sonta? Ra’ayina ne. Tinda ba wanda zai zauna mun da ita. Kuma duk munafikin da yazo ya sanar miki wallahi sai nayi maganinsa.”
Ammy ta yi tsaki sannan ta miƙa masa hannu:
“Bani wayarka nan.”
Ba tare da musu ba, Maleekh ya ciro wayarsa ya bata.
Ammy ta kalle shi sannan tace:
“Wannan wayar nayi sizing ɗinta!”
Maleekh ya yi dariya kawai, ya ratsa ta gefenta, ya wuce sama kai tsaye zuwa part ɗinsa.
Ammy tana tsaye da wayar a hannunta cikin huci.
Sai ga Farha ta shigo tana laɓe, ta tsaya ta ji duk hirar su.
Da ta ƙaraso kusa da Ammy tace cikin lallashi:
“Ammy, don Allah ki bani wayar. Nasan Amal zata ƙira shi. Ina so in caccaki durun uwarta a daren nan.”
Ammy ta yi murmushin mugunta, ta miƙa mata wayar sannan ta wuce part ɗinta.
Farha kuwa ta riƙe wayar tana murna, ta fice zuwa ɗakinta.
Ta zauna tana jiran ƙira daga Amal, zuciyarta cike da shirin tada rikici...
Misalin ƙarfe goma da rabi na dare, Amal ta gama shiryawa cikin nutsuwa. Ta ɗauki wayarta, zuciyarta cike da ƙaunar Maleekh, ta ƙira lambar shi domin ta yi masa magana kafin ta kwanta.
A ɓangaren Maleekh kuwa, wayar tana hannun Farha da ke zaune a ɗakinta tana jiran wannan lokacin. Da taga sunan Amaleekh a jikin screen ɗin, ta danne dariya, sai ta ɗaga da sauri, ta kai kunne tana shirin caccakar ta, ta ce
“Hello matsiyaciya, wani irin rashin mutunci ne zaki ƙira wayar mijin Aure na. Ke waca iriyar marar zuciya ce?” Farha ta yi magana da kakkausar murya.
Amal ta yi shiru na ƴan daƙiƙu, ta ɗan yi murmushi sannan ta ce cikin lafazi mai tsauri...
“Ke yarinya, kina sauraron kanki kuwa? Kin san da wa kike magana? Ni ce Amal Voice, wacce idan ta yi magana ana sauraro a jihohi da dama, ba wai don ina son a ji ni ba, a’a, don kalamaina suna da nauyi.”
Farha ta yi tsaki sannan ta ce
“Kina yi min ihu da wannan sunan banza naki? To wallahi ba zan taɓa barinki ba. Ni ce matar Maleekh, na fi ki komai, daga asali har ƙarshe.”
Amal ta yi dariya mai sauti, sannan ta mayar mata da martani .
“Farha, ki ji tsoron Allah. Soyayya ba da ƙarfi ake jantaba. Ni da Maleekh mutu-karaba ne, babu wanda zai iya tsayawa tsakanin mu. Ke ana soyayya dole ne? yace baya so, please ki rabu dashi ba, ko har sai kin masa fyade kafin hankalinki ya kwanta? kawai ki sa a ranki zuciyar shi ta riga ta zaɓe ni. Kuma idan zuciya ta zaɓi abu, babu sarauta, babu iko, babu kuɗi da zai iya hana hakan.”...
Farha ta yi rau-rau da ido tana cizon yatsa saboda takaicin yanda Amal ke gasa mata magana cikin natsuwa...
Amal ta ƙara da cewa:
“Ke ki bi hanyarki daban, amma wallahi idan kika cigaba da shigowa tsakanin mu, sai kin gane cewa bana wasa da yara irinku. Karki manta ni ƴar jarida ce, na san kalmar da zata zame miki tukunyar zafi. Ina da harshen da zai iya tsinewa mutuncin duk wanda ya tsaya mun a gaba. Amma ban zo yin faɗa da ke ba, kawai ina sanar miki gaskiya ne. Ke da Maleekh ba wani abu bane, haɗin bai yi ba sammm, ni kuma da shi, kalmar da ke tsakanin mu: shine Mutu-karaba.”
Ta kashe ƙiran a nan, ta bar Farha sai huci take tayi...
Farha ta cije baki, hawaye suka cika mata ido saboda takaici. Ta furta cikin tsawa:
“Wallahi Amal, sai na ga bayan ki. Ko da zai zame min mutuwa, ba zan bar ki ki more wannan soyayya ba. Sai dai mutuwa ta rabaki da Maleekh.”
Amma zuciyarta ta tabbatar mata da abu guda ɗaya, Amal ta fita iya magana, ta fita iya nuna ƙarfin zuciya. Wannan ne abinda yafi mata ciwo fiye da komai...
Farha tana gama wayar da Amal, zuciyarta ta cika da wutar haushi. Tayi saurin miƙewa, da sauri ta sauƙa falo, zuciyarta cike da muguwar manufa. Ba tare da wani tunani ba, ta nufi part ɗin Maleekh...
A hankali ta zuƙo key ɗin da aka ɗaura a jikin ƙofa. Ta tsaya jim kaɗan tana runtse ido, tana jin zuciyarta na bugawa kamar ana wasan doki. Sai ta janyo ƙofar ta saka key ɗin, ta jiyo “Klik!” alamar ta kulle shi daga waje...
Tayi murmushin mugunta, tana jin kamar ta yi nasara. Da sauri ta janye key ɗin daga ƙofar, ta riƙe shi a hannunta sannan ta juya ta nufi nata part ɗin.
Tana tafiya tana maganar zuci...
“Wallahi Amal, ni Farha ba zan bari soyayyarku tayi kwari ba. Tinda har kika raina ni zaki gane kuranki. Sai Maleekh yayi sati a kulle a ɗakinsa, ba zai ga fuskarki ba. Wallahi sai na hana shi fita, sai naga yadda soyayyarku zata dawwama a kulle.”
Ta ɗan tsaya a tsakiyar falon babban gida tana dafa ƙirji, hawaye na cika idonta saboda tsananin kishi. Sannan ta ƙara cewa a zuciya:
“Ke Amal, ba zaki taɓa cin nasara akaina ba. Idan da gaske ne ‘Mutu-karaba’ ne tsakaninki da Maleekh, to bari mu gani ko kulle ba zai iya raba ku ba. Wannan shi ne farkon shirin da zan ɗauka akan ki. Na rantse da rantsuwa, daga yau soyayyarki zata fara ruguje wa a idonki.”
Tana gama wannan tunanin ta nufi ɗakinta da murmushin mugunta a fuskarta, key ɗin na hannunta tamkar tayi wata gagarumar nasara.
Da asuba, Maleekh ne ya miƙe daga gado cikin nutsuwa. Ya ɗauro alwala a bathroom, sannan ya saka farin jallabiyarsa tare da riƙo misbaharsa, zuciyarsa cike da natsuwa da niyyar nufar masallaci...
Sai dai, da ya isa ƙofar falonsa ya murɗa handle ɗin ƙofar, ya juya da nufin buɗewa… “Klik!”
Ya ɗan tsaya, ya ƙara juyawa da ƙarfin gaske… amma sai yaji ƙofar tamau! Wani irin yanayi ya ratsashi lokaci guda.
Ya janye hannunsa ya matsa gefe, ya ƙara gwadawa. Amma ƙofar sai juyawa take, ba buɗewa!
Ya tsuguna ƙasa yana kallon ƙofar da kyau. Glass door ce, mai ƙyalli da ƙarfinsa, wacce idan aka kulle daga waje ba mutum da zai iya buɗewa daga ciki.
Zuciyarsa ta buga. Ya miƙe ya ɗan bubbuga ƙofar, sai dai babu wanda zai jiyo shi domin part ɗin nasa yana nesa da inda masu aikin gidan suke.
Numfashinsa ya ɗan rikice, sai ya dafe kansa. “Me ke faruwa haka?..”
Daurewa ya yi, ya koma ɗaki, ya shimfiɗa sallaya, ya yi sallar Asuba cikin ɗaki da zuciyar da ta cika da damuwa. Bayan ya iddar..
Sai ya zauna a gefen gado, ya haɗe hannuwa guri ɗaya, yana girgiza kai cikin ɗan murya:
“Wannan ya nuna akwai wani shiri da ake kullawa a kaina..."
A Ranar ya kwana cikin ɗaki, babu fita, babu ganawa da kowa. Abinci ma ba wanda ya kawo masa, sai ruwa kawai da ya ɗauko daga fridge ɗin ɗakin.
Yayin da yake zaune, zuciyarsa kullum na yawo wajen Amal. Tunani yake, ko dai ita ma an hana ta ganinsa? Ko kuwa har yanzu tana zaune cikin kwanciyar hankali ba tare da ta san halin da yake ciki ba?
A wancan gefen kuma, Amal ta tashi da safe cikin shauƙi. Tun kafin gari ya waye, zuciyarta na ta ɗokin jin muryar Maleekh kamar yadda suka saba. Tana ɗaukar wayarta ta ƙira shi, sai dai shiru. Kiran na shiga, amma babu mai ɗauka.
Ta sake ƙira sau biyu, uku… har ta ƙara a karo na biyar, amma babu amsa. Zuciyarta ta fara bugawa da sauri. Cikin ranta ta ce:
"Ko dai yana barci ne? Amma ko barci yake, da ya ji ƙiran wayata yake ɗaga wa. Me yasa yanzu shiru?"
Cikin rikicewa ta jefa wayar gefe, ta ɗan jingina da gado tana mai lumshe ido da tunani. Amma zuciyarta ta kasa samun natsuwa. Ta sake ɗaukar wayar ta ƙira, amma har yanzu babu amsa.
A gefe guda, Farha ce ke riƙe da wayar Maleekh tun daren jiya bayan ta kulle shi a ɗaki. Da ta ga ƙira daga Amal, zuciyarta ta ƙara ƙone wa da haushi. Ta ɗan bushe da dariyar mugunta, ta ajiye wayar gefe tana mai faɗin cikin zuciya:
"Kin yi fatan jin muryarsa ko? Wallahi yau sai kin shiga ruɗani, zaki sha mamaki. Zan koya miki how to respect someone."
Haka Amal ta wuni cikin damuwa, tana ɗaukar waya tana ƙiransa lokaci zuwa lokaci, amma babu alamar amsa. Zuciyarta ta shiga kullewa da tunani iri-iri.
🌹🌹🌹🌹
A gefe guda kuwa, Maleekh a ɗaki yana zaune kamar mai zaman kurkuku. Sai dai yayi sallarsa a ɗaki yayi wanka ya cigaba da zama, ya zauna yana ta nazari. Ga wayarsa kuwa bata kusa da shi, saboda tana wurin Ammy. Wannan yasa shi bai san cewa Amal na ƙiran shi ba...
Maleekh yana zaune a bakin gado, zuciyarsa cike da tunani mai nauyi.
Wayarsa Samsung Galaxy Z Fold 6, wacce kuɗinsa ya kai miliyoyi, bata wurinsa balle ya yi ƙira...
Ga ɗayar wayarsa iPhone 17 Pro Max ɗinsa wanda ya bar wa Amal saboda ya fi son ita ta riƙe shi...
Ya yi ƙasa da kai ya ɗan dafe goshinsa, sai ya tuna da laptop ɗinsa da yake a cikin jakar office. Da sauri ya buɗe jakar, sai ya tarar wayam. A ransa ya ce:
"Kai! Ashe na manta na bar laptop a office… da shi zan iya yin ƙira ko tura saƙo…"
Yayi firgit yana ɗan cakud'a sumar kansa, zuciyarsa ta shiga wani irin yanayi na tsarguwa...
Yana cikin wannan halin ne ya miƙe zuwa bathroom don yin wanka da alwala. Sai da ya fito ya tarar da kulolin abinci an jera masa tsaf a kan teburin ɗakin. Abin da ya ba shi mamaki shi ne—ba a kawo masa abincin ba lokacin yana zaune, sai lokacin da ya shiga bathroom kawai aka yi amfani da damar aka shigo aka ajiye masa...
Kafin ya kai hannunsa ga kulolin, sai ya ji motsin ƙofa. Da ya ƙarasa, sai ya lura an ƙara saka masa key daga waje.
Zuciyarsa ta dinga harbawa. Cikin ransa ya furta:
"Wannan wanne irin iskanci ne? Farha, nasan babu wanda zai mun wannan aika aika sai ke, ki tabbatar duk sanda na fito zamanki a gidan nan ya ƙare...."
A kwana a tashi yau an wayi gari, sati uku kenam Maleekh yana kulle, sai dai yaga an kai masa flask ɗin abinci...already yana da kayan drinks a frig dasu milk..
Cikin wannan lokaci, Farha ta fahimci yadda Amal ta shiga damuwa saboda ƙiransa da take ba ya ɗauka. Da mugun haushi ta ɗauki wayar Maleekh ta yi blocking ɗin lambar Amal, domin ta tsananta mata damuwa...
Amal kuwa…
Hankalinta ya tashi matuƙa. Sau da dama ta ƙira wayarsa, amma kullum babu amsa, yanzu kuma wayar bata shiga kwata-kwata...
Har ta kai ta kwana tana kuka da fargaba. Har ma ta saba zuwa kamfaninsa, tana tambaya ko ya zo. Amma kullum amsar da take samu ɗaya ce:
"Bai zo ba."
Ranar wata monday da ta sake zuwa, sai ta tarar da PA ɗinsa a bakin office. Bayan sun gaisa, Amal ta dubi fuskar sa da ta nuna alamar damuwa, ta ce:
"Don Allah, ina Maleekh ne? Kwanan nan wayarsa bata shiga, kuma ba ya zuwa kamfani. Na damu sosai."
PA ɗin ya kalli Amal cikin tausayi, sannan ya ce da ita
"Wallahi nima ban san inda yake ba. Na je har gidansu na tambaya, amma sai suka ce min bai da lafiya. Amma gaskiyar magana, ba wani bayani suka yi ba sosai."
Jikin Amal ya ɗauki rawa. Tana jin wani abu ya soke zuciyarta. Tace cikin firgici:
"Ina so na je gidansu yanzu, ko da zan ganshi daga nesa ne kawai."
Sai PA ya ɗaga mata hannu a natsuwa, yana faɗin:
"Kada ki je, Amal. Idan har kina son kwanciyar hankalinki, ki yi haƙuri ki jira. Ki bar shi, zai bayyana da kansa. Idan kika tura kanki can yanzu, zai iya rikitar da al’amura fiye da haka."
Amal ta yi shiru, hawaye na sauƙowa daga idonta. Ta jinjina kai a hankali, ta ce:
"Toh shikenan… zan jira. Amma wallahi zuciyata ta kasa natsuwa."
Da haka ta juya ta koma gida, jikinta babu ƙarfi, zuciyarta kuma na cike da ruɗani.
Tun daga ranar da ta ji labarin cewa Maleekh “ba shi da lafiya” hankalinta ya ƙara tashi. Cikin kwanaki biyu kacal, jikinta ya fara sauyawa, idanunta sun ƙara faɗuwa, fuskarta ta rame, har kasa cin abinci take sosai.
A daren wata Juma’a, tana zaune a falo tana ta kallon wayarta da ba ta daina ƙiran Maleekh ba, sai Inna ta shigo da hijab a jikinta. ta zauna kusa da ita, sai ta ce cikin tausasawa:
"Amal… me ke damunki haka? Kullum nakan ganki cikin tunani, abinci ba kya ci sosai, sai kuka da ƙiran waya… ke ɗin ba haka kike ba tun farko."
Amal ta runtse idonta, hawayenta na zuba, ta ce:
"Inna… zuciyata ta kasa natsuwa. Maleekh ya ɓace min gaba ɗaya, babu waya, babu saƙo. Aka ce ma wai ba shi da lafiya… wallahi ina ji kamar rayuwata ta tsaya cak. Ban san me ke faruwa da shi ba."
Inna ta kama hannunta da natsuwa, ta ce:
"Ki saurare ni, Amal. Ki tuna Allah ne ke da ikon rayuwa da mutuwa. Idan Maleekh naki ne, wallahi babu mai iya rabaku. Amma idan Allah ya rubuta wata jarabawa gare ki, sai dai ki ɗauke ta da haƙuri da addu’a. Ke dai kar ki bari zuciyarki ta ɓaci har ki sa kanki cikin rashin lafiya."
Amal ta share hawayenta, tana faɗin:
"Inna, kin san shi da kyau. Mutum ne mai son gaskiya, mai adalci, mai taimako. Ni da shi babu wanda zai iya rabamu, sai dai mutuwa kawai. Amma ganin shi bai ƙira ba, bai zo ba, ko ɗaya daga cikin ma'aikatansa ban ji wani sanar wa daga gare su ba… wallahi hakan na mun ciwo sosai."
Inna ta girgiza kai, ta yi murmushi sannan ta ce
"Ƴar jikalle na, ki yi tawakkali. Ki dage da sallah da addu’a. Kar ki bari wannan jarabawa ta karya miki zuciya. Zuciyar mace abar daraja ce idan ta kasance da haƙuri. Ki bari Allah ya fitar miki da gaskiya da hannunsa."
Amal ta jinjina kai, ta ce:
"Na gode Inna… zan yi ƙoƙarin jurewa. Amma Inna wallahi bana jin zan iya jurewa idan na rasa shi."
Inna ta lumshe ido ta ce:
"Allah ba zai bar ki ba, yarinyata. Idan har Maleekh naki ne, zai dawo hannunki da ikon Allah, babu makawa."
(Su Hajiya Inna kuɗi ya gyara tsohuwa 🤣🤣)
A Ɓangare guda kuwaa
Farha ta kwana da tunani mai nauyi, zuciyarta ta cika da hassada da ƙiyayya. Da daddare ta ɗauki wayar Maleekh ta shiga yin tracking inda Amal take. A zahiri kuwa, sai taga Amal na zaune da Kakarta a cikin wani gida mai kyau a Gwarinpa Estate...
Cikin jin haushin abin, ta ɗauki makiƙiyar shawara tana faɗin
“Wallahi zan je da kaina na same ta, zan sanar mata cewa......!." tasau murmushin mugunta sannan ta ce "ya bar ta da mummunan kunya.”..
Washegari, ta nufi Gwarinpa da motarta, bayan ta parked a gefen titi, ta sauƙa cikin izza kamar wata sarauniya. Tana tafe tana gyagygyara ɗan ƙaramin mayafinta sai kamshin perfume take... Ta iso bakin get, ta fara knocking da ƙarfi...
Mai gadi ya fito cikin alfarma yana tambaya:
“Madam, daga ina? Waye kike nema?”
A gadarance Farha ta watsa masa wani irin kallo tare da ɗaga gira ta ce:
“Ka buɗe mun kawai, ban son surutu. Gidan masoyina ne, ni baƙuwa ce ta musamman.”
Mai gadi ya harare ta, ya ce:
“To ai bazan bar ki shiga haka kawai ba. Sai na je na sanar wa masu gidan. Idan sun ce a shigo dake, sai ki shigo.”
Ya juya da sauri ya nufi cikin gidan, ya sanar da Amal cewa akwai wata “baƙuwa mai tsiyar tsiya” tana wajen get.
Amal, wacce ke zaune a falonta cikin tsananin tunani, ta ce a shigo da ita.
Ba a jima ba, sai ga Farha ta shigo cikin izza tana tauna chiwgum, tana wani irin taku kamar wata sarauniya. Amal kuwa ta miƙe tsaye cikin jin haushinta, tana harararta da idanun da ke huci kamar wuta...
Amal ta ce da ita cikin tsawa:
“Ke kuma fa? Me ya kawo ki gidana?”
Farha ta kyalkyale da dariya ta ce:
“Gidanki? Kin tabbata gidanki ne? Ko gidan Maleekh? Ki sani ina da cikakken right in shigo nan domin nan gidan masoyina ne.”
Amal ta taka zuwa gabanta cikin izza ta ce:
“Ki tambayi kowa! Wannan gida nawa ne, ba na kowa ba. Ni ce mai shi!”
Farha ta runtse ido tana dariya ta ce:
“Gidan da ya gina da kuɗinsa kike ce wa naki? Kina da hankali kuwa?”
Amal ta girgiza kai ta ce cikin karfin hali:
“Duk da haka dai, nawa ne! Tunda takardun gidan da sunana a jiki. Kar ki raina mun hankali.”
Farha ta yi tsaki, ta ciro wata takarda daga jakarta ta miƙa mata. Invitation card ce... A jikin card ɗin kuwa, sunan Maleekh ne da nata aka rubuta a matsayin ango da amarya.
Cikin izza ta ce:
“Ga shaida! Muna gayyatarki zuwa party bikin mu a mako mai zuwa. Ki tabbatar kin halarci wurin.. saboda kuwa idan ‘yar jarida ta zo, bikin zai ɗauki armashi sosai.”
Amal ta zaro ido, zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi, hawaye suka taru a idanunta. Amma kafin ta yi magana, Farha ta yi murmushi mai cike da mugunta, tana jin daɗin ganin halin da Amal ta shiga.
Amal tana hawaye ta ce cikin rawar murya:
“Ƙarya kike yi, munafikar banza! Maleekh ba zai taɓa cin amanata ba. Kin yi ƙarya matsiyaciya, ƙarya kike makaryaciya!”
Farha ta ce tana ɗaga hannu:
“Ƙarya kuma? To ga shaida a hannunki! Idan ba gaskiya ba ne, wannan meye?”
Amal ta riƙe card ɗin tana huci, tana kuka har fuskarta ta fara yin jawur abinka da farar mace. A fusace ta zabura, ta hankad'a Farha da ƙarfi. Farha ta faɗi ƙasa ta ɗan yi ihu...
Amal kuma cikin tsawa ta ce:
“Ƙarya ne! Ke munafuka ce!”
Farha ta tashi tana huci kamar wata zakanya, ta kai wa Amal mari da ƙarfi...
Amal itama bata tsaya ba. Cikin hargowa ta ɗaga hannu ta maida mata da mari ta hagun, ta ƙara zabga mata wani marin a gefen fuska ta dama, ta ƙara zabga mata mari sau uku a jere. A take Farha ta riƙe kumatunta, ta yi ƙara, sannan ta zube ƙasa sumammiya!
Amal ta tsaya tana haki, zuciyarta na bugawa, tana kallon Farha da mamaki da takaici a lokaci guda...
Amal ta tsaya tana haki, zuciyarta kamar zata fito ta bugi ƙirjinta. Idonta ya sauƙa kan Farha wacce ta zube ƙasa ba motsi..
Amal ta yi saurin dafe kai, tana furta cikin rawar murya:
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un… me nayi haka? Na kashe mutum? Ya Allah ka tsare ni da jarabarnan!”
Ta durƙusa kusa da ita tana jijjigan ta, amma Farha ko motsi bata yi ba. Amal ta yi saurin ɗauko bottle ruwan sanyi a frig tana zuba mata amma Farha ko motsi...kuka ne yaci karfinta kamar ruwan sama...
Tana faɗin
“Farha! Ki tashi don Allah. Ni ban nufin kashe ki ba. Na yi fushi ne kawai. Don Allah ki buɗe idonki, ki tashi ki yi min bala'i kamar yadda kika saba yi… ki ce munafuka kamar yadda kika saba faɗa. Ki tashi ki faɗa min cewa Maleekh naki ne! Don Allah kar ki barni cikin wannan hali…”
Amal ta fara jijjiga hannayenta, zuciyarta na harbawa da tsoro. A zuciyarta ta fara jin cewa lallai ta jefa kanta cikin babban haɗari.
“Idan har ta mutu fa? Za su ce ni na kashe ta saboda soyayya da Maleekh! To shin wace kotu zata yarda da ni?”
Cikin tsananin fargaba ta miƙe tsaye tana tafiya a falo tana ƙiran:
“Inna! Inna ki zo ki taimake ni! Na shiga uku… Innaaa!”
Sai ta dawo kusa da Farha tana kallonta, zuciyarta ta kasa yanke shawara: ta ƙira ‘yan sanda ko kuma ta ƙira Maleekh kai tsaye?
Amal ta ɗauki wayarta da sauri, hannunta na rawa. Tana danna lambar Maleekh, sai ta tuna cewa wayarsa tana hannun Ammy ko Farha, kuma tuni an yi blocking ɗinta.
Wannan tunanin ya ƙara girgiza ta. Ta kalli Farha da idanuwanta da suka cika da hawaye, ta furta cikin muryar kuka:
“Wallahi ba nufin kashe ki nayi ba. Ni ‘yar jarida ce, ba azzaluma ba. Amma wannan haɗin baki da ƙaryar da kika kawo, sai kika jefa ni cikin jarabawa.”
Amal tana cikin wannan halin sai ga Inna ta dawo..
Inna ta dawo daga kasuwa tayo siyayya, ta tarar da Amal a cikin wannan halin ga Farha a sume a ƙasin carpet, nan masu aikin gidan su biyu duk suka shigo falon jin ihun Amal, kowa hankalinsa yayi matuƙar tashi...
Ana ta watsa wa Farha ruwa amma bata motsa ba, Amal tana ta jijjiga ta amma ko motsi...
Anan ta ƙara fashewa da kuka tana faɗin
"Farha ta mutu na shiga uku. Wazai taimake ni, ni Amal marainiyar Allah. Tazo ta sanar mun cewa wani sati bikinta da Maleekh, kenam Maleekh yaudara ta yayi? Maleekh ya ci amana taaa, ga na shiga tsaka mai wuya nayi kisan kaiii..."
Har zuwa dare Farha tana kwance ko motsi...
Maleekh yana can ɓangarensa a kulle shima ya shiga damuwa matuƙa ganin sa a halin da bai taɓa shiga ba, na kullen da ya ga kansa a ciki, tsawon sati uku yana kulle...
Ammy ganin dare yayi bata ga Farha ta dawo ba yasa ta fara ƙiran wayanta...
Wayar Farha ne ya fara ringing.
Amal tana dubawa taga Ammy ta bayyana a screen ɗin wayar.
Amal ta ƙara ɗora hannu akai tana kuka tana faɗin
"Na shiga uku naaaa..."
Amal tana kallon wayar da ke ringing, sunan Ammy a jikin screen ɗin yana yi mata haske kamar an saka mata wuta a kai. Hannunta haka yake rawa, idanuwanta sun yi jajir saboda kuka.
Masu aikin gidan suka tsaya a gefe suna kallo cikin firgici, ba su san abin da za su yi ba. Inna kuwa ta tsaya cak tana rike da ledar siyayyar ta, ta kasa motsawa.
“Amal, ki ɗaga mana ƙiran nan! Koma dai menene, ki bari gidansu su san halin da ake ciki...” Inna ta furta cikin rawar murya.
“Ban isa ba Innaaa! Ban isa na ɗaga ba! Na shiga uku... wallahi na kashe ta, na kashe Farhaaa... idan Ammy ta sani fa? Wane ido zan sake duban duniya?” Amal ta ƙara fashewa da kuka tana bubbugan Farha, ta rufe fuskarta da hannuwa...
Wayar sai ringing take yi, ƙiran bai yanke ba. A ƙarshe ɗaya daga cikin masu aikin gidan ta ƙaraso ta ɗaga, cikin murya mai rawa ta ce:
“Assalamu alaikum Hajiya...”
Ammy ta ɗaga da sauri, cike da damuwa ta ce
“Wa alaikumus salam, ina Farha take? Tun da rana ban ganta ba, yanzu kuwa wayarta ba ta ɗauka ba... me ke faruwa ne?”
Mata mai aikin gidan ta kalli Amal, tana jiran amsarta. Ita kuwa ta soma girgiza kai tana kuka, tana faɗin:
“Kada ku gaya mataaa... don Allah ku ce tana lafiyaaa...”
Ammy ta sake cewa da ƙarfin murya:
“Ku gaya mun gaskiya! Ku gaya mun inda Farha take yanzu!”
Amal ta ƙara ɗora hannu akai tana kuka tana faɗin,
"Na shiga uku naaaa..."
Inna dake tsaye ta zabura da sauri ta karɓi wayar daga hannun mai aiki zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Batare da wata-wata ba ta ɗaga ƙiran....
Ammy ta kuma cewa..
"Hello… Farha! Ina kika shiga tun safe baki dawo ba?" Cewar Ammy daga can ɓangaren muryarta cike da damuwa.
Inna ta ɗan kalli Amal wacce take rawar jiki tana kuka, sai ta ce cikin ɗan ɓatar murya
"Uhmm… ehh… wai don Allah ku zo yanzu da gaggawa… an samu matsala ne… kiyi sauri ku taho kafin mu rasa rai a hannun mu."
Cikin firgici Ammy ta jefa tambaya,
"Wai me ke faruwa? Lafiya dai? Ki faɗa min gaskiya, lafiya Farha ce?!"
Hannu Inna ta ɗora akai, ta kalli Farha da ke shimfiɗe ƙasa kamar gawa, babu motsi. Sai tace cikin rawar murya...
Inna tsabar ta rikice cikin rawar murya ta ce
"Lafiya ba ta da kyau… kiyi sauri ki taho yanzu, don Allah…"
Cikin razana Amal ta sake fashewa da kuka tana faɗin,
"Wannan masifar da ta same ni ina zan saka kaina? Ni Amal na shiga uku, Allah ka cece ni…"...
NEXT NEXT NEXT....
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 62