muryar tsawa yake faɗin.
“Me ke faruwa ne haka cikin gida? Maryam, me ya faru?”
Tana kuka da huci ta ce:
“Ka tambaye shi, kaima kasan abunda ya aikata ai! Wannan ɗan naka yana da hauka! Farha yarinyar nan yanzu tana cikin cell! Ka tambaye shi me yasa ya saka ta a hannun hukuma kamar wacce bata da gata!”
Abbah ya juya yana kallon Maleekh kai tsaye.
“Maleekh! Wane irin abin kunya ne ka ƙara kawo mana haka? Shin ba ka sanar mana cewa a TV zata sanar ba? Me yasa har da hukuma?!”
MALEEKH cikin muryar tausayi, ya ce:
“Abbah... ba hukuncin kaina nayi ba. Hukuma ta riga da ta shiga cikin case. Babu komawa baya. An samu gaskiya, kuma duk masu laifi sun amsa laifinsu.”
AMMY ta zabura cikin takaici ta ce:
“Ka ce gaskiya?! Gaskiyar me? Wannan ita ce ‘yar da na raina da hannuna, da nake kallon ta tamkar ‘yata! Ka kasa daurewa ka tafi da lamarin cikin gida?”
MALEEKH ya ɗago kai yana faɗin:
“Ammy, babu wanda ya fi ni son a warware komai cikin gida. Amma idan abu ya kai ga cin zarafi, da cutar da wanda bai da laifi to adalci dole ne ya yi aiki!”
Abbah ya ja numfashi mai zurfi yana girgiza kai, zuciyarsa na tafasa da ciwon abin da ke faruwa.
ABBAH ya ce:
“Maleekh, ka sani… rayuwar mutane ba wasa bace. Idan dai kotu ta shiga, to babu wanda zai iya ja da hukuma. Amma, na baka shawara: ka kwantar da hankali, ka bar doka ta yi aikinta kawai...”
AMMY ta juya da hawaye tana kallon Abbah:
“Au kaima Alhaji yanzu haka zaka tsaya masa? Kana ganin ɗanka ya hallaka zumunci? Ni bazan taɓa yarda da wannan auren Amal ba! Tunda har ya zaɓe ta akan ƴar uwarsa, ku je kotu ta yanke hukunci ɗin...!”
Maleekh ya kalli iyayensa da idanu masu cike da tausayi ya furta a hankali.
“Ku yi haƙuri, amma hukuma ta riga ta kama hanya. Kotun ce zata yanke hukunci, ba zuciyar mutum ba.”...
Ya nufi part ɗinsa cikin natsuwa, ya bar Abbah da Ammy cikin mamaki da tsoro yayinda iska mai sanyi ta lulluɓe Ammy...
Ammy ta zube a kujera tana kuka, Abbah na zaune cikin tunani mai nauyi, yana cewa a hankali:
“Rayuwa... idan ɗa ya fara tafiya akan hanyar da yake ganin ita ce adalci, babu wanda zai iya ja da shi.”..
Washegari iyayen Farha sun sauƙa a Airport.
Zayd da kansa yazo ɗaukan iyayensa a motarsa.
Zayd ne yake tambayarsu cewa gidan su Maleekh zasu nufa?..."
Mahaifinsa a firgice ya ce
"Allah ya kiyaye, ai akwai gidan mu anan, don haka akai mu can, ai mun daɗe da raba zumunci da su. Babu mu babu su don haka mu tafi gidan kanmu..."
Zayd ya ce
"Saboda haka yasa nasa aka gyara muku gidan domin nasan bazaku taɓa rayuwa anan gidansu ba..."
Sun shiga mota suka yi gidan su acan Estate...
Bayan sun ci abinci sun huta..
Hajiya Sa’adatu ta kalli Zayd ta ce
"Ya muke akan maganar mu?..."
Zayd ya ce
"Ina sane da haka Mom, mu bari sai an gudanar da zaman kotu tukun, kuma akwai hanyoyi da yawa da za'a kawar da shi ba tare da an san wa ya kashe shi ba, mu kasance masu wayo kafin hakan..."
Alhaji Wadata mahaifinsa ya ce.
"Tabbas sai anyi tunani tukun..."
Suna cikin wannan zama sai suka ji knocking..
Zayd ne ya je ya buɗe sai ga wani babban mutum mai kuɗi wanda yaci sunansa Alhaji Gusau, asalin ɗan Gusau ne yake zaune anan Abuja, shima tsohon ɗan siyasa ne...
Ganinsa yasa Alhaji Wadata miƙe wa yana kallonsa da mamaki kafin ya ce.
"To pah Alhaji Gusau taya kasan da zuwan mu alhalin ba wanda yasan mun zo ƙasar?..."
Alhaji Gusau ya zauna sannan ya ce
"Ai daman nasan zaku zo, yau ne fa zaman da za'ayi a kotu, kuma ƴarku ake ƙara da cin zarafi..."
Alhaji wadata ya ce
"Yanzu ba wannan ba, shin meya kawo ka?..."
Alhaji Gusau ya ce
"Nazo sanar maka abin da baka sani ba, kuma kasan cewa duk sirrinka a tafin hannuna yake...A shekarun baya nasan bazaka taɓa manta babban abokin mahaifin Maleekh ba wato Alhaji Abdulsamaad...."
Alhaji Wadata ya yatsina fuska ya ce.
"Yanzu me ya kawo maganar mutumin da ya daɗe da mutuwa nan..."
Alhaji Gusau ya tintsire da wani irin dariya, sannan ya ce.
Alhaji Abdul-Majeed mahaifin Maleekh babban abokin Alhaji Abdulsamaad mahaifin Amal wacce tayi silar shigar da ƴar ku cikin cell...."
Hajiya Sa’adatu zaro ido tayi waje tana kallon Alhaji Gusau..Shima Alhaji Wadata ƙirjinsa ne yayi wani irin bugawa, shi dai Zayd bai san komai game da abunda ake faɗin ba...
Alhaji Wadata tsabar ya rikice cikin tashin hankali ya ce.
"Kana nufin ɗiyar marigayi Abdulsamaad tana raye?..."
"Hhhhhh! Har da uwar marigayin duk suna raye, su biyu suke raye anan garin Abuja, kuma Maleekh ne ya siya musu gida, tana aiki kuma a campanyn sa..."
A cewar Alhaji Gusau...
"Innalillahi wa inna ilaihi raji’un..."
Alhaji Wadata ya kama kai cikin tashin hankali...
Hajiya Sa’adatu ta ce
"Mun shiga uku, Alhaji kun kashe maciji baku sare kai ba, na tabbata wata rana gaskiya zata fito..."
Zayd yana kallonsu a baibai ya ce
"Wai akan wa kuke magana ne yanzun?..."
Hajiya Sa’adatu ta daka musa tsawa da cewa
"Kai dallah kayi wa mutane shiru.."
Alhaji Gusau ya ce
"A'a ku kwantar da hankalinku"... ya kalli Alhaji Wadata sannan ya ce "Kai ka manta da tsarin ne?..."
Ya ciro wani memory ya soka a jikin plasman...A cikin wannan memory flash babu komai a ciki sai video lokacin mutuwar Iyayen Amal...
LABARIN MUTUWAR IYAYEN AMAL...
A shekarun baya, mahaifin Amal yana daga cikin hamshakan masu kuɗin Nigeria 🇳🇬...garin Kaduna..
Kuma masu gaskiya da riƙo amana, shi da mahaifin Maleekh shiyasa wasu daga cikinsu suke jin haushinsu, a cikin maƙiyansu mahaifinsu Farha yana daga ciki...
Wata rana da daddare misalin ƙarfe 2.
Wasu motoci suka parker a ƙofar gidan Alhaji Abdulsamaad, suka fara knocking, mai gadin gidan ya tambaya suka sanar masa cewa
"Alhaji Wadata ne yazo..." dake shima abokin maigidan ne...jin hakan yasa maigadi ya buɗe tare da mamakin zuwansu cikin dare haka...
Already sun zo da ƴan daba, shigowar su suka harbe maigadi take ya mutu...
Alhaji Wadata da Alhaji Gusau ne su biyu sai ƴan daba suka kutsa ciki..
Knocking suka fara yi a ƙofar falo, a lokacin Matar gidan ta fito ɗaukan ruwa a frig, jin knocking yasa ta tsorata tana mamakin a wannan daren za'a zo musu. Tayi ƙarfin halin cewa "Waye ne?.."
Murya daga waje ne ya ce "Su Alhaji Wadata ne, abokin mai gidan..."
Hajiya Khadija cike da mamaki ta ce "abokin takarar mijina mai ya kawo shi cikin daren nan?..."
Amma ta kawar da wannan tunanin ta je ta buɗe musu..
Ganin ƴan daba sun shigo da manyan bindigai yasa ta ja baya a tsorace, sai ga Alhaji Wadata da Alhaji Gusau sun shigo suna wani irin shu'umin murmushi..
Wani daga cikin ɗan daba ne ya ɗora mata bindiga suna daka mata tsawa da cewa "ta kaisu can ɗakin da Alhajin yake..."
Hajiya Khadija a fusace ta ce
"Tsautsayi ne da ƙaddara yasa na buɗe muku domin nasan ku ɗin maƙiyanmu ne, ƴan adawarmu, kuna neman kujerar takarar mu ne yasa zaku nemi rayuwarmu? Macuta azzaluman bayi....in Allah ya yarda ƙarshen ku bazai yi kyau ba..."
Alhaji Wadata ne ya zabga mata mari tare da tura ta akan su wuce yanda Alhaji yake...
Haka suka yi gaba zuwa upstairs... Alhaji yana bacci ya ji an tura ƙofa da ƙarfi, tashi yayi tana faɗin
"Haba Khadija ke kin ƙi bacci kuma kin hanani yi? Kinsan fa gobe inada meeting da zan gudanar da sassafe, don Allah ki barni nayi bacci na .."
Ita kuwa ba abunda take sai kuka, kamar a mafarki Alhaji ya ji ance.
"Sai dai ka gudanar da meeting a lahira, ba dai a nan duniya ba..."
A zabure Alhaji ya tashi zaune..
Khadija tana kuka ta ce "Ku ma ai ba tabbata zakuyi a duniyan ba..."
Wani daga ciki ne ya buga mata bindiga a kai har sai da ta faɗi ta suma, shi kuma sun ɗago shi tare da zaunar da shi akan kujera sannan suka ɗaure shi da igiya..
Alhaji yana kallon Alhaji Wadata da Alhaji Gusau ya ce .
"Nasan daman wannan lokacin zai zo, burinku shine ku ci amanar ƙasa kuma na kafe na tsare babu wani dama, shine yanzun zaku shigo mun gida?..."
Alhaji Gusau ya ce
"Ka kalle mu tamkar mala'ika azara'ilu domin mun shigo tafiya da ranka ne..."
Abun mamaki maimakon ya ji tsoro sai ji sukayi Alhajin yana dariya, daga bisani ya ce:
"Kun ban dariya matuƙa, domin babu wanda rai yake hannunsa face Ubangiji, don haka kar kuyi tsammanin ku ma zaku bar nan a raye, domin rai a ƙididdige yake...amma sai dai komai da silar sa, idan hakane burinku to a shirye nake dana amsa ƙiran ubangijina, kuma zan tafi ina alfahari da al'umma suna yi na, na riƙe gaskiya bisa amana..."
Alhaji Wadata ya ce:
"Kar kayi tunanin haka zaka mutu ka tafi, dole sai kayi abu ɗaya domin ceton matarka da ƴarka ɗaya tilo a duniya da kuma mahaifiyarka..."
Alhaji Abdulsamaad jin an ambaci iyalainsa yasa shi girgiza ya ce.
"Inason duk hukuncin da zaku yi mun kuyi akaina kawai, ku kyale su, zan amshi duk abinda kuke so amma ku kyale mun iyalaina..."
"Okay! Abin da muke so shine, zamu kunna video recording kayi bayanin cewa babban abokinka Alhaji Abdul-Majeed shine wanda yake neman rayuwarka, kuma ka bayyana cewa yanzu zaka mutu shine yasa a kashe ka sannan ya kwashe duk takardun dukiyarka da duk abinda ka mallaka..."
Alhaji Abdulsamaad a fusace ya ce
"Akan me zanyi masa wannan sharrin alhalin bai ji ba bai gani ba? Bazai taɓa yuwa ba..."
Alhaji Wadata ya kalli ɗaya daga cikin ƴan daba ya ce
"Ku fara harbe kwakwalwar matarsa kafin guje ku ɗauko mun ƴarsa da uwarsa mu gama da su kafin shima ya bi bayan su..."
Har an kunna kunamar bindigar za'a harbe Hajiya Khadija dake kwance a ƙasi sumammiya da sauri Alhaji Abdulsamaad ya dakatar da su a tsorace yana faɗin.
"Ku dakata dan Allah, ku dakata zanyi abun da ku ka ce..."
Alhaji Gusau ya ce
"Okay, yanzu zamu since igiyar da aka ɗaure ka saboda kar ayi tunanin tirsasa ka akayi, za'ayi tunanin ka fake ne kai ɗaya ka zayyana gaskiya kafin mutuwarka..."
Kamar yanda suka tsara hakan akayi, sai da aka since shi, sannan aka haska camera ya fara video, Alhaji Abdulsamaad yana hawaye ya fara zayyana abun da suka umarce shi....
Cewar "Alhaji Abdul-Majeed ne yake neman rayuwarsa, sannan yasa karɓe masa takardun dukiya da gidajen da yake da shi da duk wani abunda ya tara ta hanyar barazanar kashe iyalainsa........"
Duk abin da ya faɗa a cikin video su suka tsara masa, bayan ya kammala ne suka sa ya basu duk takardun dukiyarsa, da check na babban bankinsa yayi musu signed yanda zasu ɗebe kuɗaɗen gaba ɗaya, yasa musu hannu a takardun gidajensa da filayensa har da gonayensa dake can ƙauye da saniyoyinsa da duk abunda ya mallaka a duniya, duk sun karɓe....Babu abin da ya saura yanzu..
A ta bakin ƙofa kuwa Inna wacce a lokacin suke ƙiranta da Uma, tana leɓe duk ta saurari tattaunawarsu daga farkon shigarsu....jin an tura wani daga cikin ƴan daba cewa, "ya je ya dubo ƴarsa da uwarsa shin suna nan?.." yasa Inna ta juya da gudu, kai tsaye ɗakin Amal ta nufa duk da ƙarama ce a lokacin bazata wuce shekara uku ba amma ɗakinta da ban.....Inna ce ta shiga ɗakin Amal ta kwanta a gefenta a yayinda Amal take bacci...
Sai da ta tabbatar da ɗan daban ya shigo ya same su suna bacci kafin ya juya yabar ɗakin, yana fita Inna ta ɗauki jakar Amal na makaranta ta zuba kuɗin dake jikinta sannan ta goya Amal a baya tana bacci suka fita da gudu, ta ɓoyayyen hanya suka fi a gidan wanda babu wanda yasan da hanyar suka fita domin ta can get ɗin akwai wasu ƴan daba da suke tsare da hanya...
Ɗan daba ne ya sanar musu cewa "Duk suna bacci..."
Alhaji Wadata ne ya ce:
"Bar su suyi baccin su yanda suna farkawa zasu tsinci kansu a lahira..."
Alhaji Abdulsamaad hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba, yanata roƙon su da Allah akan su kyale su...
"Kun mun alƙawarin idan kuka samu kpmai zaku ƙyale iyalaina, meyasa zaku ci amana, kun sa nayi wa babban abokina sharrin da bazai taɓa goguwa ba wanda hakan zaiyi silar ruguza shi, sannan na baku duk abin da na mallaka, sannan kun nemi rayuwata kuma duk na baku da sharaɗin ƙyale family na, kuma kuma Shalelena ƙaramar yarinya ce, bata san komai ba, ku ji tausayin yarinya mana..."
Haka yake kuka kamar ƙaramin yaro...
Amma duk da haka basu saduda ba, Hajiya Khadija tana sume amma haka suka sa bindiga suka harbe kanta...😭😭😭
Sannan suka sanar wa ƴan dabar cewa su zuba wa ko ina petur su ƙona gidan da mutanen dake gidan...
Suka nuna Alhaji Abdulsamaad da yatsa cewa "baza mu harbe ka ba domin bama so kayi mutuwar sauƙi wato fatt ɗaya, so muke kaita kururuwa a ciki wuta babu wanda zai jiyo ka har ka mutu, haka mahaifiyarka da Shalelenka wacce kake matuƙar ƙauna itama Allah sarki wuta ne ajalinta..."
Alhaji Wadata ya ƙara da cewa
"Ina tausayin yara da tsofi hakan yasa baza mu harbe su ba, wuta zata yi aikinta...
Su na dariyar mugunta suka bar Alhaji Abdulsamaad a ɗaure a kujera, sun bar gidan bayan sun tattara komai har da su gwalagwalai Hajiya Khadija.....
An gama saka petur a ko ina, ganin petur bazai musu yanda suke so ba suka ƙara da kunna gas...sannan suka cilla wuta a gidan..
Su kuma suka shiga motocinsu suka bar yankin kamar basu taɓa zuwa ba....
Sai washegari aka tarar da asarar da aka tabka...
Alhaji Abdul-Majeed ba ƙaramin girgiza yayi ba, har sai da ya suma kusan sau biyar, ya ji mutuwar babban abokinsa wanda bazai taɓa samun aboki like him ba...
Ganin babu wani shaida ko hujja akan abunda ya faru ne yasa aka baza cewa gobara ce ta kama cikin dare a gidan Alhaji Abdul-Majeed, an sara rayukan mutanen gidan, da shi Alhajin da Matarsa da Ƴarsu da Mahaifiyar Alhaji da maigadi......A haka labarin ya wuce...
Inna kuwa da Amal can wani ƙauye suka nufa, wato ƙauyensu Mahaifiyar Amal, ƙauyen su Malam Yawale.
Anan suka cigaba da zama, har suka yi shekara guda..... Anan ne Malam Yawale ya basu haƙurin cewa shima dawainiya ya masa yawa bazai iya riƙe su ba.. duk da yana Yayan Mahaifiyar Amal amma ya kasa riƙe su, babu yanda basu zagaya ba amma kaf ƴan uwa sun kasa riƙe su..
Sai da Inna da Amal suka ɗau shekara biyu zuwa uku suna zagaya ƴan uwa kafin suka koma cikin Kaduna ganin babu mai taimakonsu, a ƙauye Uma ta samo sunanta Inna...
Suka samu wani yanki na talakawa a garin Kaduna suka zauna, Inna ta cigaba da neman kuɗi tana biyan kuɗin haya duk shekara dubu 20 dake ƙaramin gida ne, babu fasali ga kuɗin makarantar Amal da ta sakata, ita kuma Amal taƙi ko wani school sai na ƴan gayu, wato irin makarantar da ta fara yi tin farko, ba yanda Inna ta iya haka ta sakata a private school, tana amsa ƙira Amal Abdulsamaad saɓanin asalin sunan Amatullah Abdulsamaad Cash maker..
Inkiyar sunan mahaifinta kenam " _CASH MAKER"_
A school ɗin Amal ya haɗu da babbar ƙawarta A'isha, ƙanwar Maleekh...
Har Amal ta girma ta samu aiki a gidan rediyo Rayuwa FM. Ta fara biyan kuɗin hayan gidan da suke...
Anan Inna ta sanar mata cewa "Mahaifinta ɗan siyasa ne, kuma maƙiyansa ƴan siyasa ne sukayi silar mutuwarsa ta hanyar dasa gobara saboda riƙon amana da gaskiyar da yake da shi, baya karɓan cin hanci sannan baya karɓar kuɗin ruwa, ya tara dukiya ta halal kuma an karɓe su, bamu tsira da komai ba sai da jakar makarantarki da wasu photunanki da kikayi da abokinki Maleekh, na zuba wasu kuɗi a ciki wanda zamu yi amfani da su..." Inna ta ƙara da cewa
"Wannan sirrinki ne Amal, ki zamo mai gaskiya kamar mahaifinki,..."
Amal ta sha tambayar inna "su waye suka kashe mun iyaye?..."
Inna sai dai ta sanar mata cewa:
"Wasu ƴan siyasa ne amma bata sanar mata su waye ba balle ta ambaci sunan su..."
A haka aka cigaba da tafiya hakan yasa Amal ta tsani duk wani ɗan siyasa marar gaskiya a lokacin da take aiki a rayuwa FM, ba yanzu da ta zama ƴar love ba....
An dawo daga labarin...
Alhaji Wadata da Alhaji Gusau da Hajiya Sa’adatu da Zayd suka tsaya suna kallon video da Alhaji Abdulsamaad yake magana cewa "Alhaji Abdul-Majeed ne yake neman rayuwarsa, video ya daɗe yana showing kafin suka kashe, Alhaji Wadata ya karɓi memory ya ce "shi zai ci gaba da ajiyarsa a wurinsa tinda Allah bai yi zasu basa labarin ba a wannan shekara..."
Alhaji Gusau ya ce
"Hanya ɗaya mafi dacewa a baza labarin nan shine, mu jira kotu ta gama aikinta, bayan haka sai mu sa a kashe ita yarinyar wato ƴar macijin da muka kashe, bayan mutuwar ta zamu sa a sanar cewa Alhaji Abdul-Majeed ne yasa a kashe ta, mutane zasu yanda ta hanyar ganin wannan video mahaifinta..."
Hajiya Sa’adatu ta ce
"Yanzu duniya bata riga tasan wacece Amal ba, amma zamu fitar da hakan bayan mutuwarta ta hanyar baza wannan video..."
Alhaji Wadata ta kalli Alhaji Gusau cike da mamaki ya ce
"Amma taya ka gane cewa yarinyar nan ɗiyar Marigayi ce?..."
Alhaji Gusau yayi dariya sannan ya ce.
"A Kaduna tana yawan fitowa a gidan rediyo da television dake aikinta ne, tana yawan ƙalubalantar ƴan siyasa, kullum maganarta akan ƴan siyasa ne, ta yanda na gane hakan shine a bikin A'isha ƴar Amaryar Alhaji Abdul-Majeed ta bada tarihinta duk da ba cikakke bane amma ta sanar cewa "iyayenta sun mutu ta hanyar gobara, a wani kafar sadarwa ta sanar cewa iyayenta sun mutu ta silar siyasa...Hakan yasa na ƙarfafa bincike akanta, acan bayan iyayenta na da rai tana amfani da suna Amatullah Abdulsamaad Cash maker, yanzu kuma Amal Abdulsamaad, naga ba abin da ya bambanta, da haka har na samo asalinta....."
Alhaji Wadata ya ce
"Kanada wayo sosai ..."
Duk suka kwashe da dariya...
Zayd ya kalli mahaifiyarsa ya ce:
"Mom. Ya batun kashe Maleekh?..."
Hajiya Sa’adatu ta ce
"Ka dakata mun sai an gama da wannan yarinyar kafin a dawo kansa, domin zata iya bamu matsala nan gaba..."
Zayd kamar zai yi kuka ya ce
"Mom, na fara sonta fa..."
"Son ɗin banzaaaa, dallah ja baya..."
A cewa Hajiya Sa’adatu tana daka masa tsawa...
Alhaji Gusau ya duba agogo ya ce
"Kun ga yanzu lokaci yayi, kotu tayi ƙira..."
Hajiya Sa’adatu ta zabura kamar zata yi kuka ta ce:
"Dan Allah mu tafi wayyo daughter na, inason ganinta, ban san wani hali take ciki baaa...abun kunya ƴarta ta kwana biyu a cikin cell..."
Duk suka fita..
Kai tsaye kotu suka nufa..
•••••••••••••••••••••••••••••••••
Kotun ta cika da jama’a. An jera wasu manyan kujeru, alkalin yana zaune a tsakiyar kujerarsa cikin baƙar riga da hular court, yana duba takardu a gabansa...
A gefe guda, Amal tana zaune cikin hijab ɗinta, fuskarta a nutsuwa amma idonta na nuna zafin zuciya da ciwon tozarcin da aka yi mata...ba kuma son zaman kotun nan take ba gaba ɗaya a tsorace take..
A gefenta Lawyer ɗinta ke tsaye — babban lauyan da Maleekh ya ɗauka domin kare ta...
A gefe guda kuwa, Farha tana tsaye a rikice, tana hawaye. A gefenta kuma Doctor Khalid, wanda ya taimaka wajen ƙirƙirar ƙazafin da suka yi kan Amal, yana ta zufa da motsa labbensa cikin rashin natsuwa...
Su ne “defendants” a gaban kotu...
A kujerun masu sauraron kallo Maleekh na zaune a baki baki— cikin farin suit, yana kallon Amal da idanu masu cike da tausayawa...
Bai ce komai ba, amma duk wanda ya kalle shi yasan yana cikin baƙin ciki...
Ya yi tsayin daka ya shigar da ƙarar da kansa domin kare sunan Amal, bayan tozarci da ya bazu a kafafen labarai...
Ammy tsabar takaici bata ma zo kotun ba, sai Abbah da Islam da Arfat... A gefe guda kuma Inna ce zaune da wasu mutane..
Acan baya Hajiya Sa’adatu ce take ta hararar Amal da Maleekh.. ga su Alhaji Wadata da Alhaji Gusau da Zayd..
Farha ce ta fashe da kuka tana faɗin
"Wallahi ƙarya ake mun ban aikata komai ba, Maleekh ya tilasta ni ne akan na faɗi haka a TV saboda manufarsa..."
Maleekh sake baki yayi yana kallonta cike da mamaki jin yanzu tana ƙaryata ƙarar da ake tuhumar ta...
Maleekh ne ya miƙe cikin fushi yana faɗin.
"Ƙarya kuma? Da bakin ki kika amsa laifinki fa a gaban duniya kowa ya ji kuma ya saurara, please Farha kar ki wahalar da kotu..."
Lawyer da yake Hajiya Sa’adatu ta ajiye domin kare Farha ne ya miƙe ya ce wa Maleekh
"Please ka saurara, nan kotu ne ba kasuwa ba, dole sai anyi bincike domin bazamu yadda da barazanar da kayi mata saboda wata manufarka ba, mu kotu ba shashashu bane..."
Maleekh ya ce
"To ayi bincike mana, nima ai ba shashasha bane, sai da na tabbatar da hujjoji kafin na kawo kotu..."
Alkali ne ya buga guduma yana faɗin
"Nan kotu ne ku nutsu.."
Maleekh ya zauna yana huci..
Alkali: ya dube su gaba ɗaya cikin nutsuwa
"Wannan shari'a ce tsakanin Miss Amal da waɗanda ake tuhuma Miss Farha da Dr. Khalid.
An shigar da ƙara bisa ƙarya, ƙazafi, da yaɗa labaran ƙarya a kan mutunci da suna na wannan baiwar Allah.
Kotun nan zata tabbatar da adalci, ba tare da son rai ba."
Lawyer Amal ya miƙe cikin izza:
"My Lord, mu muna gabatar da hujjoji masu ƙarfi. Wannan yarinya ta tozarta, ta rasa mutunci saboda ƙarya da makirci.
Akwai sauti da hotunan da suka nuna cewa waɗanda ake tuhuma sun tsara wannan komar da nufin lalata sunanta da kuma tarwatsa aikinta a kamfani..."
Ya nuna takardu.
Aka kunna recording wayar da aka saurari muryar Farha tana cewa:
“Na gaya miki hanyar da zaki samu Maleekh? To ki tafi gidan club. Ki je can zaki same shi, kuyi bankwana na ƙarshe.…”
Wannan Islam ce tayi recording a yayinda Farha take sanar wa Amal...
Recording na biyu.
"Kasan nan ɗin nawa ne?....Kimanin 2 billion dollers ne. Kuma duk naka ne idan ka yi mun abu ɗaya kawai."
"Yarinyar da aka kawo jiya da daddare Amal. Nasan result ya nuna ba ciki a jikinta, kuma bata sha maganin zubar da ciki ba....."
"Ina so ka canza result ɗin. Ka rubuta cewa Amal ta zubar da cikin wata huɗu, ka tabbatar labarin ya zama ya shiryu, yanda babu wanda zai iya ƙaryatawa..."
Duk wannan recording an same shi a wurin wata nursing da ta laɓe ta saurari tattaunawar su..
Jama’a suka cika da mamaki.
Farha ta sunkuyar da kai...
Doctor Khalid ya fara zufa sosai...
Alkali ya ce:
“Ina ganin akwai hujja mai karfi a nan.”
Lawyer ɗin Farha ya miƙe yana ƙoƙarin kare su:
“My Lord, abinda aka faɗa ba nufin ɓata suna bane, kawai tsokaci ne…”
Amal ta fashe da kuka tare da faɗin:
“Na rasa mutunci, na rasa suna mai kyau, saboda su suka ƙirƙiri ƙarya a kaina.
Na kunyata saboda wannan al'amarin… amma yau na dawo neman adalci.”
Kowa yayi shiru.
Lokacin da Maleekh ya kalli Amal, hawaye ne ya cika idonsa saboda tuna irin wulakanci da yayi mata, amma ya daure...
Alkali ya ce
“Kotun ta saurari ƙarar da hujjoji, kuma daga ganin gaskiyar al’amari, akwai tabbataccen shaida akan waɗanda ake tuhuma.
Saboda haka kotu zata yanke hukunci a zama na gaba. Amma kafin nan, ana buƙatar su rubuta bayani na gaskiya (written confession) kafin kotu ta ɗauki mataki na gaba.”
Ya buga guduma.
“Case adjourned till next week.”
Kotun ta watse da hayaniya.
Farha ta yi ƙasa da kai tana hawaye, a lokacin iyayenta suka nufe ta cikin tausayawa...
Amal ta durƙusa ta gode wa Allah, ko ba komai yanzu ta wanke kanta a kallon da mutane ke mata, amma har cikin zuciyarta bata son a yanke musu wani hukunci...
Maleekh ya tsaya a bakin ƙofa yana kallonta da murmushi mai taushi, idonsa cike da nutsuwa..
“Kin yi nasara, My Beb… gaskiya ta fito fili.”...
NEXT NEXT NEXT....
asmeetahwriter✍️
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 40 Chapter of 62