaddara, kuma ba a takurawa zuciya... Ni, Zayd, ina son in nemi auren Islam, ‘yar ku mai biyayya. Islam, idan kin karbe ni, ina son ki zama abokiyar rayuwata.” ​Islam ta yi mamaki sosai har ta zaro ido. Ba ta taɓa tunanin cewa Zayd zai yi irin wannan abu ba, musamman a cikin bikin suna! Jikinta ya yi sanyi da zafi lokaci guda. Fuskar ta ta sauya launi saboda tsananin kunya da firgici. ​Abbah da Ammy suka kalli juna cike da mamaki, amma kuma farin ciki ya shige su. Wannan wata alama ce ta rufe shafin baƙin ciki da kuma buɗe sabon shafi na farin ciki a cikin ahali. ​Bayan Zayd ya furta soyayyarsa da kuma neman auren Islam a gaban taro, Islam ta kasa motsi saboda mamaki da tsananin kunya. Dukkannin mutane suna kallonta, suna jiran martaninta. ​Ammy da Abbah sun kalli juna. Abbah ya yi murmushi, wanda ke nuna yarda da kuma begen farin ciki. ​Abbah ya yi magana cikin fara'a ya ce, “Islam, ki duba cikin zuciyarki. Wannan shine kaddarar rayuwa. Ga Zayd ya zo neman ki. Shin kin amince da auren Zayd?” ​Islam ta miƙe a hankali, tana sunkuyar da kai, idanunta na cike da hawayen murna ta ce, “Abbah, na amince. Na karɓe shi.” ​Taro ya cika da ihun murna da godiya. An yi jinjina ga Zayd da Islam. Hakan ya rufe mummunan shafin da ya faru a baya, kuma ya kawo sabuwar yarjejeniya tsakanin iyalai... ​Yayin da taron ya kusa ƙarewa, kuma mutane suna cikin farin ciki da annashuwa, sai ga wani ɗan aike ya shigo da sauri. Ya riƙe wani ƙaramin abu (cassette/memory card), yana mai faɗin: “Ga saƙo da aka ce in isar. Saƙo ne na musamman ga dangin Alhaji Abdul-Majeed. An ce a saka shi a nan take.” ​Kowa ya yi mamaki. Sai wani ma'aikaci ya karɓi memory ɗin, ba tare da sanin bidiyon meye ba, ya soka shi a babban plasman da aka tanada a wurin taron. ​Zayd ne ya zaro ido a ruɗe domin yasan ba alkhairi bane, da sauri ya kalli yanda iyayensa suke. Ganin Alhaji Wadata yanda yake wani irin shu'umin murmushi yasa ya ƙara tabbatar da zarginsa.. Kafin ya ankara. ​Nan take, bidiyon ya fara nunawa: Falo ne mai duhu da aka ɗaure Alhaji Abdulsamaad (Mahaifin Amal) a kan kujera! ​Kowa a wurin taron ya yi shiru. Suka fara ganin wani tsohon bidiyo wanda ya nuna: ​Fuskar Alhaji Abdulsamaad cike da hawaye da firgici. ​Ya fara zayyana maganganu da aka tilasta masa faɗa, cewa: “Alhaji Abdul-Majeed (Abbah Maleekh) shine yake neman rayuwarsa. Kuma ya sa a kashe ni sannan ya kwashe dukiyar da na mallaka….” ​An nuna takardun kuɗi da dukiya da aka karɓe daga hannunsa. ​Bidiyon ya nuna an kashe Hajiya Khadija (Mahaifiyar Amal) wacce ke kwance sumammiya.. ​Bidiyon ya yi showing na ɗan lokaci, sannan ya tsaya. ​Girgiza da tsananin firgici sun mamaye wurin taron. ​Abbah ya miƙe daga kan kujera! Idanunsa sun firfito. Ya kasa magana. ​Ammy da Islam da Arfat sun fashe da kuka mai tsanani. Sun kasa yarda da abin da suka gani. ​Amal ta kalli bidiyon cike da tashin hankali da kuma mamaki! Ta gane mahaifinta! Yanzu ta gane waye sanadin iyayenta! Ta kalli Abbah cikin tsananin mamaki da tunanin cin amana! ​A zuciyarta ta ce, “Shi ne! Abbah ne ya kashe Abbana! Shi ne ya karɓe mana dukiyar mu! Mahaifin Maleekh shine makiyinmu?! Kenam shima Maleekh yasan haka?..” ​Farin cikin bikin suna ya koma gidan alhini da gidan ruɗani a take.. Inna hawaye take tana girgiza kai gaba ɗaya bakinta ya rufe, ta kasa furta komai. Bayan da bidiyon ya tsaya, kuma sirrin mutuwar iyayen Amal ya bayyana a gaban kowa, wurin taron ya zama gidan alhini da rushewa. Mutane sun fara guduwa cikin firgici da mamaki.. ​Amal, wacce ta ga Abbah Maleekh a matsayin makiyi kuma mai cin amanar iyayenta a cikin wannan gajeriyar bidiyo da aka gani, ta kasa jurewa. Damuwar haihuwa, rashin Maleekh, da kuma mummunan cin amana da ta ji daga Abbah, duk sun haɗu. A nan take, ta suma a wurin. Ta faɗi ƙasa tare da kyawawan tagwayenta da ba su san komai ba. Cikin hanzari aka karɓe yaran. ​Abbah, wanda ya kasance mai tsananin gaskiya kuma abokin rayuwar marigayi Abdulsamaad, ya kasa jurewa wannan ƙarya da sharrin da aka jingina masa. Ya fahimci cewa akwai makirci a cikin wannan lamarin. ​Nan take, ya fara tari mai zafi da tsanani, yana riƙe da ƙirjinsa. Yana aman jini a wurin taron. Heart Attack ne yake shirin kama shi, sakamakon tsananin firgici da rashin adalci da aka nuna masa a gaban dukkan mutanen da suke girmama shi. ​Ammy da Islam da Arfat sun shiga gigicewa, gawarwaki biyu a lokaci guda! Sun fara kuka suna ƙoƙarin kula da Abbah wanda yake cikin tsanani. ​Nan take, bidiyon ya fara karade ko ina a kafafen sada zumunta na zamani. Domin an yi live ɗin taron a lokacin, mutane da yawa sun yi recording ɗin bidiyon. ​Labarin ya yadu kamar wutar daji. Mutane sun fara zargin Abbah da cin amanar abokinsa, kisan kai, da kuma kwaɗayin dukiya. ​ An yarda cewa bidiyon gaskiya ne, amma abinda Alhaji Abdulsamaad ya faɗa ya yi wa Alhaji Abdul-Majeed sharrin da bai cancanta ba... Wasu kuma suna cewa yayi video ne a lokacin da ake shirin kai masa farmaki, yasan cewa za'a kashe shi shiyasa ya yi video don abi masa hakki bayan video ya fito. Kuma wanda ya kashe shi shine babban amininsa.. ​Jami'an tsaro sun shiga cikin ruɗani. Sun fara neman bayani kan sirrin mutuwar iyayen Amal wanda aka rufe tun shekaru da yawa. ​An garzaya da Amal da Abbah zuwa Asibitin da aka haifi tagwaye a ciki. ​Amal an shigar da ita ɗakin kulawa ta musamman don ta farfaɗo daga sumewarta. ​Abbah an shigar da shi Sashen Kula da Ciwon Zuciya (Cardiac Care Unit). ​A lokacin da labarin cin amanar da aka jingina wa Abbah ke girgiza Abuja, a sansanin Sojoji kuwa, Maleekh ('Lion') ya sake shiga cikin wani hali mai ban mamaki. ​Sanyin da ya ji a jikinsa lokacin da aka haifi yaran ya canza ya zama tashin hankali da zafin rai mara misaltuwa. ​A lokacin da labarin ya fara yaduwa a gidajen rediyo har ya kai sansanin Sojoji, wani Soja ya ji labarin. ​wani soja a cikinsu ya ce, “Kun ji labari kuwa? Wani babban mai kuɗi a Abuja, Alhaji Abdul-Majeed, wai shi ne ya kashe abokinsa don ya kwace dukiyarsa! Yau an yi masa bidiyo a wurin hidima! Labarin nan ya yi zafi!” ​Maleekh ya ji sunan 'Abdul-Majeed'. Wata igiyar wuta ta shige shi a kwakwalwa. Numfashinsa ya fara sarƙewa. Wani tsanannen zafi ya kama kansa, kamar an ciro wani dutse daga cikin ƙwaƙwalwarsa... ​Maleekh A Zuciyarsa yake faɗin “Maleekh… Abdul-Majeed… Maleekh… na taɓa jin wannan sunan. Amma na manta a yanda naji!…” Da haka suka gama shan hirarsu.. Acan bangaren kuwa.. Amal tana kwance abu na farko da ta tuna shine bidiyon tsohon kisan gilla da kuma karyar cin amanar da aka jingina wa Abbah.. Ta fara kuka mai tsanani a kan gadon asibiti.. “Mahaifin Maleekh! Ka cuce ni! Ka kashe Abbana! Ka kashe Mamana! Me yasa! Ni kuma da na zauna a gidanka, na girmama ka! Ashe dukkan ku makiyanmu ne! Ya Maleekh! Ashe ka san komai!, kasan muguntar Abbanka?!…” ​Zuciyarta ta cika da ƙiyayya da baƙin ciki a kan Abbah, wanda a idonta ya zama ainihin azzalumi da ya yi wa iyayenta kisan gilla. ​Inna ce ke zaune kusa da gadonta, tana kuka a hankali, tana riƙe da hannunta. Tagwaye kuwa suna cikin wani ɗakin kulawa na asibitin. ​Inna cikin kuka ta ce, “Sannu Amatu. Allah ya kawo sauƙi. Ki kwantar da hankalinki. Ki yi ƙarfin hali saboda ‘ya’yanki.” ​Amal ta fizge hannunta da ƙarfi tare da faɗin “Inna! Kin ga bidiyon nan? Kin gani da idanunmu! Sune suka kashe Abbana! Mahaifin Maleekh shine! Ba wai gobara ba ce! Abbah! Macuci ne! Inna, mu gudu! Mu bar nan garin da asibitin nan! Dukkan su makiyanmu ne!” ​Inna ta dafe ƙirjinta ta ce “Subhanal Lahi! Amatu! Kaddara ce! Amma ba haka bane! Ba Abbanku bane, Wannan shiri ne na Alhaji Wadata! Tunda har Zayd ya zo neman auren Islam, ya kasa cin nasara a rayuwarki, yanzu yana son ya lalata mana rayuwa!” ​Amal tana girgiza kai ta ce, “Inna, ki yi shiru! Ba Wadata bane! Amma Abbana ya faɗi da bakinsa cewa Abbah Maleekh ne! Dukkan su macuta ne! Mu gudu, Inna! Kafin su kashe mu kamar yadda suka kashe Iyayena!” ​Amal ta kasa yarda da kowa... ​An sanya tsauraran matakai a wajen ɗakin Abbah, saboda jami'an tsaro suna so su kare shi daga jama'a masu fushi da kuma sababbin matakai na neman kamawa daga wasu jami'ai. ​Amal ta tattara ƙarfin hali ta fito daga ɗakinta, ta nufo ɗakin Abbah duk da tsauraran matakan tsaro. Tana son ta fuskance shi kafin jami’an su cika buri na makiyansa su kama shi. ​A bakin ɗakin, ta tarar da Ammy tana kuka mai zafi tana magana da likita.. ​Amal ta matsa kusa da Ammy, tana kallonta da tsaurin fuska ta ce, “Ina Abban Maleekh? Ina mijinki? Ina macuci?” ​Ammy ta ɗago kai, ta kalli Amal, cike da damuwa da tausayi ta ce, “Amal… ba haka bane! Mijina mutumin kirki ne! Wannan sharri ne! Ya shiga cikin haɗari … ba zai iya magana ba! Ciwon zuciya ya kama shi!” ​Amal ta ce, “Shi ne! Allah ya saka masa! Ya kashe Abbana, yanzu shine yake so ya mutu kenam?! Amma ba zai mutu ba har sai ya gaya mun dalilin da yasa ya ci amanar babban abokinsa!...” ​Amal, ta yi ƙoƙarin kutsa kai don ta ga Abbah wanda yake kwance a kayan aiki na numfashi. Jami'an tsaro suka hanata shiga. ​Amal ta fahimci cewa zama a wannan garin haɗari ne. ​Ta koma ɗakinta da zuciya mai cike da kishi da kuma azama.. ​Amal ta kalli Inna cikin kuka ta ce, “Inna! Mu gudu! Mu ɗauki jariran nan! Zan koma rugan Fulani! A can kawai na san ina da kariya! Bayan haka, zan fara neman Maleekh da kaina! Shi kaɗai ne zai gane min wa ye ainihin azzalumi a cikin wannan labarin tsakaninsa da mahaifinsa!”.. ​Ta fara shiri na gaggawa don guduwa da tagwayenta: Ar'haan da Lihaam, ba tare da sanin halin da zata shiga ba. Yayin da Amal ke shirin guduwa ta bar asibiti tare da jariranta, Inna tana kuwa tana kokarin hanata tafiya. ​Inna ta riƙe hannun Amal da ƙarfi tana faɗin “Amatu! Na san me nake yi! Ni na gudu da ke daga Kaduna saboda na san su waye ainihin masu kisan gilla! Ba mahaifin Maleekh bane! Wallahi Alhaji Wadata ne! Shi da Alhaji Gusau!” ​Amal ta fizge hannunta, fuskarta cike da fushi ta ce, “Inna! Ki daina faɗin haka! Abbana ya faɗa da bakinsa! Ba zan saurari karya ba! Shi ne ainihin azzalumi da ya ci amanar abokinsa! Sai da ya kashe su sannan ya fake da fuskar tausayi! Shi ma Maleekh saboda ɗan ahalinsu ne, shiyasa bai gaya mun gaskiya ba!”. ​Amal ta ƙi yarda da Inna, saboda karyar bidiyo ta yi mata gagarumar tasiri a zuciyarta. ​A can wani gefen kuma, Zayd yasan kullin makirci ne na mahaifinsa da Alhaji Gusau. Ya yanke shawarar tunkarar mahaifinsa duk da tsananin tsoro.. ​Zayd yana magana da ƙarfi, cike da hawaye ya ce, “Daddy! Me yasa! Me yasa kuka yi irin wannan muguntar? Ya isa haka! Zan fita fili in faɗi gaskiya, cewa ku kuka kashe iyayen Amal, ba Abbah Maleekh ba!” ​Alhaji Wadata ya ɗauke Zayd da mari, yana huci ya ce, “Rufe mana baki! Wannan sirri ne na rayuwarka! Idan ka kuskura ka fita da wannan gaskiya, zan sa a kashe ka, kuma za a kashe wanda ka sanya a cikin zuciyarka! Ka manta da hakan!” ​Hajiya Sa’adatu itama ta daka masa tsawa da cewa, “Indai ka fitar da gaskiya, to wallahi tallahi saina tsine maka duniya da lahira! Ka zaɓi farin ciki na gidan nan, ko kuma faɗawa cikin wuta!” ​Zayd ya kasa magana, ya kasa jurewa barazanar iyayensa da kuma tsinewa. Ya yi shiru da batun, amma fushin adalci ya cika zuciyarsa... Hospital. ​Amal ta samu nasarar kutsa kai cikin ɗakin da Abbah yake kwance. An cire wasu na'urorin lura don kula da shi sosai. ​Abbah yana kwance, sanye da Oxygen, idanunsa a rufe. Doctor ya sanar da ya yi paralysis, bai iya motsi ko magana ba. ​Amal ta tsaya kusa da gadonsa, hawaye na zuba a fuskarta, cike da fushi da ƙiyayya. Muryarta na rawa take faɗin “Ka ji daɗi! Ka ji daɗi da abin da ka aikata a rayuwa! Ka kashe Abbana! Ka ci amanar abokinka! Yanzu kuma kunama ta cije ka!…” “Ka kashe su da wuta, yanzu kuma Allah ya ɗaure ka! Ka ga yadda ake yi wa mutum mummunan azaba? Ina Mallam Maleekh yake? Ko da yake, shima yana sane da cin amanar nan!…” “Zan yi amfani da wannan jini da ka bari a jikina (tagwaye) in nuna wa duniya cewa kai azalumi ne kuma macuci! Ba zan taɓa yarda cewa Maleekh mutumin kirki bane, tunda kai ne Abbansa!” Islam da Arfat sun shigo ɗakin a lokacin. Suka ji tsatsar maganganun Amal a kan mahaifinsu wanda ke kwance a kayan aiki na numfashi. ​Islam cike da fushi ta ce, “Ke! Ki daina! Ki rufe mana baki! Ba za ki zo ki ciwa mahaifinmu mutunci ba, alhali yana kwance! Wannan sharri ne!…” ​Arfat ta matso gaban Amal, fuskarta cike da hawaye da fushi ta ce, “Ki fita daga nan! kuma ki fice daga rayuwarmu! Ƙarya kike yi! Ba

Chapter 55 of 62