murya:
“Banda lafiya ne, sir…”
Ya ɗan lanƙwasa wuya:
“Awa kika sanar?…”
Ta ɗan sunkuyar da kai:
“Sorry, sir…”
Ya yi dariyar raini, yana murmushin mugunta:
“Ba haka kawai ba, Amal. Akwai abubuwan da nake son sanar miki. Ba sirri bane, kuma ba ɓoye miki nake ba, domin ba tsoronki nake ji ba.”
Ta ɗan ɗago kai cikin ƙarfin hali:
“Ina sauraronka.”
Ya miƙe daga kujerarsa, yana tafe a hankali har ya tsaya kusa da taga, yana kallon waje.
“Oh, sorry ban baki izinin zama ba ko? Amma ba buƙatar haka.”
Sai ya juyo da idanu masu kaifi yana mata wani irin kallo sannan ya ce:
“Kin ma san waye Maleekh Cash Bank kuwa?”
Amal ta ɗan motsa baki:
“Na san shi tun kafin na kawo wannan matsayin. Hasali ma saboda shi na zo Abuja.”
Ya gyara murya:
“Good! Fatan baki manta irin ɗabi’unsa tun farkon haɗuwarki da shi a Kaduna?”
Amal ta ce cikin mamaki:
“Me ya kawo wannan maganar?”
Ya ɗan murmusa, yana matsowa kusa da ita kadan:
“Ina so ki tariyo baya. Lokacin da kike ƙazamar yar jarida a ƙaramar gidan rediyo Rayuwa FM Kaduna… kina sanye da kodadden kaya, kina ta surutai, kina cika mutane da maganganun banza.”
Sai ya juyo da ƙarfi yana kallonta kai tsaye:
“Kin manta irin kalaman ki a rediyo? Ke ce kike cewa Maleekh Cash Bank mai girman kai ne, mai lalata zuciya, mai sayar da zuciyar talakawa and so so so so!”
Amal ta tsaya cak. Hankalinta ya soma rikicewa.
“Me ya kawo wannan yanzu?”
Ya cigaba da magana kamar wanda yake karanta rubutu daga zuciya:
“A lokacin kin zubar mun da mutunci. A gaban mutane kika raina ni, kika ba ni suna mai tozarci. Amma na shiga zuciyarki domin baki soyayyata… na nuna miki, amma kika mayarni mahaukaci, kika sa mutane suna mun dariya. Har kina da bakin cewa ‘idan da gaske yake sona, ya fito ya furta soyayya a gaban duniya' shin ba haka kika sanar wa ƙanwata Aisha ba?.."
Ya ɗan murmusa sannan ya cigaba da faɗin.
“Na fito, Amal. Na furta soyayyata a gaban duniya. Amma me kika rama mun? Mari! A gaban dubban mutane, cin mutunci da tozarci kala-kala…
Na yi siyayya na aika gidanku amma haka kika rabar da kayan wa mutanen unguwa sannan kika riƙe kwalar rigata kika fitar dani daga gidanku, kika yi mun korar kare a gaban ƙazaman mutanen unguwar, da girma na da mutunci na da daraja ta..."
Ya juya ya kunna computer ɗinsa, ya janyo fayil, sai ga video clip ɗin lokacin da Amal ta mare shi a Kaduna.
A cikin video ɗin, muryarta tana faɗin:
“Join yourself, Maleekh! Bana sonka kuma ba zan taɓa sonka ba!”
Ya juyo ya nuna mata screen ɗin.
“Kin san irin zuciyar da Maleekh yake da ita kuwa?”
Amal ta kasa magana, ta jingina da bango, numfashinta na sarkewa...
“Ni ba na barin mutum har sai na ɗau fansa. Rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai kaya. Na ce sai na rama abinda kika mun… sai na sa zuciyarki ta ƙone kamar toka...”
Ya ɗan yi shiru, sannan ya furta da murya mai zurfi:
“Na rantse sai na yi wasan ball da rayuwarki, Amal. Sai kinyi kukan da baki taɓa yi a rayuwarki ba…”
Amal ta kalle shi cikin tsoro, tana rawar murya:
“Me kake nufi da haka, Maleekh? Me kake shiryawa?”
Ya yi wani irin dariya mai cike da ciwo, yana tafiya kusa da ita:
“Kin tuna kalmar da kike ta faɗa a baya? Tafiya ɗaya ake da yaro mai ji da kansa…”
Amal ta ɗan ja da baya.
Ya ɗan ƙarasa yana furta cikin nutsuwa:
“Broken heart shine maganinki, Amal.”
Ta ce cikin zabura:
“Me kake nufi?”
Sai ya rufe computer sa, yana murmushin mugunta:
“Hotunan ki da Zayd… duk ni na ƙirƙire su.”
Amal ta tsaya cak, idonta ya faɗa, jikinta ya yi sanyi kamar an jefa ta cikin ruwan sanyi.
Maleekh ya ɗan tafa hannayensa a hankali yana murmushin mugunta kafin ya ce,
“Duk hotunan da kika gani… waɗanda suka zubar miki da mutunci, suka karya girmanki a idon iyalai, ni ne na tsara su. Dan ma nayi miki da sauƙi da ban bayyana a duniya gaba ɗaya ba, but nasan darajar mace bazan yi haka ba..”
Amal ta kalle shi da idanu masu cike da ƙuna, kamar mai son tabbatar da abin da kunnuwanta suka ji.
Ya matsa kusa da ita, ya furta da ƙasaita,
“Ni na sa Zayd ya tura min hotonku lokacin da nayi masa bayani kan irin wulakancin da kika yi min. Lokacin da kika tarar da shi a ɗakinki, har ya kwantar da ke a gado, ni ne na shirya komai. A lokacin kuma, na shigo na tarar da ku… domin na gani da idona da abinda zuciyata ke nema.”
Numfashinsa ya ƙara nauyi, idonsa ya yi duhu kamar wanda yake daɗa jin daɗin azabtar da ita.
“Hoton da kika gani kina bacci? Ni na aika Zayd ya shiga ɗakinki ya kwanta kusa da ke. Aka ɗauka....
Sannan lokacin da kika fito da sleepy dress ɗinki, kina duba wanda ya shigo muku gida, ni na sa shi ya zagaye ki daga baya, ya rungume ki. Aka ɗauki hoto. Komai tsarona ne, Amal. Fansata ce...”
Amal ta ɗago a ruɗe, jiki na rawa. Idonta na neman fita daga socket...
Duk yana cikin ɗaukar fansa ta...
Sannan na nuna miki soyayya ne saboda ki shiga jikina har na yi broken dinki.
Na amince da aurenki sannan a ranar walimar bikin kafin washegarin aurenki dani nasa aka sace ki..."
A wannan lokacin Amal ta dago a zabure tana kallonsa a ruɗe..
Ya ce "Yess! Aikin gama ya gama tinda na gama aikin dana tsara kuma ya tafi yanda nake buƙata...
A lokacin da na sa a sace ki na kasance a wurin... kuma duk lokacin da zanje ana rufe miki fuska sannan idan zan tafi na sumbace ki yanda zan bar miki signing amma kin kasa fahimta, hakan yasa na ƙira ki yau domin na fitar ki daga duhun da kike ciki..."
Hawaye suka fara gangaro mata. Muryarta na rawa ta tambaye shi cikin rauni:
“Kenan duk soyayyar da kake nuna min… duk na ƙarya ne?…”
Ya yi murmushin gefen baki.
“Of course…”
Kalmar ta bugi kunnenta kamar wuƙa. Ta girgiza kai a hankali, hawayenta na zuba kamar ruwan sama.
“Amma ka cuce ni, Maleekh… ka cuce ni sosai.”
Ya ɗan yi shiru, sannan ya furta cikin sanyin murya kamar kankara:
“Haka nake son ji.”
Cikin zafin rai ta ɗago hannu zata mare shi, cikin sauri ya cafke hannunta da ƙarfi.
“Kin taɓa yin wannan a baya amma yanzu, hannunki ba zai ƙara taɓa fuskata ba. Idan kika yi kuskuren haka, a take zan yanke miki hannu...”
Ya tura ta baya.
Amal ta yi saurin bugan kirjinsa tana kuka, tana furta cikin ƙunci da hawaye:
“I love you, Maleekh! I love you! I love you!…”
Tana dukan kirjinsa tana kuka tare da furta "I love you , I love you, I love you.."
Kamar mahaukaciya take dukan kirjinsa da hannaye biyu, muryarta ta karye wa, zuciyarta na ƙuna.
Cikin fushi ya riƙe hannuwanta, yana kallonta cikin tsantsar tsana.
“I hate you, Amal.”
Ya hankad’a ta da ƙarfi ta faɗi ƙasa.
Shiru ya biyo baya, a lokacin kukan da ke fita daga bakinta ya koma dariya..
A hankali ta fara dariya… dariyar da ke cike da zafi da hauka.
“Hahahaha! Hahahaha!! Hahahaha!!! Hahaha!!!!”
Tana nuna shi da yatsa tana dariya, ta miƙe tare da juyawa ta fita daga office ɗin tana dariyar hauka.
Maleekh ya tsaya yana kallonta, zuciyarsa na bugawa, amma fuskarsa na nuna babu ɗan tausayin da ya rage...
Har ta sauƙa ƙasa, tana wannan dariyar, ta wuce reception. Ma’aikata suka tsaya kallonta da mamaki.
Duk da ganin yanayinta, ta wuce tana dariya..
Haka ta fita daga campany tana wannan dariyar, mutanen titin suka tsaya kallonta kowa yana nuna ta yana faɗin,
“Wayyo Allah, me ya samu Amal?…”
Haka ta riƙa tafiya tana dariya cikin hawaye, kamar mace da ta rasa komai a duniya.
Amal tana tafiya a titi tana dariya kamar wacce ta tsinci kanta a tsakanin dariya da kuka. Tayi tafiya mai nisa daga campanyn, kafafunta sun gaji, sun rasa inda zasu nufa.
Haka take tafiya tana ta dariya, tana ta waige-waige cikin duhun rana.
Cikin gari ta hangi wani ƙaramin restaurant a gefen titi, tsohon wurin cin abinci ne, cike da wasu samari masu shaye-shaye, wasu suna dariya, wasu suna ta tafka magana da ba kowa ke fahimta ba.
A hankali ta ƙarasa wurin, ta zauna a kan wani kujerar roba mai datti, ta kifa kanta a kan table.
Dariya ta tsaya ta koma kuka.
Kuka take sosai, da ƙarfi, kamar ranta zai fita...
Wani daga cikin masu shaye-shaye, wanda idonsa ya cika da ja saboda maye, ya matsa kusa da ita yana buga bayanta a hankali.
“Yar uwa, ya kika tsinci kanki a cikin damuwa haka? Ki sha wannan kwayar, duk damuwarki zata tafi,”
ya furta yana mika mata wasu ƙwayoyi guda uku da ruwa a kwalba.
Amal ta ɗago kai, tana kallonsa da idanu marasa hangen komai.
Bata yi tunani ba ta karɓi ƙwayoyin, ta zuba su gaba ɗaya a baki, ta kora su da ruwa.
Sai ta ja numfashi, ta jingina, idanunta suka fara lumshewa a hankali.
Wanda ya bata ƙwayar ya tafi yana dariyar maye, yana surutan da babu wanda ke fahimta.
Can bayan ƴan mintuna, Amal ta tashi da ƙyar.
Ta fara tafiya a hankali, tana rikicewa, tana tangal-tangal.
A lokacin maganin ya fara aiki. Jikinta ya fara rawa, idanunta suka ɗauki duhu, zuciyarta tana bugu da gudu kamar ana rera mata waƙa a ciki.
Ta shiga tsakiyar titi tana tafiya ba tare da sani ba. Motoci suna yin horn ɗin tsoro, napep suna tsayawa cikin firgici.
Ta fara bugu da jikin mota, wani lokaci ta ƙetare titi, wani lokaci ta dawowa da baya...
Wurin ya zama hayaniya, kowa na kallonta, wasu suna maganar cewa "yaushe ta fara shaye-shaye kuma?..", wasu na cewa,
“Wayyo Allah, mace ce fa! Ku taimaka mata mana!”
A dai-dai lokacin motar Maleekh ta iso daga nesa.
Shi kansa sai da ya taka burki da sauri saboda tana gab da shiga gaban motarsa.
Ya hango ta da kyau, amma zuciyarsa ta ƙi yarda ya taimake ta...
A hankali ya furta
“Ba zan iya kasancewa da ita ba…”
Sannan ya ja motarsa ya wuce cikin sauri, bai tsaya ba..
Amal kuwa ta ci gaba da tafiya a tsakiyar kwalta, tana murmushi tana faɗin,
“I love you, Maleekh… I love you…”
idanunta na cike da hawayen maye da ciwon rai.
A wannan lokacin ne wata mota ta tsaya a gefe.
Farha, wacce ta fito daga supermarket tana ɗauke da leda, ta tsaya cak da ganin Amal.
Da gudu ta ƙarasa, tana ɗaga hannu tana tsayar da motocin da ke kusa da Amal.
“Please! Please ku tsaya! Ku tsaya mana!!”
tana magana cikin tsoro.
Ta shiga tsakiyar titi da gudu, ta kama Amal tare da jan yo ta gefe da ƙarfi.
Ta rungume ta tana faɗin,
“Subhanallah! Amal! Me ya same ki haka? Subhanallah! Ki dubeki mana! Me kike yi a tsakiyar titi haka?!”
Amal ta ɗago kai a hankali, idanunta a rufe, numfashinta ya rikice.
“I love you Maleekh … yana sona… yana ƙi na…”
Ta furta cikin rikicewa kafin jikinta ya sake a hannun Farha...
Farha ta girgiza kai cikin tashin hankali.
Ta riƙe Amal sosai sannan ta buɗe murfin motarta, ta saka Amal a ciki.
Ta zagaya cikin hanzari ta shiga, ta tada motar.
Kai tsaye gidansu Amal ta nufa, zuciyarta na bugawa, hannayenta na rawa a kan sitiyari.
“Allah ka kiyaye… Amal, ki buɗe idonki dan Allah… ban ga dalilin da zai sa ki fara shaye-shaye ba, muma da muke sha addu’a nake Allah ya yaye mun…”
Ta faɗi cikin murya mai rauni, tana hawaye har zuwa ƙofar gidan Amal...
A ƙofar gidan suka tarar da Abbah ya fito zai shiga motarsa, tare da Inna da wani mutumi, Mutumin ya kawo musu gulmar cewa 'Ga can Amal tayi shaye-shaye tana ta tangad'i a tsakiyar titi...
Motar Farha ta parker. Ta fito da sauri sannan ta buɗe back seat ta ciro Amal da har yanzu tana ta surutai..
Abbah da Inna ganin an fito da Amal ne yasa suka nufi wurin da sauri.
Abbah ya riƙe ta yana faɗin
"Me ya faru da ita haka?.."
Farha ta ce, "Wallahi Abbah nima na fito a supermarket na zanyi gida na hango ta a tsakiyar titi tana maye..."
Amal kuwa ba abin da take faɗi sai "I love u Maleekh. I love u Maleekh..."
Inna ta ce, "Yanzu wancan mutumin yazo yana sanar mana.."
Abbah ya ɗaga ta suka shige gida.
Kafin Farha ta shiga sai da ta tsaya yiwa mutumin da ya zo magana.
"Ka iya kawo tsegumi amma baka iya taimaka mata ba a lokacin, na naushe ka munafiki..."
Mutumin ya wuce yana faɗin.
"Na fi ki dabanci alkur'an.."
Ya kama hanya ya tafi, itama ta shige tana zaginsa. Ga security a tsaye wanda Abbah ya ajiye su domin tsare gidan, duk suna riƙe da bindigu da bakaken suit...
*NEXT NEXT NEXT*
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 77 to 78
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Abbah ne ya shigo ɗakin Amal ya kwantar da ita, sai ga Inna da Farha sun biyo bayansa, hankalin kowa yana kan Amal wacce take ta sambatu...
Kallon Amal kawai yake, yana jin kalmar “Maleekh” na fitowa daga bakinta...
Bacci ne ya ɗauke ta na ɗan mintuna daga bisani cikin bacci, ta fara faɗin
“Maleekh… meyasa ka min haka?... ka sani ina sonka... dan Allah ka janye fansar nan… muyi aure, muyi zaman lafiya…”
Tayi shiru na ɗan lokaci, sai kuma ta ja numfashi da ƙarfi tana ci gaba da sambatu.
“Maleekh ya ɗauki fansar abubuwan da na masa a Kaduna… ya sa Zayd ya yi hoto dani ta hanyar da bata dace ba… shine yasa aka sace ni… ya rushe aurenmu… rayuwata bata da amfani, kuma ina son sa fa…”
Ta juya gefe, ta ɗaura hannunta a kan ƙirji kamar mai jin ciwon da ya daɗe yana taruwa a zuciya.
Abbah ya tsaya cak, idonsa na kan Amal, zuciyarsa na bugawa da karfi kamar ana danna ganguna.
Ya ja numfashi mai nauyi, ya furta da kyar:
“Fansa kuma?... Wannan yaron ya haukace ne?...”
Inna ta share hawayenta, Farha kuwa ta zame gefe tana jin tsoron abin da zai biyo baya.
Amal ta lumshe idanu ta yi shiru, bacci ya lullube ta gaba ɗaya.
Abbah ya jinjina kai, ya furta cikin takaici:
“Dole Maleekh ya mata wani abu… amma me ya mata?... Wani irin fansa zai ɗauka akan macen da ta baka ƙauna?”
Ya miƙe tsaye da hanzari, ya fita ba tare da ya kalli kowa ba...
Kai tsaye Abbah gida ya nufa..
A lokacin da Abbah ya shiga falonsa, ya tarar da Islam, "Ke je ki ƙira mun Maleekh. .."
Islam ta ga yanayinsa gaba ɗaya ya sanja, ta zaro ido.
Ba tare da wata tambaya ba, ta hau sama domin ƙiransa..
Knocking ɗaya biyu ya buɗe...
“Yaya Maleekh… Abbah yana ƙiran ka, amma… da fushi!”
Maleekh wanda yake tsaye a bakin ƙofa yana zukar shisha, ya yi murmushin rainin hankali.
“Abbah da fushi? To wannan ai ba sabon abu bane.”
Ba tare da ya koma ciki ba, ya sauƙo sanye da gajeren wando da singlet, yana ɗauke da shisha a hannu.
Yana shiga falon, ya zauna kan kujera yana shan shishar sa cikin nutsuwa.
Abbah na zaune a gefe yana kallonsa da wani irin yanayi mai nauyi.
Cikin tsawa ya ce:
“Zaka ajiye wannan banzar abin ko sai na ci maka mutunci yanzu?! Shashashan yaro marar tunani!”
Maleekh ya tsaya, yana kallon gefe, shishar na fitar da ƙamshi mai daɗi...Ya ajiye a gefen ƙaramin table.
Ammy ta fito da gaggawa tana tambayar,
“Subhanallah! Me ke faruwa haka?!”
Abbah ya miƙe tsaye da hanzari, yana nuna Maleekh da yatsa:
“Me ka aikata wa Amal? Me ka mata? Ka bani amsa kafin na ɗauki mataki!”
Maleekh ya ɗan yi shiru, yana mai duba gefe kamar wanda ya gama komai a zuciya.
Sai ya ce da murya ƙasa-ƙasa
“Na gaya mata gaskiya ne.”
Abbah cikin fushi ya ce,
“Gaskiyar me, Maleekh?!”
Maleekh yana kallonsa kai tsaye: “Gaskiyar ɗaukan fansa da nayi akanta.”
Da sauri Abbah ya miƙe ya zo yanda yake zaune yasa hannu ya ɗauki sumar kansa da ƙarfi, yana ɗaga murya cikin fushi kamar zai fashe.
“Fansa! Fansa! Fansa!! Wani irin fansa ne haka, kai wani irin mutum ne? Marar mutunci kawai! Da kanka kake lalata rayuwar macen da kace kana so? Kuma marainiyar Allah? Ka sani sai Allah ya saka mata..”
Ya ƙare maganar tare da fincikar gashin kansa da ƙarfi, Maleekh ya ɗan yi ƙara yana riƙe da kansa.
Ammy ta ruga ta riƙe Abbah, tana faɗin:
“Don Allah ka sassauta murya! Me yasa zaka ɗauki irin wannan zafi akan soyayyar su?!”
Abbah ya nuna su da yatsa, idonsa na cike da hawayen takaici:
“Idan wani abu ya faru da yarinyar nan, wallahi tallahi, saina saka a ɗaure ka! Kayi shekaru a prison kafin ka sake ganin rana!”
Ya juyo ya ficewa daga falon, ƙafafunsa na dukan tiles cikin ƙarfi.
Ammy ta zauna kusa da Maleekh tana rarrashinsa, tana share hawayen da suka zubo masa...
Ba komai ne ya sa shi yin hawaye ba sai don Amal tasa mahaifinsa yana ɗaga masa murya kuma har da hawaye, ya rasa meyasa haka..
Ammy ta ce,
“Kai ne ka jawo wannan, Maleekh … kasan sun riga da sun asirce mahaifinka. Bazai taɓa ganin laifin Amal ba. Kuma me ka mata ne?..”
Maleekh ya dauƙi shishar a gefe, idonsa ya cika da hawaye, amma bakin ya ƙi furta komai.
Sai kawai ya ce cikin sanyi:
“Ba zaku taɓa gane menene fansa ba… sai na gama...”
Shima ya miƙe ya bar falon, kai tsaye part ɗinsa ya nufa..
🌹🌹🌹🌹
Kwana biyu kenan da dawowar Amal cikin hayyacinta, amma dai ta kasa furta komai tinda ta farka, kamar wacce tayi mutuwar zaune...
Idonta kawai ke buɗewa, amma kalmarta ta ɓace tamkar zuciyarta.
Inna ta zauna a gefenta tana magana, tana kuka, tana dariya don ta motsa ta amma Amal kamar mutum-mutumi.
Inna tana hawaye ta ce:
“Amatu, ki ce kalma ɗaya kawai… ki ce ‘Inna’, ko ‘ruwa’ ma! Me yasa haka! Me yasa kike yi min haka, Amatu?”
Shiru.
Hawaye kawai ke sauƙa daga gefen idon Amal, amma baki ko motsawa bai yi.
Abbah ma ya zo ya zauna gefenta, ya yi mata maganar duniya, amma bata ko ɗago kanta ba.
Har sai da ya lumshe ido, ya ce cikin tausayawa:
“Duk irin laifin da kika aikata, ki yafe wa kanki. Rayuwa ba haka take ƙarewa ba, daughter…”
Shiru.
Kamar da gwinki ake magana...
Farha ta zo ta zauna, ta riƙe hannunta tana mata magana amma Amal bata ma kallonta ba.
🕯️ Sati Guda tana cikin Shiru, ko sau ɗaya Amal ta kasa furta kalma ɗaya..
Kowa yana cikin tsoro da fargana har sati guda.
Amal bata yi magana ba, bata cin abinci, bata shan ruwa.
Kowa cikin gidan hankalinsa ya tashi.
Likita ya zo, ya duba ta sannan ya ce:
“Babu wata matsalar jiki. Amma zuciyarta ta ƙone. Wannan shiru ba rashin lafiya bane, kin magana ne saboda raunin zuciya. Idan har ba a samu wanda take ji ya motsa ta ba… zata iya faɗa cikin haɗari.”
Wannan maganar ya bugi zuciyar Abbah sosai.
Da hanzari ya miƙe daga kujerar, yana faɗin cikin tsawa:
“To tunda kai likita baka da mafita, ni zan nema da kaina! Wanda ya jefa ta cikin wannan halin, shi zai fito ya gyara!”
A wannan ranar Abbah ya ƙira Maleekh akan yazo cikin ƴan mintuna...
Maleekh kwata-kwata baya ƙaunar zuwa gidansu Amal amma ba yanda ya iya..
Da daren, gidan yayi shiru.
Sai hayaniyar zuciyar kowa ke yawo.
Sai ga Maleekh ya shigo cikin gidan yana shan shishar sa kamar ba komai ya faru ba.
Kallon raini da ɗan murmushin mugunta na yawo a fuskarsa.
Abbah da Inna suna zaune a falo, Abbah ya nuna masa hanya da murya mai nauyi:
“Je ka shiga ɗakin Amal. Sai ta yi magana yau. Tunda kai ka jefa ta cikin wannan mummunan halin, sai ka fitar da ita!”
Maleekh ya ɗan kalli gefe, yana yatsina fuska cikin ƙasƙantacciyar murya ya ce:
“To ni meye haɗina da rashin maganarta? In ta ga dama kar tayi mana, ban ce ta yi ba har duniya ta nad'e.”
Abbah ya tashi da sauri, cikin fusata ya ce.
“Kar ka raina min hankali, Maleekh! Idan baka shiga ka yi abin kirki ba, wallahi saina rufe ka da duka!”
Maleekh ya ɗan ja hayaƙi daga shisha yana murmushi cikin nutsuwa, sannan ya haura sama.
💔
Ya tura ƙofar ɗakin a hankali.
Ƙamshin turaren lavender ya cika ɗakin domin koda yaushe ɗakin a cikin ƙamshi yake, dake akwai masu gyaran gidan...
Amal tana zaune a tsakiyar gado, kai a jingine da bango, idonta jawur, hawaye na sauƙa a hankali.
Bata ko motsa ba lokacin da ƙofar ta buɗe.
Maleekh ya shigo a hankali, ya zauna a bakin gado kusa da ita.
Ya zu'ko hayaƙin shisha ya busa akan fuskarta kamar yana gwada ta da gangan.
Amal ko motsi babu.
“Oh, a wancan lokacin ke baki ga abinda kika min ba? Kin tuna ranar da kika mare ni a bainar jama’a a Kaduna?... Hm, da nine a matsayinki na mace marar juriya da nima haka zan shiga halin da yafi wanda kike ciki yanzu, da yau ni ne a halin da kike yanzu…Amal voice...”
Ya ɗan matsa kusa, ya kalli idonta kai tsaye, amma bata ko lumshe ido ba.
Sai kawai ya ƙara da murya mai kaifi:
“Ki sani, fansa ta a gareki itace maslaha.
Da kin san ciwon raini kamar yadda na sani, da kin san dalilin da yasa na shiga soyayya dake. Da ba'a zo wannan ga6ar ba..... Amal yanzu da kika zauna haka shiru, kin fi kyau fiye da lokacin da kike ta ihu da surutan banzaa...”
Ya saki ƙaramar dariya mai cike da ɗacin zuciya.
“Kin san me Amal? Fansa tana da daɗi. Amma a lokacin da na ɗanɗana naki... sai na gane ba farin ciki bane, azaba ce mai baƙar wuya...”
Ya ɗan ja numfashi, ya ɗaga kansa sama yana kallon fan da take juyawa, sannan ya ce a hankali:
“Ina son ganin yadda zaki sake tashi daga wannan karyewar, saboda sai kin sake ɗanɗanar fansa ta mai sanya maye a titi....”
Ya miƙe, ya juya yana shirin tafiya, amma kafin ya kai ƙofa, Amal ta motsa hannu ɗaya ba tare da ta furta komai ba..
Maleekh ya tsaya a bakin ƙofa, ya juyo kaɗan, yana kallon ta.
Idonsa ya ɗan sauya launi,
Ya juyawa zai fita daga ɗakin sai kawai wata ƙaramar murya, mai rauni mai cike da iko ta fito daga bayan sa:
“Dakata…”
Kamar iska ta tsaya a cikin ɗakin.
Murya ce mai sanyi amma mai tsinke zuciya.
Maleekh ya tsaya cak, ya juyo a hankali, yana kallonta da mamaki.
Idonsa ya faɗa cikin nata, wanda ke cike da hawaye amma kuma akwai wani sabon haske a ciki kamar wacce ta dawo daga duhu..
Murmushi yayi sannan ya ce,
“Oh, ashe ba haukacewa kika yi ba? Iskanci ne kawai...?”
Amal bata amsa ba.
Kawai ta tashi a hankali daga kan gadon, ƙafafunta suna danna ƙasan tiles a hankali, tana takowa gare shi kamar mai zuwa wajen ƙaddara.
Hawaye na bin kuncinta,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 50 Chapter of 62