yaro na!”
Amal ta miƙe a hankali, tana kallonta kai tsaye cikin ido ta ce
“Yaronki ne yake cikin rayuwata, ba ni ba. Don haka idan kin isa dashi ki dakatar da shi daga shiga rayuwata.”
Ammy ta yi dariyar raini ta ce.
“Hahaha, baki san kanki ba! Ke ce kika jawo rikici a cikin iyalai na. Kin faɗa rayuwar Zayd ma, sai kuma ki haɗa ƴan uwa fada? Maleekh ya daki ɗan uwansa saboda ke, kina so ki haɗa fitila a tsakaninsu ko?”
Amal ta haɗe hannuwanta a kirji ta ce
“Na bar komai ga Allah. Ni bana neman su. Su suke shiga rayuwata, ai ke uwarsu bai kamata ki yi mun jan kunne akansu ba, sai ki tuntubi yaranki ki ji...”
Ammy ta harareta, murya ta ɗan karye saboda ɓacin rai ta ce.
“Wato ke baki da kunya koh? Ni kike ɗaga mury? A gaban kowa?”
Inna ta tashi tsaye cikin tsawa ta ce.
“Ke! Ki kiyaye bakinki. Wannan gidan ba gidan ku bane. Idan baki da girmamawa, mu muna da shi. Ku kuna da arziki, amma baki san kanki ba! Ba komai sai girman kai da raini.”
Malam Yawale cikin tausasawa ya ce.
“Yar uwa, don Allah ku natsu...”
Zainabu ta ce
“Allah ya sa ayi zaman lafiya. Aure fa a hankali ake tattaunawa, ba da faɗa ba.”
Inna ta ɗaga kai da izza ta ce:
“Eh! Amal aure zatayi, zata bar Maleekh da shi Zayd ɗin. Ga wanda zata aura ɗan uwanta Kabiru.”
Ammy ta ɗaga hannu cikin farin ciki ta ce.
“To Alhamdulillah. Idan aure ne, ai ni na fi kowa farin ciki. Auren ya zama hanya ta rabuwa. Ke Inna, kina cewa za ku aura mata ɗan uwan ta ne?”..
Inna ta ce
"Eh gashi nan kuwa..."
Ammy ta ce
"Ai abinda nake nema kenam, nesa tazo kusa, daman ai Amal bata yi kala da yarana ba, ko da wasa kalar zaren ba kalar yadin bane, sun fi ƙarfin ta....kin ga kuwa talaka sai talaka, mai kuɗi sai mai kuɗi..."
Kabiru ya tashi a hankali, yana kallon Amal da murmushi mai nauyi ya ce.
“Ni ne Kabiru, Ba da gaggawa ba, amma idan Allah ya yarda, zamu zama dangi ɗaya.”
Ammy ta murmusa da mamaki ta ce.
“Alhamdulillah! Allah ya sanya alkhairi. Na fi kowa farin ciki, domin Maleekh da Zayd suma sunada wanda zasu aura. Ba matsala, ga ka kaima shushushu kamar ita, duk dai haka za'a ƙare da talauci...”
Zainabu ta ce
"Ai wannan gidan yafi ace gidan talaka ne, domin a masu rufin asiri ma da wuya su mallaki irin wannan kyawun gidan.."
Ammy ta kwashe da dariya tare da faɗin.
"Ohhh Ɗan ƙauye yazo birni, wato babu kalar wannan gidan a ƙauyenku ko? Daman taya zaku samu ƙauye duk bukkoki..."
Malam Yawale shima ya ce.
"Da za ki dubi asalinki kema talaka ce..."
Ammy tayi saurin cewa.
"Tirrrrr, wallahi ƙarya ne, ku je ku binciki asalina, ban tashi cikin talauci ba, kaff zuriya ta babu talaka..."
Kabiru ya ce.
"Amma Amatu itama ba talaka bace, du bi gidan da take zaune..."
Ammy ta harare su tare da faɗin.
"Abar dai kaza cikin gashinta, amma arzikinsu bai isa siya musu gidan anan ba..."
Ta juya tana hararar Amal ta fita cikin izza....
Bayan ta fita, Amal ta durƙusa a ƙasa tana hawaye. Inna ta tsaya ta kalleta cikin tausayi, sannan ta ɗan juyo ga Malam Yawale:
Ta ce.
“To ga yarinyar nan, kuje ku shirya yadda kuke so. Amma wallahi ni har yanzu zuciyata ba ta so wannan auren…”
Malam Yawale ya ce:
“Allah ya shirya, Inna Delu. Komai da lokacinsa. Amma mu ba da mugunta muka zo ba. Dubi wannan matar da ta zo ta wulakanta ku akan yaronta, shin haka za'a aurar da Amatu a danginsu?...”
Ɓangare Maleekh..
Maleekh ya kashe wayarsa gaba ɗaya yanda babu wanda zai same shi...
Bayan kwana biyu ansa ranar bikin Amal, sauran sati ɗaya...
Abbah ne ya ziyarci Amal, ya zauna a falo shi da Amal su biyu, ta durƙusa ta gaishe shi...
Ya gaisa da sauran mutanen gidan har da Inna, daga baya aka basu wuri..
Anan Abbah yayi mata fatan alkhairi akan bikin da zata yi. Yayi mata nasiha akan ta dage da addu’a, ta zauna a gidan mijinta lafiya tayiwa mijinta biyayya.
Sannan ya bata hak'uri akan wulakanci da Ammy ta zo tayi musu domin a shigowarsa Inna ta sanar masa..
Daga nan Abbah ya roƙe ta akan ta sanar masa yanda Maleekh yake.
Amal ta sanar masa yana old villa...
Daga nan sukayi sallama.
Abbah kai tsaye ya wuce can yanda Maleekh yake..
Abbah ya sameshi shi kaɗai a daji yana rayuwarsa..
Dare ne, fitilar villa kawai ke haske. Maleekh na zaune a waje, cikin sanyi, yana kallon sararin sama. Fuskar sa cike da tunani da gajiya. Sai ga security ya kawo Abbah...
Security yayi sallama sannan ya ce.
“Sir, ga babban Alhaji, Abbah…”
Maleekh
Ya miƙe da mamaki ya ce.
“Abbah?”
Abbah Ya karasa kusa da shi, yana kallonsa cikin kulawa ya ce
“Eh, ni ne, yaro na. Na ji shiru baka koma gida ba, shine na zo in ganka da kaina.”
Maleekh ya sauƙe numfashi sannan ya ce:
“Abbah... bana so kowa ya damu da ni. Nayi nisa da rayuwar mutane, yanzu ina so in huta kawai, daga komai aiki, soyayya, tashin hankali, komai.”
Abbah ya zauna kusa da shi, cikin tausasawa ya ce.
“Na gane, amma hutu ba yana nufin gudu daga gaskiya bane. Rayuwa bata tsaya saboda ciwon zuciya, Maleekh.”
Maleekh ya juya gefe yana kallon wuta.
“Ba ciwon zuciya bane, Abbah… wannan yanke zuciya ne. Na rasa amincewa da kowa. Kowa yana neman wani abu daga gare ni. Amma ni ina neman nutsuwa kawai.”
Abbah ya girgiza kai sannan ya ce.
“Yaro na, kai namiji ne, kuma jagora. Ka koyi rike kanka. Amma kar ka kulle kanka a cikin daji kamar wanda ya gudu daga duniya. Na zo ne don in tabbatar da kana lafiya, ba don in tilasta maka komai ba.”
Maleekh ya ce.
“Abbah, ina da bukata ɗaya…”
Abbah ya ce
“Meye hakan?”
Ya ce.
“Ka bar ni a nan. Kada ka sanar wa kowa inda nake, hatta Ammy. Inason in huta. In har zuciyata ta dawo daidai, zan dawo da kaina.”
Abbah
Ya yi shiru na ɗan lokaci sannan ya ce cikin natsuwa.
“To, idan hakan zai ba ka kwanciyar hankali, zan yarda. Amma ka ɗauki tsaro. Zan bar maka maza biyu su taimaka maka a nan.”
Maleekh
Ya ɗan murmusa kaɗan sannan ya ce.
“Nagode, Abbah. Ka san kai kaɗai ne mutum ɗaya da zuciyata bata iya ɓoye masa komai.”
Abbah
Ya dafa kafaɗarsa “Karka manta da addu’a, Maleekh. Idan ka rasa kowa ka nemi Allah, zai baka nutsuwa fiye da duniya baki ɗaya.”
Abbah ya miƙe, ya kalli villa sannan ya fita cikin shiru. Maleekh ya zauna yana kallon fitilar villa, idanunsa suka cika da hawaye, yana furta a hankali:
“Amal... kin mayar da zuciyata gurɓatacciya… amma har yanzu... ina ji a jikina ba zan iya manta ki ba.”
Kwana biyu daga baya, ana gefe ana cigaba da shirye-shiryen bikin Amal da Kabiru, yayin da Maleekh ke zaune cikin dajin, ba tare da sanin komai ba. Wannan ya ƙara sanya bambanci tsakanin natsuwar da yake nema da rikicin da duniya ke shirya masa daga nesa...
NEXT NEXT NEXT...
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 55 to 56
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
A wannan rana ne kafin bikin Amal, Zayd da jin Amal zata yi Aure ya tayar da hankalinsa, sai gashi ya danna burki a ƙofar gidan cikin tashin hankali...
Knocking ya rinƙa yi maigadi ya buɗe masa, kafin maigadi ya yi wani magana Zayd ya fuu ya wuce ciki, sallamarsa shine "Pretty! Pretty!! Pretty ki fito, please ki fito. Pretty..."
Kabiru wanda yake bayi a flowowi ganinsa yasa ya dakata yana kallon Zayd wanda ya rikice..
Amal kuma daman a falo take zaune tana kallo, jin ƙira kuma alamun sun nuna mata Zayd ne, domin shine mai ƙiran ta da sunan..ta fito ta tsaye daga nesa, ta takarƙare cikin kayan gida masu launin shudi.
A hankali ta tako zuwa yanda yake kamar zai yi kuka...
Zayd cikin rawar murya, fuskarsa ɗauke da fushi ganinta yasa shi faɗin:
"Pretty… why? Kin tsani zuciyata haka ne? Kin manta da ni, da duk abinda ke tsakanina dake? Kin manta fa da soyayyar da na gina tun kafin duniya ta fahimceni.."
Amal cikin nutsuwa idanuwanta cike da hawaye ta ce:
"Zayd… soyayya ba ta isa ta rushe kaddara ba. Idan Allah ya rubuta abin da zai faru, babu mai canzawa. Ban tsane ka ba, amma wannan ba ƙaddarata bace. Kuma ai ba wai soyayya muke ba, ni na ɗauka mutunci ne a tsakanin mu, kuma taya zanyi soyayya da kai har kayi tunanin zan aure ka alhalin kana tare da Maleekh kuma ɗan uwanka ne, bari yau na sanar maka da baki na, ka riƙe a kwakwalwarka cewa 'Maleekh shine zuciyata, kuma wanda na so, wanda nake so har zuwa yanzu, ni ce yarinyar da ya yi break-up da ita..."
Zayd yana matsowa kusa, muryarsa na rawa ya ce:
"Na sani ai, Maleekh ɗin shi zai hanani soyayya da ke ne? Ba nono ɗaya nasha da shi ba balle kiyi tunanin wani abu, ni yanzu ba wai akan Maleekh nazo magana akai ba, tinda shima bata shi kike ba, aurenki zaki yi, kina cewa ƙaddara. To meye ƙaddararki? Wannan ɗan ƙauyen? (ya nuna Kabiru da yatsa) Wannan ne kika zaɓa akan ni, bayan na mayar da zuciyata gida gareki? Amal, kin fi haka wallahi!..."
Kabiru da ɗan zafi yana nuna Zayd da yatsa shima ya ce:
"Kai fa… ka kiyaye harshenka! Ni mijinta ne nan gaba, kuma ba ka da ikon tsoma baki a rayuwarta. Ka fita da mutunci kafin ka rasa shi.."
Zayd ya doke hannun Kabiru gefe yana faɗin:
"Mijin me? Ka san me ake nufi da love kuwa? Ka san menene ruwan da ke gudana a cikin jini idan zuciya ta kamu da kauna? Ba zaka fahimta ba, kai dai ka zo ne daga ƙauye da niyyar mallake abinda baka gina ba!.."
Amal ta ɗaga hannu cikin tsawa ta ce:
"Zayd! Ya isa haka. Ka girmama kanka. Ban taɓa rainaka ba, amma kar ka zubar da mutuncinka saboda ni. Ka dawo da hankalinka, Zayd — duniya fa ba ƙarama bace. Bayan ni akwai wasu..."
Zayd yana murmushi cikin ciwo ya ce:
"Duniya ba ƙarama bace, amma ni ma ba ƙaramin so nake miki ba, Amal. Ba zan iya jure ganin wani ya ajiye hannu a kan abinda zuciyata ta amince da shi ba..."
Amal tana hawaye, ta sassauta murya, ba komai ta tuno ba illa Maleekh, ta ce:
"To ka jure, Zayd. Domin rayuwa haka take tana koya mana haƙuri ta hanyar rashi. Ka bar ni na natsu. Allah zai baka wadda tafi ni a gareka.."
Zayd ya kasa daurewa, ya kauda kai yana jan numfashi ya ce:
"Wadda tafi ki? Babu wadda zata maye gurbin Pretty a zuciyata. Amma... (ya ɗaga kai yana kallonta da ido) …ki sani, ko da kin auri wannan ɗan ƙauyen, soyayyarki ba zata taɓa mutuwa a cikin zuciyata ba. Har abada..."
Kabiru yana tunkararsa cikin zafin rai ya ce:
"Ka fita kafin na sa ka fita da ƙarfi, munafukin burni!..."
Zayd yana murmushi mai ciwo, yana tafiya zuwa ƙofar fita ya ce:
"Ba sai ka tura ni ba Baƙauye... Sai dai ka kula da ita, kar ka karya mata zuciya kamar yadda na bari tawa ta karye..."
Ya juya yana kallon Amal a karo na ƙarshe. Ya ce
"Goodbye… Pretty...."
Zayd ya fice cikin hanzari, ya buɗe ƙofar da ƙarfi ya buga ta da ƙarfi. Amal ta tsaya cak tana kallo, hawaye na zuba a fuskarta. Kabiru ya kalleta da damuwa, amma ta kauda kai cikin shiru....
Kafin Kafin Kabiru yayi magana ta juya da gudu ta koma ciki...
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🩷🩷🩷🩷🩷
🌹🌹🌹🌹
An hallara a wurin event, an ƙawata shi da fitilu masu walƙiya, ƙamshi ya cika wurin, kowa cikin ado da farin ciki, sai kiɗan walima da yake tashi a hankali..
Aisha (ƙawar Amal): ta matso kusa da Amal tana murmushi ta ce.
“Amal kin zama kamar sarauniya wallahi, wannan gown ɗin ya karɓeki fiye da kowacce mace da na taɓa gani.”
Amal ta ƙara gyara zaman gyalen tana murmushin ƙarfin hali, ta ce:
“Aisha… wallahi ban jin daɗi. Babu wanda yasan halin da zuciyata ke ciki. Na rasa Maleekh… wayarsa a kashe, ban san meya faru da shi ba.”
Aisha ta ce:
“To, amma ki daure. Karki bari kowa ya fahimci kina cikin damuwa, kowa yana kallonki a matsayin amarya mai sa’a.”
Amal ta ɗan lumshe ido cikin murya mai rauni ta ce:
“Sa’a fa kika ce? Idan wanda zuciyata ke nema baya tare dani, meye amfanin wannan shigar, wannan walimar?”
Aisha ta ja numfashi sannan ta ce:
“Ki bar komai a hannun Allah. Wataƙila Maleekh zai bayyana kafin auren. Ban yarda zai iya ƙyale ki ba.”
Amal ta ce:
“Na roƙi Allah haka, Aisha. Amma har yau sati guda… babu labarinsa. Da na san haka zai faru, da ban barshi a can ba.”
Aisha ta riƙe hannunta tana rarrashi...
Aisha ta ce:
“To yanzu dai ki yi haƙuri, karki ɓata mana taro. Ga kowa yana kallonki. Abbah ma yana wurin shima yana alfahari dake kamar ƴarsa ta jini.”
A wannan lokacin Zayd ya shigo wurin event ɗin cikin suit mai tsada, idonsa cike da ɓacin rai. Farha ta hango shi ta ce da Islam da Arfat...
Farha ta ce:
“Ga Ya Zayd can, amma ya rame, kamar wanda bai san abin da yake yi ba.”
Islam ta ce itama:
“Ai duk saboda Amal, ya kasa manta ta, bai san duk soyayyarsa da Amal bai kai Yayana Maleekh ba...”
Arfat ta ce: “To ai yanzu ta zama matar wani, sai su haƙura...”
Zayd ya tsaya nesa yana kallon Amal cikin gown ɗinta, zuciyarsa na tafasa. Ya furta a hankali cikin haushi...
“Pretty… kina ta haskawa a gaban kowa, amma baki san zuciyata tana ƙone ba.”
Abbah ya hau kan stage yana ɗaukar mic, cikin murya mai cike da natsuwa ya furta..
“Assalamu alaikum jama’a. Na ƙira wannan walima ne domin bikin yarinya da na ɗauka kamar ƴa ta. Amal kyakkyawar yarinya mai tarbiyya da ladabi. Allah ya sanya albarka a rayuwar aurenki, ya muku albarka, ya sa zaman lafiya.”
(Kowa ya amsa da “Amin!”)
Ammy, Farha da Islam da Arfat suna zaune a tsararrun kujeru, Ammy ta ce cikin murya mai kaushi...
“Ai na fi kowa farin ciki yau. Wannan itace ranar da Maleekh zai farka daga mafarki. Yanzu yasan babu Amal a gare shi.”
Farha ta murmusa sannan ta ce:
“Zan je na gaishe ta, in ga yadda take da wannan farin cikin ƙaryar...”
Ta tashi ta ƙarasa wajen Amal da murmushi...
Cikin izza ta ce da ita.
“Amarya, kin yi kyau sosai. Amma kin san duniya juyawa take. Wasu lokutan abin da muka tsaya akai sai ya wuce mana.”
Amal ta kalleta kai tsaye cikin idanu sannan ta ce.
“Eh, haka ne. Amma kuma akwai wasu abubuwa da idan suka shiga zuciya… ko da duniya ta juya, ba sa fita.”..
Farha ta ɗan yi dariya ta juya ta koma wajensu Ammy...
A wannan lokacin kabiru yana gefen Amal yana ƙoƙarin riƙe hannunta amma ta ja hannunta gefe, idonta ya cika da hawaye. Aisha ta lura da hakan...
Aisha ta ce:
“Amal, ki daure, mutane suna kallo. Kada ki nuna rauni.”
Amal ta ce cikin muryar da ke karyewa.
“Ba zan iya ɓoye damuwata ba Aisha. Wannan walimar ana yi ne, amma zuciyata tana tafasa. Waye ya san halin da nake ciki?”
Aisha ta rungumeta tana faɗin “Shhhh…” tana rarrashinta. Kiɗan ya sake tashi, jama’a suna murna, amma a zuciyar Amal kamar ana binne mata rai a raye…
Cikin babban hall ɗin da aka kawata da haske da kyalli, sautunan walima da kiɗa na tashi a hankali. Kowa cikin farin ciki yake. Amal tana zaune gefenta Inna ce, fuskarta ba yabo ba fallasa duk da ta yi kyau fiye da yadda aka taɓa ganinta, zuciyarta na cike da nauyi...
Inna da murmushi tana kallon jama’a ta ce.
"Yau fa Allah ya tabbatar da burina. Gashi dai Amatu na ta zama Amarya.”
Halima ƙanwar Kabiru, itama ta sha kyau sosai..
Cikin wannan shagalin ne aka ji ƙarar ƙofar waje ta buɗe da karfi “BAAANG!” aka tsayar da kiɗan. Mutane suka juya da mamaki...
Arfat a tsorace ta furta:
“Wayyo Allah, meye haka? Waye ya buɗe ƙofa haka kamar ana faɗan daji?”
Farha ta ɗan saki kofin hannunta, ido a buɗe ta ce:
“Wait... na gane wannan buɗewar...!”
Cikin hayaƙi da ƙamshin turaren da aka saba jin yana biyo shi, Maleekh ya shigo. A sanye yake cikin baki suit, fuskarsa ɗaure, idonsa jajur kamar wanda bai taɓa bacci ba. Mutane suka fara yin kakkauce wa kamar hanya ta buɗe da kanta...
Wani daga cikin ma’aikata a hankali ya furta:
“Wannan fa Maleekh ɗin ne... oga Maleekh ne...”
Abbah ya miƙe da mamaki, yana tsoron yadda zai kasance:
“Subhanallah... Maleekh?”
Idanun Maleekh suka sauƙa kai tsaye kan Amal, tana zaune gefen Aisha da Inna, a ɗayan gefenta kuma Kabiru ne....
Shi kaɗai yake gani hasken hall ɗin, sautin mutane, komai ya daina motsi a kunnensa...
Maleekh a zuciyarsa, cikin murya mai zafi ya furta:
“Amal... har kike iya yin aure ba tare da kin ce min komai ba? Bayan soyayyar da na ba ki?”
Amal ta miƙe a zabure. Ta kasa tsayawa. Cikin zuciyarta kamar ana ja mata rai da zafi. Ta tattara doguwar rigarta mai sheƙi, ta fara gudu kamar wacce ta tsere daga mafarki...
Kai tsaye wurin da Maleekh yake tsaye ta nufa.
Tana ƙiran sunansa cikin kuka..
“Maleekh! Maleeeekh!!”
Mutane suka ɗaga kai suna kallon ikon Allah. Halima ta riƙe hannun kabiru tana faɗin "Ya salam!"...
Zayd kuwa ya tsaya a gefe yana kallo kamar wanda ake caccakar zuciya da wuka...
Kabiru ya tashi tsaye da mamaki yana faɗin.
“Wannan kuma waye, meye haka?”
Zaynabu ta dafe ƙirji ta ce:
“Laa ilaha illallah, wannan ai kamar amarya ta san shi sosai…”
Kafin a iya hanata, har ta ratsa cikin taron ta isko shi, ma’aikata da mutane suka tsaya suna kallonta.
Ta isa wurin ƙofar tana kuka, ta faɗa cikin jikin Maleekh, ta rungume shi da duk ƙarfinta tana kuka sosai..
“Ka barni haka… ka tafi ka ɗaure ni da kewar ka… me yasa baka dawo ba, Maleekh?”
Maleekh ya tsaya kamar dutse, hannayensa a buɗe.
Sai kuma a hankali ya rungumeta, zuciyarsa na harbawa da ƙarfi, ya ce a hankali cikin murya mai sanyi da raɗaɗi:
“Na dawo, Amal… na dawo kafin wani ya karɓe min ke…”
Amal tana rungume da shi murya na rawa ta ce:
“Maleekh... bazan taɓa manta wa da kai ba... wallahi bana son wannan auren...!”
Maleekh ya dafa kanta, cikin murya mai ƙarfi mai cike da ƙauna yana furta:
“Na sani... bana buƙatar jin komai daga bakin kowa, Amal. Ke tawa ce — har yanzu, har abada!”
[Kowa cikin mamaki yake kallo, wasu suna sharar hawaye, wasu kuma suna ƙaraɗa ido. Abbah ya sauƙe numfashi da ƙarfi. Ammy kuwa ta zuba masa ido cikin tsoro da fushi.
Zayd yana matse haƙora, yana faɗin cikin takaici:
“Daman... dama duk bata son mu. Ni da wannan da take cewa za ta aura. Dama zuciyarta tana wajen shi!”
Farha ta dafe kanta tana hawaye ta ce:
“Na faɗa muku! Wallahi wannan Amal ba mace bace... aljana ce kawai ta ɗaure masa kai!”
Abbah a hankali ya je kusa da Maleekh ya ce:
“Maleekh... ka yi hankali da abinda kake aikatawa. Wannan ba lokaci bane...”
Maleekh yana kallo cikin idon Amal ya ce:
“Abbah, lokacin da aka ɗauke min ita babu wanda ya tambaye ni. Yanzu kuma, ni ne na dawo domin karɓar abina.”
Amal ta dafe kirjinta tana kuka tare da faɗin:
“Dan Allah, kar ka sake bari na, Maleekh... kar ka barni...”
A hall ɗin kuwa hayaniya ta tashi. Ma’aikata da manyan baki suna ta magana, wasu na cewa a katse bikin, wasu kuma suna cewa “Soyayya kenan.”
Kabiru yana kallo cikin ɓacin rai ya ce:
“To ni fa, me kuke nufi? Auren fa nawa ne... amma yanzu sai gashi an kwace min amarya a gaban jama’a!”
Halima ta ce a hankali, tana kallon Kabiru:
“Yaya Kabiru... ni dai ina gani... wannan soyayyar ta fi ƙarfin ka.”..
Zayd ya buɗe baki yana huci, fuska cike da ɓacin rai, sai furta kalma ɗaya yake:
“To yanzu gaskiya ta fito fili… Ashe daga ni har shi ango bata sonmu… saboda shi ne a zuciyarta tun farko.”
Kabiru ya ɗaga kai cikin ɓacin rai ya kuma cewa:
“Wannan wace irin raini ne kuma a bikin aure? Wannan yarinyar ba ta da kunya!”
Inna ta taso cikin tashin hankali, tana faɗin:
“Amatu! Me kike yi haka a gaban mutane?! Ki sake shi ki dawo nan!”
Amal ta girgiza kai cikin hawaye, ta ce cikin murya mai rawa:
“Ba zan sake shi ba Inna… saboda shi ne zuciyata, shi ne rayuwata!”
Maleekh ya ƙara matse ta a jikinsa, yana kallon kowa a hall ɗin da idanu masu tsanani.
“Wanda bai ji ba yaji, Amal tawa ce… kuma zata zauna dani… babu wani aure da za’a ɗaura.”
Wurin ya hargitse.
Farha ta zaro ido tana faɗin cikin jin haushi:
“Ashe har yanzu bai bar ta ba! Wallahi wannan abun ya isa haka!”
Ammy ta miƙe a fusace, ta ce cikin tsawa:
“Maleekh! Karka raina mana hankali! Kai baka da hankali ne? Wannan talaka ce, baka isa ka tozarta iyayenka saboda ita ba!”
Amal ta ɗago kai tana share hawaye ta ce:
“Ammy, wallahi ban tozarta kowa ba, ni dai ina son Maleekh, kuma shi ne ya dawo gareni.”
Abbah ya tashi tsaye, yana ƙiran sunan Maleekh cikin natsuwa:
“Maleekh... ya isa haka. Kowa yana kallo, wannan abin da kuke yi a bainar jama’a ba dai-dai ba ne.”
Maleekh ya ce da muryarsa mai zurfi:
“Abbah, ni dai na faɗi gaskiya. Bana buƙatar auren Amal da wani. Idan hakan za ta faru, to wallahi sai dai ku ga gawata.”
Amal ta kalle shi tana kuka, zuciyarta cike da ruɗani da tsoro, tana faɗin cikin rauni:
“Ka rage zafin rai, Maleekh… don Allah ka saurare su…”
Maleekh ya riƙe hannunta sosai ya ce:
“Zan saurare su, amma ba zan sake ki ba.”
Shiru ya sake ratsa hall ɗin.
Kowa na kallo.
A yau, walimar aure ta koma farkon rikicin soyayya, alfahari, da zafi sun gauraya cikin zuciyoyin jama’a...
Da ƙyar Abbah ya ja Maleekh da Amal suka koma gida..
A babban falon gidan Amal suka hallara gaba ɗaya, bayan taron an watse. Iska tana busowa daga window, ɗan ƙamshin turaren flowers da aka kawata da su ya cika ɗakin. Amma babu wanda ke jin daɗin zaman.
Abbah ne ya zauna a babban kujerar tsakiyar falo, yana kallon Maleekh da Amal da suka zauna a gefensa. Inna da Malam Yawale suna gefe, Zainabu na lulluɓe da mayafi, Kabiru kuma yana zaune yana murɗa yatsunsa cikin rashin haƙuri.
Abbah ya gyara murya, ya ce da nutsuwa:
"To yanzu, tunda kowa ya zauna, ina so muyi magana cikin natsuwa. Wannan abin da ya faru yau, abu ne da ya girgiza ni. Amma ina so mu magance shi ba tare da tashin hankali ba. Maleekh, ka nutsu ka saurare ni."
Maleekh, da fuskarsa a haɗe, ya ce cikin tsananin murya:
"Abbah, me kake so in saurara? Bayan gobe za’a ɗaura wa Amal aure da wani? Amal ɗina? A gabana?"
Amal ta sunkuyar da kai, hawaye na gangarowa a fuskarta ta ce:
"Ina ruwana da duk wani abu da suka tsara, Abbah wallahi ban amince da wannan auren ba. Wallahi ni bana son Kabiru, kuma bana son in aure shi!"
Inna ta kalle ta da mamaki ta ce:
"Ke Amatu, baki da kunya? Wannan magana ce zaki furta a gaban manya? Ai ni da bakina na amince da wannan auren, kuma sai da na sanar miki kema, Meyasa tun farko baki ce bakya so ba? Sai da wannan yaron Maliku yazo ya hure miki kunne zaki mana tawaye? To wallahi auren nan ba fashi kin kuma san ikon da nake da shi a kanki."
Malam Yawale ya shigo cikin magana yana ɗan ɗaga murya ya ce:
"To ai dole ne a yi aure, auren zumunci
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 37 Chapter of 62