Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tsaye suna tafi, wasu kuma suka dubi Maleekh da ido domin ganin yanda zai yi, shin da son ransa ne ko kuma Suprise ne kamar yanda aka sanar.. Maleekh ya tsaya cak kamar wanda aka yi masa sihiri. Bai taɓa tsammani wannan ba... Amal tana zaune a falonta, falon da aka kawata cikin nutsuwa da kyan gida na zamani. Wani ƙaramin flower vase ke tsakiyar table, TV ɗin da ke manne a bango kuwa na nuna live cinema broadcast na taron da Ammy ta shirya domin ɗanta. Amal na zaune ne gefen sofa tana cin abinci a hankali, sai kawai ta ji jawabin Ammy....zaro ido tayi tana kallon TV daga baya MC a hall ɗin ya nanata da cewa: “Ladies and Gentlemen, please rise and welcome… Farha & Maleekh the couple-to-be tonight!” Amal ta zabura! Abincin hannunta ya zube ƙasi, kofin drink ɗinta ya biyo baya ya zube a tiles. Hannayenta suka fara rawa, zuciyarta na bugawa kamar zata fito daga kirjinta. Ta miƙe da sauri, idanunta sun cika da hawaye tana faɗin: “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un… baiko? Baiko kuma Maleekh da Farha? Maleekh ya yaudare ni?” Ta kai hannu kan zuciyarta tana jin wani irin bugawa da ciwo. TV ɗin na nuna Farha cikin wata farar riga mai tsada, rigar da aka kawata da diamonds stones masu walƙiya. An zaunar da ita kusa da Maleekh a kujerar da aka tanadar musu. Farha ta yi kyau sosai, tana murmushin alfahari, kamar wacce ta ci nasara. Iyayenta daga London suma suna zaune a gaba cikin kujera ta musamman, suna ta tafa hannu cike da jin daɗi da alfahari. A gefe kuma aka nuna A’isha ƙawar Amal daga Kaduna tare da mahaifiyarta wato kishiyar Ammy, da ƙannenta mata biyu. Sai camera ya nuna Ammy na nuna rashin jin daɗinta, ta ƙarasa wurinsu Mahaifiyar A'isha tana habaici tana cewa: “Meya kawo ku wannan shagali? Ai ban gayyace ku ba, kuma ku ka zo. Amma dai ku zauna ku gani, wannan baiko ne da ba ku isa ku hana ba.” Amal ta ɗan ja da baya, tana tari sakamakon kwaruwar da tayi, ta ɗauki ruwa ta kora, hawaye na silalowa. Tana faɗi da ƙarfi: “Wallahi ba haka ba ne! Taya Maleekh zai mun haka? Kenan yasan da maganar baiko shine ya bani card ɗin gayyata da hannunsa...kuma ya zauna tare da ita?” Ta fashe da kuka, zuciyarta na tafarfasa. Sai ta ji ƙarfin zuciya ya shige ta. Ta fice daga gidan ba tare da ta shirya ba. Babu gyaran kai, babu kwalliya, babu mayafi mai kyau. Kawai ta ɗauki jakarta ta rataya a kafadarta..Ta riƙe wayarta da ƙarfi a hannu ɗaya, ta zura takalmin slippers, ta fita da gudu kamar wacce zuciya take tura ta. A HALL ƊIN TARON Maleekh kuwa, duk da cewa yana zaune kusa da Farha, gaba ɗaya jikinsa a takure yake. Idanunsa na yawo cikin hall ɗin yana kallon ko'ina domin duba ko Amal tazo.. Ya roƙe ta akan tazo, yana zaune sai kuma ya tuna lokacin da ya bata VIP invitation card yana ce mata: “Amal, koda duniya zata yi gaba dani, kin zama wata ta musamman a rayuwata. Kawai ki kasance tare da ni ranar, zan gabatar dake a matsayin masoyiyata..." Amma yanzu babu ita, babu kamshinta, babu murmushinta. Zuciyarsa ta cika da baƙin ciki. Abokan sa na gefe suna ta murna, suna tura masa cup na wine suna cewa: “Happy Birthday King Maleekh!” Amma kwata-kwata baya jin daɗin wannan ranar. A ransa yana cewa: “Ina Amal? Me yasa bata zo ba? Ko kuwa an dakatar da ita ne? Ko… bata ɗauki rayuwata da mahimmanci ba?” Ya ji ransa yana tafarfasa, amma bai nuna wa kowa ba... ☆☆☆☆ A wannan lokacin Amal na ta gudu tana ƙiran taxi. Taxi ɗin ya tsaya, ta shige ciki tana hawaye. Ta ce “Driver, please… Hilton Event Center… yanzu yanzu, kayi gudu!” Driver ya dubeta ta madubi, ya ga fuskarta cike da hawaye. Ya ɗaga kai kawai ya ce: “Okay madam.” Motar ta yi saurin tafiya cikin titunan Abuja da fitilun titin ke walƙiya. Amal ta jingina kanta jikin glass, hawayenta na gudu tana faɗin a hankali: “Ya Allah ka bani ƙarfin zuciya. Wallahi idan na shiga hall ɗin, Allah kada ka bawa Maleekh damar da zai amince da baikon nan....” Wurin nada nisa da gidan Amal, hakan yasa har yanzu bata iso wurin ba. A hall kuwa ana kan gudanar da wani wasa. An tayar da Maleekh tsakar filin, aka ɗaura masa farin kyalle a idonsa. Wani wasa ne irin na masu kuɗi, sunan wasan dumi-dumi tsakanin ƙawayen Farha, manyan ’ya’yan masu kuɗi... Ka’ida: Maleekh zai rinƙa tafiya a hankali, ido a rufe, hannunsa a miƙe. Duk wacce hannunsa ya sauƙa a kanta, ita ce za suyi rawa tare a gaban jama’a. Shi kuma Maleekh ya tsare fuskarsa da ɗan murmushin dole. A ransa kuwa ba ma wasa yake so ba, ba kuma baiko da Farha yake muradi ba.... Sai dai abokansa da suka fahimci akwai damuwa a tattare dashi sai suka fara lallamin shi akan kada ya nuna rashin jin daɗinsa a bainar jama’a, kada ya kunyata iyaye, kada ya lalata yanayin shagalin. “Ka bari komai ya wuce, daga baya sai kayi komai,” suka shawarce shi... Sai ya yarda da haka, ya fara tafiya a filin, ido a rufe, yana miƙa hannu, yana neman wanda zai kama. ’Yan matan a gefe kuwa suna tsalle-tsalle da dariya, suna ɓuya suna ƙara motsa nishaɗi. Jama’a suna ta tafi suna dariya. A gefe kuwa mahaifin Maleekh na zaune, fuskar sa cike da farin ciki da alfahari da ɗansa, yana ta jinjinawa taron. A wannan lokaci ne Amal ta iso. Ta nuna card ɗin da Maleekh ya bata tun farko, security suka dubeta, duk da shigar ta ba ta masu kuɗi bace, sai suka barta ta shiga. Tana sanye da doguwar riga, kanta babu gyaran salo irin na taro, ƙafarta sanye da slippers. Hasken fuskarta da kamalarta sun bambanta ta a cikin jama’a. Da ta shiga, idonta ya sauƙa kan Maleekh da aka ɗaura masa farin kyalle a idonsa. Yana yawo cikin filin, yana wurga hannu yana neman kama wata. Zuciyarta ta buga. Bata tsaya tunani ba ta ruga da gudu ta nufi tsakiyar filin, zuciyarta na tafasa da niyyar kada a aikata abinda zuciyarta zai buga... Kafin ta yi wani abu, sai ga hannun Maleekh ya cabke ta!.. Lokaci guda ya ji wurin yayi tsittt, ba dariya, ba ihu, ba tafi....ganin haka yasa ɗayan hannunsa ya cire kyallen da aka ɗaura masa, ɗayan hannun kuma yana riƙe da kafaɗar Amal... A nan idonsa suka haɗu da nata. Tsitttt! Wurin ya yi shiru! Kowa ya dakata da numfashi, idanun kowa ya sauƙa kan kyakkyawar fuskar Amal wacce bata daga cikin ’yan matan masu kuɗin.... Wata nutsuwa ta bayyana a idanun Maleekh lokacin da ya gane yana riƙe da hannun Amal ne.. A gefe kuwa Farha da aka zaunar da ita a kujera ta miƙe da zafin rai, fuskarta ta canza daga farin ciki zuwa baƙin ciki, zuciyarta tana tafasa da haushin wannan yarinyar da ta kutsa musu wasa... Ammy kuwa ta kaɗa kai a fusace, tana hararar Amal, zuciyarta cike da ɓacin rai, tana jin kamar Amal ta zo ta ɓata musu shiri a gaban iyayen Farha da kowa da kowa... Sai dai A’isha, ƙawar Amal, na cikin jama’a. Ganin Amal ya sanya ta tashi da farin ciki, tayi dariya da tafi tana goyon bayan abokiyar tata...A fusace Ammy ta juyo ta kalle ta tana hararar ta kamar idanu zasu faɗo, ai ba shiri A'isha ta zauna tare da nutsuwa, domin a wurin iya tafin ta ne kawai ya ratsa kunnuwan kowa... (Ina Amaleekh fan's readers, shin ya ku ka a wannan lokacin?😅😅🫣) MC, wanda bai san komai game da Amal da Maleekh ba, ya ɗauka wannan al’ada ce ta wasa. Shi ma sai ya nufi mic ɗin ya ce da murya mai ƙarfi: “Alhamdulillah! An samu wacce aka kama. Yanzu kuwa babu sassauci tare zasu yi rawa!” Sai ya ƙira DJ ya kunna kiɗan rawa.. Kafin a sake DJ, Farha ta daka uban tsawa cikin zafin rai, ta ɗaga hannu faɗin “Ku dakata! Ba wani rawar da za a yi a nan. Wannan yarinya ai ba kowa bace face wata matsiyaciya ballagaza! Bata daga cikin mu, wai ita a dole son Ya Maleekh take. ta ƙuduri aniyar cewa sai ta mallake shi!” Jama’a suka ɗaga kai, wasu suka yi tsit suna kallon abin da zai biyo baya. Amma kawayen Farha da ’yan uwanta kuwa, sai suka kwashe da dariya, suna nuna Amal da hannu, suna yi mata kallon ƙasƙanci da raini... “Shine zata shigo cikin mu? Ni kam ba zan taɓa yarda ba!” wata daga cikinsu ta faɗa tana harararta. Sai dai abokan Maleekh ba duka suka ji daidai da wannan kalaman ba. Wasu daga cikinsu suna kallo suna murmushi, suna ganin Amal da gaske ta dace da Maleekh. A idanunsu, kyawunta ya wuce kima, kyakkyawa ce mai tsarin halitta, idan dai ta samu kuɗi kamar nasu, to ba ƙaramin daraja za ta samu ba. Amma kuma wasu daga cikinsu sun fi son ganin auren ɗan mai kuɗi da ’yar masu kuɗi kawai. A ransu suna faɗin: mai kuɗi sai mai kuɗi, talaka kuma sai talaka... A lokacin ne Maleekh ya ɗaga hannunsa ya nufi jama’ar wurin da murya mai ƙarfi, yana kallonsu da idanu masu ɗauke da ƙarfin gwiwa, yana faɗin “Wannan itace zaɓi na. Ita zan aura! Baikon da aka yi mini da Farha na soke shi yanzu nan a gaban kowa, domin bana ƙaunar ta. Abin da nake so shi nake faɗa a nan gaban duniya. Kuma wacce kuka gani a gabana, Amal itace tarihin rayuwata.” Ya juyo yana duban MC kai tsaye, fuskarsa babu annuri sai da ƙuduri ya ce “Kada mu ɓata lokaci. DJ, saka mana waƙa irin ta masoya. Yanzu haka, wannan ita ce rawar zuciyata.” MC ya tsaya kallonsa cikin razana, amma ganin ƙarfin da kalaman suka ɗauka sai ya ɗaga hannu ya bada izini. DJ ya kunna waƙa, kiɗa ya cika hall ɗin. Maleekh ya matso kusa da Amal, ya kama hannunta cikin girmamawa, sannan ya fara jujjuya ta cikin kiɗan... Jama’a suka yi shiru na ɗan lokaci, kafin wasu daga cikin abokansa suka kwad'a uban tafi suna ihu cikin farin ciki. “Ya dace da ita wallahi! Su biyu sun yi kyau sosai!” wani daga cikinsu ya furta cikin jin daɗi. Amma daga bangaren ’yan uwan Maleekh kuwa, babu wanda ya nuna goyon baya. Fuskar su tamkar an sassaka ta cikin dutse, babu murmushi, babu farin ciki. Ammy kuwa ta zauna cak, zuciyarta kamar zata fashe. Wani irin baƙin ciki ya lulluɓe ta, har kowa ya lura da fuskarta ta kumbura sosai.. Abbah, mahaifin Maleekh, ya miƙe ya fice daga hall ɗin da wayarsa a kunne, kamar yana yin waya. Ba wai saboda bai goyi bayan ɗansa ba, a’a, kawai ya fita ne saboda gudun zargin jama’a. Bai son mutane su yi tunanin shi ne ya sa Maleekh ya nuna adawa da Farha. Amma a ransa ya yi murmushi, domin shi ya fi son ɗansa ya zaɓi wacce yake so. Iyayen Farha kuwa, fuskar su ta canza gaba ɗaya. Zuciyoyinsu sun cika da haushi da ƙasƙanci, suna ganin an tozarta ’yarsu a bainar jama’a. Amal kuwa, duk da cewa tana tsaye a hannun Maleekh tana rawa da shi, gaba ɗaya jikinta ya mutu da tsananin kunya. Bata saba irin wannan ba, musamman a gaban jama’a da suka zuba mata ido. Tana jin kamar ƙasa ta buɗe ta shige tsabar kunya.. Amma Maleekh ya riƙe ta da ƙarfi, yana jujjuya ta da murmushi tamkar yana so ya tabbatar wa duniya cewa babu mai iya rabasu.. Maleekh ya ɗauki Amal da hannunsa biyu kamar wani gwani a rawa, ya juyo da ita cikin natsuwa, idanunsa suna ƙafe a nata. Kowa ya gane ba wai rawa ce kawai yake yi ba, kamar yana furta wata soyayya ce ta cikin zuciyarsa, yana sauƙar da ita cikin tafin Amal... Kiɗan ya ƙara ɗagawa, MC na ihu da dariya yana ƙarfafa jama’a: “Ladies and gentlemen, ga masoya a gaban ku! Let’s give them a big round of applause!” Sai kuma aka ji wani irin sautin tafi daga cikin abokan Maleekh, wasu daga cikinsu har ihu suka fara yi suna kwatanta irin soyayyar nan da suke gani.. “Amal and Maleekh forever!” wani ya faɗa yana dariya. Amma a gefe guda kuwa, ’yan uwa da dangin Maleekh suka ƙara jinjina kai da kaɗa hannaye. “Wannan abin kunya ne a bainar jama’a ɗan hamsha'kin mai kuɗi yana rawa da matsiyaciya ƙasƙantacciyar talaka, wacce take sanye da slippers a ƙafarta..,” wata daga cikin dangin Ammy ta furta a hankali tana huci... Ammy kuwa ta kasa ɓoye haushinta, tana zaune a kujerarta tana jijjiga ƙafafunta da sauri kamar wacce zuciyarta ke ƙoƙarin tsallewa daga kirjinta. Wani lokaci tana kallon Farha, wacce ta tsaya tana huci kamar za ta cinna wa kanta wuta. Idanunta sun cika da hawaye.. Abbah a wajen da ya fita, ya tsaya a bakin kofar hall yana kallon cikin gilashin babban tagar hall ɗin. A zuciyarsa ya furta: “Da gaske yarona ya yi abin da zuciyarsa take so.” Sai ya yi murmushi a hankali, sannan ya ɗaga wayarsa ya ci gaba da maganar da yake yi da wani abokin business ɗinsa, kamar ba shi da wata damuwa... A gefe kuwa, iyayen Farha sun kasa ɓoye fushinsu. Mahaifinta ya miƙe yana kallon Ammy cikin ɓacin rai, ya ce cikin harshen turanci mai ɗauke da fushi: “This is a total disgrace! How could you allow this in public? My daughter deserves respect, not humiliation!” Ammy bata samu damar ba shi amsa ba, domin hankalinta gaba ɗaya ya tattaru wajen ganin yadda Maleekh ya ci gaba da juyawa da Amal kamar sarautar rawa ta dogara da su... Amal kuwa jikinta gaba ɗaya ya yi sanyi. Hannunta na cikin na Maleekh, zuciyarta na cike da nauyi. Idanunta sun rufe da hawaye masu kauri, amma tana ƙoƙarin ɓoye su domin kada duniya ta ga raunin da take ciki. Duk da haka, a zuciyarta tana jin soyayyar Maleekh na sauƙa gareta.. Sai ga wani irin danna haske da akayi a hoton bidiyon da ake nuna wa a babban screen, an ɗauki Amal da Maleekh suna rawa, aka ƙara slow-motion, inda Maleekh ya juyo yana kallonta da murmushi mai cike da alamar “na mallake ki.” Jama’a suka sake ɗagawa da ihu, wasu cikin sha’awa, wasu cikin mamaki, wasu kuwa cikin takaici. Wani daga cikin abokan Maleekh ya yi ihu: “Wallahi wannan shine birthday gift ɗin shekara! Baiko ya zama soyayya ta gaskiya!” Farha ta kasa jurewa, ta fice daga hall ɗin da gudu tana riƙe da rigarta, tana kukan kuka mai sauti... (Ai da nine Farha da tin farkon abun zan fice don kada zuciyata ta buga 🤣🤣)... MC kuwa ya rufe maganar da dariya yana faɗin: “Ladies and gentlemen, wannan shine soyayya! Ko dai a so aure, ko a mutu da ƙiyayya. Tonight, we have witnessed the beginning of a new chapter.” Maleekh ya matso kusa da kunnen Amal, ya yi mata raɗa cikin murya mai sanyi: “Na bayyana ki a gaban duniya, ko kina jin tsoron hakan?” Amal ta kasa amsawa. Sai kawai hawaye suka sauƙo daga idanunta, tana jin ƙaunarsa ta ƙara shige mata jiki. Live Broadcast Ba kawai hall ɗin da ke cike da hayaniya ba, hatta duk gidajen masu kallo a gida da wajen ƙasar nan suna kallon shagalin birthday ɗin Maleekh Live on Cinema. Gidan su Amal kuwa.. A falo, Inna tana zaune da masu aikin gida, su ma kallon suka kafa a babban TV plasma. Da suka ga Amal a hannun Maleekh, suna rawa a gaban kowa, gaba ɗaya gidan ya ɗauki ihun farin ciki. “Innalillahi! Amal ce a hannun Maleekh?!” Inna ta zabura tana dariya tana tafa hannuwa... Masu aikin gida suka kwashe da ihu: “Lallai wannan soyayyar ce ta gaskiya! Tab yau Farha zata haɗiyi ranta..!” Inna ta jinjina kai, tana murmushi ta ce “Allah ya albarkaci dangantakar ku, Amal… ai tunda duniya ta ga haka, babu mai iya raba ku...Sai dai tsorona kada su cutar mun da Amal..” ☆☆☆ Bayan DJ ya rage kiɗa, jama’a suka fara watsewa da surutai kala-kala. Wasu suna ta jinjinawa rawar soyayya. Wasu kuwa suna ɗaga ƙafa cikin fushi, musamman dangin Ammy. Abokan Maleekh na dariya suna jin daɗi, suna ɗaga wayoyinsu suna ɗaukar hotuna da bidiyo suna sakawa a social media. Bayan an dawo gida.. Farha ta rufe kanta a ɗaki tana zabga ihu tana wurgi da pillows. Mahaifiyarta tana buga ƙofar tana kuka tare da faɗin “Farha please open this door! Ki bari mu yi magana! Don’t kill yourself because of this boy!” Mahaifinta shima haka yake buga ƙofar da ƙarfi yana cewa “Open the door now Farha! Stop disgracing us more than this!” Sai kawai aka ji muryarta daga ciki tana tana faɗin “Na tsane shi! Na tsani Amal!! Wallahi bazan yarda da wannan wulakanci ba!” Tayi maganar cikin kuka.. Sunyi akan Farha ta buɗe amma taƙi, haka suka hak'ura suka koma falo.. Ammy tana zaune a sofas, Mahaifin Farha yana tsaye yana huci, ya juya ya kalli Ammy a fusace ya ce: “This is nonsense! Absolute nonsense, Maryam!” ya ce cikin ƙarfi... “You humiliated my daughter in front of the whole world! Do you know who I am in London? Do you know how many businesses I control? And today my only daughter was disgraced like this?” Mahaifiyar Farha ta karɓa da kuka tana faɗin: “Maleekh bai yi wa yarinyarmu adalci ba! Yaudarar mu kika yi, Ammy! Kin ce za su yi baiko, amma ki kalli yadda ya tozarta ta a gaban kowa. Wannan abun ba zai taɓa wucewa haka kawai ba!” Ammy ta riƙe kanta tana huci, zuciyarta cike da kunya..ta ce “Dan Allah kuyi haƙuri. Ni kaina ban san hakan zai faru ba… ni na shirya komai domin ku, amma ga shi abin ya juya.” Dake duk ƴan uwan juna ne, su a danginsu basa Auran na waje sai haɗin gida.. Abbah da Ammy haɗin gida ne domin su ɗin ƴaƴan baffanu suke.. Mahaifiyar Farha da Mahaifin Farha suma ƴan uwan juna ne, su kuma ƴaƴan kawunai ne.. Amma Ammy da Mahaifiyar Farha Yaya da Ƙanwa ne.. Hakan yasa suke yiwa ƴaƴansu Auren haɗin gida kamar yanda aka musu.. Abbah ne kawai da zai ƙara Aure na biyu yaje ya auro ta waje wato mahaifiyarsu A'isha, nan ma ansha rikici sosai, shiyasa Abbah bai wani takura Maleekh akan wacce yake so ba.. ☆☆☆ Abokan Maleekh kuwa duk Hotel suka kama kafin washegari su wuce.. Maleekh ne ya kai Amal har gida, sai da suka taɓa soyayya kafin yayi mata sallama... A wannan ranar Maleekh bai koma gidansu ba saboda yasan idan ya koma komai zai iya faruwa.. Kai tsaye hotel ɗin da abokansa suke nan yaje zai kwana dasu.. A hotel.. Suna cikin babban suite ɗinsu, ƙamshin shisha ya gauraye ɗakin. Ga ƙamshin turare ya cika ko'ina, duk suna kwance suna tafka dariya kan labarin da suka gani a TV. Maleekh yana zaune akan katifa yana pressing phone ɗin sa alamar chat yake.. Abokin sa Samir ya ce yana dariya: “Guy, wallahi kai ka bada show na shekara. Duk social media fa labarinka ne yanzu. Wallahi trending number one!” Wani daga cikinsu, Khalid, ya ɗaga glass yana dariya: “Bro, forget about Farha. Duk wanda baya son ku, ya mutu da haushi. Amal ce take da soyayyar gaske a idanunka, kuma ita za ta baka natsuwa. Kai dai ka tsaya kan maganarka, kada kowa ya juya maka zuciya.” Sauran abokai suka kwashe da dariya suna shan shisha, suna furta kalamai: “Wallahi Amal ce ta dace da kai, ba Farha ba. Ga ta da hankali, ga ta da ladabi. Kuma gaskiya soyayyarta ta fito karara a wurin rawa.” Maleekh ya lumshe idanu yana murmushi a hankali ya furta “Wallahi ban san me yasa amma idan Amal na kusa da ni, zuciyata tana samun kwanciyar hankali… Na yanke hukunci, ita ce zaɓina.” Abokansa suka ce gaba ɗaya: “Cheers to love! Cheers to Amal!” suka ɗaga cups ɗin lemon juice suna dariya, ƙamshin shisha da kamshin turarensu yana tashi.. ☆☆☆ Amal tana kwance a gida zuciyarta cike da farin ciki da tsoro lokaci guda... NEXT NEXT NEXTTT.... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 31 to 32 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Washegari bayan shagali… Gidansu Maleekh bai taɓa yin shiru irin wannan ba, gida ya koma gidan makoki, Tun da gari ya waye nan ma ta ƙi buɗe ƙofa.. Mahaifinta sai kai kawo yake yana ta masifa. Cikin bacin rai, tinda gari ya waye yake yiwa Ammy bala'i tare da faɗin “This is nonsense! Absolute nonsense! How could your son, Maryam humiliate my daughter in public like that? In front of thousands… and even on live TV?! This is unacceptable!” Yana jujjuya kai cikin tsawa, duk falon sai rawar muryarsa ne yake tashi.. Ammy dai zaune kan kujera, idonta a ƙasa, zuciyarta cike da nadama. Ta kasa amsa wa, sai hawaye da ke makalewa a idanunta. Mahaifiyar Farha ta sa baki cikin haushin ta ce “Wallahi wannan rashin adalci ne! Ƴa ta da aka yiwa alƙawarin aure da ɗanki, amma gashi ya tozarta ta da wata a gaban duniya. Me kike tunanin mutane za su ce mana?!” Falon ya cika da hayaniya, baƙi masu kwana a gidan suna jinjina kai. Duk wanda ya ɗago tv ɗin da ke gefe, sai ya ga replay na Amal da Maleekh suna rawa tare, suna murmushi kamar an haɗa jini da jini. Ammy ta runtse ido da nauyin kunya, tana maida numfashi... Ammy cikin murya ƙasa ƙasa ta ce “I… I didn’t expect this. I only wanted peace between our families. But… things fell apart.” Mahaifin Farha ya daka tsawa tare da faɗin “Peace?! You call this peace? You call public disgrace peace?! No, Maryam, you failed us!” Ɗakin ya ɗauki shiru, sai kukan Farha da ke cikin ɗaki yana fitowa, tana ƙoƙarin karya zuciyar iyayenta gaba ɗaya. Scene ɗin Maleekh da Abokansa🥳 A babban hotel mai tsadar gaske a tsakiyar birni, an kunna AC, cikin walwala abokan Maleekh suna zaune suna ta yi masa barkwanci. Maleekh ya kwanta luf kan kujera, yana danna wayarsa da murmushi — hotunan Amal da suka yi tare kenan ke yawo a kafafen sada zumunta... Aboki na 1 yana dariya, yana busa hayaƙin shisha y ce “Kai Maleekh, you kill it yesterday, bro! That dance, that kiss, damn… you trended more than the president himself. Wallahi the whole country dey talk about you and Amal.” Suka kwashe da dariya gaba ɗaya. Aboki na 2 yana zuba juice a glass cup ya ce “Bro, forget that Farha matter. You don’t love her, and everybody knows. Amal is the vibe. She’s natural, classy, she completes your energy. Don’t let anyone force you into what you don’t feel.” Maleekh ya kalli gilashin ruwan lemo a hannunsa, ya ɗan murmusa sannan ya ce “Amal… wallahi she’s different. For the first time in my life, I feel alive. The way she looked at me yesterday… it was real. Not fame, not money, just… me.” Aboki na 3 yana dariya, yana tafa masa hannu ya ce “That’s it! Follow your heart, man. We got your back. Marry the one you love. Forget family politics.” Maleekh yana jin daɗin shawarwarin da abokansa suke bashi hakan yasa koda yaushe yake tare da su... Suka ci gaba da shan shisha, suna dariya, suna bada shawarar “ba’a ɗaure zuciya a soyayya.” PA ɗin Maleekh na zaune shima a gefe, sai ya kalli Maleekh da wani irin murmushi, da sigar dariya, ya kalli Maleekh yana cewa “Boss! What about your ɗaukan fansa akan Amal na marin da ta yi maka in public.....?..” Sai yayi shiru yana dariya ganin irin kallon da Maleekh ya wurga masa.. Zuciyar Maleekh ta buga dimmm! Wani zafi ya tsaya a ƙirjinsa. Maleekh ya ɗan harari PA sannan ya ce “What the hell are you talking about?..” Abokansa suka ji, suka ɗaga kai gaba ɗaya. Aboki na 1 da mamaki ya ce “Kamar ya ɗaukan fansa? Wani fansa?..” PA

Chapter 21 of 62