Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
juyi ta kasa yin bacci, jin maganganun da mutane ke faɗi tsakanin ta da Maleekh... A ranta ta furta "daga ceto sai a fassara lamarin?..." Inna ce ta shigo ta same ta sai faman juyi take, ta zauna a gefen katifar ta tare da furta "Amal..." Amal ta tafi dogon tunani bata san Inna ta zaune gefenta ba, Inna jin bata cikin hayyacinta ne yasa ta buge ta a baya tare da faɗin "ke Amal..." A ruɗe Amal ta tashi zaune tare da faɗin "Ni ba soyayya nake da Maleekh ba ...." Inna ta zuba mata ido ta ce "too pahh..." Sunkuyar da kai Amal tayi... Inna ta ce "abinda ake faɗa ashe gaskiya ne? daga ƙiyayya sai a fake da soyayya?..." Amal ta ce "wallahi Inna ba gaskiya bane..." Inna ta dankwale ta tana faɗin "Kan jatumarki, munafuka, har gida aka zo aka nuna mun video ke da wancan yaron, ashe bakida hankali Amal? sai yanzu na raina iliminki da tunaninki, to ki sani ke abin magana zai shafa ba shi ba, tinda shi duk abinda yayi ado ne, ki kula da irin yaran nan, tamm...." Inna tana kammalawa ta tashi ta koma wurin kwanciyar ta... Amal ganin ta rasa yanda zata yi ne yasa ta fara marin kanta tana faɗin "Na shiga uku! Na shiga uku!! Na shiga uku!!! Ni Amal ya zanyi..." Itama haka ta gama shawaginta sannan ta kwanta bacci ɓarawo ya ɗauke ta.... Washegari da safe Gidan 📺 TV PROGRAMS DA BLOGGERS sun sake fitar da wani bayani akan Amal da Maleekh... “Gaskiyar Bidiyon Amal da Maleekh...” Wani babban shiri a Channels TV yana nazari akan bidiyon yana ƙiran masanan zamantakewa da kwararrun masu fassarar al’amura... “Is This Power Play or Love Story?” Wani ɗan jarida a Arise News yana tambaya ko akwai wani ɓoyayyen abu da suka kasa faɗa... Bloggers irin su ‘Naija Juice’ da ‘GistMe247’ suna cewa: “Was this attack real or planned to create attention? Yanzu haka Amal ta zama celebrity.” 📻 A RAYUWA FM: Amal ta yi jawabi... Bayan gani da jin abubuwan da ke yawo a dandalin sada zumunta, Amal ta dawo cikin studio ɗin Rayuwa FM, ta zauna tana fuskantar mic kamar yadda ta saba, sai dai wannan karon akwai ɗan fara'a da nutsuwa a fuskarta, ta fara jawabi kamar haka.. “Zan yi magana domin ku sani: Ban san Maleekh daga baya ba har sai wata rana da ya fito da ikonsa ya shiga rayuwata. Amma faɗa ne ya haɗa mu ba soyayya ba. Kuma idan faɗa ne zai haifar da jituwa, toh wannan Allah masani....” Sauraren wannan kalmarta ya sanya mutane sun sake tofa albarkacin baki. Wasu na ganin tayi hikima, wasu kuma sun ɗauka zata iya faɗar gaskiyar zuciyarta... ❤️ A gidan mahaifinsa, Maleekh yana kallon wani ƙaramin talabijin a ɗakinsa ana kan dawo da bidiyon nan akai akai. PA ɗinsa ne ya shigo yace masa: “Sir, Nigeria ta riga ta ɗauka kuna soyayya. Koda ba haka bane, yanzu labarin yana raye.” Maleekh cikin ɗan murmushi mara kwari ya ce “Soyayya? Suna tunanin zuciyata ta buɗe… Amma shin ta karɓe ni kuwa?” Sai ya ɗauki wayarsa, yana kallon hoton Amal da aka ɗauka lokacin da take faɗa, fuskar jarumta da ƙarfi a idonta. Bai ce komai ba, sai kawai yace: “This girl... is ruining me gently.” ● Bayan sati biyu... Rayuwa FM ta shiga labaran duniya da sabbin jita-jita bayan an sanar da cewa an dakatar da Amal daga aiki ba tare da cikakken bayani ba. Jama’a ne suke tambaya "me ya faru?", "wace laifi ta aikata?", amma duk da tambayoyin da ke ci gaba da yawo, hukumar rediyon ta yi gum da baki. Wani babban rikici ya ɓarke ne daga bayan fage, wasu gurɓatattun 'yan siyasa da suka ji tsoron shaharar Amal da yadda kalamanta ke wayar da kan talakawa, sun haɗu suka ba shugaban gidan rediyo Rayuwa FM maƙudan kuɗaɗe kimanin ₦100 Billions domin kawai a kori Amal daga aikin ta. An hana ta dawowa ofis. Bayan mako guda da aka dakatar da ita, wani ƙaramin rubutu kawai aka turo mata: “Rayuwa FM regrets to inform you that your services are no longer required.” Amal ta karanta saƙon da idanuwan da suka saba da jarumta, amma a cikin zuciyarta ta ɗan firgita. Ba saboda aikin ba, sai dai saboda yaudara da cin hanci ya kashe gaskiya a gaban idonta. Yanzu Amal ta dawo gida. Ta cigaba da kula da hidimomin gida, ta watsar da komai, ta ɗauka yanzu komai ba komai bane... Inna ba ƙaramin farin ciki ta shiga ba, domin bata son aikin Amal, kullum a cikin tashin hankali da faɗa da masu kuɗi da ƴan siyasa. Amal ta share hawaye cikin nutsuwa. Tana son kwantar wa Inna da hankali amma zuciyarta ta cika da wata irin murɗaɗɗiyar baƙin ciki da rashin gaskiya da ta gani a duniya. Ta fahimta: gaskiya bata da matsuguni a cikin tsarin da suka sayar da komai. Amal tana zaune da Inna cikin raunanniyar murya ta ce “Inna... na san da yawa za su ce na yi rashin nasara. Amma gaskiya ba ta ƙarewa da aiki. Ta fi haka girma.” Inna ganin yanda Amal take cikin damuwa ne yasa ta fara rarrashinta tare da ƙarfafa mata gwiwa akan haƙuri... A DANDALIN SADA ZUMUNTA... Mutane da yawa sun fara fahimtar cewa dakatar da Amal ba bisa ƙa'ida ba ne. An ƙirƙiri hashtags masu ƙarfi: #JusticeForAmal #RayuwaFMHasFallen #TruthVsBillions Wani shahararren marubuci ya wallafa: “Sun koreta daga Rayuwa FM amma sun kasa koreta daga zukatan talakawa.” 💥 Amal ba zata zauna ba haka nan ba, domin zuciyarta na tafarfasa. Kuma tana da sabbin matakai da zata ɗauka domin cigaba da yaƙi da ƙazantar tsari. Ta yanke hukuncin za ta ƙirƙiri shafinta mai zaman kansa (YouTube ko Podcast) don ci gaba da faɗin gaskiya da wayar da kai.... Amma sai dai dakatarwar da aka mata ba iya wurin aiki ba, har da huld'a da social media gaba ɗaya an hanata.. Tana ƙara fuskantar ƙarin barazana daga ƴan siyasa, domin za su ga cewa ba a iya tsayar da ita da kuɗi ko tsoro. Amal ta fuskanci tozarta daga gwamnatin da ta sayar da hankali da hange da biliyoyi. Amma ita ba ta sayar da murya ba... Amal tana kuka ita kaɗai sai surutai take a ɗaki kamar wacce ta fara haukacewa, tana faɗin “Na rasa aiki. Na rasa tallafi. Amma ban rasa murya ba. Kuma murya ɗaya idan ta faɗi gaskiya na fi biliyan da suka saye shiru.” Kullum a cikin maimaita wannan kalmar take, domin sai da ta kwanta rashin lafiya sosai... Ba ci ba sha kullum a cikin kuka, ga ba kuɗin tafiya hospital, sai dai Inna ta lalla6a zuwa chemist ta siyo mata magani, amma ciwo ƙaruwa yake, Inna har ta rasa kuɗin zuwa chemist ma... Suka cigaba da jinyar gida, sai da Amal ta ɗau sati biyu a kwance, gaba ɗaya ta lalace... A wannan rana Inna tana zaune a tabarma sai Amal dake kwance akan cinyar ta sai faman juye-juye take... Wasu zafafan motoci ne manya baƙaƙe masu tayoyi ta baya kusan guda goma suka Parker a ƙofar gidan su Amal.. Mutanen unguwa kuwa kafin kace me wuri ya cika da mutane, yara da manya yanda kasan a ƙauye tsabar rashin wayewa irin mutanen unguwar...dake unguwar talakawa ne. Wasu manya-manyan bodyguards ne suka fiffito daga cikin motar suna riƙe da manyan bindigu, sun sha black glass gasu baƙaƙe wuluk, yanda kasan sojojin Amurkawa.... Ɗaya daga cikin security ne ya buɗe murfin motar da babu wanda ya fito daga cikinsa, bayan mintuna wanda yake ciki ne ya wurgo da kafarsa ɗaya, kana ganin sawun kasan ɗan manyan mutane ne, shi ɗin ba abin rainawa bane sai wanda bai san shi waye ba, in ba Amal ba babu wanda zai nuna masa yatsa ya zauna lafiya... Lokaci guda Makeekh ya miƙo daga cikin motar yana sanye da baƙin glass, ko kallon mutanen wurin bai tsaya yi ba kai tsaye ya kutsa cikin gidan, domin yau ya kudurta cewa sai yayi maganin Amal, tasa mutuncinsa ya zube a gari, kowa yana masa dariyar cewa ya fara soyayya da ƴar talakawa.... Maleekh da wasu bodyguard biyu ne suka shiga gidan, sauran kuma duk a waje suka tsaya... Inna na ganinsu ta zabga uwar salati tana faɗin "Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, sojoji kuma a gidan nan? dan Allah ku rufa mana asiri wallahi Amatu ta daina aikin jarida, gata nan rai a hannun Allah, babu lafiya..." Maleekh saida ya bari Inna ta kammala magana kafin ya ce "Assalamu Alaikum warahmatullah..." Inna ta amsa cike da mamaki... Maleekh zare glass ɗin kan dara-daran idanuwansa yayi ganin halin da Amal take ciki, a ruɗe ya ƙarasa wurin da take kwance akan cinyar Inna, shima zama yayi akan taburmar tare da ɗago ta akan cinyar Inna ya kwantar da ita akan tasa cinyar yana faɗin "Amal ce ta dawo haka? me me me meya faru da ita?..." Ganin yanda ya ruɗe ne ya bawa kowa mamaki, haka security suke kallon juna domin tin kafin su taho Ogan nasun ya sanar cewa "zai zo ne akan ya wulakanta Amal, ganin yanda video sa yake yawo tare da ita..." yanzu kuwa labari ya sauya.... Maleekh bai tsaya jiran komai ba ya miƙe da Amal, cikin gaggawa yake faɗin "Please Mama ki sako hijab hospital zan kaita..." Inna da saurin ta jin zasu tafi asibiti, haka Maleekh yayi mata ɗaukan lud'a ya fita da ita. A motarsa ya kwantar da ita sannan ya shige suka miƙe asibiti, ita kuma Inna daga baya aka taho da ita... A babban asibitin Kaduna aka kwantar da Amal, sai da Maleekh yayi jinyar ta na kwana uku kafin yayi sallama da Inna ya koma Abuja, already ya gama biyan kuɗin komai na asibitin, da abinda za'a buƙata duk ya gama biya... Sannan ya sanar wa doctor cewa 'idan da damuwa ya sanar masa a waya' .. Inna tayi matuƙar farin ciki sosai da bajintar da Maleekh yayi musu... Maleekh yana tafiya washegari Amal ta farka, ta samu sauƙi sosai, duk wata damuwa ya yaye mata, domin ba ƙaramin kulawa ta samu a asibitin ba... Bayan an sallame su ne, suna gida Amal take tambayar Inna "Inna! Aina aka samu kuɗin kaini asibiti? bayan bamu da sauran kuɗi, kuma naga babban asibiti muka je..." Inna tayi murmushi sannan ta ce "Ɗan Albarka ne.." Cikin rashin fahimta Amal ta ce "wa kenam?..." Inna ta ce "Maleekh mana..." A zabure Amal ta ce "Wani Maleekh wai?..." Inna ta ce "ke bana son shegen tambaya, Maleekh nawa kika sani..." Amal cike da mamaki take jinjina batun... Har aka ƙare makon nan Maleekh bai ƙira Amal ba sannan Amal bata ƙira shi ba, Inna tayi da ita akan ta ƙira shi tayi masa godiya amma sam Amal ta ƙi, wai ita sai idan shine ya fara ƙira tukun.... Da haka har aka sharar da zancen Maleekh.... ♡♡♡ ○○○ Amal ta shafe wata guda a cikin gida tana juyawa da rayuwa cikin tawali’u da haƙuri. Ta zamo abokiyar tafiya ta Inna daga girki zuwa gyaran gida, sannan kuma ta buɗe ƙaramin kasuwanci na siye da siyarwa a cikin gida. Tana saida kayan kwalliya, kayan miya, da snacks da ta ke sarrafa da kanta. A kullum ana jin dariyarta da sautin walwalarta da Inna.. Amal tayi alkawari wa kanta cewa "Na riga na bar aikin rediyo. Babu komawa. Gaskiya zata rinƙa faɗuwa idan na dawo gurin da aka hana ni murya.".. Wata rana Amal tana zaune kusa da Kakarta, suna shan hira, tare da tura kayan kasuwa cikin leda, sai ga muryar sallama daga bakin ƙofar. "Assalamu Alaikum..." Amal ta ɗago kai tana sakar murmushi cikin mamaki ta ce "A’isha?! Kece a nan gidan mu??" A’isha ta nufo ta da murmushi, suka rungumi juna. Kawarta ta makaranta tin secondary.. A’isha ‘yar gidan wani Minister ce, wacce ta taso cikin alatu, amma bata taɓa manta ƙawarta Amal ba. Bayan sun gaisa da Inna, ta zaro wata ƙaramar takarda mai kyalli daga jaka, ta miƙawa Amal tana faɗin “Katin bikin aurena ne! Na ce bazan bari wani ya kawo miki ba, domin sai da wannan katin ake shiga. Kuma bana so a hanaki shigowa...” Amal ta tsaya daidai. Ta kalli katin tare da murmushin da ke haɗe da dakiya. Amal cikin jin nauyi ta ce “Hmm A’isha, anya kuwa zasu bari na shiga? Na san irin mutanen da zasu taru. Ƴaƴan masu kuɗi ne ke can... kuma ni yanzu dai bana da matsayi...” A’isha ta katse ta da cewa “Kinga Amal, ki manta da komai. Yanzu kowa yana kallonki a social media, kin dai sani, kinyi fice. Kin zama celebrity ba tare da kin nemi hakan ba. Kuma mutane da yawa ciki har da ni muna alfahari da ke. Wannan bikin kuwa, bana so kije a hanaki. Ni da kaina zan karɓe ki a ƙofa.” Amal ta riƙe katin kamar kuɗi, tana kallon shi da ƙwarin gwiwa..... Inna ta yi gyaran murya tare da faɗin “Amal, Allah ne ke kawo mutum da wadata ta hanyoyin da ba ya zato. Ƙila wannan katin ba kawai na biki bane... wataƙila ƙofar sabon fata ne.” Bayan tafiyar A’isha, Amal ta zauna da katin a hannunta tana kallonsa kamar tana karanta sirrin duniya a jikin sa. A gefe kuma Inna ta na harhada kayan miya, amma tana kallonta da ido ɗaya, ta ce "Ke dai Amal... Allah na tare dake. Ki tafi ki je biki, amma da addu’a. Ki sani ba kowanne gayyata ce da nufin sharri ba, wasu ana kawo ta ne don alkhairi." Amal ta kada kai tana murmushi, amma daga ciki zuciyarta tana cike da tunanin tsaro, tsoro da kuma ciwon da zuciya ta sha kwanan nan. Duk da haka, akwai wani saƙo da ya fara janyo hankalinta, zuciyar ta tana ce mata wannan ba biki kaɗai bane… wata alama ce daga sama... Bayan kwana biyu Amal tana zaune tana kallon kayanta cikin akwati, Ba komai mai tsada a ciki, amma akwai wani ƙaton atamfa da ta fi so. Tuni ta zaɓe shi domin tafiye-tafiye na girmamawa... Ta wanke gashin kanta da man shafawa... Ta yi kwalliya sosai, ba ƙaramin kyau tayi ba, ga ta fara ce tass ko bata yi kwalliya sosai ba farin ta zai ƙara mata kyau, ga gashin giran nan ya kwanta luff, komai ya tsaru a jikinta. Yanda kasan ƴar India, amma ita ɗin fulani ce ta asali.. Bayan ta kammala shirinta ta fito tana faɗin "Inna, nayi kyau?.." Inna ta yaba sosai tare da yi mata fatan alkhairi.... Bayan sallar la’asar, motar da A’isha ta turo ta iso a bakin titi. Amal ta fito cikin riga mai launin sky blue, riga da sket sun matse ta sosai, ga ta sha takalmi mai tudu, asalin surar ta ya fito sosai, ba abun rainawa a jikinta masha Allah, fuskar ta kamar ba mutum ba, powder da ta shafa yasa farinta yayi dauuu har ɗaukan ido yake.. Inna ce ta leƙo daga ƙofar gida tana faɗin "Ki tsaya na makj addu’a ƴarnan...." Amal ta tsaya Inna Ta ɗora hannu a kanta, tana karanta ayoyi cikin murya mai raɗa. Bayan haka, ta ce: “Ki je da aminci. Idan alkhairi ne ki dawo da ƙarin daraja. Idan sharri ne, Allah ya 6atar da shi kafin ki isa.” Amal ta amsa da "Amiin".. A cikin motar, Amal tana kallon waje cikin natsuwa. Duk inda suka wuce, mutane suna tafiya da abubuwan rayuwarsu amma zuciyar Amal na tafiya da saƙo.. tana magana a ranta "Zan je, zan tsaya a cikin taron masu daraja. Amma zuciyata za ta zauna cikin ƙasƙanci, domin ni yar gajiya ce, ba ƴar isa ba..." An shirya wajen bikin yayi kyau fiye da yadda Amal ta hango a tunaninta. Babban filin da aka tanadar ya sha kwalliya da furanni, fitilu masu launi, da gilashi masu walkiya. Kowane mutum da yake cikin bikin yana nuna jin daɗi, daraja da kima. Kamar yadda A’isha ta faɗa, sai da katin gayyata ne ake shigowa. A lokacin da Amal ta ƙaraso bakin shiga, jami’an tsaro suka tsaya suna duban ta. Miƙa musu katin tayi a hankali, suna dubawa suka ce: "Welcome, ma’am." Ta shiga.... Kamar wani wutar lantarki da aka kunna, idanuwa da dama suka karkata gareta. Tana tafiya cikin nutsuwa, tafiyarta na ɗauke da tarin tausayi da kima. Wasu daga cikin ƴaƴan masu kuɗi da ke cikin bikin sun ganta ne daga cikin video da ya yaɗu, video ɗin Maleekh yana kwance a kanta. Wasu suka fara magana suna faɗin “Wannan ba ita bace wadda Maleekh ya faɗi a kanta?” “Yar talakawa ce fa… amma tana da kwarjini.” “Kin san sun ce sun kore ta daga aiki saboda politics?” Wasu kuwa sun hau ƙiran sunanta a social media, suna cewa: #QueenOfCourage #AmalOfThePeople #MaceMaiKwarjini A nesa daga cikin VIP section, shigowar Maleekh kenam, ya zauna cikin rigar shadda white color, mai bala'in tsada, domin bazaka taɓa samun irin shaddar a Nigeria ba, ga ya ɗaura white glass ɗan siriri akan golden eyes ɗinsa, yana motsi da ɗan ƙaramin lips ɗinsa da ya sha lip glowin sai sheƙi yake, ga wata farar hula da ya ɗora akan sumar sa da ya sha gyara, shima ba ƙaramin kyau ya yi ba, chocolate handsome guy, ga wani gyara da yayi wa sajensa sai ɗaukan ido yake.... Duk ƴan matan wurin idonsu akan sa yake, farashin Maleekh na da matukar tsada, ga kyau ga kuɗi ga ilimin boko da Arabic, ƙaramin shekaru, bazai wuce 30 ba... Yana tare da wasu manyan baƙi, ciki har da wasu ministoci da mutanen ƙasashen waje, yana duba yanayin taron, dake bikin ƙanwarsa ake, sai dai ita A'isha ba mahaifiyarsu ɗaya da Maleekh ba, A'isha da kannenta mata biyu da mahaifiyarsu suna zaune ana Kaduna. Maleekh kuma da kannensa mata biyu da mahaifiyarsu su kuma suna Abuja... Ɗago kai da zaiyi kwatsam idanunsa suka sauƙa a kan Amal dake zaune ita kaɗai.. Zuba mata ido yayi ko kibtawa babu, a zuciyarsa ya ce "Tana kallon kamar ba ta damu da duniya ba. Amma duniya ce ta damu da ita yanzu..." 🌟 A lokacin da MC ke gab da gabatar da wani ɓangare na shirin, aka sanar da cewa za’a bawa wasu baƙi kujerun VIP saboda "irin jajircewar su a rayuwa." Abin mamaki Amal na daga cikin jerin sunaye! MC ya faɗi suna da ƙarfin murya tare da faɗin "Amal Abdulsamaad, mace mai daraja daga cikin matan ƙasar nan da suka tsaya da gaskiya fiye da kuɗi da ƙarfi!" Kowa ya zaro ido. Amal ta tashi cikin ladabi, amma zuciyarta cike yake da mamaki... Maleekh cikin murmushi yake kallonta domin shi yasa a bata... Bayan ta zauna.. A cikin nutsuwa da salon kwarjini, Maleekh ya tashi daga kujerarsa, yana matsowa kusa da ita. Mutane ne suka zuba ido, domin kowa idonsa akan su yake... Amal jin mutum a gefenta yasa ta kalli wurin, ganin Maleekh ne yasa ta zaro ido waje tana kallon sa.. Maleekh cikin sassanyar murya ya ce "Zan iya magana dake Amal?" Kafin ta amsa, A’isha ta zo yanda suke cikin kayan Amare ta ce: "Let me steal her for a second Yah Maleekh." Ta janyo Amal gefe, sannan ta raɗa mata a kunne: "Duniya tana kallon ku. Ki tsaya da gaskiyar ki, ko ma meye zai biyo baya.".. Maleekh ganin yanda mutane suka zuba masa ido yasa ya koma yaje ya zauna a yanda yake... MC ne ya bayyana a filin wurin. (Jama’a kowa ya nutsu. Fitilu na lilo a sama. Idanun mutane suka koma kan dandalin yayin da MC ya taka gaba cikin kwarjini.) MC cikin fara’a ya ce "‘Yan uwa maza da mata, da fatan za ku tar6i wata baiwar Allah wacce bata buƙatar gabatarwa, jaruma, hazika, muryar matasa Amal Abdulsamaad!” Tafi ya karaɗe wurin. Wasu na tafawa saboda kaunar da suke wa Amal, wasu kuwa domin sha’awa, wasu kuma saboda mamaki.... Amal ce ta miƙe cikin natsuwa, tana tafiyarta cike da nutsuwa ta sa kowa kallonta. Ta isa muryar mic, ta sauƙe numfashi. Ta fara... “Assalamu alaikum warahmatullah. Sunana Amal Abdulsamaad. Ni ƴar asalin Kaduna ce, kuma yanzu haka ina da shekaru 22 da haihuwa. Na rasa iyayena ne tun ina da shekara uku a duniya, sanadiyyar wani hari na siyasa da ya shafi iyayena. Tun daga wannan lokaci, kakata take kula dani wato mahaifiyar mahaifina. Ita ce ta koya min gaskiya. Ita ce ta gina ni akan jarumta. Kuma ta koya min cewa talauci ba laifi ba ne amma rayuwa ba tare da gaskiya ba, tabbas azaba ce.” (Jama’a kowa yayi shiru. Har Maleekh sai da ya ɗan matso gaba daga inda yake zaune.) “Ban taso a cikin dukiya ba. Na tashi a cikin gaskiya. Ban yi makaranta a ƙasashen waje ba. Amma a makarantar mu ta ƙasata na samu abokiya ta gaskiya wato ita ce A’isha.” (Ta kalli amarya A’isha da murmushi wanda ya bayyana zurfin kaunarsu.) “Tun a makaranta A’isha ce ta fara raba abincinta da ni lokacin da ba ni da nawa. Ita ce ta fara tsayawa min idan ana yi min dariya saboda talaucina ko saboda natsuwata. Ta daina kallon banbancin mu. Iyayenta na gwamnati, nawa kuwa na cikin kabari amma mu mun kasance ‘yan mata, abokai, ƴan uwa.... **“Rayuwa ta raba hanyoyin mu, ni na zama mai magana da jama’a, A’isha kuma ta kasance jakada ta ladabi da ilimi. Amma yau ga mu nan kuma komai bai canza ba. Ina alfahari da ita, kuma ina alfahari da kaina.”** (Ta tsaya. Muryarta ta lafa, cikin tausasa murya) “Idan akwai abu ɗaya da nake so kowa ya tuna daga wannan jawabi, shi ne: Ba sai kana da babban suna ba kafin ka zama babban mutum. Ba sai kana da izini ba kafin ka faɗi gaskiya. Kuma ba sai kana da iko ba kafin ka zama mai ƙarfi.” (Matasa suka fara tashi suna tafi. Wasu manya suka bi sahu. A’isha tana goge hawayen farin ciki) Amal ta rufe da cewa: “Gare ki amarya A’isha nagode da kasancewa kamar yadda kika kasance. Gare ku masu saurare nagode da wannan dama. Kuma gare ku ƴan Kaduna daga kowanne gida muryarku na da tasiri.” (Ta sunkuyar da kai cikin girmamawa ta koma kujerarta. Hotuna na ci gaba da ɗauka. Wurin taron ya cika da amo.) MALEEKH yana kallonta Bai tafa hannuwa ba. Yana zaune ne kawai, laɓɓansa a gimtse, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, yana maganar zuci "Ba kawai murya ce ta rediyo ba... juyin juya hali ce a cikin jikin Amal...." asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 13 to 14 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 MC ne ya karɓi mic ɗin daga hannun Amal cikin fara'a, ya juya ya dubi taron, sannan ya kalli Amal wacce take shirin barin wurin. MC ya ce “Eh-eh! Amal bamu gama dake ba fa! Mutane da yawa suna da tambaya, mu ma muna da tambayoyi. Kuma nasan akwai waɗanda suka zo ne saboda ke.” Jama’a ne suka fara dariya da tafi. Amal ta murmusa kaɗan, ta tsaya daidai gefen MC. Ya miƙa mata mic. MC cikin nishadi ya ce “Amal, mun san ki ba kawai a nan ba, har a kafafen watsa labarai na ƙasashen waje. Yanzu idan da ace wani ne ya samu irin shahara da goyon bayan da kika samu, da tuni yana da gida na alfarma, manyan motoci, kudi a account amma meyasa har yanzu kina zaune a irin yanayin da mutane da dama ke ƙira ‘talauci’?” Amal ta ɗan gyara tsayuwarta. Ta ɗago kai cikin natsuwa ta ce “Na gode da tambayar. To gaskiya talauci ba laifi ba ne, kuma arziki ba a tantance mutum da shi. Ni na zaɓi rayuwar gaskiya akan rayuwar ƙaryar kuɗi. Inada ikon in karɓi cin

Chapter 8 of 62