a tsakiyar falon yana kallon mahaifiyarsa da Farha ya ce,
“Ya! Meke faruwa anan?”
Farha ta miƙe cikin hanzari, ta juya zuwa ga Zayd:
“Yawwa Yaya! Dan Allah idan kasan kana da hannu a ɓatan Amal ka gaya mana! Ka fita daga rayuwarta! Nasan ba mai haka sai kai, daman ka ci alwashin raba soyayyarsu!”
Hajiya Sa’adatu ta juya zuwa ga Farha ta ce.
“Au ke! An ɗora miki sharrin sace ta, ke kuma kin zo ki ɗora wa ɗan uwanki sharrin sace ta? Me kike nufi kenan!?”
Zayd ya kalli mahaifiyarsa yana sarrafa fushinsa, ya juya zuwa ga Farha cikin tsananin iko:
“Na rantse idan ban kwaɗa miki mari ba, ki sanja mun suna! Kin raina mun wayo, ni da nake shirin kwamushe ta, kwatsam naji labarin bacewar ta, kuma yanzu kin zo kina mun wani irin question? ‘Yarinyar da akace tabi saurayinta. Kuma shima Maleekh ya tabbatar da hakan…”
Hajiya Sa’adatu ta ƙara murya da cewa:
“Ka rabu da ita! So take azo a kamaka! Ai idan zaka ji tawa, kawai ka nemi wata! Amma wannan kam ta gama amfani...”
Farha tana kuka, ta ja numfashi mai ƙarfi tare da faɗin:
“To dole na yi zargin haka… saboda ku kuka yi silar hatsarinta sannan kuke shirya kashe ta! Duk naji komai ai.. ”
Hajiya Sa’adatu ta tsaya, kirjinta na bugawa da ƙarfi, ta kalli Farha da mamaki da fushi lokaci guda ta ce:
“Ke! In ƙara jin wannan maganar ta fito daga bakin ki wallahi sai nayi mungun sa6a miki, wawuya kawai...!”
Farha ta ru ga da gudu saman upstairs yanda ɗakinta yake...
Hajiya Sa’adatu ta riƙe ƙirji tana kallon Zayd ta ce
"Ka duba yarinya zata jawo mana bala'i?..."
Bayan Sati guda...
Yanda Amal take a wannan karon an rufe mata fuska gaba ɗaya.
Wani hamshakin mutun ne mai tafiya akan iska ya fito daga cikin tsararren motarsa. Yanayin tafiyarsa kasan handsome guy ne, yana tafiya yana zukar shisha.
Bodyguards suka yi escort ɗinsa har ciki yanda Amal take.
Yana shiga ya tsaya a gabanta ba tare da yayi magana ba yayi alama da hannu cewa 'a miƙo masa wayarta..'
Hakan akayi ya karɓa ya buɗe wayar sannan ya shiga wurin message ya goge saƙon da aka turo mata, ya shiga wurin Gmail ya goge domin yasan kan wayar duk abinda ya shigo cikin wayar sai yayi saving a email...
Sannan ya kashe wayar ya bayar akan a cigaba da riƙe wa...
Ƙerarren mutu yana tsaye, komai nashi a tsare, yatsun hannayensa a jere da zobina kala-kala, ga hannun farin tas irin na ƴan hutu. Ɗayan hannun yana riƙe da shisha.
Ya durƙusa a gaban Amal da fuskarta yake a rufe ga baki a toshe, hannaye da kafafuwa a daddaure....
Haka yake zuƙo da hayaƙin shisha yana busa mata akan fuskar da yake rufe...
Ya gama yin sa ba tare da ya furta komai ba, daga bisani ya manna mata kiss akan goshi sannan ya miƙe ya fita. Bodyguards suna biye dashi a baya, wasu kuma sun cigaba da tsaya wa a gun da Amal take ɗaure...
Shiga tsararren motarsa ya yi, ya zauna a backseat sannan security yayi driving ɗinsa.
Sauran Bodyguards kuwa suka tsattsaya suna gadin dajin...
(Ni iya ƙafafunsa da hannayensa zuwa wuya na gani 😄 ban ga fuskar ba balle nayi muku gulma 🤭😝😝....)
AMMA ZAN BADA CHANKI-CHANKI!... DUK WANDA YA CHANKI DAIDAI ZAN MASA KYAUTA MAI TSOKA 🤣🤣🤣🤣
SHIN WAYE????.....
*_NEXT NEXT NEXT_* ...
asmeetahwriter✍️
*🎤AMALEEKH🎤*
*AMAL AND MALEEKH*
Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth.
*Writing and Storytelling By*
Asma'u Muhammad Auwal
Asmeetah writer
*HASKEN JAJIRTATTU*
*MARUBUCIYAR:*
*Matar Damisa*
*My Enemy*
*Hasken Ruhi*
*And know AMALEEKH*
Bauchi State Nigeria.
*WhatsApp 09065443871*
Follow my channel 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
BOOK ONE page 73 to 74
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Sati Biyu Bayan Bacewar Amal
Gidansu Amal ya koma gidan shiru.
Sai ƙarar agogo da ke bango shi kaɗai ke yi, tik...tik...tik...
Gidan da yake cike da dariya, kiɗa da annashuwa, yau ya koma gidan jimami.
Inna ba ta da wani natsuwa. Ba ranar da zata faɗi, ba ta ambaci sunan Amal ba.
“Ya Rabbi... ina jikata? Me ya same ta? Me Amal ta yi har ta cancanci haka?…”
Hankalinta ya tashi sosai, har ta ɗan rame. Idanunta sun kumbura da kuka, jikinta ya yi sanyi kamar mara rai.
Duk lokacin da zata yi sallah, sai ta roƙi Allah cikin kuka:
“Ya Allah ka dawo min da Amatu ta, ko da matacciya ce kawai in ganta in saka ta a idanuwa na...”
Abbah ya dage sosai. Ya kasa kwantar da hankalinsa, kullum sai ya nufi ofishin ƴan sanda.
Kusan kullum sai an nemi wayar Amal ko za'a samu damar yin tracking ɗin wurin da take amma lambar kullum “The number you have dialed is not reachable at the moment…”
Ƴan sanda sun bazama suna bincike daga CCTV har zuwa makwabta, daga motar da ta ɗauke ta, har zuwa duk inda ake zargi.
Sun saka hotonta a gidan rediyo da talabijin.
“Wannan yarinya mai suna Amal Abdulsamaad, shekaru 22, ta ɓace tun ranar walimar bikinta. Duk wanda ya ganta ko ya san inda take, a tuntubi ofishin ƴan sanda mafi kusa.”
Kowa ya ji labarin.
Mutane suna ta fassara lamarin da zato..
“Wata kila saurayinta ta bi...”
“Ko an sace ta ne saboda kishi...”
“Ko dai akwai makirci a tsakanin danginsu…”
Amma Inna ta san jikarta ba irin waɗannan mata bace. Ita dai kuka kawai ta iya sai addu'a.
A ɓangaren Maleekh kuwa, babu alamar damuwa.
Yana kwance a ɗakinsa, ya jingina da gadonsa, yana kunne da headphones.
Gaba ɗaya ya cire kansa daga lamarin..
Ƴan sanda sun zo har gida, amma bai damu da su ba.
Idan Abbah ya ƙira shi, sai ya ce,
“Amal dai ta bi hanyar da ta zaɓa. Ina fatan tana jin daɗinta.”
Kowa ya daina gane Maleekh..
Duk san da akayi masa maganar Amal sai ya ce
“Inda ta je, ta sani. Zan jira ranar da gaskiya zata fito..”
🕯️
Mutanen da suka zo daga Borno da Kaduna sun koma gida.
Gidansu Amal ya watse.
Sai Inna da ƴan aiki, kowa ya koma yanda ya fito.
Inna kullum tana zaman jiran saƙo. Duk lokacin da taga motar da ta tsaya a bakin titi sai ta miƙe da sauri, tana cewa:
“Ko Amal ce? Ko labari ne daga gareta?”
Sai dai kullum amsar duniya ɗaya ce, shiru.
Abbah yana zuwa kullum da safe, yana bata haƙuri da cewa:
“Ki daure, Mama. Allah yana gani. Insha Allahu, Amal zata dawo lafiya.”
Inna ta share hawaye, ta ce da murya mai rauni:
“Alhaji, ni dai bazan daina addu’a ba. Allah ya dawo min da jikata, ko da a mafarki ne.”
☆☆☆☆☆
Haske ɗaya kacal ne ke fitowa daga ƙaramin rami a bango, yana zana layin fuskokin mutane da inuwa.
A cikin ɗakin, Amal tana zaune a kujera; an ɗaure hannaye da ƙafafu da igiya mai ƙarfi. An toshe mata baki, sai ƙanƙanin numfashin da take fitar wa. Gashin kanta ya zubo gaba ya rufe mata fuska...
A kusa da ita, wasu matasa uku ne, fuskokinsu a rufe da baƙar hula, hannunsu riƙe da bindigogi, wasu kuma suna riƙe da wayoyi. Sun zauna kamar suna tattauna aiki, amma a kowane lokaci suna duba Amal kamar dabbobi cikin yunwa...
Jagoransu ya zauna a kan kujerar kusa da ita, ya buɗe kwalin abinci, ya ɗan ciro lemo a leda. Ya dubi Amal a hankali, murya tamkar goge tabo,
Jagoran ya ce, “Kar kina jin kunya, yarinya. Wannan ba kuɗin banza ba ne. Aiki ne kawai. Ki yi shiru, ki zauna da haƙuri, za mu juya miki labari.”
Amal ta lumshe ido, ta gwada motsa leɓe, ta ƙara yin ƙoƙarin faɗi wani abu amma gam ɗin baki ya hana ta..
Ya yi dariya mai ƙarfi sannan ya ce “A, kina ƙoƙarin magana ne? To dai ki tuna, komai zaki faɗa zai koma gefen mutumin da ya aika mu. Don haka shiru kawai.”
Ya ji wayarsa tayi ƙarar shigowar message ya duba sannan ya ce,
“Boss, client ya aiko saƙo yanzu: ‘Ku an kare guys domin kar ku bari bincike ya yo ta wurin ku, ƴan sanda suna kan bincike kar ku bari a same ta, ku shirya yadda za ku ɓoye ta gaba ɗaya but please kar ku barta da yunwa kuma kada wanda yayi ƙoƙarin cutar da ita..’.”
Other one: “Dole mu mishi yanda yake so domin Boss ba wasa fa, ya turo da kuɗin da yace zai bamu mu raba?”
Jagoran ya ce: “Eh. An riga an tura da yawa ma. Amma ya ce mu jira umarni na biyu, kar mu yi wani abu har sai an ƙira mu.”
Jagoran ya miƙe ya matso kusa da Amal, ya share gashin fuskarta da hannu,
“Mun dafa miki abinci da ruwa. Duk da haka, kar ki yi ƙoƙarin gudu. Kowane ƙoƙarin gudu zai cutar da ke.”
Ya kun ce mata hannu sannan ya bata...
A hankali ta ɗauki spoon tana caccakar abincin kamar bazata ci ba...
Daga bisani ta ɗan taɓa, bayan ta kammala ta sha ruwa aka sake ɗaure mata hannayen..
Cikin zuciyarta tana mamaki "Me yasa? Wane irin zunubi na yi da ya sa ake mini haka? Ta tuna saƙon da Maleekh ya turo mata, tana murmushi haɗe da hawaye ta ce "Allah sarki bawan Allah, maybe ya gaji da jirana ne yasa ya tafi, bayan tafiyar kuma hakan ya faru da ni..."
Tana ƙoƙarin motsa ƙafafunta domin sunyi matuƙar gajiya da tsami, igiyoyin suna da ƙarfi. Ta jujjuya kai, ta kalli wani rami a bango, waje ne da ba za ta iya gani sosai ba amma da duk kan alamu nan daji ne...
*1 MONTH LATER*
Waya ce take ringing.
Jagoran ya amsa ƙira a wayarsa. Ya ɗaga wayar a hankali, ya sa a kunne, yana magana:
“Yes, boss... mun tsare ta da kyau. Ba mu cutar ba... bata gane komai ba, mun rufe wayarta. Muna jiran umarnin ka.”
Muryar a waya: “Kada ku sanar mata komai, ku jira gobe da safe. Zan sanar muku abin da zakuyi. Kada ku dameta sosai tukuna. Idan ta yi hayaniya, ku mayar da ita cikin shiru.”
Jagoran ya katse ƙira, ya dawo wajen sauran yana faɗin.
“To, mu shiryawa safe. Mu yi bincike kafin mu fito dan Da safe za mu kai ta wani wuri. Kada kowa ya kusanci jejin gidan nan.”
🕯️
Washegari da safe suna jiran saƙon da za'a aiko musu..
A gefe, wani ya ɗaga hannu ya ce cikin natsuwa:
“Mu jira umarnin client. Da safen nan, za mu zamo masu aiki, amma a hankali. Kada kowa ya san inda muka kai ta. Wannan aikin ya fi kuɗi.”
Jagoran ya kalle su sannan ya ce:
“In ba haka ba, idan wani ya sanar, za su fara bincike, su neme mu. Da mun riga mun kai ta wuri mai kyau, babu wanda zai taɓa gane komai.”
A wannan lokacin misalin 9 na safe.
Tana ɗaure da sauran security masu gadinta.
Ita dai ta kasa fahimta duk lokacin da Boss ɗinsu zai zo sai sun rufe mata fuska yanda bazata iya ganinsa ba. Kuma idan yazo baya magana har ya tafi, kuma duk sanda zai tafi sai ya sumbace ta akan goshi. Kuma abinda yake ƙara ɗaga mata hankali shine ƙamshin turaren Boss ɗin irin na Masoyinta Maleekh ne amma ta kasa yadda da hakan...
Bayan ya gama ganinta yayi abin da ya saba wato ya sumbace ta akan goshi. Sai bayan ya fita can outside ne ya tara su sannan ya ce.
“Ku shirya. Ku fita da ita yau da daddare. Ku rufe mata fuska yanda bazata gane ko'ina ba. Ku a jiye ta a bakin gidansu, ku wuce ba tare da kun tsaya ba.”
Security biyu suka kalli juna, ɗaya daga cikinsu yace:
“Boss, muna nufin mu sake ta? Kai tsaye?”
Boss ya ce, “Eh. Ku tabbata ba wanda ya ganku. A yi abin cikin tsari. Bayan kun aje ta, ku ɓace kafin ta shaida ku.”...
Daga bisani ya shige motarsa ya tafi kamar walƙiya...
Da daddare misalin ƙarfe 12.
Amal tana zaune kamar yadda suka saba ajiyeta, Wasu daga cikinsu su biyu suka ƙaraso da rigar fuska, ɗaya ya kwance igiyar hannunta da ƙafarta..
Security na 2 a hankali ya furta, “Ki yi shiru, Madam. Kada ki yi magana.”
Suka riƙe ta suka fitar da ita zuwa mota, suka zaunar da ita a baya. Mota ta kama hanya cikin nisan gari, babu wanda ke magana. Sai numfashinta kawai ke ji.
Awa guda da wuce wa, mota ta tsaya. Aka buɗe ƙofa da sauri.
Security na 1 ya ce, “Ki zauna seconni biyu, sannan sai ki fita.”
Bayan sun tabbatar da ba kowa a layin suka fitar da ita, suka aje ta a bakin titi kusa da gidansu. Sannan ɗaya daga cikinsu ya zare fuskar da aka ɗaure mata fuska da ita.
Amal ta ɗan rintse ido, haske ya bugi idonta kamar wuta! Ta lumshe, tana jin dishi-dishi. Idanuwanta sun yi duhu sakamakon ɗaure su da akayi ba..
Hasken fitillun ne suke ta haskawa amma wurin shiru ba motsin kowa..
Ta buɗe ido a hankali, tana ganin haske, titin da ta sani… sannan ta ɗago kai cikin rawar murya:
A hankali ta furta “Wannan… wannan gidanmu ne…? Wannan unguwarmu ce?”
Tana ƙoƙarin juyawa ta ga motar da ta kawo ta, amma wayam, motar ta ɓace! Ta ɗan kalli kewayenta, tana jin kamar mafarki take....
Zuciyarta ne ya fara bugawa. Da gudu ta nufi cikin unguwar, ƙafafunta na rawar sanyi da farin ciki a lokaci guda..
A bakin ƙofar gidansu ta tsaya tana buga ƙofar da ƙarfi.
Tana kuka tana furta, “Mai gadi! Mai gadi don Allah buɗe ƙofa! Ni ce! Ni ce Amal!”
Mai gadi wanda ke zaune a cikin bukkarsa, ya fito da fitilar hannu. Idanunsa a zazzare ya ce,
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Amal?! Ke ce haka? Subhanallah! Ke dai gaske ke ce kuwa?!”
Amal ta kalle shi cikin hawaye, ta ce da rawar murya:
“Ni ce Mallam Musa… ni ce wallahi… don Allah ka buɗe ƙofar… ka bari in shiga gida!”
Da sauri ya buɗe ƙofar.
Tana shiga ciki, ta fara ƙiran:
“Innaaa!! Inna taaa!! Ina kike Innaaa!!”
A cikin falo, Inna tana zaune tana duba hoton Amal da hawaye a idonta. Da ta ji muryar Amal, ta tsaya cak, hoton ya zame daga hannunta.
Ta tashi da gudu ta fito daga falon, tana faɗin:
“Subhanallah! Wannan murya… Amal… Amal ce!”
Inna tana fito wa Amal ta faɗa mata a jiki, suka rungumi juna.
Amal tana kuka sosai ta ce: “Innaaa! Na dawo! Na dawo Innaaa! Na gaji! Na sha wahala Innaaa!”
Inna ta fashe da kuka tare dafaɗin: “Ya Allah na gode! Ya Rahman! Na rasa muryarki, na rasa dariyarki! Amal ɗina kin dawo… kin dawo min lafiya!”
Suna kuka suna rungume da juna.
Inna ta zare daga jikinta ta ɗaga fuskarta tana duba Amal da hawaye, tana shafa kumatunta ta ce:
“Amal... kina raye? Meya faru dake? Su waye suka yi miki haka? Ina suka kai ki?”
Amal tana girgiza kai cikin kuka ta ce, “Inna… ban sani ba… ban san inda nake ba, ban san me yasa ba, amma na dawo Inna…”
Inna ta rungume ta da ƙarfi kamar tana tsoron kar ta sake ɓacewa.
Inna tana kuka ta ce, “Shikenan Amal… shikenan. Allah ya isa. Ki shiru, ki huta. Ki gode wa Allah. Ya dawo da ke gare ni.”
Mai gadi ya tsaya bakin ƙofa yana share hawaye, yana kallon ikon Allah.
Mai gadi a hankali ya furta, “Wallahi ikon Allah babu iyaka… wata guda, duk muna tunanin ta mutu…”
Amal ta sunkuyar da kai cikin jikin Inna, zuciyarta na bugawa cikin tsoro da farin ciki. A cikin ƙasan ranta, ta rantse, duk wanda ya aikata min wannan, sai na san wanene...
Suka shige ciki, a wannan daren Inna ta ƙira Abbah ta sanar masa dawowar Amal...
Ana salar Asuba duk suka nufo gidan.
An sanar wa ƴan sanda su ma sun zo.
Ƴan sanda, Abbah, Ammy, Islam, Arfat, har da Maleekh kansa, da Farha wacce ta tsinci labarin daga bakin Islam duk sun hallara a falon gidansu Amal.
Amal tana zaune a kujera, jiki a sanyaye, idonta yayi jawur tsabar kuka. Farha na gefenta, tana rarrashinta, yayin da Islam ke miƙe a gefe tana kareta da kallo..duk ta rarrame tayi baƙi.
Ƴan sandan suna ta mata tambayoyi, amma duk abin ya yi musu duhu.
Ɗaya daga cikin ƴan sanda ya ce,
“Kinyi hakuri, Amma kin ce ba ki san inda aka kai ki ba? Kin tuna fuskar wanda ya yi miki haka?”
Amal tana hawaye ta ce, “Wallahi ban sani ba... kullum suna sanye da hular fuska. Ban taɓa ganinsu ba, ban san inda nake ba. Duk lokacin da wani yazo, sai a rufe idona, ba magana ake ba...”
Ƴan sandan suka kalli juna da mamaki, ɗaya daga cikinsu ya ja biro yana rubutu.
A gefe kuwa, Maleekh yana tsaye, hannuwansa cikin aljihu, fuskarsa cike da ɓacin rai.
Ya ɗaga murya cikin ƙasaita:
“Ai baza ku samu wani bayani daga gareta ba. Tasan inda ta tafi, ba wai an sace ta bane. Ta tafi gantalinta da saurayinta.”
Wuri ya ɗauki shiru. Kowa ya kalle shi.
Amal da ke zaune ta ɗago kai a ruɗe, idonta ya haɗu da nasa.
Kuka ya ƙara taso mata.
Tana girgiza kai ta ce, “Ya Maleekh... wai me kake faɗa haka?...”
Farha ta kamo hannunta tana faɗin,
“Amal ki nutsu, don Allah ki zauna.”
Islam ma ta kalle shi cike da mamaki ta ce,
“Yaya, wannan magana ba daidai bane. Amal bata da ƙarfin halin nan.”
Inna da ke zaune can gefe, ta share hawaye, tana girgiza kai da damuwa, ta kasa cewa komai.
Abbah ya kalli Maleekh cikin ɗaga murya ya ce,
“Kai Maleekh, bana son hauka fa! Yanzu wannan yarinyar da take a rame tayi baƙi saboda wahala, shine zaka ce gantali ta tafi? Kana muzanta ta da irin waɗannan maganganu.”
Ammy ta ɗan juyo daga inda take zaune ta ce cikin gadara.
“Ai gaskiya ya faɗa. Kowa yasan wannan yarinyar ta iya wasa da hankali. Kar a wahalar da ƴan sanda akan irin wannan shashanci.”
Amal ta ɗago kai, tana girgiza kanta cikin hawaye,
“Wallahi banyi haka ba! Ban san meya faru dani ba! Na farka a wani wuri, an ɗaure ni, kullum duhu, ba rana, ba magana... don Allah ku yarda da ni!”
Maleekh ya ɗaga hannu yana nuna ƴan sandan,
“Please, ku tafi. Wannan lamari na gida ne. Ku bar mu da ita domin babu wani abin da zaku samu..”
Ƴan sandan suka kalli Abbah, suka ce:
“Toh Alhaji, idan haka ne, zamu bar ku da ita. Amma idan wani abu ya taso sai a sanar da mu.”
Suka tafi.
Cikin tsananin damuwa, Amal ta tashi tsaye ta ce da rawar murya:
“Wai meyasa baza ka fahimce ni ba, Ya Maleekh?... Me yasa baka yarda dani ba, shin zaka bada shaidar haka nake?....”
Maleekh ya matsa kusa da ita, idonsa cike da ɓacin rai.
Kafin kowa ya yi magana, cikin zafin nama ya ɗaga hannu ya zabga mata lafiyayyen mari!
“Ahhh!”
Tayi ƙara tare da dafe kuncinta, hawaye suna sulalowa da sauri...
Kowa a falon ya tsaya cak!
Inna ta dafe ƙirji,
Wani irin shiru ya mamaye falon gaba ɗaya.
Maleekh ya tsaya, yana kallonta da fuska a murtuke..
A tsawa ce yake faɗin
“Ta ya zan fahimce ki bayan kin karya mun zuciya? Kin tozarta ni, kin wulakanta ni. Kin wuce gona da iri. Ki sani da ke gwara mutuwa.”
Wani irin huci da kuka ya taso mata
Ta cire hannunta daga fuska, ga fuska ta kumbura, ta yi ja, tana nuna shatar hannunsa...
Amal cikin kukan takaici ta ce, “Ya Maleekh… me yasa? Har zuwa wannan matakin?...”
Farha ta miƙe kusa da Amal tana rarrashinta, yayin da
Abbah ya zauna cikin kaɗuwa, yana kallon Maleekh kamar ya miƙe ya fara dukansa a wurin...
Inna a gefe, tana ta share hawaye da mayafi, yayin da Amal ta durƙushe a ƙasa, tana kuka kamar ranta zai fita.
Sai a lokacin Abbah ya daka masa tsawa cikin murya mai nauyi, wacce ta girgiza falon:
“Maleekh! Meye dalilinka na yin haka? Wace irin zuciya ce kake da ita har ka ɗaga hannu ka mari matar da kake ikirarin so? Me yasa kake zarginta da abunda ka san bazata taɓa aikatawa ba? Idan baka son aurenta sai ka faɗa a fili, amma kar ka zalunce ta da shaidar ƙarya!”
Ɗakin ya ɗauki shiru.
Maleekh ya ɗan gyara tsayuwa, ya janye hannunsa daga aljihu.
Ya kalli Abbah kai tsaye cikin murya mai sanyi sannan ya ce.
“Abbah, akwai dalilai da yawa. Ba kuma zarginta nake ba, ina magana ne da hujja. Akan daidai nake tafiya.”
Ya jawo wayarsa daga aljihu, yana cewa cikin kasaita:
“Zan nuna muku wasu hotuna da zasu tabbatar da cewa wannan yarinyar bata da kamun kai... tana wasa da hankalin kowa.”
Ya kunna projector ɗin da ke cikin falon, wato na'urar haska bidiyo a bango
Duk idanu suka koma can.
Sai hotuna suka fara bayyana ɗaya bayan ɗaya...
Na farko: Hoton da Zayd ke cikin ɗakin Amal, yana kwance a kanta, rigarsa a cire, ita kuma tana kare kanta tana ƙoƙarin turesa.
Amal ta kalle su a ruɗe, tare da riƙe ƙirjinta...
Inna cikin rawar murya ta ce, “Subhanallah!... a gidan nan?... Amal wannan ɗakinki ne kuwa?”
Amal ta buɗe baki cikin kuka tana girgiza kai:
“Wallahi ba haka bane! A lokacin muna kokuwa ne, yana ƙoƙarin ya ci zarafina, ban yarda ba... Allah ya sani!”
Farha itama bata san lokacin da hawaye ya sulalo mata ba, ganin ɗan uwanta ne...
Maleekh ya murmusa yana kallonta, ya ce:
“Kokuwa? Haka ake kokuwa a kan gado har da cire kaya?”
Inna ta lumshe ido, ta kasa cewa komai.
Abbah kuwa ya haɗe gira, yana kallon Maleekh cikin tuhuma.
Sai Maleekh ya ƙara danna wayar, ya nuna hoton na gaba.
Photonta tana bakin get ɗin gida, daga ita sai sleeping dress, wani mutum yana rungume da ita ta baya, fuskarsa a rufe.
Hankalin kowa ya ƙara tashi.
Ammy ta ɗan ja numfashi tana cewa:
“To yanzu kun gani da idanunku... Ni da bakina nace, wannan yarinya bata da tarbiya. Kyan ɗan maciji ne.”
Amal ta fashe da kuka sosai, tana faɗin:
“Wallahi ban taɓa yin haka ba! Wannan hoton an yi min sharrin photoshop ne! Ba ni bace wallahi! Wannan ma barawo ne!”
Sai Maleekh ya sake matsa kusa da projector, ya nuna hoton na ƙarshe:
Photonta tana bacci a ɗaki, wani mutum yana gefenta cikin blanket ɗaya.
Maleekh yana duban kowa ya ce, “Kuma wannan fa? Hoton bacci ɗaya da saurayi. Yana wani rufe fuska don kar a gane shi. Amma ku gane abinda nake gaya muku...”
Ɗakin ya yi shiru.
Amal ta riƙe kanta tana faɗin:
“Ya Allah!... waye yake yi min haka?... waye yake son halakar da rayuwata?...”
Maleekh ya juya ya kalli kowa a cikin falon, yana murza hannunsa tare da faɗin:
“To kun gani da idanunku. Wannan ce wacce nake son aura? Allah ya kiyaye! Na gode wa Ubangiji da baka sa na auri wannan karuwar yarinya ba. Mazinaciya dabbiya, wacce ta gama lalacewa! Ki sani, daga yau babu ni, babu ke! Ko da mata sun ƙare a duniya, bazan taɓa aurenki ba.”
Hasken projector ya daina aiki, falon ya koma shiru.
Sai Ammy ta ce cikin jin daɗi:
“Dakyau ɗana, haka nake son ji. Sai yanzu ka nuna jarumtaka. Ka tuna, duk wanda ya tsarkake kansa daga irin wannan muguwar baiwa, Allah yana ƙara masa daraja.”
A lokacin ne Abbah da ke zaune ya ɗago kai a fusace, ya miƙe tsaye yana huci.
Cikin lokaci guda ya taka gaban Maleekh ya ɗaga hannu cikin zafin rai ya zabga masa lafiyayyen mari, sai da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 48 Chapter of 62