Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fita daga ranta ba. 🕊️ Kwatsam, ƙarar ƙofar ɗaki ta turo. Amal ta yi saurin jan gyale ta rufe kanta, tana share hawayenta... Inna har ta buɗe baki zata zazzago masifarta sai kawai ta ga wanin irin kallon da Amal take mata, abin da yafi tsoratar da ita shine ganin yanda kwayoyin idanuwanta suka ƙara girma ga sun yi jawur kamar gobara... Inna a tsorace ta saki murmushin dole tana faɗin: “Amatu… har yanzu baki tashi ba? Ko baki shirya zuwa campany ɗin bane yau?” Amal ta girgiza kai a hankali, ta ce da muryar da ta yi rauni sosai: “Inna… nayi mafarki, kuma sai yanzu zuciyata ta tsaya. Naga Ya Maleekh… naga kamar zai tafi ya barni har abada…” Inna ta tsura mata ido, ta sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi. Sai ta ce da ƙarfin hali: “Kin dai san mafarki ba komai bane. Amma Amal, idan kina son kwanciyar hankali to ki guji abin da zai sa ki zama zance a idon mutane. Kiyi tunani sosai, duniya ba ta da tabbas.” Amal ta miƙe a hankali ta tako gaban Inna, ta manta da ƙiyayyar da Inna ke mata...Kuma Innan ma ganin halin da Amal ke ciki yasa ta tsure... Amal ta dafa hannun Inna a tausashe ta ce: “Inna ki yi min addu’a kawai. Domin zuciyata bata yarda da kowa sai shi, kuma idan na rasa shi… na rasa komai a rayuwata.” Inna ta girgiza kai, bata iya cewa komai ba. Ta fita a hankali, ta bar Amal cikin tunani mai nauyi. Bayan Inna ta fita, Amal ta sake fashewa da kuka. Tace: “Ya Maleekh… idan da gaske baka sona, me yasa zuciyata ba zata iya barinka ba? Me yasa ko a mafarki sai ka dawo kana rikitar da ni?…” Sai ta ɗauki wayarta ta sake ƙiran lambar Maleekh, amma kamar kullum switched off. Bayan tayi kuka ta wanke fuska, Amal ta ɗaura gyale ta fito da nufin zuwa hospital...Domin sake ganawa da Maleekh, zuciyarta tana bugawa da sauri, kamar zata faɗi. A zuciyarta tana faɗin: “Zan je domin tabbatar da Ya Maleekh ko yana raye, zan duba idan har yanzu yana raye… Allah yasa yana numfashi, domin mafarkin da nayi ya nuna cewa ya mutu...” Ta shiga motarta a gaggauce, ta tafi ba tare da tsayawa ko’ina ba har ta iso gate ɗin hospital.. 🏥 Tana shiga ciki da sauri ta tambayi nurse: “Please, ɗakin da aka kwantar da patient Maleekh pag?” Nurse ɗin ta kalleta a tausashe sannan ta ce: “Sorry Madam… an sallame su jiya da yamma. Sun koma gida.” Amal ta tsaya cak! Numfashinta ya tsaya na wasu daƙiƙu.. “Me… me kika ce? An sallame su?” Nurse ɗin ta gyada kai: “Eh, family ɗinsa sun zo sun ɗauke shi. Ba a nan yake yanzu ba.” Amal ta riƙe handbag ɗinta da ƙarfi. Idonta ya cika da hawaye, ta juya a hankali ta fice daga hospital ɗin... Bayan ta fita harabar hospital ta jingina da motarta tana girgiza kai cikin kuka.. “Ya Allah… har yanzu ina cikin duhu. Ba zan iya ganin shi ba, ba zan iya jin muryarsa ba… Shin wannan alama ce daga gareka ka nuna mun cewa ba shi ne rabona ba?…” Sai ta buɗe mota ta shiga, tana kuka tana ƙiran sunan Maleekh a zuciyarta. Duk da haka zuciyarta ta ƙi yarda da cewa Maleekh na raye. Amal kai tsaye zata shahada ta nufi gidansu Maleekh duk da tasan gidan da ake wulakantata ne amma burinta shine taga Maleekh... Tana zuwa bakin get ɗin gidan ta sauƙa daga mota. Security suka tareta dake babban gida ne, gidan minister ne dole sai da matakan tsaro.. Ta ce da su: "Na zo duba jikin Maleekh ne.." Ɗaya daga cikine ya ƙira wayan gidan ya sanar dasu cewa anyi baƙuwa.. Aka bada izinin ta shigo ba tare da an san wacece ba. Amal ta tsaya cak a harabar gidan bayan security sun buɗe mata. Hannunta na rawa, zuciyarta na bugawa kamar zata tsage ƙirji.. Amma ta ɗaura niyya ko wulakanci ne, sai ta ga Maleekh.. Bayan ta taka ƙafar ta zuwa babban falon... Tana shiga gaba ɗaya idanun kowa ya koma kanta... Maleekh yana zaune a gefe, farin riga mai laushi a jikin shi, har yanzu yanayin mara ƙarfi na jinya yana tare da shi. Abba yana gefensa da murmushin tausayi a fuska. Ammy kuwa ta ɗaga gira cikin ɓacin rai. Farha ta ƙafe Amal da idon da yake haɗe da kishi da tsanar da ba’a iya ɓoyewa. Islam ta kalleta da tausayi, tana jin wani abu na motsawa a zuciyarta. Arfat kuwa ta ɗauke ido tana ta wasa da phone ɗinta... Falonnan mai yalwa ya cika da shiru na tsawon wasu sakanni. Har kowa yaji kamar iska ta tsaya. Amal ta yi shahada a ranta sannan ta tsaya tana kallon Maleekh kai tsaye. Idonta ya cika da hawaye, muryarta ta karye tana cewa: “Na zo… don na ga halin da kake ciki Ya Maleekh. Na kasa jurewa na zauna a gida ban san ya kake ba, ban damu da me za ku faɗa ba. Ka yafe mun, idan ka tsane ni, to ka tsane ni da gaskiya, amma kar ka barni cikin duhu ina ƙiran sunanka babu amsa…” Hawayenta ya zubo, ta durƙusa a ƙasa...Tana kuka. ⚡ Reaction in the Room Ammy ta miƙe da sauri ta ce cikin ɗaga murya: “Subhanallah! Daman wannan ce aka bari ta shigo cikin falona? Wane irin sakaci ne wannan? Amal! Kina da bakin dawowa nan bayan abinda kika aikata?!” Farha ta ɗora da muryar kuka da nufin jin tausayinta: “Yaya Maleekh, ka ga dai ni da gaske nake tare da kai, amma wannan yarinyar da kake biye mata har yanzu tana neman ta zame maka illah!” Abba ya ɗaga hannunsa yana cewa: “Ku nutsu! Bari muji dalilin zuwanta.” Maleekh bai iya magana ba, ya lumshe ido hawaye suna taruwa, yana jin zuciyarsa na bugawa cikin ciwo da rauni. Islam ce ta kalli Amal da idon tausayi,sannan ta miƙe ta je yanda take, ta ɗago tare da shigo da ita ciki, ta zaunar da ita, ta ce a hankali: “Ki zauna, Amal… ki faɗi abinda ya kawo ki.” Abba ya ɗago ido da mamaki yana kallon Amal. Ya yi ƙoƙarin tuna inda ya taɓa ganin wannan fuskar sai nan da nan ya tuna. Da mamaki, cikin muryarsa mai cike da natsuwa ya ce: “Daman kece yarinyar da ake ta cece-ku-ce akai? Ba ke bace muka haɗu a asibiti lokacin da kika buge min takardu?..” Amal ta share hawayenta tana girgiza kai cikin rawar murya ta ce: “Ni ce… ni ce...” Ita ma tayi mamakin ganin cewa wannan mutumin kirki da ya ba ta shawara a asibiti, shi ne mahaifin Maleekh! Islam ta ji jikinta ya motsa da tausayi... Ammy da Farha kuwa, kamar za su fashe da kuka tsabar takaici. Farha ta ƙame tana cije leɓenta, idonta na kan Amal kamar zata huda ta da kallo. Ammy kuwa buge cinyarta tayi tana huci a zuciya, amma ta yi shiru don ganin halin da Maleekh yake... Arfat kuwa ta maida hankali kan wayarta, zuciyarta cike da ƙin shiga rigimar nan. Tunaninta ya dawo lokacin da Maleekh ya mareta ya kuma sumar da ita, alkawarin da ta ɗauka a ranta: “ba zan sake tsoma baki a wannan shirgi ba.” Falonnan ya ɗauki wani irin nauyi na shiru kafin Maleekh, wanda yake jingine da kujera ya juyo cikin baƙin ciki, muryarsa cike da rauni a fusace ya ce: “Me ya kawo ki nan?” Amal ta durƙusa a gaban shi, hawaye na zuba, zuciyarta na rawa ta ce: “Na zo ne don na roƙe ka. Ka yafe min Ya Maleekh. Wallahi ba ni da masaniya akan abinda ake zargina da shi. Don Allah ka daina zargina da abinda ban sani ba!” Maleekh ya ɗaga murya cikin tsawa mai ƙarfi har kowa a falo ya tsaya suna tsoron kada ciwon ya motsa. “Wani irin zargi Amal?! Doctor ya tabbatar da komai da idona! Kuma kina ce magana akan zargi?!” Abba ya ɗan motsa da damuwa, zuciyarsa na tsoro kada wannan tashin hankali ya ƙara jefa ɗansa cikin ciwon zuciya, musamman da Doctor ya ja musu kunne akan kada su tada hankalinsa. Amal cikin kuka, jikinta na rawa, ta ce: “To kazo muje a ƙara gwadawa… wallahi zaka tabbatar da gaskiyata!” Maleekh ya girgiza kai, muryarsa mai tsanani ta sauya zuwa takaici: “Ban da lokacin ki, Amal. Ki fita daga cikin rayuwata!” Amal ta zuba masa ido, zuciyarta na tafarfasa ta ce: “Yanzu kana nufin baka sona?…” A fusace ya ce: “Bana sonki, Amal!” Hawayenta ya zubo sosai. Ta matso kusa da shi da rawar murya: “Ka taimaki rayuwata, kada ka faɗi wannan kalmar, Ya Maleekh…” A nan kuwa, Maleekh ya miƙe tsaye da hanzari, zuciyarsa na tafasa. Ya kamo hannun Farha ya ɗaga ta tsaye, ya dafa kafaɗarta yana kallon Amal da idanu masu cike da hawaye ya ce: “Kin ga Farhat? Ita ce wacce zan aura! Ita nake so yanzu. Ke, ki fita daga rayuwata!” Amal ta yi ƙoƙarin miƙewa amma ta kasa, ta durƙusa tana kuka mai ƙarfi. Maleekh ne ya ɗaga murya cikin tsawa ya ce: “I SAID GET OUT!” Amal ta ɗaga idonta cikin hawaye ta ce da ƙarfi: “I will not go anywhere, my bee!” Zuciyarsa ta ƙara karye wa, a fusace ya ce: “I’m not your bee! Sunana Maleekh. Kuma daga yau bana son jin sunanki!” Ya ɗago Amal da ƙarfi, ya ja ta da hanzari zuwa bakin ƙofar falo. Kowa na kallo cikin razana amma babu wanda ya iya yin magana. Har suka fito bakin get, ya tura ta waje da ƙarfi sannan ya juya ya bar ta a can, ya koma ciki da numfashi mai nauyi. Ya shige falon ba tare da ya yi magana da kowa ba, ya haura sama zuwa ɗakinsa. Falon ya dawo da wani irin shiru. Farha kuwa, zuciyarta ta cika da farin ciki yau dai Maleekh ya bayyana ta a matsayin wacce yake so. Abba ya sauƙe ajiyar zuciya, Islam ta ji zuciyarta na karyewa saboda tausayin Amal. Ammy kuwa ta sake haɗe fuska cikin jin daɗin ganin abin da ta jima tana jira ya faru.... Abbah shima tashi ya yi tare da haurawa saman ɗakin Maleekh.... TO PAH AUNTY HABIBA ABIN DA KIKE JIRA YA FARU, FATANKI MALEEKH YA ƊAUKI FANSA AKAN ABIN DA AMAL TAYI MASA A KADUNA TO GA SHI.... AUNTY KHADIJA AFUWAN FA, DAUGHTER KI TA SHIGA TSAKA DA SOYAYYA, HAR TANA SHIRIN MAKANCE WA...SAI KIN TAYA TA DA ADDU'A.... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 45 to 46 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Bayan Maleekh ya haura sama, falon ya ɗauki wani irin shiru. Kowa na jin sautin bugun zuciyarsa. Ammy ce ta fara sauƙe ajiyar zuciya tana murmushi cikin jin nasara. Ammy ta juyo tana kallon Farha, murmushi mai nuna ƙwarin gwiwa na yawo a fuskarta: “Kin gani ko Farha? Kin gani yadda ɗana ya nuna a fili cewa ke ce ƙaunarsa? Wannan ita ce amsawar addu’ata, yau Amal ta sha kashi.” Farha tana jin daɗi sosai har hawaye suka cika idonta, ta ce cikin shagwaɓa: “Ammy, wallahi burina ya cika yau. Ganin yanda ya ɗaga hannuna a gabanta ya ce ni zai aura, na ji kamar zuciyata ta gama samun natsuwa. Yaya Maleekh ya zama nawa.” Islam kuwa ta ɗan zura musu ido, sai ta girgiza kai kawai ta juya gefe tana murmushi mai zurfi. Ba don farin ciki da su ba, sai don ta san labarin zai ɗauki sabon salo. Ammy ta sake cewa da farin ciki: “Kina ji ba, ki ƙara samun nutsuwa yanzu. Ki kula da shi sosai. Ki nuna masa soyayya da kulawa. Amal ta gama, ta fita daga jerin waɗanda za su taɓa rayuwarsa.” Farha ta yi dariya mai sauƙi, ta jingina da kujera tana share hawayen farin ciki. Arfat kuwa ta ci gaba da latsa waya kamar ba komai ya faru ba, tana jin haushin wulakancin da Maleekh ya mata kwanaki, shiyasa ta fi son zaman shiru ba tare da ta nuna tausayin Amal ba. 🕊 A gefe guda kuma, Abba ya bi bayan ɗansa kai tsaye zuwa part ɗinsa. Yana tafiya a hankali, cikin tunanin yadda zai rarrashe shi ba tare da ya sake tada masa hankalin da zai iya shafar lafiyarsa ba. Da ya shiga ɗakin, ya tarar da Maleekh zaune a gefen gado, kansa a jingine, hannunsa na rufe da fuska. Idanuwansa sun cika da hawaye amma ya daure ya maida su ciki. Abba ya ƙarasa a hankali ya zauna kusa da shi, ya dafa kafaɗarsa cikin lallashi kamar yadda ake yi wa jariri: “Maleekh ɗana… ka kwantar da hankalinka. Kada ka bari wannan abun ya shafi lafiyarka. Na ji zafin abinda ya faru, amma dole ka tuna da nasihohin likita.” Maleekh ya ɗago idonsa da suka yi ja saboda hawaye, ya ce cikin murya mai cike da raɗaɗi: “Abba, ta ya zan iya? Na ba Amal zuciyata gaba ɗaya, amma ga sakamakon da ta bani. Abun da ya fi mutuwa ciwo, shi ne a ce wanda kake so ya ci amanarka…” Abba ya yi shiru, ya dafa hannunsa yana girgiza kai cikin tausayi. “Na fahimta, ɗana. Amma rayuwa haka take. Wani lokacin abin da muke buri ba shi ne ƙaddarar mu ba. Idan har Amal ba ta dace da kai ba, Allah zai baka wacce ta fi zama alheri gare ka.” Maleekh ya sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi, ya jingina da gado yana ƙoƙarin danne kukan da ke son subucewa. A bakin get ɗin gidan, Amal ta tsaya cak, idonta cike da hawaye, zuciyarta na bugawa kamar za ta faso kirjinta. Kamar yadda aka jefo ta haka ta tsaya kamar gawa a tsaye. Motarta na tsaye a gefen titi, amma ƙafafunta sun kasa motsi. Hannayenta biyu ta dafe kirjinta tana kuka mai ciwo: “Ya Allah… me yasa Ya Maleekh zai furta haka? Bana da wani laifi… me yasa duniya ta haɗa kai akaina haka?” Jikinta ya gama yin sanyi da haka ta ƙarisa bakin titi, ƙafafunta sun karye, ta sulale ta zauna a ƙasa, tana kuka cikin karyewar zuciya.. Wani security ne ya matsa kusa yana ce mata cikin muryar tausayi: “Haba Madam, ki shiga mota, kar ki zauna haka a titi…” Amal ta ɗago ido cikin hawaye ta ce da murya mai rauni: “Shi ne rayuwata… idan ya ce baya sona, wace riba zan samu da wannan rayuwar?” Girgiza kai Security yayi cikin tausayawa sannan ya koma bakin aikinsa... Zama ta ci gaba da yi a bakin titi ta haɗe kai da gwiwa tana kuka mai cin rai... Ta ɗau lokaci tana zaune ita kaɗai tasan mai yake mata ciwo a ranta, tana cikin wannan halin sai ta ga an miƙo mata farin handkerchief, ba tare da ta ɗago ta ga waye ba ta karɓa tana goge fuskarta da ya ji'ke da hawaye, sannan ta saita hancinta ta faco majina tana dunƙule handkerchief a hannunta, jin wani irin bugun turaren da yake dukan hancinta ne yasa ta ɗago a slow tana kallon gefen da aka miƙo mata handkerchief, a zabure ta ja gefe tana kallon fuskar mutumin cikin rashin sanin waye... Durƙusa wa ya yi a gabanta yana ƙare ta da kallo, sannan ya ce "Sannu koh.." Amal dai ba tare da tayi magana sai idon da take binsa da shi.. A hankali ya furta: "Sunana Zayd, ni ba'ko ne a wannan ƙasar duk da ƙasata ce amma tsawon shekaru domin tin ina ƙaramin yaro na bar ƙasar... yanzun ma na zo gudanar da wani aiki ne, ina tunanin na dawo domin ci gaba da aiki a nan ƙasar, fatan za ku karɓe ni hannu bibbiyu..." Amal dai ga abin da yake damun ta amma yazo yana cikata da surutu, a hankali ta juyar da eyes ɗinta gefe alamun 'bai shafe ta ba...' Zayd ya ci gaba da cewa "Kiyi haƙuri na ga kina cikin damuwa, shin zan iya sanin damuwar ki, ko zan iya taimaka miki?..' Sai a lokacin Amal tayi magana tare da faɗin "A'a damuwata bai shafeka ba, sirrin zuciya na ne..." Zayd ya ja numfashi sannan ya ce: "Amma bana jin daɗin ganin kyawawan mata irin ku suna kuka, shin daman ana sanya kyawawan mata kuka anan Nigeria ne? mu a can kyawawan mata lalla6a su muke..." Amal tana kallonsa ta ce "Munanan mata fa?..." Ɗan sosa sumar kansa yayi cikin murmushi ya ce "I means duk mata, ina daraja mata gaba ɗaya...domin mata iyayenmu ne.." Amal ta sake juyar da eyes ɗinta gefe tare da faɗin "Da kyauuu..." Zayd ya lumshe eyes ɗinsa sannan ya ce "Amm dan Allah ki daina sa damuwa a ranki, yanzu ba wani wadataccen lafiya muke da shi ba, abu kaɗan sai ki ji ciwo ya shige mu..bazan so wani abu ya same ki ba.." Amal ta ce "Meyasa?..." Ya ce "No domin bama son mu rinƙa rasa kyawawan mata a duniya.." Amal ta miƙe tare da faɗin "OK thanks..." Ya dube ta da kyau sannan ya ce "Kamar ba kiyi farin cikin ganina ba.." Amal tayi dariyar da ya kawatar da fuskarta har sai da Zayd ya lumshe ido yana kallon kyakkyawan fuskarta duk da yayi ja tsabar kuka....Wani irin lotsatstsen dimples ne yake lotse wa akan fuskarta tana kallon Zayd ta ce "Shin wurina kazo ne da kake batun kamar banji daɗin zuwanka ba..." Zayd yana murmushi shima ya ce "Nigeria na zo kuma kina cikinta.." Amal ta ce "OK thanks ni zan wuce.." Zayd ne ya miƙa mata hannu akan suyi musabaha.. Amal hararar hannun tayi ta kuma cewa. "Thanks..." Ta buɗe murfin motarta ta shige tana ƙoƙarin ta da engine motar... Jikinta gaba ɗaya ya haɗe da gumi saboda tashin hankali. Idanunta sun kumbura, muryarta ta dusashe a cikin ranta take faɗin. “Ya Maleekh… ko da ka kore ni… wallahi sai na ci gaba da addu’a don ka dawo cikin rayuwata. Ina sonka fiye da yadda nake son numfashina…” Ta jingina kanta da sitiyari, tana kuka mai ban tausayi. Tayi ƙoƙarin tada motar amma hannunta na rawa. Sai ta runtse ido tana roƙon Allah: “Allah, kar ka barni cikin wannan ƙunci. Ka ba ni haƙuri da ƙarfin zuciya… idan kuwa ƙaddarata ce in rayu da shi, to ka dawo da shi cikin rayuwata.” Bata ankara ba ta ji ana knocking ɗin glass ɗin motar, a zabure ta kalle shi ita har ta manta da yana wurin... Zayd ya tsaya a glass ɗin motar da cewa. "Na ga kamar you are so weak, shin zan iya kai ki yanda zaki je?..." Amal ta dube shi sannan ta ce "Thanks.." daidai lokacin da ta tada motar, a ɗari tabar wurin... Motar ta fara tafiya amma zuciyar Amal ta rage masa nisan tafiya domin kalaman Maleekh suna maimaituwa a kunnen ta kamar ana kunna waƙa mai ciwo. Shi kuwa tsaya bin bayan motar ya yi da kallo yana murmushi...daga bisani ya shiga ƙaton motarsa ya nufi get ɗin gidansu Maleekh... Yana zuwa security suka dube shi sannan suka buɗe masa ya shige ciki already sun san da zuwansa.... A falo ya tarar da iyalan gidan... Ammy, Islam, Arfat, da Farha.. Yana tarar da su ya ce "Hellooo my families..." Wani irin tsalle Farha ta buga tare da nufansa da gudun gaske tana faɗin: "Ya'yaanaaaaaa...." Tayi tsalle ta kamo wuyansa ta d'ale shi cikin farin ciki.. Shima rungumarta ya yi yana ɗauke da ita, yana faɗin. "Oyoyo my beautiful lady sister.." Duk sauran miƙe wa suka yi cikin farin ciki.. Islam da Arfat su ma zuwa suka yi suka rungume shi su na masa "your welcome.." Zayd ya nufi Ammy ya gaisheta. Cikin farin ciki ta amsa masa tare da faɗin "Sannu da zuwa Zayd, tin ɗazu muke ta duban ka sai yanzu..." Zayd ya ce: "Wallahi Ammy kaya ne suka tsayar da ni.." Ammy ta ce "Ayyah ai da kayi waya, ai da anje an taryeka a Airport ai..." Zayd ya ce "Kawai bana son wahalar da ku ne..." Daga baya Zayd ya tambayi Ammy cewa: "Ina mutumin ne kam?.." Ammy ta ce. "Yana ciki can part ɗinsa..." Zayd yana dariya ya ce "Ni gaba ɗaya gidan ya rikice mun, bana gane ko ina.." Ammy itama dariya tayi tare da faɗin. "Ai dole rabonka da nan Nigeria tin kana shekara goma fa, lokacin ba'a yaye Islam daga nono ba..." Islam kawar da kai tayi gefe cikin jin kunya..." Ga Arfat Auta ba'a haifeta bama... Zayd yana murmushi ya ce. "OK wani yamun escort zuwa part ɗinsa kar na ɓata..." Duk suka yi dariya. Farha ta ce: "To mu je na rakaka Yaya.." Ammy tayi saurin cewa: "A'a ki bar shi, bari Islam ta raka shi..." Farha dakatawa tayi tana kallon Ammy da murmushi daman wannan rana Ammy take jira, Allah ya kawo Zayd ta daidaita soyayya tsakaninsa da Islam... Islam kallon Ammy tayi tana shirin yin magana, Ammy ta hankad’a ta gaba tana faɗin. "Je ki! Je ki!!..." Islam ba yanda ta iya haka ta sa Zayd a gaba zata kai shi part ɗin Maleekh.... Farha cikin shagwaɓa ta ce. "Ammy nima dai ina son ganin Ya Maleekh ne dai..." Ammy ta ce "Ki bari daga baya kya gan shi, tin da kuna tare yanzu..." ☆☆☆☆ Abbah yana zaune a bakin gadon da Maleekh yake zaune shima, sun jeru kamar masu hira... Abba ne yake ta bashi haƙuri akan ya daina sa damuwa a ransa yanzu, sannan ya daina gaggawar ɗaukan hukunci.... Abbah ya ce "Maleekh na ga tsantsar soyayya a idon wannan yarinya, dan Allah ka tsaya kayi bincike sosai kafin ka yanke hukunci, kallo ɗaya nayi wa wannan yarinyar na fahimci cewa bazata taɓa aikata abinda ake zarginta akai ba, naga nutsuwa a tattare da ita..." Maleekh ya ce "Abbah please ni yanzu bana son jin maganarta, zan yi abin da ya kamata idan na nutsu..." Su na cikin wannan halin sai suka ji knocking... Abbah ne ya bata izinin shigo wa.. A falon ɗakin suka ji sallamar Islam.. Abbah ne ya yi magana da cewa: "Ya akayi ne shigo ciki mana.." Islam ta ƙara yin sallama sannan ta buɗe ƙofar bedroom ta shigo, a bayanta kuwa Zayd ne yake biye da ita... Abbah ganin Zayd yasa shi faɗin. "Ha'a yau babban ba'ko muka yi ne?.." Zayd yana dariya ya durƙusa yana gaishe da Abbah.. Abbah ya amsa cikin nutsuwa sannan ya tashi ya yabar musu ɗakin...domin yasan Maleekh da Zayd manyan abokai ne... Maleekh miƙe wa yayi yana murmushi suka rungumi juna....Zayd ya bubbuga bayansa tare da faɗin: "Man ya jikin nakan, naji ance ka haɗu da break heart..." Maleekh jin haka yasa ya harare shi ya zauna a bakin gadon.. Islam kuwa sallama tayi musu sannan itama ta fita... Idon Zayd ne ya sauƙa akan wani glass pictures na yara biyu suna rungume da juna.. Murmushi ya yi tare da ɗauka yana duba wa... "Har yanzu ka kasa cire Baby a ranka..." Maleekh ya ce yana kallon hoton hannun Zayd. "Da ba dan rasata da nayi ba, da babu wani heart break da zan fiskanta...A yanzu zan ci gaba da jiran fiance ɗina..." Zayd ya ce "Idan kuma ta mutu fa?.." A zabure Maleekh ya kalle shi tare da girgiza kai yana faɗin "Kar ka sake faɗin haka..." Zayd ya ce. "Kana hauka ne? amma kowa yasan cewa ita da iyayenta sun mutu sakamakon gobarar wuta da aka dasa musu.." Maleekh a hankali ya furta. "Idan iyayenta sun mutu to ita tana raye kuma zan ci gaba da jiranta.."... ☆☆☆☆ Da ƙyar Amal take tuƙi, hawaye na zuba kamar ruwan sama. Gaba ɗaya titin da take bi sai ya rikice mata a ido. Sau biyu tana kusan yin karo da mota saboda tsananin tunanin da ya mamaye ta. “Ya Allah… me yasa rayuwata ta zama haka? Na rasa wanda zuciyata take so… Na rasa farin cikina gaba ɗaya…” Ta dafe kirjinta, tana jin kamar zuciyarta ta tsinke gida biyu. Duk inda ta dubi gilashin mota, a madubin gaba sai ta hango fuskar Maleekh. Idanunsa masu ƙarfi, muryarsa mai dukan zuciya, da kalmomin da suka fi kowane makami ciwo: _*“Bana sonki, Amal… bana sonki.”*_ “Ya Maleekh…” ta furta da rawar murya. “Wallahi ban aikata laifin da ake zargina ba. Na rantse da Allah kai kaɗai nake so. Na rantse da Allah kai ne numfashina. Ka yarda da ni, My Bee… kada ka ƙi ni haka.” Sai hawaye

Chapter 31 of 62