Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
suka kaɗa suka cika da bacin rai. Sai dai ya danne komai cikin sirri, ya juya kamar ba komai, ya wuce da ƙarfin hali zuwa ofis ɗinsa. Amal ta gane a lokacin yanzu fa Maleekh zai iya yin komai saboda wannan Zayd ɗin. Amal a ranta ta furta: “Ya Allah… wannan ba kyauta bane kawai, wannan zai tayar da bala’i.” Zayd ya ɗago kai yana kallon ta da murmushi: “Na gaya miki pretty, Zayd baya yin nasara a rabin hanya. Look at you, you’re shining like queen of gold!” Amal ta yi murmushi na ɗan lokaci, amma cikin zuciyarta tana jin tsoro da damuwa. Ta san Maleekh ya ga komai kuma yanzu yana cikin zafin kishinsa ... Amal tana zaune a office ɗinta, ta ji ƙira daga intercom. “Miss Amal, CEO is calling you to his office… now.” Muryar secretary ɗin na rawa, alamar ta gane akwai wani abu a ɓoye. Amal ta ɗan gyara, ta fesa turare, ta nufi office ɗin Maleekh. A ƙofar, zuciyarta na ta bugu kamar ana buga ganga. Bayan ta tura ƙofar ta shiga, ta ganshi a tsaye fuskar sa ba annuri, idonsa sun kaɗa, hannunsa yana kan desk yana girgiza yatsunsa kamar mai tsare abun hari.. Maleekh a hankali cikin murya mai zafi ya ce: “So... wannan shine aikin da kike yi a company? Kinyi kyau sosai… da sabon takalmin da masoyinki ya sa miki a gaban mutane.” Amal ta tsare shi da ido sannan ta ce: “You have no right, Sir. Ba kai ne mahaifina ba, ba mijina ba. Sannan kai kace mun rabu — to let me live my life!” Maleekh ya ɗaga murya cikin fushi ya ce: “Your life? A company ɗina? A gaban idona? Kin bari wani yaro ya durƙusa gaban ki, ya sa miki takalmi kamar... kamar me?!” Amal ta daga murya itama ta ce: “Eh! Saboda kai baka ganin darajata ba! Yana gani na kamar Sarauniya, kai kuma kullum faɗa da tsawa! Ka ce ka rabu da ni amma ka kasa barin zuciyarka ta sake!” Idon Maleekh ya ƙanƙance, numfashinsa ya yi nauyi. A hankali ya matso kusa da ita. “Ki faɗa min gaskiya... kina sonsa?” Amal ta kalle shi da hawaye sannan ta ce: “Idan na ce eh fa? Me zaka yi?” Kafin ta gama maganar, Maleekh ya zabga mata mari mai ƙarfi! 😢 A cikin ɗan lokaci ta firgita, ta faɗi jikin kujerar executive tana riƙe da kuncinta, numfashinta na rawa, hawaye na bin fuskarta.. Maleekh ya tsaya yana kallonta da ido masu zafi, yana girgiza kai. Cikin murya mai raɗaɗi ya ce: “I warned you... ki guji wannan abin. Amma kin ɗauki maganata wasa.” Ya juya da sauri, ya fice daga office ɗinsa, yana tafiya cikin takaici. Amal ta miƙe a ruɗe, tana ƙiran sunansa cikin kuka: Amma bai tsaya ba ya nufi office ɗinta kai tsaye. Ya shiga ya buɗe drawer ɗinta, ya ɗauko takalmin gold ɗin da Zayd ya bata, yana kallonsa kamar abu mai ban tsoro. Sai ya ɗauki takalman biyu, ya fice daga building ɗin cikin fushi kamar hadari. Amal da gudu ta biyo bayansa tana ƙwala masa kira: “Maleekh! Don Allah ka tsaya! Ka faɗa min me kake yi haka?!” Ya fita zuwa bayan company, hasken rana na haskawa kan fushinsa, ya tsaya a fili ya zaro ashana (lighter) daga aljihunsa. Ya ajiye takalman a ƙasa, ya zuba petur ya kunna wuta… Amal ta karaso tana kuka tana ƙiran sunansa cikin firgici. “Maleekh! Stop it please! Ka tsaya! Maleekh! Don Allah ka daina! Wannan kyauta ce, ka bar shi!” Maleekh cikin fushi ya ce: “Kyauta ce daga wanda kike so ko? To ku biyu ku huta, bana so ina ganin komai daga gare shi!” Ya sa wuta kan takalman. Suna ƙonewa suna sheƙin zinare.. Amal ta durƙusa a ƙasa tana kuka, tana kallon wutar tana magana cikin murya mai rawa: “Ka yi hakan ne saboda kishi... ko saboda ƙiyayya, Maleekh?” Shi kuwa ya tsaya yana kallonta, idanunsa suka cika da hawaye amma bai nuna ba. Ya juya kawai, ya bar wajen cikin shiru.. Motarsa ya shiga ya bar campany... Ita kuwa Amal tayi saurin tarar ruwan fanfo dake gefe da ita, ta kashe wutar amma sai dai takalman sun fita hayyacinsu.. Tana kuka ta bar wurin itama.. Washegari da safe... Tunda ta fito daga gida har ta shiga mota, idonta kumbure saboda kuka. Tun daga bakin gate ta lura ma’aikata suna ta magana a hankali, suna nuna hannayensu zuwa bayan company. “An samu wuta fa jiya… takalmi masu tsada sun ƙone!” “An ce gift ɗin CEO Assistant ne…” Amal ta tsaya cak, numfashinta ya tsaya. Zuciyarta ta fara dokawa kamar ana danna gangar yaƙi. Ta san ana magana ne akan ƙonewar takalman, amma ba wanda yasan wa ya aikata hakan.. Ta yi shiru kawai, ta shiga ciki tana ɗauke da wani nauyi a zuciya. Amma a fuskarta babu komai sai “professional smile.” Da ta shiga reception, sai ta hango Zayd yana tsaye yana dariya tare da ma’aikata biyu. Yana riƙe da kwali mai kyau, an nannade shi da ribbon. Da ta shigo, Zayd ya juya ya hango ta, nan take ya ciro sabon gift daga cikin kwalin. “My Pretty! I was looking for you... amma fa na zo da gift ɗinki, me yasa kika bar wancan a company jiya? Na ga a waje, wai an ce ya ƙone 😳.” Amal ta tsaya cak, zuciyarta ta buga. Ta ɗan washe baki cikin karfin hali, ta ce: “Eh… ban ma san yadda hakan ta faru ba. Maybe wani ne ya bar wuta kusa da shi…” Zayd ya ce: "Aina kika ajiye? Amma a waje fa aka same su.." Amal ta ce "Maybe wani ne ya kai can.." Zayd ya ce "Bar su hassada ce kawai..." Zayd ya dafa kafaɗarta a hankali, yana murmushi. “Sorry fa, my Pretty. Ni fa bana son a sa ranki a wani abu mara kyau. Kin san ai duk abin da nake miki, daga zuciya yake.” Ta murmusa kaɗan, tare da sauƙe hannunsa daga kafaɗarta cikin raunanniyar murya ta ce “Na sani, Zayd. Na gode sosai… Allah ya saka da alkhairi.” Zayd ya matsa kusa, yana kallon fuskarta da kulawa. “Amma fa… naga kin canza yau. Kin yi kuka ne?” Ta girgiza kai tana ɗan dariya: “Kuka kuma? Ina! Na yi bacci ne kawai sosai.” Sai ya ɗan murmusa, ya riƙe hannunta da ta kasa janye wa.. “To idan kina buƙatar faranta rai, bari na fitar da ke yawo yau. No office stress, no Maleekh calls, just us.” Ta ɗan kalle shi cikin ido, tunawa da kalaman Maleekh jiya: “Ki zaɓi… Ni ko Zayd.” Zuciyarta ta yi nauyi, ta ɗan janye hannunta a hankali, tana murmushi. “Ba yanzu ba Zayd… muna da meeting da company masu saka jari. Maybe later.” Zayd ya gyara rigarsa, yana dariya: “To na yarda my Pretty. Amma ki yi min alkawari za ki bani lokaci na gaba. Ni dai Zayd bana fushi da ke, ko kina so ko baki so…sannan ga sabon gift nan” Amal ta ce "Kai dai baka gajiya, kawai leave it.." Ya ce: "Okay idan kika fito zaki amsa ai.." Ya fara yin gaba. Yana tafiya yana juyowa, yana kallonta da murmushi, Amal kuma ta tsaya tana binsa da ido, hawaye suka taru a idanunta. A zuciyarta ta ce: “Zayd mai kirki ne… amma zuciyata har yanzu tana da rauni da sunan Maleekh.” Bayan Amal sun fito daga meeting room. Kai tsaye kitchen ɗin campany ta wuce domin haɗa tea. Zayd yaga shigarta hakan yasa ya bi bayanta.. Amal ta shigo kitchen ɗin da nutsuwa tana buɗe flask ɗin ruwan zafi. Kamshin coffee da mint ne suka cika wurin. Ta ɗan sauƙe ajiyar zuciya tana haɗa tea. Zayd ya biyo bayanta cikin shiru. Ya tsaya daga nesa yana kallonta na wasu sakanni kafin ya ƙaraso kusa da ita. “Yau kyautar ta zobe ne…” ya furta da murya mai sanyi. “Ban taɓa miki kyautar zobe ba, kuma shine farkon da ya kamata in baki.” Amal ta ɗan yi murmushin rashin jin daɗi. “A’a ka bari kawai, bana buƙata.” Zayd ya ɗan matsa kusa. “Kar ki ƙi. Wannan fa na zuciya ne.” Tana ja da baya tana girgiza kai, “Zayd, don Allah” Amma ya riƙe hannunta yana ƙoƙarin saka zoben. A lokacin ne suka fara jayayya, ta ƙi karɓa ne saboda tana gudun matsala daga Maleekh, shi kuma yana ƙoƙarin nuna soyayyarsa. Daidai lokacin ƙarar buɗar ƙofa ta karade kitchen ɗin. Maleekh ya tsaya a bakin ƙofar, idonsa a rufe da zafin rai. Idonsa ya sauƙa a hannun Amal da Zayd ke riƙe. “Zayd…” ya furta a hankali, murya cike da tsawa. Kafin kowa yayi magana, ya ƙaraso da sauri ya cafke kolar rigar Zayd.. Amal ta firgita ta matsa gefe tana faɗin, “Maleekh, don Allah ka saurara” Amma kafin ta ƙarasa, Maleekh ya zabga wa Zayd mari..cikin zafin rai ya kai masa naushi a baki... Sai da bakin ya fashe.. “Bros! Me nayi maka kake dukana?” Zayd ya furta yana kare kansa. Maleekh ya ɗauke shi da wani marin da yasa rigarsa ta ɓalle... “Amal is mine!” ya furta cikin bacin rai.. Lokaci guda ya fara kai masa naushi yana marinsa. Ya ja shi waje yana dukansa.. Amal tana kuka tana bashi haƙuri amma sam ya ƙi. Har sai da suka fito reception..Yana dukansa. Ma’aikata suka fara fitowa daga ofis, kowa ya tsaya da mamaki. Wani murmushi mai tsoro ya bayyana a fuskokin wasu domin kowa ya san labarin Amal da Maleekh, sai dai sun yi tunanin sun rabu. Amal tana kuka tana ƙoƙarin tsayar da shi amma ya ƙi. Sai da ya ja Zayd har zuwa tsakiyar reception yana dukansa... Sai ya juyo ya kamo Amal, ya mannata a bango, jikinsa na ruri da fushi ya ce: "Baki yadda da abinda na gaya miki ba ko?..." Ya wurgata tsakiyar wurin ya ce: "Yanzu faɗa da ƙarfi kice... Ni Amal matar Maleekh ce.." Tana kallonsa da hawaye ta ce, “Bazan faɗa ba! Dukansa ba zai canza komai ba!” “Faɗa!” ya tsawata. “Faɗa da kanki — ki ce ni Amal, matar Maleekh ce!” Tana girgiza kai, tana kallonsa cikin takaici. Kallon su duka ma’aikata ke yi.. Cikin zafin nama Maleekh ya ɗaga ta, ya ɗauke ta sama kamar jaririya. Kowa ya yi shiru yana kallon su. Ya fita da ita daga reception zuwa harabar waje. “Maleekh! Ina zaka kaini?!” Ta furta tana kuka.. Ya buɗe motarsa ya jefar da ita cikin seat, ya rufe ƙofar da ƙarfi. Tana kuka tana bubbuga glass, “Maleekh, don Allah ka saurare ni!” Shi kuwa ya kunna motar cikin huci, bai ce komai ba sai kallo ɗaya da ke cike da haɗari. Engine ya yi vrrrm! motar ta nufi titi da gudu… Cikin mota shiru ya mamaye su. Amma shiru ne mai nauyi kamar ana iya jin bugun zuciyoyinsu. Ƙarar engine da A.C motar, da hucin iska daga window ne kawai ake ji. Amal tana zaune tana kuka a hankali, hannunta a gefe tana share hawaye. Maleekh kuwa yana tuƙi da hannuwa biyu a steering, idonsa a hanya, amma zuciyarsa na tafarfasa. Cikin murya mai nauyi ta ce, “Maleekh… kai ka faɗa min cewa nayi nesa da Zayd, sannan ina ƙoƙarin yin nesa da shi. Amma me yasa haka? Me yasa zaka dake shi a gaban mutane? Kamar ba ɗan uwanka ba...” Ya ƙara danne ƙafarsa kan accelerator, motar ta ƙara gudu... “Saboda bana son ganin wani na taɓa ki!” Amal ta zaro ido.. “Taɓa ni? Mai kake tunani ne? Wallahi ba abinda ya faru, kuma ba abin da zai faru, Zayd mutumin kirki ne..” “Na ganki!” ya katse ta cikin tsawa. “Na gan ku a kitchen, hannunsa a kan naki, kina dariya kamar babu komai!” Amal ta ɗan matsa baya tana girgiza kai.. “Ka yi tunanin hakan yana nufin soyayya ne? Zayd kawai yana ƙoƙarin saka min zobe. Amma ni na ƙi!” “Zobe?” ya yi dariya mai ciwo. “Toh me yasa kika ƙi ƙaryata shi a wajen jama’a? Me yasa kika tsaya kina kallo lokacin da yake ƙoƙarin saka miki?” “Saboda bana son rikici!” ta faɗa cikin kuka.. “Bana son a sake ganin ka haka, Maleekh! Ka san yadda jama’a ke kallonmu? Ka lalata min mutunci a gaban kowa!” Ya kalle ta da idanu masu kaifi, “Mutuncin ki?” ya maimaita cikin muryar tsawa. “Wato ni ban da mutunci? Amal, kina son ki yi wasa da ni?!” Ta yi shiru tana huci tana kallonsa. Sannan ta ce cikin rawar murya, “Ba wasa nake da kai ba, amma kai ba zaka taɓa fahimta ta ba. Kai kullum fushi, tsawa, da iko. Ka manta ni ma ina da rai!” Motar ta tsaya cak! Ya taka brake da karfi har jikin Amal ya bugi dashboard. Ya juyo ya kalle ta, idonsa jawur, numfashinsa yana fita da ƙarfi.. “Amal… bana wasa da ke. Na gaya miki zaɓi biyu ne kawai.” Ta juyo tana kallonsa cikin hawaye, “Ka ce min fa… idan na zaɓi Zayd?” Ya ɗan rufe ido kamar yana ƙoƙarin hana kansa fushi, sannan ya buɗe su a hankali. “Zan kashe ki… sannan in kashe shi.” Amal ta riƙe cikinta da hannunta, tana girgiza kai da firgici.. “Ka rasa magana me kyau sai wannan? Wato rayuwata ta koma wasan hannunka?” “Rayuwarki tawa ce!” ya furta da ƙarfi. “Bazan iya ra6an ki da wani ba. Ki yi tunani Amal, wallahi indai inada rai ba zan bari wani ya mallake ki ba.” Tana kallonsa cikin hawaye ta ce, “Kana ƙiran wannan da soyayya kuma? Wannan fa tsoro kake dasa mun a zuciya, sannan ka zalunci bai ji ba bai gani ba..!” Ya ɗan yi shiru na ɗan lokaci, sai murya ta sauya, ta koma kamar mai kuka: “Zalunci ne amma saboda ƙauna nake yi. Wallahi bazan iya ganin ki da wani ba. Kullum ina tunanin tafiyar ki da yanda zamu kasance tare...” Amal ta ɗan yi shiru, zuciyarta na bugawa da tausayi da tsoro a lokaci guda. Ta ce a hankali, “Idan haka kake jin ƙauna… to wallahi, ba ka sona. Son mallaka kake yi mun.”.. Maleekh ya ɗan kalli steering, ya dafe kansa da hannu ɗaya, yana maida numfashi da wahala. Sannan ya juyo ya ce a hankali, “Ki sani… ki na abin da na kasa bari, Amal.” Shiru ya biyo. Motar ta ci gaba da tafiya a hankali har duhu ya fara shiga domin tafiyar na da nisa, domin har su ɗan fita daga cikin gari.. Amal ta rufe idonta tana kuka, shi kuma yana tuƙi yana kallon hanyarsa kamar wanda ya manta inda yake nufa… Iska na kaɗawa a gefen villa ɗin, wacce ta daɗe babu mai zama a cikinta. Hasken chandelier ɗin falon yana ta rawa kamar zai mutu. Maleekh ya ja Amal har cikin babban falon, yasa key ya kulle sannan ya jefa key ɗin a aljihunsa... Amal ta tsaya tana kallonsa da kumburarren ido... “Maleekh me yasa muka zo nan?” ta ce cikin rawar murya. Ya juyo da wani murmushi mai sanyi amma cike da ɓacin rai. “Honeymoon muka zo, baby…” ya ce cikin muryar da ke cike da sarƙaƙƙiyar soyayya da iko. “Zamu huta anan, mu biyu… kafin zuciyata ta sauƙo daga wutar da kika kunna.” Amal ta ɗan matsa baya tana girgiza kai, “Honeymoon? Ka ɗauke ni da karfi ka kawo ni cikin daji, ka ce honeymoon?”. “Na gaya miki bana wasa da ke,” ya ce yana ɗaukar laptop daga saman kujera ya kunna, ya jingina da sofa. “Yanzu zan tambaye ki abu ɗaya, kuma bana so kiyi mun wasa.” Amal ta ƙure idonta a kansa tana huci.. “Me kake son sani?” Maleekh ya zaro wani file daga cikin jakarsa, ya jefa mata a gabanta. “Wannan rahoton ne daga likita,” ya ce cikin sanyi, muryarsa na dukan kunne kamar ƙaho. “Yana cewa kin zubar da cikin wata huɗu. Wannan rahoton ne daga club ɗin da aka sameki cikin jini.” Zuciyar Amal ta buga. Ta dago a hankali tana kallonsa, hawaye suka cika idonta. “Maleekh…” ta ce da muryar da ke rawa. “Ka kasa saurara na tun lokacin… ka kasa tambayata me ya faru.” Ya ɗan jinjina kai cikin ɓacin rai.. “To yanzu nake son jin ki. Ina sauraronki yanzu.” Amal ta miƙe da sauri tana faɗin, “To yanzu kake buƙatar ji na? Bayan ka riga ka yanke hukunci? Bayan ka riga ka ɗauke ni a matsayin mai laifi?”.. Amal tana surutai ta nufi ƙofa zata buɗe ta tafi taji ko ina a kulle. Haka ta haƙura tana kuka. Maleekh yana danna computer Ya ce. "Ke, bana wasa dake! Yanzu gaya mun, a kwanakin baya meya faru aka sameki a gidan club hakan ma a cikin jini sannan doctor ya ce, kin zubar da cikin wata huɗu..." Amal tana harararsa ta ce "Tin lokacin Meyasa ka kasa saurara ta?.." Ya ce cikin izzah. "Yanzu..Ina sauraronki.." Amal ta ce. "To nima banida lokaci yanzu.." Wani irin gigitaccen tsawa ya daka mata har sai da ta gigita. Sauran kaɗan ta fece jikinta na 6ari..." "Gaya mun na ce.." Muryarta ta rikice, tana girgiza kai, jikinta na rawa...Ta ce: “Ka yi mun hukunci ba tare da shaidar gaskiya ba, Maleekh! Ba ciki na zubar ba!” Ya ɗan miƙe daga kujerar, ya sauƙe ido daga kanta yana furta a hankali, “To menene ya faru, Amal? Me yasa aka sameki cikin jini a club?” Tana kallo cikin idonsa, murya ta fara karyewa, “Na ji labarin Aurenka da Farha shine nayi ta ƙiran ka, baka ɗaga ba. Na fita saboda ina sonka na je gidanku aka sanar mun cewa kana club, hankalina ya kasa kwanciya hakan yasa naje domin dubo ka. Na samu wasu ƴan mata suka sanar mun cewa kw fita amma zaka dawo yanzu...Na sha juice da suka kawo, sai na ji duniya ta fara juyawa… daga nan ban sake sanin komai ba. Ina farkawa sai a asibiti... Bayan zargina da ake akan batun nan naje wani hospital domin tabbatar da kaina. Likita yace babu wani cikin da aka zubar, amma an zuba wani abu a cikin abin sha na.” Ya ɗan tsaya shiru, idonsa ya ƙanƙance kamar mai son yin kuka amma ya danne cike da iko ya furta. “Me kike nufi? An drug ɗin ki?” Amal ta gyaɗa kai cikin kuka, “Eh… amma baka saurare ni ba. Ka bar ni cikin rauni, ka yi min hukunci kafin ka ji gaskiya.” Da sauri ta fara lalu6o wayarta yanda tayi snap ɗin result ɗin da doctor ɗin ta ya bata cewa babu abinda ya faru illah drugs da ta sha... Ta ce cikin rawar murya. "Ka ga..." Ya karɓa ya duba da kyau sannan ya jinjina kai ya ce: "Wa ya tura ki wurin? Ina nufin wa ya sanar miki cewa ina club?..." Amal ta girgiza kai ta ce "Kawai kayi haƙuri komai ya wuce.." A tsawa ce ya ce "Wa ya sanar miki?..." A ruɗe ta ce: "Fa F Far Farhaaa.." Ya rufe ido da hannu ɗaya, yana maida numfashi cikin wahala. Sannan cikin tsawa mai rauni ya ce, “Me yasa baki faɗa min tun farko ba?” Ta ɗaga kai tana kallonsa cikin hawaye, “Saboda baka tambaye ni ba.” Shiru mai nauyi ya sauƙa tsakanin su. Ƙarar iska daga window kawai ake ji tana shigowa tana motsa labulen bakin gilashi. Amal ta juyo gefe ta share hawayenta, ta ce cikin murya mai sanyi, “Wannan shine dalilin da yasa nake son barinka. Kai ka kasa sauraro na sai lokacin da zuciyarka ta riga ta yanke hukunci.” Maleekh ya kalleta sosai, idonsa ya canza daga fushi zuwa nadama. Ya matso kusa da ita a hankali, amma kafin ya iya cewa komai Amal ta juya ta kama ƙofa, ta fara dukan ƙofa tana faɗin, “Ka buɗe ƙofar, Maleekh. Ka barni in tafi.”.. Ya tsaya a gefe yana kallonta, muryarsa ta yi rauni sosai. “Idan na buɗe, ki gaya min gaskiya bakya sona?” Amal ta tsaya ta juyo tana kallonsa da hawaye, “Na taɓa sonka, amma yanzu tsoranka ne kawai a zuciyata.” Ta juya ta zauna a ƙasa tana kuka. Maleekh ya zauna yana kallonta, zuciyarsa ta rikice gaba ɗaya.... A bangaren Zayd kuwa... Zayd ya shigo gida da jiki gaba ɗaya a raunane. Rigar sa ta tsage, fuska ta kumbura, leɓensa ya fashe. Ya tsaya a bakin ƙofa yana riƙe da ciki da hannunsa, yana fitar da numfashi da ƙyar.. Ammy da yaranta suna zaune a babban falon suna hira da dariya, sai suka juyo da ganin yadda yake jina-jina... Ammy a tsorace ta ce: “Subhanallah! Zayd! Me ya same ka haka? Waye ya maka haka?” Zayd ya zauna a kujera yana jan numfashi. Ya share jinin da ke gefen leɓensa sannan ya ce cikin muryar da ke cike da haushi: “Maleekh ne... Maleekh ya kwace min masoyiya sannan ya dake ni kamar ɗan yaro a gaban mutane...” Falon ya ɗauki shiru, kowa ya kalle shi da mamaki. Ammy ta ɗaga gira ta ce: “Masoyiya kuma? Wace yarinya ce da zata sa Maleekh yayi maka haka?” Zayd ya ce: “Amal... Sunanta Amal. Tana aiki a cikin campany ɗin mu.” Daga nan kowa ya girgiza kai. Arfat ta zabura da sauri tana faɗin: “Tabbas ai dole ne Yaya Maleekh ya maka duka! Kai baka san yanda yake ji da Amal ba? Har sumar dani yayi saboda ita, wallahi a lokacin na ɗauka kashe ni zai yi saboda wata Amal!” Islam ta ƙara da murmushi mai cike da raini: “Ai ba kwace maka masoyiya yayi ba, dan tun farko ita masoyiyarsa ce. Amal ta Maleekh ce, kai dai baka san komai ba.” Zayd ya kalli Islam da Arfat, idanunsa suka kaɗa da fushi. “Shi yasa ke kike magana kamar kina farin ciki da hakan!? Idan masoyiyarsa ce me yasa yake rayuwa kamar wanda ya tsane ta? Me yasa baya nuna cewa yana son ta? Yake toshe mata hanya, yana tsareta kamar bai damu da ita ba?” Arfat ta ɗaga kai tana murmushi mai ɗan raini ta ce: “Eh to... Wannan ai shi ne irin soyayyar Maleekh, mai zafi, mai daɗi, mai ƙarfi. Kai dai baka san komai game da su ba, in taƙarƙare maka to akanta Yaya Maleekh ya kwanta jinya, ya samu matsalar zuciya...” Farha ta harare su duka biyu cikin bacin rai ta ce: “Dallah ku daina wannan sakarcin magana! Naga yanzu Maleekh ba ya son Amal, wallahi ba ya yinta. Dole ne ku gane hakan.” Zayd ya miƙe tsaye a hankali, yana goge jinin da ke gefen fuskarsa. Idonsa ya sauya, ba na zafi kawai ba, har da na ƙuduri... Ya ce da muryar da ke cike da alƙawari: “Ko da Maleekh yana so ko baya so... sai na mallake ta. Amal zata zama tawa ko ta halin ya ya ne.”.. Ya juya da fuskar da ta haɗa zafi, rauni da azama, sannan ya nufi ɗakinsa... NEXT NEXT NEXT.... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 53 to 54 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Fitowar hasken safiya, rana ta fara bayyana a saman tagogin gidansu Amal. Inna tana zaune a falon ƙasa, tana sanye da hijabi tana lissafin tasbihi, amma idonta duk ya nuna damuwa. Tana tunanin dalilin da yasa Amal bata dawo gida ba tun jiya. Ƴan aiki suna ta motsi a kusa, wata na share falo, wata na haɗa breakfast. Cikin wannan yanayi ne maigadi ya shigo yana ƙiran Inna. Maigadi yana tsaye a ƙofar falon ya ce: “Inna, anyi baƙi.” Inna ta ɗago kai da mamaki ta ce: “Baƙi kuma? Da mota ne suka zo?” Maigadi ya ce “A’a Inna, da ƙafa suka zo. Wani dattijo ne da matarsa, sai wani saurayi da wata ƙaramar yarinya..” Inna ta haɗe gira ta ce “Toh, to. Kace su shigo nan cikin falon.” Maigadin ya juya ya fita. Ba da jimawa ba, sai ga su sun shigo cikin falon, dattijon yana da farin gashi da tsintsiya, matarsa tana sanye da hijabi mai launin toka, sannan wani saurayi da ya cika kamar ɗan gari, kyakkyawa da tsawo, sai karamar yarinya mai kimanin shekara 17 zuwa 18. Inna tana kallonsu har suka ƙaraso. Tana ganin dattijon sai ta zabura ta miƙe tsaye da mamaki. Inna da mamaki da farin ciki ta ce “Yawale!? Kai malam Yawale! Ashe kai ne?” Malam Yawale yana dariya ya ce “Na’am Inna Delu! Kin gane ni ke nan.” Inna tana dariya ta ce “Wallahi na kasa gane ka, Malam Yawale! Ai shekaru sun ja fa. Ina Zainabu? Ga ita nan ko?” Zainabu matar Yawale, tana murmushi ta ce. “Eh ni ce, Inna. Na gode Allah da naga fuskar ki bayan shekaru.” Inna ta ce. “Lallai yau gida yayi albarka. Kun taho daga ina haka?” Malam Yawale cikin farin ciki ya ce “Daga ƙauyen Gajeren Rafi a cikin Kaduna Local Government. Ai kin san shi can bayan Rijana, hanyar zuwa Kachia. Mun daɗe muna shirin zuwa ganin ku, sai yau muka samu dama.” Inna ta gyara

Chapter 35 of 62