zama ta ce
“Toh, ai kunzo gida. Ku zauna. Allah ya kawo ku lafiya. Yanzu ga wannan saurayin da karamar yarinyar nan fa?”
Malam Yawale yana nuna su ya ce
“Wannan ɗana ne, Kabiru. Ga matata Zainabu, kuma wannan karamar yarinyar mu ce wato auta kenan Halima. Dake yaran duk sun mutu sai iya biyun nan, Kabiru da Halima ne suka rage mana, ai Halima tunda aka gaya mata akwai ƴar uwarta Amatu a burni sai ta nace zata zo ta ganta da idonta.”
Cikin jin wannan kalma, Inna ta ɗan tsure, sai ta murmusa da ƙyar tana danne tsoro.
Inna ta share gumi a goshi ta ce:
“Eh, eh... Amatu dai tana wurin aiki yanzu. Tunda safe ta fita ba ta dawo ba. Aikin campany ne, kin san dai irin aikin birni babu sauƙi.”
Zainabu ta ce cikin kalar tausayi.
“Eh ai haka rayuwar burni take. Amma sai ta dawo fa mu ganta. Mun daɗe muna son muje mu gaisheta, tun bayan rasuwar mahaifiyarta.”
Inna tana murmushi amma idonta cike da damuwa ta ce.
“Insha Allahu zata dawo. Ku huta da gajiya. A girka muku abin ci. Ke Halimatu! Je ki ce a dafa muku tuwo da miyar taushe.”
Halima ta tashi da hanzari kamar wanda aka zabure ta..
Kabiru yana duban falon ya ce
“Ai gidan nan ya ginu sosai. Amatu kenan ke zaune a irin wannan gida? Lallai ta samu albarka a burni.”
Inna tana dariya cikin ɗan ɗoki ta ce
“Eh, ai Amatu yarinyar kirki ce. Ta dage da aiki sosai. Allah ne ya bamu arziki ta hannunta.”
Malam Yawale yana kallon Inna ya ce.
“Toh Alhamdulillah. Sai dai Inna, muna fatan komai lafiya. Na ji kamar kin damu ne tun muna shigowa.”
Inna tana ƙoƙarin boye damuwarta ta ce.
“A’a, lafiya lau. Kawai gajiya ce ta kwanan jiya.”
Suka zauna suna hira, amma Inna tana ɗan duban ƙofa lokaci-lokaci zuciyarta cike da fargaba, tana addu’ar kada Maleekh ya dawo da Amal cikin wannan yanayi, musamman yanzu da danginta daga ƙauye suka iso.
Bayan an ci an sha, an jera kofin shayi a kan teburi. ƙamshin tuwo da miyar taushe ya ratsa ko ina. Kowa ya ɗan yi nishaɗi, ana hira a hankali sai Malam Yawale ya tashi ya gyara zama, fuskar sa cike da murya mai nauyi...
Malam Yawale yana kallon Inna ya ce:
“Inna Delu, daman ina so mu yi wata magana mai muhimmanci.”
Inna ta gyara zama, tana miƙewa a hankali ta ce:
“To malam yawale, ina jinka. Me ke ranka? Me kake so mu tattauna?”
Malam Yawale ya ɗago kai yana kallon duk wanda ke falon, ya dubi Kabiru da Halima a gefe sannan ya koma kan Inna.
Malam ya ce
"Kin dai san ni Yayan Mahaifiyar yarinyar nan ne wato Amatu, kuma iyayenta mahaifiyarta da mahaifinta sun juma da rasuwa tin tana ƙarama, yanzu abinda na yanke shine, me zai hana zumuncin mu yayi karko, mu haɗa zumunci sosai, inaso zan haɗa ɗana kabiru da Amatu Aure.."
Kabiru yana gefe yana farin ciki...
Inna taji batun baiyi mata daɗi ba ta ce
"Wai malam yawale taya ma kuka san muna nan Abuja?"
Malam ya ce
"Ai mun shiga Kaduna can gidan da kuke akace kun daɗe da barin Kaduna kun dawo Abuja. Shine muka zo Abuja munata nema saida muka yi sati guda anan Abuja kafin muka samu gidan ku.."
Inna ta ce
"Aww saboda kun ji munyi arziki shine zaku wanko ƙafa kuzo wai akan a haɗa aure ko? To sannu masu son zuciya.."
Malam ya ce
"Me kike faɗa haka Inna Delu?.."
Inna ta ce
"Lokacin da iyayen Amatu suka rasu tin tana yarinya ba ƙin kula da ita kukayi ba? Saboda babu dukiyar iyayenta duk sun ƙone a gobara shine kuka guji ɗiyarsu, kuma alhalin lokacin da iyayenta suke da rai babu abinda kuke rasawa daga wurinsu, kullum a cikin maula kuke, ni mahaifiyar mahaifin Amatu ce inada iko akansa amma ban hanashi taimaka muku ba, shi kaɗai na haifa a duniya bashi da wa bashi da qani...Na tabbata da inada wasu ƴaƴa bayan shi nasan zasu taimaka mun...amma dake babu kowa, ku da kuke ƴan uwan mahaifiyarta sai kuka kama gabanku, wai bakwa so a ɗaura muku dawainiya, saboda iya Amatu kawai, amma ai kuna riƙe da ƴaƴanku ko? Marasa imani kawai, badan zuciyar musulunci ba ai bazan kalli yanda kuke ba tinda kuka kasa riƙe ɗiyar ƴar uwarku saboda bata da rai, kun ji kunya, yanzu kuma ko kunya babu kunzo wai batun auren zumunci, to baza'ayi baaa...."
Malam yawale ya ce
"To bamuda halin taimaka muku ya zamuyi? Shiyasa muka daina zuwa yanda kuke...ba gashi yanzu tayi arziki ba, nima dai inada iko akan Amatu, don haka sai anyi auren nan..."
Zainabu ta tsoma baki cikin maganar ta ce:
“Inna Delu, ba mu zo ne don mu tayar da hayaniya ba. Mun zo ne saboda mu gyara kuskuren da muka aikata a baya, mu tayar da zumunci, mu ba wa Amatu gida na gaskiya. Mun zo ne da niyyar taimako, ba da tada faɗa ba.”
Malam Yawale yana jin zafi amma cikin nutsuwa ya ce:
“Inna, gaskiya ba mu zo don mu yi ruɗu ba. Na san abin da kuka ji lokacin da iyayen Amal suka rasu, amma ni da matata, duk lokacin da muka yi tunani, zuciyarmu ta cewa mu taimaka. Ina son Amatu tun tana ƙarama. Yanzu da akwai damar a gyara, me ya hana mu haɗa Kabiru da ita? Zan riƙa kula da ita, in ba haka ba za ta ci gaba da zama a burni ita kaɗai a yayin da babu ranki..."
Inna ta dafe goshi, idanuwanta sun cika da hawaye. Ta kalli Kabiru, ta ji raɗaɗi a ranta. Sai ta miƙe hannu ta ɗaga ƙofin shayin ta karɓa..
Inna ta yi sanyi sosai, ta tsinke muryarta da cewa.
“Kun bar ta lokacin buƙata, kun guje ta saboda rashin dukiya yanzu kawai kun dawo saboda nufin ku ɗaura mata aure da ɗanku? Ai ni mahaifiya ne, na san halin da ƙasa take; Ba da sauri zan yarda ba, Malam Yawale. Zumunci abu ne mai tsarki; amma gina zumunci ya danganta da niyya, tausayin juna da gaskiya ba don abun duniya ba.”
Malam Yawale ya kusanci Inna, ya yi magana da murya mai laushi da ƙarfin gwiwa ya ce
“Inna, ina roƙon ki da zuciya ɗaya: ki yi la’akari da abin da zai faru da Amatu idan ta ci gaba ita kaɗai, ko da Aure zata yi dole fa sai an nemo ƴan uwanta, shin waye madaurin auren ta?. Ni ba zuzzurfan arziki nake nema ba; ina neman ‘yar uwa, ina neman wurin da za ta samu gida. Kabiru ba ɗan son duniya ba ne; yana da niyyar gaskiya. Inna, ki kalla zuciyarta ki nuna karamci. In ba mu yi ba, me zai faru da ita? Zamu haɗa zumunci ne domin ta samu gida, ba domin mu mallaki dukiya ba.”
Inna ta rufe baki, idanuwanta sun yi ja. A gefen, Zainabu ta kalli mijinta ta ɗan matsa masa hannu: suna ƙoƙarin nuna jituwa. Kabiru ya yi ƙasa ya yi murmushi, sai ya tashi ya yi jinjina kai ya ce
“Inna, ina roƙonki. Zan riƙa kula da ita saboda gaskiya ce a raina. Ba ni da wata buri sai kula da Amatu, mu gina mata gida mai cike da nutsuwa.”
Halima ta ɗago itama ta ce
“Inna, don Allah, ki ba mu dama. Mu za mu yi mata biyayya, mu kula da ita kamar matar gida.”
Inna ta ɗan yi shiru, ta duba fuskokin su duka, ganin kyakkyawan niyya a idonsu ya sa zuciyarta ta ɗan sassauta, amma tana riƙe da ƙarfin magana ta ce:
“Zan yi tunani, Malam Yawale. Ba zan ɗauka a sauƙaƙe ba. Ku ba ni lokaci nayi tunani. Kuma ku sani: idan kuka yi niyya na gaskiya, zan yi marhaba amma idan niyyarku ta sha alamar biyan buri ne kawai, to ku bar ni kawai. Kada ku yi tsammani na yarda da gaggawa.”
Malam Yawale ya yi godiya, ya yi jinjina, Zainabu ta yi murmushi, Kabiru ya sunkuyar da kansa cikin godiya. Suka gyara zama, an dawo da yanayin hira amma a hankali, Inna kuwa ta nufi ɗaki ta zauna tana tunani...
Anan ne bayan Inna ta zauna a ɗaki tana dogon tunani, tana ta kai komo tsakanin abin da zuciyarta ke so da abin da al’adun rayuwa ke ɗora mata. Bayan ta yi tunani, ta tashi ta fito falo cikin sanyin jiki. Dukkan su Malam Yawale suna zaune suna hira a hankali, Halima na wasa da ƙaramar wayarta, Kabiru kuma yana ta kallon ƙasa yana murmushi lokaci zuwa lokaci.
Da suka ga Inna ta fito, duk suka gyara zama.
Inna Delu ta zauna a kujera, ta kalli Malam Yawale sannan ta ce
“To malam Yawale, bayan tunani mai zurfi da nayi… na yanke shawarar cewa babu laifi idan zumunci ya tabbata. Na amince da auren nan.”
Malam Yawale ya ɗaga kai cikin farin ciki, ya saki murmushi mai nuna godiya.
Malam Yawale ya ce
“Alhamdulillah! Wallahi Inna Delu, kin faranta mana rai sosai. Wannan zumunci ba zai gushe ba in sha Allah.”
Zainabu ta dafa kafadar mijinta da murmushi ta ce:
“Na faɗa maka ai, Inna Delu mai zuciya ce. Allah ya saka da alheri.”
Halima ta tafa hannuwa da murna tana faɗin.
“Wai da gaske ne? Amatu za ta zama babbar yayata? Amma naji daɗi sosai.”
Kabiru ya murmusa cikin jin daɗi, ya sunkuyar da kai yana jin kamar ya yi nasara mafi girma a rayuwarsa.
Kabiru a hankali ya furta.
“Alhamdulillah… zan nuna mata ƙauna fiye da yadda ta zata.”
Sai kawai Inna ta ɗan gyara zama, ta miƙa hannu tana nuna alamar magana.
Ta daidaita murya sannan ta ce
“Amma ba ƙauyenku zata koma ba, ko? Ni ban yarda ku kai ta can ba.”
Malam Yawale ya yi saurin girgiza kai da murmushi mai kwantar da hankali ya ce
“Ke da kanki kin san yau zaman ƙauye ya zama tarihi gare mu. Mun bar can. Muna nan Abuja yanzu, kuma zamu cigaba da zama tare da ku nan kusa. Ba mu zo da zancen kai ta ƙauye ba.”
Inna ta ɗan ɗaga gira tare da faɗin.
“Too… kenan zaku cigaba da zama anan tare damu kenan?”
Zainabu ta amsa kafin ma mijinta ya buɗe baki.
“Eh ai duk mun taho da kayayyakin mu gaba ɗaya. Mun sayar da shanayen mu, mun siyar da gonakin masara saboda hidimar auren nan. Mun yi niyya da gaskiya. Wannan aure muhimmi ne a wurinmu.”
Inna ta ɗan rintse ido tana murmushi amma zuciyarta ta yi nauyi. Ba ta so zama da mutane masu hayaniya ba, amma a wannan lokaci ta kasa yin musu magana mai zafi.
Inna a hankali, tana numfasawa ta ce:
“To Allah ya sa alheri. Amma fa ku sani, wannan gida ba wurin zazzafar hayaniya bane. Kowa ya san iyakarsa.”
Malam Yawale da girmamawa ya ce.
“Insha Allah, komai zai tafi da nutsuwa, Inna Delu. Mun gode sosai da wannan karɓa. Allah ya saka da alheri.”
Kabiru cikin farin ciki, yana miƙa hannu ya ce
“Inna, na gode sosai. Wallahi zan yi duk abin da zai tabbatar miki cewa na cancanci amincewarki.”
Inna da ɗan dariya ta ce
“To ka tabbata kana son ta da gaske, ba saboda ‘yar birni ce ba?”
Kabiru ya ce:
“Da gaske, Inna. Ba saboda burni ba, saboda ita ce wadda zuciyata ke gani har yanzu a mafarki.”
Kowa ya yi murmushi. Falo ya cika da sanyin iska, amma a cikin zuciyar Inna akwai shakku, da tambayoyi da ba ta so ta faɗi a baki. Sai ta kalli ƙofa inda Amal ke saba shigowa da murmushi... sai kawai ta furta a zuciyarta:
"Ya Allah ka shiryar da komai, ka kare ta daga abinda ba alheri ba..."
Kwana uku kenan rabon da Amal ta fito daga cikin tsohuwar villa ɗin da Maleekh ya kulle ta a ciki. Wurin yana da yalwa, amma babu farin ciki, babu annuri sai tsananin shiru da bugun zuciya....
Amal tana zaune a kan kujerar falo, ta lumshe ido tana jin karar sautin agogo da ke bango “tick… tick… tick…” kamar yana ƙara mata damuwa. Idonta ya kumbura saboda kuka da rashin barci.
A gefe kuma, Maleekh yana zaune a kan kujera mai launin duhu, gaban sa akwai laptop, yana danna keyboard ba tare da kallonta ba. Duk da haka, idonsa na bibiyarta lokaci zuwa lokaci.
Amal a kasalance ta ce
“Maleekh… sau uku nake tambayarka, har yanzu baka ce min me kake nufi da wannan tsarewar ba. Wannan ai kamar ɗauri ne.”
Maleekh ya tsaya daga typing, ya ɗago ido yana kallon ta daga bisani ya ce
“Ba ɗauri bane, Amal. Hutu ne. Hutu daga duniya, daga Zayd, daga duk wanda ke son shiga tsakaninmu.”
Amal ta tintsire da dariya cikin takaici ta ce
“Hutu? Hutu da kuka? Hutu da tsoro? Hutu da ƙunci? Wallahi kai ba ka sona, kana son mallakata ne kawai.”
Maleekh ya miƙe tsaye, yana tafiya a hankali zuwa gareta ya ce.
“Na fi kowa sanin abinda ke cikin zuciyata, Amal. Idan mallaka ce kike gani, to saboda bana so wani ya shiga cikin zuciyarki, ko da kuwa hakan yana nufin ki tsaneni.”
Ya tsaya a gabanta, idonsa ya cika da zafin so. Hannunsa ya kai ya taɓa fuskarta, da sauri ta ja kanta gefe tana hawaye..
Amal cikin murya mai sanyi da zafi ta ce:
“Idan kana son kare ni, to ka bar ni in zaɓi rayuwata da kaina. Wannan… wannan tsarewar ai azaba ce, ba kariya ba.”
Maleekh ya janye hannunsa a hankali, ya koma ya zauna yana sauƙe numfashi.
Sai shiru ya cika falon na tsawon mintuna. Sautin iska daga taga na ta kaɗawa.
Daga nan sai ya ɗauki magana a hankali kamar wanda yake magana da kansa:
“Na yi alkawarin bazan bar wani yaci zarafinki ba, bana son wani ya sake taɓa ki. Amma ki faɗa min gaskiya Amal…”
Ya ɗaga kai yana kallonta kai tsaye cikin ido sannan ya ce
“…me ke tsakaninki da Zayd. Har yanzu zuciyarki na rawa idan aka ambaci sunansa?”
Amal ta girgiza kai cikin takaici ta ce
“Babu komai tsakanina da shi! Wallahi babu komai. Sai dai ban san me yasa kai kullum kana ɗauka akwai wani abu ba…”
Maleekh ya katse ta, cikin ɓacin rai..
“Saboda idan kika dubi idanunki a lokacin da yake kusa da ke, sai suyi kama da yadda suke kallona a da.”
Amal ta share hawaye ta ce.
“Ka manta ne? A da kaine ka fara juya idanunka daga gare ni.”
Suka kalli juna na wasu daƙiƙu masu zafi, zuciyoyi biyu masu rauni, amma kowanne cike da ƙiyayyar soyayya.
Maleekh ya lumshe ido, ya furta a hankali.
“Na kasa tsoratar da ke kamar yadda nake so. Amma wallahi Amal, idan kika fita daga wannan gidan ba tare da iznina ba, sai duniya ta ga sabon Maleekh.”
Amal ta miƙe tsaye tana kallonsa cikin kuka ta furta:
“Duniya ta riga ta gani tun ranar da ka fara rufe ƙaunarka da fushi…”
Ta juya ta shige ɗaki ta rufe ƙofa da ƙarfi...
Daman wurin kwanciyarta cikin ɗakin can bedroom, shi kuma a kujerar falon..
Maleekh ya tsaya a tsaye yana kallon ƙofar da ta rufe, hannunsa na karkarwa. Sai kawai ya sau numfashi a hankali, yana furta
“Ko da ke ce azabata, sai na kare ki daga duk wanda ba ni ba.”
Washegari da asuba bayan sun yi sallah suka koma bacci, yanzu misalin ƙarfe 9 hasken safe ya fara ratsawa ta ƙofar window mai yalwa. Rana ta fara bayyana a hankali. Amal ta tashi daga kan gadonta, ba ta yi barci ba. Tun asuba zuciyarta ke sarƙaƙiya; tunanin Maleekh, da Inna komai ya rudeta..
A hankali ta miƙe, ta nufi tagar da take kallon harabar gidan. Wani ƙaramin tsuntsu ya tsaya a kan reshen bishiyar mango yana waka, kamar yana kiranta da “taho ki fita daga wannan zullumi.”
Amal ta lumshe ido, ta furta cikin muryar da ke rawa:
“Ya Allah… ban san me yasa soyayya ta zama kamar ɗaurin kurkuku ba.”
Ta ɗauko gyalenta da ke kan kujera ta lullube jikinta da shi. Ta duba gefen falon, inda Maleekh ya kwana bisa kujera yana bacci a gajiye — laptop ɗinsa a gefe, hannunsa ɗaya a jikin kujera. Idonsa a rufe, amma yana numfashi da sauri, kamar wanda yake cikin mafarkin tashin hankali.
Ta tsaya tana kallonsa na daƙiƙu da dama. Zuciyarta ta ƙuna tsakanin ƙauna da tsoro.
Amal a cikin zuciya ta furta.
“Ka ɗaure ni saboda kana son kare ni… amma daga me? Daga kai ne ko daga wasu?”
A hankali ta fara matsowa da sauri, ta nufi ƙofar falon. Sai kuma ta tsaya ta dawo tana duba jikin kujerar Maleekh. A kan stool ɗin kusa da shi akwai makullai.
Ta ɗan tsaya tana saurarar numfashinsa har yanzu yana bacci. Sai ta matso da sannu ta ɗauki makullin a hankali, ta riƙe a tafin hannunta...
Amal a hankali, cikin zuciyarta ta furta.
“Ka gafarce ni, Maleekh… amma sai na gudu daga wannan soyayyar da ta fi ƙauna zafi.”
Ta nufi ƙofa, ta cire makulli tana ƙoƙarin buɗewa. A lokacin ne ƙaran “click” na makullin ya ɗan motsa. Maleekh ya motsa a hankali, ya buɗe idanu.
Idonsu ya haɗu.
A wannan lokacin lokaci kamar ya tsaya, iska na kaɗawa, zuciyoyi na bugawa.
Maleekh da taushin murya mai cike da umarni ya ce
“Amal… ina zaki je?”
Ta tsaya a ƙofa tana rawar jiki, hawaye na silalowa a kumatunta.
“Zan tafi gida… Zan koma wajen Inna.”
Maleekh ya miƙe a hankali daga kujera, yana tafiya zuwa gareta.
“Ba zaki tafi ba.”
Amal ta ce:
“Ka tsaya Maleekh… ka barni. Na gaji da zama cikin fargaba. Ka barni in tafi, wallahi zan dawo idan lokaci ya dace.”
Maleekh ya tsaya da nisan matakai biyu daga gareta, idonsa a kanta ya ce:
“Idan kika fita a yau, ki manta da ni gaba ɗaya. Kuma kar ki sake dawo da sunana a bakin ki.”
Amal ta share hawaye sannan ta ce:
“Idan hakan ne… to zan manta da kai, amma bana fatan na manta da ƙaunarka.”
Ta buɗe ƙofa ta fita da gudu...
Maleekh ya tsaya a tsaye yana kallonta ta bar gidan, jikin sa na rawa, idonsa cike da ƙwalla da zafin ɓacin rai.
Ya daka tsawa yana furta:
“Kin gudu a yau, Amal… amma soyayya ba ta da hanyar guduwa, zata dawo da ke gare ni.”...
☆☆☆☆☆
Ƙamshin turaren wuta ne ya cika falon lokacin da Amal ta shigo cikin gidan a hankali. Idonta cike da hawaye, amma a yau farin ciki ya fi fitarwa — ganin Inna bayan kwanaki huɗu a tsare.
Amal ta murmusa tare da yo wa kan Inna.
“Innaaa…”
Inna da sauri ta miƙe, tana rungumarta...
“Subhanallah! Amal! Ina kika shiga ne har kwanaki huɗu? Na kusa hauka fa!”
Malam Yawale da murmushi amma cikin mamaki ya ce
“Wani irin aiki ne haka da mace ke kwana huɗu bata dawo gida ba?”
Amal ta kalli ƙasa, tana neman magana...
“Ina… ni dai…”
Inna tayi saurin katsewa cikin ladabi.
“Aiki mana ya riƙe ta, Malam. Tunda ta fara wannan aikin dai ta shiga hannu sosai, sai yanzu ta samu hutu.”
Malam Yawale yana girgiza kai ya ce
“To ai Allah ya kyauta, amma mace ta san iyaka da fita. Kwana huɗu fa ba wasa bane.”
Ya koma ya zauna, yana ɗan ɗaga rigarsa cikin nutsuwa.
Inna ta kama hannun Amal, tana jan ta ciki:
“Zo mu shiga ciki mana, ki sha ruwa ki huta, tukunna.”
Suna shiga ɗaki, Inna ta rufe ƙofa, ta kalli Amal da idon tambaya.
“Amal, yanzu fa ki faɗa min gaskiya. Ina kika tafi da Maleekh har kwanaki huɗu...?”
Amal ta sauke numfashi, muryarta tana rawa ta ce.
“Inna… ya tsare ni ne saboda kishi. Ba don komai ba. Bai yarda in fita ba, saboda wata magana da ya ji.”
Inna ta ɗan numfasa, tana kallonta da tsantsar tausayi ta ce:
“To ai kishi ba hujja bace ta tsare mutum, Amal. Amma yanzu ba wannan ba, saurara.”
Amal ta ɗaga kai da fargaba ta ce:
“Mene ne kuma, Inna?”
Inna ta kalle ta a hankali sannan ta ce.
“Sun zo ne Malam Yawale da iyalinsa da batun haɗa ki aure da yaronsu. Sun ce idan kin yarda, zasu cigaba da zama damu a nan har bikin ku ya yi kusa.”
Amal ta firgita, idonta ya faɗa sosai ta ce:
“Aure? Da yaronsu?”
Inna ta gyara zama ta ce.
“Eh mana, Malam Yawale ya faɗa da bakinsa. Da ma suna son hakan tun da daɗewa. Ni kuma ban ce komai ba, na ce sai na ji ra’ayinki tukunna.”
Amal ta lumshe ido, tana jin zuciyarta ta buga kamar zatayi kuka ta ce:
“Inna… ni kuwa Maleekh fa?”
Inna ta kalleta kai tsaye ta ce.
“Na san kin kamu da shi, amma kin ga irin halayensa. Kin ga irin duniyar da yake ciki. Ki yi tunani sosai, Amal, aure ba soyayya kawai ba ce, idan kika auri Maleekh baza ki taɓa samun kwanciyar hankali ba, domin duk iyalansa basa sonki, ga uwarsa ga kannensa da suka zo har gida suka miki dukan tsiya, sanadiyyarsu kika shiga hannun ƴan sanda, ki nutsu Amal, auren masu kuɗi bala’i ne gashi suna gadara da gidan da muke ciki ɗansu ne ya siya mana, kin ga wulakanci kuwa sai mun ture....”
Amal ta durƙusa, idonta cike da hawaye ta ce:
“Inna… wallahi ban san yadda zan yi ba. Zuciyata ta fi karfi na.”
Inna ta dafa kafadarta ta ce
“To ki natsu, ki bar komai a hannun Allah. Amma ki sani, rayuwa tana tafiya da hankali, ba da zuciya kaɗai ba.”
Iskar yamma ta busa a hankali, tana ɗauke da ƙamshin hayaki daga kicin inda Zainabu ke dafawa. Rana ta fara faɗuwa, hasken ta ke ta ratsa gilashin windows na gidan da nutsuwa.
Amal ta fito daga ɗakin Inna cikin doguwar riga, ta ɗaura veil ɗin kanta da nutsuwa, amma fuskarta cike da ruɗani da tunani.
A can gefe, sai ta hangi Kabiru yana zaune a kan chair kusa da bishiyar flower, yana wasa da wayarsa. Fuskarshi mai cike da kamala, yana murmushi kamar wanda bai san komai ba.
Zainabu ta fito tana faɗin.
“Kabiru, ina ƙanwarka Halima ta kawo muku kunu, ku sha kafin abincin yamma.”
Kabiru yana murmushi ya ce:
“Na gode Mama, amma dai sai mu ci gaba da zama lafiya a gidan nan, ko?”
Zainabu da murmushi ta ce:
“Insha Allah, ai yanzu dai mun zama dangi ɗaya. Komai Allah ya haɗa.”
Sai Amal ta ƙaraso a hankali, ta tsaya tana kallonsu.
Zainabu ta hango ta ta ce:
“Ai gata nan fa Amatu. Zo nan yarinya, kin huta koh”
Amal ta ɗan yi murmushi mai nauyi sannan ta ce.
“Eh, Alhamdulillah.”
Kabiru ya tashi tsaye da murmushi mai cike da fara’a ya ce:
“Sannu da dawowa, Amatu. Na jima ina son in ganki. Sun faɗa min labarinki sosai.”
Amal ta ɗan ɗaga kai cikin ladabi ta ce:
“Na gode.”
Kabiru yana kallonta ya ce
“Mama tana ta cewa mu ne muka dace, saboda zumunci. Amma ba lallai kina ganin hakan ne, ko?”
Amal ta yi shiru, tana kallon ƙasa sannan ta ce
“Ni ban san me zan ce ba… komai yanzu sai abunda iyaye suka tsara...”
Kabiru ya matso da murya a hankali ya ce.
“Ni dai bana son a ce an tilasta miki. Amma ina fata ki gane ba wai aure kawai nake nema ba, ina son a riƙa zama da juna lafiya, kamar ‘yan uwa cikin mutunci. Na ga yadda kike da kunya, ina girmama hakan.”
Amal ta ɗan yi murmushi mai rauni ta ce
“Na gode Kabiru. Allah ya saka da alheri.”
Sai shiru ya rufe tsakanin su, iska na kaɗa flowowin wurin...
Sai dai a zuciyarta, Amal tana ji kamar ta kulle kanta ta yi kuka.
Domin ko da Kabiru yana da halin kirki, har yanzu hoton Maleekh bai bar kwakwalwarta ba.
Daga nesa, Inna ta leƙo daga window tana kallonsu, zuciyarta cike da damuwa da shakku tana so ta ga farin cikin ‘yarta, amma tana jin tsoron cewa soyayyar Amal da Maleekh zata kawo bala’i.
Washegari da safe..
Rana ta fito. Falo cike yake da mutane Inna Delu, Malam Yawale, Zainabu, Kabiru, Halima, da Amal wacce take zaune a gefe cikin nutsuwa amma fuskarta cike da damuwa.
Ammy ce ta shigo gidan cikin sheƙin kaya, da ƙamshin turarenta mai ƙarfi. Tana rike da jaka mai tsada, fuskarta cike da ɗaga kai da girmankai.
Maigadi ya biyo bayanta yana gaisuwa, tana amsa kai tsaye da ƙasƙantacciyar murya.
Da zarar ta shiga falo, idanunta suka tsaya akan Amal.
Ammy cikin ɗaga murya ta ce.
“To, ashe nan kika ɓuya? Shine kika janye ɗana daga gida, kika mai da shi ɗan wahala, ashe kina nan kina zaune lafiya!?”
Inna ta ce
“Subhanallah, Hajiya, lafiya kuwa? Kamar dai baƙuwa ke ba! Me yasa ki shigo gidan mutane haka kina ɗaga murya kamar a kasuwa?”
Ammy ta harari Inna tare da faɗin.
“Ba magana nake da ke ba, tsohuwa! Ke dai kin iya boye ‘yar marainiya a nan, to indai kinada hankali, ki gaya mata ta bar ɗana, kar na manta asalin ta…”
Ta kalli Amal da ɗan murmushin raini.
“Kin ji ni ko, yar talakawa, jikar matalauta! Indai kinada zuciya to ki fita daga rayuwar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 36 Chapter of 62