Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mu tafi ko bakya so..." Nan Maleekh ya ji do musu akwatuna... Ba a ɓata lokaci ba, aka nufi filin jirgi. Duk tafiyar ta Maleekh ta cika da hawaye da addu’a. Yana cikin jirgi, hannunsa na riƙe da hotonta a wayarsa, hoton da take dariya da idanu masu cike da kyalli... “Amal, ki tsaya ki jirani... don Allah kar ki barni.” ✈️ A Abuja Da suka sauƙa, Abbah ya sanar cewa su fara zuwa hospital. Ammy ta ce "Ni kam zan wuce na gaji.." Abbah ya ce "Sai mun je kinga halin da sirikar ki take.." Ba yanda ta iya haka ta haƙura. Kai tsaye hospital suka nufa cikin gudu da motar da aka kawo musu airport.. Jikin Maleekh sai rawa yake, zuciyarsa kamar zata faso ƙirji.. A bakin ƙofar asibiti, likitoci da nurses ne suka cika wurin, haka suka kutsa ciki, Maleekh yana shiga kowa ya tsaya kallonsa saboda hotunansa sun bazu a kafafen labarai, kama shi da akayi a london sakamakon miyagun kwayoyi da aka gani a jakarsa... Abbah ne yayi magana da cewa: “Excuse me! Where is Amal Abdulsamaad? The accident victim from last night!” Wata nurse ta ce: “Room 204… but sir, her condition is very critical.” Suka nufi ɗakin kamar zasu fira.. Ita kuwa Ammy a nutse take takun ta.. Abbah shima dakatawa yayi sakamakon wata Nurse da ta sanar musu cewa "Ku ɗan dakata ana duba majinyaciyar, ga can wurin zama..." Kafin ta ƙarasa Maleekh har ya buɗe ya shige ciki. Abbah girgiza kai yayi yana mamakin ɗan nasan da taurin kai. Haka suka nufi wurin zama kafin ayi musu iso.. Bayan ya shiga, Maleekh ya tsaya cak.. Amal na kwance cikin farin zanin asibiti, fuskarta duk raunika ga an zagaye kanta da bandeji, jinin da aka ɗaura mata ya kusan ƙarewa.. Hankalinsa a tashe ya ƙarasa kusa da ita ya riƙe hannunta, muryarsa na rawa: “Amal… kina ji na? It’s me… Maleekh. Don Allah ki buɗe idonki… kar ki barni.” Nurse dake kusa ta ce: “Bamu da isasshen jini, kuma jinin nata AB positive ne mai wuyan samu, wannan ma da ƙyar muka samu, yanzu muna neman ledar jini uku.”.. Maleekh ya miƙe, yana faɗi cikin murya mai ƙarfi: “Ni O- ne. Ku ɗauki nawa! Ku ja jini daga jikina yanzu! Don Allah ku ceto ta!” Nurse ta kalle shi da mamaki: “Kai ne za ka bayar?” “Eh! Ba tare da tunani ba. Ku fara yanzu!” Maleekh ya ce yana jan ye hannun rigarsa... Ɗakin ya cika da sanyin AC, duk da haka gumi ke keto a goshin Maleekh saboda tashin hankali. Amal tana kwance, oxygen a hancinta, jini na gudana daga bututun da aka haɗa a hannunta.. Likita ya fito daga wani ƙaramin ɗakin dake cikin room ɗin da sauri yana faɗin "Meke faruwa anan?..." Nurse ce ta sanar masa cewa. "Sir wannan ɗan uwanta ne yazo..." Maleekh ya ce "Me kuke kike jira ne? Ki ja ki farfaɗo mun da ita..." Doctor ya kalli Nurse sannan ya ce "Kun yi ne akan zaki ja jininsa? Sannan kin sanar masa adadin jinin da ake buƙata ne?.." Nurse ta sunkuyar da kai cikin kikkina ta ce "Sir. Shi ya ce a ja ukun..." "Mtssww you are not serious..." Doctor ya ce tare da kallon Maleekh ya ce... “Mun jira babu wanda yazo a cikin ƴan uwanta, meyasa sai yanzu? Shin baku damu da ita bane?...." Maleekh ya goya hannayensa akan ƙirji ya ce "Look Doctor! Kar ka nemi ka gaya mun magana, yanzu haka daga London nake, a yau nake jin labarin, kuma ni mijinta ne..." Doctor ya ce "Okay! Bamu da isasshen jini, kuma jinin nata AB positive ne, wanda yake da wahalar samu a halin yanzu. Wannan ma da ƙyar muka samo leda ɗaya, yanzu muna neman ledar jini uku kafin ta iya farfaɗowa gaba ɗaya.” Maleekh wanda ke tsaye yana fuskantar Doctor ya ce cikin murya mai ɗaure kai, “Nurse ta mun bayani. Amma taya AB zai yi wahalar samu? Jini na O-negative ne, ku janye daga jikina yanda zai iya mata..!” Likitan ya kalle shi da mamaki, “Amma Sir Maleekh, jinin O- yana da tsada sosai ga jikin mutum, kuma jini leda uku bazai jitu da lafiyarka ba. Zai iya raunata zuciyarka.” Maleekh ya ɗan ɗaga murya cikin ƙarfi, idonsa ya cika da hawaye, “Na ce ku janye! Tunda rayuwarta tana cikin haɗari, babu wani abu da ya fi muhimmanci fiye da ta rayu. Ku janye ku bata tunda jinin nan da kuke gani yana gudana ne saboda ita!” Likita ya tsaya na ɗan lokaci kafin ya ce, “To shikenan, amma dole mu lura da lafiyarka. Wannan haɗari ne, sai mu shiga can bangaren ka kwanta bayan an gama don a saka drip ɗin ƙarfi a jikinka.” Dake room ɗin babba ne, ya kwanta a ɗan nesa da ita wanda glass ne ya tare tsakaninsu..amma yana iya hangota ta cikin glass ɗin... Maleekh ya ɗan murmusa cikin damuwa, yana duban Amal daga nesa ta cikin gilashin ƙofar d'akin jinya, “Ina roƙon Allah ya karɓi wannan jinin ya mayar da shi da albarka a jikinta. Ko da zan rasa rayuwata, ta rayu kawai.” Likitan ya girgiza kai da tausayi, “Wannan soyayya ce mai haɗari, amma Allah ya sa ta tashi lafiya.” Sai aka ɗauki bututun jini aka haɗa da hannun Maleekh, zuwan jinin a cikin bututun yana fitowa a hankali. Maleekh ya lumshe ido, jikinsa yana rauni amma zuciyarsa cike take da natsuwa. A gefe, Ammy da Abbah suka shigo cikin gaggawa. Bayan nurse ta sanar dasu halin da ake ciki... Suka shiga Ammy ta nufi Maleekh da gudu. Ammy ta ce cikin rawar murya, “Me ya faru da shi? Me yasa aka haɗa shi da na’urar jini?” Likitan ya kalle su cikin ladabi, “Yana ba wa Amal jini ne, saboda babu wanda yake da jinin da ya dace da nata.” Abbah ya tsaya ya goya hannayensa akan ƙirji, yana kallonsa da idanu masu cike da ƙauna da damuwa, “Maleekh… ka cika jarumta. Amma me yasa baka faɗa min ba kafin ka yanke wannan hukuncin?” Maleekh ya buɗe ido a wahalai, ya ce cikin rauni: “Abbah… idan na rasa jini saboda ita, to hakan ma bai kai na rasa Amal ba.” Ɗakin ya ɗauki shiru na mintuna biyu, sai ƙarar na’urar jinin da ke motsi, tana nuna ana cigaba da tsotsar jinin. Likitan ya kalli ma’aikata ya ce da sauri, “Ku kula, kada ku wuce pints biyu kawai. Wannan jarumin zai iya faɗuwa a nan idan kuka wuce.”.. Bayan mintuna talatin, aka sake ɗaura wa Amal jinin da aka ja daga Maleekh... Doctor yana kallon Maleekh ya ce "ka jira zuwa nan da awa 5 za'a sake jan na biyu.. Maleekh ya ce "Ni kam ku cire gaba ɗaya bana son jinkiri, 2 pints ku ka ce, sannan 3 ake buƙata kuma kun cire 1..." Doctor ya ce, "Sorry..." Kafin ya ƙarasa Maleekh ya katse shi da "Sorry for what?..." Doctor ya cigaba da jan jinin kamar yanda ya buƙata... Jinin Maleekh yana shiga cikin Amal a hankali, likita yana kallon monitor ɗin zuciyarta. Sai suka ga bugun zuciya ya fara motsawa a hankali. “Doctor! Heartbeat is rising!” “Keep it steady. Don’t stop the transfusion!” A cewar wata Nurse... Maleekh juyar da kansa yayi cikin damuwa yana tuna abubuwan da suka faru a tsakaninsa da Amal.. Haka al'amura suka cigaba da tafiya... Bayan doguwar suma na kwanaki uku, Amal ta fara motsi. Idanunta sun fara buɗewa a hankali, Inna da Abbah dake ɗakin, ba ƙaramin farin ciki suka yi ba, suna hamdala cikin nutsuwa... Likita ya shigo, ya dubi lafiyarta da bugun zuciyarta. “Lafiyarki tana nan, amma za ki buƙaci hutu da kulawa sosai,” in ji likitan. Amal kuwa ba abunda take faɗi illa ƙiran Maleekh: “Ina ya Maleekh? Ina yake? Ina son ganinsa...” Ganin ta damu da ganin shi, Abbah ya ɗauki waya da gaggawa, ya ƙira Maleekh. Bayan wasu mintuna kaɗan, sai ga Maleekh ya shigo cikin haɗa rai. Fuskar sa cike da damuwa, idonsa na nuna nauyi da ƙiyayya, tunanin hoton da ya gani na Amal da kuma ganinta akan gado da Zayd a ɗaki ya cika ransa da rikici. Amma zuciyarsa ta ɗan tsaya: zai amince ya aure ta bisa umarnin Abbah, duk da cewa yana son Amal sosai. Maleekh ya zauna a gefen gadon asibiti, bai kalli Amal ba. Kamar yana ɓoye wani abu a zuciyarsa, ya nisanci kallonta da duk wani murmushi da zai iya bayyana. Amal ta ɗan yi motsi, ta gane cewa shi ne ya shigo, sai hawaye suka gangaro mata tare da murmushi mai rauni a bayyane akan fuskar ta. Ta riƙe hannunsa tana jin ɗumin jikinsa, tana jin ƙaunar sa da kewar sa... Maleekh ya yi ƙoƙarin daidaita numfashinsa, bai jan ye hannunta ba haka ya daure yana danne fushinsa. Daga baya, Inna da Abbah suka tashi suka bar ɗakin, suka basu wuri su biyu kaɗai.. Amal ta ɗan motsa, idanunta suka haɗu da na Maleekh. Hawaye suna gangarowa amma fuskar ta na cike da farin ciki. Ta miƙa hannu ta shafa fuskarsa tana wasa da gemun... “Maleekh… kai ne?..." Ya ce "Uhm! Uhm bani bane...ke ce.." "Wallahi na daɗe ina kewarka…” Ta ce tana murmushi... Maleekh ya ɗan kalleta ta wutsiryar ido, bai amsa da tsawo ba. “Hmm…” Amal ta ɗan yi murmushi, tana jin ɗumin jikinsa. “Na yi kewarka sosai… watanni da babu kai…” Maleekh ya kawar da kai gefe, yana ɗan lumshe idonsa. “Ba komai…” Amal ta ɗan yi dariya, ƙaramar muryarta na rawa ta ce: “Na yi tsammani zan rasa ka, har na firgita…” Maleekh ya ɗan girgiza kai, amma bai yi magana mai tsawo ba, sai ya ce: “Ki tsaya… lafiya nake yanzu.” Amal ta ɗan yi murmushi mai rauni, ta rungume hannunsa da ƙarfi, tana jin kamar komai zai daidaita yanzu. A cikin shiru, Maleekh ya ɗaga murya da cewa “Meye dalilin hatsarinki?” Amal ta ɗan ɗago, muryarta na rawa saboda raunin jinyar: “Ban san dalili ba… me yasa ina yawan ƙiran ka, amma ba ka ɗauka?” Maleekh ya kawar da kai gefe, yana murmushi cikin natsuwa ya ce “Uhm… nothing.” Amal ta ɗan kalli fuskar sa, da bai nuna wani abu ba. Haka suka zauna, yana amsa mata magana sama-sama, cikin shiru mai cike da nauyin zuciya. Maleekh yana ƙoƙarin ɗaukar damuwarsa, yana tunani akan abin da ya gani a hoton da aka ɗauka. Amma a zuciyarsa, akwai ƙauna mai ƙarfi ga Amal sai dai bai bayyana hakan a halin yanzu, saboda damuwa da haushin abin da ya gani. A gefe guda, Amal kuwa tana jin ƙarfin zuciya saboda ganin sa a gefenta, duk da raunin jikinta, tana jin kamar komai zai daidaita... Hannu yasa ya ɗaga ta daga kansa dake yana zaune ne a bakin gadon da take. Ya kwantar da ita akan gadon. Cike da mamaki take binsa da kallo ganin ya ɗaga ta daga kansa. Amma haka ta sharar.. “Inaso na aure ka… please, yaushe ne auren mu?” Maleekh ya ɗan danne zuciyarsa, haushin ganin ta cikin wannan yanayi da kuma tunanin abinda ya gani, yana lumshe ido ya ce: “Kina kwance a hospital za’ayi auren?” Amal ta ɗan girgiza kai, tana jin sautin kamar ba Maleekh ɗinta ba: “Ko baka sona yanzu?” Maleekh cikin fusata ya ce: “Please ki kyale ni da wannan shirmen nakin…” Amal ta ɗan ƙira sunansa cikin raunannen murya: “Ya Maleekh…” A wannan lokacin, Abbah, Inna, da Islam suka shigo cikin ɗakin. Abbah yana murmushi, idonsa kan Amal ya ce: “Ƴata, kwantar da hankalinki. Mun dawo ne da shirin auren ki da Maleekh.” Lokaci guda Amal ta ruɗe, tana ƙoƙarin sauƙa daga kan gado: “Da gaske Abbah? Muje a ɗaura yanzu, dan Allah… banaso Ya Maleekh ya sake kubuce mun.” Abbah ya ɗan saki murmushi, yana mai sassauta yanayi: “Ki yi haƙuri. Maleekh yana nan tare da ke. Ki bari sai kin ƙara samun sauƙi tukun ko…” Amal gaba ɗaya ta ruɗe, zuciyarta cike da gaggawa ta ce: “A’a Abbah, na samu sauƙi yanzu ma… muje kawai!” Tana miƙe wa sai hajijiya ya ɗauke ta ga ƙafarta a ɗaure da bandeji. Maleekh da sauri ya rungume ta, idanunsu suka haɗu. Sun tsaya a haka na ɗan lokaci, suna kallon juna cikin shiru, daga bisani suka dawo cikin nutsuwa. Maleekh ya kwantar da ita a gadon tare da faɗin: “Ki shiga taitayinki fa…” Ya juya ya fita daga ɗakin, idanunsa suna ɗauke da haɗin damuwa da kulawa. Amal ta tsaya kallon bayansa har ya ɓace. Inna ta ɗan murmusa, tana kallon Amal: “Ai nasan yaran suna ƙaunar junansu, shiyasa suka tsaya kallon juna…” Amal a hankali ta furta: “Abbah… me yake faruwa da Ya Maleekh ne?” Abbah ya ɗan saukar da murya, yana mai sassauta murya: “Ki bar shi, ai kinsan ya fito ne daga cell, shiyasa. Amma in ya nutsu, hankalinsa zai dawo…” Amal ta ɗan yi shiru, idonta a shanye kamar mai jin bacci, amma zuciyarta na jin ɗumin soyayya da ƙarin aminci ga Maleekh.. 《》《》《》《》 Babban falon gidan su Zayd.. Zayd yana cikin tashin hankali, zuciyarsa cike da damuwa da fushi akan hatsarin da Amal tayi. Ya tsaya, idonsa akan mahaifinsa ya ce: “Dad, meyasa zakuyi haka? Kun yanke hukunci ba tare da sanina ba, meyasa bazaku iya barin Amal da rayuwarta ba? Meye laifinta? Ka tura mutanenka su je su buge ta da mota, to Allah ya cece ta, bata mutu ba…” Alhaji Wadata ya kalle shi cikin fuska mai nuna rashin fahimta: “Meye damuwarka da ita?” Zayd ya ɗan girgiza kai, zuciyarsa cike da ƙarfin hali da soyayya ya ce: “Ni ma sonta nake. Inaso nayi takara da Maleekh akan soyayyar Amal. Dan Allah kada ku sake yunkurin kashe ta. Bata cancanci haka ba…” Alhaji Wadata ya ɗan ɗauke kansa, yana mai nuna tsauri: “Mutuwar Amatullah ya zama dole. Idan bazaka iya ganin mutuwarta ba, ka koma London…” Zayd ya kalli mahaifinsa cike da kwarin gwiwa ya ce: “Idan har ina raye, bazan taɓa barin haka ba… Duk abubuwan da nake mata inayi ne saboda na rabata da Maleekh, sannan a tsorata ta, amma banda mutuwa…” Alhaji Wadata ya ɗan nuna fushi a fuskarsa sannan ya ce: “Kana jayayya dani ne?!” Zayd ba tare da ya tsaya ba ya juya ya bar falon. A wannan lokacin, mahaifiyarsa, Hajiya Sa’adatu, ta sako baki cikin shiri da tsauri: “Alhaji, nayi wani tunani. Tinda Zayd yana sonta, a barta da rayuwarta, yayi duk abinda zai yi ya rabata da Maleekh. Kai kuma, Alhaji, sai ka raba mahaifin Maleekh da kujerar siyasar da yake nema. Ita kuma, yarinyar Amal, da zaran Zayd ya aureta, anan ne zamu musguna mata, sai muyi mata duk abinda muke so…” Alhaji Wadata ya ɗan hango fuskar Hajiya Sa’adatu, yana mai nazarin shawarar: “Wannan shawarar taki tayi. Alhaji Abdul-Majeed daga wannan kujerar zai nemi kujerar governor, kuma ni zan nema. Don haka, zanyi takara dashi, shi kuma Zayd yayi takara da ɗansa ta wurin soyayya. Inaso na gansu kullum a ƙasa…” A wannan lokaci, Farha, wacce yanzu ta dawo daga prison, Maleekh ya ciro ta, ya kawo ta har gidan iyayenta anan Abuja. Tana tsaye a bakin ƙofa, duk taji tattaunawar da sukayi tin daga farkon da Zayd yayi har ya bar falon da shawarar da iyayen natan suka yanke.. daga baya kuma Maleekh wanda ya kawo ta ya tsaya fitar mata da jakakkunanta da siyayyar da yayi mata. Ya iso wurin da take a tsaye. Ya tsaya a gabanta, ya ce: “Ki buɗe mu shiga ciki mana…” Farha ta ɗan tsaya, duk ta rarrame tayi baƙi, ta buɗe ƙofar, suka shiga cikin gidan. A falo ta tarar da iyayenta. Hajiya Sa’adatu ba ta iya ɓoye farin cikinta ba, ta tafi da gudu ta rungumi Farha tare da faɗin: “Wayyo, Daughter na, ta dawo! Allah na gode maka, nayi farin ciki sosai da ganinki...” Alhaji Wadata shima, idonsa cike da farin ciki, ya dubi ‘yar sa sannan ya ce: "Your welcome my daughter.." Maleekh ya dube su dakyau sannan ya ce, “Ga ƴar ku nan. Na ciro ta daga prison, daga nan muke yanzu. Ku cigaba da riƙe ƴar ku sannan ku ja mata kunne akan shiga shirgin da bai shafe ta ba…” Maleekh ya juya, idonsa cike da kulawa da tsaro, ya fice daga falon. Alhaji Wadata ya tsaya a wurin, yana kallon Maleekh cikin wani irin kallo mai cike da nazari, tsauri, da kuma ƙiyayya na abin da zai yiwa Maleekh... Zayd ya shiga dakinsa, zuciyarsa cike da tunanin Amal. Ya zauna a bakin gadon, ya ɗaura hannunsa kan fuskarsa, yana mai ƙoƙarin kwantar da hankalinsa, amma duk da haka, zuciyarsa ta kasa kwanciya.. Zayd cikin zuciyarsa yake faɗin: “Ban taɓa jin mace mai zaƙin yawu kamar Amal ba… tun ranar da ta fito daga gidan ta har zuwa yau, gaba ɗaya ta mamaye tunanina. Sumbata ɗaya ya gamsar da ni, zuciyata ta tsumu… Muradina yanzu shi ne, sumbatarta ko da sau ɗaya… domin idan hankalina ya kwanta, zan iya mallakar ta gaba ɗaya...” Rufe idonsa yayi, lokaci guda tunaninsa ya koma wurin lokacin da suka kasance a baya, lokacin da Amal ta tsinci kanta a hannunsa a cikin dare, sumbatarta ɗaya kawai ya ratsa zuciyarsa kamar wutar lantarki. Ya ji kamar komai ya tsaya cak, zuciyarsa tana taƙaicewa, a hankali yake furta. “Yanzu kullum sai nayi mafarkin Amal… Kullum… Duk lokacin da na kwanta, dole sai na yi mafarki cewa mun zama ma’aurata. Ba zan iya barin tunaninta ya tafi ba, duk lokacin da nayi mafarkin ta dole sai na yi wankan tsarki... please Amal kada ki lalata mun zuciya da tunaninki da mafarkin ki.…” Ya saki dogon numfashi, idanunsa sun yi jawur, yana kallon bango kamar wanda ya tafi dogon tunani mai zurfi. Duk cikin dare, zuciyarsa tana tashi da wani irin salo na ƙaunarta, tana nuna masa irin son da yake yi wa Amal, son da bai taɓa ji a rayuwarsa ba. Ya jingina kansa a bango, idonsa a rufe, yana mai ƙoƙarin kwantar da hankalinsa, amma zuciyarsa ta ƙara tsunduma cikin mafarki da tunanin Amal... Duk dare ɗaya, Zayd yana cikin wannan hali: kewarta, son ta, da kuma tsoro kada wani ya aure ta... 《》《》《》《》 Maleekh ne ya shigo falon gidansu, ya tarar da Ammy ita kaɗai zaune a kujera tana kallon TV. Ya yi murmushi a hankali, ya zauna kusa da ita, idonsa cike da nutsuwa. "Ammy, bazaki ce wani abu akan batun aurena da Amal ba?" Ammy ta ɗan juyar da kai, tana mai shafa hannayenta cikin natsuwa, sannan ta ce: "Maleekh… to mezance? Har cikin zuciyata bana ƙaunar Amal, kuma bazan taɓa kaunarta ba. Amma ba yanda na iya… dole na haƙura ku auri juna. Duk faɗan da yafi ƙarfinka, sai ka mayar shi wasa. A dalilin haka Farha take prison, zumunci ya yanke a tsakanina da ƴan uwana gaba ɗaya. A dalilin Amal kaima ka faɗa hannu har kayi zaman cell a ƙasar da ba naka ba, kullum tashin hankali, kullum damuwa, duk akan wannan yarinya. To tinda haka ne, gwara kawai kuyi auren. Allah ya bada sa'a, ya baku zaman lafiya… Ni bazance komai ba." Maleekh ya sauƙe dogon numfashi, idonsa ya yi ja, ya ɗan jingina kansa a jikin kujera. "Abbah yana son haɗin nan… amma ina bakya jin haushina? Domin banaso ki rinƙa kwana da damuwata." Ammy ta kallesa cikin murmushi mai taushi, ta ce: "Ko kaɗan bana jin haushinka, Maleekh… akan meye to? Nayi maka addu’ar fatan alkhairi." Maleekh ya ɗan murmusa, ya ce: "Shikenan, Ammy… sannan zan gaya miki cewa na sa an fitar da Farha daga prison. Yanzu haka na kaita gidan da iyayenta suke." Ammy ta ɗan yi tsalle cikin farin ciki, idonta na walwali ta ce: "Da gaske Maleekh? Ai kuwa nagode! Zumunci zai dawo. Amma meyasa baka fara kawota nan ba?" Maleekh ya yi shiru, sannan ya ce cikin nutsuwa: "Gwara ta je can kawai… bana son damuwa." Ammy ta ɗan saki murmushi, idonta cike da nishaɗi: "Shikenan, ni zan je gidan nasun na gano ta. Duk da nasan da wuya zumuncin ya dawo kamar da… amma zan je." Maleekh ya kalli Ammy, idonsa na nuna damuwa da kulawa, amma bai faɗa komai ba. Kansa a jingine da kujera, zuciyarsa cike da tunani akan yadda zasu magance halin da Amal take ciki da kuma zaman lafiya a tsakanin su gaba ɗaya..... _NEXT NEXT NEXT_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 69 to 70 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Bayan Sati Biyu Hasken rana yana sauƙa a hankali daga taga. Amal tana zaune a kan kujera cikin doguwar riga street gown mai launin pink, jikinta ya nuna alamun samun sauƙi, amma idanuwanta cike yake da damuwa.. Inna itama na zaune a one seater suna kallo. Suna zaune suka ji ƙarar motar da ta tsaya a waje. A zabure Amal ta miƙe tare da leƙa wa ko Maleekh ne. Ganin Abbah ne yasa ta zo ta zauna. Ba'a juma ba sai ga mai gadi ya shigo yana cewa: “Inna, ga Alhaji minister ya iso…” Da sauri Inna ta miƙe tana murmushi, ta fito harabar gidan tana marabtar shi. “A’a Alhaji! Maraba da zuwa..” Abbah yana murmushi ya ce: “Ai inaso nazo amma sai dai aiki ne yake hanani zuwa. Yaya jikin Amal?” Inna ta amsa suka shige babban falo. Amal ta ɗan tashi daga zaune cikin ladabi, ta durƙusa, ta gaishe shi. “Sannu da zuwa Abbah… Allah ya saka da alheri.” Abbah ya ce: “Yauwa ƴata, kin ɗan ƙara kyau. Allah ya ƙara lafiya.” Amal ta ɗan lumshe ido, ta ce cikin muryar da ke nuna damuwa: “Abbah… tun ranar da na farfaɗo daga asibiti ban ƙara ganin Ya Maleekh ba. Sati uku yanzu, bai dawo wurina ba. Lafiyarsa kuwa?” Abbah ya ɗan yi murmushi, yana kallon Inna kafin ya kalli Amal: “Kar ki damu, ƴata. Maleekh ma baya jin daɗin jikinsa ne, shiyasa yake hutu. Amma yana ta kiranki a zuciyarsa.” Amal ta sauƙe numfashi, ta ɗan saki murmushi mai taushi. “Na gode Abbah. Ina roƙon Allah ya bashi lafiya.” Sai aka yi shiru na ƴan daƙiƙu, daga nan Abbah ya gyara zama, ya dubi Inna da nutsuwa: “Inna, abinda ya kawo ni yau kenan. Na zo neman auren Amal ga ɗana Maleekh.” Inna ta ɗan ɗago kai da mamaki, murmushi ya bayyana a fuskarta. “Mashaa Allah, wannan dai albishir ne Alhaji. Ai daman muna jiran wannan ranar. Insha Allahu zan sanar wa ƴan uwan mahaifinta dake Borno, su zo su karɓi auren ta.” Abbah ya yi dariya a hankali, yana girgiza kai: “A’a Inna, ba sai sun zo ba. Mu zamu je da kanmu. Mu ma muna son mu nuna girmamawa da ɗa’a.” Inna ta ce cikin farin ciki: “Wallahi Alhaji wannan magana ta yi kyau. Allah ya daɗa haɗa zumunci, ya tabbatar mana da alkhairi.” Amal tana sauraron su tana wasa da hannunta, hawaye na taruwa a idonta saboda farin ciki. Ta ce cikin muryar da ta cika da godiya: “Abbah… nagode sosai. Allah ya saka da alheri, Allah ya bawa Ya Maleekh lafiya da natsuwa.” Inna ta ce "Ke do Allah yi mana shiru, ke ko kunya bakya ji? Har da wani godiya? Kaiii yaran zamanin nan sun lalace. To a zamanin mu lokacin da za'a zo neman auren ka ma guduwa kake, kuma har ayi aure yarinya bazata yadda ta haɗa ido da miji ba balle uban miji..." Abbah ya yi murmushi mai ɗan taushi, yana kallon Amal da Inna cikin kulawa. “Amin ƴata. Insha Allahu komai zai tafi lafiya. Ki cigaba da hutawa, komai zai tabbata a lokaci mafi kyau.” Bayan tattaunawa da Abbah akan aure Inna ta lumshe ido tana kallon Abbah, muryarta ta ɗan canza cikin nutsuwa da tausayawa ta ce “Dan Allah Alhaji … ga amanar Amatu. Domin kai mahaifi ne a wurinta, kuma bazaka so wani abu ya cutar da ita ba. Kaima me karɓa mata aure ne a wani wuri… hakika kai aminin mahaifinta ne, kuma ɗan hannun damansa. Ban manta da kai ba tun daga

Chapter 45 of 62