Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
lokacin da muka fara ganawa.” Ta ɗan yi shiru, hawaye suna taruwa a idonta ta cigaba da cewa. “Nasan kai ma ka shaida ni, ko da yake shekaru sun ja kafin mu sake haɗuwa.” Abbah ya tsaya yana kallonta, numfashinsa ya ɗan yi nauyi. Guntun hawaye ya zubo masa, ya share cikin natsuwa. “Tabbas Mama… ni ma ban manta ba. Amma bansan me yasa kika ɓoye kanki ba. Ganinki a haka, baki bayyana cewa kin sanni ba, yasa nima ban nuna hakan ba saboda ban san dalilinki ba. A tunani na gobarar da ta cinye abokina, wato mahaifin Amal da matarsa… har da ke a ciki, shi ne ya sa na shiga ruɗani. Ganinku a raye yasa na shiga tunani… Ikon Allah kenan.” Inna ta juyo da murmushi mai raɗaɗi, ta ce cikin sautin da ya haɗa baƙin ciki da natsuwa: “Yanzu kai ka yadda cewa ɗana abokinka da matarsa Khadija gobara ce haka kawai ta cinye su?” Abbah ya girgiza kai a hankali, yana duban Amal da ke gefe tana sauraro cike da mamaki sannan ya furta. “A’a Mama, ban yadda ba gaba ɗaya… amma babu hujja da zata tabbatar min da an sa musu gobara da gangan. Amma ki gaya min, meye silar mutuwar su? Har aka sa musu gobara?” Inna ta ɗan lumshe ido, ta saki guntun murmushi mai nuni da sirri. “Zamuyi maganar daga baya Alhaji … ba yanzu ba.” Sai aka yi shiru na daƙiƙu. Abbah ya ɗan kalli Amal, ya ce cikin muryar tausayi: “Amal, my daughter… ke baki gane ni ba ko?” Amal ta ɗago kai, idonta cike da hawaye ta ce, cikin rawar murya: “Abbah… na daɗe da ganeka. Tun lokacin da na gane Ya Maleekh shine Leekh ɗina na yarinta… amma shi har yanzu bai gane ni ba.” Abbah ya ɗan yi murmushi, yana kallonta cikin ƙauna. “Allah sarki daughter… wato baki manta Maleekh ɗinki ba kenan. Gashi, ikon Allah, kun sake haɗuwa da shi. Gaskiya, ya kamata shima Maleekh ya gane ki, yasan cewa ke ce yarinyar da yake tare da ita tun ƙuruciya, fiancé ɗinsa tun yarinta.” Amal ta share hawayen da suka sauƙo a kumatunta, ta ce cikin dariya: “A’a Abbah, dan Allah, kar ka gaya masa yanzu. So nake sai ya aure ni kafin nayi masa wannan albishir. Na tabbata idan ya sani kafin aure… to ba irin farin cikin da nake zato zai yi ba.” Abbah ya saki murmushi mai taushi, yana girgiza kai: “Wannan babban albishir ne a wajensa. Akoda yaushe, burin Maleekh kenan ya sake haɗuwa da masoyiyarsa ta yarinta. Allah ya tabbatar da hakan da alkhairi, ƴata.” Amal ta yi dariya, tare da faɗin “Amin Abbah, Allah ya saka da alheri.” Inna ta tashi tana fatan alkhairi, ta kalli Abbah: “Allah ya daɗa haɗa zumunci, Alhaji. Mun gode sosai da kulawa.” Abbah ya miƙe, sannan ya kalli Amal da murmushi mai cike da natsuwa. “Sai mun sake ganawa, ƴata. Ki kula da kanki sosai.” Yana fita, Amal ta zauna ta jingina da kujera, tana lumshe ido cikin tunani mai daɗi da fargaba a lokaci guda, ta tabbata lokaci ne da sirrinta zai bayyana nan ba da jimawa ba.. Da daddare misalin ƙarfe 11 Ƙamshin turaren “oud” ya cika ɗakin, sai ƙarar agogo da ke danna lokaci a hankali kamar yana bin bugun zuciyarta. Amal ta zauna a gaban taga, hannunta ɗauke da ƙaramin photo. Tana kallon shi, hoton da suka ɗauka da Maleekh tun suna yara, ita sanye da uniform ɗin primary, shi kuma yana sanye da uniform ɗin junior. Ta riƙe hoton sosai a kirjinta, hawaye na taruwa a idanunta, ta furta cikin sanyi: “Ya Allah… wannan shi ne Leekh ɗina…” Numfashinta ya ɗan ɗaure, ta jingina da bango tana kallon sama. Sai tunanin baya ya fara dawowa cikin kwakwalwarta kamar fim. Flashback, shekaru goma sha takwas da suka shuɗe Da yamma a cikin gidan su Maleekh, yara suna wasa a tsakar gida. Amal ƙarama ce, ƙarama sosai tana sanye da doguwar riga na kanty, ta ɗaure gashin kanta da rivon. Shi kuma Maleekh, ɗan shekara goma sha uku, murmushi da wasa ba su gushe daga fuskarsa ba. Yana dariya tare da faɗin: “Ke Amatu, ki tsaya ki gani zan iya rubuta sunanki da ƙasa!” Amal ta ce: “Ai ban yarda ba! Yanda baka iya rubutu sosai ba, zaka ɓata min suna.” Maleekh ya ce: “Ki kalli nan!” Ya ɗauki sanda ya rubuta a ƙasa “A + M = ❤️”, sai ya kalleta yana murmushi. “Gashi nan, A Amal, M Maleekh. Idan mun girma, za mu zama A + M na gaskiya, babu wanda zai raba mu.” Amal ta riƙe hannunsa tana dariya, ta ce: “Ka yi alkawari? Wallahi idan ka manta, zan faɗa wa Ammy da Mommy.” Ya ɗan yi dariya yana riƙe da hannunta sosai: “Na yi alkawari, Amatu. In na girma, sai na aure ki.” A gefe kuwa, iyayensu suna kallonsu da murmushi. Abbah da mahaifin Amal suna ta dariya suna cewa: “Wannan yarinyar taka ta zama tamkar gold a wurin Maleekh. In Allah ya yarda, idan sun girma, sai na haɗa su aure.” A cewa Mahaifin Amal... Haka nan aka ɗaura soyayya a kalma ɗaya amma ƙaddara bata bari ba... Ranar gobarar bata manta ba. Wuta ta tashi a gidan su Amal, Inna ta rungume ta tana gudu cikin duhu, ita kuwa tana kuka tana ƙiran sunan mahaifinta da mahaifiyarta. > “Mommyyy! Daddy!!!” Amma babu wanda ya amsa. Daga wannan rana, komai ya ɓace rayuwa ta canza, ƙauna ta rabu hanya biyu. Ta tashi a cikin wani sabon gari, sabon suna, sabon rayuwa. Babu Maleekh, babu Mommy, babu Daddy....... Koma wa ga yanzu Amal ta share hawayenta da hannunta, tana kallon hoton da ke hannunta. “Kai ne ka ce zaka dawo, ka aure ni… amma yanzu kana gabana, baka ma gane ni ba.” Ta ɗauki biro ta buɗe littafinta na rubutu, ta fara zana haruffan sunansa da nata a jere: A + M = ❤️ Sai ta lumshe ido, ta murmusa cikin zafin kewar soyayya: “Ko da bai gane ni ba, zuciyarsa zata tuna… zuciyarsa dole ta tuna da Amatu ɗinsa.” A hankali ta jingina kanta a bango, tana jin hawaye suna zuba amma wannan hawaye ba na baƙin ciki bane gaba ɗaya, akwai ɗan farin cikin tunawa da soyayyar da ƙaddara zata sake haɗa ta da ita a sabon zamani... Kamar yadda ta kasa bacci a wannan daren tana tunanin Maleekh. Shima a ɓangarensa. Maleekh yana zaune cikin ɗakinsa. Ɗakin da yake cike da hutu da tsari, amma a yau wani irin shiru ne ya lulluɓe shi. Ya jingina da kujera, yana kallon wani ƙaramin agogon yara da ya jima yana boyewa cikin drawer, agogon da ya rasa dalilin da yasa bai iya jefar da shi ba, duk da shekaru da suka wuce. Yanzu haka yana riƙe da shi a tafin hannunsa, yana juya shi cikin nutsuwa. Wani sanyi yana ratsar masa jiki, kamar ana busa masa iska daga wani wuri mai nisa. Ya tuna lokacin da yake zuwa junior Amal ta sanya masa agogon, duk san da yaje school da shi sai an masa dariya da cewa “Agogon yara ka sa!” Amma har zuwa yanzu ya kasa rabuwa da shi, saboda ƙaramar yarinya ce ta bashi shi. Yarinya mai fara’a, mai murmushi irin wanda yake gyara dukkanin ranarsa, amma kamanninta ya ɓace daga zuciyarsa… Sai dai hoto da ƙamshi ne kawai suka rage masa a tunani... Ya furta cikin natsuwa, muryarsa yana raɗa tamkar yana magana da iska: “Wani lokaci ina jin kamar zuciyata na sanar mun cewa zata dawo gare ni... Domin a zuciya na, na san akwai wadda na taɓa yiwa alƙawarin aure, amma wata zuciyar na sanar mun cewa ta mutu...” Ya lumshe idanu, yana jin wani irin nauyi a ƙirjinsa irin ƙiran da zuciya ke yiwa ɗayan zuciyar ba tare da kalma ba. A daidai wannan lokacin, a can nesa Amal ma ta lumshe idanu tana tunani. Zuciyarta na bugawa da irin sautin da yake kama da wanda yake buga a kirjin Maleekh. Ba su san suna magana da juna ba, amma ruhohinsu sun haɗu. Kamar iska da ruwa, kamar haske da inuwa kowanne yana jin ɗayan.. Iska ta ɗan motsa labulen tagar ɗakin Maleekh, agogon ya yi ƙara “tik… tik… tik…” kamar yana tuna masa da wani alƙawari da bai cika ba. Ya ɗaga agogon zuwa fuska, yana kallonsa da murmushi mai raɗaɗi. “Kina so na manta ki ne?” ya furta a hankali. “Meyasa bazaki dawo gareni ba? Duk da kina zuciyata amma zan sanar miki cewa zanyi aure, zan aure macen da take mun kama da ke....” Cikin wannan tunanin bacci ya ɗauke shi.. 《》《》《》 Washegari da safe, hasken rana yana ratsa gilashin window ɗin babban office ɗin CashTalk. Maleekh yana zaune a kujerarsa mai juyawa, ya jingina da baya, yana kallon taga amma zuciyarsa tana nesa, cikin duniyar da ba ta da suna.. Sai kawai ƙofar office ɗin ta buɗe da ƙarar “click”, sectaria ta shigo cikin ladabi. Tana riƙe da wata envelope, ta ce da muryar kasaita: “Sir, wannan wata ce mai nikab ta kawo, tace in baka yanzu yanzu. Ta tafi kafin in tambaye ta komai.” Maleekh ya ɗan ɗaga kansa cikin mamaki, ya karɓi letter ɗin. Ya ɗauki biro, ya tsinke envelope ɗin a hankali amma bayan ya fara karantawa, zuciyarsa ta buga! A cikin letter ɗin aka rubuta: *Assalamu alaikum masoyina na yarinta, fiance ɗinka ce me magana bayan tsawon lokaci. Naji ance zakayi aure, to kar ka manta da alkawarinmu tun yarinta. Iyayenmu sun yi mana alƙawarin aure, kuma akwai soyayya mai zurfi a tsakaninmu. Idan kayi aure ka auri wata ba ni ba, ka sani ka ci amana, kuma Allah ba zai barka ba. Ina bibiyarka akoda yaushe. Kada ka damu da ganina yanzu, akwai lokaci zan bayyana maka kaina, kuma zamu cika burinmu na aure. Nidai kamun alkawarin, bazaka auri wata ba, in ba ni ba... Daga masoyiyarka, your fiancee… 💌* Bayan ya kai ƙarshe, letter ta sulale daga hannunsa, idonsa a zazzare. Numfashinsa ya ɗan tsaya na ɗan lokaci, kamar wanda aka tsayar da lokaci a jikinsa. Ya miƙe cikin razana, ya fita da gudu daga office, har zuwa harabar campany... Ya fara magana cikin ruɗani: “Ina take?! Ina fiancee ɗina?! Ina take?! Meyasa baku riƙe ta ba lokacin da ta kawo saƙon?!” Ma’aikata suka tsaya suna kallonsa da mamaki. domin ba su taɓa ganin CEO dinsu cikin wannan yanayi ba. Daidai wannan lokacin, Amal ta iso, ta sauƙa daga napep, Ta dawo wurin aikinta tunda jikinta ya fara sauƙi bayan hatsarin motarta. Ganin Maleekh cikin wannan halin yasa ta ƙarasa da sauri cikin damuwa ta ce: “Ya Maleekh, lafiya kuwa? Meyake faruwa ne haka?” Maleekh ya juyo cikin hargitsi, idonsa ya cika da hawaye. Ya ce cikin rawar murya: “Rayuwata ce tazo har nan campany, ta aiko mun da letter amma na rasa ta! Na rasa fiancée ɗina!” Ya dafe goshinsa yana girgiza kai kamar wanda ya rasa fahimta. Amal cikin mamaki ta ce: “Rayuwarka kuma?...” Cikin ƙarfi da tashin hankali ya juyo yana fadin: “Eh rayuwata! Fiancee ɗina ce tazo! Wacce na daɗe ina jiran dawowarta! Wanda aka ɗaura alkawari tsakanina da ita tun muna yara!” Maganar ta fito daga bakinsa kamar ƙara, Ma’aikata suka yi shiru kowa kallon kowa. Wasu suka riƙe baki, wasu suka ɗauke kai. Amal ta tsaya cak! Idonta ya cika da hawaye. Zuciyarta na bugawa da sauri, kamar ana murza mata wuta a cikin ƙirjinta. Tayi tunani cikin zuciyarta: “To wacece wannan ‘fiancée’ ɗinsa bayan ni?.. Ni ce fa fiancée ɗinsa tun yarinta! Amma ban gaya masa ba har yanzu... Wacece zata rubuta masa letter ta yi amfani da sunana domin ta rikita shi?...” Amal ta ce da rawar murya: “Ya Maleekh… ni ce… ni ce” Amma kafin ta gama, Maleekh ya ɗaga mata hannu cikin takaici, idonsa a ƙasa, bai bari ta ƙara magana ba. “Ki bar ni Amal, bana cikin hayyacina yanzu… don Allah ki barni.” Ya juya, ya nufi mota, yana share gumin goshinsa cikin tashin hankali. Amal ta tsaya cak a wajen, tana kallon bayansa da hawaye masu zafi. Sai ta juyo da hankali cikin natsuwa, ta shige reception kai tsaye elevator ta shige ta kaita sama, tana fita ta nufi office ɗinta, ta kulle ƙofa, ta kifa kanta akan table tana kuka... “Har yau, har yanzu baya iya kallona da soyayya… me na masa ne haka?, ya canza mun, baya ganina a matsayin masoyiyarsa…” Cikin shiru Amal ke zaune a office ɗinta, tana kuka kamar yarinya da ta rasa uwa. Hawayenta na sauƙa a kan takardun da ke kan tebur, zuciyarta na murɗawa da zafin kalaman Maleekh. Sai kawai taji ƙofar ta buɗe a hankali. Tayi zaton wata ma’aikaciya ce, saboda haka bata ɗago ba. Sai kawai ta jiyo wata muryar da ta dasa mata tsoro da farin ciki lokaci guda. “Meye dalilin kukan?...” Tayi saurin ɗago kai. Idonta ya haɗu da na Maleekh, yana tsaye a bakin ƙofa, hannuwansa a aljihun wandonsa, yana kallonta da ido masu cike da raunin zuciya. Zuciyarta na bugawa.. Ware mata hannu yayi, ya furta a hankali: “Zo nan…” Kamar wacce aka ja da ƙarfi, Amal ta miƙe da sauri, ta ƙarasa da gudu ta faɗa ƙirjinsa. Ta kwantar da kanta a kirjinsa tana kuka sosai. Maleekh yana shafa bayanta a hankali. “Na ce meye dalilin kukan haka?” Amal cikin rawar murya ta ce: “Saboda kai… saboda kalamanka, saboda ina jin kamar kana ƙaunar wata fiye da ni…” Ya ɗan yi murmushi cikin gajiyar zuciya, ya ɗago fuskarta da hannunsa biyu, ya kalle ta kai-tsaye cikin ido. “Amal… kar ki sake kuka saboda haka. Zan aure ki. Amma ki sani idan fiancé ɗina ta bayyana… dole sai na aure ta itama. Domin ni ɗaya aka halicce ta, haka ma ita ɗaya aka halicce ni. Amma saboda ke, saboda ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba… zan aure ki kafin ta bayyana.” Amal ta tsaya tana kallonsa, zuciyarta tana bugawa da zafi da farin ciki a lokaci guda. Tana so ta ce masa ni ce fiancé ɗinka, amma ta kasa. Zuciyarta ta ce “a bari lokaci ya nuna masa gaskiya.” Da murmushi mai zafi ta ce cikin ƙaramar murya: “Na amince… tunda kai ne, ko mai zaka faɗa zan yarda.” Maleekh ya ɗan murmusa, yana jin yadda kalamanta suka rage masa nauyin zuciya. Ya ce: “Na gode Amal. Kiyi haƙuri da komai, rayuwa ce ta jirkita mana abubuwa. Amma na tabbata alkawarin da na miki zan cika shi.” “Wani alkawari?” ta tambaya tana kallonsa da murmushi. “Alkawarin cewa bazan taɓa watsar da ke ba… ko mai zai faru, komai zaki zama.” Kalaman sun sosa mata zuciya. Ta yi dariya cikin hawaye. “Na yarda, Ya Maleekh…” Suka ɗanyi shiru. Sai hancin ta da yake shakar ƙamshin turarensa, da bugun zuciyarsa da ke dukan kunnenta. Ya zaro envelope daga aljihunsa, ya miƙa mata cikin nutsuwa. “Ga invitation card ɗin bikin… next week. Ke ce amaryata, ki shirya, ki zamo matar CEO...” Amal ta karɓa da hannuwa biyu, tana kallon rubutun da ke jikin card ɗin. “Wedding Ceremony of Maleekh Abdul-Majeed & Amal Abdulsamaad ” Ta fashe da dariyar farin ciki mai haɗe da hawaye. “Bayan wahala… sai farin ciki.” Maleekh ya ce yana kallonta da murmushi mai taushi: “Ko me zai faru, karki sake barin wani ya share miki wannan murmushi.” Ta ɗaga kai ta ce: “Sai kai ne kawai zaka share mun hawayena.” Ya ɗan ɗago habarta da yatsansa, ya ce: “Da izinin Allah…” Suka yi shiru. Sai A.C da ke busa cikin Office... 《》《》《》《》 Farha ta shigo falon da idanu jajawur, tana busar da numfashi. “Yaya… dan Allah… kada ka sake sakani a cikin wannan masifar. Indai akan Maleekh da Amal ce, ni babu ruwana a ciki. Ka barsu suyi auren su, ka bar komai ya tafi cikin tsari.” Zayd ya ɗago kai a hankali, muryarsa ta yi sanyi ya ce “Yanzu kenan Farha… kin haƙura da Maleekh? Bayan duk abinda kika ce min, kin daina son shi haka kawai?” Farha ta kalli gefe tana share hawaye. “Na haƙura, Yaya. Wallahi na haƙura da shi. Wannan soyayyar bata da amfani gare ni. Ban ga dalilin da zai sa mu ƙara cin mutuncin mutane saboda kishin da babu amfanin shi ba.” Zayd ya ajiye da gilashin ruwan, ya jingina da kujera. “To, shi kenan ke kin haƙura… amma ni Farha, bazan haƙura ba. Bazan haƙura da Amal ba. Ta rusa mun duk masarautar zuciyata, ta mayar da ni kamar wani ba shi da daraja… kuma bazan bar komai haka kawai ba.” Farha ta juya da sauri tana kallonsa da fargaba. “Yaya! Me kake nufi? Har yanzu baka gane cewa Allah ne ya haɗa wannan auren ba? Ka bar komai zuwa ga Allah, kada ka ƙara lalata rayuwarka saboda ta Amal! Ga mata kala-kala sai ka zaɓa” Zayd: ya yi dariya mai taurin gaske sannan ya ce. “Kin manta da kalmar da ki ka faɗa Farha? ‘Auren Amal da Maleekh bazai taɓa yiwuwa ba’. Kin manta ke kika fara taimaka wajen rushe komai? To yanzu kin dawo kina nuna tausayi kenan?” Farha: ta durƙusa kusa da ƙafarsa, tana magana cikin tausayawa. “Yaya, don Allah ka saurare ni. Na yi kuskure, na shiga abin da bai kamata ba. Amma yanzu na gane kuskurena. Yau zan je gidansu Amal na nemi yafiyarta. Indai har ni ce sanadin rikicin da ya lalata rayuwarsu, zan roƙi Allah ya gyara tsakanin mu.” Zayd ya zuba mata idanu, yana tauna lebensa, bai ce komai ba. Farha ta ci gaba da magana cikin murya mai rauni. “Yaya, Ammy tana son ka auri Islam, ‘yarta. Ka bar Amal ta zauna da wacce zuciyarta ke so. Kada ka ƙara ninka zunubi da makirci akan rayuwarta…” Zayd ya dafa hannuwansa a goshi, yana furta cikin muryar da ke ƙunshe da ɓacin rai “Farha… kin yi rauni sosai. Kina ganin zaki iya zuwa wurinta yau, ki nemi yafiya, kamar babu abin da ya faru? Kina ganin haka zai goge komai?” Farha ta kalle shi cikin nutsuwa. “Eh Yaya. Domin babu wanda yake girma akan kuskure. Amma kai zaka ci gaba da rayuwa cikin ƙiyayya ne? Zaka dinga jin zafi a duk lokacin da ka ji sunanta ne? Ka bar komai da Allah, don ni wallahi na gaji da wannan makirci.” Zayd ya kalli ƙasa, yayi shiru na ɗan lokaci. Sai ya ce a hankali “Farha… idan kin je wurinta… kada ki faɗi komai game da ni.” Farha ta ɗan murmusa cikin tausayi sannan ta ce “Na sani. Ba zan faɗa ba. Amma ina roƙonka da ka sake zuciyarka, Yaya. Kada wannan soyayyar ta lalata maka rayuwarka gaba ɗaya.” Zayd ya kalleta sannan ya ce. “Ki tafi Farha. Amma ki sani… wannan labarin bai ƙare ba.” Farha ta miƙe, ta fita daga falon cikin nutsuwa, tana addu’a a zuciyarta: “Ya Allah, Ka kawo ƙarshen wannan fitina cikin salama.” Zayd ya rage hasken fitila, ya jingina da kujera yana kallon duhu, alamar zuciyarsa bata cikin natsuwa... Dab da mangariba sai ga Farha ta iso gidansu Amal, bayan Mai gadi ya tabbatar da bada tashin hankali tazo ba, ya buɗe mata ta shige.. Inna tana zaune ita kaɗai a falo, ganin Farha yasa ta zabura tana kallonta, lokaci guda ta ɗaure fuska cike da fushi, ta ce. “Daga fitowarki a prison har kin dawo neman bala’i? Saboda kinji wannan satin bikin masoyan ko?!” Farha ta durƙusa cikin ladabi, tana sanye da dogon hijabi, fuskarta cike da tawali’u.. “Inna ina wuni… dan Allah kiyi haƙuri, ban zo da wata fitina ba.” Inna bata ce komai ba, ta juya gefe da ɗan tsaki. Kafin su ƙarasa magana, sai ga Amal ta sauƙo daga bene tana riƙe da glass cup na juice. Idonta ya sauƙa akan Farha, cike da mamaki ta tsaya cak, muryarta cike da mamaki. “Laa Farha kece?!” Farha ta miƙe daga tsugunonta cikin sauri, zuciyarta kamar zata burtso. Ta ƙarasa wurin Amal ta rungumeta da hawaye a fuskarta.. “Amal… na yi kuskure. Na zo ne da zuciya ɗaya. Dan Allah ki yafe mun…” Amal ta tsaya cak, hannunta a bayanta, tana kallon Farha cikin mamaki. Inna kuwa tana zaune a hankali tana kallonsu, har yanzu bata ce komai ba. Amal a hankali ta furta. “Ki zauna Farha…” Suka zauna a kan kujera guda, Inna na kallonsu. Amal ta ɗan murmusa cikin natsuwa.. “Ki kwantar da hankalinki, komai ya wuce Farha…. " Farha ta share hawayenta sannan ta ce. “Na gode Amal. Wallahi na zo da niyyar samun yafiyarki. Abinda nayi miki bai dace ba. Na ɓata miki suna, na jefa ki cikin tozarci. Amma yanzu na tuba, na daina, na kuma haƙura da Yaya Maleekh. Ina muku fatan alkhairi da zaman lafiya.” Amal ta ɗan murmusa. “Ki daina kuka. Komai ya wuce, ki cire ranki akan abin da ya faru. Allah ya saka da alheri.” Farha ta ɗan duƙa kai, tana kallon ƙasi ta ce. “Amal… jiya ina so in faɗa miki gaskiya. Bazan ɓoye ba, nice na aikawa Yaya Maleekh da letter cewa fiancée ɗinsa ce…” Amal ta ɗan buɗe baki da mamaki ta ce. “Amma… ina kika san fiancée ɗinsa?” Farha ta girgiza kai sannan ta ce. “Ban santa ba. Yayana ne Zayd ya bani labarin wata first love ɗin Yaya Maleekh tun suna yara. Ya ce sun rabu lokaci guda, kuma tun daga lokacin bai ƙara ganin ta ba. Shine ya bani shawara na rubuta cewa ni ce fiancée ɗinsa, in ce kada ya auri kowa saboda har yanzu tana raye tana jira…” Ta yi shiru, ta share hawayenta sannan ta ƙara magana da cewa. “Yaya Zayd ya ce, a duniya babu macen da Yaya Maleekh yake so kamar fiancée ɗinsa, har ya ce ko Amal ba zata kai fiancée a wurinsa ba…” Inna wacce ta saurare su ta girgiza kai, muryarta ta sauya cikin nutsuwa mai haɗe da tausayawa..Ta ce “Farha… fiash (fiancée)ɗin da kike magana akanta... ita ce Amatu.” Farha ta kalli Amal da mamaki ta ce. “Ban gane ba…” Inna ta soma magana cikin zafin rai da ƙarfi, “Ai Amatu ce fiash ɗinsa tun yarinta! Maleekh da Amal sun daɗe da alkawarin soyayya, sannan sun sha bambanci na ƙaddara amma soyayyarsu ta ci gaba da numfashi har yau!.. A lokacin tana ƙarama ce sosai, shekara biyar kacal a duniya, amma ta riga ta saba da Maleekh. Shi kuwa yana da shekara goma sha uku, ɗan saurayi mai wayo da murmushi wanda yake burge kowa. Sun taso tare tamkar ‘yan uwa, saboda iyayensu abokai ne na ƙud da ƙud, musamman mahaifiyar Maleekh da mahaifiyar Amal kawaye ne, aminan juna da ke yin komai tare. Ko da yake Maleekh ya girme ta da shekaru takwas, shi ne mai bata dariya, mai kora mata karnuka idan ta tsokano su, mai bata lemo da sweet idan ta yi kuka. A gidansu Amal ake yawanci samun su suna wasa, wani lokaci kuma sukan koma gidansu Maleekh. Har ma iyayensu suka saba da cewa, “Ku dai idan kun girma, aure zamu muku, ku zama daya har abada.” Wannan magana tana nan cikin zuciyar Amal kamar alƙawari mai tsarki. Ta yi imani cewa da zarar ta girma, shi ne mijinta, shi ne abokin rayuwarta. Sai dai rayuwa ta juyo da wata fuska. Wata rana da dare, gidan su Amal ya kama da wuta. Gobara ta cinye komai mahaifiyarta, mahaifinta… komai ya ƙone. Sai ni ce nazo da gudu na ɗauke ta muka tsere cikin duhu, muna kuka, muna neman mafaka. Tun daga wannan rana Amal bata sake ganin Maleekh ba, bata sake jin labarinsa ba... Amma a zuciyarta, tana rayuwa da hotonsa, ƙaramin yaro mai murmushi, wanda yake saka zuciyarta jin daɗi. Hotonsa ta riƙe har zuwa yanzu, wanda ta gani cikin wani tsohon jakar makarantarta... Irin wannan hoton ta gani cikin ɗakinsa a manne ita da shi, shi ne ya tabbatar mata wannan ne Maleekh nata… A yau kuma, shi ne mutum ɗaya da zuciyarta ke bugawa saboda shi..." Farha ta sake baki tana kallonsu cike da mamaki, ta ce "Amma me yasa bai gane ta ba? Me yasa har yanzu yake kallonta kamar ba su taɓa sanin juna ba?..." Amal ta lumshe idanu tana sauƙe ajiyar zuciya mai raɗaɗi. Ta ɗan murmusa cikin ɓacin rai. “Rayuwa… tana da ban mamaki,” ta furta a hankali. “Mutumin da aka rubuta a zuciyata tun ina ƙarama, yau yana gabana amma bai san ni ba.” Farha ta riƙe hannunta, idanu a cike da hawaye ta ce. “Subhanallah… amma ai da kun sanar da shi da wuri!…” Amal ta ɗago kai cikin mamaki da shiru mai cike da tsoro da farin ciki lokaci guda. Zuciyarta ta yi wani irin nauyi. “Maleekh…” ta maimaita a cikin zuciya, “ko da bai gane ni ba, ƙaddara ta dawo da mu.” Ta ɗan kalli Inna sannan ta ce cikin nutsuwa.. “Inna, mu bar komai haka. Farha, ki min alkawarin kar kowa ya ji wannan magana. Iya ke kaɗai ce yanzu

Chapter 46 of 62