ya yi dariya, ya ɗan zaro wayarsa.
Yana murmushi da tsokana ya ce
“Hehehe… lemme show you something, guys.”
Ya kunna screen ya nuna musu tsohon bidiyo lokacin a Kaduna inda Amal ta mare Maleekh a bainar jama’a tana faɗin:
“Join yourself, I said: join yourself Maleekh!”
Sai kuma ta zabga masa mari a fuska, mutane suka yi ihun mamaki a wajen.
Ɗakin hotel ɗin ya kaure da dariya.
Abokansa duk suna ta tsalle da dariya, ɗaya daga ciki ya ce
“What?! Hahahaha! Oh my God! So this love started with a hot slap?!”
Aboki na 2 yana tintsirewa da dariya sosai ya ce
“Waiii, bro, you got slapped in public by your queen! And now you’re dancing with her on live TV! Epic storyline!”
Suka kwashe gaba ɗaya da dariya kamar ba za su daina ba.
Maleekh ya ɗaga pillow da sauri, ya wurga wa PA a fusace.
Yana ɗaga murya cikin bacin rai
“You are stupid! I told you it was a secret, dumb ass! How dare you show them that video?!”
PA ya ƙara yin dariya, yana bashi haƙuri.
Yana kare jikinsa tare da faɗin
“Sorry boss, just vibes… wallahi sorry…”
Amma dariyar abokansa ta ƙara tunzura shi.
Aboki na 3 yana bugun tebur cikin dariya yake faɗin
“Oh my God, the almighty Maleekh got slapped! Bro, she tamed you from day one!”
Maleekh ya ɗaga pillow ya wurga musu, ya ɗauki wani pillow ya kwad'a wa wani. Suka fara dariya suna guje-guje a cikin ɗakin kamar yara. Ya dinga kwad'a musu pillow, wani ma sai da ya sha naushi a baya...
Maleekh yana tsawa cikin dariya ya ce
“Shut up all of you! Crazy idiots!”
Abokansa duk da dariya, suna tsokanar shi..
“Boss, boss, take it easy! Don’t be mad… we love you!”
Ɗakin ya cika da annashuwa da dariya, ƙamshin shisha, wasan pillow fight da tsokana.
Bayan sun gama wannan shagalin suka watse kan kujeru, suka fara sauƙar numfashi.
Sai ɗaya daga cikin abokan ya ɗauki gilashin cup ya ɗago sama yana faɗin:
“Listen bro, forget about revenge. Love is not about ego. Amal loves you, you love her… end of story. Don’t spoil it with nonsense.”
Aboki na 2 yana gyaɗa kai ya ce
“Wallahi. A true man doesn’t take revenge on the woman he loves. He protects her. That’s the real game.”
Maleekh ya jingina, ya lumshe ido. Cikin zuciyarsa, kalmomin sun dake shi. Har yanzu yana tuna marin Amal, amma kalmar soyayyarta da murmushinta ta sha fiye da duk wani rauni.
Maleekh a ransa ya ce
“Revenge? No… she’s worth more than that.”
Sai ya ɗago kai ya kalli abokansa da murmushi a fili ya furta
“You’re right. Amal is my peace now… no more revenge.”
Ɗakin ya sake kaurewa da dariya, amma wannan karon dariyar ta soyayya ce, ba ta tsokana ba.
🌹🌹🌹
Farha ta killace kanta a ɗaki. Bayan ta gama shan kuka, ta buɗe drawer ɗinta ta ciro kwayoyi da allurai irin na masu shaye-shaye. Hannunta sai rawa yake yi amma zuciyarta ta cika da baƙin ciki da kunya.
Ta zauna ta huda hannunta, ta zuba wa kanta allura. Ta ɗauki ƙwayoyi ta sha over dose. Cikin ɗan lokaci maye ya mamaye ta. Idanuwanta suka fara juyawa, ta zube a ƙasa tana dariya ita kaɗai.
Ƙarar dariyarta ta ɗan tsaya..
Bayan mintuna babu motsinta. Iyaye da masu aiki suka taru a bakin ƙofa suna ƙoƙarin shiga amma ta ƙulle ƙofar. Da ƙarfi aka buɗe ƙofar, sai ga Farha kwance a ƙasa tamkar gawa. A kusa da ita allurai da kwayoyi a wajen, hannunta cike da jini.
Mahaifiyarta ta durƙusa tare da rungumar ta da kuka
“Ya Allah, ƴata shaye-shaye? Farhaaa wake up, please wake up!…”
Mahaifinta da mamaki, yana girgiza kai ya ce
“My daughter? Drugs? Injection? How… how did this happen under our roof?”
Ammy na tsaye a gefe, jikinta na rawa. Idanuwanta cike da tsoro da damuwa.
Da sauri aka ɗauki Farha zuwa asibiti.
A Falo
Ammy ta zauna ita kaɗai a falo, tana riƙe da kanta cikin damuwa. Ga Maleekh yaƙi dawowa gida saboda ya san abin da zai tarar.
Sai ga Mahaifiyar A’isha (kishiyarta), ta shigo falo a hankali tare da murmushin taushin zuciya.
Mahaifiyar A’isha cikin rarrashi ta ce
“Don’t worry Hajiya… abin da ya faru ya faru, komai zai wuce. Allah zai ɗauki. Kiyi hakuri, komai zai dai-daita.”
Ammy ta ɗago kanta, idanuwanta sun sauya. Ta miƙe a fusace, ta shaƙe mata wuya a tsawa ce take faɗin
“Waye ya gayyace ki shagalin ɗana? Hm? Da akayi bikin ƴarki A’isha kin ganni na je? To me yasa bazaki fita daga rayuwata ba?! Ki zauna a yankin ki da ƴaƴanki ki barni!”
A’isha da ta fito ta tarar da abin da ke faruwa ta ruga cikin tashin hankali, ta riƙe hannun Ammy tana kuka...
Cikin sigar lallashi take faɗin
“Please Ammy ki saki Mamata! Don Allah ki sake ta, kiyi hakuri!”
Arfat da Islam ‘ya’yan Ammy suka nufo wurin suna kare mahaifiyarsu.
Arfat cikin fushi ta ce
“Wannan ya wuce gona da iri! Ke A’isha, baki isa ki shiga rayuwar Ammynmu ba!”..
Salma da Ummi ‘ya’yan mahaifiyar A’isha suma suka fito, suka ruga suka tsaya a gefen uwarsu.
Salma ta furta da ƙarfi cewa
“Baza mu bari ku ci zarafin Mamarmu ba! Duk da gidanku ne, amma itama tana da hakki akan gidan...tin da gidan mahaifin mu ne muma!”
Sai kawai lokaci guda aka kaure da faɗa a falon.
Arfat da Salma suka cafke juna, suka hau damben faɗa, da zage-zage...
Islam da Ummi suma suka rikice, suka fara wurgi da juna...
Ammy da kishiyarta kuma sun rungume suna kai wa juna duka da zagi iri-iri..
A’isha tana kuka tana ƙoƙarin raba su amma babu wanda ke sauraronta..
Ƙarar ihu, naushi, da zage-zage suka cika gidan gaba ɗaya. Falon ya rikide tamkar kasuwa...
Sai kawai ƙarar buɗe ƙofa ta ɗaki kunnen kowa...
Gaba ɗaya suka tsaya cak suna numfashi da huci jin irin tsawar da Abbah ya daka musu...
Abbah ya shigo, cikin shigar manyan mutane, wayarsa a hannu, fuskarsa a ɗaure kamar dutse...
Da kallo guda ya tsayar da rikicin. Kowa ya ja jikinsa gefe yana jan numfashi.
Abbah cikin muryar tsawa yake faɗin
“Subhanallah… me nake gani haka? Wannan gidan ku ka rikide kamar kasuwa? Ƴaƴa kuna dambe? Ku ma iyaye kuna shaƙe juna? Me yasa baku da kunya? Wani irin jahilci ne wannan?!"..
Ammy ta na huci ta ja baya, tana share gumin fuskarta. Kishiyarta ma ta gyara mayafinta cikin hawaye domin ko kaɗan bata taɓa tunanin zasu aiwatar da haka ba a gaban ƴaƴanta..
Arfat da Islam suka saki kwalayen rigunan juna suna ja da baya, Salma da Ummi suma suka ja gefe suna huci.
Abbah kamar zai haɗiyi ransa yana nuna su da yatsa tare da faɗin
“Dukanku! Waye ya kawo wannan tashin hankali a gidana?.."
Ammy ta sunkuyar da kai tana rawar baki, tana son yin magana amma Abbah ya katse ta da cewa
“Shiru! Ba na son magana yanzu. Kowa ya natsu. Wallahi wannan gidana ne, ba zan lamunci ku mai da shi dandalin zagi da ashar ba!”
Abbah ya kuma cewa
“Wallahi wannan tashin hankali da na gani yau… Maryam (yana kallo Ammy), ke kika jawo shi. Domin na fuskanci bakya son zaman lafiya da ƙanwarki...”
Ammy ta yi saurin mayar da martani da cewa
“Ai dama kai kafi son ta fiye da ni! Ka fifita ta akaina tun farko, to shikenan ka ja mata kunne kada ta sake takowa gidana nan Abuja. Wannan gidana ne, ban yarda da ita ba.”
Abbah ya ɗaga hannunsa da yatsa yana nuna Ammy, fuskarsa a cunkushe da fushi ya ce
“Ki saurare ni da kyau, Maryam. Wannan gida na ne ba gidanki ba. Kuma duk matana suna da hakkinsu a kaina. Itama matata ce kamar yadda ke kike matata. Wallahi ki kiyaye ni! Ban yarda da wannan shirmen da kike yi ba.”
Ammy ta harare shi, ta ɗaga hannu tana nuna Maman A’isha, ta ce:
“To ai saboda kana son ta ne kake cewa haka. Ni kuwa wallahi yau sai naci babban buro uban ta a gidan nan!”
Kafin ta ƙarasa, Abbah ya tako da ƙarfi zuwa gabanta. Idanunsa sun canza, ya girgiza kai yana furta cewa
“Ni kika zaga ko ita?! Ni kike nuna wa rashin kunya a gaban iyalaina?”
Wanne irin jahilci ne wannan? Maryam, ke kullum zaman lafiya baya yi miki. Uwargida ce ke, amma baki da haƙuri. Ki kalli kishiyarki, tana da haƙuri, ke kika jawo rikici.”
Ammy cikin fushi ta mayar masa da magana:
“Ai daman ita ka fi so, shine kake fifitata a kanta! To wallahi kar ta sake zuwa gidana! Taje ta zauna a Kaduna can.”
Abbah ya katse ta da tsawa yana faɗi
“Enough! Idan ba za ku iya zaman lafiya ba, kowacce ta koma gidanta. Ni ban kawo ku don nayi sulhu da mace ba, an gudanar da shagalin ɗana. Kuma yanzu shagalin ya zama abun kunya, kuma duk saboda ke Maryam, kin jawo cece kuce akan ɗana, masu zaginsa su suka fi yawa, to wallahi ki sani duk wanda ya zagi ɗana a bayan idona ban yafe ba, idan kuma naji a gabana to kotu ce zata rabamu, domin bazan lamunta ba, sannan kinzo kin ta da rigima a cikin gida ke da abokiyar zamanki m, shin akan ki aka fara ƙara aure ne? kina so ki koyawa yarana rashin kunya da ƙin mutane, to wallahi ki kiyaye ni..."
Kowa ya yi shiru, falo ya koma tamkar an zuba ruwa.
Sai Abbah ya zauna a babban kujera ya dafe kansa, a hankali, cikin takaici ya kuma furta.
“Wannan abin da ke faruwa yana ƙara tabbatar min… wannan gidan zai tarwatse idan babu wanda ya tsaya masa...”
Maman A’isha cikin nutsuwa ta ce:
“Ka yi haƙuri Alhaji, ba komai. Don zaman lafiya, ni da ƴaƴana za mu koma Kaduna.”
Ammy ta saki tsaki ta ce:
“kar ma ki koma dan uban ku daga ke har ƴaƴan nakin, gaba ɗaya saina hallaka ku idan kuka cigaba da zama mun...!”
Abbah miƙe wa yayi a fusace ya nufi Ammy cikin fushi:
“Ni kike zagi ko ita?”
Shiru ya ratsa falon. Kowa ya tsaya kallon ikon Allah.
Sai Maman A’isha ta share hawaye, ta dubi Abbah cikin ladabi ta ce:
“Yi haƙuri Alhaji… Ni dai yau zan bar mata gida, zan koma Kaduna da ƴaƴana, kada abun ya sake rikidewa.”
Abbah ya girgiza kai, ya tsaya tsayin daka sannan ya ce:
“Ba zaki tafi ko’ina ba. Wannan gidana ne, ba gidanta ba. Kinada ‘yancin hutunki a nan Abuja, kamar yadda itama take da ‘yanci ta je gidanki Kaduna. Amma wallahi bana son in sake jin hayaniya irin wannan a gidan nan. In na sake… sai na ɗauki mataki a kanku.”
Maman A’isha ta sunkuyar da kai, ta ce da siririyar murya:
“Na ji Alhaji… Zan yi haƙuri.”
Abbah ya sauƙe numfashi mai nauyi, ya dafa kafaɗarta cikin tausayi ya ce
“Allah ya saka da alheri. Ki zauna ki nutsu, ki sani duk matana ɗaya suke a wurina. Abin da ya sa na raba gidanku tun farko kenan saboda rashin zaman lafiya. Ke ki zauna a Kaduna, ita ta zauna nan Abuja. Amma ki tabbata, wannan gidan nawa ne, ku duk kuna da hakki akansa.”
Ammy ta ce
"Ai wallahi ba'a isa a wulakanta ni a gidan nan ba..."
Abbah nuna ta ya yi da yatsa yana faɗin
"Wallahi zan kwad'a miki mari yanzu idan baki kiyaye ni ba.."
Da sauri Ammy ta ja tsaki ta bar falon, tana ganin Abbah ya fusata.
Abbah ya kalli Maman A’isha yana faɗin:
“Kije ki zauna, kiyi haƙuri. Wannan gidana ne, duk kuna da hakki a kai. Amma wallahi kada na ƙara jin hayaniya a nan.”
Maman A’isha ta juya tare da iyalainta..
Su ma iyalain Ammy barin wurin suka yi suna taya uwarsu kishi..
Shima Abbah haura saman part ɗinsa ya yi...
Dalilinda yasa Abbah ya raba musu gida kenam saboda rikici basa zaman lafiya, Ammy take zaune a Abuja, Maman A'isha kuma a Kaduna...
Bayan washegari, Farha tana kwance akan gadon asibiti ɗaure da drip a hannunta, ga Mommynta a gefen gado suna so su tafi da ƴarsu..
A zabure Farha ta tashi zaune tana faɗin..
"Wallahi sai nayi maganin ku, tin da ni zaku wulakanta a gaban mutane, nima sai na tozarta ku..."
Mahaifiyarta dake kusa da ita ne ta rungumeta tare da rarrashinta..
Sai yanzu Farha ta dawo cikin hayyacin ta tana bin asibiti da kallo kamar wata baƙuwa..
Tana cijan leɓe ta ce
"Wa ya kawo ni hospital? ku ma kun san cewa ina shaye-shaye ko?.."
Mommynta ta ce "ki kwantar da hankalinki zamu tafi dake London a yau, daman jiran tashinki muke.."
Farha tasa hannu ta fincike drip ɗin hannunta tare da miƙe wa tana faɗin
"I will not go anywhere, burina bazai taɓa cika ba in har Maleekh bai aure ni ba, inhar ya auri wata bani ba..." ta jinjina kai sannan ta ce
"Kashe kaina zanyi domin banida wani amfani, na tsani rashin nasara..."
Mommynta gaba ɗaya ta tsorata ta ce
"Baza ma ki mutu ba insha Allahu, kuma sai kin cika burinki....ina supporting ɗinki my daughter, amma kafin ki ci nasara sai kin bi wata hanya guda..."
Farha ta tsaya tana sauraron mommynta..
Uwar ta ci gaba da faɗin
"Inaso ki shiga jikin Amal yanda zata yadda dake sannan ki tarwatsa mata rayuwa, inason Maleekh ya tsane ta lokaci guda, ke Daughter kin san hanyar da zaki bi..."
Farha ta jinjina cike da murmushin mugunta...
Daga wannan lokacin aka sallame su, bayan sun koma gida Ammy tayi farin cikin ganin Farha..
Ammy ta ɗau alƙawari wa iyayen Farha cewa saita aura wa Maleekh Farha, ko yana so ko bayaso, domin duk suna son farin cikin ta, Ammy duk da itace babba da mahaifiyar Farha tana matuƙar tsoronta da mahaifin Farha, shiyasa take son faranta musu da ƴar su...
A wannan ranar suka koma London, gida dai kowa ya watse ya dawo yanda yake..
Yau kwana uku da gudanar da Birthday amma Maleekh bai koma gida ba...
A wannan ranar Farha ta nemi Islam da ta rakata gidan Amal...
Ba musu Islam ta biye ta suka shirya tare da jan mota suka tafi....
Bayan sun isa gwarinpa estate a layin gidan suka Parker motarsu a bakin titi, sannan suka ƙarasa bakin get tare da knocking...
Maigadi ne ya buɗe musu, ganin farha yasa shi faɗin
"Ke kika ƙara dawowa kuma.."
Farha ta ce
"Ka ga ba wurinka muka zo ba, ka ci gaba da aikin ka kawai.."
Maigadi ne ya ƙira wayan cikin gidan, bugu ɗaya aka ɗauka ya sanar musu cewa sunyi baƙuwa, jinjina kai maigadi yayi sakamakon bada izinin shiga..
Kallonsu yayi sannan yayi musu iso...
A falo Suka tarar da Inna a zaune Bayan Maigadi ya barsu sun shiga.
Inna da ganinta ta zabura ta miƙe tare da faɗin
"Meya sake kawo ki gidan nan Fara? Kinzo ne ki ƙara saka jikata a matsala? Kinaso ta ƙara komawa wurin folin tetion ne? (Police station)..
Sai ga Amal ta sauƙo daga upstairs, fuskar ta cike da annuri. Makeup ɗinta ya haskaka fuskarta domin ba ƙaramin kyau tayi ba, inda tayi foundation da launin ruwan pawder, kalar gyalen kayan . Gashinta an ɗaure shi a tsakiyar kai cikin salon da ya bazu da kyau, sannan an yi masa styles a gaban gashi da ya kwanta yayi kyau. Sanye take da dankareren less wanda ya yi daidai da jacket ɗin wayarta iPhone 17 dake hannunta, da kuma plate shoes da suka yi daidai da kayan da ta saka.
Ta zauna a kan sofas, tare da ɗora ƙafa ɗaya a kan ɗaya, sai da ta ja ajinta kafin ta faɗi cikin murmushi:
"Sannun ku da zuwa, meke tafe daku..?"
Farha ta murmusa, zuciyarta cike da shiri, ta ce cikin nutsuwa:
"Kiyi haƙuri, Amal. Banzo da niyyar faɗa ba, sulhu nazo nema. Naga kamar yanda kika faɗa ke da Yaya Maleekh, mutu karaba, na gane hakan. Shiyasa na tako nazo yanda kike, domin baki haƙuri, sannan ina mai sanar miki cewa nabar miki Yaya Maleekh."
Islam cike da mamaki take kallon Farha, tana tunanin shin har zuciyarta take faɗin haka kodai akwai abinda take shiryawa.
Amal ta jinjina kai sannan ta ce
"Allah yasa da gaske kike"
Inna ta ce
"Ke Fara ba abin yadda bane, kinzo da salon ki ko?.."
Farha ta ce
"wallahi ku yadda dani, bazan iya juran cin mutunci ba shiyasa na haƙura da soyayyarsa.."
Suna cikin wannan sai suka ji sallama an shigo falon..
Duk kallon bakin ƙofar falon suka yi,
Maleekh ne da abokansa sun zo ganin Amal kafin su wuce garuruwansu, daman shagalin birthday ne ya kawo su kuma yanzu angama zasu tafi sun gama shirinsu..
Maleekh ganin Farha yasa shi nuna ta da yatsa
"Keee meya kawo ki wurinta again?.."
Farha kamar zatayi kuka ta ce
"Nazo bata haƙuri ne da neman sulhu.."
Amal ta miƙe tana murmushi ta ce
"Rabin raina kar ka damu, Farha tazo ne bawai da neman rigima ba.."
Maleekh yana hararar Farha domin bai gama yadda da ita ba.
Amal ta kalli abokan Maleekh tayi musu sannu da zuwa, duk zama suka yi suna yabonta tare da faɗin
"Wannan dacewar yayi kyau tsakanin Maleekh da Amal..."
Masu aiki ne suka kawo musu kayan drinks da delicious food da aka dafa musu daman Maleekh ya sanar mata cewa zasu zo..
Amal ta gayyaci Farha da Islam su zauna su ci abinci tare. Farha ta yi murmushi, amma zuciyarta cike da shiri da takaici.
Haka suka sha hirarsu har da Inna..
Daga baya Maleekh ya sanar wa abokansa cewa zaiyi wa masoyiyarsa babbar kyauta..
Maleekh ya miƙe tare da kamo hannun Amal ya miƙar da ita sannan ya damka mata makullin mota mai tsada.
Jeep mai ƙira ta musamman Jeep Wrangler Rubicon 2025, kalar Black Steel.
Farha da Islam suka zaro ido suna kallonsu da mamaki. Farha ta yi tunanin ta rausa ihu, sai kawai ta jure. Abokansa duk sun tafi cikin farin ciki, Inna ta yi dariya tana tafa hannu, Amal kuma ta rufe bakinta da hannaye biyu, tana mamakin wannan surprise.
Maleekh ya ƙara da cewa:
"Na ba wa masoyiyata Amal appointment a kamfanina mai suna CashTalk, ita zata maye gurbin Assistant ɗina, wacce a halin yanzu tayi aure ne a ƙasar waje. Na bawa Amal miƙamin ta."
Duk farin ciki ya cika falon, abokansa, Inna, masu aikin gidan, da ita Amal. Farha kuwa, zuciyarta cike da rashin jin daɗi, tana kallon wannan nasara da Maleekh ya yiwa Amal.
Maleekh ya ƙara da cewa:
"Ba wai nayi hakan da kaina bane, sai da na nemi shawarar mahaifina sannan yayi supporting ɗina akan Amal."
Bayan an gama ƙaramin shagali a gidan su Amal daga baya Farha da Islam suka bar gidan cike da takaicin abinda suka tarar..
Suna daga cikin motarsu Farha take faɗin...
“Dole ne in mayar da martani… in nuna masa cewa ni ce haƙiƙanin zaɓinsa, ba wai Amal ba…”
Islam tana zaune kusa da ita, tana kallonta cikin damuwa ta ce
"Aunty Farha, kina nufin zaki zo a gaba da Amal? Kina sane da cewa Yaya Maleekh har yanzu bai amince da zuciyarki ba?"
Farha ta jinjina kai, da murmushi a fuska ta ce:
"Ina sane da haka, amma duk wani sirri yana da hanyarsa. Zan yi hankali, duk da haka zan samu damar nuna masa cewa ni ce mafi dacewa.
Zan yi amfani da hankali na, ba rigima ba. Dole Maleekh ya gani cewa ni ce wacce zata iya zama mata mai hankali da daraja,”
Islam ta ce
"Ki tuna, Aunty Farha, komai bazai zo da sauƙi ba. Amma idan kika yi hankali, Yaya Maleekh zai fara lura da canji a jikin ki."
Farha ta ce.
“Dole ne in yi shiri sosai, in nuna masa darajata. Wannan lokaci ne na nuni da hankali, ba rigima ba. Komai zai fara nan gaba…”
Ammy tana kan jiran dawowar Maleekh yau kwana uku bata ganshi ba,
Bayan sun dawo gida, a falo suka tarar da Ammy..
Farha ta zauna a kan kujera, tana kallon Ammy cikin nutsuwa sannan ta ce:
"Ammy, Maleekh yayiwa Amal kyautar mota..."
Ammy ta girgiza da jin wannan batun, a fusace ta miƙe da sauri:
"Me kike faɗin Farha?!"
Farha ta ci gaba da faɗin
"Tabbas kuwa, sannan ya ba ta aiki a kamfaninsa, a matsayin mataimakiyarsa ma."
Ammy ta tsaya cike da tsananin fushi, tana ƙoƙarin jurewa, sai kawai ta fara jin hajijiya tana shirin faɗuwa a gefen ta Islam ta riƙe ta, tana ƙoƙarin kwantar da hankalinta:
"Sorry Ammy…"
Islam ta zaunar da ita.
Ammy ta ce
"Wato Maleekh ya raina ni koh?
Sai ga Maleekh ya turo ƙofar falon da sallama a bakinsa, tsabar damuwa basu ji shigowar motarsa ba har yayi parking ya fito ya shigo falon...
Ammy na ganinsa tayi saurin miƙe wa ta nufe shi da sauri, tana zuwa ta zabga masa mari a fuska, kafin ya ankara har ta ƙara zabga masa wani marin tana kuka...
Ammy ta juyar da fuskarta cike da fushi tana faɗi
"Wato Maleekh ka raina ni ko? Bayan abinda ka aikata a gaban al'umma, ka rushe baikon dana saka maka da Farha, sannan kayi rawa da wacce na tsana a rayuwata, still yanzu kayi mata kyautar mota da aiki a kamfaninka? MALEEKH!"
Maleekh bai ce komai ba, ya tsaya tsaye kamar dutse, idonsa na kallon Ammy da nutsuwa, ba tare da ya nuna fushi ko tsoro ba.
Farha da Islam suna kallon abin da ke faruwa cikin mamaki. Farha tana murmushi a ranta, tana jin yadda shirin da ta fara tunanin zai fara aiki a hankali.
Ammy kuwa, tana tsaye, har yanzu tana riƙe da ɗan damuwar fushi, ta ce
"Ka san dai, Maleekh, ba zan iya yarda da wannan ba. Duk abinda ka aikata ba daidai bane… Ya kamata ka san inda yake maka ciwo!"
Maleekh ya ja numfashi mai zurfi, ya matsa zuwa ga Ammy, yana ƙoƙarin ɗan sassauta lamarin ya ce:
"Ammy… kada kiyi haka, ina son ki… amma wannan lokacin bai dace da faɗa ba. Zan yi bayani, amma ki saurara min."
Ammy ta ja kai gefe, har yanzu tana cike da fushi da rashin yarda..
Farha ta kalli Islam cikin sirri, tana murmushi a ranta ta ce
"Nan gaba, Maleekh zai fara lura da ni. Wannan farkon shirin ne kawai…haɗa shi da mahaifiyarsa"
Ammy ta ce
“Ka san irin yadda nake ji kuwa? ka san irin rainin da ka ja wo mun kuwa? To kaima yanzu ka raina ni Maleekh!”
Islam ta matsa kusa da Ammy, tana riƙe da hannunta, tana faɗin:
“Ammy, ki yi haƙuri, kada ki fusata da shi yanzu, mu saurari abinda zai aiwatar.”
Maleekh ya juya hannunsa ya riƙe Ammy a hankali, cikin sanyin jiki, yana murmushi mai ɗan tsananin sanyi. Ya ce a hankali:
“Ammy… ni ban raina ki ba. Na san kina jin haushin abin da na yi, amma abin da na aikata ga Amal… ba wai don bana son farin cikin ki ba ne, ko don na fi son ta a kanki… ba haka bane. Na aikata shi ne saboda zuciyata ta amince da hakan, kuma nayi tunani, kuma mahaifina ya goyi bayan hakan.”
Ammy cikin tsawa take faɗin
“Na yi haƙuri? Ka aikata laifi a gaban kowa sannan kace na yadda da kai?! Ka yi rawa da wacce bata da wani amfani a wurina! Ka ɓata Farha a gaban kowa, yanzu kuma ka yi wa Amal kyautar mota! Menene a zuciyarka Maleekh? Kodai duk wannan Mahaifinka ne ya umarce ka da kayi mun haka?..."
Maleekh ya ɗan saki hannunta, yana kallonta ya ce
“Ammy… ku yi haƙuri da ni. Amma ki saurare ni, ki yi ƙoƙarin fahimta ta… Zuciyata yanzu ta fahimci gaskiya, kuma ba zan sake yin abinda zai raina ki ba. Ina so ki gane cewa ni da Amal… akwai soyayya tsakaninmu, amma hakan ba yana rage hakkin ki a zuciyata ba.”
Ammy ta gyaɗa kai cikin rashin gamsuwa, hawaye na zuba daga idonta. Islam kuwa ta matsa kusa da ita, tana ƙara kwantar mata hankali.
Maleekh ya ja numfashi, ya miƙa hannu ga Ammy yana faɗin
“Ki amince da ni, ki yarda dani Ammy, bazan so ganin hawaye a fuskarki ba..."
Ammy ta ce
"Idan kana son ganin farin cikina Maleekh to ka amince da auren Farha.."
Ya share guntun hawayen da ya zubo masa sannan ya ce
"Shikenan zan yi yanda kike so ɗin..."
Ammy ta tsaya a tsaka-tsaki, tana kallon Maleekh, zuciyarta na bugawa cikin haɗi da damuwa.
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 62