Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Sai ta latsa OFF a mic ɗinta da ƙarfin ikon zuciya, sannan ta fita daga studio ba tare da faɗa wa kowa ba. Jawabin Amal ya girgiza Nigeria. Yana nan a YouTube, Twitter, da kafafen duniya. Jama’a sun daina kallon Amal a matsayin karamar yarinya daga gidan talakawa, yanzu tana da murya da muryarta ta girgiza kujerun gwamnati. BBC Hausa ta buƙaci hira da ita. CNN ta wallafa labarinta tare da taken: “The Girl Who Said No to Billions” TVC da NTA sun fara duba yadda zasu kare kanta da shari’a ko rahoton kare hakkin ɗan adam. Youths a duk faɗin Najeriya sun fara wallafa hotonta da taken #AmalVoiceOfTruth Masu adawa da gwamnati sun fara cewa: “A sa Amal cikin tsaro kafin wani abu ya faru da ita.” A Rayuwa FM, ma’aikata sun tsaya kafaɗa da kafaɗa da ita. Hatta wasu da suka fara ganin kamar ba'a cikin hayyacinta take ba, yanzu suna ganin she's the real deal. Maleekh kuwa, da ya koma gida bayan ganawar su, yana jin kalmomin da Amal ta furta a kafafen sada zumunta da rediyo, zuciyarsa ta ɓaci matuƙa. A fusace yake, yana cikin babban ɗakin sa a gidan Abuja, yana cizon yatsa yana kallon screen ɗin laptop ɗinsa tare da faɗin: “She played me? In front of the whole country? Na zo da girmana, na zo da kuɗina, she made me a fool!” PA ɗinsa ya shigo yana ba shi shawara. Ya ce: “Sir, ba za ka iya murƙusheta da girman kai ba. Ka bita a hankali. Ka rinƙa nuna kuɗaɗe. Ka bari ta ga salama. Ka sa ta yi tunanin muna ba ta girma, muna mutuntata da darajata.” Maleekh ya lumshe ido, ya juya daga window, ya furta: "Fine. Za mu bi ta da salo cikin nutsuwa. Amma ka fahimta da kyau, zan mallaki muryar yarinyar nan, ko kuma na kashe ta. Babu wanda ke ran Maleekh Abdul-Majeed a ƙasarsa!".... Sun shirya: Zasu haɗu da wata ƙungiyar kamfani daga ƙasar waje da suka zo kafa sabuwar FM a Abuja. Zasu yi collaboration da Rikky Blaze wanda shima yana da muradin karɓar Amal daga Rayuwa FM. Zasu shirya mata alƙawari da tsarin waje da zata je yi interview, sai su jawo ta da kuɗi, matsayi da haɗa baki da manyan masu ruwa da tsaki. Amma ba su sani ba Amal ta riga ta bar haske a zukatan mutane kuma idan aka ɗan taɓa ta, zasu taɓa wuta mai cin ciyawa a duniya. Bayan jawabin Amal ya karaɗe Nigeria da duniya, Maleekh da PA ɗinsa sun dawo da dabaru masu laushi ba da nuna dama da kwarjini ba, ba da haɗari da bugu kai tsaye ba. Wannan shine shirin da suke ƙira da Soft Power Strategy. "Ba za mu yi faɗa da ita ba. Zamu jawo ta ne. Mu saka ta cikin kwanciyar hankali, mu sa ta gane cewa zama da mu shine mafita." Abubuwan da suka haɗa da shirin: ☆ Sanya mata gayyata daga kamfanin waje: Wani kamfani daga ƙasar Amurka, wanda Maleekh ya haɗa da Rikky Blaze, ya rubuta mata wata gayyata zuwa taron masu ruwa da tsaki akan ‘Freedom of Media in Africa’. Amal na ɗaya daga cikin waɗanda aka zaɓa. Za’a biya duk kuɗin tafiya, hotel, da tsaro. Zasu kuma saka mata alƙawarin idan ta bayyana ra’ayinta a taron, to zata samu damar aiki da Al Jazeera ko BBC. ☆Tura mata saƙo daga sunan wani NGO: Sun kafa wani bogus NGO suna kare ‘yan jarida mata a Afrika. Suna son bayar da grant na miliyan dari (₦100 million) don kafa Gidan Matasa Na Gaskiya. Amma sharaɗin shine dole ta daina sukan gwamnati kai tsaye kuma ta yi “neutral” reporting. Bayan an aikawa Amal wannan saƙon, ta karanta sharuɗɗan kuma ta fara jin cewa wannan ba taimako bane wata hanya ce ta rufe bakinta da kuɗi.... Amal sam ta ƙi yadda da wannan batun, tana shirin watsa musu ƙasa a ido ... An sa wasu fitattun 'yan jarida da take daraja su, da su ƙira ta, su janyo hankalinta... Haka take ganin saƙon wasu daga cikin manyan ƴan jarida su na faɗin: "Kar ki wuce gona da iri. Amal..." "A da akwai irin ki, amma a yanzu sun ɓace, babu labarin su .." "Mu mun daɗe muna fafutuka, amma muna da hikima, ba zafi-zafi ba." Amma Amal ta fahimta: suna ƙoƙarin daƙile zuciyarta da sunan shawara da nasiha ne.. Amal ta ci alwashin babu wanda zai ci nasara akan ta Indai ba ta hanyar Allah ba... A wannan karon ma ta sake bijire musu... Ganin haka yasa maleekh yin amfani da hukumomi ta hanyar barazana.. Maleekh ya yi amfani da ƙarfin mahaifinsa, babban ɗan siyasa mai ƙarfi a Abuja. Ya fara saka kafafen gwamnati su dinga kawo matsalolin Amal ta hanya biyu. Hukumar Bincike (CID) sun fara watsa bayanai akan Amal, sannan suna gayyatar ta... "Tana watsa bayanan ƙarya da ke haddasa rikici.” "Sun ƙirƙiri ƙorafi akan ta bisa wasu hotuna da suke cewa sun wuce gona da iri a social media ta hanyar Editing... Sun tura mata “Notice of Investigation” da barazana. idan ta ƙi halarta, zata fuskanci ɗaukar mataki bisa doka. Gidajen rediyo da ke da alaƙa da gwamnati sun fara ƙin gayyatar ta: An hana ta shiga wasu forums. An daina wallafa labaran da suke ƙara mata daraja. An saka ido akan Rayuwa FM. Haka nan an tura mata barazana ta email cewa: “If you don’t stop, someone else will stop you.” An kafa wasu “fake social media accounts” suna ɓata sunanta: Suna zagin ta da ƙiran ta marar ladabi... Suna yaɗa cewar tana ƙarya da ƙirƙirar labarai. Suna cewa Amal tana da “hidden sponsors” daga jami’an ƙetare.... Amma duk da wannan, Amal tayi amfani da mic ɗin ta Ta ce: “Wannan duk bai game ni ba, domin kowa yasan wace ce Amal Abdulsamaad.... Wannan game da 'yan Nigeria ne. Idan suna ƙoƙarin tsoratar da ni to muryata ƙara volume take wurin faɗan abinda basa son ji... Idan suka yi shiru, haka nan zan cigaba da gudanar da aikina akan tsari na....” Duk da wannan barazanar Amal bata je gayyatar da aka mata ba daga (CID) domin ta san duk shirin Maleekh ne, tana ji a ranta cewa ta gagare shi.... Yau ce ranar da aka fi sauraron Rayuwa FM tun kafuwarta. Mutane daga kowane lungu na Najeriya da ma ƙasashen waje sun sa kunne, domin sun ji labarin cewa Amal zata bayyana a cikin shirin rana na musamman mai taken: "Gaskiya Bata da Tsoro." A cikin studio, Amal na zauna a gaban microphone. Fuskar ta ɗauke da murmushi, idanunta cike suke da ƙarfi da jarumta. Bata buƙatar takarda a gabanta, zuciyarta ita ce 'kundin bayananta. Da Muryar ta mai sanyi ta fara da sallama... “Assalamu alaikum, masu sauraro. Sunana Amal Abdulsamaad, kuma ni ce ke magana da ku a yau daga Rayuwa FM. A yau zan faɗi gaskiya, komai tsanani, domin ina sane da cewa rayuwar gaskiya ta fi rayuwar tsoro tsawo.... A cikin kwanakin baya, na fuskanci abubuwa da ba zan iya karyatawa ba. Na sha wahala, na sha barazana, na sha alƙawari masu laushi da makudan kuɗaɗe. Amma ni ɗaya ce kuma da ikon Allah zan tsaya tsayin daka.” ta numfasa, murya ta ɗan ɗaga.. Sannan ta cigaba “Sun ƙirani da ƴar talakawa eh, hakane. Ni ƴar talakawa ce. Amma ku sani, ƙarfin talaka a Najeriya yana cikin muryarsa. Kuma muryar nan, ku na ƙoƙarin kashe ta ta hanyar tsoro, da kuɗi, da bita-da-'kulli.” “Na karɓi gayyata daga kamfanin waje. Na karɓi ‘offer’ na biliyoyi don inyi shiru. Na fuskanci barazanar kashe ni da kakata. Amma ku sani, ina da abin da ku ba ku da shi, gaskiya da amana ga al’umma. Wanda kuke tsammanin zai saye ni da kuɗin duniya, ku gaya masa wannan: ‘Amal ba tasa ba ce.’ Ni ba za a taɓa saya ta ba. Ni ba zan yi shiru ba. Ni ba zan zuba ido gwamnati ko ɗan siyasa ya ci mutuncin talaka ba."..... ta tsaya kaɗan, sannan cikin rawar murya take faɗin: “Kuma ku sani... Ku da kuke cewa ba zan daɗe ba, ku da kuke cewa za a wayi gari ba labarina yau kuna ji na, duniya tana ji na. Idan na faɗi gobe, tarihin zai tuna da ni.” A lokacin da ta gama jawabin, Facebook, Twitter (X), Instagram da YouTube sun cika da hashtag ɗin: #AmalGaskiyaCe #BabuSiyasarKarya #TalakaNaDaMurya #RayuwaFMForTruth Mutane sun yi ta mayar da martani. Wasu suna kuka da yabon jarumtar ta. Wasu daga cikin ‘yan siyasar da ke biyayya ga Maleekh sun shiga rikicewa da neman hanyar kare kansu. A Ƙarshen Shirin: Rayuwa FM ta ƙara daraja. An ƙira Amal daga kasashen waje domin gabatar da jawabi a UN Women Conference. Wasu daga cikin matasa a Najeriya sun fara kafa #AmalMovement, wata sabuwar fafutuka akan gaskiya, adalci, da kariyar ‘yan jarida.... Bayan jawabin Amal da ya girgiza kasar, gidajen rediyo da kafafen sadarwa suka bazama da labari. Amma wannan ƙwazon da gaskiya bai yiwa manyan masu mulki daɗi ba. A rana ta uku bayan jawabin: An aika wa Rayuwa FM da Takarda daga Hukumar NBC (National Broadcasting Commission) cewa: “Mun lura da yadda gidan rediyonku ke gabatar da shirin da zai iya tayar da ƙayar baya, tunzura jama’a da kuma barazana ga zaman lafiya da ɗorewar tsarin dimokuraɗiyya. Dole ku kare kanku ko a dakatar da lasisin ku na wucin gadi.” Wannan wasiƙar ta rikita shugaban Rayuwa FM. Amal, da sauran ma’aikata, suka shiga damuwa. Amma Amal ta tsaya da kafafunta tana faɗin “Idan muryarmu ce matsala, to me ya rage ga talaka? Idan gaskiya ce laifi, to me ya rage wa ƙasa?” Masu goyon bayan gwamnatin mahaifin Maleekh sun shiga aiki: Wasu kafafen yaɗa labarai da suke da nasaba da gwamnati sun fara ƙirƙirar rahotanni kan cewa Amal tana da alaƙa da wasu foreign agents da ke shirin juyin mulki da tada hankali. Sunce wai “Amal tana amfani da media wajen ɗaga hankali a Najeriya”. Wasu rahotanni na bogi sunce Amal tana karɓar kuɗi daga ‘yan adawa. A hakikanin gaskiya, komai ƙarya ne amma yana da nufin ɓata suna da haddasa tsaiko a karfinta. Wasu Manyan ‘yan siyasa sun shirya ƙulla zargin da zata iya jefa Amal cikin matsala. An fara tattaunawa akan ƙirƙirar Fake Account da za su ɗora mata zargin “Cyber Crime”. Ana shirya “leak” na wasu bayanai na ƙarya don nuna cewa Amal tana amfani da Rayuwa FM wajen tura saƙonnin da suka saɓawa dokokin Najeriya. Suna so su fitar da hujja cewa tana da alaƙa da “Groups of Dissidents”. Shugaban Rayuwa FM ya shiga firgici. Ya kira Amal a office ya ce “Amal… kina so in rasa lasisi? Kina so a kulle ni da iyalai na? Wannan ba yaƙi bane na jarida, yaƙi ne da gwamnatin da ba ta jin tsoron amfani da ƙarfi.” Amal ta kalle shi cike da tausayi, amma bata nuna tsoro ba. Ta ce da shi. “Ina da gaskiya. Idan muka mutu da ita, zamu rayu cikin tarihi. Amma idan muka yi shiru zamu rayu cikin jin kunya ne.”... ★★★ Ƙungiyoyin kare ‘yancin faɗan albarkacin baki daga waje kamar su Amnesty International da Reporters Without Borders sun fara nuna damuwa. Sun fitar da sanarwa suna kare Amal da Rayuwa FM. Sunce. “Ƴancin faɗar gaskiya shine ginshikin demokirad'iyya. Kowane hari akan Amal hari ne akan ‘yan jarida a Afrika.” Reactions daga Jama’a: Matasa sun fara zanga-zangar lumana. Sun ɗauko kwalaye suna rubuta: “Babu Rikon Gaskiya Sai Rayuwa FM” “Amal Voice of the Voiceless” “Kada Ku Kashe Gaskiya” Amal ta tsinci kanta a tsakiyar wani yaƙi wanda ko za ta tsaya ta faɗi gaskiya, ko ta ja baya ta zauna cikin tsoro....... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 11 to 12 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Bayan kwana biyu, Amal tana zaune tare da Innar ta sai ga ƙira daga wayanta, dubawan da zata yi taga unknown number, cike da mamaki take bin ƙiran da kallo har ya yanke, still ƙiran ne ya sake shigo wa, Inna ta ce "Amal wa yake ta danna miki ƙira haka? ki ɗauka mana..." Amal tana girgiza kai ta ce "Inna ƙiran ba number ba suna, ban san waye bane..." Inna ta ce "Kada ki kuskura ki ɗauka to, kar kije masu shan jini ne, yanzu su zuƙe mun ke, ga shi ba wani auki gare ki ba..." Murmushi Amal tayi tana kallon Inna ta ce "Inna ke ma dai kinsan inada kumari, yanzu ne da matsaloli suka yi yawa ne duk na rarrame..." Har Inna ta buɗe baki zata yi magana suka sake jin wayar tana ringing, still irin ƙiran ɗazu ne, Amal ta ce "Inna bari kawai na ɗaga, ba abin da zai faru da yardar Allah..." Inna ta ce "To! Kiyi Bismillahi. .." Amal tana ɗaga ƙiran tayi shiru, tana sauraron wanda ya ƙira, jin wani irin sassanyar murya ne yasa ta lumshe ido domin har cikin zuciyarta ta ji shauƙin muryar.... Other site. "Amal Abdulsamaad! Da bazaki ɗauki ƙiran bane?..." Amal ta ce "wa ke magana?..." Ya ce "Maƙiyin ki..." Murmushi Amal ta yi sannan ta ce "Maƙiya na suna da yawa, sai dai ban san waye a ciki ba..." "Your big enemy..." in short answer ya bata... Ta ce "Ina sauraronka Maleekh Abdul-Majeed..." "Ina so mu haɗu urgently, wannan karon ba wai siyan gaskiyarki zanyi ba..." Ta ce "ai kaima kasan gaskiyata bazata taɓa sayuwa ba, koda zaka ƙarar da dukiyarka gaba ɗaya. .." Girgiza kai ya yi a bangaren sa, yana Jajanta wa kansa domin Amal tana kashe shi da magana.... Ba tare da ya ƙara furta wani abu ba, ya ce "PA ɗina zai zo ya ɗauke ki, ki shirya..." Daga nan ya katse ƙiran.... Inna ce take kasa kunne taji meke faruwa, tana kallon Amal ta ce "Ke da wa kuma?..." Amal ta ce "inaso zan je ƙiran sa ne, ko ma menene zan je naji, domin naga alamar wasan bai ƙare ba..." Inna ta ce "Kar kuma kije ya cutar da ke..." Amal ta ce "kiyi haƙuri kawai Inna, amma sai na je..." Bayan karɓar ƙira daga Maleekh, Amal ta gyara shigar ta cikin tsari, Duk da cewar tana cikin haɗari, amma zuciyarta na da natsuwa da ƙarfin hali. Inna ta riƙe hannunta tana faɗin “Amal… ki je da addu’a. Kina kare gaskiya, domin Allah baya barin mai gaskiya. Ki kula da kanki.” ●● ● A bakin titi wani mota mai duhu ne ya tsaya. Amal ta shigo cikin motar ba tare da tsoro ba, domin ta gane PA Maleekh ne ke cikin motar. Yayi mata sallama cikin ladabi, yana ƙoƙarin ɓoye wani damuwa a fuskarsa. “Please, ki kwantar da hankalinki. Boss yana so ku fahimci juna ne kawai,” in ji PA Maleekh. Ba tare da Amal ta saurare shi ba haka ya ja motar suka tafi... Sun yi tafiyar da ba ta wuce mintuna 20 ba zuwa wani wuri bayan gari mai cike da sirri da shuke-shuke, inda aka tanada wani ɗan fili da kayan alatu. Maleekh yana zaune a kujerar fata yana zuƙar shisha, idonsa a lulluɓe cikin tunani mai nauyi. Bai ce komai ba lokacin da Amal ta iso, Sai bayan ta zauna, ya ɗago kansa a hankali yana faɗin “Amal… I didn’t call you here to fight. I just want you to see that we can both win, not lose...” Amal ta gyara zama da natsuwa, idonta a kansa ba tare da kamewa ba ta ce “Kayi min tayin da ya ƙunshi yarjejeniyar kuɗi da murd'iya. Amma abinda kake so shine sayen raina ne, ba haɗin gwiwa ba.” Kafin su cigaba da magana, sai ga motoci biyu sun shigo da gudu. Mutane kusan shida suka fara fitowa da gaggawa sanye da baƙin kaya, fuskokinsu a lulluɓe, suna riƙe da manyan bindigogi. PA ya firgita yana duban Maleekh ya ce “Sir! Su waye waɗannan? Wa ya turo su? Kai ne ake nema ko Amal?” Maleekh ya miƙe da sauri yana faɗin: “Wallahi I don’t know them! This is not my doing!” Mutanen sun fara harbin sama, tare da nufar wajen da suke. Amal ta tsaya gaban kujerar da Maleekh yake a da, tana duba ko wani zai yi harin kai tsaye. A gabansa ta tsaya tana masa kallon ƙurilla sannan ta ce “Ka shirya kashe ni ne a gabanka Maleekh? Ko wannan wani sabon shiri ne na buga min drama?” Maleekh bai ce uffan ba. Zuciyarsa ta shiga ruɗani domin bai san da shirin komai ba. Kamar yadda ake gani, wannan farmakin ya danganta da wasu makarkashiyar siyasa da mahaifinsa ke ciki... Amal na dafe da zuciya tana kallon Maleekh da tuhuma ta kuma cewa “Ka zaɓi harkar da zata hallaka ka, ba harkata ba. Zan kare gaskiya har ƙarshen numfashina. Kuma wallahi idan ka shiga sahun Maƙiyan talakawa, na rantse da Allah sai na fallasa ka, kai da duk abinda kake wakilta.” Maleekh ya kasa cewa komai. Wannan shine karon farko da wani ya fuskance shi da irin wannan nauyin magana, ba tare da jin shakkar sa ba... Wurin yayi shiru na ƴan daƙiƙu kafin ƴan daban su kewaye su, ƴan daba fiye da shida, kowanne da bindiga da sanda da wuƙa a hannu. Sun kewaye Amal da Maleekh da PA cikin yanayi na barazana. Maleekh zama ya yi akan kujerarsa tare da ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya, yana ƙoƙarin naɗe hannun rigarsa yana shirin faɗa da su, sai dai kamar wanda bashi da kwarin guiwa sosai. PA yana gefe da baƙin gilashi yana satar kallon waɗanda suka kewaye su.... Amal tana tsaye a tsakiya. Idonta kamar wutar lantarki, zuciyarta kamar karfe. Bata motsa ba sai lokacin da ɗaya daga cikin ɗan daban ya ƙaraso da gaggawa yana son ɗora hannunsa a kanta. “Karka kuskura!” Ta faɗa cikin murya mai ƙarfi. Kafin yayi wani motsi, naushinta ya sauƙa a tsakiyar tsuriyarsa, ihu ya sakar tare da juyawa gefe yana faɗin “Kai! Wace irin mace ce wannan?” Da sauri sauran suka nufi wurinta amma su ma, Amal bata tsaya jira ba. Cikin basira da saurin motsi kamar wacce ta sha horo daga dakarun sojoji, ta fara kai musu naushi, harbin ƙafa da karfi, nan ta kayar da mutum biyu ƙasi... Wurin da tasan dole idan aka daki namiji a wurin zaiji nan take kai harin ta... Maleekh da PA sun tsaya cak! cikin mamaki. Maleekh har yanzu yana sanye da baƙin gilashin idanu, amma zuciyarsa ta fara harbawa da sauri. Ya kasa furta kalma, zuciyarsa na tantama “Wannan yarinyar me take da ita?” Amal ta ɗaga wani ƙarfe a ƙasa, ta fara dukansu da shi, tana buga musu akai, duk da bindigunsu da wuƙake ba abinda suka iya.. Sai dai a gefe guda, wani daga cikin ‘yan daban ya ratsa gefe, ya zagayo bayan Maleekh da wuƙa a hannu kai tsaye yana son ɗora masa wuƙa a wuya, daman wurin shi aka turo su... “Maleekh!” Amal ta furta da ƙarfi, sannan da gudu ta finciko shi daga kujerar da yake har suka faɗa ƙasi... Maleekh ne ya faɗo kan Amal, ya rufe ta da jikinsa. Amma wannan motsi ya sa jikin Maleekh yayi weak, yana kwance a kanta, zuciyarsa na bugawa kamar wacce zata fasa ƙirjinsa. Suna kallon juna. Amal kwance a ƙasa yayin da shi kuma Maleekh yake saman kanta. Haka numfashinsu yake haɗuwa yana bada sabon sautin, kallon juna suka shiga yi ba wanda ya iya ɗagewa, haka suka ji tamkar lokaci ya tsaya cak. Duniya ta daina motsi..... Kamar wani abu mai girma yana shirin faɗowa cikin zukatansu … PA ne ya ƙaraso da sauri, ya yi ƙoƙarin ɗago Maleekh daga saman Amal yana cewa: “Sir! Ka tashi… mutane sun taru… ’yan jaridu sun fara ɗaukar video!” Da sauri Maleekh ya tashi, ya nufi motarsa ba tare da cewa komai ba. Ya shige cikin motarsa, zuciyarsa cike da d'imuwa da ruɗani. PA ya zagaya cikin gaggawa ya ja motar, barin wurin da mutane ke ɗaukar hotuna da bidiyo yayi amma idon Maleekh na kan Amal har suka bar wurin... Amal kuma... Mata biyu daga cikin ma’aikatan gidan rediyo Rayuwa FM suka ƙaraso cikin gaggawa. Sun ɗago da ita suna ƙoƙarin karkaɗe ƙasa daga jikinta, tare da faɗin “Ki daure Amal… ki tsaya mana… kin fi kowa ƙarfin hali!” Amal bata iya magana ba, tana sauƙe numfashi, tana kallon saman sararin sama, kamar me fassara zuciyarta. ●●● An riga an ɗauki video lokacin da Maleekh ya faɗo kan Amal yana kwance, lokacin da ta ceto rayuwarsa, lokacin da kallon idonsu ya haɗu. Duniya bata ji bayani ba tukuna, amma magana ta fara yawo. Kwanaki biyu bidiyon Amal da Maleekh ya karkaɗe duniya, Twitter, TikTok, Instagram da dukkan kafafen labarai sun ƙone da sharhi, faɗa, jin daɗi, mamaki da ruɗani. 🌍 RA'AYIN JAMA'A: “Wannan fa jaruma ce, ba mace ba!” “Wata mace ce ta ceci babban attajiri kamar Maleekh?” “Da alama akwai wani abu a zuciyar Maleekh yanzu…” “Gaskiya Amal tayi bajinta, wannan video yafi duk hoton soyayya da na gani.” JARIDU SUN YI RUBUTU. Vanguard, Premium Times, The Nation da Daily Trust sun buga labarai kamar: “Amal, Matar da ta ceci rayuwar Maleekh a harin ƴan daba” “Ɗiyar Talakawa da ta juyar da hankali a Najeriya, Wacece Amal?” “CashTalk FM ya shiga rikici bayan bidiyon Shugabansu da Amal” RAYUWA FM🎤 Bayan kwana uku, Amal ta koma Rayuwa FM, cikin shiri na musamman da suka yi wa suna: “Soft Power: Lokacin da ƴan talakawa suka dawo da iko.” Tana sanye da doguwar riga abaya, kanta a rufe da gyalen abaya, Tana da kwarin guiwa, da nutsuwa. Ta kunna mic ɗinta, sannan ta ce cikin murya mai ƙarfi da lumana ta fara jawabi “Assalamu Alaikum wa rahmatullah… Sunana Amal Abdulsamaad. Ni jika ce ga Inna, talaka ce, mace ce mai cikakken hankali da imani. A cikin wannan bidiyon da kuka gani, ni ce a ƙasa. Na ceci rayuwar wanda yake da iko, kuɗi, suna da ƙarfafa gwamnati. Na ceci Maleekh. Amma kafin hakan, an yi ƙoƙarin kashe ni, a tsorata ni, a siye ni, a ruɗe ni da maƙudan kuɗaɗe, An nemi in miƙa gaskiyata domin su mallaki zuciyata. Amma ku sani, kuɗi ba gaskiya bane. Iko ba shine girmamawa ba. Gaskiya bata cika da ƙarfin tsiya. Bata jin tsoro. Kuma daga yau zan ci gaba da faɗan gaskiya a kowanne lokaci.” Amal tayi wannan jawabin ne domin ta kawar da wannan maganar video da ake jita-jitar sanar da cewa soyayya ce.. Jama'a a kafafen sada zumunta sun ɗaura taken: #AmalVoice #JarumaAmal #TruthShines Kuma Rayuwa FM ta samu ƙarin masu sauraro fiye da kowane lokaci.... ●●●● Maleekh yana kwance a cikin yacht ɗinsa a cikin swimmingpool dake cikin wantalelen gidan su, yana kallon bidiyon da aka ɗauka lokacin da ya faɗo akan Amal..... A cikin ransa ya furta “Why can't I stop watching this video... Who are you, Amal?” A lokacin ne PA ɗinsa ya shigo, ya ce masa: “Sir… da alama gaskiya ta fara kashe ƙarya. Abinda ka yi da Amal ya fara cin riba.” Maleekh bai ce komai ba. Ya zuba ido cikin bidiyon… ya maimaita kalmarta da murya mai sanyi... “Kuɗi ba gaskiya bane.” RA'AYIN JAMA'A A KAFAFEN SADA ZUMUNTA.. @RealTalkNaija: “Maleekh na kwance akan Amal kamar drama na Nollywood 😭 Abin ya fita a rai!” @QueenLami: “Wannan ba ceto bane kawai. Wannan soyayya ce da basu shirya yarda da ita ba 😍” @VoiceOfKaduna: “Kusan shekara biyar kenan da ba a ga Maleekh da mace a dandalin jama’a ba. Amma yanzu Amal ta jawo shi da zuciya.” #AmLeek #AmalAndMaleek #RayuwarSoyayya A wannan ranar Amal kwana tayi tana

Chapter 7 of 62