Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zai iya narke wa.” Amal ta kwaɓe baki, tana kallonsa da shagwaɓa ta ce “To Baby…” Maleekh ya yi dariya yana girgiza kai ya ce “Wannan sunan ya fi dacewa da ni in kiraki da shi, ba ke da ni ba. Kenan kin ɗauke ni jariri kenam?” Ta ce cikin dariya: “To Shalele…” Ya turo baki kamar mace, ya ce: “Ni ɗin mace ce?…Za ki sa ayi mun dariya wallahi.” Amal ta ɗaure fuska tana dariya a hankali ta ce “To Bee Heart…” Maleekh ya zaro ido, yana kallonta da mamaki ya ce “Meye Bee Heart kuma? Wani sabon kalma kika ƙirƙira ke kaɗai?.” Amal ta tintsire da dariya tana ce wa “Ƙudan zuman zuciya mana, ai soyayya ce…” Ya yi dariya sosai, yana kallonta da ƙauna ya ce “To a’a fa, ba zuciyar ƙudan zuma za ki ce, wannan sunan ko armashi babu....” Amal ta cije lips ɗinta, tana kallonsa da shagwaɓa ta ce: “Wayyo Allah, to kai ka zaɓa sunan da kake so. Honeybee, Sweet Bee, My Bee…” Kafin Maleekh ya ba da amsa, ƙofar ta buɗe. PA (manager ɗin kamfanin) ya shigo da gaggawa, amma da ya ga irin hirar soyayyar da suke yi, sai ya saki murmushi ya ce: “Na zaɓa masa! My Bee → tamkar ace masoyina, kai ne ƙudan zumana. Boss ɗina tamkar ƙuda ne mai addabar zuciyarki…” Amal ta tafa hannu da shewa, tana dariya sosai ta ce “Yeeeeeee! Gaskiya ne wallahi. You are my Bee 🩷🩷🩷” PA ya kunna kiɗa a ƙaramin speaker ɗinsa, ya ce: “Yau mu yi rawa mu sha soyayya!” Nan take Amal ta miƙe tsaye tana juyawa cikin nishaɗi, ita da PA suka hau rawa suna tikar rawa sosai, suna dariya suna zagaye ofishin. Maleekh kuwa ya zauna a kujerarsa yana kallonsu da murmushi, sai ya girgiza kai yana ce wa. “All of you are just childish.” Amal ta tsaya cak tana kallonsa cikin shagwaɓa, ta ce: “Mu ne yarinta ke damu, my Bee?..” Ya kalli idonta ya ce: “Eh mana! You’re all behaving like kids.” Amal ta yi tsalle tana dariya, ta koma ta ci gaba da rawa tare da PA. Maleekh kuwa ya juya yana duba computer ɗinsa, yana murmushi a ransa, zuciyarsa cike da ƙaunar Amal duk da shagwaɓarta. PA yana rawa yana ɗaga hannu sama, yana cewa: "Amal, ki ga yadda nake rawa saboda boss ɗina ya zama ƙudan zumanki. Ai yau zan yi mishi gasa a kan soyayyarki!" Amal tana dariya sosai har tana riƙe ciki, ta ce: "Ka shiga uku, ka isa kayi wa Yaya Maleekh ɗina gasa?" PA ya ɗan karkata kai yana kwad'a rawa, ya ce: "Ba Yaya Maleekh ba, My bee fa! Daga yau shi My bee, ni kuma zan zama your sugar manager." Amal ta fashe da dariya tana tafa hannu ta ce "Wayyo Allah! Sugar manager fa!" Maleekh wanda yake zaune yana bin su da kallo ya yi murmushin ƙarfin hali, amma a zuciyarsa sai yake ji kamar kada Amal ta dinga taɓa shi da barkwanci haka, saboda tsantsar soyayyar da yake ji gareta. Ya ɗan yi ƙasa da muryarsa yana cewa cikin zuciya: "Ta ina zan fara nuna mata yadda nake jin soyayyarta ya cika min zuciya? Ta ina zan bayyana mata cewa ban taɓa yin soyayya irin wannan ba?" Sai kuma ya ga PA ya kama hannun Amal suna juyawa cikin rawa. Nan fa Maleekh ya hargitso cikin tsananin kishi ya yi saurin tashi ya isa wajensu, ya ce da ɗan tsawa mai taushi: "Enough Amal!" Amal ta tsaya cak, tana dariya, tana kuma kallonsa cikin shagwaɓa ta ce "My bee… me kuma? Mu dai muna nishaɗi ne kawai fa…" Maleekh ya ja hannunta a hankali, ya sa Amal ta zube a jikinsa. Ya rungumeta sosai kamar ba zai sake ta ba, sannan ya lumshe ido ya ce a hankali cikin wayincewa: "Amal… ba nishaɗi kawai ba ne. Kin zama zuciyata gaba ɗaya. Kin zama numfashina. Kin zama dalilin farin cikina." Dariya ta tsaya a bakin Amal, idonta ya cika da hawayen farin ciki, Ta ce a shagwaɓe: "My bee… da gaske ka ke?" Ya ɗan haɗe goshinsa da nata, yana furta: "Eh Amal, da gaske nake. Na faɗa a karon farko, ki sani… ina sonki fiye da komai." PA kuwa ya ja bakinsa gefe yana kallon su da shagwaɓa ya ce: "To ai yanzu kun bani kunya. Na bar muku fagen soyayya… amma ku tuna dai ni sugar manager ɗin ku ne!" Suka kwashe da dariya gaba ɗaya. Bayan wannan ɗan nishaɗin soyayya, Amal ta yi murmushi ta kwace kanta daga jikin Maleekh, ta ce: "My bee, yanzu dai bari na wuce zuwa office ɗina kafin jama’a su fara ganin kamar ni ban da aiki sai soyayya kawai…" Maleekh ya ɗan kwaɓe fuska, cikin shagwaɓa ya ce: "To ai ni ne aikinki, ki zauna nan kawai." Amal ta yi dariya sosai har ta rufe baki da tafin hannu ta ce "Wayyo Allah, kai wallahi My bee kana da wasa. Amma bari na wuce, akwai report da nake son duba kafin broadcast ɗin yau." Ta kama hannunsa a shagwaɓe ta ce: "Za ka zo mu ci lunch tare da rana?" Ya kalli idonta yana murmushi mai zurfi, sannan ya ce: "Idan baki ƙira ni ba, bazan zauna da kowa ba. Dole Lunch ɗin yau ya zama tare da ke." Suka yi murmushi da juna, sai Amal ta juyo ta nufi office ɗinta... Shi kuma Maleekh yana shirin barin campany zai koma gida.. Da ta shiga, sai taga komai ya gyaru, an shirya mata sabuwar kujera, sabbin system, da flowers masu ƙamshi a gefen teburinta. Amal ta tsaya cak tana kallon komai da mamaki, sai ta ce cikin muryar da take rawa: "Subhanallah… wa ya shirya min haka?" PA wanda ya leƙo daga ƙofa ya ce: "Ni ne sugar manager, amma Boss ɗin ki ne ya bayar da umarni. Ya ce office ɗinki ya dace da irin darajar ki a matsayin Amal Voice." Amal ta runtse ido da murmushi, zuciyarta cike da daɗi, ta furta a hankali: "My bee… kai kaine komai nawa." Bayan Amal ta zauna a sabon office ɗinta, ta duba system ɗinta, sai ta ga an shirya mata speech ɗin da zata gabatar a yau a matsayin mataimakiyar shugaban kamfanin CashTalk FM. PA ya shigo da sauri, yana ɗauke da mic da camera crew. Ya ce cikin annashuwa: "Madam Amal, lokaci yayi, kowa ya shirya don broadcast ɗin yau a CashTalk TV. Jama’a dubun-dubata za su kalli muryarki." Amal ta ɗan ɗaga kanta da murmushi mai cike da kima, ta ce: "Alhamdulillah… wannan rana ce da bana tsammanin zata zo haka da wuri. Amma yanzu na shirya." Da aka kunna camera, aka fara live, Amal ta miƙe tsaye cikin kyan suturarta da kyakkyawar kwalliya ta manyan mata. Ta fara da cewa: "Assalamu alaikum wa rahmatullah. Ni ce Amal Abdulsamaad, a yau ina tare da ku a matsayin Executive Assistant to the CEO of CashTalk Group. Wannan rana ce ta musamman, domin ina mai sanar da ku sabbin shirye-shirye, manufofi, da tsare-tsare da kamfaninmu ya kawo domin ƙara haɗin kai, ƙarfafa ɗabi’ar gaskiya, da kuma bayar da damar fitar da muryar talakawa." Muryarta mai daɗi ta cika ɗakin, kowa ya tsaya kallonta, daga ma’aikata har zuwa masu kallo a gidajen su. An kawo camera kusa da fuskarta, sai ta ɗan murmusa ta ce: "CashTalk ba wai kamfani bane kawai, CashTalk Voice ce muryar ku, muryarmu, muryar gaskiya!" Bayan Maleekh ya koma gida, yana zaune a babban parlour ɗin su tare da Ammy da Farha. Da suka ga Amal a television cikin wannan kyan jawabi, sai Ammy ta yi tsaki mai ƙarfi ta ce: "Wallahi Maleekh ka bani kunya, har wannan yarinyar zaka sa a ranka haka? Har ta samu damar fitowa a TV tana magana a matsayin assistant ɗinka? Ka ji kunya wallahi" Farha kuwa ta buga ƙafa ƙasa ta ce cikin haushi: "Ba zan lamunta ba! Amal ce zata zama assistant ɗin mijina a gaban duniya? Wallahi bazan yarda ba!" Maleekh kuwa, maimakon damuwa, sai murmushi ya yi cikin nutsuwa ya ce: "Kuna iya jin haushi, amma ba za ku iya hana gaskiya fitowa fili ba. Amal is my choice, kuma duniya zata shaida hakan." Da Amal ta gama jawabi aka rufe shirin, nan take kowa a cikin kamfanin ya yi mata ihu da tafi. Wasu suka ce "Amal Voice is back! Amal ta dawo!" Social media kuwa ya hargitse. Hashtag ɗin #AmalVoiceReturns ya bazu. Kowa na posting hotonta, yadda take tsaye cikin nutsuwa, tana jawabi da murya mai ƙarfi da girmamawa. ☆☆☆☆ Kaduna Gidan rediyon Rayuwa FM (tsohon gurinta) Ma’aikata da tsoffin abokan aikinta suna kallo, suka tsaya da mamaki. Wata kawarta Maryam ta ce cikin hawaye: "Alhamdulillah! G Amal ɗin da aka zalunta aka kora ta hanyar cin hanci, Gashi yanzu ta koma babban matsayi a Abuja, assistant CEO!" Wani tsohon producer ya ce cikin jin kunya: "Rayuwa da gaske juyi-juyi ce. Mun ga Amal ta fāɗi fururu, yanzu kuma mun ga ta tashi tsaye. Yanzu mun ga ta zarce mu gaba ɗaya." Makotansu a Kaduna sun taru suna kallo a TV. Kowa sai mamaki da tafi. Wata tsohuwa ta ce: "Allah ya ɗaga darajarta. Yarinya mai gaskiya ba ta taɓa faɗi ƙasa har abada. Ga shi yanzu ta fi duk wanda ya zalunce ta." ☆☆Jawabin rayuwa Voiceover☆☆ Ana nuna hotunan Amal tun daga lokacin tana ɗan ƙaramin table a gidan rediyon Rayuwa FM, tana ɗauke da littafi tana rubutu da paper. Ana kuma nuna lokacin da aka koreta... Sai kuma a juya hoton zuwa lokacin yanzu tana tsaye a gaban camera a babban kamfani, tana jawabi cikin nutsuwa... Muryar narrator ta shiga: "Rayuwa tafiya ce mai cike da darussa. Wani lokaci tana jefa mutum ƙasa, wani lokaci tana ɗaga shi sama. Amal Abdulsamaad ta sha wahala, ta fuskanci zalunci, ta shaida cin hanci da rashin adalci. Amma ta ƙi fāɗuwa ƙasa. Yau, ga shi daga ƙaramin matsayi a Kaduna, zuwa babban matsayi a Abuja. Wannan shi ne rayuwa daga ƙananan ƙalubale, mutum na iya tsayawa ya ɗaga kansa har ya zama abin koyi ga duniya.".. Inna dake nan Abuja har da hawayenta ganin yanda ake ta yabon Amal.. daga talauci yanzu sun dawo masu dukiya.... Yau ranar weekend babu aiki Amal tana tare da Inna... Soyayya a tsakanin Amal da CEO Maleekh ya zurfafa sosai... A can gidan su Maleekh kuwa.. Saboda tsananin tsanar Amal da kuma ganin tana samun ɗaukaka ta sanadiyar Maleekh yasa Ammy ta fāɗi ƙasa ta tayar da bori... Ammy ta tayar da aljanun ƙarya sai ihu take tayi a gidan, ga Abbansu baya Nigeria.. Gaba ɗaya Ammy ta rikice gidanta da ihu.. Ammy ta na burgima a ƙasa tana ihu, tana zabura tana jifa maganganu irin kamar aljanu ne suke magana, tana faɗin "Zamu haukatar da mahaifiyarku! Indai Maleekh bai rabu da Amal ba! Indai Maleekh bai auri Farha ba! Zamu shiga duniyar mahaifiyar ku, mu hallaka taaa!" Arfat da Islam suka zube da kuka, zuciyarsu cike da tsoro da ruɗani. Suka kamo hannun yayansu Maleekh suna roƙonsa: "Dan Allah Yaya, ka amince da auren Farha. Kaga idan ba haka ba, Ammy zata mutu wallahi!" Farha ma ta haɗe hannu da hawaye tana matsowa kusa: "Yaya Maleekh, dan Allah ka amince ka aure ni. Nasan baka son mahaifiyarka ta hallaka ko?.." Maleekh ya rasa yanda zai yi. Zuciyarsa na ci masa gaba ɗaya. Wani ɓangare na zuciyarsa na bugawa da ƙarfi saboda soyayyar Amal, wani kuma na rikicewa saboda ganin mahaifiyarsa a kwance tana bori. Nan take ya yi saurin ɗaukar wayarsa, ya ƙira wani babban malamin addini da yake girmamawa, yana masa bayanin abin da yake faruwa... Nan malamin ya sanar cewa yana zuwa.. Bai jima ba, malamin ya iso gidan cikin nutsuwa da salati a bakinsa. Yasa a shigar da Ammy wani ɗaki.. Farha da Islam ne suka ɗaga Ammy suka kaita ɗakin ta, sannan suka dawo falo, duk suka zauna a falon.. Malamin ne ya shiga ɗakin, ya tarar da ita tana burgima a kan carpet, tana ihu tana nanata kalmomi masu tayar da hankali: "Maleekh dole ya rabu da Amal! Dole ya auri Farha!!" Malamin ya tsaya ya na kallonta cike da shakku. Sai zuciyarsa ta ce: "Wannan ba aljanu bane gaskiya, wannan shiri ne." Ya matso da nutsuwa, ya ce mata da murya mai cike da iko: "Ki daina wannan kwaɗayin yaudara, ba aljanu bane na sani. Ki tashi ki faɗa min gaskiya, me ya sa kike wannan abu a matsayinki na uwa?!" Ammy ta yi shiru na ɗan lokaci. Sai daga baya ta tashi zaune ta fara rawar murya cikin hawaye ta ce "Idan ban yi haka ba, Maleekh bazai taɓa jin maganata ba! Na tsani Amal a zuciyata! Na tsani ganin ta tare da ɗana! Saboda haka nayi wannan shirin bori don ya ji tsoro ya rabu da ita!" Malamin ya girgiza kai, ya ce: "To, wai saboda ɗanki ya ƙi auren wacce kike so, ya zaɓi wacce zuciyarsa take so, shiyasa kika kai kanki ga irin wannan ƙarya? To idan ya auri Farha, shin ke ce zaki zauna masa da ita? Ko kuwa kai tsaye zai zauna da ita a matsayin matarsa?" Ammy ta ce cikin kuka: "Don Allah Malam, ka yi masa magana. Ka ce ya yi abinda nake so. Ban yarda Amal ta cigaba da zama cikin rayuwarsa ba, wallahi ba zan taɓa yarda ba!" Malamin ya yi shiru na ɗan lokaci. Daga nan ya ce: "To shikenan. Zan yi masa magana. Zai yi abinda kike so, zai auri Farha insha Allah. Amma ki ji tsoron Allah ki daina yin wannan bori na ƙarya. Ba kyau, ba daraja ga mace mai mutunci bane." Bayan wannan tattaunawar, malamin ya fito tare da Ammy daga ɗakin. Duk yaran da Farha suka yi shiru suna jiran amsa... Ammy ta fito tana share hawaye, amma idonta na cike da murmushin farin ciki. Malamin kuwa ya ɓoye gaskiyar da ya gano, bai gaya musu cewa bori ne na ƙarya ba, saboda ya ja mata girma a wajen ‘ya’yanta. Ya ce musu cikin nutsuwa: "Ku kwantar da hankalinku. Zancen ya ƙare, komai zai yi daidai. Ku cigaba da addu’a kawai." Arfat da Islam suka natsu suka yi godiya. Farha kuwa ta yi dariya cikin sirri, zuciyarta ta ce: "Yanzu dai dole sai na zama matar Maleekh." Maleekh dai ya tsaya can gefe zuciyarsa na tafarfasa. Yasan akwai wani abu.. Malam da Maleekh ne suka yi waje, zama suka yi domin akwai maganar da malam yake son sanar da shi.. Malam ya zauna gaban Maleekh, Ya dubi Maleekh da ido mai cike da natsuwa, ya ce da shi: "Maleekh, kai ɗa ne mai biyayya. Na san yadda kake ƙaunar mahaifiyarka. Kuma na san yadda take ƙaunar ka. Duk tsanarta ga Amal saboda ƙaunarka ne. Yanzu ina roƙonka da ka yi wa mahaifiyarka biyayya. Cika mata buri. Ka auri Farha. Wannan ne zai sanyaya ranta." Maleekh ya girgiza kai, zuciyarsa na harbawa da ƙarfi. Ya kalli Malam cikin tsananin ɓacin rai amma ya tare harshensa saboda girmama shi. Maleekh ya ce "Ni auren Farha? Kenan dole sai na rasa Amal? Kenan dole sai na hallakar zuciyata saboda farin cikin mahaifiyata? Wayyo Allah." Malam ya zauna cikin nutsuwa yana duban Maleekh da damuwa sannan ya ce "Maleekh, ka sani uba da uwa su ne ginshiƙin ɗa. Ka kuma sani, mahaifiyarka tana da buri babba a kanka. Ka san yadda ta dage wajen ganin kai ne abin alfahari ga wannan gida. Don Allah ka yi haƙuri ka bi abinda take so. Aure da Farha ba zai cutar da kai ba, sai dai ya cika mata burinta. Ka yi tunani, ba dukkan lokaci muke samun damar girmama iyaye da rai ba." Maleekh ya lumshe ido yana jin zafin zuciya, yana ta harbawa da ciwo ya ce "Malam… na sani. Na san girman iyaye. Na san darajar uwa. Amma zuciyata kamar tana so ta fasa kirjina ta fito. Ban taɓa jin tsanar aure irin wannan ba a rayuwata. Amma saboda kai, saboda maganarka, malam… ba komai." ya furta cikin murya mai rauni.. Malam ya dafa kafaɗarsa da tausayi ya ce "Ka yi Haƙuri. Wannan rayuwa ce, wani lokaci tana ɗauke da abu da zuciya ba ta so amma tilas ka rungume shi. Allah ya sauƙaƙa maka." Maleekh bai iya cewa komai ba sai ya yi shiru, yana jin kamar yana shirin nutsewa a cikin baƙin ciki. Ya sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi, sannan ya ce a fili cikin ladabi: "Ba komai Malam. Zan yi duk abinda ku ka ce." Malam ya ɗan yi murmushi cikin gamsuwa ya ce.. "Allah ya saka da alheri. Wannan ne alheri a gareka." Tun daga wannan rana Maleekh ya rikid'e. Bai sake zama cikin dariya ko annashuwa ba. Ko a company an lura da shi baya cikin nishaɗi, baya yin dariya kamar da. Amal kuwa a matsayin mataimakiyarsa tana lura sosai da halinsa. Ita ce tafi kusa da shi a ofis, ita ce take tare da shi a ayyuka, amma yanzu kullum tana ganin damuwarsa... A ofishinsa suka zauna. Amal ta matso kusa da shi tana kallon fuskarsa. Ta ce "My Bee… me ke faruwa da kai? Kwanan nan kana canzawa sosai. Ba ka cikin annashuwa, baka cikin wargi da dariya kamar da. Ka fara bani tsoro wallahi." Maleekh ya ɗago ya kalleta, idonsa cike da damuwa. Ya so ya faɗa mata, amma ya kasa. Hannunsa ya ɗora akan nata, yana jin zafin soyayyarta a jikinsa.. A ransa yake faɗin "Taya zan gaya mata cewa dole ne in auri Farha? Taya zan hallaka zuciyarta? In fa ta ji wannan maganar cewa zata rasa ni, shin wane hali zata shiga?" Sai kawai ya danne zancen ya ce a fili: "Ba komai Amal… kawai damuwar aiki ne. Ki kwantar da hankalinki." Amal ta runtse ido, zuciyarta na tsananin damuwa ta ce "Kai kaɗai ne farin cikina yanzu, bana son ganin ka cikin damuwa. Don Allah ka gaya min gaskiya, ni fa zan iya jurewa komai muddin kana lafiya." Maleekh ya kalleta, idonsa ya kaɗa ja saboda yawan tunani. Sai ya saki hannunta a hankali, ya juya kansa gefe ya ce. "Na gode, amma ki kwantar da hankali. Komai zai yi daidai." 📍 Amal ta koma ofis ɗinta cike da tambayoyi. Zuciyarta tana bugawa: "Me ke damun Maleekh haka? Shin wani abu ya same shi ne? Ko wani abu yake ɓoye min? Ya Allah, kada wannan soyayya ta lalace." Daga wannan ranar Maleekh ya ɗauke ƙafarsa da zuwa wurin aiki... Saboda tsananin damuwa yanzu Maleekh ya daina zuwa company, kullum yana ɗaki daga masallaci sai ɗakinsa...zazzabi da ciwon kai da damuwa sun sako shi a gaba... Amal tana company a office ɗin ta.. Ta kifar da kanta akan table, ta shiga damuwa sosai ganin halin da Maleekh yake ciki, gashi yanzu ya daina zuwa wurin aiki, tana ƙiransa a waya, amma wayar switch up, kuma ta kasa zuwa gidan su... Hakan yasa washegari da safe kafin Amal ta wuce wurin aiki, sai da ta biyo ta unguwar Maitama layin gidan su Maleekh, tayi parking motarta a gefe guda tana cikin motar tana tunanin Taya zata samu Maleekh. Ga wayarsa ba ta shiga... Tana cikin wannan tunanin ne ta hango shi daga nesa nesa ya fito daga wani tsararren masallaci wanda yake gefe da gidansu.. Da sauri ta fita tana ambatar sunan sa.. Cike da mamaki yake bin ta da kallo, ya ce "Amal lafiya kuwa?..." Amal bata san komai ba. A wurinta Maleekh yana cikin shiru ne saboda damuwar aiki. Ita kam tana ta fama da tambayarsa: Ta tsaya a gabansa tana faɗin "Maleekh, me yake damunka ne? Na lura ka canza sosai. Ba kamar da ba, ko a wajen company. Koda nake tare da kai, ba na ganin murmushinka kamar da." Maleekh ya kasa magana. Sai ya kalli fuskarta cikin tausayawa, zuciyarsa na karyewa. A ransa: "Taya zan faɗa miki, Amal? Taya zan gaya miki cewa Ammy ta ɗaura mun alƙawarin aure da Farha? Idan na faɗa, halinki fa? Karyewar zuciyarki fa? Ba zan iya ba." Sai kawai ya ɗauke kansa, ya ce da ita da cikin rauni: "Amal, babu komai… kawai gajiya ce." Amal ta ce "Shikenan, kai dai kana ɓoye mun ne amma nasan baka da lafiya ne, shiyasa na kasa jure wa nazo duba jikinka, yanzu zan wuce wurin aiki, zan kula da komai in sha Allah, Allah ya baka lafiya _AMALEEKH_...." Sai da Maleekh ya ji wani sabon bugun zuciya jin ta furta wannan sunan... Ba tare da ya furta komai ba ya juya daidai lokacin da hawaye yake zubo masa... Amal kuwa ta ji damuwa sosai, zuciyarta ta soma yin nauyi, tana ta tunanin meke faruwa da shi... Haka ta juya itama cike da damuwa ta shige motarta, kai tsaye Campany ta nufa... _Bayan Sati Uku_ Amal’s office, CashTalk HQ Amal ta kifar da kanta a kan table ɗinta, zuciyarta na tafarfasa. Wayarta ta sake dubawa, amma har yanzu wayar Maleekh switch off. Hawayen damuwa sun cika idonta. Bata san yadda zata isa gidansu Maleekh ba, ba kuma zata iya boye wa kanta irin damuwar da take ciki ba. Sai kawai ta ji ƙarar buɗar ƙofa. Da sauri ta ɗago kai. Amal a firgice ta furta “Innalillahi… Farha?!” Farha ta shigo da kwarjini, tana sanye da kaya masu tsada, murmushi cike da izza a fuskarta _ta ce_ “Ina miki sannu da rashin cin nasara, Amal.” Amal ta miƙe a zabure, zuciyarta na tsalle ta ce “Subhanallah! Rashin nasara kuma? God forbid! Ni kullum a cikin nasara nake. Nasara ce ma ta kawo ni inda nake yanzu!” Farha ta yi dariya cikin raini sannan ta ce “Nasara? Rashin nasararki ta farko shi ne rasa Maleekh a rayuwarki. Na zo jan kunne ne kawai, ki fita daga rayuwar mijina. Kin ji ko? Abbah na dawowa daga ƙasar waje za'a saka mana ranar biki.” Amal ta ji ƙirjinta ya buga. Wani irin shock ya rufe jikinta gaba ɗaya. Amma ta daure ta yi shiru, ta ƙuduri cewa baza ta bata martani ba.. Sai ta buɗe ƙofar office ta window side yanda take hutawa tana kallon kowa dake ƙasin building..Tana kallon ƙasan compound ɗin daga sama, zuciyarta na yi mata nauyi. Kawai sai ga Farha ta biyo ta, ta tsaya a ta bayanta, tana murmushin mugunta ta ce “Me ya faru Amal? Allah yasa yau ba zuciyarki ce za ta buga ba, sai kin ga bikina da Maleekh” Amal ta ji hawaye sun fara gangaro mata. Ta juya da tsananin kishi da zafin zuciya ta ce cikin rawar murya. “Irin ranar da kike mafarki kenam? To bazata taɓa zuwa ba. Shiyasa kike addu’ar kar na mutu. Amma ki sani, Maleekh bazai taɓa auranki ba!” Farha ta yi tsaki tare da faɗin “Hmm, to mu gani! Shin umarnin mahaifiyarsa zai bi ne ko umarninki? Wacce matsayi kike da shi a rayuwarsa?!” Amal cikin tsawa ta furta: “Ƙarya neeeee!!!” Cikin hargowa suka shaƙi juna, suka fara tururuwar dambe a saman bene, wuri mai cike da haɗari. Daga ƙasa, mutanen company da security suka taru suna kallonsu da firgici. A nan ne sai aka ga wata mota ta shigo cikin harabar company, motar Maleekh! Ya fito cikin hanzari, yana ɗaga kansa sama. Ganin Amal da Farha a tsaka da dambe a wuri mai haɗari, zuciyarsa ta tsinke! Maleekh yana ɗaga murya, zuciyarsa na harbawa ya ce “Amal!!! Farha!!! Ku dakata da wannan shirmen! Wane hauka ne wannan?!” Amma basu tsaya ba. Amal da Farha suna faman turje-turje, saboda hayaniya ba sa jin komai. Maleekh ya riƙe kansa, yana kallon inda suke, zuciyarsa kamar zata tarwatse. Idanunsa suka kaɗa da ja, jin tsoron kada wani abu mai muni ya faru.. Farha ce ta yi turus ta tura Amal baya da ƙarfi! Amal cikin razana ta yi figici, bayanta ya bugu da ƙarfen da ke zagaye bakin tsalalleku. Sai kawai jikinta ya kife, ta tsallake ƙarfen da baya, ta kai ga faɗuwa ƙasa. Sai dai cikin azama, Amal ta yi saurin riƙe ƙarfen wurin da hannunta ɗaya. Amma jikinta gaba ɗaya na ƙasa, yana kaɗawa cikin iska. Da zarar ta sake wannan ƙarfen, tana faɗowa kai tsaye mutuwa ce kawai, domin tsakanin su da ƙasa akwai tazara sosai.. Maleekh wanda yake kallon sama yanda suke, zuciyarsa ta yi wani irin tsalle. Cikin razana ya shiga kururuwa: “Amal!!! Amal!!! Kada ki sake! Ki riƙe! Zan iso gareki yanzu… zan iso…!” Amal kuwa cikin tsananin fargaba da hawayen tsoro, ta riƙe ƙarfen da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma ta kama ƙafar Farha da take tsaye a sama. Amal tana kuka tana faɗin “Farha… don Allah… kada ki bari na faɗi…!” Sai dai, saboda mugunta da hassada, Farha ta fara dukan hannun Amal da ta riƙe ƙafarta. Tana take hannun da ƙafarta, tana yakushin hannunta da ƙarfi domin ta sake ta faɗi ƙasa. Farha ta na ihu cikin mugunta tana faɗin “Ki sake ni Amal! Ki faɗi ɗin mana! Duniya ta huta da ke! Maleekh zai zama nawa ni kaɗai!” Ƙasa kuwa jama’a sun taru suna kallon tashin hankalin da ake ciki, kowa addu’arsa kada Amal ta gaji ta sake ƙarfen.. Maleekh yana ganin haka, zuciyarsa ta yi wata irin guguwa. Ya ruga da gudu cikin gaggawa zuwa elevator, zuciyarsa na bugu kamar ta tsinke ƙirji. Maleekh a ransa yake faɗin “Ya Allah, kar

Chapter 25 of 62