Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yarinya nasan idonta na sauƙa akan kuɗin nan zata iya karɓa ta mayar masa, ita da baza'ayi abun alheri da ita ba...." Amal tana zaune a bakin katifa sai mulmula wurin da Inna ta cije ta take, amma hankalin ta na kan Maleekh, ba wai tayi haka don saboda bata sonsa ba, tayi ne saboda ta ja masa aji sannan yana kan gwajin ta ne, in har zai iya jure duk wulancin da zata masa na tsawon wata watanni to zata amince da soyayyarsa, amma in har ya kasa, ya nuna mata zuciya sannan ya daina zuwa yanda take to itama zata sharar da shi, wannan shine gwajin.... Murmushi tasau marar fassara sannan ta kwanta a saman katifa tana kallon ceiling.... A bangaren Maleekh kuwa ya koma GRA unguwar da yake zaune anan Kaduna, yana zaune akan sopa idonsa akan plasman amma hankalinsa na kan Amal, yana tunanin ta yanda zai ja wo hankalinta kansa, ta kamu da matsanancin son sa... A fili ya furta "Amal bazan bari ki sha ba, zan ci gaba da naci har sai kin kamu da soyayyata, bazan taɓa yin ƙasa a gwiwa ba, sai kin so ni, domin babu macen da zan furta soyayya akan ta tayi rejected ɗina, ƴan mata da yawa su suke neman soyayya ta, ban taɓa furta kalmar soyayya akan wata ƴan mace ba, sai akan Amal sannan ta wulakanta ni? wani irin zuciya ne da ita na ƙashi? but I will try my best..." Bayan kwana biyu Maleekh ne ya ziyarci gidan ƴar uwarsa ƙawar Amal wato A'isha... A'isha tayi farin cikin ganin Yayanta Maleekh a gidanta. Ta haɗa masa kayan ciye-ciye da kayan fruits, sun juma suna wasa da dariya kafin daga bisani Maleekh ya yi gyaran murya... Yana kallon A'isha ya ce "Bayan ziyara akwai wani abu mai muhimmanci da ya kawo ni wurin ki..." *NEXT...* asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 15 to 16 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 A'isha ta ƙafe idonta akan Maleekh cike da mamaki ta ce "Ehen! Ina sauraron ka Yaya..." Sai da ya sauƙe numfashi kafin ya ce "maganar akan Amal ne, inaso ki mun wani taimako..." A'isha ta ce "Amal kuma? meya faru?..." Maleekh yana lumshe sexy eyes kamar mai jin bacci ya ce "na kamu da matsanancin ƙaunar ta, amma ita sam ta ƙi yarda da ni, shiyasa nake so ki taya ni kamfe..." A'isha zaro ido tayi lokaci guda ta saki dariya tare da faɗin "Yau kuma Yaya Maleekh ne mai neman kamfe akan mace? very surprised 😮, but abin da nake son sani shine, a lokacin party bikina Amal kamar ta nuna tana supporting ɗin ka why now?..." Maleekh ya sau murmushi shi kaɗai yasan abinda yake shiryawa a ransa, shi kaɗai yasan irin tarkon da yake ɗana wa Amal, amma ya basar yana nuna wa A'isha cewa "Da gaske nake son Amal, ta nuna ba komai a gaban mutane but yanzu tana mun kallon biri I don't know why..." Aisha ta ce "shikenan Yayana ina supporting ɗinka sosai kuma zan yi farin ciki idan soyayyar ku ta 'kullu, insha Allahu zan je gidan su Amal, zan same ta da maganar amma da sharaɗi Yaya..." Maleekh ya jinjina kai sannan ya ce "meye sharaɗin?..." A'isha ta ce "kasan yanda nake ji da Amal, bana son wani abu ya same ta, ka riƙe mun ita da amana, kada ka cutar mun da ita, but wallahi idan kayi broken heart ɗin ta, uhmmm bazan yafe ba Yaya, duk da ka kasance ɗan uwana na jini..." Murmushin gefen baki Maleekh ya yi tare da nuna yardar sa amma a cikin zuciyarsa cewa yake... "Tafiya ɗaya ne da yaro mai ji da kansa, maganin irin su Amal broken heart, anan zasu gane cewa da ruwa ake shayi..." Anan suka yi sallama Maleekh ya yi tafiyarsa... Da daddare misalin ƙarfe 9 Amal tana kwance sai ji tayi wayarta na ringing.. Ɗago wayar tayi tana duban number, ganin sunan da ya bayyana akan Screen ɗin wayar ne yasa zuciyarta bugawa, (Amaleekh) sunan da ya bayyana kenan, murmushi tasau tana riƙe da wayar tana jiran ƙiran ya yanke sai ana biyu ta ɗauka domin tasan nacin sa bazai daina ƙira ba har saita ɗaga... Ƙira na biyu ne ya sake shigo wa nan ma sai da ta kusan yanke wa kafin ta ɗauka tare da karawa a kunne, lumshe golden eyes ɗinta tayi tana jiran sauƙar zazzakar muryarsa... Shima daga can ɓangarensa yana kwance akan katafaren gadonsa, a hankali ya furta "Amincin Allah ya tabbata a gareki sarauniyar kyawawan halittu..." Wani irin farin ciki taji ya ziyarci zuciyarta, sai da ta daidaita kanta tukun cikin rashin mutunci ta ce "Waye akan layi?..." Maleekh ya yi murmushi sannan ya ce "kin manta ba'a gidan rediyo kike ba fa..." Ta ja dogon tsaki sannan ta ce "wai kai wani irin nacaccen mutum ne? wai sau nawa kake so na sanar maka cewa ka fita daga cikin rayuwata? i hate you..." Maleekh ya danne zuciyarsa saboda a rayuwarsa mace bata taɓa tsayawa a gabansa tana gaya masa maganganu haka ba, har ma tace ta tsane shi... Cikin sassanyar murya ya ce "kiyi haƙuri, ba yanda na iya ne, nacin zuciyata akan soyayyarki na so yafi ƙarfin kwakwalwa ta Amal, ki tausaya mun mana..." Cikin fusata ta ce "ka ga malam dakata, da can meyasa ka zamo abokin gaba ta? sai yanzu zaka dawo mun wai soyayya? shin kana cikin hankalinka kuwa? anya baka shaye-shaye? ko dan kana shan shisha ba abinda baza kayi ba, in ance kwakwalwarka ma ta juye ba laifi, gargad'i na ƙarshe kada ka sake ƙiran wayata..." Daga nan ta ƙatsar da ƙiran sannan ta ɗora wayar akan ƙirjinta tana sakin kayataccen murmushi... A hankali ta furta "tafiya ɗaya ne ga yaro mai ji da kansa, wannan girman kan naka saina sauƙe maka shi akan titi Maleekh, rashin mutuncin da ka daɗe kana shukawa yanzu ne daidain girbe wa..." A ɓangaren Maleekh kuwa bayan katsar da waya a take yayi wurgi da wayarsa sai a jikin bangon ɗakin, nan wayarsa ƙirar IPhone 50pro ya tawarwatse, bai shigo Nigeria ba tukun 🙄.. A ruɗe yake faɗin "Ni ne mahaukaci? ni ne nake shaye-shaye? Innalillahi yau mace ce take ƙira na da mahaukaci?..." Nan ya fara wurgi da pilillikan gadon, ya sauƙo yana dukan jikin bango da ƙarfi, wani irin ihu yake na baƙin ciki da tsantsar tsanar Amal, wani irin naushi ya kai wa mirror ɗakin, nan take ya tawarwatse, ya dun'kule hannunsa yana nausar jikin bango tare da furta. "Sai na kashe ki Amal! sai na juya rayuwarki Amal!! sai na ja kanki a tsakiyar titi Amal, na tsane ki Amal, nine mahaukaci? zan nuna miki ni cikakken mahaukaci ne wanda zaiyi raga-raga da rayuwar ki, ƴar matsiyata, ƴar talakawa, ƴar shegiya ..." Da gudu PA ya shigo jin ihun Maleekh, zuwa yayi ya riƙe shi sosai yana ƙoƙarin rungume shi, domin dukan bangon da yake yi yasa hannunsa ya farfashe, ga hannu kalar na hutu bai taɓa ɗaukan abu mai wahala ba, fashewar hannun abu ne mai sauƙi... Da ƙyar PA ya samu damar zaunar da shi a bakin gado yana rarrashinsa.. Maleekh yana huci ya ce "Ta ƙira ni da mahaukaci, sannan ta ƙira ni da mai shaye-shaye, shin wani irin hukunci zan mata ne wanda zai sa na huce? idan ban kashe ta na daina ganinta a duniya ba bana tunanin zan huce..." PA yana bashi haƙuri ya ce "Boss yanzu kana cikin raɗaɗin zuciya, komai ma zaka iya faɗa, idan kanaso ka cimma burinka to ka zama mutum mai juriya, ka daure ka ɗauki duk wasu kalamanta na 6atanci amma kasa a ranka akwai ranar da zata biya, biya mai tsoka, yanzu ka fara tunanin jawo hankalinta kanka, ka rinjayi zuciyarta sannan sai lissafi ya tafi dai-dai, zamu koya mata darasin da ba'a koya mata a school ba, tin da har tasa Boss ɗina ya zubda hawaye to saita biya..." Maleekh jin PA yace ya zubda hawaye ne yasa ya miƙe a ruɗe yana goge hawayen fuskarsa tare da faɗin. "Akan me zan zubda hawaye akan wannan ƙasƙantacciyar yarinya marar class, ƴar talakawa fa'kiriya irin ta, god forbid hawaye na bazasu taɓa zuba akanta ba, tayi kaɗan wallahi..." Da ƙyar PA ya rarrashi Boss ɗinsa....sannan ya ɗauko boxing na magani, yazo ya yi treats ɗin hannunsa da yaji ciwo.... 《☆Bayan kwana biyu☆》 Amal na zaune akan tabarma tana rubutu a wani takarda, sai ga sallamar A'isha, ɗago kai Amal tayi, ganin A'isha yasa ta miƙe ta ruga da gudu ta rungumeta cikin farin ciki take faɗin "Yau Amarya ce a gidan mu? yaushe ma akayi Auren har zaki fara fita yawo?..." A'isha ta ce "ai ke kika fito da ni..." Amal ta ce "ni kuma? taya kenan?.." A'isha ta ce "ta hanyar cutar mun da zuciyar ɗan uwana mana, yana can zai hallaka kansa saboda tunanin ki da damuwar da ya ɗaura wa kansa saboda ke..." Amal tsummm tayi tana kallon A'isha daga bisani ta ja hannunta suka ƙarasa ciki, Amal ce ta leƙa ɗakin Inna tana faɗin "Inna A'isha tazo..." Amal idonta ne ya sauƙa akan kifi baje-baje a gaban Inna sai turawa take tayi... Amal cike da mamaki ta ce "Inna aina kika samu kuɗi har da siyan kifi har haka?..." Inna ta ce "A gidan uwarki.." ta faɗa daidai lokacin da ta ƙara tura kifi bakinta... Amal ta ce "Inna nasan bakida sisin kobo a gidan nan, kuma ba wani ne yazo ba balle kice anyi miki kyauta ne..." Inna tana harararta ta ce "Wato sai inta zama da bushashshen baki kamar naki koh? Allah ne ya kawo mun buɗi lokaci guda, don haka zanyi amfani da damata ce, ke ki je can ki ƙarata..." Amal ta ce "Inna, in baki gaya mun wanda ya baki kifin nan ba, wallahi bazaki ci ba..." Inna a fusace ta ce "Idan kin hana kin ci gwafar ubanki, Maleeku ne ya bani kuɗi na saya ko zaki karɓe ne?..." Amal ta ce "Maleekh kuma?...ina kuɗin da ya baki?.." Inna ba shiri ta zari taɓarya a gefenta tare da miƙe wa tana huci ta ce "In ban ragargaza miki kai anan ba ki canza mun suna, in kin isa zo ki karɓe kuɗin, saboda mugunta irin naki waton kina mun baƙin cikin kyautar da ake mun koh? Ni in banda Maleeku da naci ban ga abinda ya gani a jikin ki ba, kina wulakanta shi, Allah dai ya karkato kansa kaina cikin kwana biyu zance a ɗaura mana Aure, shashashar yarinya..." A'isha ce ta riƙo hannun Amal tana cewa. "Kin ga Amal zo mu shiga ɗakin nakin..." Sannan A'isha ta kalli Inna ta ce "Inna kiyi hakuri ki ci kifinki ki ƙoshi, duk kyautar da ya miki ki karɓe kar ki zauna da babu, Maleekh halattaccen sana'a yake yi balle ace kuɗin jini ne..." Inna tana huci ta ce "ai ko kuɗin ɗiwa ne saina ci ɗin, kuma tayi magana in fiffige mata nonuwa inyi wurgi da su, ai Maleeku idan yaga babu su tinin zai dawo kaina..." Aisha ta kwashe da dariya har da kama ciki.. Amal tana ji ta ce "A wasu shanyayyun kirji da suka gama shekaru a yanƙwane..." Da gudu Inna ta fito da taɓarya zata rausa mata, ai kuwa itama Amal da gudu ta shige ɗakinta ta rufe, haka Inna take doka taɓarya a ƙasi tana ihun ƙauraye... "Ki fito in kin isa, akan Maliku saina sheme ki a gidan nan..." A'isha ce take bawa Inna haƙuri, ganin Inna ta ƙi sauƙowa ne yasa tayi saurin cewa. "Inna kuliya kifinki, ya shiga ɗakin ki..." Ai da gudu Inna ta shiga ɗakin tana faɗin "Yau na shiga uku ni Delu kifina..." haka take tsinewa kuliya, tana kururuwar kifinta kar kuliya ta cinye mata... A'isha kuwa daman ƙarya take itama da sauri ta tura ƙofar Amal ta shige suka sake rufe wa... Saida suka gama shan dariyarsu mai isarwa a cikin ɗaki, kafin suka dawo dai-dai... Sai da suka huta can suna kwance sai Amal ta taɓo A'isha tana faɗin "Yawwa me kike cewa ne akan Maleekh? kika ce yana cikin damuwa?..." A'isha ta harareta sannan ta ce "ban sani ba, ai nasan kema kina sonsa, shine zaki na wulakanta mun da ɗan uwa, Allah bakida kirki Amal..." Amal ta sauƙe numfashi sannan ta ce "wa ya gaya miki ina son sa? shine dai yake nace mun, ni kuma banida lokacin soyayya da shi..." A'isha ta ce "iyeee a gaban nawa kike cewa bakya son sa? to meyasa a wurin taron bikina kika nuna cewa ba komai..." Amal ta kalleta sannan ta ce "Amma nace inasonsa? Ban faɗa ba, kawai dai banaso na tisgashi a gaban mutane shiyasa na nuna masa goyon baya amma bayan haka babu soyayyarsa a zuciyata kuma ba'a soyayya dole, ki gaya masa cewa bazai samu shiga ba, yayi haƙuri ya nemi wata..." Aisha ta ce "Amal meyasa kika koyi wulakanci ne? Ke fa da bakin ki kike cewa 'mutum yaso mai sonsa, kada ka wulakanta wanda ya furta maka kalmar soyayya..' shin duk ƙarya ne bai je zuci ba, wato kinaso ki ɗora mutane akan hanya ke kuma kina tafe a gefen hanya..." Amal ta ce "nace haka amma ba mutum irin Maleekh ba..." Aisha cikin nuna fushi ta ce "shi meye ne? Meye aibunsa?..." Amal ta ce "Ina tsoron mutum irin Maleekh, duba da irin ƙiyayyar da ya nuna mun a baya...bana son na shiga tarkonsa..." A'isha ta ce "shin baki yadda dashi bane, wani irin soyayya zai nuna miki wanda zaki yadda da shi?..." Amal ta ce "Ya fara fita yaje television ya fuskanci mutane ya tsago kalaman soyayya wa Amal, sannan yayi alƙawarin zai riƙe Amal bisa gaskiya. Idan yaci amana kuwa to amana zata ci shi..." A'isha ta ce "inada tabbaci akan ɗan uwana, saboda tinda yake a rayuwarsa bai taɓa kallon idon mace yace yana sonta ba, sai akanki Amal, idan haka kike so yayi miki zaiyi..." A'isha ta miƙe tana riƙe da jakarta ta ce "ni zan wuce, sai ki fara duba television da sauraron rediyo domin jin ƙarin bayani..." Daga nan Aisha ta tafi, amma bisa alamun ranta ya sosu sosai...itama Amal ta fahimci haka, murmushi kawai tayi tana jinjina kai.... Washegari A'isha ne ta je gidan Maleekh da batun.. Maleekh yana zaune a cikin babban falonsa da ke gidansa, yana kallon fuskar ƙanwarsa A’isha wacce ta zuba mishi ido tana jiran amsar da zata fito daga bakinsa. Ita kanta tana mamakin yanda lamarin ya rikice haka tsakanin Amal da ɗan uwanta. A’isha ta girgiza kai tana cewa: "Yaya Maleekh, ga dai sharaɗi Amal, indai kana sonsa da gaske to dole sai kayi abinda ta umarce ka, domin Amal bata da saurin yadda, tanaso ka bayyana hakan a idon duniya kafin ta amince da kai..." Maleekh ya ɗaga hannunsa yana dariyar da ta nuna ba ya ɗaukar maganar da muhimmanci sosai. Ya ce “A’isha, kin san ni ai. Ban taɓa shiga wasan da ba na da tabbacin nasara. Soyayyar Amal kuwa, wata hanya ce kawai ta nuna ikon da nake da shi a gaban jama’a. Zan fito a tv in faɗa wa duniya cewa ita ce masoyiyata… duk duniya zata gane cewa ni Maleekh, wanda babu mai iya tsayar da shi, na ɗauki ƙaramin abu kamar ita na mai da shi sanadin farin ciki na.” Ya tsaya ya ɗan lumshe ido, sai kuma ya ƙara da cewa a cikin ransa... “Idan na bayyana soyayyarmu a fili, za ta zame min hanyar da zan wulakanta ta, ta yadda duk irin darajar da ta tara a idon mutane zata ruguje. Ni dai kawai ina so in nuna wa duniya cewa babu mace da zata guje ni, komai yanda take da suna ko tsarki.” A’isha ta sau murmushi ba tare da sanin shirin ɗan uwanta ba...ta ce “Inaso ka fahimci cewar yaudarar Amal tamkar kana ci gaba da tunkarar raguwar mutuncinka ne, Yaya Maleekh? Amal ba irin sauran matan nan da zaka taɓa ba ne. Wallahi kana da wuya ka shawo kanta da wannan dabara. Kuma ina jin tsoron wata rana ta juya maka da abinda baka zato, saboda haka inma kanada wata manufa a ranka to kayi gaggawar cire wa....” Maleekh ya saki murmushi mai cike da izza, ya matso kusa da ita, a cikin zuciyarsa ya fara da cewa. “Ni Maleekh, na san yadda zan sarrafa komai. Kin ji ni ko, A’isha? Zan fito a tv, na faɗa cewa na fa ɗa soyayya da Amal, duniya ta ji. Bayan haka kuma, ita kanta zata sha mamakin irin sakamakon da zata gani. Wulakanci ne nake nema a kanta, ba soyayya ta gaskiya ba.” A fili kuwa ya furta "Ƴar uwa kenam kema baki yadda dani bane?..." A’isha ta ja dogon numfashi, ta san Yayanta zai iya amfani da soyayya ya ruguza mace, duk da bai taɓa aikatawa ba amma tana da tabbacin zai iya. Ta kalli Maleekh da ido mai cike da damuwa, tana fatan abin da ya tsara kar ya zama sanadin halakar shi da rayuwar Amal gaba ɗaya, amma wata zuciyar ta yadda da shi..kuma ta kudurta taya shi yaƙin neman soyayyarsa.. A’isha bata san meye a zuciyar ɗan’uwanta ba. Ita a tunaninta soyayya ce kawai ta kama shi, sai dai ba ta san irin tsananin shirin da ya ɗaura ba. Wanda yasan ainihin shirin shi kuwa ba kowa ba ne face PA ɗinsa (Personal Assistant), wanda kullum yake tare da shi, yana ɗaukar sirrinsa yana kuma ƙarfafa shi akan wannan tafiyar. PA ɗin nasa kuwa bai tsaya kawai da goyon baya ba, har ma shi ne yake tsara hanyoyin da Maleekh zai bi don cimma manufarsa akan Amal. Shi ke yi masa tunatarwa, “Boss, ba’a samun irin wannan mace sau biyu. Ka nace, ka da ka bari ta kuɓuce maka.” A wannan ranar ne Maleekh ya shirya fitowa television, a cikin shirin da Maleekh ya ƙulla, ya shirya ya fito a talabijin a wani shiri na musamman da kamfaninsa zai gudanar. Ba don komai ba illa ya bayyana soyayyarsa ga Amal a bainar jama’a, ta yadda ba ita kaɗai zata ji ba, duniya ma zata shaida. Wannan matakin kuwa babban rikici zai tayar domin zai kama Amal ba tare da ta shirya ba... Maleekh yana zaune a cikin babban ɗakin taro na kamfaninsa dake nan kaduna, inda aka shiryawa TV interview. Hasken kyamarori yana haskawa, muryar ɗan jaridar da ke tambayarsa tana cika wurin. “Sir Maleekh,” ɗan jaridar ya fara da ladabi, “a kwanakin nan ana ta rade-radin cewa kuna da alaƙar soyayya da wata matashiya mai suna Amal, wacce aka sani da sahihiyar murya wajen magana da gaskiya da adalci. Shin wannan gaskiya ne?” Maleekh ya ɗan murmusa, ya ɗan lankwasar da wuyansa, yayi kalar tausayi ya ce. “Eh, gaskiya ne. Ina sonta da gaske. Amal ce hasken zuciyata. Na yarda cewa in ba tare da ita ba rayuwata ba zata cika ba.” PA ɗinsa yana tsaye gefe yana kallon shi da murmushi mai nuni da cewa shirin nasu yana tafiya yadda suka tsara. A wajen duniya, Maleekh na nuna so mai zurfi kamar ransa zai fita saboda Amal. A'isha kuwa, ƙanwarsa, tana zaune a gidanta tana kallon TV tana murna, zuciyarta cike da alfahari: “Allah ya haɗa kan su, wannan soyayyar gaskiya ce ta zuciya.” Ta ɗauke shi da gaske, bata san cewa a cikin zuciyar ɗan uwanta akwai wani mugun shiri ba. Maleekh a cikin zuciyarsa yana tunani: “Sai na shigar da soyayyata a cikin zuciyarki Amal, sai kin amince. Bayan kin kamu sosai, zan nuna miki cewa ke ba kya da wata daraja a idanuna. Zan nuna miki ƙasar duniya ta banbanci tsakanin mu biyu.” Ya ƙara jefa kalmomin soyayya a cikin amsoshin interview ɗin, wanda hakan ya sa jama’a suka yi ta jinjina masa a matsayin saurayi mai gaskiya da kishi. Duk da cewa Amal ta ji daɗin ganin Maleekh a talabijin yana yabonta, tana ɗaukar taken “ƙarfin murya ta mata masu gaskiya”, bai hana ta ɗaure fuska ba. A idon duniya, bata nuna ta amince da shi ko ta ji daɗin yabon sa ba. Ta yi kamar bata damu ba, domin Amal mace ce mai dauriya, mai son a yabe ta bisa aikinta ba wai saboda wani namiji ba. Amma a cikin zuciyarta? Wani irin farin ciki ya cika mata ƙirji. Kalaman Maleekh sun daɗa ƙarfafa ta, sun bata kwarin gwiwar cigaba da tafiyarta. Sai dai ta yi ƙoƙarin boye wannan farin ciki daga kowa, har ma daga kawarta A’isha. Shi kuwa PA ɗin Maleekh yana gefe yana kallon wannan shirin, yana dariya cikin ransa. Shi ya fi kowa sanin cewa duk wannan shirin Maleekh akan Amal akwai zurfi babu wasa a ciki. Kuma saboda yana goyon bayan shi, ya riga ya ɗauki wannan al’amarin tamkar nasu su biyu ne. A’isha kuwa bata fahimci komai ba. A ganinta Maleekh dai mutum ne mai son fitowa fili yana yabon kowa. Bata san asalin dalilin da yasa yake ƙoƙarin shiga zuciyar Amal ba. Ita dai abin da ta gani shi ne Yayanta yana ƙoƙarin nuna soyayyarsa a bainar jama’a... A ranar kuwa A'isha ta koma gidan su Amal..Suna zaune su biyu, Inna kuwa bata nan.. A’isha tana dariya tana kallon Amal ta ce “Amal, kin ga yadda ya fito a tv saboda ke? Yayana fa ya fito duniya ta sani saboda soyayyarki. Kina da sa’a wallahi.” Amal ta ɗauki remote ta kashe ƙaramin tv dake manne a ɗakinta, ta yi ɗan murmushi ba tare da ta dubi A’isha ba ta ce. “Wannan ba yana nufin zan amince da shi bane. A’isha, kin san halin Yayanki. Ban ga dalilin da zai sa in ɗaura kaina a rayuwarsa ba.” A’isha ta ɗan turo baki sannan ta ce “Ke dai kin fi kowa sani. Amma wallahi ina ganin wannan soyayyar gaskiya ce.” Amal ta ɗauke fuska, amma zuciyarta na cike da farin ciki ta ce “Bari dai lokaci ya nuna gaskiya. Amma ni ban amince ba tukuna.” Suna cikin hira sai ga wayar A'isha na ƙara, tana dubawa taga sunan Yaya Maleekh ya bayyana akan Screen, murmushi tayi tare da ɗaga wa, a bangaren Maleekh kuwa cewa yayi. "Kina tare da Amal ne?..." A'isha ta bada amsar "eh..." Ya ce "Toh! Ki ɗauke ta kuje kiyi mata shopping, ta taya ki zaɓen duk abinda take so a supermarket, Nima zan je wurin zan biya kuɗin..." A'isha ta ce "To ba damuwa..." Ta katsar da wayar tana duban Amal, sannan ta ce. "Yanzu dai tashi ki rakani shopping.." Amal ta dube ta tace "kinga ban fa yi wanka ba, kuma ki bawa Angonki yayi miki mana..." A'isha ta ce "ai ba Angon ne zai sa abinda zan saka ba, kuma inaso ki taya ni zaɓen kayayyaki ne.." Amal ta ce "To jira ni nayi wanka.." A'isha ta jinjina kai, tana jira har Amal ta kammala komai sannan suka tafi..dake A'isha da motarta a cikin motar suka wuce... Bayan sun shiga, suka cika cart da kaya iri-iri. Amal tana taimaka mata ɗaukar kayan da suka burgeta ba tare da ta san a ita ake wa shopping ba. Da suka iso wajen biyan kuɗi, sai Cashier ya sanar dasu cewa. “Madam, ba sai kin biya ba. An riga an biya dukkan kuɗin kayan nan.”.. Amal ta kalli A’isha cikin mamaki ta ce “Waye ya biya kuma?” A'isha ne ta sanar mata cewa "Duk kayayyakin nan nata ne.." Amal ta ce "nawa kuma taya?..." A'isha tana murmushi ta ce. "Yaya Maleekh ne yace na kawo ki shopping, shi ya biya kuɗin...." A’isha ta fara fito waje da kayayyakin, Amal tana tsaye tayi tsumuuu, itama daga baya ta biyo A'isha, suka fito... Cikin mamaki Amal ta hango Maleekh tsaye a wajen motarsa a bakin titi, yana murmushi kamar wanda

Chapter 10 of 62