Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Amal? Ai wannan... akwai ƙalubale a cikin sa in har zaki fara zuwa garuruwa ke ba ƴar kowa ba, amma idan da gaske ne kuma halal ne Allah ya buɗa miki.” Amal ta riƙe hannun Inna da murmushin dole ta ce: “Inna, wallahi ban san ko me yasa mutane ke bani kulawa haka ba... amma dole ne idan kana irin wannan aiki, ka sa rai da farin ciki yana iya janyo kishi da ƙiyayya.” ♡♡♡ ♡♡ ♡ Maleekh yana duba social media sai poster ya bayyana a fuskar laptop ɗinsa an rubuta: “Coming Up: AMAL ABDULSAMAAD The Voice Behind Kaduna’s Radio Gold, Live on Nigerian Voices Podcast with Rikky Blaze!” Maleekh ya tsayar da numfashi, a cikin ransa yake faɗin: “So... she’s really trending now? Abuja? Seriously? wannan ƴar talakawan yarinya ta kai wannan mataki? Nigeria really is upside down, but let’s see... let’s see how far she can go.” Ya janyo wayarsa tare da ƙiran ɗaya daga cikin abokan cinikinsa a Abuja... yana shirin tura mutum don ganawa da Rikky Blaze... ♡♡♡ ♡♡ ♡ AMAL A AIRPORT ZUWA ABUJA Amal na sanye da doguwar riga da ƴar hijabin ta marar nauyi tana lanƙaye da jakar ta, Mutane da dama na kallonta a harabar jirgi suna murmushi. Yaran wasu ma na cewa: “Mama kinga Aunty Amal ta cikin rediyo!” Amal ta ce a zuciyarta “Duniya kenan... tun da na fara aiki a ƙaramin gidan rediyo, ban taɓa tunanin har podcast na ƙasa zai gayyace ni ba, amma wallahi zan tsaya akan gaskiya, ba zan canza wa kaina ba.” Wasu zafafan motoci ne suka zo ɗaukan ta, kai tsaye babban hotel na masu kuɗi aka kaita, yanda aka tanadar mata da komai... Bayan ta ci ta sha tayi wanka tare da tsayar da sallah ta huta cikin kwanciyar hankali har bacci ya ɗauke ta, ga sanyin A.C na ratsa ta kamar ba'a duniya take ba, ita kanta tasan ta shigo duniyar masu kuɗi, Washegari da safe ta kammala shirin ta tsaff, already motar na jiran ta a compound na hotel zasu je wurin da za'a gudanar da shiri.... THE NIGERIAN VOICES PODCAST" Amal ta tsaya a gaban duniya, domin a wurare da dama ana kallon tattaunawar da zasu gudanar... Abuja, babban studio na Rikky Blaze. Amal na zaune a gaban mics guda biyu, sanye take da rigar abaya da gyalenta marar nauyi, Rikky ya zuba mata ido cikin girmamawa yana murmushi, gyaran murya ya yi tare da faɗin “Ladies and gentlemen, today we have with us a very special guest, she may not have a mansion, or billions in her bank account, but her voice has broken down walls and reached the souls of thousands. Amal Abdulsamaad welcome to Nigerian Voices.” Amal cikin nutsuwa ta furta: “Thank you very much, Mr. Blaze, It’s an honour to be here. And I speak not with power, but with pain because pain is universal.” Rikky ya gyara zama sannan Ya ce: "Akwai lokacin da kika ce, "Idan har ya zama dole ne sai ka cutar da wani, to kar ya zamana ka cutar da wanda ya taɓa ƙaunarka’ wannan magana ta bazu sosai a duniya.... Daga ina kika samo ta?" Amal ta ɗan gyara zamanta, ta kalli mic cikin sassanyar murya ta ce: "Na samo ta ne daga ganin mutanen da suke shan wahala a asirance, na taɓa yin hira da wata yarinya da aka kashe mijinta saboda ya kare ta daga ‘yan ƙungiyar asiri, ba ta kai wa kowa kukan ta ba… sai dai kawai ta zuba ido, kuma hakan ya karya zuciyata. Ba kowace zafi ke yin ihu ba, Malam Blaze… wasu dai suna nan kawai… suna jiran a ji yo kukan su...." Wannan maganar ta saka ɗakin yin shiru, har cameraman ya tsaya yana kallon ta. Rikky cikin nutsuwa Ya ce: “You don’t speak, you cut. But in a good way like surgery.” Amal ta murmusa kaɗan, idanunta sun kaɗa da ƙwalla, tayi gaggawar kawar da kai ta tsaya cikin ƙarfin hali. Ta ce: “I’ve seen people mock the poor... I’ve seen people say, your background is your curse But wallahi, Mafi ƙarfafa mutane da na taɓa haɗuwa da su, su ne waɗanda ba su da wani ginshiƙi sai Allah kaɗai, kuma ina magana ne a madadinsu.” ♡♡♡ ♡♡ ♡ Maleekh na zaune kan sofa, yana kallon wani big screen, amma ba podcast ba yana duba data a kasuwancin sa. A gefe guda kuma laptop ɗinsa na nuna thumbnail ɗin Amal a podcast amma bashi da lokacin duba ta... Maleekh yana maganar zuci.. “Tunanin ta ya isa haka, i don’t need this noise, there are millions like her why should i care?” ɗaukan remote ya yi yana shirin kashe screen ɗin gaba ɗaya, amma kafin ya kashe, yana ganin Amal cikin nutsuwa tana faɗin “Muna tashi ne ta hanyar ɗaga waɗanda ke ƙasa da mu…” Maleekh jan tsaki ya yi yana faɗin: “Ƴar talakawa kawai, ƙaramin abu ya dameta, kuma yanzu kowa na wahalar da kai wurin sauraron maganarta.” Ya ɗauki wayarsa ya ƙira PA ɗinsa, bugu ɗaya aka ɗauka, Maleekh Ya ce: “Tell Alhaji Dikko in Abuja he should handle that oil deal directly. And tell him to stop this social media buzz about any radio girl. I’m not interested.” Recording Amal da Rikky ya janyo tasiri har zuwa duniyar siyasa, sannan wata kafar TV ta Abuja tana neman ta zama host ɗinta, lamarin da ya tayar da hankali a RAYUWA FM. 🌍🎙️ A cikin maganganunta ta sako har da ƴan siyasa, duk wata gaskiyan da suke ɓoyewa tana shirin binciko wa, tana ƙaryata maganganun su akan talakawa na cewa zasu taimake su nan kuma cin amana ne da kuma yaudara, truth out maganganun ta akan siyasa ta yi su, kuma ta ba da isasshen lokaci..... THE ECHO OF TRUTH” LABARIN AMAL YA GIRGIZA MANYA A babban ofishin wani ɗan siyasa da ake zargi da cin hanci a Abuja, TV yana nuna podcast ɗin Rikky Blaze tare da Amal, wani babban hadimi yana kallon boss ɗinsa da fargaba Ya ce: “Sir… ina ganin wannan yarinyar za ta zama matsala, ta ambaci matsalar ƙarancin ruwa, har da adadin alkaluman da ka umarce ni in ɓoye.” Ɗan siyasan ya miƙe da sauri yana kaɗa hannu cikin zafin zuciya Ya ce: “Who gave her that data? Ta yaya ƴar gidan rediyo ta Kaduna ke da wannan cikakken bayani? Shut it down! Cancel the links, do damage control! I don’t want her voice on the internet again!” Hadimi Ya ce: “But sir... it’s already viral. The clip is trending on Twitter, YouTube, even BBC Africa quoted her...” Ɗan siyasan ya ɗaga hannu cikin tsawa yana faɗin: “To hell with BBC! If we don’t silence her now, she’ll open more cans we thought were buried, find out who trained her. And who she works for.”... Abuja TV Headquarters Bayan kwana biyu.. A cikin babban ɗakin taro da aka yi wa ado da fatauci da na’urorin zamani, Amal zaune ce a gaban babban kwamiti na Abuja TV. A gabanta akwai wata fitacciyar producer, Madam Ebun, mace mai lallausar murya da kuma cike da dabara. Madam Ebun cikin murmushi Ta ce: “Amal, your voice touches the soul, we are impressed, but on national TV, we don’t just speak we control narratives.” Amal ta ɗaure fuska tare da faɗin: “I control only the truth. Nothing more.” Wani daga cikin committee ya kalli wata takarda sannan Ya ce: “Kin ce Ministan Muhalli ya yi amfani da kuɗin ruwa wajen abin da bai dace ba, wannan magana ta yi haɗari da yawa, kin ƙira hakan cin amana ga yaran da ke cikin jin ƙishirwa, idan muka ɗauke ki aiki, muna son kauce wa maimaita irin wannan magana kai tsaye a fili.” Amal ta lumshe ido cikin nutsuwa Ta ce: “Abin da na faɗa ya fito ne daga rahoton da tashar ku ta yi watsi da shi If you’re scared of truth, then I’m not your girl.” Ɗakin yayi shiru kamar ba mutane. Amal ta miƙe, ta ɗauki jakarta tana shirin barin wajen, amma wani daga cikin Committee Member Ya ce: “Wait. Kina da jarumta, amma ki sani ƙin amincewa da mu yana nufin yanzu kin zama abin bibiya. ’Yan siyasa sun san sunanki yanzu. Ki yi hattara.” Amal Ta ce: “They should be careful too. I have a microphone.” ♡♡ ♡ England, Maleekh's Private Apartment Maleekh yana zaune a gaban babban taga yana kallon gari da motocin dake wuce wa, hannunsa na cikin gashinsa yana murɗawa cikin takaici, ya koma ya zauna kamar marar lafiya. A gefensa laptop na nuna headline: “Kaduna Girl With Radio Courage Lands Abuja TV Offer” Yayi tsaki, ya tura laptop ɗin gefe, ya miƙe yana shawagi cikin ɗakin da kayan alatu ke ko’ina, yana lumshe da idon da ke bayyana karfin hali da ƙiyayya. Maleekh yana zancen zuci yana faɗin : “Ajin me? Yarinyar da bata da kafa da tuta a rayuwa tana ƙoƙarin taka manya? wane irin raini ne wannan?” Ya ɗauki waya ya ƙira wani ɗan sanda dake aiki a Abuja. Maleekh Ya ce: “I need someone to pull her files, i don’t trust that girl, i want to know who is backing her or if she’s just another loud mouth.” Muryar ɗan sandan ne ya fito yana faɗin: “Sir, you want us to tail her?” Maleekh Ya ce: “No... Not yet. Let her shine small. But if she crosses me again, i will remind her that power... is not in the mic. It's in money.” Ya kashe wayar yana fitar da numfashi, amma wata kalma daga bakin Amal tana yawo a kunnen sa: “Gaskiya ba ta da albashi, amma tana biya da gadon suna bayan barinka duniya....” Maleekh ya ƙara jan tsaki yana faɗin: “Tsk! Yar talakawa da poetry…” ♡♡♡ Rayuwa FM, Kaduna... Amal ta dawo daga Abuja da takardun offer da ta samu, Babban producer tasharsu, Mr. Salis, ya ƙira ta ofishinsa. Amal bayan ta huta gajiyar ta a gida duk da jirgi ta shiga, daga baya ta amsa ƙiran Ogan ta dake gidan rediyo Rayuwa FM.. Gidan rediyo na RAYUWA FM, Amal na shigowa, fuskarta ɗauke da fara'a, tare da karfin zuciya. Babban editan tashar yana tsaye yana taya ta murnar dawowa.. Editor yana ƙoƙarin bayyanar da murmushin sa Ya ce: “Amal... welcome back. Yayi kyau. Amma akwai batun da zamu tattauna da gaggawa.” Amal ta tsaya, tana dubansa kai tsaye Ta ce: “Na san me kake nufi. Abuja TV sun aiko mun da offer. They want me to be their national youth host for a new program. They want truth and i have it.” Editor ya ɗan dafe goshinsa sannan Ya ce: “But this is RAYUWA FM, Amal. We trained you. We gave you the mic. Ba za mu iya kallon ki kina tafiye tafiye ba... and Abuja TV na da sauƙin sayar da ra’ayi you’ll be controlled.” Amal Ta ce: “But wallahi a nan ma ana ƙoƙarin dakatar da ni, i speak for the people ba wai domin na yi suna bane, Idan rayuwa zata zama cin hanci da gori, to ba zan ci albashi dubu ashirin haka nan ba...” Shiru ya biyo baya kamar an kunna recorder a zuciyar kowanne ma’aikaci. Amal ta bar wurin kai tsaye ofishin Mr Salis ta nufa daman shi ke neman ta, haka ta shiga office ba tare da jin komai ba, a zuciyarta tana tunani tare da maganar zuci: “If they want to fight me for speaking truth, I’ll still speak. One mic. One voice. Millions of hearts.” Murya cike da damuwa. Mr. Salis Ya ce: “Amal, muna farin ciki da irin cigaban ki. Amma… idan kika karɓi wannan offer, za ki fice daga Rayuwa FM ne....” Amal ta kalle shi kai tsaye tare da faɗin: “Na zata zaku yi alfahari da ni, ba ku ja ni ƙasa ba.” Mr. Salis Ya ce: “Wannan ba batun kishi bane, batun tsari ne. Gidan rediyo yana da policy idan an same ki da wata kafa na waje, sai an cire ki daga jerin ma’aikatan nan...” Amal cikin takaici ta furta: “To ni wallahi idan akwai inda zan iya faɗin gaskiya ba tare da an tsoratar da sunan gwamnati ba ni can zani.” Ta miƙe ta bar ofishin, a bakin ƙofa ma’aikata da yawa suna kallonta da mamaki da tausayawa, wasu na ta cewa “kada ki tafi Amal, kin fi ƙarfin Abuja TV su rufe ki da dokokin su...” Amma Amal bata tsaya ba. A zuciyarta murya ɗaya take faɗi: “Mic ɗina ba mallakin ku bane. Na talakawa ne.” Amal ta dawo gida daga aiki, fuskarta cike da gajiya da damuwa, bata tsaya ko'ina ba sai a ɗakin Inna, a zaune Inna take akan tabarma tana tsane ganye, Idonta ya sauƙa akan Amal da take ƙoƙarin boye damuwarta. Inna ta ɗaga ido cikin tausayawa Ta ce: “Amal, zo ki zauna mana, ki zauna nan gaban Inna, yau zaki saurari shawara, ko ba haka ba?” Amal ta zauna a gefen Inna kamar wata yarinya da aka kama da laifi, ta ɗaura hannu biyu a cinya, idanunta sun kaɗa da kwalla... Inna Ta ce: “Amal, ki dubi maraicinki ki zauna kiyi haƙuri, ki tuna ke ƴar talakawa ce, karki manta da asalinki, wannan Abuja da kike shirin komawa, meye a cikinta? Siyasa? Kuɗi? Ko alfahari?” Amal ta kalli Inna tana share hawaye, amma bata iya cewa komai ba. Inna ta cigaba da faɗin: “Masu kuɗi sun fi ki iko, a lokacin da kike haskawa, kowa zai dinga ƙiran sunanki, amma idan kika faɗi ƙasi wallahi babu wanda zai tsaya miki, su masu mulki sai sun ɓata miki suna, su wulakanta ki, su jefar da ke kamar marar daraja, bayan ke kaɗai kika rage mun, idan kika tafi Abuja, wa zai dinga kula da ni?” Amal ta fashe da kuka tana faɗin: “Inna...idan har bakya son na koma Abuja...zan haƙura. Wallahi zan zauna dake, zan ci gaba da aiki a Rayuwa FM.” Inna ta janyo Amal ta rungume ta tana share mata hawaye. Inna Ta ce: “Allah ya miki albarka, wallahi ban hanaki ci gaba da rayuwa ba, amma bana son ki afka cikin tarkon siyasa da haɗin kai da masu kuɗi, ki dage akan ilimi da gaskiya nan ma za’a gan ki.” RAYUWA FM.... Bayan kwana biyu Amal ta koma tashar Rayuwa FM da murmushi a fuska, kowa ya nuna farin ciki da dawowarta, shirin ta na yau ya kasance mai taken: “Kaunace ko Wulaƙanci?” Amal ta shiga studio cikin kwanciyar hankali, ta ajiye headset ɗinta, sannan ta fara magana cikin tausasawa: “Assalamu Alaikum wa rahmatullah masu sauraro na Rayuwa FM. Ina tare da ku ni ce Amal Abdulsamaad. A yau zan ɗan ba ku labari mai raɗaɗi labarin soyayya da ƙyama...” Ta ɗan yi shiru, tana murza idonta da tissue, muryarta na ɗan karyewa. Ta cigaba da cewa: “Wani saurayi da budurwa ɗalibai sun shafe shekaru uku cikin soyayya mai tsafta, basu da komai sai soyayya da girmama juna. Amma wata rana...an tarar da gawar su a cikin motarsu...an harbe su.” Daga nan muryarta ta shiga rawa sosai. Ta cigaba akan cewa: “Wai meyasa ƙiyayya take cin nasara akan soyayya? meyasa mutane basa jin zafin rasa wanda suke so? wannan duniya fa babu tabbas…” Idon Amal ya cika da kwalla, amma har yanzu kalmominta na fita cikin turanci mai hikima. Tana faɗin: “Matasa ne, talakawa, amma al’umma ta hana su damar rayuwa. Saboda kawai ba su da suna, ba su da kuɗi, ba su da iko… an kashe muryarsu.” Amal cikin kuka Ta ce: "May Allah grant them peace. Ameen." A lokacin da take magana, a can nesa a England, Maleekh na kwance kan gadon sa, yana sanye da 3quarter a jikinsa da singlet, laptop ɗinsa na nuna live stream na Rayuwa FM. ya harari screen ɗin yana tura keyboard da karfi. Ya ce: “Damn it! wannan yarinyar har yanzu tana da baki? ta ɗauki kanta kamar wacce tasan komai... Ƴar talakawa ke baƙin ciki da soyayya...” Yana buɗe wata folder a laptop ɗinsa wanda yake ɗauke da sunan: "CASH TALK FM PRIVATE." Maleekh yana murtuƙe fuska yana faɗin: “Zan janye ta daga Rayuwa FM... by force or by money... She will work for me. She must!” Sai ya ɗaga waya ya ƙira wani hadiminsa daga Abuja. Maleekh Ya ce “Hello!...Prepare the contract, i want Amal Abdulsamaad. She'll join us at CashTalk FM. Abuja is waiting...” Bayan Amal ta ci gaba da aikinta a Rayuwa FM, koda yake tana ƙunshe da damuwa a ranta sakamakon matsin lambar siyasa da kuma saƙonnin barazana da ake aiko mata daga Abuja TV. Duk da haka, ta cigaba da shigowa cikin shirye-shiryenta cikin ƙwazo, musamman shirin “Ra’ayinka Hakkinka” inda take ba mutane dama su bayyana damuwarsu game da rayuwa da halin ƙasar. Sai dai, bayan kowanne shiri, Amal ta fi zama shiru a cikin office. A zuciyarta tana jin kamar tana yaƙi ne da manyan da ke son murƙushe ta, amma shawarwarin Inna kullum su ke kwantar mata da hankali: "Ki tsaya da ƙafafunki, Amal. Talaka baya rasa daraja idan har yana da gaskiya da himma." A Ƙasashen Waje A can England, Maleekh Cashbank ya gama tsara duk wata hanya da zai jawo Amal zuwa sabuwar tashar sa, CashTalk FM. Amma ba don yana sha’awar ta ba, A'a, yana so ne ya mallake ta da kuɗi, ya ɗorata a ƙarƙashin ikonsa, domin ta yi masa mummunan rauni a gaban duniya. Yana zaune cikin ɗakin sa na musamman, yana duba zafafan shirye-shiryen Amal da ke ta yawo a social media, yana wani tsaki da cizon yatsa. Kallonsa ya koma sama, ya furta: "Ƴar talakawa ce fa! Me yasa nake jin kamar maganganunta suna shiga jikina? wannan wulakancin da ta min ta rediyo sai na rama shi a duniya." Ya buga laptop ɗinsa da ƙarfin zuciya, yana ƙara hura hayaƙin shisha... Location: Kaduna... Amal ta samu wani ƙira daga wata baƙuwar lamba a cikin mako, tana ɗagawa sai wata murya ta ce: "Miss Amal, muna so mu tattauna da ke akan wata sabuwar dama a tashar rediyo, muna neman fitattun muryoyi masu rinjayar jama’a." Amal Ta ce: “Waye ke magana? Kuma wace tasha ce?” Other site: “Zaki ji komai idan kika zo Abuja, muna fatan zaki ɗauki wannan damar da gaske.” Amal ta amsa cikin ladabi amma a zuciyarta ta ƙuduri aniyar ba zata sake barin Rayuwa FM ba.... ★★★ Maleekh ya aika da tawagarsa ta PR su je Kaduna a asirance domin su fara tattara duk wata dama da zata iya kawo Amal zuwa CashTalk FM. Ba don yana buƙatar taimakonta ba, sai don ya wulakanta ta ya nuna mata duk ilimin ta da basirar ta ba zasu hana shi murɗa ta ba...... NEXT TARGET 🎯🎯 READERS INASON JIN DAGA BAKIN KU, A CIKIN AMAL DA MALEEKH WAYE KUKE SON JIN SCENE ƊINSA?.... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 5 to 6 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 ___________________________________________ Kaduna Gidan rediyon Rayuwa FM Amal ta dawo cikin ayyukanta amma a bayyane take cewa "An fara sanyaya yanayin da nake ciki..." Daga ranar da ta gabatar da shirin da ya fallasa yanda wasu ‘yan siyasa ke yin amfani da talakawa don cimma burinsu, wasu na jin tsoro, wasu na jin karayar zuci amma Amal bata tsaya biye wannan ba. A bayanin ta a gidan rediyo Tana cewa: “Ku sani, talaka ba ƙaramin abu bane, kada ku yarda a rinƙa amfani da ku a lokacin zaɓe, sannan a watsar da ku bayan an ci zaɓe, Kuyi hankali da waɗanda ke muku alƙawuran ƙarya. Ku tambayi kanku: ina ƴan takara suke bayan zaɓe?” Wannan magana ta yaɗu sosai, har aka ɗora ta a TikTok da X (Twitter), inda mutane suka rinƙa cewa: “Amal ce muryar gaskiya!” “Allah ya kare ki Amal, daga sharrin masu sharri...!” Amma akwai wasu da hakan bai yi wa daɗi ba. Bayan kwana biyu Wata rana, Amal na tsaka da shiri a ofis ɗin Rayuwa FM, sai aka kawo mata wata leda mai ɗauke da kwali. A ciki akwai envelope guda ɗaya, a jiki aka rubuta: "Ki yi shiru kafin a rufe miki baki da ƙarfi." Cikin takardar, akwai hotunan Amal tana fita daga gidan rediyo da kuma wasu bayanai da ke bayyana cewa ana bin sawunta. A ƙarshe akwai kalmar da taji wanda ya sanyaya mata zuciya: “Mu muna da ikon gyara muryarki kar ta mutu.” Amal ta daɗe tana kallon takardar. Hankalinta ya tashi, amma ta daɗe kafin ta nuna damuwa a fili. A zuciyarta, tana addu’a kawai. A bakin ta kuwa murmushin ƙarfin hali take tare da faɗin: “Toh su sani zan cigaba da faɗan gaskiya. Idan zasu kashe ni, to su fara kashe gaskiya gaba ɗaya kafin nan...” Bayan Amal ta dawo gida da dare, tana zaune a ƙasan tabarma gaban Inna tana ta ƙarewa letter barazana da kallo. Inna na kallon fuskarta, cikin damuwa ta ce: “Ki daina gaya musu gaskiya cikin ƙarfin murya haka Amal. Ki tausaya mana. Me zamu ce idan wani abu ya same ki? Gaskiya gaskiya ce, amma a Nigeria gaskiya tana buƙatar wayo.” Amal ta share hawayenta. Ta ce: “Inna, idan muka yi shiru, su waye zasu kare talakawa? Idan ba ni ba, wa zai faɗi makircinsu? Su sun daɗe suna rura wuta, yanzu lokaci yayi da za’a haska gaskiya.” A can Abuja, wasu manyan mutane sun fara tattauna yanda zasu “rufe bakin Amal” ta hanyar amfani da hukumar da ke kula da watsa labarai National Broadcast Control Commission. Sun nemi hukumar ta dakatar da Amal daga gabatar da shirye-shirye saboda "kalaman tada zaune tsaye". A yau an samu wata jarida da ta fara ɓata sunanta da wasu rubuce-rubuce marasa tushe, suna cewa: “tana tada zaune tsaye ne saboda tana neman suna daga ƙungiyoyin waje.” Duk da waɗannan matsaloli, Amal ta koma rediyo da safiya take cewa cikin murya mai ƙarfi: “Wanda ke tsoron gaskiya shi ke son murɗe ta. Amma ku sani, mutuwar muryata ba zata rufe gaskiyar da ta fita daga bakina ba. Idan Allah Ya so, rayuwarmu zata canza.” A lokacin da take faɗar hakan, Maleekh yana duba ta daga laptop ɗinsa a England, kifa kansa ya yi a kan tebur yana furta: “Wannan yarinyar ba ta tsoro? me yasa na kasa kawar da tunaninta a raina?” Tsaya wa ya yi tare da wani ɗan nazari daga baya ya ɗauki wayarsa tare da ƙiran wani Manager campanyn sa a Nigeria garin Kaduna, kamfanin gudanar da kasuwancin chanjin kuɗaɗe daga Dala zuwa Naira da kuma kamfanin tace finafinai da shooting, sunan kamfanin sa CASHBANK hakan yasa ake ƙiran sa da suna Maleekh cashbank, asalin haifaffen garin Kaduna ne iyayensa suka koma Abuja amma akwai sauran family a Kaduna, Bayan ya ƙira Manager bugu ɗaya aka ɗauki ƙiran, Manager ne ya fara faɗin: "Hello Sir! Barka da wannan lokaci...." Maleekh cikin izzah yana yamutsa fuska Ya ce: "Campany na! komai yana tafiya normal?..." Manager Ya ce: "Komai normal Ogah, ana tafiyar da komai yanda ya kamata, sannan ana samun ƙaruwa sosai...." Maleekh Ya ce: "Good! Gobe da safe zan shigo Kaduna, inaso zan ziyarci gidan rediyo Rayuwa FM, sannan zan zauna na ɗan wani lokaci domin gudanar da aiki a kamfani na...." Manager Ya ce: "Haba Ogah ka rasa ina zaka kai ziyara sai a wannan ƙaramin gidan rediyo? ga manya-manyan gidan rediyo masu capacity....." Kafin manager ya ƙarasa maganar Maleekh ya katse shi da cewa "Nan nayi niyyar zuwa...zan sauƙa a gidana na GRA a mun gyara na musamman...." Manager Ya ce: "Okay Sir...." Daga nan suka yanke wayan... Maleekh ya sa a karɓa masa tikiti domin a yau zai bar England, yana so zai sauƙa a Abuja domin gaishe da iyayensa, idan ya kwana da safe sai ya wuce Kaduna..... Bayan Awanni

Chapter 2 of 62