zaki zarge mu da kisan kai ba!…”
Amal ta ce, "meye a cikin rayuwar takun banda sharri..."
Islam ta ce, "Duk da sharrin da muke da shi bai hanaki haɗa jini damu ba ai.."
Arfat ta ce, "ha haka kika nace mana, muna korarki kamar wata kariya amma kina ƙara tuso kanki kamar wata mayya, sai dai kika samu gurbi a cikin ahalin da kike raina wa.."
Amal ta daka tsawa tana faɗin "Ku dallah ku rufe mun baki, a wata rayuwar takun masu amfani da jinin al'umma..."
Islam ta ce, "a haka kuma mun rufa miki asiri, ƴar bola kawai..."
Amal cikin fusata ta zabga mata mari tare da faɗin "ni ƴar bola ce amma ai da dukiyar mahaifina kuke amfanu wa..."
Nan suka fara dambe, suna shirin faɗa a cikin ɗakin. Sai Ammy ta shigo da gudu, ta raba su cikin kuka.
tana raba su, muryarta a raunane, “Ku dakata! Ku dakata! Ya isa! Ku bar ta ta tafi!…”
Amal ta fita daga ɗakin tana faɗin maganganu, da cewa
“Babu ni, ba kuma iyalan ku! Kuma jarirai na, Ar’haan da Lihaam, ba za su taɓa shiga cikin ahalinku ba! Na rantse da Allah! Ban ƙaunar Maleekh tunda shima ɗan ahalinku ne! Zan bar garin nan!”
A wannan ranar, an sallami Amal da tagwayenta. Sai da Inna ta mari Amal a gaban mota jin abin da ta aikata, maganganun rashin da'a da ta riƙa faɗa. Haka suka koma can gidansu rai a ɓace...
Abban Maleekh kuwa har yanzu jikinsa ba sauƙi.
Wannan bidiyon da aka baza ya yi mummunan tasiri a Kotu. Kotun ta fara neman Abbah (wanda yake paralysis) domin za a kama shi don amsa tambayoyi kan kisan abokinsa.
Amma sakamakon halin da yake ciki yanzu za'a bar shi ya ɗan samu sauƙi tukun.
☆☆☆☆☆☆
Cikin daren wata rana, ƙungiyar Boko Haram sun afka musu sansanin cikin bazata. Nan da nan, yaƙi mai zafi ya kaure. Sojojin, tare da jarumta da tsari, sun yi martani mai tsauri.
Maleekh ('Lion') ya kasance a sahun gaba na yaƙin. Yana jagorantar Sojojin, yana amfani da dabaru na musamman (tactics) da ya koya. Duk da mantuwarsa, basirarsa ta yaƙi ta bayyana.
An yi ruwan harsasai da kukan bindigogi a ko'ina. An kashe Sojoji da yawa a cikin wannan yaƙin na tsawon lokaci.
Yayin da Maleekh ke tsaka da faɗa da wasu 'yan Boko Haram, wani ɗan Boko Haram wanda ke ɓoye a baya ya samu damar buga masa ƙarfe mai tsauri (metal bar) a kan sa cikin ƙarfin tsiya.
Maleekh ya ji wani mugun zafi wanda ya fi zafin yaƙin da yake yi.
Ya fara jin 'Zuuuuuuu' a kunnensa, kuma duniya ta fara juyawa masa. Yana ganin dishi-dishi a idanunsa. Wani abu kamar haske ya shige shi..
Cikin ƙiftawar ido, ya faɗi sumamme a tsakiyar filin yaƙin. Wannan buguwar ƙarfe ta biyu a kan kansa (bayan faɗuwar rami) ita ce makullin tunawa da kwakwalwarsa ke buƙata.
Bayan an yi yaƙi mai tsawo kuma an yi wa ƴan Boko Haram galaba, abu ya lafa. Sojojin sun ragu sosai, wasu sun mutu, amma sun kashe ƴan Boko Haram da yawa.
Sojojin da suka rage suka fara neman waɗanda suka ji rauni. Sun samu Maleekh a kwance sumamme, wanda ya yi kama da ya mutu. Sun ɗauke shi, suka kai shi wurin jinya na sansanin.
Washegari da asuba, kafin hasken rana ya fito sosai, Maleekh ya farfaɗo.
Ya buɗe idanunsa, a lokacin ya yi tsammanin ganin Amal a gefensa. Ya tuna tafiyarsu ta daji, guduwarsu, da kuma wurin da ya faɗi.
Maleekh cikin raunannen murya, ya ce “Amal!… Ina Amal!?”
Ya farka da sunan Amal a bakinsa!
Ya tuna sunansa (Maleekh), ya tuna Abbah, ya tuna Ammy, ya tuna dukkan rayuwarsa kafin ya shiga rami. Buguwar ƙarfen ta dawo masa da kwakwalwarsa!
Maleekh ya miƙe da sauri duk da raunin da ke kan sa.
Ya duba hannayensa da jikinsa yana faɗin “Ni ne Maleekh!… Maleekh Abdul-Majeed! Ina sansanin Sojoji ne? Me nake yi a nan? Na tuna! Na tuna komai!”
Sojojin da suka ga Lion ya dawo, kuma yana ƙiran wani suna Amal, sun yi mamaki sosai. Sun san cewa Lion ya sake samun kwakwalwarsa.
Maleekh ya fara tambayoyi nan take game da Abuja, iyayensa, da kuma Amal. Wannan tunawar ta Maleekh ta faru ne a daidai lokacin da ake zargin mahaifinsa da kisan kai, kuma Amal ta yi tsammanin cin amana daga dukkan su...
_NEXT NEXT NEXT_
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 89 to 90
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Bayan kwana biyu da farfaɗowar Maleekh, an kammala shirye-shiryen dawowarsa hayyacinsa. Sojoji biyu sun rakoshi har zuwa bakin babbar hanya, suka tabbatar da ya shiga motar haya lafiya zuwa Abuja. Suka biya masa kuɗin mota kuma suka yi masa bankwana cike da kewa saboda 'Lion' ya bar su.
A cikin Abuja kuwa, Amal ta ƙuduri aniyar barin garin. Tana ganin Abban Maleekh a matsayin maƙiyi, kuma Inna ta ƙi yarda da bin ta saboda tana da yakinin gaskiya..
Inna tana hawaye ta ce, “Amatu! Ba zan iya bin ki ba! Ba za ki gudu daga gaskiya ba! Ki yi wa rayuwarki adalci!”
Amal sam taƙi yarda da abin da Inna take faɗi, ta bar Inna cike da fushi, ta ɗauki tagwayenta da kayansu. Ta shiga Napep don zuwa bakin babbar hanya inda za ta samu motar haya zuwa Kaduna..
A bakin babbar hanyar Abuja, aka sauƙe Amal. Ta fitar da keken jariran (Baby Stroller) mai ƙarfi, wanda ke da wurin kwanciya na jarirai biyu (tagwaye). Ta kwantar da Ar’haan da Li’y a ciki, ta sa musu bulun botul (Pacifiers) a bakinsu, suna tsotsa cikin nutsuwa.
Ta juya baya don ba wa mai Napep kuɗinsa.
Ikon Allah! Wani iska mai ƙarfi ne ya zo, tyres na keken jariran suka goce ba tare da an lura da hakan ba. Keken ya fara tafiya da kansa a kan gangaren hanya, yana gudu a hankali.
Amal tana riga-runguma da mai Napep a kan canjin kuɗi (change), ba ta san haɗarin da ke zuwa ba..
Juyowar da Amal za ta yi, sai ta ga babu yara! Babu kekensu! A ruɗe ta fara waiwayawa.
Can ta hango keken jariran yana gudu, yana tunkarar babban titi mai cike da motoci masu gudu!
Amal ta jefar da jakarta da ke hannunta, ta fara gudu da tsananin ihu don taro su.
Cikin ihu take faɗin, “Yarana! Ku taimake ni! Motoci! Ku tsaya!…”
Gudu take, amma mutane a gefen titi babu wanda ya yi tunanin taimako. Sai dai tsayawa suna ɗaukar bidiyo da kallo saboda sun ga abin mamaki.
Keken jariran ya hau babban titi na Abuja, inda motoci ke gudu da tsananin gaske!
Dai-dai lokacin da keken jariran ke shirin shiga tsakiyar motoci, sai ga wani zabgegen mutumi ya sha gabansu da tsananin gudu da ƙarfi.
Wanda ya sauƙo daga motar haya 'yan mintoci kaɗan da suka wuce, ya tsallake hanya zuwa bakin titi! Ya ga haɗarin da ke zuwa, kuma ya yi amfani da karfinsa don ceton tagwayen..
Ya riƙe keken da ƙarfi, ya hana shi shiga cikin motoci!
Amal ta iso wurin tana haki da kuka. Ta rufu kan jariranta, tana rungume su cike da godiya ga Allah.
A fusace cikin tsananin zafin nama da fushi a kan rashin kulawarta da ya jefa yaran cikin haɗari:
Ya ce, “Me kike yi! Me yasa zaki bar yara haka! Baki da hankali!….”
Ya riƙe damtsenta da ƙarfi, ya ɗagota sama, ya kai hannunsa zai mare ta saboda tsananin fushi…
Sai kawai idonsa ya sauƙa akan fuskarta!
Maleekh ya daskarar da hannunsa a sama! Ya kasa motsi.!
“Amal!… Amal!…”
Ita kuwa Amal ta rufe ido sosai tana ƙoƙarin kare fuskarta daga marin. Can da ta ji shiru, sai ta buɗe idonta a hankali…
Itama idonta ya sauƙa a kan fuskar Maleekh!
Ta ruɗe, ta zazzaro ido, baki a sake, tana kallonsa da mamaki! Maleekh ne! Cikin tsari da tsananin kyau!
Amal da Maleekh sun tsaya, ido cikin ido, a kan titin Abuja. Firgici da mamaki sun cika fuskokinsu. Maleekh a matsayin Jarumi mai Rauni da Tunani ya dawo masa.
Amal muryarta na rawa, kamar ta ga fatalwa ta ce,
“Maleekh! Maleekh ne!…”
Maleekh ya jefa hannunsa da ya daskare a sama, ya shafa kansa. Cikin murya mai rauni ya ce,
“Amal! Ni ne Maleekh! Ta ya kika tsira?! Nasan daman dole zaki tsira domin fatana kenam! Me kike yi anan? Kuma me kike yi da waɗannan yaran?!”
Amal ta fara kuka da tsananin zafi saboda ta tuna zargin bidiyon
“Abin da nake so na sanar da kai shine, na ƙi ka yanzu! Ka rabu da ni! Ban san yaya ka tsira ba! Amma me ya kawo ka nan! Ka zo ka kashe ni ne? Saboda kaji labarin asirinku ya tonu shine zaka bayyana? Ka ga cewa ka yi nasarar cin amana!”..
Maleekh ya ƙara fusata. Bai fahimci ma’anar cin amana da take faɗa ba. Sam bai fahimci abin da take nufi ba.
“Cin amana kuma! Waɗannan yaran fa? Me ya haɗa ki da su! Me yasa zaki jefa su cikin haɗari! Wane ne ubansu!?”
Amal ta rungume jariranta da ƙarfi, tana kare su da jikinta.
“Maza bar nan! Ba ruwanka! Su ba naka bane! Su ba ‘yan ahalinku bane! Abun takaici ne kawai kuka zo ku cece su daga haɗari! Ka rabu da ni!”
Maleekh ya dube ta da mamaki na ƙiyayya da take nuna masa, sannan ya kalli jariran da ke cikin stroller. Sai ya fara jin wani bugu a zuciyarsa wanda ya fi zafin yaƙin da aka yi masa. “Shin kin haukace ne? Kodai baki yi farin cikin ganina bane?..yanzun ina kike shirin zuwa? Waima yaran waye waɗannan?..."
Wani mai wucewa wanda ya lura da rikicin su, ya gane Maleekh wanda labarinsa ya yadu. Ya matso kusa da su.
Mai Wucewa ya kalli Maleekh sannan ya ce,
“Kai ne Maleekh? Kai ne ɗan Alhaji Abdul-Majeed? Labarinku ne ya cika garin nan! Ana zargin Mahaifinka da kisan abokinsa! Yanzu Kotu tana nemansa a yayinda yake kwance a gadon asibiti..!”
Maleekh ya daskare a wurin! Kisan kai? Abbana? Wani zafi ya ƙara kama kansa..
Cikin rashin fahimta ya ce,
“Zargin me? Wane Abbana? Kotu kuma? Wace irin magana ce wannan!”
Mai Wucewa ya ce.
“Bidiyo ya nuna hakan! An nuna mahaifin yarinyar nan (Amal) yana jawabin cewa Abbanku yana ƙoƙarin kashe shi don ya ci dukiyarsa! Shi yasa yarinyar nan take shirin guduwa! Tana tsoron kar a kashe ta!”
Maleekh ya juya, ya kalli Amal, cike da tashin hankali da kuma zargin cewa ta yarda da wannan ƙaryar har tana nuna masa ƙiyayya..
Maleekh ya riƙe kansa, wanda yana ɗan jin zafin raunin da ya ji.
“Wannan ƙarya ne! Zargin sharrin Abbana! Amma ke… Amal! Ke ma kin yarda da wannan sharri har kike cewa kin ƙi ni! Kin yarda Abbana makiyin ku ne!…”
Amal ta gane cewa Maleekh gaskiya yake faɗa saboda tsananin raɗaɗin da yake ciki. Tunanin da ta yi na cewa Maleekh ya san komai ya zama ƙarya..
Maleekh ya kalli jariran da ke cikin keken, cike da tsananin tausayin kansa, ya durƙusa a gaban keken, ya kalli Ar’haan da Li’y. Wani abu ne ya cake shi a saitin zuciya.
“Waɗannan … su wanene… sun yi kama da ni… suna da… wani annuri da na sani…”
A lokacin Maleekh ya tuna da sadaukarwarsu a ruga. Ya tuna da kwana uku da aka ba su. Ya duba jariran da kyau.
Ya jefa kansa sama, ya kalli Amal da idanu waɗanda suke rufe da hawaye.
“A-mal! Waɗannan… ba yaranmu bane! Su ne tagwayenmu! Sun zo ne! Sun zo?!…”
Ya ɗauki Ar’haan da Lihaam a hannunsa, yana kuka da murna da azaba lokaci guda.
“Ba zaki gudu ba! Ba zan bari a kama Abbana ba! Ba zan bari a cutar da shi ba! Kin yi shari’a a kaina, kin yi a kan Abbana! Yanzu lokaci ne na wanke shi!…”
Maleekh bai bai wa Amal damar musawa ba. Ya riƙe hannunta da ƙarfi, ya saka ta a Napep (Keke Napep), shima ya shiga tare da jariransa a hannunsa. Sun nufi gida..
Amal muryarta na rawa ta ce, “Ni ba zan je gidanku ba! Bazan sake shiga gidan maciya amana ba!…”
Maleekh ya dube ta sannan ya ce, “Rufe mun baki! Ba mu da lokacin faɗa! Kaddara ta haɗa mu a nan! Zaki bi ni! Ba zan bari a cutar da Abbana ba!”
Bayan an sauƙe su a gidan, kai tsaye ciki suka nufa.. Maleekh ne ya tura ƙofar falon, ya shiga da tagwayensa a hannunsa, da Amal a bayansa.
A falon, Ammy tana asibiti jinyar Abbah. Sai Islam da Arfat ne ke zaune cikin tsananin baƙin ciki da kuma ruɗanin bidiyon.
Kannen sun ɗaga kai, suka ga Maleekh! Sun ganshi tsaye kuma yana riƙe da tagwaye!
Suka zama kamar sun ga fatalwa!
Islam ce ta fara yin ihu ta miƙe tana faɗin. “Yaya Maleekh!…”
Arfat ta miƙe itama, da muryar kuka “Yayana!…”
Nan da nan, suka ru ga da gudu, suka rungume shi, suna kuka mai tsanani da godiya da murna.
Maleekh yana riƙe da su, yana hawaye ya ce, “Na dawo! Kuna lafiya! Ina Ammy? Me ke faruwa?”
Bayan sun saki Maleekh, sai suka ga Amal a bayansa. Farin cikin su ya koma kallo na fushi da baƙin ciki.
Islam ta harari Amal, cikin tsanaki ta ce. “Me kike yi a nan! Bayan kin zagi Abbanmu! Ba kya jin kunya!…”
Arfat itama ta ce, “Ki fita daga nan! Yaya Maleekh, me ya kawo ta nan! Wannan macuciya ce! Ta yarda da ƙaryar bidiyon nan!…”
Maleekh ya ɗaga musu hannu yana faɗin, “Shiru! Ku dakata! Ba mu da lokacin faɗa! An gama zargin sa! Yanzu za mu gano gaskiya! Ina bidiyon!?”
Maleekh ya ajiye tagwayensa a hannun Islam da Arfat (wanda hakan ya rage musu fushi). Ya buƙaci su bashi memory ɗin da bidiyon ke ciki.
Islam ta ba shi memory ɗin. Ya saka shi a babban Plasman falonsu. Sun kunna bidiyon, Maleekh ya zura ido sosai yana nazari (analysis) na bidiyon.
Amal ma ta matso, tana kallo saboda tsananin sha’awa na yadda Daddynta ke jawabi, tayi kewar fuskarsa sosai.
Ya zauna a gaban Plasman sosai don nazarin bidiyon da ake zargin mahaifinsa da kisan kai. Amal ta tsaya a gefe, tana kuka da hararar Maleekh,
Maleekh ya kalli video tas. Ya kalli Abbah Abdulsamaad (Mahaifin Amal) yadda yake magana da murya mai rauni. Duk da cewa bidiyon yana zargin mahaifinsa, Maleekh ya lura da wasu abubuwan mamaki waɗanda ba kowa ya lura da su ba.
Abubuwan da Maleekh Ya Lura da su:
A lokacin da mahaifin Amal ke jawabi, Maleekh ya lura da yadda hannun Abbanta yake kaɗa yatsunsa a ɓoye.
Yana ɗan girgiza kai, yana ƙibkibta idanu a wani yanayi na musamman.
Maleekh ya fahimci cewa wannan alamar sirri ce, wanda ke nuna cewa akwai lauje cikin naɗi kuma an tilasta wa Abban Amal jawabin.
Bayan ya gama kallo, ya zare memory ɗin, ya miƙe jiki a sanyaye..
Amal ta kasa jurewa, tayi masa tambaya mai zafi, tana harararsa.
“To! Shin wata shaida ka samu? Kana so ka kare mahaifinka ne? To mahaifinka shine mutumin da ya kashe mun mahaifi!…”
Maleekh ya tsaya cak! Wani mugun zafi ya kama shi a zuciyarsa saboda rashin yarda da zargin da take yi masa. Fushin da ya ji ya sa shi manta da rauninsa gaba ɗaya.
A fusace ya darara mata tsawa mai ƙarfi, ya ɗaga mata hannu da cewa,
“Enough, you stupid girl!”
Zuciyarsa ce take raɗaɗi kamar wuta. Nan da nan idanunsa sukayi jawur, yana kallon cikin kwayar idanunta kai tsaye!
“Ke, abun farin ciki ne a kama mahaifina da zargin kisa? Me yasa zai kashe babban abokinsa wanda yake alhinin rashinsa har yanzu? Shin meyasa zai ɗauke ki tamkar ɗiyarsa alhalin shi ya kashe mahaifinki? Kin taɓa samun farmaki ko hantara a wurinsa? Kin taɓa ganin wani sauyin fuska a tattare da shi?…”
Amal ta yi shiru, ta kasa bashi amsa. Ta tuna da tausayi da girmamawar da Abbah Maleekh ya nuna mata.
Maleekh ya harzuka da rashin amsarta da kuma zarginta na ƙarya. Ya daka mata tsawa da murya mai ƙarfi: “Answer me!”
Amal ta tsorata da tsawar, ta fara hawaye ba zato ba tsammani.
Maleekh ya fahimci cewa magana ba zai kai su ko'ina ba. Abbansa yana buƙatar ceto nan take.
A fusace, ya yi wa su Islam hannu, ya tattara jariransa.
“Islam, Arfat! Ku biyo ni! Za mu nufi asibiti! Za mu ga Abbah! Kuma za mu gano gaskiya!…”
Islam ta rungume Ar’y (Ar’haan), Arfat kuma ta riƙe Lihaam. Haka suka fita da gaggawa, suka bar Amal ita kaɗai a tsaye a cikin falon, zuciyarta cike da ruɗani da kuma nadamar zargin da ta yi.
Yayin da Maleekh da ƙannensa ke kan hanyarsu ta zuwa asibiti, Amal ta tsaya a falo, hankalinta a ruɗe. Ta kasa yarda cewa Maleekh ya dawo, kuma ta yi masa mugun zargi.
Amal ta ɗauki memory ɗin da suka manta akan TV stand, ta saka a Plasman nan take. Ta fara kallon bidiyon cike da damuwa da kuma ruɗani. Tana maimaita kallon akai-akai, tana neman alamar makirci da Maleekh ya faɗa, amma ta kasa samun hujja daban mai ƙarfi.
Maleekh da ƙannensa suka isa asibiti.
Ammy tana zaune a bakin ɗakin Abbah cikin tsananin damuwa da kuka. Ganin Maleekh a tsaye, cikakke kuma ba tare da rauni ba, ya zama kamar abin al'ajabi a gare ta.
Ammy ta taso da gudu ta rufo shi, ta rungume shi tana kuka mai tsanani.
Muryarta na rawa, cike da murna da zafi ta ce. “Maleekh! Kaine ka dawo gare ni?! Na gode Allah! Na gode Allah da Ya dawo da kai! Na yi tunanin na rasa kowa!…”
Maleekh ya rungumeta da ƙarfi yana faɗin, “Mom! It’s okay! Na dawo! Kuma Abbah zai tashi da yardar Allah! Ba za mu bar shi ba!…”
Ammy ta ɗago, ta ga Islam da Arfat riƙe da tagwaye!
Cikin tsananin mamaki da rawar murya ta ce, “Yara na! Waɗannan kuma…? Ina uwar tasu?”
Islam cikin jin haushin Amal ta ce, “Mun barta a gida. Ba za ta yarda ta zo ba.”
Ammy ta yi shiru, ta fahimci cewa rikicin bidiyon ya raba kan Maleekh da Amal.
Maleekh ya shiga ɗakin Abbah. Abbah yana kwance, ya ƙazantu da na'urorin jinya. An tabbatar da cewa zuciyarsa ta ɗan tsaya ne, kuma na'ura ce ke riƙe da numfashinsa. Likita ya sanar da su cewa zai ɗauki lokaci mai tsawo kafin ya farfaɗo.
Maleekh ya zauna a gefen gadon, ya riƙe hannun Abbansa mai sanyi. Hawaye na zubo a idanunsa saboda rashin adalci da azabar da Abbansa ke fuskanta.
Maleekh yana magana cikin raunanniyar zuciya.
“Abbah! Ba zan taɓa yarda cewa kai ne ka aikata wannan ba! An yi maka sharri a ƙasar nan, kuma an yi maka sharri a cikin zuciyar masoyiyata! Amma na rantse da Allah, za mu wanke ka! Zan yi amfani da kowane irin ƙarfi da Allah ya ba ni don in fito da gaskiya! Ka sani cewa yaran nan suna nan! Ba zan bari kaddarar cin amana ta raba mu ba!”
Maleekh ya sumbaci hannun Abbansa, ya ƙuduri aniyar fara yaƙi da makircin duk wanda ya aikata haka..
Bayan wasu awanni, Amal ta gaji da kallon bidiyo mara ƙarin bayani. Ta ƙuduri aniyar samo gaskiyar al’amarin da kanta. Haka ta koma gidanta tare da Inna.
Bayan ta isa,
Inna ko kallonta bata yi ba saboda fushin yadda Amal ta zargi Alhaji Abdul-Majeed da iyalansa..
Inna cikin sanyin murya ta ce, "Kin fasa tafiyar ne? Meyasa kika dawo? Ina jariran?”
Amal cikin gajiyar zuciya ta ce,
“Suna wurin Maleekh. Ya dawo...”
Inna ta zabura! Farin ciki ya shige ta! Ta san cewa yanzu Allah ya ba ta damar yin amfani da shaidarta ta gaskiya ga mutumin da ya dace..
Inna ta zabura, ta yafa mayafinta ba tare da ko kallon Amal ba ta ce,
“Maleekh ya dawo? Yana ina?!”
Amal ta bata amsa a takaice “Yana asibiti wurin Abbansa.”
Inna ta fita a guje! Ta ɗaura niyyar sanar da Maleekh gaskiyar al'amarin. Ta san cewa Amal tana da ƙaramar ƙwaƙwalwa kuma ba za ta fahimce ta ba. Yanzu Maleekh ne shugaban gida, kuma shi ne wanda zai iya fahimtar komai...
_NEXT NEXT NEXT_
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 91 to 92
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
A cikin Abuja, zanga-zangar ta yi ƙarfi saboda zargin Alhaji Abdul-Majeed da kisan kai. Hakan ya sa go-slow ya tsananta, kuma Inna ta makale a hanya.
Amal kuwa ta damu matuƙa da jariranta da Maleekh ya riƙe, sannan ga Inna bata dawo ba. Tana ganin Maleekh ya ɗauke su don fansa saboda zargin da ta yi masa.
Misalin ƙarfe 8 na dare, Amal ta nufi asibiti ganin bazata iya jure kwana ba tare da jariranta ba..
A daidai lokacin da ta isa, sai ga hargowa! Wuta ta kama a wani ɓangare na asibitin. Makiyan Abbah ne suka turo 'yan daba don su ƙona shi gaba ɗaya.
Mutane suna ta fitowa da gudu daga cikin asibitin. Ammy tana tura gadon da Abbah yake kwance kai, tana fitowa da gudu.
Wani ɗan daba ne ya fito da gudu da jarkar petur (gallon of petrol) a hannunsa. Ya wurgar da ita a gaban Amal da ke tsaye.
Amal ta ɗauki jarkar tana dubawa! Zuciyarta tana bugawa da mamakin dalilin da yasa za a ƙona asibitin!
Dai-dai lokacin da Amal ke tsaye riƙe da jarkar petur, Maleekh ya iso da gudun gaske a motarsa.
Inna ma ta iso a lokaci guda da mai Napep bayan sun samu wurin wucewa.
Amal kamar wacce aka daskarar da ita, tana tsaye riƙe da jarkar petur a hannunta, tana kallon wutar da ke ci.
Nan take, kowa ya zagaye ta!
Inna cike da mamaki da zargi ta furta “Amatu! Yanzu ƙiyayyar taki har takai ki ƙona asibitin kowa-da-kowa ya mutu? Har zaki zo ki kashe Alhaji Abdul-Majeed?…”
Amal ta zaro ido tana kallonsu! Ta kasa cewa komai. Makirci ya karya ta lokaci guda..
Ammy tana kuka da mamaki ta ce, “Amal! Kin zo ki ƙona Abbanku? Saboda kina tunanin shi ya ƙona iyayenki? Wani irin zuciya ne da ke haka?…”
Maleekh ya kasa magana! Zuciyarsa sai harbawa take da ƙarfi! Wani irin tsanar Amal ya shige shi! Ya tuna duk faɗan da suka yi, da yadda ta zargi Abbansa! Ya ɗauka ta shirya wannan ne don ramuwar gayya!
Nan motar agaji na ruwa ta iso, aka fara kashe wutar.
Maleekh ya tunkari Amal a fusace. Ya yi mata wani irin shaka mai ƙarfi, ya shake mata wuya sosai yana zaro manya idanunsa.
“Macuciya! Kin zo ki kashe Abbana! Kin so ki hallaka iyalaina!…”
Amal ta ɗage numfashinta! Da ƙyar take jan numfashi, tana riƙe da hannun Maleekh da yake sha'ke da wuyanta.
Idanun Maleekh sukayi jawur saboda fushi da raɗaɗi. Motar ‘yan sanda (Police) ta iso nan take..
Daƙyar aka janye hannun Maleekh daga sha'kar da yayi mata, cikin fusata ya sake ta. Ya kalli ’yan sanda, ya yi umarni da ƙarfi cikin zafin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 56 Chapter of 62