lips touch na tsawon lokaci da aka yi missing juna. Amal ta kasa jurewa ta buɗe idonta, lokaci guda ta rufe su ta sakar da wani irin numfashi mai taushi...
Sun tsaya haka na ‘yan dakiku suna jin numfashin juna, hannayensa a gefen fuskarta, nata hannayen a kirjinsa. Wani irin kewar juna ya lulluɓe su gaba ɗaya...
Sai daga baya Amal ta ja numfashi ta janye jikinta ta koma gefe a hankali, idonta a ƙasa, hawaye suna gangarowa. Maleekh kuwa ya sauƙe hannayensa, ya juyo gefe, zuciyarsa na bugawa kamar zata fashe...
A hankali cikin rawar murya ta ce:
"Ni zan tafi ..."
Ba tare da ya bata amsa ba ya ƙara tako wa yanda ta ke. Yasa hannu yana ɗago da ha6arta..kallon juna suka yi daga bisani ya ƙara mannata a jikin bango...
Ya ce: "kina so ki je wancan yaron ya ci gaba da shiga jikinki?.."
Ya matseta sosai a bango, idanunsa suna tsiyayar da ƙiyayya da kishi, amma zuciyarsa ta cika da kewar da ya kasa ɓoye wa.
“Na tsane ki, Amal…!” ya furta cikin rawar murya, amma idanunsa sun bayyana akasin maganar.
Amal ta runtse idonta tana hawaye, zuciyarta tana karyewa. “Ka tsane ni… amma zuciyarka har yanzu tana kirana Maleekh. Idan ba haka ba, me yasa kake tsayawa kusa dani haka?..”
Shiru ya ratsa su. Numfashinsu ya haɗu, jikinsu ya haɗu.
A hankali hannunsa ya zame daga jikin bango zuwa fuskarta, ya ɗago haɓarta. Amal ta buɗe idonta ta kalle shi, su biyun suka tsaya kallon juna, idonsu na magana da ɗaruruwan kalmomi.
Sannan kamar wani abu ya rinjaye shi, Maleekh ya sauƙe ƙaramin bakinsa akan nata a hankali. Wani irin sanyi ya ratsa zuciyar Amal, ta yi ƙoƙarin janye kanta amma ta kasa.
Ya fara soft, yana tsotsa a hankali kamar mai roƙon gafara. A hankali ta lumshe ido tana mayar masa da martani, sai sumbatar ta rikid'e zuwa mai zafi, kewar da suka daɗe suna dannewa ta fashe gaba ɗaya.
Hannayenta suna kan kirjinsa, jikinta a manne da jikinsa. Hannunsa ya koma bayanta yana rungumeta sosai, tamkar zai haɗiye ta gaba ɗaya.
Sun tsaya cikin doguwar sumbata mai ɗauke da soyayya, ciwo, da kewar juna. Duk wani ɓacin rai da zargi ya rikide zuwa zafi mai cike da soyayya.
Da ƙyar suka rabu da juna, dukansu sun kasa numfashi yadda ya kamata. Amal ta jingina kanta a kirjinsa tana sauƙe numfashi, shi kuma yana shafa kanta yana rarrashi zuciyarsa na bugu..
Numfashinsu ya ragu ya koma nauyi, kallo ɗaya suke iya yi wa juna.
Amal ta ɗago idonta, idanunta sun cika da hawaye. A hankali ta furta da murya mai rawa:
“Wannan… bai kamata ya faru ba, Maleekh.”
Ta zame jikinta da ƙarfi daga hannunsa, tana girgiza kai kamar wacce aka yi wa asiri. Hawaye suka cika a idanunta...
“Ka daina… kar ka ƙara kusantata haka,” ta faɗa cikin tsananin ruɗani, kafin ta juya da gudu ta fice daga office ɗinsa.
Maleekh ya tsaya a tsaye, hannunsa yana kan bango, zuciyarsa na tsananta bugawa. Idonsa ya kaɗa ja, ya shaƙi iska kamar zai yi ihu...
“Amal…” ya furta da ƙasa-ƙasan murya, kamar yana magana da zuciyarsa.
Shi dai ya kasa bin bayanta, kawai ya buga hannunsa da ƙarfi a kan tebur, gilashi ya girgiza. Ya dafe kansa, yana ƙoƙarin murƙushe kewar da ta sake tashi cikin jikinsa.
Amal kuwa da gudu kai tsaye ta shige cikin office ɗinta. Ta rufe ƙofa ta jingina tana huci, tana kuka.
Ta dafe bakinta da hannunta tana ambaton Allah a zuciya:
“Me yasa haka yake faruwa? Me yasa ban iya tsanar Maleekh ba duk da abinda ya min?… Ya Allah ka bani ƙarfin zuciya…”
Ta zauna a kan kujerarta, da biro a hannunta, amma jikinta na rawa. Amma abin da zuciyarta ke bugawa shi ne ɗan ɗanɗanon sumbatar da har yanzu ba ta iya mantawa da shi ba.
Amal tana zaune a kan kujerarta tana ƙoƙarin danne kukanta, tana share hawayen da ba su daina zuba ba. Ganin wani ƙaramar gift box a kan desk ɗinta yasa ta dakata tana kallonta.
A hankali ta miƙa hannu ta ɗauka. A saman akwatin an rubuta da ƙaramin salo:
“To my pretty 🌹 From Zayd.”
Amal ta tsaya cak tana kallo, zuciyarta na wani irin bugu. A hankali ta buɗe akwatin, duk da tasan meye a ciki...
A ranta take faɗin
"Wannan mutumin bai tafi da wannan abun nashin ba?.."
Ta ciro ƙayataccen necklace mai ɗauke da ƙaramin heart pendant.
Ta ɗaga shi sama, hasken office ɗin ya daki pendant ɗin ya ƙara haskawa da kyau.
Wani irin nauyi ya sake saukar mata a zuciya. Ta rufe idanunta, ta tuna da kalaman Zayd kullum yana kiranta “my pretty”, sannan ta tuna yadda Maleekh ya kalleta a ɗazun cikin kishin da bai iya ɓoyewa ba.
Hawaye suka sake zubo mata, ta jingina da kujerarta tana riƙe da necklace ɗin.
A hankali ta furta cikin shessheƙar kuka:
“Me yasa rayuwa zata min haka?… Me yasa kowanne yana ƙoƙarin mallake ni, amma zuciyata bata son kowa face shi da ya kore ni?”
Ta ajiye necklace ɗin a kan desk tana kallonsa, kamar yana yi mata tambaya. Zuciyarta ta ƙi amsa.
☆☆☆☆☆
Ranar weekend, gidan ya yi shiru bayan sallar la’asar. Amal da Inna zaune a falo suna kallon wani tsohon shirin Hausa a TV. Sai ga maigadi ya shigo da sallama.
Maigadi ya ce:
“Amatu, anzo ana cewa sallama dake a waje.”
Amal ta ɗago daga kan remote tana dubansa da mamaki.
Ta ce:
“Maleekh ne?…”
Inna tayi saurin katse ta da cewa.
“To waye in ba shi ba? Kaje ka ce ya shigo mana, ai ya cancanci ya shigo ba tare da tambaya ba, ai nan ma gidansu ne.”
Ta ƙarasa tana kallon Amal da ɗan harara..
Amal ta kalleta kawai, bata ce komai ba, ta maida kai ga TV.
Maigadi ya tashi ya fita. Bayan ɗan lokaci sai suka ji knocking a ƙofar falo.
Inna ta juyo ta dubi Amal.
Ta ce:
“Je ki buɗe masa falon mana.”
Amal ta tashi da ɗan rashin son takura, tana sanye da guntun jeans da t-shirt mai ɗan siriri. Da take bata shirya baƙo ba, sai tafiyar ta ɗan yi nauyi.
Ta kai hannu ta buɗe ƙofar… sai ta zaro manyan idanu tana kallon Zayd, wanda yake tsaye da ƙayataccen jan flower irin na masoyan soyayya.
Zayd ya tsaya yana murmushi, idonsa yana biye da ita daga sama har ƙasa.
Yana murmushi ya ce:
“Mu shiga ciki mana, Pretty. Na gaisa da Mama ko?…”
Kafin Amal ta samu damar magana, sai ya ratsa gefenta cikin sauƙi ya shiga falon.
Inna da ta ɗaga kai tana sa ran ganin Maleekh, sai ta haɗa ido da wani sabon fuska mai ɗauke da annuri..
Ta sake baki tana faɗin:
“Amatu! Wannan kuma a wane daji kika samo shi? Ko shima ɗan club ne?!”
Amal ta tsaya bakin ƙofa tana mamakin yanda ya shigo gida da sauƙi haka.
Zayd ya yi murmushi yana kallon Inna cikin natsuwa.
Ya ce:
“Wannan da dukkan alamu kakarki ce, ko Pretty? naga kwakwalwarta ta fara juyawa…”
Inna ta zabura ta miƙe tsaye, ido a waje tana faɗin
“Ni kake ƙira mahaukaciya? Kai ɗan iskan yaro!”
Zayd ya ɗaga hannunsa cikin nutsuwa yana faɗin
“A’a, Kaka, kwantar da hankalinki. Wallahi ba haka nake nufi ba. Ina nufin kamarki irin na ƴan birni, da surutu irin na masu kuɗi...”
Amal ta hanzarta tsoma baki da cewa.
“Inna… wannan ɗan uwan Maleekh ne.”
Inna ta tsaya cak. Fuskar ta sake kamar wadda aka zare wuta daga jikin lantarki.
Inna ta ce:
“Uhmm… ai na ga shi ma akwai kyau, kamar irin ƴaƴan Ƙaruna. To shigo, shigo, ya zama dole ai a tar6e ka...”
Ta zauna tana hararar Amal, ita kuwa Amal bata san inda zata saka idonta ba.
Zayd ya miƙa flower ɗin hannunsa ga Amal yana murmushi, sai ya zauna kamar mai gidan, ya ɗora ƙafafunsa cikin natsuwa.
Ya zauna a kujera cikin kwanciyar hankali, ya ɗora flower ɗin a gefen Amal. Yana gyara zaman rigarsa, idonsa na bin Amal a hankali.
Ya furta
“Kaka, wato wannan irin kallo da kike min yanzu, zai iya sa mutum ya fi ƙarfin soyayya.”
Inna ta ce
“Soyayya kuma? Kai dai ka bayyana, ɗan wane kai? Ko ma dai ɗan waye, kada ka zo mana da zancen club nan.”
Zayd ya yi murmushi, yana jingina da kujera ya ce:
“Toh, ni dai ni Zayd ne. Na dawo daga ƙasar waje wato London, yanzu haka dai ban saba da kowa ba sai Amal.”
Amal ta yi saurin kakkabe maganar da cewa.
“Eh, amma dai Inna, ni ba abinda ya haɗa mu da shi sosai. Ɗan uwansa ne dai Maleekh …”
Zayd yana katsar mata magana da lumshe ido ya ce
“Ɗan uwana? Ni ma na ji kamar ɗan uwana ne.”
Inna ta kalli Amal sannan ta ce
“Amatu, wannan saurayin kuma sai kace an yi masa training a club. Yadda yake surutun nan ya fi maza nan garin. Toh, kai ɗan wane ka ce? Kuma kai ne babban ɗan uwan Maleekh ko ƙarami ne?”
Zayd ya ce:
“Ni dai zan fi son ki ƙira ni Angon amarya tunda na shigo gida.”
Inna tayi dariya tare da rashin fahimtar sa ta ce:
“Yau na ga wannan yaron, akwai raini da sa dariya sosai. Amma duk da haka, akwai kyau.”
Amal ta ɗan kauda kanta gefe, zuciyarta na bugawa. Bata taɓa tunanin Zayd zai shigo har gidan ta ba..
Zayd ya ɗauki flower ɗin ya miƙa mata da murmushi, yana faɗin
“Wannan ba domin Kaka bace, don ke ne. Pretty, ke kika jawo ni har gidanku.”
Amal tana kallonsa ta ƙi karɓa..
Inna ta harareta tare da faɗin:
“Amatu, karɓi kyautar nan mana, ki ajiye. Ai mace ba ta ƙin kyauta, ko daga wane ne.”
Sai ta juyo tana kallon Zayd da murmushi.
Inna ta ce.
“Toh Zayd, ina wannan ɗan uwanka ne? Shi ma ya zo ne?”
Zayd ya ɗan gyara murya, ya ce:
“Shi?… yana can wajen guda. Amma Kaka, bari na gaya miki gaskiya, ni dai Amal ce nake so, ba wani abu ba.”
Amal ta kalli Inna a firgice, idonta cike da faɗuwa.
Inna kuwa tayi dariya tana girgiza kai ta ce:
“Toh Amatu! Ai yanzu komai ya fito fili. Wannan ɗan uban yaron ya fi ƙarfin ɓoye ɓoye. To Allah ya sa alheri. Tin da wancan ɗin ya ƙi ki sai ki kama wannan kar kiyi sake reshe kama ganye...”
Amal ta kaɗa kanta a hankali, zuciyarta cike da rikici tsakanin Maleekh da kishinsa, da kuma Zayd da kulawarsa..
Inna ta kalli Amal da murmushin sannan ta miƙe tana faɗin:
“Ni dai zan je ɗaki na kwanta, ku ci gaba da hirarku. Amma Amatu, ki tuna da maganata, mace ba ta ƙin kyauta, ko nawa ya baki ki karɓa …”
Ta wuce tana dariya, ta bar su biyu a falon. Amal ta yi shiru, ta kasa kallon Zayd kai tsaye, zuciyarta na buga wa..
Zayd yana jingine a kujera, yana mata kallon soyayya ya ce.
“Pretty, gaskiya yau na samu farin ciki. Na yi tunanin zaki kore ni daga ƙofar gida, amma sai ga ni har cikin falonku, na zauna lafiya.”
Amal ta ɗan gyara zaman ta, tana wasa da flower ɗin da ya kawo ta ce:
“Ni ban taɓa tsammanin zaka iya zuwa gidana haka ba, bare har ka sami damar zama a nan.”
Zayd yana matsowa kusa da ita a hankali ya ce:
“Kina so in gaya miki gaskiya? Ni dai ina ji kamar kin tsare zuciyata. Duk sanda naga murmushinki, komai a raina yana sauka.”
Amal ta ɗan ja numfashi, tana ƙoƙarin boye fargabar da ke cikinta.
Ta ce:
“Zayd, don Allah ka tsaya… bana son irin wannan maganar.”
Zayd yana ƙanƙance ido, yana matsowa kusa sosai ya ce
“Wani lokacin magana ba ta isa, sai zuciya ta furta kanta. Ki duba idona Amal, kiga gaskiyar da ke ciki.”
Ya ɗan kai hannunsa yana ƙoƙarin taɓa hannunta me flower, ya riƙe tafin hannunta. Amal ta yi saurin janye hannunta, tana jin zuciyarta na bugawa fiye da yadda ta saba.
Amal cikin murya mai rawa ta ce:
“Don Allah ka daina. Wannan abun bai dace ba.”
Zayd yana murmushi cikin natsuwa ya ce:
“Shikenan, zan daina faɗa… amma ba zan taɓa daina ji ba. Komai ya faru, Amal, na tabbatar ina ji dake.”
Amal ta yi shiru, ta kasa cewa komai. Ta ji kamar idan ta zauna da shi naɗan lokaci, zuciyarta zata rufta gaba ɗaya. Sai kawai ta miƙe tsaye, tana daidaita flower ɗin a hannunta.
Ta ce:
“Na gode da ziyara, Zayd. Yanzu fa sai ka tashi.”
Zayd ya kalleta cikin natsuwa, sannan ya murmusa.
“Ba damuwa, pretty. Zan tafi yanzu… amma ki sani, ni ba zan fasa ba.”
Ya miƙe, ya nufi ƙofa, sai kuma ya juyo ya sake kallonta.
“Ki bar wannan flower a zuciyarki, koda kuwa baki karɓi zuciyata ba.”
Ya fita a hankali, ya bar Amal tsaye a falon tana riƙe da flower ɗin, zuciyarta cike da rikici.
☆☆☆☆
Bayan komawar sa gida...
Zayd ya shigo gida cikin annashuwa, yana ta tauna chewing gum da murmushi a fuskarsa. Sai ya nufi babban falon da Maleekh yake zaune, yana kallon TV amma hankalinsa ba a wajen shirin yake ba.
Da ya hango Zayd, sai kawai ya ce da sanyin murya.
“Lafiya yau sai farin ciki kamar wanda ya ci award?”
Zayd ya zauna a gefensa yana dariya ya ce:
“Bros! Wallahi zan gaya maka gaskiya… na ziyarci pretty ɗina.”
Maleekh ya ɗan ɗago kai a hankali kamar wanda aka kai masa duka, yana tambaya da yanayin da bai dace ba:
“Wace pretty?”
Zayd yana wasa da key ɗinsa ya ce:
“Wace kuma idan ba Amal ba? Wato assistant ɗinka nan. Kai bros, gidan nata kuwa cikakke ne, Kakarta ma ta sanni yanzu.”
Maleekh ya kasa amsawa. Kallon Zayd yake da wani irin yanayi da ba za a iya fassara shi ba. Zuciyarsa ta cika da kishi, amma fuska ta ɓoye komai.
Zayd yana murmushi, bai ma lura da halin Maleekh ba ya ce
“Wallahi bros, Amal ba irin sauran girls bane. Tana da nutsuwa, tana da kamala. Ka ga ai da irin wannan mace ce za ta zama wife ɗina, company ɗinka ma zai sami nutsuwa”
Maleekh ya tsaya cak, muryarsa ta sauya.
“Zayd.”
Zayd ya tsaya yana kallonsa, yana mamakin yadda muryarsa ta yi nauyi.
Maleekh ya ce:
“Ka ce ka je gidanta?”
Zayd yana murmushi ya ce
“Eh mana! Me yasa?”
Maleekh yana jujjuya glass cup a hannunsa, yana ƙoƙarin danne damuwarsa ya ce
“Ba komai... kawai na tambaya ne. Ka ce Kakarta ta karɓe ka da fara’a?”
Zayd ya ce:
“Fara’a kuwa sosai. Gaskiya sun karɓeni sosai. Amal ma... hmm bros, idan ka ga yadda ta yi kyau cikin casual wear ɗinta kai, ba zan iya mantawa da wannan kallo ba.”
Maleekh ya kalli gefe, yana maida numfashi da ƙarfi, kamar wanda zuciyarsa ke ƙonewa amma yana ƙoƙarin zama cool.
Maleekh da murmushi mai ɗaci ya ce:
“To, ai sai ka cigaba... idan kana ganin hakan zai sa ka farin ciki.”
Zayd ya yi dariya yana faɗin:
“Ni kuwa ina da tabbaci bros! Zaka ga yadda pretty ɗina zata sauko cikin soyayya ba da daɗewa ba.”
Ya miƙe yana jefa key ɗinsa sama yana catching.
Ya ce:
“Goodnight bros, ka huta. Ni zan fara tsara plan na gaba.”
Ya fita da murmushi.
Da ƙyar Maleekh ya iya ɗaukar numfashi. Ya riƙe glass ɗin da yake riƙe sosai, har sai da ya ji yana girgiza.
Sai kawai ya furta cikin ƙasa da murya, zuciyarsa na rawa:
“Amal... me kike son yi min?”
Ya miƙe a hankali, ya nufi window, yana kallon dare kamar yana neman amsar da zuciyarsa ta kasa faɗa masa...
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 51 to 52
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Ƙarfe 12 na dare, Maleekh ya kasa bacci. Duk jikinsa cike yake da wani irin zafi da naci. Ya kasa jure tunanin Zayd yana kusa da Amal, yana bata kyauta, yana murmushi da ita.
Ya miƙe ya ɗauki key ɗin motarsa, ba tare da ya faɗa wa kowa inda zai je ba.
Security na bakin gate suka tsaya da mamaki suna tambaya:
“Sir, midnight fa... ina zaka je haka?”
Amma ya wuce su tamkar ba ya jinsu, fuskarsa ta cika da nufin ɗaya..
A ɗari yake gudu da motar ya nufi gidansu Amal..
Bayan mintuna ya isa.
Motarsa ta tsaya a gaban gidan Amal.
Ya yi horn sau biyu, maigadi ya fito da sauri.
“Haba Oga Maleekh! Wannan lokaci fa?”
“Buɗe mun ƙofa.”
Ya furta cikin murya mai sanyi mai cike da iko ta sa maigadin bai sake tambaya ba.
Ya shiga cikin gidan, falo a kulle an rufe ko ina, duhu ya lulluɓe komai..
Ya ƙira Amal a waya, ringing... amma babu amsa.
Yayi shiru yana sauraron numfashinsa, sai daga bisani ya ɗaga kai zuwa sama, inda taga windown ɗakinta yake..
Ya furta a hankali.
“In gan ta... ko da sau ɗaya ne.”
Window ɗin a ɗan buɗe take.
Babu jinkiri ya haura yana taka wuraren da zai iya kai shi sama.
A hankali ya tura window ɗin,
Da kyar ya shige, ya tsaya yana kallon ɗakin komai tsaf, ya ji ƙamshin turarenta da ya saba ji a ofis.
A nan ya tsaya…
A katafaren gadon nan, Amal na bacci, tana sanye da soft pink sleepy dress, gashin kanta ya bazu saman pillow, fitilar ɗakin ta haskaka fuskarta cikin nutsuwa.
Maleekh ya zauna bakin gadon. Ya jingina hannu da cinyarsa, yana kallonta.
Daga bisani ya miƙar da hannu yana shafar fuskarta a hankali kamar wanda yake taɓa mafarki.
“Amal…”
“My pretty…”
“Kina tunanin zan iya jure ganin wani yana miki kyauta?”
Muryarsa ƙasa ƙasa, ya furta hakan..
Amal, a cikin baccinta, ta ji kamar ana taɓa fuskarta.
Ta motsa, ta buɗe ido a hankali
Ganinsa yasa ta zabura ta tashi zaune cikin tsoro.
Ta buɗe baki zata yi ihu
Da sauri ya toshe mata baki da hannunsa.
Maleekh cikin raunin murya ya ce
“Shhhhh! Amal... it’s me. Ni ne Maleekh.”
Jin muryarsa yasa hawaye taruwa acikin idanunta.
Zuciyarta ta tsaya cak.
Idanunsu suka haɗu a cikin duhu, hasken wata na sauka saman fuskarsu.
Amal cikin muryar kuka ta ce
“Me kake yi a nan, Maleekh...? Me yasa zaka shigo min gida cikin dare haka?”
Maleekh ya ce
“Saboda bazan iya bacci ba... Bazan iya jure ganin wani yana sonki ba, Amal.”
Ya miƙe tsaye yana kallonta, numfashinsa na fita a hankali, kamar mutum da yake yaƙi da kansa.
“Na rantse ban zo don in takura miki ba... Na zo ne don in faɗa miki gaskiyar zuciyata.”
Tana kallonsa da shanyayyun eyes ɗinta. Numfashinta yana saurin fita...
A hankali ya furta cewa
“Ina so muyi magana, Amal.”
Ta kasa cewa komai. Sai kawai ta jinjina kai, tana dubansa cikin rashin fahimta.
Ya ƙaraso kusa da ita, idanunsa suka cika da wani irin kishi mai nauyi.
“Amal, akwai abu guda biyu da nake so ki faɗa min yau a daren nan.
Ni kike so… ko Zayd?”
Ta kalli ƙasa, muryarta ta kasa fita.
“Maleekh…”
Ta furta sunansa a hankali...
Ya ce:
“Kada ki ƙira sunana idan baki da tabbaci.”
Shiru ya biyo.
Sai a hankali ta buɗe baki ta tambaya:
“Idan na zaɓe ka fa?”
Ya ɗan saki numfashi, ya ce da murya mai taushi mai cike da iko:
“To ki daina karɓar kyauta daga hannunsa. Ki daina bari ya taɓa ko yatsanki. Kuma kada ki sake barinsa ya kusance ki.”
Ta jinjina kai, idanuwanta na ɗauke da hawaye.
Sai kuma ta ce da ƙaramin murya:
“Idan kuma Zayd na zaɓa fa?”
Maleekh ya ɗan janye daga kusa da ita. Ya ɗauki numfashi mai zurfi, sai kuma ya furta cikin sanyi:
“Zan kashe ki… sannan na kashe shi.”
Kalmar ta tsaya a kunnenta kamar ƙarar guguwa.
Ta zaro ido tana kallonsa da tsoro.
Shi kuwa ya tashi tsaye, bai sake cewa komai ba.
Ya nufi window ɗin da ya shigo ta, ya fita a hankali, ya ɗinka harabar gidan cikin duhu..
Yana fita daga gidan.
Motarsa ta tashi da sautin injin mai ƙarfi, ya bar gidan da zuciya mai raɗaɗi da kishi...
_Washegari_
Amal ta farka da safe cikin wani irin nauyin tunani da bugun zuciya.
Tunanin abin da ya faru da daddare bai bar kanta ba.
Ta zauna a gefen gadonta tana kallon window ɗin da Maleekh ya shigo ta jiya, zuciyarta na bugawa kamar ana danna ƙaho a ciki.
“Zan kashe ki… sannan na kashe shi…”
Kalmar ta koma tana juyawa a kwakwalwarta.
Ta dafe kanta da hannaye biyu tana numfashi mai nauyi.
“Ya Allah! Ka sauƙaƙa mun halin da nake ciki”
Ta miƙe ta shiga toilet ta watsa ruwa, amma har cikin ruwa tana jin kamar hannun Maleekh yana shafar fuskarta, irin taushin hannunsa, amma kuma da dumin barazana a cikinsa..
Ta fito ta shirya tsab..Tana riƙe da handbag da waya, ga wani irin takalmi mai tudu da ta sanya, tana sanye da blue jeans da wani ƙaramin t-shirt sai ta ɗora abaya mai tsaguwa ta gaba daga sama zuwa ƙasa yanda Jeans ɗin da ta sa zafi fito wa...
Ta fito elegant look 😍
Da ta fito ta nufi kitchen, ƴar aikin gidan ta tarar da ita da murmushi tana faɗin.
“Hajiya Amal, antashi lafiya? Tin jiya ban ganki ba sai yau…”
Amal ta yi murmushi sannan ta ce
“Lafiya kalau… kawai dai na gaji.”
Amma cikin ranta tana cike da ruɗani.
Tana zaune a dining tana breakfast sai ga ƙiran Zayd a waya, ta kasa ɗagawa.
Ga kuma saƙon da ya turo “Good morning my pretty 🌹” ta duba kawai ta rufe wayar.
Kowanne numfashi nata ya cika da tambayoyi:
Me yasa ya je har ɗakina da dare?
Me yasa yake da irin wannan kishi?
Shin Maleekh na sona har haka? Ko kuma yana so ya mallake ni ne kawai?"
Bayan ta kammala breakfast.
Ta tsaya gaban madubi dake manne a wurin dinning tana kallon kanta, sannan ta furta cikin sanyi:
“Zayd baya da laifi... amma idan Maleekh har zai iya haka saboda ni to wannan ba abin da za'a ɗauka da wasa ba.”
Ta ɗauki jakar ta fita zuwa office.
Amma kafin ta shiga mota, zuciyarta ta sake fasa tambaya:
“Ko dai in faɗa wa Zayd gaskiya? In gaya masa cewa Maleekh ni ɗin ta Maleekh ce?”
Sai kuma ta girgiza kai.
“A’a… idan nayi haka zai iya haddasa fitina da Maleekh… kuma Maleekh zai iya aikata duk abin da yace…”
Ta shiga mota cikin ruɗani, idonta ya cika da hawaye, zuciyarta ta kasa zaɓar tsakanin soyayya da tsoro...
Kai tsaye campany ta nufa..
Motar Maleekh na tafe cikin nutsuwa, iska tana kaɗawa daga gilashin da aka ɗan buɗe.
A gefensa Zayd ke zaune, yana ta lalubar jakar da ke jikinsa da murmushi mai cike da nishadi.
Zayd yana murmushi ya ce
“Bros, ka ga wannan kuwa?”
Ya zaro wata kyakkyawar golden shoe mai sheƙi kamar rana.
“An yi order ɗinta ne daga London, limited edition, ba wanda ke da irin ta a Afirka gaba ɗaya. Kyautata ce ga pretty — Amal!”
Maleekh bai amsa ba, sai kawai ya kalle shi da ido masu zurfi, ya ɗan gyara steering ɗin motar cikin natsuwa.
Maleekh ya ce:
“Hmm… expensive taste.”
Zayd yana dariya ya ce
“Kai bros, kai ba zaka gane ba. Pretty deserves special things. Ba irin sauran mata bane…”
Maleekh ya murmusa kaɗan amma idanunsa sun ɗan kaɗa, yana danne wutar kishi da ke tasowa a zuciyarsa...
“If you say so…”
Suka isa company, suka fito daga mota cikin natsuwa. Ma’aikata suna gaida su cikin girmamawa.
Sai dai lokacin da suka shiga reception, abin da suka gani ya sauya yanayi gaba ɗaya.
Amal tana zaune a kan kujera mai tsari, da ƙaramar handbag a gefenta.
Idonta ya ɗan gaji da tunanin daren jiya, amma ta ƙoƙarta ta ɓoye shi da murmushi.
Zayd, idonsa ya sauƙa kanta, sai fuskar sa ta yalwata da farin ciki.
Ya zaro golden shoe ɗin daga jakarsa ya yi gudu kamar ɗan wasa, yana faɗin:
“Surprise my pretty!!! 🌹💛”
Kafin Amal ta ankara, Zayd ya durƙusa a gaban ta gaban jama’a.
Ya sa hannu ya cire takalmin ƙafarta, sannan ya ɗaura mata golden shoes ɗin da kansa.
Kowa a reception ya tsaya, wasu suna dariya, wasu kuma suna yaba kyan takalmin..
Amal ta kasa motsi, ƙirjinta na bugawa da sauri, idonta na neman Maleekh, wanda ke tsaye a gefe cikin wani irin yanayi na shiru da raɗaɗin zuciya.
Maleekh ya kasa ɓoye fushin da ke cike da kishin da bai taɓa ji ba.
Ya ɗaure fuska sosai, sai idonsa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 34 Chapter of 62