da dafe ƙirjinta.
Duk mutanen wurin ne suka mimmike suna zaro ido a rikice.
Maleekh yayi saurin cire glass yana kallon Amal wacce take a tsorace tana kallonsa. A tunaninsa ya tsiratar da ita da harsashi.
Jin an ambaci "Farhaaaaa…" Daga wajen jama'a
Nan ya juya baya ya ganta a zube a ƙasa. A ruɗe yayi kanta da gudu ya durkusa tare da ɗagota ya ɗora ta akan cinyarsa.
Amal itama zaro ido tayi ta toshe bakinta cikin ruɗani..
Zayd a hargitse yayo kan Kanwarsa yana furta sunanta.
Aure ya koma tashin hankali! Maleekh ya ceci Amal, amma ya rasa Farha..
Maleekh yana riƙe da Farha a kan cinyarsa, jinin Farha na zubowa a jikinsa. Ya kasa yarda da abin da ya gani. Aiki ya kasance kan Amal, amma Farha ce ta biya sadaukarwa.
Zayd ya durƙusa gefensa cikin ruɗani, amma Maleekh ya riga ya shiga cikin yanayin aiki na gaggawa (professional mode).
Maleekh ya ɗago Farha da gaggawar gaske a hannayensa.
Da ƙarfi yake faɗin
“Maza ku kira motar asibiti! Kuma ku kulle hall ɗin nan! Kada wanda ya fita!!”
Ammy da Inna suka yi tsalle cikin firgici..
Amal tana tsaye, jikin ta na rawa tana kallon Maleekh yana tafiya da Farha wacce yanzu ta zama jini gaba ɗaya.
Cikin kuka mai zafi take faɗin "Maleekh! Maleekh!..."
Amma Maleekh bai ko juyo ba. Ya fara gudu da ita daga saman hall zuwa ƙasa.
Duk mutanen da ke hall ɗin sun fara ihu da gudu don tsira.
Ammy ta rungume Amal don kwantar mata da hankali, yayin da kuma Inna ta fara addu’o’i da furuci na al’ajabi game da muguntar mutane.
Maleekh ya fita da Farha daga hall ɗin. A halin da ake ciki, motocin Maleekh na alfarma suna nan a waje. Ya sanya Farha a cikin motar sa kai tsaye, sannan ya shiga gefen direba ya fara tuki da gudun gaske zuwa Asibiti mai zaman kansa wanda ya sani.
Zayd da Islam da kuma wasu ƴan sanda na sirri waɗanda ke tsaron Maleekh sun bi bayansu nan take.
Suna isa Asibiti, an kai Farha ɗakin tiyata (Emergency Surgery) nan take.
Maleekh ya tsaya a wajen ɗakin tiyata yana duban jinin Farha da ke jikinsa, yana kallon hannunsa wanda har yanzu yana riƙe da tabon jinin Farha. Ya dafe kai cikin damuwa da haushi kan makircin da aka tsara...
Ya san cewa harbin ba don a kashe Farha bane..
A zuciyarsa ya fara furta.
"Alhaji Wadata! Ka nuna min cewa ba kawai kai ɗan siyasa bane, kai ne kasurgumin mai kisa... Yanzu zan nuna maka cewa ka yi kuskure!"..
Bayan da aka harbi Farha, Alhaji Wadata ya fita daga Hall ɗin cikin ɓacin rai, yana fafatawa da mutanen da ke gudu don tsira. Ya yi hasashe cewa Amal za a harba, ba Farha ba.
Yana isa wajen Parking Lot, ya kira mai aikin sa wanda ya harba.
Cikin tsawa da murya mai rawa ya ke cewa
“Waye ya gaya maka ka harbi ƴata? Waye?!”
Mai Harbin ya ce,
“Muna neman gafara ranka ya daɗe! Mun saita bindigar ne a kan Amal, amma Maleekh ya ɗauke ta da gaggawa… Bullet ɗin ya wuce ya kama matar da ke bayanta…”
Wadata ya katse wayar ya jefar da ita a ƙasa. Ya shiga motarsa cikin tsananin takaici da haushin gazawa.
Ya nufi Asibitin da aka kai Farha.
Wadata ya isa Asibitin cikin shiga ta tashin hankali. Ya tarar da Maleekh a wajen ɗakin tiyata, har yanzu yana cikin kayan ango amma da jinin ƴarsa a jikinsa.
Wadata ya nufo Maleekh da gaggawar gaske, ya ɗaga hannu zai mare shi.
Maleekh ya riƙe hannun Wadata a sama da ƙarfi. Ya kalli Wadata da idanun da suka yi ja saboda haushi.
Alhaji Wadata ya ce,
“Maleekh! Ka kashe min ƴata! Ka taɓa furta cewa 'za mu yi amfani da auren don cin nasara' Sannan ka nuna rashin adalci a shagalin, yanzu kai ka jagoranci kisan kai! Me kake son aiwatar wa da Farha?”
Maleekh ya furta "kai ne wanda zai kashe ƴarsa domin kawai ya ga Maleekh ya mutu!”
Zayd ya fito da sauri daga wani gefe, ya tsaya a tsakanin su, yana hana su rigima..
“Daddy! Don Allah a kwantar da hankali! Yanzu ba lokacin wannan bane! Mu yi wa Farha addu'a! Maleekh, don Allah a kwantar da hankali!”
Maleekh ya saki hannun Wadata ya ja baya.
Alhaji Wadata Yana huci da fushi ya ce,
“Maleekh! Nayi nadamar baka auren ƴata! Zan tsige ka daga dukiyarka! Zan nuna maka ainihin ni! Ba za ka yi amfani da Farha don girmama karuwar da kake aure ba!”..
Maleekh ya kalli Zayd, sannan ya kalli Wadata da murmushi mai zafi.
“A yanzu Farha matata ce! Kuma zan kasance mijinta har sai ta warke! Amma zan gano wanda ya yi wannan harbin! Kuma zan nuna maka ba kai bane ka kawo ni duniya ba, kuma ba kai bane zaka fitar da ni! ”..
🪸🪸🪸
A wurin Hall, sumar Hajiya Sa’adatu biyar ana farfaɗo da ita ganin Ƴar ta aka harba. Da ƙyar ta yunkuro. Gaba ɗaya iyalai suka nufi Hospital.
A wannan ranar a Asibiti suka kwana har da Amal. Kowa hankalinsa a tashe. Amal ma ta shiga tashin hankali sosai ganin halin da Farha take ciki, duk da har yanzu ba a basu damar ganinta ba.
Har aka wayi gari, aka sake wuni. Sauran duk sun koma gida banda Maleekh, Zayd, Amal, da mahaifiyar Farha (Hajiya Sa’adatu). Alhaji Wadata bai zo asibitin ba domin ya shiga tashin hankali sosai kuma ta silar sa hakan ya faru.
An tsawaita bincike sosai akan wanda ya kawo farmaki domin ba a tantance waye ba, amma Zayd ya san shirin mahaifinsa ne amma ya kasa faɗi sai kuka.
Maleekh ya tambaye shi akan ya sanar masa waye, domin ai shi ya kira ya sanar cewa akwai ƴan ƙunar baƙin wake. Amma Zayd ya kasa faɗi...
Maleekh ya dafa kafaɗarsa yana faɗin
“Zayd! Ka daina ɓoye min! Ka kira ni a waya! Waye ya aikata wannan? Muryarka ce na ji! Don Allah ka gaya min kafin na ɗauki mataki marar kyau!”..
Zayd yana jujjuyawa cikin kuka, yana ta ƙoƙarin magana amma bakinsa ya ƙi buɗewa,
“Ni-ni… wallahi ni… ban sani ba… ba zan iya…” Ya kama kansa cikin zafi...Yana jijjigawa.
Maleekh ya furta yana kallonsa.
“Ka tuna! Na san layar rufe baki ne a kan ka! Ka yi ƙoƙari ka kashe shi! Waye ya harbi Farha?!”
Zayd Ya dafe kirjinsa, idanunsa na nuna tsananin zafi na rashin iya magana.
“Aure… Aure ya ci nasara… Farha… ita ta sani… ” Ya faɗi ƙasi yana tari...
Maleekh ya haƙura da tambayarsa duk da yana zargin mahaifinsu ne ɗari bisa ɗari. Maleekh ya kudirta cewa: “Koma waye asirinsa zai tonu…”
A daren yau an bada izinin ganin Farha, an fito da ita daga ɗakin tiyata. An kaita wani ɗaki na musamman.
Bayan sun shiga: Maleekh, Zayd, Amal, Hajiya Sa’adatu, da Alhaji Wadata da Alhaji Gusau sun zo a wannan lokacin. Ammy da Inna dasu Islam da sauran ƴan uwa da suka zo biki duk an hallara a ɗakin Farha.
Farha ta farfaɗo ba abunda take sai kuka. Ta kasa yin magana da kowa.
Mahaifiyarta (Hajiya Sa’adatu) ce ta zauna a bakin gadon tana rarrashinta, amma Farha sai ta fizge hannunta daga na uwar.
Cikin sanyin murya take faɗin
“Ku tafi! Bana buƙatar kowa, ku tafi!”
Hajiya Sa’adatu ta ce,
“Farha kinga…”
Farha ta katse ta da cewa,
“Bana son ganinki! Ki fita!”
Ba yanda ta iya haka ta fita. Alhaji Wadata yazo zaiyi mata magana, ta ce:
“Kar ka mun magana! Bana son jin muryarka! Daga yanzu har zuwa ƙarshen numfashina bana buƙatar ka!”
Alhaji Gusau ya ja Alhaji Wadata suka fita. Haka kowa ya fita domin tana buƙatar hutawa.
A daren nan iya su uku kawai suka kasance a ɗakin Farha: Maleekh, Amal, da Zayd.
Farha ta ɗago hannu tana shirin yiwa Maleekh magana. Da sauri ya riƙe hannun yana ɗan shashshafa mata. Ta sa ɗayan hannun ta buɗe tafin hannunsa ta ajiye masa mic ɗin da ya sanya mata. Wanda ya gano sirrinsu da shi.
Maleekh ya ɗago yana kallon Zayd ya ce,
“Ga Amal ka kaita gida please, zan zauna da Farha…”
Amal ta ce cikin kuka.
“A’a ka bari zan zauna da ita, tinda mace ce duk abinda take buƙata zanyi mata…”
Maleekh ya girgiza kai ya ce:
“Ki je ki kula da yara kawai, Zayd ku tafi…”
Amal ta juya, suna shirin tafiya sai sukaji an ƙira wayar Maleekh, Ya ɗaga. Jami’ai sun sanar dashi akan cewa an kama waɗanda suka kai farmaki.
“Okay ina zuwa yanzu…” Abin da Maleekh ya furta kenam.
Ya kalli Amal ya ce: “Ki zauna da ita…” Ya ce da Zayd: “Mu tafi…” Nan suka fita..
Amal ta zauna a kujerar jikin gado ta ce,
“Sannu Farha, ya jikin nakin?…”
Farha idonta akan Amal cikin sanyayye murya ta ce:
“Amal dan Allah ki yafe ni, na miki abubuwa da dama a baya, kuma lokacin da zan tafi ya gabato, nasan bazan cigaba da rayuwa a doron duniya ba, ki yafe mun…”
Amal ta riƙe hannunta da yayi sanyi sosai tana tayata hawaye da cewa:
“Na yafe miki Farha, tun a baya na yafe miki, kuma insha Allahu zaki cigaba da rayuwa damu, kuma na fahimci cewa wannan harin ani aka kawo sai kuma ya same ki, ban so Maleekh ya janye ni ba domin da yanzu kina cikin lafiya da burin cigaba da mijinki, kiyi haƙuri…”
Farha ta ce,
“Kar ki damu, Allah daman ya rigada ya rubuta hakan, idan Allah ya kare bawansa ba wannan ya isa yayi masa komai, don haka kina daga cikin kariyar Ubangiji domin Allah ya dubi maraicinki sannan ki cigaba da kula da yaranki…”
Farha ta ja dogon numfashi ta ci gaba da faɗin
“Waɗanda suke son ɗaukan rayuwarki ba ƙananan azzalumai bane, kuma su ɗin ba wasu bane face iyayena… Suna son ganin bayanki Amal saboda su suka kashe miki iyaye…”
Amal ta ji wani abu kamar daga sama, tana kallon Farha ido cike da hawaye.
Ta cigaba da faɗin
“Nasan bazaki ji daɗi ba, to amma ya zakiyi kina tare da manyan makiyanki, wanda kike tunani ba shi bane, Abban Maleekh mutumin kirki ne, bashida hannu ko masaniya akan mutuwar iyayenki, sharri aka ɗaura masa…”
Ta ci gaba da tona asiri..
“A lokacin da za a kashe iyayenki, an tilasta wa mahaifinki akan ya sanar cewa Abban Maleekh ne ya kashe su, idan baiyi haka ba to anyi barazana da za a kashe ki da mahaifiyarki hakan yasa yayi haka… daga baya kuma suka aikawatar da kisan....
To mahaifina ne da abokinsa Alhaji Gusau sai kuma daga baya Mahaifiyata taji labari itana ta rufa musu asiri… kuma take goyon bayansu… Amal Maleekh ya gano hakan kuma akwai shirin da yake son aiwatarwa dalilin da yasa yaso aurena kenan…”
Ta bayyana dabarar Maleekh.
“Yana so ya ɗauke ni daga gaban iyayena yanda idona bazai ga abinda zai aiwatar ba, sannan yana son aure na saboda mummunan ƙudurin da iyayena suke shiryawa… Nasan zakiji kamar almara amma gaskiya nake gaya miki…”
“Maleekh yasan gaskiya ta hanyar dasa mun mic a cikin sumar gashina ba tare da na sani ba, iyayena suna yawan magana a gabanmu ni da Yaya Zayd abinda ya shafi sirrin nan saboda suna ganin sun rufe mana baki ta hanyar asiri, bazamu iya sanar da wani sirrinsu ba, ta hanyar nan Maleekh ya saurari komai ta mic da ya dasa mun…"
“Na gano haka lokacin da nake gyaran gashina, na ciro na gani kuma na tuna lokacin da ya sanya mun, a lokacin naji daɗin hakan sosai na ƙara maidawa cikin gashina, daga lokacin nake yawan zama a cikin iyayena sannan ni zanta janyo maganar da zaisa suyi ta maganganu akai suna faɗan abubuwa da yawa da ya shafi rayuwarsu da kuma ƙudirinsu sannan su suka tura a kone asibitin da Abbah yake ciki har aka ɗora miki laifin hakan…”
Daga nan Farha ta fara jan numfashi da ƙyar.
Amal ba abinda take sai kuka tana riƙe da hannun Farha.
“Jikina ya ɗau zafi da sanyi…” a cewar Farha tana numfashi sama-sama..
Amal ta tashi a zabure ta ninka mata mayafi.
Farha ta ce,
“Ƙafata ciwo suke…”
Amal ta je saitin sawayenta ta fara mata tausa a hankali tana kuka. Taji ƙafar ta ɗau sanyi sosai kamar kankara.
Amal ta daɗe tana ɗan tattausa mata Ƙafar daga bisani Farha ta ce: “Ya isa haka kizo ki huta…”
Amal ta zo ta zauna tana riƙe da hannun Farha tana mata wasa da hannu. Har dare ya tsala sosai sai da Amal ta tabbatar da Farha ta fara bacci kafin itama ta kifar da kanta a bakin gado hannunta riƙe da na Farha. Ba jumawa bacci ya ɗauke ta itama..
Asirin shekaru ashirin ya tonu! Abokan gaba sune iyayen Farha. Maleekh ya riga ya kama ƴan farmakin da suka harba Farha, kuma zai yi amfani da su don tonawa Wadata asiri..
Da misalin tsakar dare, Maleekh da Zayd suka isa Ofishin ‘Yan Sanda inda aka ajiye waɗanda suka kai farmaki (ƴan ƙunar baƙin wake). An yi wa mutanen dukan tsiya kafin Maleekh ya iso.
Maleekh ya shiga cikin ɗakin tambayoyi. Ganin waɗanda suka harbi matarsa Farha, Maleekh ya cika da fushi da damuwa game da rayuwar Farha..
Da murya mai ƙarfin tsoro da azaba ya ke faɗin
“Ku gaya mun wa ya aiko ku! Da sunan waye kuke aiki?!”
Masu laifin sun yi ƙoƙarin ɓoye sunan Wadata, amma Maleekh bai yarda ba. Ya ɗauki wani ƙaton ƙarfe, ya fara dukan su ba tare da tausayi ba...
“Ku faɗa! Ko zan tabbatar da cewa wannan dare shine na ƙarshe a rayuwarku!”
Maleekh ya ci gaba da dukansu har sai da jini ya fara tsiyaya daga jikinsu. A ƙarshe, ɗaya daga cikinsu ya faɗi gaskiya a tsorace.
“Mu na roƙonka, Ranka ya daɗe! Alhaji Wadata ne! Shi ya umarce mu! Amal ya ce mu harba, ba Farha ba!”
Maleekh ya daina dukan su, yana haki breathing heavily cikin fushi. A wannan lokacin, Zayd ya shigo ɗakin tambayoyi. Gaskiyar da Farha ta faɗa wa Amal, yanzu ta raunana layan rufe baki da ke kan Zayd da Inna..
Zayd ya kalli Maleekh da idanu cike da hawaye da kuma tuna baya..
Zayd murya cikin tsawa kamar an cire katanga a makogwaronsa.
“Ni zan faɗa maka! Daddy ne! Gaskiya ne! Shine! Shine makiyinmu duka!”
Maleekh da DPO wanda ke gefe yana sauraro sun zaro ido suna kallon Zayd cikin mamaki da firgici.
Maleekh ya ce,
“Zayd! Wane ne Daddy?.."
Nan Zayd ya gaya musu komai game da mahaifinsa da abokinsa Alhaji Gusau..
Already Maleekh ya san da hakan kawai ya nuna bai sani bane saboda a samu hujjoji..
DPO ya tsaya mutum-mutumi, yana jin gaskiyar da ta girgiza shi fiye da harbin bindiga...
DPO ya kalli Maleekh sannan ya ce,
“Malik, a kwantar da hankali! Ku rubuta duk wannan a takarda! Wannan shaida ce mai ƙarfi! Zayd, zo ka rubuta duk abin da ka sani! Yanzu za mu damƙe Alhaji Wadata da Alhaji Gusau nan take!”
Zayd ya shiga rubuta dukkanin sirrin da aka rufe a kansa na shekaru da yawa. Maleekh ya bar wa DPO waɗanda suka harba don su ci gaba da aiki, amma zuciyarsa ta riga ta koma Asibiti inda Farha ke kwance.
Maleekh da Zayd basu bar wurin jami’an ba sai dab da asuba. Suka nufi asibiti kai tsaye domin Maleekh yana fargaban kasancewar Amal a wuri ita kaɗai saboda neman rayuwarta da ake yi, kuma masu son kasheta zasu iya binta asibiti domin suga bayanta..
Haka yake ta tunani a tsorace. Basu wuce ko ina ba sai asibiti.
Da gudu Maleekh ya sauƙa a mota ya nufi cikin Hospital. Zayd a bayansa. Suna isa suka tura ƙofar suka shiga. Daidai lokacin ake ta kiraye-kirayen sallar asuba..
Ganin Amal tana kwance da kanta a kan gadon da Farha take kai, tana shan bacci.
Maleekh ne ya zauna a bakin gadon yana shafa sumar kan Amal da ke bacci. Sannan ya maida idonsa kan Farha wacce itama idonta a rufe suke. Yasa hannu yana shafa mata fuska cikin kulawa...
Zayd yana tsaye ya sau murmushi tare da faɗin
“Yanzu fa duk waɗannan zafafan matan matanka ne koh?”
Maleekh ya furta “Uhmmm!”
Zayd ya cigaba da faɗin
“Allah sarki masoyiyata da yanzu muna tare a ɗaki ɗaya…”
Maleekh ya ce,
“Yanzun ma zaka iya zuwa ka sameta ai…”
Ya ce, “A’a kamm! Shalelen ƙanwata tana cikin wannan halin ina zan samu ƙarfin zuciyar aiwatar da wani abu…”
Maleekh ya sau murmushi yana kallon Fuskar Farha.
Can sai ga Doctor ya shigo sanye da glass ɗinsa. Ya musu sallama suka gaisa.
Doctor ya sanar musu
“Yanzu na dawo daga masallaci nasan bakuyi sallah ba, ku je akwai masallacin da basu shiga sallah ba yanzu anan kusa…”
Maleekh ya furta.
“Shikenan Doctor amma ya jikin marar lafiya?…”
Doctor ya ce,
“Normal jikinta, amma bari na ƙara dubata ko akwai wani abun da za a mata…”
Doctor ya ɗora mata stethoscope (abin gwada numfashi) a saitin kirjinta.
Yana gwadawa nan Doctor ya dube su a ruɗe ganin akwai abun da ba daidai ba. Maleekh da Zayd ganin yanayin Doctor suka zuba masa ido.
Doctor ya gama gwada ta, yaji ba numfashi. Da sauri ya kalli wurin computer da yake nuna mutum yana numfashi ko ya mutu. Nan yaga ya nuna line mai tsayi (flatline).
Doctor a tsorace ya cire abun kunnen yana salati.
Zayd a tsorace ya furta.
“Lafiya Doctor?…”
Maleekh kuwa ba bakin magana ganin yanda Doctor ya zama.
A hankali Doctor ya furta:
“Allah ya yi mata rasuwa…”
Wani irin hajijiya ne ya d'ebi Maleekh sauran kaɗan ya faɗi. Kawai ya dafe jikin bango.
Zayd hannu ya ɗora a kai yana faɗin..
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…”
_NEXT NEXT NEXT_
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 99 to 100
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Maleekh yana jingine da bango, jikin sa na rawa saboda abin mamaki da raɗaɗin rasuwar Farha. Zayd kuma ya fita daga ɗakin, ya tsuguna a bakin ƙofar shiga ya kifar da kai yana kuka.
Amal tana kan bakin gado, hannunta riƙe da na Farha. A hankali ta fara motsi, tana shirin tashi daga baccin ta na gajiya.
Ta ɗan murmusa tana tunanin ko Maleekh ya dawo..
Amal ta ji sanyi a hannun da take riƙe da shi. Ta so zame hannunta don miƙewa ganin ɗan haske alamun asuba tana son yin sallah, amma hannun Farha na riƙe da hannun. Ta sake janyowa, amma Farha ta kankame hannunta da ƙarfi kamar tana riƙe da wani abu mai daraja wanda take son kare shi kafin ta tafi.
Amal ta buɗe idon ta gaba ɗaya. Ta kalli Maleekh da ke jingine da bango, da kuma Doctor da ke tsaye kusa da gadon, dukkanin su cikin yanayin tashin hankali da baƙin ciki.
Sai ta kalli fuskar Farha wacce ke da alamun nutsuwa, amma launinta ya canza zuwa fari fat. Hannun Farha kuma ya yi sanyi sosai kamar kankara.
"Ya Maleekh meke faruwa ne?.."
A hankali ya furta "ta rasu.."
A razane ta buɗe ido sosai tana kallonsa, sai dai numfashinta ya ɗan tsaya kafin ta waigo ta kalli fuskar Farha..
Hannu tasa tana ɗan bubbuganta tana ambaton sunanta "Farha! Farha!! Farha ki tashi mana nasan bacci kike yi..."
Doctor ya ce "ta riga ta rasu fa, taya zata amsa miki.."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji’un " abun da Amal ta iya furta wa kenam.
Can tana ƙoƙarin barin wurin tana kuka sai kuma taji still hannun Farha na riƙe da hannunta..
Tana kuka tana ƙoƙarin cire hannunta sai kuma taji abu yaci tura, abu kamar wasa ya zamo firgici, Farha ta riƙe hannunta gamm ko motsi baya yi..
Ganin alamun hannun bazai sake ta ba yasa ta fara ihu tana kuka saboda firgici da tsoro na sanin gaskiyar cewa Farha ta rasu amma kuma hannunta yaƙi rabewa da nata..
Wani irin Ihu mai tsananin tsoro ta sake.. “Ahhhhhh! Hannuna! Maleekh! Me ke faruwa? Hannunta yaƙi rabuwa! Nima mutuwa zan yi?!”
Doctor ya matso da gaggawa, yana ƙoƙarin dabararsa don raba hannun Farha daga na Amal, amma hannun yaƙi sake wa. Ko da ya danna wurin, kankamewar tana nan daram.
Maleekh ya fara gudu zuwa wurin. Ya san cewa Farha tana ƙoƙarin bayyana wani abu na ƙarshe ne.
Ya rungume Amal yana rarrashinta duk da raɗaɗin zafin mutuwar Farha da yake ji a zuciyarsa.
Muryarsa cike da baƙin ciki yake furta...
“Shhh! Kada ki tsorata! Ba zaki mutu ba! Farha ta riga mu gidan gaskiya! Ba ta so ta sake ki ne, saboda tana son ta kare ki ne har na dawo!”
Doctor ya ce, "Wannan kam sai dai a yanke hannun mai rai ɗin a bisine da gawar..."
Amal jin haka yasa ta sakin fitsari a wurin..
Fitsari cikin baho duk ta juye shi a wurin, ga yanda jikinta yake kakkarwa gaba ɗaya ta haɗa zuffa tako ina.
Idonta yayi jawur..
Maleekh dake rungume da ita yana iya jin bugun zuciyarta.
Yayi akan hannun ya rabu shima ya kasa..
A lokacin ya fara tofe hannayensu da addu’a, adduoi yake ta karantowa yana tottofe hannun, bayan can ya matsa kusa da Farha, ya shafa mata goshinta a karo na ƙarshe.
Ya raɗa mata a kunne
“Nagode Farha! Na ji abin da kika yi, kuma na fahimci sadaukarwarki! Na riga na kama su! Kin cika alƙawari! Yanzu ki saki Amal! Zan kula da ita da dukkanin gaskiya da ƙarfi!”
Bayan Maleekh ya faɗi haka, hannun Farha ya sake hannun Amal a hankali.
Amal ta ciro hannunta da tsananin tsoro.
Ta rungume Maleekh da ƙarfi tana kuka mara sauti.
Zayd ya shigo ɗakin, jikin a sanyaye. Ya durƙusa a gaban gadon, ya ɗauki hannun Farha ya sumbace shi cikin girmamawa da baƙin ciki.
Amal ta durƙusa sai kuka take domin ta ji mutuwar sosai. Haka take ta kuka ba kakkautawa. Da ƙyar Maleekh ya samu ƙarfin zuciyar ɗago ta ya rungumeta.
Bayan nan aka sa Farha a Ambulance domin kaita gida, ba tare da an sanar wa kowa ba don hana rikici kafin a binne ta. Maleekh da Zayd da Amal sai wasu likitoci masu rakiya. Kai tsaye gidansu Maleekh suka nufa.
A falo tuni labari ya tarwatsu. Ammy da Mahaifiyar Farha (Hajiya Sa’adatu), wacce tayi danasanin goyawa mijinta bayan aiwatar da laifi, sai Inna wacce ta gama sanar dasu gaskiyar labarin kashe iyayen Amal da akayi.
Ammy ta girgiza sosai domin bata taɓa tsammanin Alhaji Wadata zai aiwatar da haka ba. Sai kuka take tayi. Hajiya Sa’adatu ta sanar cewa Amal akaje kashewa ba Farha ba.
Inna tana kuka ta ce, “Yanzu rashin imanin har ya kai a kashe iyayenta sannan itama a kashe ta?!”
Hajiya Sa’adatu tana kuka itama tana neman yafiyar Inna da kuma Allah.
Suna cikin wannan sai suka ji ƙarar jiniya na Ambulance. A zabure suka miƙe domin sun san ba lafiya ba. Suna falo sun kasa motsawa.
Can sai ga Maleekh ya shigo da Zayd suna ɗauke da Farha a nannade da mayafi. A kan kujera suka kwantar da ita.
Ammy cikin kuka ta furta “Meye wannan Maleekh?…”
Maleekh kai a sunkuye ya ce,
“Ku ƙira wacce zata mata wanka a suturtata, Allah yayi mata rasuwa…”
Ammy da Inna lokaci guda suka furta “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Baki a haɗe.
Hajiya Sa’adatu kam dafe kirji tayi daga nan ta faɗi sumammiya.
Cikin awanni an sanar da rasuwar Farha a ko’ina.
Alhaji Wadata da ke gida yana zaune yana shan tea. Aka ƙira shi a waya aka sanar dashi mutuwar ƴarsa. A lokacin kofin tea ya faɗi daga hannunsa. Ya miƙe a zabure tare da furta: “Whatttt…”
Bayan an katsar da ƙiran a ruɗe ya ɗauki key ɗin mota kai tsaye gidansu Maleekh ya nufa domin an sanar masa tana gidan.
Yana isa ya samu har an suturtata an fito da ita za a yi mata jana’iza. Mutane an taru sosai. Ta ko ina zuwa suke. Ta samu mutane sosai domin har daga wasu garuruwa an zo.
Ran Alhaji Wadata ya ɓaci sosai ganin ba a sanar masa a lokacin da ta rasu ba, sai da har daga wasu garuruwa sun zo.
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 60 Chapter of 62