“We have an issue here…”
Maleekh ya kalli fuskar su cikin mamaki.
“What? Is there any problem?”
Suka nuna masa allon: cikin jakarsa akwai ƙwayoyi masu hatsari waɗanda a ƙasar nan hukuncinsu ɗaya ne da kisa...
Cikin rawar murya, ya ce:
“That’s… impossible. That’s not mine! Wallahi I don’t know about that!”
Amma ba wanda ya saurare shi.
Nan take suka kwace wayoyinsa, suka sa masa handcuff, suka tura shi cikin wani ƙaramin ɗaki mai duhu, inda ake tsare waɗanda ake zargi da laifin safarar miyagun abubuwa...
A nan ya zauna, ba tare da kalmar da zata fito daga bakinsa ba.
Abinda ke masa yawo a zuciya shi ne “Amal… idan ta ji wannan fa?”
A can gida kuwa, kwana uku suka wuce ba labari.
Ammy tana ganin kamar ya kashe wayarsa ne don ya huce.
Abbah kuma ya ce,
“Ku barshi, zai dawo da kansa.”
Sai rana ta bakwai sati guda kenam, lokacin da Amal ta isa kamfani da safe, cikin kaya masu kyau amma idonta kumbure saboda rashin kwanciyar hankali. Ta shiga reception da sallama, ta amsa gaisuwar ma’aikata da natsuwa, tana ƙoƙarin ɓoye ɓacin ranta...
phone ɗin receptionist yana yawan ring..
Receptionist ta ga wani number da yake meta da rubutu: “International Airport Authority. URGENT CALL”. Kafin Amal ta wuce sai ta ce cikin girmamawa:
“Miss Amal. Wani ke ƙira daga Airport London. Sun ce akwai buƙatar a yi magana da dangin Maleekh.”
Amal cike da mamaki take kallon receptionist ɗin da take ƙoƙarin bata wayar:
Amal ta karɓa da faɗuwar gaba, zuciyarta na dukan kamar ana buga ganguna a ƙirjinta.
Da ƙyar ta furta,
“Hello....“Hello? …Waye ke magana?”
Sai wata murya mai sanyi ta amsa daga can ƙetaren teku:
“We’re calling from Heathrow Airport. A man named Mr. Maleekh Abdul-Majeed has been detained in our custody for drug trafficking. We need his family or representative.”
Wayar ce take ƙoƙarin faɗuwa daga hannunta, da ƙyar ta riƙo wayar da sauri ta ƙara karawa a kunne.
Cikin tsoro ta matsa kusa da receiver tana faɗin.
“A, Mr… wai… me kuke cewa? Maleekh? Amma… ya tafi ne, ya riga ya sauƙa? Ya… ya faɗa muku da abin da ya faru?”
Ma’aikata suka tsaya kallonta yanda ta firgita. Idonta ya cika da hawaye...
Officer ya kuma cewa:
“Muna neman mu tabbatar da gaskiya. An tsare shi ne lokacin da aka samu kayan miyagun kwayoyi a jakarsa. Yana nan a interrogation room yanzu. Muna buƙatar wanda zai zo a matsayin danginsa ko wakili. A halin yanzu wayoyinsa an kwace, kuma ana nazarin jakarsa. Muna bukatar lambobin danginsa: akwai yiwuwar mu yi contact da su don sanarwa….”
Amal a ruɗe ta ce
“What…? Maleekh…?”
Ƴar amsa kawai ta fito daga bakinta kafin ta durƙusa, ta dafa tebur tana huci, hawaye na zuba kamar an kunna famfo....
A wannan lokacin, wurin ya yi shiru kamar anyi mutuwa. Wasu ma’aikata suka juya suna kallo Amal. Zayd ya tsaya a gefe, fuskarsa ta canja launi. Idanunsa sun yi kama da wanda ya yi farin cikin labarin amma matsayinsa ya kasance, ya yi saurin ciro muryar nuna damuwa...
Zayd ya matso da sauri yana faɗin
“Me!? Maleekh?! Amma… wannan ba zai yiwu ba! Ashe abun da ya faru da shi kenam...?!
Pretty … Amal! Me ye abun yi yanzu?”
Amal ta daka masa tsawa cikin kuka ta ce:
“Ka daina ƙirana da sunan nan! Ka rabani da shi, yanzu kuma wannan! Ka ji daɗin hakan ko Zayd?”
Zayd ya ja da baya, amma ya ɓoye murmushi a ƙarƙashin haƙoransa.
Amal ta riƙe kanta da hannuwa biyu tana kuka tana faɗin:
“Allah na tuba… Maleekh, Allah ka kare ka… duk wannan saboda ni... saboda son da na kasa karewa...”
Amal ta yi ƙoƙarin ƙara yin magana amma jikinta ya mutu. Don haka ta miƙawa receptionist waya da rawar hannu, murya na kakkarwa ta ce:
“Ku ba su lambar ofishin Mahaifinsa ko Mahaifiyarsa… da wani ofishin lauyanmu. Ku gaya musu su yi contact da su nan take!”..
Receptionist ta tura musu lambar Abbah...
A can London kuwa suna ganin lambar suka danna ƙiran number Abbah.
Ganin international call ne yasa Abbah ɗaga wayar tare da faɗin.
“Sannu…wa ke ƙira?”
Officer ya fara bayani:
“Alhaji Abdul-Majeed, muna neman mu sanar da ku cewa an tsare ɗanka, Mr. Maleekh Abdul-Majeed, a Heathrow Airport. An samu abubuwan da ake zargi a cikin jakarsa. Muna buƙatarku da ku zo ko ku tuntubi ofishin jakadancin nan da nan. An kwace wayoyinsa kuma yana nan a tsare. Muna bukatar wanda zai zo ya tabbatar da shi.”
Innalillahiwa’inna ilaihirraji’un, Abun da Abbah yake ta maimaitawa kenem, Abbah ya kasa magana na ɗan lokaci. Sai ya tambayi:
“In…in yaushe hakan ya faru? Yaya lamarin yake?”
Officer ya ce:
“Ya sauƙa ne tin last week Mr. Abdul-Majeed, kuma an kama shi a lokacin da ake bin diddigin tafiyarsa ko a lokacin da ya sauƙa. Muna tuntubar masu gabatar da shari'a, kuma ana ci gaba da bincike. Muna bukatar ku hanzarta zuwa nan, ko ku tuntuɓi ofishin jakadanci.”...
Abbah ya ajiye waya, zuciyarsa ta tsaya. Ya kashe wayar da rawar murya, ya miƙe da sauri gaba ɗaya ya rasa me zai yi tsabar ruɗewa. A gefe, Abbah ya ƙira Ammy da kyar, suna mamakin abin da ya faru...
Abbah ya samu yin waya daga hukumar jirgin a wannan lokacin, ko wani ne ya masa canji... a firgice yake tambayarsu...
Ammy ta zauna tana kuka cike da nadama, tana zargin Amal ce ta jawo wa ɗanta wannan bala’in...
A wannan ranar suka fara shirye-shiryen tafiya London don ceton Maleekh...
☆☆☆☆☆☆☆☆☆
A cikin office, Amal ta ji kamar ƙasa ta tsage ta shige. Gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, idonta na zubar da hawaye da ba zata iya ɓoyewa ba...
Tana cikin wannan halin sai ga lawyer (wanda yake senior counsel na kampani) ya shigo da sauri lokacin da aka sanar da shi... Yana waya da ofishin jakadanci, ya soma neman hanyoyin tuntuɓa. Bayan ya gama, sai ya koma ya tsaya a gaban Amal..
Yana faɗin
“Miss Amal, ke da family ɗin Mr. Maleekh dole ku tashi ku tafi London ko ku tuntuɓi ofishin jakadanci nan take. Wannan lamari ne na ƙasa da ƙasa. Zan shirya duk takardun da ake buƙata; amma ku sani, a irin wannan hali gwamnati na iya ɗaukar matakan doka masu tsauri. Dole mu yi gaggawa.”
Amal ta nufi taga, ta kalli sararin sama kamar mai neman mafita, zuciyarta cike da laifi da fargaba...
“Amal zata zauna a Nigeria, domin bani da wani ƙarfin zuwa tuntubar hukumar ƙasar waje, iyayensa ne suke da alhakin hakan kuma an sanar musu, ina tunanin a yau zasu tafi....
Ya Allah… wannan duk saboda ni ne? Ko saboda wani ne yake son wargaza rayuwarsa? Maleekh… ina nan… ina addu’ar kar su cutar da kai….”
A gefe Zayd yana la6e a bakin ƙofa ta waje yaba sauraron komai, lokaci guda ya sauƙe numfashi tare da sakin murmushi kamar wanda yayi wata gagarumar nasara...
●●●
Amal kuwa, bayan ta koma gida da dare, ta kasa kwanciya. Wayarta a hannunta, tana ta ƙiran lambar Maleekh kamar wata mahaukaciya, amma komai shiru.
Cikin ƙarfin kuka ta durƙusa ta ce:
“Ya Allah, idan akwai wanda ya shirya masa, ka bayyana gaskiya… ka kare min shi, domin ni ba zan iya rayuwa ba tare da shi ba…”
Wannan shi ne farkon azabar da ƙaddara ta shimfiɗa musu.
Tun daga ranar da aka ɗauke Maleekh, gidan su ya shiga tashin hankali. Abbah ya kasa bacci, Ammy kuma kuka da addu’a ke damunta. Cikin kwanaki biyu da zuwa London domin ganin yaron nasu. Amma ba'a basu damar ganinsa ba tukun...
Sai yau kwana uku da zuwansu..
Sai yau aka fitar da Maleekh daga ɗakin duhu domin ganawa da iyayensa.
Maleekh zaune ne a ƙaramin kujerar ƙarfe. Idonsa ya kumbura, gashin kansa ya fita daga tsari, gaba ɗaya haskensa ya dusashe..
Ƙofar ɗakin ta buɗe...
Ammy ce ta fara shigowa, tana sanye da farin hijab, sai Abbah dake biye a bayanta..
Da zarar Maleekh ya gan su, hawaye suka cika idonsa, ya miƙe tsaye kamar wanda aka zare masa numfashi..
“Abbah… Ammy…” ya ƙira da muryar da ta karye, yana kuka kamar yaro...
Ammy ta nufi gare shi da sauri, ta rungume shi, tana girgiza kai, tana kuka...
“Maleekh ɗana, me suka yi maka haka? Waye ya maka wannan sharrin?”
Maleekh ya runtse idanu, hawaye na zubo kamar ruwan sama...
“Ammy, wallahi ban san da komai ba!”
Ya fashe da kuka, muryarsa ta cika da rawar zuci.
“Na bar Nigeria da jakata a hannuna, amma lokacin da na sauƙa suka ce sun ga wani abu a ciki. Na rantse ba jakar da na ɗauka bace! Jakar iri ɗaya ce da tawa, amma kayan ciki sun bambanta. Na gane daga baya cewa an sauya ta, amma kafin in yi magana, sai suka rufe ni..."
Abbah, wanda yake tsaye a gefe, yana ɗaure da fuska ganin halin da ɗansa yake ciki, idonsa ya cika da hawaye.
Ya matso kusa, ya zauna kusa da ɗansa, ya dafa kafaɗarsa tare da faɗin...
“Na yarda da kai, ɗana. Ban taɓa ganin ka da makamancin irin wannan abu ba. Amma su ba su san Maleekh ɗina ba, sun manta da irin tarbiyyar da muka baka.”
(A'a Abbah yana shan Shisha faa 🤣🤣🤣🤣)
Abbah ya share hawayensa da yatsansa, ya ci gaba da magana cikin sauti mai nauyi:
“Za mu bincika gaskiya. Ba zan bar wannan lamarin ya wuce haka ba. Na riga na fara tuntuɓar lauya da ofishin jakadancin Najeriya. Amma ka yi haƙuri, ɗana. Kar ka bari wannan ƙaddara ta karya maka zuciya.”
Maleekh ya girgiza kai yana kuka,
“Abbah, ina ji kamar mafarki ne. Na rasa komai, mutunci na, sunana, rayuwata. Wallahi Abbah, ni ba mai laifi bane!”
Ammy ta riƙe hannunsa da ƙarfin zuciya, ta ce cikin kuka:
“Allah yana tare da kai, ɗana. Ba mai gaskiyar da yake jimawa dole sai ka tsira. Zan roƙi Allah a kowace raka’a ya tabbatar da gaskiyarka.”
Ƙarar ƙofar ta buɗe, jami’an tsaro sun dawo don su fitar da su daga ɗakin ganawa.
Ɗaya daga cikinsu ya ce da nauyayyen murya:
“Time’s up, please.”
Ammy ta ƙara riƙe hannun ɗanta, tana kuka, tana faɗin:
“Ka tsaya da addu’a, Maleekh. Kada ka bari shaidar ƙarya ta ci nasara akan ka.”
Abbah ya miƙe, ya kalli ɗansa da idon da ke cike da ƙarfin hali irin na uba:
“Ka san me ya fi ƙarfi akan duk wata shaidar ƙarya? Gaskiya. Kuma gaskiyar ka zata fito. Na rantse da Allah, zan tabbatar da hakan.”
Jami’an suka buɗe ƙofar, suka ja Maleekh zuwa yanda aka fito da shi...
A lokacin yana waiwayen iyayensa, yana hawaye, yana faɗin cikin murya mai rauni:
“Abbah… Ammy… ku yarda da ni…ku sanar musu... wallahi ban taɓa aikata irin wannan kazantar rayuwa ba…”
Ƙofar ta rufe da ƙarfi, ɗakin ya sake yin shiru da duhu... tin daga ciki yake jin kukan Ammy....
●●●●●
Amal kuwa, tun bayan wannan tashin hankali, ta fara ganin abubuwa masu ban tsoro.
Da farko tana cikin mota akan hanyar gida sai ta lura da wata motar black jeep tana binta a baya. Tana ƙoƙarin wucewa, motar na binta kamar ana bibiyanta...
Tana isowa mai gadi ya buɗe mata gate, kafin ta shige, sai ta hango wani mutum a bayan gilashin motar sanye da black hoodie, yana kallonta da ido razana, tamkar ba mutum ba...
Ta shiga cikin gida da gudu jikinta na rawa, zuciyarta na bugawa kamar za ta faso ƙirji...
A razane ta fito daga motar ta nufi ciki da gudu, Inna tana zaune a falo bata tsaya kulata ba tsabar tsoro...
Tana kaiwa ɗaki ta rufo ƙofa, ta jingina da bango tana huci. Hannunta na rawar jiki, ta ɗauki wayarta da gaggawa ta ƙara ƙiran Maleekh...
“The number you’re trying to reach is not available at the moment…”
Kamar daga sama ta fasa ihu tare da faɗin
“Ya Allah! Me yake faruwa dani ne?”
Knocking aka fara yi, Inna tana faɗi
"Lafiya dai ko Amatu? Me yake faruwa ne?..."
Amal cikin kuka take faɗin.
"Inna ki tafi kawai ba komai, kai nane ke ciwo, ina buƙatar hutawa, bacci zanyi ...."
Inna ta ce:
"Yanzu saboda ragon taka Amatu a ciwon kai ne zaki shigo a razane sannan kina ihu haka? To Allah ya kiyaye ..."
Ta juya....
*NEXT NEXT NEXT*
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 65 to 66
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Cikin dare misalin ƙarfe 2, Amal tana zaune a ƙasan gado tana kuka, sai faman tura message take zuwa ga Maleekh amma no reply... Ta kasa bacci kwata-kwata..
Tana cikin wannan halin sai ta ji sautin ƙwanƙwasa ƙofa.
Da farko ta zaci mai aiki ce, amma sautin ƙwanƙwasawar ya sake maimaituwa, wani irin ƙara ne mai ƙarfi, da ban tsoro...
“Waye ne!?” ta tambaya cikin murya mai rawa.
Babu wanda ya amsa..
Ta tattara ƙarfin hali ta ƙarasa kusa da ƙofar, ta ɗan buɗe, amma babu kowa.
Sai dai takardar white envelope a ƙasa. Ta ɗauka, jikinta yana rawa, ta buɗe cikin takardar ta ga an rubuta:
“You can’t hide from us.”
A lokacin ta saki takardar, ta soma karkarwa gaba ɗaya.
Hawaye suka fara sauƙa a fuskarta. Ta yi ƙoƙarin ƙiran Zayd, amma sai ta tuna da abin da ya aikata mata. Ta ɗan yi jinkiri, ta ɗaga kai ta dubi hoton Maleekh da yake jikin mirrow. Tana hawaye ta furta
“Ka dawo gare ni, dan Allah… karka barni haka. Ina fama da tashin hankali da rashin nutsuwa..duk saboda rashin ka..”
Tana faɗin haka ta fashe da kuka.
Tun daga ranar da ta samu takardar “You can’t hide from us,”
Amal ta rasa natsuwa gaba ɗaya.
Cikin kwanaki biyu ta lura da abubuwa da ba su da ma’ana:
Wayarta tana kunna kanta da kanta.
A ofishinta, tana jin kamar ana kallonta daga cikin gilashin taga.
Kuma kowace rana, idan ta fito daga gida, sai ta ga wata motar black tinted a can nesa, ba ta san ta wa bace...
Amal ta fara samun matsanancin damuwa. Bata taɓa jin irin wannan fargaba ba.
Ranar Litinin, bayan ta idar da sallah da asuba, ta ɗauki shawarar zuwa wajen aikinta da wuri fiye da kowane lokaci...
Bayan ta fito harabar gidan tana shirin shiga motarta sai kwatsam ta tsinci wani farin envelope a saman motarta, kamar irin wanda ta gani a baya...
Da gaggawa ta buɗe.
A ciki aka rubuta da jan biro:
“Stop asking questions about Maleekh, or you’ll be next.”
Jiki a sanyaye ta shiga motar ta ja a hankali, zuciyarta cike da tunani daban-daban..
Kafin ta isa wurin get mai gadi ya buɗe mata, kafin ta fita kuwa sai da ta dubi mai gadi sannan ta tambaye shi, "Da daddare akwai wanda yake shigo wa gidan nan?..."
Maigadi ya bata amsa da cewa:
"Wallahi Hajiya babu wanda yake shigo wa, tin lokacin da kika tsawatar mun da cewa, 'kada na kuskura na ƙara barin wancan yaron wato zaydu ya sake shigo wa, tin daga ranar ban ƙara ba, shekaran jiya ma yazo nayi masa koran kare...."
Amal ta jinjina kai sannan ta ce:
"Ba Zayd kaɗai ba, ko ma waye kada a bar mun kowa ya shigo mun gida indai ba wanda yake da alaƙa da gidan ba..."
Maigadi ya ce "har da oga Maleekh?..."
Ba tare da ta bashi amsa ba tayi ficewarta...
Tana fita sai motar black jeep ɗin da ta saba gani ta tsaya a can nesa, fitilunta na kunne kamar dai tana jiran ta motsa...
Cikin ƙarfin hali ta ja motar ta bar wurin, ɗayar motar ma ta bi bayanta, duk bayan mintuna saita dubi motar ta glass da haka ta isa campany...
Tana shiga ofishinta, tayi ido huɗu da wani envelope again... A zabure ta nufi tebur ta buɗe..
"Your welcome fine girl, ina miki albishir da cewa daga yau ki fara ƙirga kwana kin mutuwarki, kamar yanda iyayenki suka tafi, ki tabbatar zaki bi su, ka da kiji tsoron fito wa domin ko akan gadonki zaki mutu. HAHAHAHA...."
Da gudu ta je ta rufe office tare da sa key..
Tsaya ƙare wa ofishin tayi da kallo ƙirjinta ta bugawa da ƙarfi, jiki a sanyaye ta je ta zauna..
Ɗaukar telephone tayi ta ƙira secretary ɗinta,
“Karki bari kowa ya shigo min yau. In wani ya tambaye ni, ki ce ban zo ba.”
Ta kifar da kanta akan tebur cikin tashin hankali...
_____________________________________
Kunna system ɗinta tayi, ta fara binciken bayanan cikin company musamman files na security footage, tana son ganin ko za ta gano wanda ya ajiye takardar.
Bayan mintuna goma sha biyu, ta hango wani abu mai tayar da hankali.
A cikin video ɗin CCTV, wanda ya saka takardar a saman tebur ba kowa bane bace Zayd...
Ta zaro ido, tana kallon allon screen kamar wacce ta hango fatalwa.
Hannu ta kai ta rufe bakinta...
“Zayd…? Shi ne bayan komai…?”
Tana nan cikin tsoro sai ƙofar office ɗinta ta buɗe da ƙarfi!
Zayd ya shigo cikin sanyi, da murmushi a fuskarsa.
“Ke dai kina da curiosity sosai, pretty.”
Amal ta ja baya, tana faɗin,
“Me kake nufi da hakan Zayd? Me yasa kake bibiyata? Me kake son gani daga gareni?”
Ya yi dariya mai ɗan ban tsoro.
“Kin san me yasa na fi son ki, Amal? Domin kina da jarumtar tambaya amma akwai tambayoyin da a duniya ba’a amsa su sai da mutuwa.”
Yana matsowa kusa da ita, Amal tana ja da baya cikin tsoro tare da faɗin,
“Karka kuskura ka matso kusa dani, wallahi zan ƙira ‘yan sanda!”
Zayd ya tsaya, ya ɗora hannunsa akan teburin cikin sanyi, ya ce:
“Ki ƙira su mana. Amma kafin su zo, zan tabbatar baki sake ganin Maleekh ba har abada.”
Ya ciro wata ƙaramar bindiga a aljihu ya saita goshinta da shi, kafin ka ce mai ya harba akan goshinta..."
A zabure ta ɗago kanta daga kan tebur tare da faɗin, Innalillahi wainnailaihiraji’unu, cikin tana rawar jiki take zanga addu’o'i, hannunta na kan kirji, tana jin kamar numfashinta ya tsaya. Ga gumin da yake yanko mata, a ɗan kifar da kanta da tayi har tayi wannan mummunan mafarki...
“Ya Allah… menene yake faruwa dani?”
A wannan ranar sam bata yi wani aikin azo a gani ba, haka ta tattari jakarta ta bar company..
Har dare ya tsala haka take wannan mummunan tunanin mafarkin da tayi..
Cikin wannan halin bacci ya ɗauke ta, amma ba baccin da ke kawo natsuwa ba,
Sai mafarki mai tayar da hankali.
A mafarkin, ta ga kanta tsaye a cikin wata tsohuwar falo mai cike da hayaƙin wuta.
A gabanta ta ga wata mata da take kama da ita sosai tana kuka, wani mutum kuma yana roƙon wasu maza masu bindiga su kyale ta.
Sai ga wani ya harbi matar, sannan aka fara ƙona gidan.
Amal ta yi ihu, ta ce
“Mooommm! Dadddd!!!”
Tana neman nufansu sai wata murya mai rauni ta ce:
“Amal... gudu ki gudu... kar ki yarda su same ki...”
A zabure ta farka da kuka, jikinta duk ya jiƙe da gumi, zuciyarta na bugawa.
Ta dafa kirjinta tana ambaton “Inna... Innaaa...Innalillahi wa inna ilaihi raji’un....”
Ta tashi cikin daren, ta fito falo, ta ga fitillu a kunne sai plasman da yake kunne alamar akwai wanda ya kunna bayan an kashe kafin a kwanta...Domin yanzu ƙarfe 3 ne na dare...
Idonta ta kai kan ƙofar falo ta ga a buɗe yake. Da sauri ta nufi ƙofa, sai ta hango wata ƙaramar takarda a ƙasa bakin ƙofar.
Ta ɗauka, ta buɗe tana karantawa..
“Truth always returns, just like fire. 🔥”
Nan take ta saki takardar tana girgiza kai.
“Wannan me yake nufi? Wane gaskiya ake nufi?”
A lokacin ta kukunna fitullun gidan gaba ɗaya, har na waje dana can ƙofar gida..
Ta fito a tsorace tana kalle-kalle, daga ita sai sleeping dress mai gajeren wando iya cinya sai riga ƙarama mai hannun breziyya...
Da sauri ta nufi get da ta gani a wangale. Tana isa ta fice waje tana dudduba ko zata ga wanda ya fita..
Tana tsaye kwatsam taji an rungumota ta baya, tana shirin yin ihu taji an juyo da kanta tare da toshe mata baki da bakin wanda ya rungume ta..
Kissing ɗin bakinta aka rinƙa yi sosai tare da mammatsa mata nonuwa...haka hannunsa yake ta shafa duk ilahirin jikinta har su ƙasin mararta, still ba'a sake mata baki ba..
Alamun akwai wani shirin da ake son haɗa wa...
A lokacin kuwa, wani ne daga cikin masu bibiyanta ya ke ɗaukar hotonta daga mota mai tinted da ke tsaye a nesa.
Sai da ya ɗauki hotuna sannan ya kunna wayarsa ya tura su cikin group ɗin sirri da ke da suna Operation Cash Maker..
Duk kissing da hugs da sock and lick duk an ɗauki hotunan like da saninta akayi, irin ba tilastata akayi ba...
A cikin group ɗin kuma mutanen da suke ciki basu fi mutum biyar ba...
Alhaji Wadata da Zayd da kuma Alhaji Gusau da kuma Maleekh da akayi joining ɗinsa a ciki...But sun cancanza numbobi yanda Maleekh bazai gani ko mutum ɗaya a ciki ba, da zaran an fito da shi daga international cell...domin sun san cewa tin da mahaifinsa ya je to bazai dawo ba sai da Maleekh...
Wanda yake kissing Amal kuwa baza'a taɓa gane ko waye ba domin yana sanye da bakaken kaya ne sai kuma black fenti da yayi a fuskarsa... ga kuma haske dadau dadau...
Amal tana ta ƙoƙarin kwace kanta, bayan ya gama ya hankad’a ta, ta faɗi ƙasi har sai da ta buga gwiwar ta sosai...
Kafin ta ɗago kuwa mutumin ya ruga da gudun gaske ya nufi motar, yana zuwa ya shige suka ja suka tafi...
Bayan ta gama koke-kokenta da shan kuka ta tashi da ƙyar tana ɗingishi ta shige gida..
Tana shiga ta fara buga wa mai gadi ƙofa, can ya fito da torch ɗinsa mai uban haske duk da hasken fitullun gidan.. ga ƴar sandarsa a hannu..
Yana fito wa ya ci karo da Amal, cike da mamaki yake binta da kallo sannan ya ce.
"Hajiya lafiya kuwa?..."
A fusace ta ce. "Meye aikinka a gidan nan? Shin an kawo ka saboda ka bar get a buɗe kayi ta bacci?..."
Maigadi cike da mamaki ya ce. "A buɗe kuma Hajiya? ..."
Idonsa ya kar wurin get ya ga a wangale, ya sake baki tare da faɗin.
"Ah!Ah!Ahhh, to wallahi sai da na kulle get ɗin nan har da bida, ya akayi a buɗe haka?..."
Amal tana kuka ta ce "To wa ya buɗe get ta waje kuma?..."
Maigadi ya haska ƙasi yanda aka fasa kwad'on a yayin da za'a fita amma ba'a san ta yanda aka shigo ba, abun ya bada mamaki sosai...
A zabure Maigadi ya yi waje da gudu yana faɗin
"Yau sai na kamo ɓarawon da ya shigo mana wallahi..."
Ita dai ta tsaya tana kallon waje gaba ɗaya jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba...
Haka kawai take jin tsinkar jikinta yana zuba wa, gabanta yana faɗuwa, da gudu ta zabura tayi ciki tana dingishi... Tana shiga falo ta kulle tare da sa key, sannan ta haura saman upstairs nan ma ta kulle bedroom, ta zauna a tsakiyar saman gado tana kuka....
《》《》《》《》《》《》《》《》《》
A gefe guda kuwa, a London, Abbah da Ammy suna cikin tashin hankali...
Suna ta tunanin sanar musu cewa an kama ɗansu Maleekh Abdul-Majeed a filin jirgi saboda samun kwayoyi masu haɗari a jakarsa...
Tin lokacin da suka baro wurin Maleekh da kuma halin da yake ciki gaba ɗaya sun rasa sukuninsu..
Suna zaune a wani gidansu dake nan London..
Abbah yana zaune ya riƙe kansa, ya ce da murya mai rauni:
“Na san ɗana ba zai taɓa yin hakan ba… akwai makirci a nan.”
Ammy tana zaune a gefensa tana kuka,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 43 Chapter of 62